Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ka
fita zaki sa na yi abunda daga ni har ke za mu yi
danasani,i tell you! Rai bace ta ce zan fita,ka yi duk
abunda ka ga dama,idan har abunda ka yi jiya be hana
Suraj kara zuwa waje na ba,to babu abunda za ka yi ya
hana shi,no way! Ya saki murmushi tare da fadin way!
Yayinda ya bude motar,ya ce as u wish. Ai kuwa sai ta fita.
Khalid ya girgiza kai tare da fadin dax it! Da ba ki fita ba
Hajjo,wit d feelings am having ryt now,I don't knw wat
am capable of.
Fitar ta ta karasa wajan Suraj ta na dan Allah ka yi
hakuri,ban san za ka zo ba. Rai bace ya ce wayar ki fa? Me
ya sa ba ki dagawa? Ta ce wlh ya na jaka ban san....ganin
Khalid gefen ta,ya sanya hannun shi cikin na ta ya sa ta
daskarewa,za ta fincike da karfi sai ta yi tuntube,da sauri
ya dago ta ba tare da bari Suraj ya gane tuntuben ta yi
ba,ya hada ta da jikin sa,ya yi hugn din ta kam a jikin shi.
Daga ita Har Suraj ba wanda be yi mutuwar tsaye ba!
Kwakwalwar ta daskare,ji ta yi kamar zuciyar ta ta daina
bugawa...ta yunkura da niyar kwacewa,Khalid ya ruke ta
kam,ya kalli Suraj ya ce she mine,stay away! Suraj ya
gyada kai tare da fadin na gane,kar ka damu,ya juya zai
shige motar shi,Khalid ya saki Hajjo ta daga hannu ta
sauke kan kuncin shi,ji ka ke tas ko motsawa be yi ba.
idanun ta na spark sanna ta bi bayan Suraj da tuni ya
shige motar sa,ta ce Suraj dan Allah,dan Allah fito ka
saurare ni! Duk da idanun sa sun yi jajur,sam ba ya gane
komai sai ya murmusa,ya ce bazan iya ba Hajjo,idan har
zai iya mi ki haka a gaba na,Allah ya kadai ya san me zai yi
a bayan ido na,ni namiji ne mai kishin kan sa da abunda
ya ke so,na barki lfy,wish you d best in lyf! Ya tada motar
sa,ta na Suraj! Suraj! Suraj!! Ina hankalin ya yi gaba,ba ko
waiwaye ta na ji na gani ya fita daga rayuwar ta. Ta juyo
ga Khalid da ke jingine jikin ta sa motar,ta ce Khalid na
tsane ka fiye da tunanin ka,na gode da gudunmawar da
ka bani a matsayi na na diya mace! Ta juya za ta shige
cike,ya biyo bayan ya da niyar dakatar da ita,amma ina ta
shige da sauri. Ya yi aiken yara har ya gaji,gashi wayar
Sani na wajan sa bare ya kira shi,dan ya san tabbas Sanin
ba ya nan ne,da ya na nan aiken da ya ke ta mu su da tuni
ya fito. Da wannan ya juya ya koma kano,ran sa shi ma
ba dadi ganin halin da Hajjo ta shiga.
Wata daya ba Suraj,duk yanda za ta yi ta ji daga gare shi
ya yanke. Ta yi kokan har ta gaji,ita bakin cikin ta zubar
ma ta da mutunci da Khalid ya yi a gaban Suraj,ya ma zai
yi ya ma ta haka,Khalid da ko hannun ta be taba kokarin
rukewa ba yayi hugn din ta gaban wanda ya ke san ta,ya
ke so ya aure ta tsabar shi bai da adalci! Kamar Suraj din
shi ma Khalid raban ta da shi wata daya kenan,ya raba ta
da me san ta ba dole ya dauke wuta ba! Abunda Hajjo ke
fadi kenan duk sanda ya zo ranta,gashi kuma ya na yawan
zuwa din. Ta yanke shawarar yin aure da gaggawa ta
karbe diyar ta ko Allah ya raba ta da Khalid ta huta.
Bangaran Khalid kuwa karfin hali kawai ya ke,so dayawa
ya kan dauki mota yayo hanyar kumurya sai ya kai rabi
sai kuma ya sake shawara ya dawo. Ko hanya ba ta hada
sa da asibiti ba sai ya san yanda yayi ya yi zagaye ya biyo
ko Allah zai sa ya sa ya hadu da Hajjo. Har cikin ransa
missing din ta ya ke,missing din kallan ta,kamshin ta da
uwa uba fadan su. Wani sa'in shi kadai sai a ganshi ya ma
murmushi har dariya ma,toh ya tuno wata rigimar ta sa
da Hajjo,hatta randa ya fara ganin ta tana fada da dan
adaidaita akan naira hamsin ya tuna dariya ya ke sosai,it
appears dat Hajjo ta shiga rayuwar sa. Ba kuma mai
yawan tado ma sa da Hajjo kamar Neena,da ta yi wani
abu ko be yi niyar tuno Hajjo ba sai ya tuno ta,kan ka ce
mai sai ga Khalid ya fara fita hayyacin sa,hankalin Hauwa
ya fara tashi dan ta kasa gane me ke damun mijin na
ta,har ta fara zargin ko rashin haihuwan ta ne,ita ma ta
fara daga hankalin ta,ta zaunar da shi tai ta ma sa kuka,ya
ce kar ta damu,ba komai amma ta ki ji,sai kawai ma ta kai
korafi wajan Hajiya. Hajiya ta yi kiran sa,su ka sa shi a
gaba ita da Jabir a lalle sai ya fada mu su damuwan
shi,Hajiya ta ce ji fa har ya fada,ko wani abu Hauwan ta yi
ma ne? Khalid ya girgiza kai ya ce lfy lau fa,ita dai ta damu
kan ta,na fada ma ta ba damuwan ta ba ne! Jabir ya ce ya
za ka ce damuwan ka ba zai zama na ta ba? Shez ur wife
bro.
Hajiya ta ce Khalid,na san da akwai da abun da ke da mun
ka,hakan nan ba za ka fada ka ramr haka ba,let d cat out
of d bag!ya kalli Jabir,ya ce Hajiya ya dan ba mu
wuri...Jabir ya ce ku ji mara kunya,ba in da zani,Hajiya ta
ce ka dan ba mu wurin ma na Jabir,Jabir ya ki
motsawa,ya ce ai damuwar Khalid shi ma damuwar sa ce.
Da dai su ka ga da gaske be motsawan,Hajiya ta ce Khalid
ya yi hakuri ya kyale sa,ya fadi damuwar sa. Khalid ya dan
sunkuyar da kai saboda nauyin abunda zai fita da ga
bakin sa,ya ce Hajiya wlh kan maganar Hajara ne......wato
wani irin dariya Jabir ya sheke da,har da mingirowa daga
kan kujera!,ita kan ta Hajiyar daurewa ta yi ba ta yi na ta
dariyar ba,ta fara yiwa Jabir fada ka ga yayan
banza,menene abun dariya?.dole ya ce ka bashi wuri.
Khalid ya murtuke fuska,dan ya san za a yi haka. Jabir na
kwalla tsabar dariya ya ce Khalid yau kuma ina tunkaho
da ji da kan na ka? Ina kuma takamar? Nan fa ce min kayi
da ka fada ma ta murna za ta hau,ai ni da na ji shiru na
zaci an gama magana,ashe kanina na nan ya na garuwa!
Khalid ya ta shi a fusace zai fita,Hajiya ta dakatar da shi,ta
ce dawo ka zauna,shi ya kamata ya fita,idan ba za ka
bashi shawara ba ka tashi a sauka lfy. Da kyar ya iya daina
dariyar. Hajiya ta ce ba na so na sa baki zancen nan na ku
da Hajjo,shi ya sa ka ji na mu ku shiru,amma yanda za a
yi yau ka sake komawa,ka gwada shawo kan ta,idan ba ta
yarda ba,sai mu sa baki,ko Jabir? Ya na murmushin
mugunta ya ce haka Hajiya,ka je ka lallabo child abuse
din ka,ka kwantar da kai,ba wai ka je da gadara da jiji da
kai yanda ka saba ba,kila ka shawo kan ta. Duk da dai ta
shakiyanci ya ke maganar,shawarar ta yiwa Khalid,ya
tashi da sauri ya na fadin yanzu hudu na san ta na kan
hanyar komawa,bara na yi sauri na shirya na tafi,ya fita
da sauri,ya na jiyo dariyar Jabir,shi abun ya ma sa dadi.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
DIYA MACE
Har in da za ta sami mota Ayush ta sauke ta,ta na dada ba
ta baki akan halin da ta ke ciki. Hajjo ta ce ba komai,ta so
dai in ma rabuwa za ta yi da Suraj suyi na girma da
arziki,ba irin wanda su ka yi yanzu ba. Ayush ta ce kar ta
damu,a hankali zai gane. Su ka yi sallama,ta hau motar da
zai kai ta kumurya. Da ke a tasha ta sauka sai da ta kara
hawa wata motar,ta sauke ta a titi,ta tako dumin
karasawa gidan Indo. Ta wuto ta wata majilasar yan
zaman banza,suna ganin ta su ka fara maganar ta kamar
yanda su ka saba duk sanda ta gifta ta wajan,wani ya ce
ummmm ga fa iyayen boko,wa zai ce wannan diyar garin
nan ce! Gaba daya sai saura su ka sa baki a ka sa Hajjo a
faifai,cikin su har da Nuhu abokin Garbati,sam ba ta lura
da shi ba. Takalmi ya sa bi bayan ta,ya ga gidan da ta
shiga ya tabbatar Hajjon ce da gaske sannan ya juya da
sauri sai gidan su Garbati. A kofar gida ya tadda shi,ya yi
dakal dakal da shi,ga kazanta ga talauci,ga rashin
haihuwa,ya yi aure auren har ya gaji amma shiru be sake
samun haihuwa ba,sai ma mata da ya ke aure mai nakada
ma sa na jaki duk sanda be kawo na cefane ba,Iyalle da
Baba kadai ke iya cetan sa. Yanzun ma tunanin inda zai
samu na dare ya ke Nuhu ya zo ya tadda shi.
Bayan Hajjo ta yi wanka ta na cin abunci sai ga yaro ya zo
ya ce wai ana sallama da Hajjo,ni kuma? Kai ka ce ba ta
nan. Indo ta ce ba a haka Hajjo,ko lekawa ne ki yi mana ki
ga wake sallamar,je ka ce ta na zuwa. Rai bace ta cire
hannu daga abunci,tuwo ne miyar yauki,ta wanke
hannu,ta yafa mayafi ta fito. Lekowar ta ta yi arba da
Garbati da Nuhu. Cikin mamaki dan ta gane su sarai ta ke
kallan su,shi kuwa Garbati sam be gane ta ba,zubewa kasa
yayi ya na Hajiya ina wuni? Nuhu ya dan bige shi tare da
fadin kai dallah tashi Hajjon ce fa,dallah Hajjo ce,gane ta
ne ba ka yi ba! Garbati ya tashi da sauri ya na aw aw ashe!
ya kalli Hajjo da kyau ya ce yasin ita ce,Hajjo ai kin zama
kamar diyar yan birni shiya sa ban gane ki ba!
Murmushin ta kaici ta saki,ta ce lfy? Garbati me ya kawo
ka guna? Garbati ya ce eh na'am? Nuhu ya zingure shi.
Sannan ya ce dama dai kin san saki daya na mi ki,na zo ne
mu sasanta mu gyara auren mu ko kuwa ki bani diya
ta......dariya Hajjo ta sa,har ta kusa kwarewa,Garbati ya ce
yo menene abun dariyar? Kar fa ki bata min rai na! Ta na
dariya ta ce ko ba ran ka ba? In yayi dubu toh zai
dauwama a bace Garbati! Tin dosowar Khalid layin ya
hangi Hajjo tsaye tare da wasu,har zai fara kunar rai sai
ya ga wasu almajirai ne ma,ba shakka sadaka su ka zo
nema,sai ya saki ran sa ya faka motar ya fito. Tin da Hajjo
ta ke ba ta taba farin ciki da ganin Khalid ba sai yau,ya fito
tas da shi cikin farar shadda ta sha bugu da guga,dinki
boda an masa aikin sama da shudin zare,ga wani shudin
hula da ta sha kari ya sanya ta a karkace,ga takalmin sa
shudi,hunnun ruke da mukullin mota ya karaso wajan su
Hajjo,tuni kamshin sa ya maye su,su kan su su Garbati
sun kiyaya. Ta kasa dauke ido da ga kallan shi,ya ce Suger
yanda ki ke kallo na.... kar ki damu i miss you more!ya
kashe ma ta ido. Ta dauke kai ta na fadin in ba ka yi fariya
ba ba sunan ka Khalid ba. Murmushi yayi tare da fadin na
zo mi ki da magana mai muhimmanci yi sauri ki sallame
su,taimako su ka zo nema gurin ki ko? Ya sa hannu a
aljihu ya fito da dubunne farare kal ya ce nawa ku ke
bukata bayin Allah? Ganin kudi makudai hannun Khalid
tuni hankalin su ya tashi,Garbati ya ce eh na'am diya ta
na zo karba,diyar ka? Khalid ya maimaita,ya kalli Hajjo ya
ce Suger kin kuma fara ruke diyar mutane? Turo ma sa
diyar ta sa ma na ya kama gaban sa,if u realy need a
daughter dat much da kin fada min na kawo mi ki Neena.
Hajjo ta murmusa tare da fadin ai Neena ya ke nufi!
Khalid ya kalli Garbati ya ce kina nufin wannan local
champion din is ur.....ex- husband ta karasa ma sa. Sai da
yayi dariya mai isar sa,sannan ya ce amma Allah ya isan ki
Suger. Ya mayarda kudin sa cikin aljihu,Nuhu ya hadiyi
yawan bakin ciki ganin komwar kudin,Khalid ya ce kun ga
wannan? Mata ta ce! Karo na farko da ya kira ta mata ta
ba tare da ta musa ba. Ya kuma ce diyar da ka ke magana
akai,tin shekara gomashabiyu da su ka shude ta zama
diya ta. Ran da na sake ganin ku anan sai na sa an kama
mun ku,an kulle am batar mun da ku! Abun ku da yan
kauye tuni su ka tsorata,dama ga damin kudi sun gama
gani hannun Khalid ba mamaki ma su ne masu kasar.
Garbati ya ce ba ma sai an kai ga haka ba,bara mu tafi,ya
ja Nuhu,su na dan yin gaba Nuhu ya fara sirfa ma sa
masifa,wai ai gashi ya mu su asara,mai makon ya hakura
su zauna a almajiran da Khalid ya yi zato,ko ya ce a ba shi
wani abu ko a bashi diyar sa,yanda su ka yi za su fada. Shi
ko Garbati ganin yanda Hajjo ta koma,ga kuma wanda ke
kiran kansa mijin ta ne ya kashe ma sa jiki,wai yar Hajjon
sa da ya sani a matsayin matar sa,Allah kenan! Allah
kenan! Allah kenan! Abunda ya ke ta maimaitawa kenan.
Bayan tafiyar su Hajjo ta ce me ya kawo ka mallam?
Khalid ya murmusa ya ce is dat a way of sayin thank you?
Ta ce thank you for wat? For saving u from dat local
champoin u ar callin an ex-husby!Hajjo ta ce ko ba ka zo
ba dama zai tafi,ya ce u ar glad am came Suger,admit it.
Ta yi shiru. Da ya ga ba ta niyar magana ya ce magana za
mu yi,za mu iya zama a soro? Kafin ta ba shi amsa ma har
ya shiga,ta ce dan ma su gida! Ya ce na'am biyo shi ta yi ta
ce no ba magana na yi ba. Murmushi kawai ya ma ta dan
ya ji abunda ta ce saraj. Ta shige ciki dauko abun zama,ta
ke fada ma Indo Khalid ne fa ya zo. Indo ta ce shi ne za ki
zaunar da shi a soro? Cikin awaki,ki shigo da shi tsakar
gida mana. Ta ce toh,ko dan darajar korar ma ta da
Garbati da ya yi. Sai ta dauko tabarma duk da ta san ba ya
zama kan tabar ma ta shimfila,sannan ta ce ya shigo ciki.
Ya shigo sai ya ga tabarma,ta na jira ya ce ba zai zauna ba
sai kuma ya ba ta mamaki ya zauna. Indo ta fito suna
gaisawa sai ga Hajjo nan ta kawo ma sa ruwa a kofin
roba,bayan ta san baya sha ko cin abunci a roba. Indo ta
ce ya za ki kawo ma sa kofin roba ga na karfe Hajjo,ta na
murmushin mugunta ta ke kallan sa,ta ce ya fi san na
roba,ko Khalid? Shi ma murmushin yayi,ya san abunda ta
ke yi,dan haka sai ma ya daga sha ya koshi ya aje sannan
ya ce kwarai kuwa. Cike da mamaki Hajjon ta ke kallan sa.
Sai ta kara da bara na kamasa abunci,na san shi da san
miyar yauki. Ihu ne kawai Khalid be kurma ba,ba shakka
Hajjo niyar ta ta kashe shi,duk abun da ta san ba yayi shi
ta ke ma sa,wa ya sani ma ko guba za ta sa ma sa a abacin
ya mutu ta huta,duk duniya idan akwai abuncin da ya
tsana ya bi bayan miyar yauki. Ciki Indo ta koma ta na
fadin saka ma sa mana,ki hado da yajin daddawa ma. Toh
ta amsa cike da farin ciki. Ta kawo ma sa tuwon. Ga
mamakin ta sai ya wanke hannu,ya dan ci kadan,dandai
ya kunya ta ta,amma da kyar ya ke hadiya,har ya dan
bata ma sa gaban riga. Bayan ya wanke hannu ya zauna
ya ji zuciyar sa na tashi,ya ce dan Allah suger taimaka min
da leman tsami,da har za ta hana shi,sai ta tausaya ma
sa,ta dauko ta yanka ma sa,sai da ya dan sha kadan
sannan ya samu nutsuwa,ya dago ya kalle ta,ya ce come
here Suger,ya nuna kusa da shi. Ta harare shi ta ce Hajara
ce ba diyar ka ba da za ka min irin kiran yara. Tashi yayi
ya na murmushi,ya zo gaban ta,ya durkusa gwiwowi biyu
a kasa,ya ce Hajara yau ga Maighty Khalid gaban ki,ya zo
da kokan baran sa......baki bude ta tsaya ta na kallan sa.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)


[11:38pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Hajara ki yi duba da soyayyar da mu kewa diya
daya,diyar ki,kuma diya ta,ki amince na zama miji a gare
ki dan cigaba da gina zuri'ar da za su kasance tsatso
daya,idan ki ka ki aure na,za ki raba ni da diyar ki,ta riga
ta shiga rayuwa ta,haihuwan ta ne kawai ban yi ba. Kuma
za ki iya auren wanda kuma zai hana ki rukon ta,tin da
uba aka sani da alhakin riko 'yaya ba uwa ba,kin ga kenan
mun yi biyu babu. Hajjo ta ce dan Allah ka tashi,kar wani
ya gan ka haka na banu. Ya ce answer me first sai na
tashi. Ta ce ba zan iya auren ka ba Khalid...saboda me ya
sa? Saboda am nt ur type? I wil try to adjust to ur
type,kawai ki fada min ya type din na ki ya ke. I promise
to b good,zan yi respectn din ki untill my last breath,zan
kuma so 'ya'yan mu na ba su kulawa kamar uba na
kwarai. Hajjo ta ce ba soyayya,ka san ba na san ka,ta ya
za mu zauna?
Khalid ya murmusa,ba soyayya,amma akwai respect,ba
kya so na,i can do wit dat,ni ma wai san na ki na ke
ba,amma ina san diyar ki Ameena zan kuma so yaran da
za mu samu a gaba inshaAllah..duk da dai ita ta fara furta
zancen rashin soyayyar sai da amsar ta shi ta ma ta
daci,ita ta fada ne dan ta na san ji ya yake ji game da
ita,ashe it is ol abt haihuwa da kuma diyar ta da ya ke so.
Gashi ita har ran ta ta na jin sa,wanda kuma ke san na ta
ya raba ta da shi. Yawun takaici ta hadiya dan jika
makogaranta da ya bushe,ta ce ba ni kadai ba ce mace
mai haihuwa a duniya,ka ne mi wata mana! Ya
murmusa,ai nan gizon ke saka,ke zuciya ta ta zaba,ke ce
zabin rai na,ba dan haka ba da ina tuni ma na yi watsi da
zancen,i don't go after gurls,gurls come after me,nd olryt
u ar an exceptional. Babu yanda zan yi. Hajjo ta ce ka
raba ni da mai sona,Khalid ya amsa da ba zai so diyar ki
ba Hajara,dan haka be dace da ke ba! Ajiyar zuciya ta
yi,sannan ta ce zan yi tunani a kai. Tunani akai? Kamar ni
Khalid na zube gwiwowi na kasa na rokeki amma ki ce sai
kin yi tunani?gaba daya kin taba tsarin rayuwa ta,har kin
min gibi. Hajjo ta daga kafada ta sauke tare da fadin dax
in za ka iya jira,idan kuma sauri ka ke sai ka sake saban
lale. Tashi yayi ya na murmushi,ya ce ba sauri,amma ki
sani da ga yau bazan sake bibiyan ki ba,da fatan za ki yi
tunani da kyau,dan Allah ki yiwa sirika ta sallama,sai na zo
maganar auren mu,ya zira takalmi,ya na murmushi ya
fice,Hajjo ta bi bayan shi da kallo,kamar ta ce ya dawo ta
yarda,dan ba wai yardan ne ba ta yi ba,ta na jin tsananin
tsoran kishi da Hauwa,dan ta fita komai,bare uwa uba
mai san auren na ta ba ma san ta ya ke ba.nan ta yi
zaman ta sai da Indo ta fito ta same ta,ta yi nisa cikin
tunani. Da ta matsa sai Hajjo ta fada ma ta damuwar ta
ne sai ta fada ma ta yanda su ka yi da Khalid. Indo ta ce to
menene na ki na kin yarda? Menene laifin Khalid,Hajjo
kar fa ki yiwa kan ki asara! Mutum mai asali ga ilimi da
komai na rayuwu? Ya na san ya aure ki,ya na kuma san
diyar ki,ba kowani namiji za ki aura ba ya yarda ki zauna
ma sa da agola ba,shi gashi saboda ita din ma ya dage ki
aure shi,wani zancen ba ya san ki ki aje,ki ka iya zama da
Garbati ma bare mutum kamar Khalid? Hajjo ta nisa tare
da fadin ni fa kishi da matar shi ne bazan iya ba,ta fini
komai,ni da ita ba gami. Indo ta ce Hajjo,ya fa san da
matar ta shi ya dage sai ya aure ki,saboda kina da abunda
ya ke bukata matar shi ba ta da shi,yar ki da kuma 'ya'ya
tsatson ki ya so,kin ga kuwa ba ta fi ki komai ba din
kenan. Hajjo ta ce wulakanci ne ban so Indo. Indo ta ce ai
kin fi karfin wulakanci Hajjo,bare ma Khalid ba zai
wulakanta ki ba,a de bar shi da jin kai,amma ba
wulakanci....Hajjo ta dara,ta ce aw ashe ke ma kin san
halin nan na shi. Indon ma dariyar ta yi,ta ce waye be
sani ba. Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ki dai kara nazari
Hajjo,ki kuma cire san zuciya ki zabi hanyar da zai fisshe
ki. Hajjo ta ce amen amen,inshaAllahu,Allah ya sa mu
dace. Ta amsa da amen.
Da tunanin Hajjo khalid ya isa kano,shi kan shi ya kasa
gane dalilin da ya sa ta mamaye zuciyar sa,gaba daya ta
mamaye zuciyar sa,ji ya ke kamar ya kusa fara numfasa
sunan ta tsabar yawan yanda ya ke tunanin ta a rana. Duk
da haka ya ki yarda wai san Hajjon ya ke,shi a na shi daga
Hauwa ba zai iya kara san kowace diya mace ba. Shigar
shi gida be ga Hauwa da Neena a falo ba,kai tsaye
bankaran Hauwa ya nufa,ya jiyo su a daki. Da shigar sa
dakin kamshi da ya sani,ya ke balain so ya shaka,ya bi ta
hanci ya shige har cikin zuciyar sa,be san sanda ya yi
subul da baka ba ya ce ya na ke jin kamshi Suger? Hauwa
da ke zaune kan gado ta na yiwa Neena kalaba,da tuni ta
ankare da shigowar sa,ta amsa ma sa zuciya daya ta ce ba
Suger ba ne,Humrah ne fa ya dade ajiye a kan dressing
mirrow na Neena ta zubar garin tabe taben ta. A sannan
ya gane kwaban da ya kusa tafkawa,yayi saurin bin ta ta
hanyar yin kwana shi ma ya ce aw Humrah sunan turare?
Kai amma yayi dadi,ki na da shi amma ba ki amfani da
shi? Hauwa ta ce wlh be dame ni ba ne. Khalid ya karaso
kusa da su,ya zauna tare da fadin ni ya dame ni,ki na
amfani da shi daga yau. Hauwa ta dara,toh zan sa a kawo
min wani,ina kasan kamshin humrah? Tambayar ta sa
gaban sa ya fadi,ya na tuninin amsar da zai ba ta da
gaggawa Neena ta ceto shi, Daga yanda ta ke a
durkushe,ta ce sannu da zuwa Dady. Da sauri tare da
maraba da gaisuwar ta ta ya amsa da yauwa sannu my
beloved one. Ya kiriniya? Hauwa ta ce kasan ba kiriniya
sai shagwaba. Ya na murmushi ya tashi gudun kar a koma
maganar humrah,ya ce ki yi san ranki indai shagwaba ba
ce,diyar Khalid ki ke. Neena ta ce yauwa Dady. Hauwa na
dariya ta ce dama kai ka ke kara shagwaba ta. Ya ce ita
diya tilo ya bazan shagwaba ta ba? Hauwa ta ce gaskiya fa.
Ya ce in kun gama kwasame ni a bangare na. Hauwa ta
amsa da toh. Ya fice ya na dirga sa'ar shi na yau,amma
lokaci yayi da zai sanar da Hauwa kudirin sa akan Hajjo.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[11:50pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Kusan sati daya kenan raban Hajjo da Khalid,kamar
yanda ya ce ma ta din ya daina bibiyan ta,amsar ta ya ke
jira. Da ya sanar da Hajiya da Jabir yanda ya yi da Hajjon
amma be fada mu su har tsugunna ma ta ya yi ba gudun
sharrin Jabir. Jabir ya ce ahaf,dama na fada mi ki
Hajiya,jin kai irin na Khalid ba zai bari ya iya shawo kan ta
ba,gashi kullum rama ya ke kamar kudin guzuri. Hajiya ta
ce Jabir ai sai ka sa baki. Jabir ya ce toh Hajiya,gobe zan je
na same ta inshaAllahu. Hajiya ta ce toh Allah ya kai mu.
Ba karamin dadi ya ji ba jin Jabir zai sa baki,ya san Hajjo
ta kusa shiga hannu kenan. Tattaunawar Hajjo da Jabir a
asibiti Hajjo ta nuna amincewar ta kan auren Khalid. Jabir
ya ji dadi matuka da yanda Hajjo ta ke ma sa,komai ya ke
so ta yi,wuyan ta ya yi magana kamar yanka wuka haka ta
ke aiwatar da shi. Ya ma ta alqawarin tsaya ma ta a komai
kan auren,sannan kuma ta ba su sati biyu za su zo su
nemi iyayen ta dan yanke maganar auren. Da kamar za ta
fada ma sa tsakanin ta da Baba,sai ta ga ai kamar tonawa
kan ta asiri ta ke,gwara su je da kan su,su ganewa idan su.
Da wannan maganar su ka yi sallama.
Cikin dalleliyar motar shi da ya sake ya nufi gidan Khalid.
Bayan ya gama ma sa tsiya da Allah ya san ya
alkhairi,Jabir ya ce albishirin ka? Khalid ya ce goro,bayan
motar ka siyi private jet ko? Jabir ya make shi tare da
fadin shegen maza,sai na siya ai,ka san da kudin. Khalid
ya ce ni ko na san da su,ci ne dai kawai ba a yi. Jabir ya
murmusa tare da fadin da kasan albishirin da zan ma ka
da ba ka tsaya jan wannan shirmen da ka ke fada min
ba...Khalid ya gyara tsayuwa,ya ce toh fadi na ji. Jabir ya
ce na ga Hajjo yau. Cikin kaguwa ya ce dan Allah,ya ku ka
yi? Jabir ya ce sai ka biya. Khalid ya ce kaiya! Dan

Please Login or Register in order to submit comment