Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai sake dawowa gidan nan ba.
Maganar ta bata ma ta rai matuka,har ta bude baki za ta
yi magana,sai ta kuma ta fasa ta juya da niyyar komawa
ciki,ya dada tsaida ta ta hanyar fadin yaushe raban ki da
Baban ki? Dum maganar ta daki kunanta,ji ta yi komai ya
tsaya ma ta cak na dan sakanni,sanna ta kara daga kafa
ko taku uku ba ta yi ba ta ji ya sake fadin diya mace da jin
kai aka san ta,musammam na iyayen ta,amma yanda na
ki lamuran su ke kin sa ina kokon tan haka,ur father
Hajara is very ill,shin ki na neman albarka kuwa?juyowa
ta yi a hankali,dan bacin rai idanun ta har spark su ke,ta
sake bude baki da niyyar magana,sai ta kasa. Yanda ya ga
ta na kallan sa kamar kura ta ga nama,ga idanun nan na
spark dan masifa sai ta ma sa kyau,ya ma kusa manta da
bacin ran da ke tare da shi. Juyawa ta sake yi,dan gani ta
ke magana be da amfani a yanayin da ta ke jin kanta,lalle
zaman ta a gidan nan ya zo karshe! Da wannan kudiri
cikin ranta ta shige ciki. Wato shirun da ta yiwa Khalid ya
dada kona ma sa rai,shi tin da ya zo duniyar nan be taba
ganin mace da ta ke bata ma sa rai kamar Hajjo ba,nd d
more ta ke bata ma sa rai,d more he want to get close to
her saboda shez so differant,an adventure for him. Rai
bace shi ma ya shigo gidan,ganin Hajiya ba ta dukka falon
sai ya wuce dakin ta.
Ita kuwa Hajjo ta na shiga dakin ta sai ta fashe da
kuka,kuka mai ban tausayi,ta tsani Khalid har ranta
saboda ya ta kura ma ta,ya shiga rayuwar ta,tin da dai
nan din gidan su ne hade na ta ya na ta za ta yi ta koma
kumurya ta na doko sammako kullum zuwa aiki. Gashi
jin rashin lfyar Baba ma ya sosa ma ta rai,ko me ke
damun shi? Allah sarki Innar ta,sai mutuwar ta dawo ma
ta. Ta na kuka ta fara hade yan kayan ta,kan kace mai ta
hade kayan da za ta bukata tsaf,kannan magariba ta
gabato,ta dauro alwala ta yi sallah. Ta na kwance bisa
daddumar da ta yi sallah sai ga Hajiya ta shigo,ta ce Hajjo
kar dai kin yi bacci? Hajjo ta tashi ta na murmushi,ta ce
idanu na biyu Hajiya. Ganin yanda idanun Hajjon ya yi
jajur Hajiya ta ce kuka ki ke ko Hajjo? Dazu Khalid ke fada
min mahaifin ki ba lfy,na san shi ya sa ki damuwa,kar ki
damu Allah zai ba shi lfy. Hajjo ta murmusa tare da fadin
amen Hajiya,dama ina so na zo wajen ki,ina so na koma
kumurya na dan wani lokaci. Lfy? An mi ki wani abu ne
Hajjo? Ai gwara ki zauna tinda mahaifin na ki AKTH ya ke
kwance. Hajjo ta ce Hajiya dama saboda yaran yayar
tawa zan koma can din,dan ina ga ita za ta na kwana da
Baba,ni kuma ina kwana da yaran ta saboda aiki sai na ke
biyo Baban Aysha mu taho,Hajjo ta yi karya. Ba a san ran
ta ba dan sam bayanin Hajjon be yi ma'ana ba,ta ce toh
shikenan,amma dai za ki dawo ko? Nan din kamar gidan
ku ne,an dade an saba,na dauke ki ne kamar diyar ciki na.
Cikin jin dadin maganar Hajiya Hajjo ta ce na gode
Hajiya,nan din gidan ne ai,zan dawo da Baba ya sami
sauki. Hajiya ta ce toh Allah ya ba shi lfy. Hajjo ta ce
amen. Nan su ka ci gaba da hirar su kamar yanda su ka
saba kamar diya da uwa.
Washagari Khalid ya ce AKTH billing office domin biyan
bills din Baba,aka ce ai tin da sassafe aka yi settln bills din.
Sai ya ce owk ba mamaki Jabir ne. Ko da ya yiwa Jabir
maganar bayan ya duba Baba sun fito,sai Jabir ya ce
shigowar sa kenan,be ma zauna ba. Sai Khalid ya ce ba
mamaki daya daga cikin yaran sa maza ne. Indo ya kara
tambaya,da ga ganin yanda ta amsa ya san ta san wanda
ya biya din,tunanin sa ya tabbata,dan ce masa ta yi daya
daga cikin yan uwa ne aka samu aka biya da sasafe.
Khalid ya ce Allah sarki,wank mai neman albarka
ne,Hajara kuwa ta zo ta duba shi? Indo ta ce tukunna dai
amma za ta zo. Khalid ya ce toh Allah ya sa,sai ta ce
abubuwa sun ma ta yawa, Hajaran sa ce halin ta sai ita.
Uhum kawai Indo ta ce,ba dai a tone tone. Komawa gidan
Hajiya da yayi ya tadda Hajjo ba ta nan ba karamin kunci
ya shiga ba,har sai da Hauwa ta fara kokawa da al'amaran
sa,tin da su ka dawo gida ya bi ya sukurkurce,idan ya na
da damuwa ne ko kuma ta ma sa laifi ya fada ma ta,gani
ta ke kamar zugo shi ake ma,sam ya rage ba su kulawar
sa,ba ta san shikam hankalinsa na kan Hajjo ba,be da buri
da ya wuce ta zama ta shi,so ya ke Neena ta zama ta
shi,haka kuma ya sami 'ya'yan sa na cikin sa. Amma
lokacin fadawa Hauwa be yi ba,saboda haka sai ya ta bata
kowani excuse da ya zo bakin sa.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[4:26PM, 6/6/2015] AAG: [11:29pm, 6/5/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Kwanan Baba biyu a AKTH ya fara gane mutane,Diabetes
da hypertention ne su ka fara damkar sa. Bayan
warwarewar sa be da magana da ya wuce na Hajjo,bini
bini ya ce ko yaushe zan sa diya ta Hajjo a ido? Diya ta
Hajjo kaza,diya ta Hajjo kaza,musammam da ya san waye
Khalid,hakan ya na sosawa Khalid rai,ya kasa gane shin
wai menene tsakanan diyar nan da mahaifinta ta har ta
kasa zuwa ta duba shi. Sati daya yayi a AKTH ya sami sauki
sosai,ya dage lalle shi fa a sallame shi,ya gaji da asibitin.
Da aka duba aka ga zai iya tafiya din sai aka sallame shi
din,ya na ta ciwa Khalid albarka. Mudi da yayi jinyar sa
tare da taimakon Indo su ka hada na su ya na su su ka
komo gida.
Satin Hajjo biyu a kumurya,Sani ta ke biyowa,wani
lokacin kuma ta hau motar haya,musammam idan za ta
dawo. Sam zirga zirgar ba dadi dan haka kullum cikin
zargin Khalid ta ke akan takurawa rayuwar ta. Tin da ta
koma Kumurya be taba waiwayan ta ba bare ya kira ta
waya,duk da tana kokarin kau da tunanin daga ran ta sai
da ya dan dame ta,ta na dai yawan waya da Hajiya.
Zancen Inna kuwa kullum ya na ranta,ta na so ta je ta
ganta,amma ta na gudun abun da zai biyo bayan
haka,dan haka ta yanke hukuncin yin aure da Suraj ya
dawo diyar ta ta dawo kusa da ita.
Allah ya dawo da Suraj,ya na Allah Allah ya ga Hajjon
sa,ta ke fada ma sa ta na kumurya,ya ce garin mosoya ba
ya nisa,washagarin ranar da ya dawo ya kama
weekend,ya bakunci Kumurya. Duk yanda Hajjo ta so ta
sawa ranta murna da doki ganin Suraj sai da ya
gagara,amma ta yi kokarin ma sa kwaliyya,ta yi kyau
matuka dan tin zaman su a soran gidan Indo Suraj ke
yabata,ta ma sa kyau kwarai kamar ya dauke ta ya tafi da
ita inji shi. Ita ko Hajjo sai kokarin ma sa hira ta ke,da ta
so ma sa maganar rayuwar ta na baya,sai wani abu cikin
ranta ya hana,har ta yanke shawarar bari sai ya sake
dawowa wani karan ta ma sa. Zaman ta da Suraj lami
sam ba wani chemistry,har so ta ke su hada ido da shi ko
za ta ji yanda ta ke ji ta hada ido da Khalid,amma ina d
combition din sam be hau ba. Zai tafi ta rakoshi bakin
mota,ya dauko tsaraba jaka guda ya ba ta,ta karba ta na
waiwaiwai wannan duk nawa ne? Ko lefe ka fara ragewa
ne? Ya na dariya ya ce ai kin fi karfin wannan ma kin
sani,lefe kuma ai sai kin ture gimbiya. Duka su ka yi
dariya. Tsayuwar wata tsalleliyar mota da ta yi biyun ta
Suraj ce ta ja hankalin su duka,ita dai Hajjo ba ta taba
sanin mai mota irin wannan ba,so sai ba ta kawo wajan ta
ma aka zo ba.
Tin da ya shigo lungun gidan ya hangi Hajjo da wani ran
sa ya baci. Ya zo duba Baba ne,ko gidan be iya karasawa
ba ya biyo ya fara ganin Suger da yayi sati biyu be sa ta a
ido ba.Ya dubi Neena da ke kwance a baya ta na sharar
baccin ta,ya murmusa yayin da ya juya ya gyara ma ta
kwanciya,ba shakka wannan karan da ita zai yi garkuwa
ya harba wannan dan gajeran saurayin na Suger. Fitowa
yayi cikin isa da shan kamshi,ganin sa gaban Hajjo ya
fadi,shikenan ya biyo ta,Allah kadai ya san da me ya zo
kuma yau. Shi kan shi Suraj sai da Khalid ya ma sa
kwarjini saboda yanayin sa da cika ta kamala da Allah ya
ma sa. Shekarunsa 37 amma yafi kama da dan 30 saboda
baiwa da Allah ya ma sa sam baya tsufa. Sanye cikin farar
shadda dinkin tazarce,abun ku da dogo sai ta ma sa kyau.
Wajan na su ya karaso ya na kokarin sanya idanun sa
cikin na Hajjo ga wani mischievous smile din nan da ya
saba ma ta duk san da ya shiryo wata shiryayyiyar. Da
sauri Hajjo ta yi kasa da na ta ido,hannu ya ba shi,gami
da yin sallama. Suraj ya karba ya amsa da fara'ar sa. Ya
kalli Hajjo ya ce Suger ya dai? Is dat a way to great d man
you so much miss? Da sauri ta daga ido ta kalle shi,ya
kashe ma ta ido daya,duk a kan idan Suraj,ya ce ban gane
ba pls,Hajjo who is dis man? Hajjo ta ma rasa me za ta
ce,kawai ta yanke hukuncin fadan gaskiya,ta ce shi ne
autan Hajiya....kuma uban diyar ta Ameena!Khalid Ya ba
da na shi gudun mawar. Ihu ne kawai Hajjo ba ta kurma
ba,dan cikin ranta ihun ta ke,maganar Anty Hussaina ke
ma ta ihu a kunne na "kar ki bari ya ji a bakin
wani..."wanin ma kuma ya kasance Khalid shikenan yau
Khalid zai cuce ta! Hajjo ta ce wasa ya ke,as in kar ka
saurare shi,ina tuni zuciyar Suraj ta motsa,ya ce da Khalid
i beg ur pardon! Wata diya ka ke magana akai? Khalid ya
ce aw ba ta fada ma ba? Who exactly ar you? Hajjo ta ce
Suraj pls kar ka saurare shi,ka bari ma yi maganar daga
baya. Suraj ya ma ta banza,ya ce da Khalid sunana Doctor
Suraj,wanda zai auri Hajjo nan ba da dadewa ba. Khalid
ya murmusa tare da fadin nan ba da dadewa ba amma u
don't knw abt us? Ba ta fada ma ba? Me haka ya ke nufi
Suger? Idanun Hajjo na spark ta ce Khalid don't temper
wit my future,i wil nt forgive you for dat! Worry not
Suger,kawai ina taimako ne wajan fadawa saurayin ki
abunda be sani ba,am aure be san da diyar mu ba! Rai
bace da batun Khalid,Suraj ya ce pls ka fito baro baro ka
fada min abunda ka ke so ka fada. Khalid ya na
murmushi,ya nuna motar sa ya ce je ka duba bayan
motar can,amma ka tabbatar diya ta ba ta tashi ba. Suraj
ya juyo ya kalli Hajjo,ta girgiz kai ta ce ba gaskiya ba
ne,kar ka je...ya juya ya nufi motar,ko da ya leka sai ga
diya kwance ta na ta baccin ta,ya bude motar ya kalli
fuskar Neena sosai,tamkar Hajjo ya ke kallo,dan dai
wannan fara ce kuma yarinya ce shakaf da sai ya ce yar
biyun Hajjo ce! Abun da ya zo ran sa shi ne kanwar Hajjo
ce,duk da dai Hajjo ta fada ma sa ita ce auta,Allah kasa
kanwarta ce addu'ar da yayi a fili kenan,Hajjo is too
young to b her mother. Ji ya yi kamar ya tada Neena,sai
kuma ya fasa ya dawo wajan su Hajjon da tuni idanun ta
ya kawo ruwa. Hajjo ta ce let me explain plsssss Suraj.
Khalid na gefe murmushi fal fuskar shi,yau dai kam
tarkon da ya sa ta kam katan zaki ba kurciya ba. Suraj ya
ce Hajjo,tambaya daya zan mi ki,ki kuma gaggauta fada
min gaskiya,aaa ko ah ah,waccen diyar da ke kama da ke
sak,diyar ki ce? Ya Allah ka sa ta ce ah ah! Kallan Hajjo ya
ke kamar rayuwar sa depend on her answer. Hajjo ta yi
kasa da ido,ji ta ke kamar kasa ya bude ta shige ciki,abun
kadan da ya kamata ta fada ma sa tuntuni ya zama
babba. Suraj ya ce ke na ke sauraro Hajjo! Murya a kasa
ta ce eh Ameena diya ta ce...
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[11:55pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Juyawa ya yi ba tare da sake furta komai ba ya shige
motar sa. Hajjo na fadin dan Allah ka tsaya na ma ka
bayani Suraj! Tuni ya figi motar sa ya tafi. Cikin tsana
Hajjo ta ke kallan Khalid,ta ce dan me ya sa haka? Me na
tsare ma? Me na taba ma ka da na cancanci wannan
hukunci daga gare ka Khalid? Ya ce marry me,jst marry
me suger! Ni na san da 'ya'ya na cikin ki,kuma bazan bari
ba sai inda karfi na ya kare,sai kin haifa min su
Suger....kallon sa ta yi irin kallan da ake yiwa wanda su ka
sami tabin hankali,ta ce Allah ta baka lfy! ta juya ta shige
gida a fusace,ta na ji ya na kwalla ma ta kira ta ma sa
banza,ta na shiga gida ta karasa daki da gudu sai ta fashe
da kuka. Indo ta shigo da sauri ta na fadin lfy! Lfy Hajjo!
Me ya faru! Cikin kuka Hajjo ta ce Indo Allah ya raba ni da
Gatbati tin da dadewa amma yanzu ya hada ni da Khalid!
Ya matsa min,ya isheni! Na tsane shi! Na tsane shi fiye da
yanda na tsani Garbati tin da ya raba ni da Suraj.Kai
gaskiya wannan bawan Allah ya yi lefi,amma zauna bar
kukan,zauna ki bani lbry. Ba ta dena kuka ba har ta gama
ba wa Indo labari tin daga sanda Khalid ya dawo har
zuwa yau da ya raba ta da Suraj,me san ta dan soyayya
ba dan ya na so ya aure ta saboda wani bukatar shi na
daban kamar Khalid ba. Indo ta ce toh ki yarda ki aure shi
mana Hajjo,menene a ciki tin da ya na kaunar diyar
ki...bazan aure shi din ba,ni bazan taba auren mutum mai
ji da kai da dagawa irin Khalid ba! Gwara ma kar na yi
auren kwatata!!! Ba fa so na ya ke ba,kawai dan matar shi
ba ta haihuwa zai aure ni,ga machine ta haihuwa ya samu
ba! Ya aure ni ya hada ni da matar nan ta sa kamar
balarabiya su ji dadin wulakanta ni,duk lalacewar rayuwa
ta Indo na fi karfin wulakanci. Cikin tausayawa Indo ta ce
yi shiru Hajjo,ki ta addu'a da istikara Allah ya zaba mi ki
ma fi alkhairi. Hajjo ta ce babu alkhairi a tare da
Khalid...kul Indo ta katse ta,ki dai yi addua na ce,zabin
Allah ya shi ne zabi,Allah ya zaba mi ki. Hajjo ta ci gaba da
kukan ta.
Tin shigar Hajjo gida Khalid ya ja motar shi, shi ma ya je
yayi abunda ya kawo shi,wato gaida Baba,har yau ma sai
da ya tambaye shi Hajjo,Khalid ya yi mamakin ta na garin
ma amma ba ta zo ta duba shi ba? Halin Hajjo sai ita. Da
kyar Neena ta yarda Baba ya ruke hannun ta da ke Khalid
tada ita yayi da su ka isa gidan dan Baba ya ga jikar ta sa.
Ita ko Neena ce wa ta yi sam ba kakan ta ba ne,ita kakan
ta na kano,wato mahaifin Hauwa,da shi ta saba, har cikin
ranta tsoro Baba ya ke ba ta.Baba ya ce Allah sarki mai
sunan ki mutuniyar kirki,ba dai ta cutar ba sai da a cuce
ta,Allah ya ji kanta da rahama. Khalid ya amsa da amen.
Neena ce ta matsa su tafi,dan haka ba dadewa su ka juyo
abun su,zuciyatt sa cike da tunanin ko wani Hali Hajjo ta
ke?
Bayan ta sha kuka ta koshi ne ta yi kokarin kiran wayar
Suraj,amma a kashe. Ta kira ta Ayush ta ba ta lbryn
abunda ke faruwa,ta ce haba shi yasa Ya Suraj ke nema
na,ya zo da magariba ba na nan,kar ki damu zan ma sa
bayani inshaAllahu zai gane. Hajjo ta ce toh Allah ya sa.
Su ka yi sallama. Sai a sannan ta bude jakar ta,Jewellery
ne ma su kyan gaske Indian design,da kuma turare iri
iri,sai kuma takalma da pakistans na gani na fada. Hajjo
ta yi ajiyar zuciya ta re da fadin Allah sarki Suraj,Allah ya
sa ka gane,amen.
Suraj kuwa tin da ya je gidan su Ayus ba ta nan ya koma
gida ya kasa zama,abun da ke daure ma sa kai shi ne ta
yaya wannan za ta zama diyar Hajjo? Ai wannan ta yi
rabin shekarun Hajjo,ta yi yarinta a ce ta na da diya
kamar wannan,dama ba budurwa ba ce? Ta taba aure?
Toh ma ta ce Khalid autan Hajiya ne,shin ta yaya ya zama
mahaifin diyar Hajjo?me ya sa ba ta taba sanar da shi ba?
da wannan tambayoyi ya sake komawa gidan su Ayush
cikin daren,dan ba zai iya kwana ba su yi maganar ba. Ya
ko ci sa'a ta na nan. Ta ji dadin ganin sa duk da ba dan ita
ya zo ba,dan case din sa da Hajjon sa ne. Bayan zaman su
yay ta jero ma ta tambayoyi,har dai ta banbance ma sa
zare da abawa,ta bashi lbryn yanda aka yi Hajjo ta ke da
diya kamar Neena,kuma Khalid ya kira kansa ne mahaifin
Neena ba dan komai ba sai dan shi ne ke rukon
Neena,kuma ya ke san auran Hajjo.
Jikin sa ya yi sanyi ya ce amfanin bayani kenan in a
relationshp,sam boye boye be da dadi,da ta fada min
tuntuni da duk haka be faru ba,wai dan ta taba aure ba ya
na nufin zan dai na san ta ba,I love her nd i wil olways
love her. Ayush ta gyada kai ta na murmushi,duk da kuwa
maganar ta dan taba zuciyar ta,ina ma ta ji wannan
maganar da ga bakin wanda ta ke so,kuma ace da ita ya
ke,da burin rayuwar ta ya cika. Bayan yayiwa yan gida
sallama Ayush ta raka sa har mota,ya ce gobe zai koma ya
sami Hajjo,amma kar ta fada ma ta,zai ma ta suprise visit
ne. Ta na murmushi ta ce ka gaishe ta,su ka yi sallama ya
tafi ta dawo gida zuciyar ta fal da san maso wani.
Washagari Hajjo na asibiti Hajiya ta yi kiran wayar ta,ta ce
idan ta tashi ta biyo gidan ta za su gidan kanwar Hajiya su
ga wasu kayan kitchen da kanwar ta ta ta shigo da su. Da
kamar ta ce da Hajiyar ba za ta sami damar zuwa ba,sai
kuma ta guji bacin ran Hajiyar,dan ita ta tsaya tsayin daka
Hajjo ta fara siyan kayan aure tin da ta fara daukan
albashin ta,ta kuma sa Hajjo a dashi na daidai yanda
Hajjon za ta iya. Duk wata shawara ita take bawa Hajjo ita
take sa ta a hanya. ta amsa ma ta da toh,zan zo Hajiya.
Bayan aje wayar ta ce ya Allah kar ka sa na hadu da
wannan dan anacen har na je na tafi.
Kayan kitchen din ko sun mata,dan har kwasar wasu ta
yi,saboda ita ta gida ce aka ma ta ragi. Bayan dawowar su
ta aje su dakin da ta ke taro. Ta ce Hajiya bara na kama
hanyar na tafi kar dare ya yi. Hajiya ta ce jira ma na Sani
ya dawo sai ku tafi tare. Hajjo ta ce ay na zaci ya tafi,bari
na jira shi. Nan su ka zauna ita da Hajiya suna tadi,Hajjo
na cin abunci. Har ta gama shiru shiru Sani be dawo ba.
Sai Sallaman Khalid su ka ji,Shikenan gashi abun da na ke
gudu ya zo! Hajjo ta fada cikin ranta. Ba kunya kamar
babu lefin da yayiwa Hajjo ya raba ta kusa da ita ya zauna
kusa da Hajiyar sa,bayan sun gaisa Hajjo ta daure ta
gaishe shi,ya amsa,tare da fadin yar kumurya ta dawo
kenan. Hajiya ta ce ba dawowa ta yi ba,Sani ta ke jira ya
dawo su tafi,kuma na ji ma wayar sa a kashe. Khalid ya ce
wani Sani kuma da ya tafi tin bayan la'asar? Hajiya ta ce
haba dan Allah? Ya ce wlh,sai ma da ya biyo ta gida na da
ke na neme sa. Hajiya ta ce Allah sarki na tsaida
Hajjo,rashin sani. Kwayar idanun sa na rawa ya ke kallan
Hajjo da tuni ta ji komai ya gama jagole ma ta,ga shi
akwai wani file da za ta yi submitn gobe goben nan,kuma
ta baro sa a gidan Indo. fuskar sa cike da murmushin
mugunta ya ce Hajiya kar ki damu,dan dai nan da
Kumurya ai sai na kai Hajjon ta ki. Da sauri ta daga ido ta
kalle shi,ya kashe ma ta ido,ta ce Hajiya wlh na hakura
zan kwana! Hajiya ta ce wa zai kawo mi ki file din da za ki
yi submitn goben? Ta ce na kira Baban Aysha ya taho min
da shi. Khalida ya sa hannu a aljihu ya fito da waya ya ce
ga wayar Sani tare da ni,ya ji dadin girkin Hauwa ya
manta kan kujera,abun da ya kawo ni gidan nam kenan
na kawo ma sa na kuma mi ki sallama Hajiya,gome zan
leka Abuja.
Hajjo ta girgiza kai,ita dai kwanannan ba ta da sa'a kamar
ta buge bakar karya da bakar mota. Hajiya ta ce Hajjo ba
komai dare bai yi ba ai,ba a dade da kiran sallah ba,idan
kun idda sallar magaribar sai a kai ki. Toh Hajiya,amsar ta
kenan,ta tashi ta shige ciki,ta bar Hajiya na yiwa autan ta
godiya na kai Hajjo da zai yi,fadi ya ke Hajiya ai yiwa kai
ne... ni ma fa haka na gani,yiwa kai indeed.
Tin da su ka dau hanya ba wanda ya yiwa wani
magana,sai da su kusa isa Kumurya Khalid ya ce Suger?
Ta ma sa banza,ya kara da Hajara? Ta daga ido ta kalle
shi,ya murmusa ya ce ashe idanun ki biyu,na zaci kin yi
bacci. Ta ce dama za ka yi shiru mu karasa kawai. Ai na
mi ki shiru ne kar in zo na mi ki magana na kunna ki ki ce
na tsaya ki sauka a dajin,amma tin da mun kusa shiga
gari,i can open up! Ta ma sa shiru. Ya ce fushi ki ke wai
dan na raba ki da wannan gajeran saurayin na ki? A
hasale ta ce Suraj ba gajere ba ne! Khalid ya murmusa
sannan ya ce well cikin dogayen maza irina gajere
ne,cikin mata irin ku Suger ina ga shi ne za a kira shi
dogo,kai kamar ma tsayin ku daya ma fa,shi dogo ke
kuma doguwa! Hajjo ta watsa ma sa harara. Ya kara da
kina da elegant man kamar Khalid ina mamakin me za ki
yi da mutum laba laba kamar mace! Hajjo ta katse shi da
fadin ban san cin fuska! He is my husby to be! Khalid ya
dara,ya ce ba ku dace ba,you deserve someone lyk me.
Hajjo ta ce no,u ar nt my type,plus ban san ka!! Dariya
yayi mai kayatarwa,ya ce Suger Suger my dear innocent
Suger! Ban da ke da abun ki ai ba maganar so mu ke
ba,maganar making family mu ke,you don't luv me nd i
u,equation balanced,u love ur daughter nd i her,ina so na
haihu nd u need a fmly,in dat case we both need each
oda Suger... Hajjo ta murtuke fuska tare da fadin no ni
ban bukatar fmly,in ma ina bukata din ba dai da kai ba,sai
dai da Suraj...sun shigo kumurya,sun kama hanyar
unguwar su Hajjo.
Shiru Khalid yayi,daga bisani ya ce d more u try to push
me away,d more find you interesting,you ar such an
adventure in my lyf dat i can't resist Suger,so get use to it.
Banza ta ma sa,cikin ranta kuwa tafasa ta ke,ya maishe ta
kamar toy da zai na having fun da,burin shi ya takura ta a
kullum yaumin ya ji dadi,gashi Allah sai hada su ya ke.
Ganin mota fake kofar gidan Indo ya sa ta sake kallan
wajen da sauri. Ya salam! Suraj,motar Suraj ne,ai kuwa
sai ta hango shi jin gine jikin motar. Ya dade yana jiran
ta,ya kira ta ba ta daga ba,gashi waje da da nisa bare ya
ce zai je ya dawo. Allah Allah ya ke ya sa ta a idan sa,tin
bayan rabuwar su da Ayush ya ke shiraya abunda zai fada
ma ta,son ta yake ji ya na ma sa ambaliya cikin ran sa,tin
da ya ji lbryn ta ya ke tausayin ta,idan be auri Hajjo ba
gani ya ke ya yi asara babba.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[10:01PM, 6/6/2015] AAG: DIYA MACE
Ganin abun da ya dauke ma ta hankali zuciyar Khalid ta
kada,ran sa ya fara baci,wato wannan be hakura ba
kenan. Ya ja mota ya faka daga gefe,sai a sannan ta ji
karar wayar ta,kafin ta dauka ta katse,ta dubu ashe Suraj
ne,ya jima ya na kiranta ba ta ji ba,ya ma ta miss calls ba
adadi. Daga ido ta yi ta kalli inda ya ke tsaye,wayar ruke a
hannun sa. Ba shakka ya gane motar,motar jiya ce,kuma
ya gane wanda ke zaune cikin motar tare da
Hajjo,mutumin jiya da ta kira autan Hajiya ne,wato
Khalid,dama dan tana tare da shi ne ta ki daga wayar sa?
kishi da bakin ciki su ka taru su ka ma sa malulu kasan
makogaro.
Da sauri ta yunkura za ta bude mota ta na Suraj! Khalid
ya sa lock tare da fadin idan ki na san kanki da arziki kar
ki fita Hajara!ta juyo a fusace ta ce Khalid kar fa ka kai ni
bango! Ka kusa kai ni bango! Idanun sa sun fara kadawa
suna ja,lalle fadan rashin gaskiya. Rai bace ya ce ni dama
a bangon na ke,ga shawara ta kar ki fita,idan kuma

Please Login or Register in order to submit comment