Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din,i can't jst hurt you!
Hajjo ta ce gwara kin yi hurtn kan ki Ayush? For
you information,wallahi ban taba jin soyayyar Suraj
cikin rai na ba,I was doing it for u mumu! It was all
for ur sake!Duka su ka sa dariya,budurwar ce ta
kara dawowa,kafin ta yi magana Hajjo ta ce gata nan,pls a
yi hakuri. Ta ce da Ayush ina ne wajan
bikin? Ayush ya ce ta yafe ma ta wlh ga hadari ga
tsohon ciki! Hajjo ta ce wlh babu abunda ya isa ya
hana ta zuwa auren Ayush da crush,so kawai ta
fada ma ta,ta na fada ma ta,Hajjo ta taya ta share
hawayen fuskarta,su ka fito. DIYA MACE
Tin shigar ta mota Aysuh ke kokarin gayawa
angon na ta suna da babbar bakuwa,amma ina
mitar ta ki fitowa da wuri ga hadari da ya ke ta ma ta ya ki
bari ma ya ji,dan haka sai ta yi fushi ta ma sa
banza. Sai da su ka shiga su ka zauna a dakin taron
sannan Hajjo ta sami damar karasawa a na ta
motar. Har ta fito sai ta tuno alkawarin da ta tabawa
yiwa Suraj,ta ga lalle tin da Allah ya nuna ma ta
ranar,dole ta cika,dan haka sai ta dauko ajiyayyar lapcoat
din ta da ke cikin mota,ta sanya.
Tin da ta shigo ya ke kallanta,ba komai ne ya ja
hankalin sa ba sai lapcoat din da ya gani sanye jikin
ta,haka ma dayawa daga cikin jama'ar wajan kallan
ta su ke,mace mai tsohon cikin da ke rinjayar ta dan
girma,ta na taku da kyar ga lapcoat ta daura,likitocin da
su ka gane ta kuwa dariya kawai
su ke,dax Doc Hajara for them,komai na ta da
gaske ta ke yi. Suraj was lyk wacece wannan?
Maganar sa da Hajjo ce ta fado ran sa,lapcoat?
Sanya lapcoat ranar bikin sa? Mutum daya ce da
wannan aiki! Ya juya ya kalli amaryar sa da alamar
tambaya,murmushin da ke fuskar ta ya gasgata ma
sa Hajjon ce ba kowa. Kai tsaye wajan ango da
amarya ta nufa,ta isa gaban su Suraj ya dara tare da
Fadin dax Hajjo for us! kin dai sa hankalin ki ya
kwanta! Duka dariya su ka sa,da ke ya taba bawa
Ayush lbryn sanda suna shawarar irin shigar da za su yi.
Hajjo ta ce ana bikin Doctors ai ban yi adalci
ba idan na kasa cika alkawari. Suraj ya gyada kai,ya
ce yes,thank you for dat,amma you tooo heavy,ya
kamata ki koma gida kar ki haihu wajan bikin
doctors! Ayush ta ce menene ciki? Gwaggaro za mu
aje mu karbi dam bebyn mu. Duka dariya suke,Hajjo ta
tsaya tsakiyar su da tambatsatsen
cikin ta aka mu su hoto,sannan ta mu su sallama da
fatan alkhairi,zuciyar ta fari fat da annuri ta baro
wajan.
Tana shiga gida gaban ta ya fara faduwa,Khalid
jingine jikin motar Hauwa,kallo daya za ka ma sa ka
tabbatar da bacin ran da ke tattatare da shi,ya cika
yayi fam dawowar Hajjo ya ke jira,tin dawowar sa
da ya ga ba ta nan gaba daya hankalin sa ya gama
tashi,gashi ba ta daga waya. Gefe ta faka,ta fito da
fa'ar ta ta ce sannu da zuwa...bin ta yayi da kallo ya
tabbatar da lfyn ta lau,fuska tsuke ya ce ke ce da sannu ke
da ki ka fita bayan kin san na hana tsabar
ba ki san ciwan kan ki ba! Nxt tym idan za ki fita ki
aje min ciki na a gida sai ki je duk inda za ki! Ban
mukullin motar! Rai ba dadi ta mi ka ma sa,tare da
fadin ka yi hakuri! Banza ya ma ta,ya shige ciki ta
na biye da shi,sai shunan sa ta ke da baki,ta na fadin
masifaffe kawai! Da su ka shiga ciki ya juyo ya
ce mekika ce? Ta ce ah ah ba magana na ke ba!
Cikin takaici ya ce ina ma ki je? Ta ce wlh bikin
Ayush ake,yace wacece Ayush? Ta ce kai Khalid
kawar tawa ka man ta? Aysha? Ya ce cousn din
tsohon saurayin ki? Ta ce yauwa Suraj din ma ta
aura...WHAT bikin tsohon saurayin ki ka je! Hajjo ta
ce Khalid! Ina ya hau ta inda ya ke shiga ba tanan
ya ke fita ba,gaba daya ya masife ta tsaf! Kafin ya
haye bangaran sa,sai ga Hauwa ta fito ganin Hajjo
tsaye ta kuma jiyo masifar Khalid din ta ce lfy kuwa
Hajjo? Hajjo ta ce wannan masifaffan mijin na ki ne ke
masifar rashin gaskiya. Hauwa ta ce ahh ran
maza ya baci,aje a lallabo shi. Hajjo ta tabe baki ta ce
caf bar ni na ji da kai na kin ji,can ma sa,sai dai ke ki
lallabo shi din ba dai ni ba. Hauwa ta ce ah ah wane
ni,ban shiga wannan fadan Hajjo. Hajjo ta ce toh ya
je can ya karata,ina jin dan ciwo kadan,bari na je na
kwanta ko zai lafa.
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[6:42PM, 6/14/2015] +234 816 848 0287:
[2:35pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Hauwa ta ce ko dai abun ne? Tana tafiya Hajjo ta ce
ah ah,da saura dai,kawai ban jin dadi ne. Ta shige
ciki Hauwa na ma ta sannu. Da aka zo cin dinner
Hajjo ba ta fito ba,haka ma Khalid da ke fushi. Da ke
Hauwa ta san haka sai su ka ci abuncin su ita da
Neena. Sai da ta gama ta leka Hajjo,sai ta ga ta na
bacci,ta kyale ta ba tare da ta tashe ta ba. Garin yayi
baki matuka,hadari ya hadu sai walkiya,dan haka
Hauwa da Neena ma da wuri su ka yi kwanciyar su.
Cikin bacci ta ke jin ciwan na tsikarar ta sama sama,tin
tana iya jurewa kamar a mafarki,abu ya
zama unbearable har sai da ta farka,ta tashi zaune
cikin zufa,sai da ciwan ya lafa sannan ,ta duba
agogo ta ga karfe tara na dare. Tashi ta yi ta watsa
ruwa,ta sanya wata rigar ta iyaka gwiwa,ta koma ta
kwanta. Ciwan be kara motsa ma ta ba sai kusan wajan
goma,one hour interval kenan,da ta ga haka
ta tabbatar naguda ta ke,amma ta san da saura,za
ta iya kaiwa ma zuwa asuba. Sai ta saki jikin ta ba ta
kira Khalid ba,shi da ma ya ke fushi da ita ta ma
kashe wutar dakin dan ta san ba shigowa zai yi ba.
Haka ta yi zaman ta,tin tana kan gado sai ga ta ta sauko
kasa,wato ya kara motsa ma ta kenan.
Khalid kwance bisa gadan sa,ya na so ya kaurace
Hajjo yau dai daya,amma abu na so ya gagare shi.
Kamar wanda aka kira ya tashi da sauri,ya sauko
sai gashi bakin kofar dakin Hajjo. Ya bude kofar a
hankali,ganin wutar dakin a kashe ya san ta yi
bacci,amma idanun sa na matukar san ganin ta duk
da ita mai laifi ce. Dan haka sai ya shiga
dakin,makunnin wuta ya danna,haske ya gauraya
a dakin,ga mamakin sa gadan na ta ba kowa,ya na
tunanin ko ta shiga bandaki,ya nufi bandaki da
niyar kwankwasawa,sai ya hange ta can gefe,zaune dai dai
bisa carpet,da sauri ya karasa
wajan ta yana Suger ya dai? Ta na murmushi ta ce
labour na fara. Ya ce ya salam! Ya ba ki kira ni ba!
Bari na kira Hauwa mu tafi hsptal! Ta yi saurin ruko
hannun shi ta ce da saura,pls ka dan barta
tukunna,ina ga sai ma zuwa asuba zan haihu. Kallan ta
yake kamar ma neman gaskiya daga
fuskar ta,daga bisani ya ce tun yaushe ki ka fara jin
ciwan? Ta ce tin dawowa ta gida. Ya ce da hadari
Hajara,tin kafin ruwa ya sauka mu je asibiti. Ta ce
blv me da saura Khalid. Sai da ya dan yi
tunani,sannan shi ma ya zauna kusa da ita,ya janyo ta
jikin sa. Bini bini sai yayi kissing kumatun ta,ko
hannu ko wuyan ta. Can ya ce Hajara? Ta ce ummm
ta yaya za mu gane kin kusa ne mu tafi? Ba ana
gwadawa ba?ya ake yi?da me ake yi?
Da ke ciwan ya lafa sosai,kamar ba ita ke yi ba,sai ta
murmusa ce ita diya mace in tana labour abin da ake fara
dubawa shine wannan hanyar da dan
yake futowa aga yana budewa to in ya na
budewa,budewar shine Cervical dilation ko
Dilatation of cervix,sai a gwada hw many Cm ta
ke,yatsa daya shine 2cm,biyu 4cm,uku 6cm,hudu
8cm, biyar kuma 10cm. Idan diya mace tana 2cm xata
iya kaiwa 6hrs bata haihu ba, Idan taje 5 still
she is on the way xata Iya taking 3hrs kafin ta
haihu, It depends on multip ce ko primid, In primid
ce xata dade saboda itace haihuwarta ta farko, In
multipce baxa takai hrs din primid ba saboda
tataba haihuwa,kamar ni kenan, Buh duk inda akaje 8
haihuwa taxo kusa xata iya haihuwa
within 30mint, In kuma akace fully dilated dax
10cm tofa yanxu xa aga kan da.
Khalid ya ce yaya kenan ke da ba wanda zai iya
dubawa? Ta ce kar ka damu,na riga na kintati
lokaci base on yanda ciwan ya ke tashi. Shiru su ka
yi,daga bisani ya ce yaushe raban ki da abunci? Ta
ce kafin na fita na ci. Ya ce kin dade,bari na samo mi
ki,ta ce noo i can't eat,bazan iya ba,ka dai bani
black tea,shi zai iya keeping dina strong,ya ce owk
ina zuwa ya fita jiki na rawa,sai gashi ya dawo
dauke da flask din ruwan zafi,ya hada ma ta tea din,ya
dawo ya dada jawo ta jikin sa,ta na sha suna
dan hira. Tin suna jin saukar yayyafi sama
sama,tuni ruwa ya tsuge kamar daga bakin
kwarya,Khalid ya ce Allah ya taimake mu ruwan
nan ya tsagaita san da za mu fita. Ta ce amen amen.
Sai da ma ta manta shaf sannan ciwo ya dawo,mara ta
fara juyawa,ta damki hannu Khalid, gaba daya ya
kideme sai sannu Hajara,sannu sannu Hajara,me
zan yi? Me zan mi ki na rage mi ki ciwo? Baki cize ta
dafa bayan ta,ganin haka sai ya fara shafa ma ta
bayan,sai sannu da surutai ya ke kamar shi ke jin
ciwan ma. Can kuma kamar abun iska sai ciwo ya
lafa,yayi hugn din ta gam daga zaune,ya na da ana
daukewa da na dauke mi ki suger,I love you soo
much! Ita dai uhum kawai ta ke cewa,ita ta san
abunda ta ke ji. Haka su ka kusan raba dare,ciwo
ya tashi ya lafa,tin yana after one hour,ya dawo
40mnts,30,25,20.....wajan uku da rabi sai fa abu yazo
gangaganga,gashi ruwa ake sosai,ba karamin
tashin hankali Khalid ya shiga ba. Da gudu ya taso
Hauwa,tare su ka dawo kan Hajjo,gwara Hauwa
atlest yayar ta Zeena ta taba haihuwa a gida dan
haka ta na dan san kadan daga yanda za ta yi.
Khalid ya kira wayar Jabir ba adadi amma saboda ruwa
wayan be shiga,haka na matar sa. Gani ya ke
laifin sa ne da yarda da maganar Hajjo,da sun tafi
asibiti tuntuni da tuni hankalin su kwance.
Carpet mai kamar leda Hauwa ta shimida gaban
Hajjo,Khilid ya ce me ki ke yi haka? Asibiti fa za mu
kai ta! Hauwa ta ce cikin ruwan nan? Kan mu karasa ta
haihu,dubi kafar ta ka ga! Wani farin
ruwa ne mai jini jini ya ga na bin kafar Hajjo,ta ce
wannan zaki ne ke fita,daga shi sai faya,sai kuma
kan da fa! Khalid ya ruko hannun Hajjo da ta ke ta
nishi,ta na wayyo,wayyo,Hauwa ta ce addua
Hajjo,summas sabila yassara! Summas sabila yassara!
Caraf kuwa sai ta kama,tin tana fada a
hankali,har ta fara fada da karfi. Idanun Khalid cike
da kwalla,ya ce Hauwa ki taimaka min! I can't bear
this! Hauwa ta ce ka fita kawai Khalid,ya tashi zai
fita,wani ihun da Hajjo ta yi sai gashi ya dawo da
sauri ya na sannu! Sannu Hajara! Haka mata ke yi! Haka
Hajiya ta ta yi? Hauwa Hajara ta jigata! Wanda
be daraja uwar sa ba yayi asara!
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[2:55pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Hauwa ta ce taimaka mu sa ta on her kneels,ga faya
ta fashe,na kuma ji kan da, Ko da ya ga yanda Hajjo
ke zufa,tana cize lebe kamar za ta gatsa,sai ya tashi
a gigice ya na fadan i can't take it,I can't take dis! A guje
ya fice ko takalmi be sanya ba,haka ya fita
cikin ruwa ya tada mai gadi ya bude ma sa gate,sai
gidan Jabir.
Da fitar shi,Hauwa ta ce da Hajjo yi nishi,yi nishi
Hajjo da yardar ubangiji! Hajjo ta ce dallah kyaleni!
Ba zan yi ba! Ba zan iya ba! Wayyo Inna! Allah ka ji kan
Inna ta! Wayyo Inna! Allah ka gafartawa
Inna...wayyo summassabilayassara! Innalillahi!
Wayyo Allah! Hauwa ta ce ga kan dan ki,yi nishi! Ai
kuwa da yardar ubangiji wani karfi ya zowa
Hajjo,ta nisa da karfi sai ga katan dan ta ya sullubo
mai kama da Khalid sak,har tsayin! Tuni ya fara callara
ihu Hauwa ta yi saurin riko shi,Allahu akbar
Khalid ya yi da. dan murna hawaye wiwi ke zuba
daga idanun Hauwa,ji take kamar ita ta haihu,ta aje
yaro a gefe ta ce saura mabiyiya,sa hannu mai za ta
ji? Cike da mamaki ta ce Hajjo..Hajara...wani kan ne!
Ai kuwa sai Hajjo ta fashe da kuka,ta ce kumamawa?na
baki wlh,dan Allah na baki,wlh
bazan iya ba,bazan iya haifo shi ba! wayyo Inna ta!.
Hauwa ta ce na gode,amma sai dai kimin addua ni
ma na haihu dan bazan iya haifo na cikin ki ba,ke
kadai za ki iya,yi nishi ya fito. Hajjo ta ce na mi
ki,Allah ka sa Hauwa ta haihu,Allah ka sa ta haihu,Allah ka
sa ta haifo har na ciki na! Hauwa ta
murmusa,cikin lallabi ta ce Allah ya amsa,amma sai
kinyi nishi,Hajjo ban yi nishin ba! Ke ki yi nishin
mana! Dallah ki barni na ji da abunda ke damu n!
Wayyo Inna,karfi na ya kare,Hauwa ta ce
daure....da karfi duk da dai be kai wanda ta yi na fari ba,ta
nisa,sai kuwa subul na biyun ya fito
wanda be da bambamci da na farko! Ya na fitowa
shi ma ya callara na shi kukan,tuni mabiyiyi ta biyo
sa,ba kari sam ba ta karu ba,nan ta kwanta ta na
mayar da numfashi,Hajjo mai kuka sai gashi ta na
murmushi. Hauwa ta ce Khalid sak mu ka samu har su
biyu,ya zan yi na yanke cibiyar? Daga kwance
murya shake tana mayar da mumfashi Hajjo ta ce
duba cikin waccan drawer akwai saban reza da
zare,ki dauko. Jarirai na kuka Hauwa ta
dauko,Hajjo ta ce awna da danyatsan ki na
tsakiya,daidai tsayin za ki yanke,sai ki daure karshen da
kyau,in be dauruba jini zai zo yana
zuba tawajan.
Yanda ta gwada ma ta,hakan ko Hauwa ta yi,ta
nade su cikin shalw,ta ba ta daya ta bashi
nono,sannan ta fara gyaran wajan. Kafin Hajjo ta
shiga wanka sai da ta ba su nono dukkan su,sai dai
wannan karan ma tana wannan ciwan cikin kamar
na haihuwar Neena.
Ruwa ya tsagaita sai yayyafi,da ke asuba ta yi ,an
fara kiraye kirayen sallah,tana wanka Hauwa zaune
da babies sai ga Khalid jike jagab,Jabir biye da
shi,shi ma din ya jige amma ba sosai ba. Ganin jarire har
biyu Khalid ya rikice,gashi jike ya ke ba damar
dauka,hugn din Hauwa yayi, fadi ya ke
dukwannan nawa ne? Alhamdulillah ka ga kyautar
Allah,da ya tashi bani sai ya bani biyu!!! Jabir ya ce
dama yanda cikin nan kamar tulu ya kumbura sis
dina ai sai dai biyun!Ya Hajaran ta ke? Hauwa ta ce lfy
lau,sai dai ciwan ciki,Jabir ya ce yea dama wasu
na yi,PCM ya kamata a mata,da an yi mata allurar za
ta sami sauki inshaAllahu,idan gari yayi haske sai
kawai ku kai ta hosptal dan duba su da
kyau,haihuwan gidan nan ban fiya san shi
ba,gaskiya ka yi sakaci,Allah kuma ya kawo da sauki. Toh
toh toh Doctor!ahhh ai bazan sake ba!
Khalid ya fada cikin murna. Hauwa da Jabir dai uziri
kawai su ka ma sa,Gaba daya a rude ya ke,ya kalli
wannan sai ya dawo ya kalli wannan,ya daga waya
ya kira Hajiya,ita ma Hajiya murnar gun ta kamar ta
fito ta wayar,cewa ta yi gari na haske za su ganta.
Masallaci su ka tafi,kafin su dawo Hajjo ta fito ta
shirya tsaf. Hauwa ke ba ta lbryn kyautar da ta ma
ta tin kan ya fito duniya,har da gwada maganar ta
Hajjo. Dariya su ke sosai,har Khalid ya shigo,ya na
mata murmushi cike da kauna,ya ma manta Hauwa
na wajan ya jawo ta jikin sa,Hauwar ta shige bandaki ta
wayance da wanke hannu,shikuwa
Khalid hugn matar sa yayi gam,sannan ya bi
fuskarta da kiss ta koina,ya na na gode maman yan
biyu,na gode na gode. Jabir zai iya shigowa ya gan
ki? Ta ce eh bissimillah. Sai da ya shigo da Jabir
Hauwa ta fito. Cikin nuna kulawa su ka gaisa. Khalid ya
dau babban dan sa,ya zauna kusa da
Hajjo ya ce Suger da wani suna zan ma sa huduba?
Ta kalli Jabir sannan ta ce sunan yaya na,ka ma sa
da suna JABIR! Farin ciki da alfahari su ka bayyana
fuskar Jabir,sai gyada kai ya ke. Khalid ya ce toh
Khalid ya haifi Jabir kenan! Sai a yi din. Duka su ka sa
dariya,yayiwa yaran huduba da Jabir,Jabir ya
karbi takwarar sa,Khalid ya karbi na biyun,ya ce
wannan fa? Sabir ne? Hajjo na dariya ta ce wannan
kuma sai dai ka tambayi maman sa,baki bude
Khalid ya ce wata maman ta sa kuma? Hajjo ta ce ga
ta kusa da kai. Ya juya ya kalli Hauwa,sai murmushi ta
ke,ya ce ta yaya ki ka zama maman shi? Hauwa ta
ce tin kafin ya fito aka min kyautar sa ai,kai amma
Hajjo daban ki ke,da gaske ni zan zaba ma sa suna?
Hajjo ta gyada kai,Hauwa ta ce toh a sa sunan Baba
na,Abbakar. Khalid ya gyada kai,ya ce madallah da
Baba,ya ma sa huduba da sunan Baban Hauwa,shi ma ya
ce da ya sani ya tsaya da kila ta haifi uku,shi
ma ya sami na shi. Da wasa da dariya ya raka Jabir.
Ya dawo ya tadda Hauwa da Neena wajan
Hajjo,murna ya cika Neena,atlast! Ita ma ta na da
kanne. Hauwa ce ta janye ta,su ka fita suna jin ta ta
kira baban ta tana Baba an sami karuwa fa,na haifo
takwarar ka! Sai murna ta ke!
Khalid ya janyo Hajjo jikan sa,ya ce ba fa ko
dayaushe za ki na ba su nono su ta tsotsa ba,daga
ganin yaran nan tsotso za su yi! Hajjo ta ce toh idan
ban ba su ba me zan yi da shi? Kayya! Me za ki yi da
su? Ai nawa ne! Bazan barai su lalata min mata ba! Hajjo
ta ce Ah wannan ai child abuse ne!! Ya ce eh
na yarda,in kin ga dama ma kira ni Child abuse in
dai kan wannan ne zan amsa! Duka dariya su ke,ya
ce kara kara dai in dai kara ce sai DIYA MACE! Ya
bazan so ki ba? I love you big. Ta ce hw big? Ya ce
bigger nd larger than lyf. Ya fara kissing din ta,babies su
ka callar kuka a tare,ya dago da sauri
ya na nifa ba za a matsa min ba!kar fa a bata min rai
na!! Hajjo na dariya ta ce me aka ce da maza??
Takura indai irin wannan yanzu ka fara gani! Ba dai
ka zama Baba ba? Wlcm to d system..........!!!!
"Every female is an angel Don't west tym in selecting
Unique,instead spend tym in
Undstanding them........"
ALHAMDULILLAH
TAKU KHADIJĂ€ SIDI
Dan Aunty


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment