Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amen. Allah ya bada
zaman lfy.
Hajiya ke neman ta ido rufe,da ta tashi daga aiki sai ta
biya gidan ta. Hajiya ta na ta tsokanar ta wai Hajjo ta
zama sirika. Wani nauyi da kunyar Hajiya ta ke ji sosai,ta
ka sa sakin jiki su yi maganar auren da kuma sauran
abunda Hajjo za ta bukata saboda kusan rabi tare su ka
siya da Hajiya kafin ma Khalid ya dawo a fara maganar
auren su. Da Hajiya ta ga dai Hajjo ta ka sa sakewa sai ta
hada ta da kanwar ta,tare su ka cigaba da shirye shiryen
biki,ba Jabir ba,har Hajiya sai da ta dunkula dukiya mai
tsoka ta damkawa Hajjo dan shirye shiyen biki,ba shakka
sun ma ta karamci kwarai. Gyara kam Hajjo na sha
kwarai daga wajan Doc Hussaina,dake Doc Hussaina
duniya ce.
Hauwa kuwa sai da Khalid ya hada ta da Hajiya tai ma ta
nasiha sosai sannan ta sauko. Ana sauran sati guda daurin
aure ta tare saban gidan Khalid. Gidan ya hadu ya tsaru
kamar gidan turawa,da ke ma su abu da abun su,abu na
so Khalid bluiders of d world. Bangare uku ne,bangaren
Khalid a sama,sai kuma katan falo a kasa wanda ya sada
ban garan Hauwa da Hajjo matan na Khalid,sai kuma
katan kitchen ma dauke da dining area,dakin Neena ma
bangaran Hauwa ya ke,Gidan cike ya ke fal da kayan
more rayuwa,gashi very spacious. Hatta bangaran Hajjo
Shi ya zuba kaya,ya dai aika Sani ya tambaya ma ta colour
din da ta ke so.
Ranar juma'a aka daura auren Khalid da Hajara,Khalid ya
biya sadakin sa dubu hamsin. Su Ayush ne amara,duk da
ba wani bidi'a aka yi ba,daga wuni da aka yi a
kumurya,sai walimar da aka yi gidan Hajiya sannan aka
wuce da amarya akai Hajjo dakin ta. Kuka wajan Hajjo
abun ba magana,rayuwa ta sake canzawa,ta shiga saban
babi...

DIYA MACE
Hannu Hauwa aka damka amanar Hajjo,sai cika ta ke ta
na batsewa ita da yan uwanta,habaici da guda kuwa yan
uwan Hajjo sun sha. Ga wani ado da kyau da Hauwa ta yi
kamar ita ta yi kanta dan kyau,sai a sannan Indo ta gane
matsalar da Hajjo ke gujewa kan ta dan gaskiya Hauwa ta
cika mace,su Doc Hussaina kuwa ba dan sun san wacece
Hajjo ba sun kuma yarda da shirin da su ka ma ta da sai
sun daura hannu a ka sun ce sun shiga uku.
Bayan su Indo sun kara ma ta fada sai su ka watse,su ka
bar Hajjo tsakiyar gadan ta ta na sharbar kuka. Ango
Khalid ya shigo cikin shigar angwaye na alfarma,sai ma ya
dada zama yaro kamar wanda ya yi auren fari.Hauwa
zaune bangaran ta,ita ma yan uwanta sun watse,Neena
na dakin ta ta yi bacci,Hauwa ta sake ado ta yi kyau
kamar ita tai kanta ango Khalid ya shiga ya same ta. Shi
kan shi kyan na ta ya ruda shi,ya janyo ta jikin sa ta zille
ta na malam yaya ne,ba fa ni ba ce da kwanan ba yau! Ya
dara tare da fadin an ma fara min gori kenan. Ta ce ya
bazan ma ka ba gori ba tunda irin rayuwar da ka tsarawa
kan ka kenan. Ya murmusa gami da sake janyo ta jikin,ya
na hussssh,say no more. Ina Neena? Ta ce ta dade da
kwanciya ita dai kam. Ya ce toh ki fito falo ki same
mu,bari na kira kanwar ta ki. Da kamar za ta ce ba za ta
zo ba,sai kuma ta ga kamar hakan zai sa Hajjon ta raina
ta,ta ce toh ta na fitowa.
Bangaran Hajjo ya shiga,ya tura komar a hankali,wani
kamshi mai dadi ya daki hancin sa. Yayi sallama tare da
shiga daki. Idanu ta daga ta kalle shi,wannan karan Khalid
Khalid ne ke neman numfashi ba Hajjo ba,tsabar kyau da
kwarjini irin na amare gaba daya ta sauya yanayin sa. An
ma ta ado cikin farin leshi,ga farar lufaya an nada
mata,ga gyaran jiki da ta sha wajan su Doc Hussaina fatar
nan na ta wankan tarwada har wani sheki yake. Da kyar
ya daure,ya na wani basarwa dan kar ta gane tarkon ta ta
kama kurciya ya ce muna jiran ki falo amarya. Juyawa
yayi ya fita ba tare da ya ji amsar ta ba.
Falon kasa da yayi dan zaman iyalan na sa duka ya zauna.
Hauwa ce ta riga fitowa,ta zauna kusa da shi suna dan
hirarrakin su,sai ga Hajjo ta fito,idanun ta a kasa,fuskar ta
rufe da mayafi ta zauna a na ta kujerar da ga gefe,Khalid
ya ce ta so ta zauna kusa da shi kamar yanda Hauwa ta
zauna,ma'ana su sa shi tsakiya. Ran Hauwa ya sosa da
kishi,wato dai sai ya jera su,ya nuna ma ta matsayin su
daya,bare ma fitowar Hajjo yanda ta ji tana kamshi
kamar diyar shuwa ya sa zuciyar ta tsinkewa. Ba musu da
ke gaban uwar gidan sa su ke sai ta tashi ta koma kusa da
shi din. Ya mu su nasiha sosai da fatan za su hade kan
su,ya kuma roki Hajjo da ta kara yiwa Hauwa kara akan
Neena,tin da duk an zama daya,dan Allah ta karanta.
Cikin ranta kuwa cewa ta ke indai kara ne kunzo wajan
ta,ita ba matsala gare ta ba.
Ya kare nasihar shi da addu'a. Hauwa ce ta fara tashi ta
tafi,Khalid ya bi bayan ta. Ita ko Hajjo tashi ta yi ta koma
na ta bangaran. Ta yi wanka fito daure da shawl dan
yanda Khalid ya dade be fito ba sai ta dauka can zai
kwana ta saki jikinta,ta zauna ta na shafa mai. Kamar da
ga sama sallamar shi da shigowar sa lokacin guda ne...
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[1:14am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Da sauri Hajjo ta tashi,ta kuma koma ta zauna ta na jan
shawl din kan gwiwar ta. Da ganin na ta da kuma yanda
ya ga ta rude sai ya bashi dariya,dariyar ta sa ya bawa
Hajjo haushi,dama kuma kule ta ke da shi. Ta yi saurin
jan lufayan ta ta rufe jikin ta tana mallam menene za ka
shigo min daki ba sallama! Ya na murmushi ya ce na yi
sallama Suger,ta ce me ya sa ba ka tsaya na ba ka izinin
shigowa ba kawai za ka shigo min?ya ce gida na ne,auren
ki na ke. Ta cije leba gami da ka fita ka bar min daki,pls ka
fita! Ya ce ni ki ke kora Hajara? A daren auren na mu na
fari ki kore ni? Idanun ta kwalakwala,sai a sannan ta tuna
fa ashe wai daren auren ta ne,ta tuno yanda na ta ta
kasance da Garbati,tuni idanun ta ya rufe,ta ce eh kai na
ke kora,pls ka fita. Duk da hakan be ma sa dadi ba,amma
jin kai ya sa ya ki nunawa,sai ma murmushi da ya sakar
ma ta,ya karasa cikin daki,gaban ta ya kara faduwa. Ya
lura da hakan,sai da ya kai dab da ita,ta dada dunkulewa
cikin mayafi,ya na murmushi ya aje ledar gaban ta yana
fadin ga abunci,na san yunwa ki ke ji. Ya sunkuyo fuskar
ta,Hajjo ta runtse ido,kumatun ta yayi kissin ya dago ya
na dariyar yanda ta sankare,kana ya ce suger,Khalid is a
gentle man,so ki sa a ranki ba zan taba kwana cikin dakin
ki ba sai dai idan ke ki ka gayyace ni da kan ki. Ya juya ya
fice. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta saki jikin ta. Cikin
azama gudun kar ya dawo ta sanya rigar baccin ta iya
gwiwa. Sai da ta nutsu sannan ta bude ledar da Khalid ya
aje,kaza ce gashasshiya da fresh milk,ta ci ta koshi,sannan
ta dan taka a tsakar dakin gudun bacin ciki,ta kwanta ta
sha baccin ta dake dama ta tara gajiya.
Sai da ta yi sati daya a gida ta koma kan aikin ta. Sam
Khalid ba ya gaban ta bare kuma matar sa,kwana uku uku
su ka raba kwanan duk da kuwa duk ranar kwanan Hajjo
dakin sa ya ke kwana bisa ga alkawarin da yayiwa
Hajjon,ita kuwa Hauwa da ta lura da haka,sai ta kara jin
kan ta,wato da gaske dai ba san Hajjon ya ke ba tinda ya
aje ta tamkar fanko ne kawai. idan ranar girkin Hajjo ne
kafin ta fita ta ke musu brkfast da abuncin rana,da ke
7:30 ta ke fita,8 ta ke fara aiki. Da ta dawo 4 sai ta daura
na dare. Kuma bisa al'adar su,tare a ke zama a ci abuncin
kan dinig table da ke cikin kitchen din na su,nan Hajjo ta
ke ganin kissa da kisisi na wajan Hauwa,ita abun har
mamaki ya ke ba ga Neena na wajan ita ko kunya ba ta ji?
Tai ta jan shi da hirar da be ma shafi Hajjo ba yanda za su
ware,ita kuwa Hajjo ko a tafin kafarta,ita dai ta cika cikin
ta tashi idan ma hadiye shi za ta yi tayi can ma ta.Khalid
ya dame ta da korafin shi ba zai juri hawan adaidaitan ta
ba,kullum wani gardi ya ke jin kamshin ta,dan haka lalle
ta yi shirin koyar driving dan ba zai juri yay kai ta ya na
dauko ta ba,haka kuma ba zai dau driver ba. Tsakanin ta
da diyar ta nesa nesa,dan ita ganin ta take kishiyar uwa ba
ma uwa ba,ita kuma Hajjon sai ta ke wa Hauwan kara,ta
ke dauke kan ta daga kan Neenan.
Randa ta cika sati biyu a gidan ta,bayan ta gama girki an
zauna anci,sai ta tashi ta shige bangaran ta ta bawa
Hauwa waje ta yi abunda ta ke so. Ta na shiga ciki Khalid
shi ma ya tashi,ya sake kaya cikin sport wears din sa ya
fita jogging. Wanka Hajjo ta yi,ta sanya rigar baccin ta
pink mara hannu da nauyi,ga laushi iya gwiwa ta tsaya
ma ta,ta kama kan ta da ya ke a tsefe ta rasa mai kitso,ta
yi kalaba guda biyu,abun ku da kan ba gashi sai kuwa su
ka tsaya gudil gudil da su kamar kaho. Ita kanta da ta kalli
kanta a madubi sai da ta yi dariya,ta yi kama da yar
yarinya sak. Ta ja kujerar karatun ta gaban table,ta kunna
system ta fara sana'ar na ta,wato research.
Bayan Khalid ya dawo,a tsakar dakin sa daga shi sai
gajeran wando da shawl a rataye wuyar sa ya na shirin
shiga yayi wanka,sai ya ji duk duniya idan be tsokano
Hajjo ba ba zai ji dadi ba,dan yanzu ba wacce ya ke son
zolaya kamar ita. Kawai sai ya fasa shiga na shi toilet din
ya nufi bangaran na ta. Ta yi nisa cikin research,ba ta
ankara ba ta ji an bude kofa,da sallamar sa da shigowar
sa lokaci daya ne. Ta daga ido ta kalle shi,ganin yanayin
shigar ta sa ta yi saurin yin kasa da ido. Murmushin nan
na sa na tsokana ya sakar ma ta,tare da fadin nawa toilet
din is faulty,i wil use urs in ba damuwa....ya na magana ya
na nufar kofar bandakin,jin ta yi shiru ya juyo ya kalle
ta,ya ga sam hankalin ta ma ba ya wajan sa,sai a sannan
ya lura da kahon gashin ta biyu,ya ce like seriously Suger
iyakan gashin ki kenan ko kuwa kin boye wani karkashin
filon ki? Dagowa ta yi ta kalle shi,sai kuma ta tuna yanayin
da ya ke ta kara saurin kau da kai,gaba daya magana ma
ta kasa dan takaici da kuma takurar da shigowar sa ya sa
ta. Ganin ta ma sa shiru ya shige ban daki ya rufo. Sai a
sannan ta saki ajiyar zuciya. Kamar za ta koma falon ta,sai
kuma ta fasa gudun kar yayi tunanin tsabar tsoran sa ya
sa ta gudun. Amma gaba daya ta ma kasa gane
komai,burin ta ya zo ya fita ko ta sami nutsuwa. Ile ko sai
gashi ya fito daure da shawl,kirjin sa duk a waje ga ruwa
na diga daga cikin sa,hannun shi ruke da dan karamin
shawl din ta ya na goge kan sa. Da wayo ta saci kallan
sa,su ka kusa hada ido ta yi sauri janye na ta ido. Ya na
murmushi ya ce ba sai kin saci kallo na ba Suger,am ol
urs,saki jikin ki u can stare as long as u want. Maganar ta
sa sai ta bawa Hajjo haushi,ta yi karfin hali ta kalle shi ido
cikin ido sannan ta ce ni Hajjo na saci kallan ka? Me zan
kalla Khalid? U ar nt man enough for me.....sai da ta fada
sannan ta yi dana sanin dan subul da baka da ta yi,da za
ta iya shanye kalmomin ta na karshe da ta shanye ganin
yanda idanun sa ke shining,fuskar sa dauke da
mischievous smile ya nufo in da ta ke,dan tsoro kasa
motsawa ta yi,kamar wacce aka sa igiya aka daure,har ya
karasa kujerar da ta ke,ya sunkuyo da fuskar sa dabda na
ta,Hajjo ta yi kasa da na ta idon gaban ta na dukan uku
uku,ya sa hannu ya dago da haban ta ya na kokarin sanya
kwayar idanun sa cikin ta,amma ta ki dagawa ta kalle,ta
na jin saukar numfashin sa kan fuskar ta,ya ce maimaita
abunda ki ka ce Hajara. Tsit ka ke jin Hajjo kamar wacce
ruwa ya shanye,ya ce fadi na ji,who is nt man enough for
u? Ta yi shiru,hannun sa bisa fuskar ta,ya fara wasa da
yatsan sa kan lips din ta da yake kallo kamar mai
nazari,kan ta ankara tuni ya mikar da ita ya hada da jikin
sa ya fara kissing din ta. Da ke Hajjo ta ji saban abu,abun
da sai dai ta gani ana yi a tv ta dauke kai ko kuma ta
karanta a littafafai wai shi Khalid ke ma ta, ta fara kokarin
zullewa har ta hakura ta dai na...
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[11:30am, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Ya kusa shagala ya manta da inda ya ke haka ita ma Hajjo
da ta shiga wani duniyar,da kyar ya iya yaki da zuciyar
sa,ya dago ya na kallanta,idanun ta runtse tana numfashi
a hankali,ya maida ta jikin sa,yayi hugn din ta sosai kamar
za ta shige cikin sa,sai da ya sami nutsuwa,cikin rada ya
ce mata dis is jst a kiss Suger,ba dan Khalid is a
gentleman ba da na gwada mi ki ya Man ya ke,amma a
sannu Suger,cikin kunnan ta ya rada ma ta am much
more dan Man enough for all the women in d world
Suger......ya janye jikin sa a hankali,sai da Hajjo ta yi
saurin dafa table dan gani take ba za ta iya tsayuwa ba,
shi kuwa ficewa yayi da sauri kafadar nan a tsaye dan jin
kai. Da fitar shi ta yi saurin hayewa gado,ita dai kam ta
shiga nau'i,bargo ta ja ta dukunkuna,abunda ya faru
tsakanin ta da Khalid ya sa ta dai na gane komai,ya tsayar
ma ta da duniyar cak.
Shima wajan gugan na ta hakan ta ke,tin komawar sa daki
ya kasa sukuni,he jst can't blv Hajjo can b dis innocent
yea Innocent nd sweet at thesame tym,sam da dukkan
alamu yanda ta yi reactn ya san saban abu ne a wajan
ta,hakan ya kara sa shi san more,he love every bit of it,He
want her dan da kyar ya iya jurewa be koma ba,amma
daran ranar sam bacci ya nema ya rasa,tunin Hajjo ne ya
raya ma sa daren.
Washagari ko karyawa ba ta yi ba ta gudu wajan aiki
gudun haduwa da Khalid,dake ta yi sa'a ba girkin ta bane.
Dab da la'asar bayan ta dawo daga aiki,ta yi wanka,sai ta
fito babban falon su,nan ta tadda Neena a na game,ta ce
Neena ba gaisuwa? Hankalin ta kan game tace ai ban gan
ki ba Aunty,sannu da zuwa. Hajjo ta ce sannun ki,ta sami
waje ta zauna,sai ga Hauwa ta fito daga kitchen ta ce
Neena a tashi a yi shirin islamiya. Neena ta make
kafada,ni wlh na gaji. Ga mamakin Hajjo sai ji ta yi Hauwa
ta ce toh ai shikenan,ta cigaba da aikin ta. Har Hajjo za ta
sa baki,sai kuma ta yi shiru,amma har ranta ba ta ji dadin
abun ba. Ana kiran sallar la'asar,Hajjo ta tashi ta yi na
ta,ta na zaune kan dadduma Hauwa ta sake shigowa ta ce
da Neena a tashi a yi Sallah ma na. Idanun ta kan game ta
ce sai an min game over Momma,Hauwa ta ce toh ai sai
ki ta yi,ta shige kitchen. Ran Hajjo ya baci,ta ce ke aje
game din nan ki je ki yi sallah. Ko kallan Hajjo ba ta yi ba
bare ta aje game din,ta ce ai na ce sai an ce game
over.....a fusace Hajjo ta tashi ta fizge handle din,tashi
maza ki je ki yi sallah ko na sabar mi ki! Ta daka ma ta
tsawa,a kideme Neena ta tashi,ta fashe da kuka da ke ba a
saba ma ta tsawa ba,ko a jikin Hajjo dan ji take kamar ta
make ka ta huta,ta ce dan iskanci ana mi ki magana ki na
jin mutane sai kin gama game za ki yi sallah! Ki je islamiya
kin ce kin gaji! Wlh ba zan juri wannan saken ba! Sai ga
Hauwa ta shigo da sauri,ganin ta Neena ta karasa wajan
ta da gudu ta na kuka,sai tambayar ta take lfy? Dukan ki
ta yi? Kuka ya ci karfin Neena ta ka sa magana,sai Hauwa
ta ce je ki dakin ki ina zuwa,sai kuwa ta shige bangaran
Hauwa da gudu,ta na jiyo Hajjo na fadin ki tabbata kin yi
sallah! Hauwa ta kalli Hajjo ta ce me ki ka ma ta? Kar dai
dukan ta ki ka yi. Hajjo ta ce ban dake ta ba,amma kiris
ya rage na dake ta,yarinyar is too spoiled,ya kamata a
fara handling din ta wit iron hands. Hauwa ta ce ke kar ki
nemi ki fada min magana! Me ki ke nufi? Ki na nufin ban
iya tarbiya ba? Hajjo ta girgiza kai,ta ce ba haka na ke nufi
ba,Hauwa ta ce haka ne mana,wato iko za ki nuna
min,ban iya tarbiya ba muna sangantar mi ki da diya.
Hajjo ta ce ba ki fahimce ni ba,gyara kayan ka ai ba zai
zama sauke mu raba ba...ke tsaya matsayin ki! Hauwa ta
daka ma ta tsawa,ta ce har ke kin isa ki fada min magana
dan mijina ya auro ki,ki na ganin ba na haihuwa shi ki ke
tunanin za ki iya min gori kan diyar ki......Hajjo dai tura ta
kai bango,ita ma ta fusata ta ce eh an mi ki gorin,karya
ne? Ba diyar tawa ba ce? Ko ke ki ka haifa min......karaf sai
a kunnan Khalid da shigowar sa kenan ya tsinci maganar
Hajjo,ran sa ya baci matuka. Ganin sa tsaye Hauwa ta
juya ta shige bangaranta da gudu. Hajjo ta yi kasa da
idanun ta,yanda ta ga idanun Khalid sun kada sun yi ja ya
sa ta kokarin ma sa bayani....ya dakatar da ita ta hanyar
fadin dama haka ki ke? Na zaci ke me rufa min asiri
ce,amma ji yanda ki ke gorantawa mata ta? Ki da ki ke
haihuwar ba Allah ne ya baki ba? Ko dabarar ki ce aka ce
mi ki? Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce ba haka ba
ne,she pushed me to d extrem wall ne,dole na yi
magana,ba zan iya jure ganin yanda Ameena ke tashi ba
kwaba ba! Ba zan iya jure ganin ta na tashi kamar Baban
ta ba,God shez becoming d personication of her
biological father! Khalid ya cize lebe,ni ma gorin za a min?
Na ji ba ni ne baban ta ba am so what? Hajjo ta ce me
zan yi ku gane? Menene laifi dan na gyarwa diya ta
tarbiya? Karya ne ba diyar tawa ba ce?yanda na san ciwan
ta wlh ba zan sa ido ta tashi yanda ta ke yanzu ba,ba gata
ba ne wannan,diya mace ce,uwa kuma za ta zama nan
gaba...Hajara! Ya daka ma ta tsawa,enough of ur insult!
Ita din da ki kewa gori ba taimaka mi ki ta ke ba?ki na da
lokacin diyar ta ki ne?idan ki ka sa kafa ki ka bar gidan
nan tin 8 ba ki dawowa sai 4,ina ki ke da lokacin kan ki
bare na tarbiyar yara? Murya kasa kasa Hajjo ta ce no
you ar mistaking,ku bani diya ta mana kuga ko zan gaza
tarbiyartar da ita,ko bani ita ku ka ko za ta gaza samin
lokaci na! Never underestimate d power of mother! Zan
iya zama both! A responsible mother as well as a
dedicating Doctor!Khalid ya daga kafada,Wuce ki bawa
mata ta hakuri! Hajjo ta ce Khalid dan me ya sa? Dan me
ya sa zan ba ta hakuri? Dan ni ba mutum ba ce ko dan ni
ba a sona? Dan me ya sa? Me na mata da zan ba ta
hakuri? Fuska murtuke ya ce a matsayi na na mijin ki na
ce ki ba ta hakuri,it is an order! Rai bace,kwalla na shirin
sauka ta makale,da sauri ta nufi bangaran Hauwa,ko da ta
shiga dakin ta,ta ganta kwance,sai ta sake shawara,ta juyo
za ta fita ashe Khalid na biye da ita,ya ce juya ki ba ta
hakuri! Hajjo ta juya ta ce Hauwa Allah ya baki hakuri. Ta
juyo tana kallan Khalid ido na spark din kwalla da bacin
rai ta ce na bawa matar ta ka hakuri,ta fice da sauri.
Shigewa dakin yayi,ya jawo Hauwan jikin shi ya na kara
ba ta hakuri.
Hajjo na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,sam ba za ta
iya zaman gidan ba,dama ta san wulakanta ta Khalid ke
da niyar yi shi ya sa ya auro ta. Tuni ta hada yan kayanta
cikin karamar jaka,ta dau kudin mota,ta fito ba tare da
kowa ya sani ba sai hanyar Kumurya. Sai da ya tabbatar
Hauwa ta saki ranta,sai kuma hankalin sa ya koma ga
Hajjo,ya fara ji kamar be kyauta ma ta ba tunda be ma ta
uziri ba ya ji kanun zance,kawai tsintar ta yayi ta na
gorantawa uwar gidan sa rashin haihuwa. Dakin Neena ya
je,ya tambaye ta me ya faru ta yi kuka? Da ke yaro be fiya
karya ba sai ta bashi lbrn yanda aka yi har kin zuwan ta
islamiya da ma kin yin sallah. Jikin shi ya yi sanyi,ya tashi
da sauri ya nufo bangaran Hajjo,amma me zai gani?
Wayam babu Hajjo babu alamar ta,ya bi daki daki na
bangaranta,har bandaki ya duba amma shiru,tuni ya
rude,hankalin sa ya tashi. Da sauri ko takalmi be iya sawa
ba ya fito wajan maigadi ya na tambayar ko ya ga fitowar
amaryar sa? Maigadi ya ce kai be gani ba,in ma ta fita
watakila sanda ya zaga bawali ta fita din.....
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[11:55am, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
A kidime ya koma ciki,takalmin da ya sako ma hadin
bauta ne be sani ba,tashin hankalin sa ina Hajjo za ta da
yamma likis haka? Ko sallama be yiwa Hauwa ba ya figi
motar sa dan bin sawun Hajjo. Ko da ta isa
kumurya,idanun ta sun kumbura da kuka,sai tadda Indo
ba ta nan sai yara,su ke fada ma ta wai Indo ta na gida
dazu aka zo aka ce Baba ya kone. Nan tsakar gida ta saki
jakar ta,bayan shekaru da dama sai ga ta ta dau hanyar
gidan su,dan idan ba ta ga halin da Baba ya ke ciki ba
hankalinta ba zai kwanta ba. Ganin yanda kofar gidan ya
kwarabe sai da gaban ta ya fadi,bare da ta shiga
gidan,kamar ba nan ne Innar ta ke rayuwa ciki ba
da,gidan ya lalace,ya kazance. Muryar Indo ta ji ta na
musayan magana da matan su Mudi,Indo na fadin wlh
sam ba ku kyau ta ma na ba,amma ba laifin ku ba
ne,laifin mazajen ku ne,idan ku be haife ku ba ai su ya
haife su. Tare su ka ce eh mun ji din,yo ba shi ya ce a
bashi garwashin ba,sai mu hana shi?ace mun yiwa siriki
rowa? Muna fama da yara muna fama da tsoho,ai idan ba
a gode mana ba ba a zage mu ba. Baba kwance gaba daya
hannun sa na dama ya kone,yatsun duk sun durkushe,sai
nishi ya ke dan azaba,bakin sa karkace daga alama barin
jikin sa ya shanye. Hajjo ta yi sallama jiki sanyaye. Indo ta
amsa ta na yauwa Hajjo gwara da Allah ya kawo ki,ji
yanda Baba ya sanya hannun shi cikin garwashi ya kone
dan Allah! Sai ta sa kuka...Matan Su Mudi su ka rude ganin
Hajjo,dake sun santa tin kafin ta auri Garbati,tare su ka yi
wasa,amma zaman kauye sun tsufe sun tsomare kamar
ba sa'annin Hajjo ba. Su ka fara laha'ila Hajjo,Hajjon ce
kuwa! Ko ta kan su ba ta yi ba,ta karasa wajan Baba da tin
randa ya ce ta zauna wajan Indo ba ta kara sa shi a ido
ba,gaba daya ya tsufe ya tsomare saboda cuta da rashin
gata. Gaban shi ta zauna ta na hawaye. Jin ana Hajjo
Hajjo! Idanun sa runtse sai yayi sauri ya bude ya na ina
Hajjo? Ina diya ta Hajjo,ku hada ni da Hajjo na nemi
gafarar ta! Indo ta ce yi magana Hajjo,taba shi ya jiyo ki!
Hajjo ta sanya hannun ta cikin na Baba,ta kasa magana
sai kuku. Tana kuka Indo na kuka. Su kuwa matan su
Ayuba sai abun ya zama mu su na kallo.
Sani Hajjo ta nema,su ka yi sa'a shigowar sa kumurya
kenan,ya ce gashi nan tafe. kafin su iso Indo ke ba ta
lbryn yanda aka yi Baba ya kone,wai cewa yayi a bashi
garwashi zai yi turare,da ke Baban ba lfy gare shi ba,ya na
cikin turaren ya yanki jiki ya fadi,sai hannu ya fada
garwashi,gashi bangaran jikin sa ya shanye,ba daman
ihu,baki ya karkace ko ya yi ihu ba mai ji bare a ka masa
dauki,matan 'ya'yan sa ba sa iya kula da shi,sai da babban
dan Mudi ya gifta ta dakin ya ga Baban ya fasa ihu,shi ne
fa aka zo aka cire hannun. Mudi da Ayuba sun dawo,sai
mita su ke wai laifin Baba ne,shegen rigima na tsoho,ina
shi ina turare! Abun mamaki da kudirar ubangiji a nan
shine diyoyin matan na sa da ya guja ya ke kyama,ya ke
kira da jidali su ke jin kan shi su ke tausayin shi,su kuma
'ya'yan na sa maza da ya nunawa gata sam ba su damu
da shi ba,shi ne ma ya zame mu su jidali su

Please Login or Register in order to submit comment