Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

YAR KURMA

GODIYA

Dukkan godiya ta ga ubangijin talikai, daya hallice ni cikin ni'mar musulunci. Ya kuma bani ikon d'aukar alk'alami dan yin karambani a kan wani tak'aitacen lamari bisa san sanin makamar aiki. Har gobe nid'in me neman gyara ce daga na sama dani harma na k'asa nà kasantuwata k'ank'anuwa cikin harkar adabi.

Cikin takaici ta nuna Marwanatu da hannu, zuciyarta na yi mata k'una saboda dariyar da take yi mata. A zafaffe ta kai mata bahagon duka, amma kash! Bata same ta ba ta saki wata giggitaciyar k'ara, ji kake kauuuuuuu! A kunnuwan Marwanatu. Benaziratu ta k'yalk'yale da dariya ta buga k'afa irin na Bebaye ta murd'a yatsu, take suka bada sauti d'as! 'Das!! Das!!! Alamun gargad'i tuni Marwa ta ranta ana kare.
Bata jinkirta ba ta rufa mata baya, ai kuwa suka kasa a guje. In baka yi bani waje, basu samu matsaya ba sai a d'akin Hajja Yakura, bisa tsatsauyi suka zubar mata da biskin geron da ta ajiye. Ai kuwa cikin hargowa ta yo kansu, Marwanatu ta falle caraf ta kama Benaziratu."Wato ke 'yar kurma bakya jin magana ko?". Benaziratu ta turo baki, bata ji abinda ta furta ba amma bakinta da ta kala ta gane me furucinta yake nufi. Tuni ta hau tirje-tirje Allah ya bata sa'a ta k'wace a guje ta bar sashin. Kafar! Sukai karo da shi, a razane ta d'ago sukai ido hud'u dashi Baana. Cikin razana ta so kaucewa kamunsa amma ina ta makaro. Yana rik'e da ita ya shiga gidan, da salama Yakura ta d'ago tana amsa masa mamakin ganinsa a wannan lokaci yasa ta kasa magana cikin yaransu take kiran mai gidanta tana sanar masa. Bakura ya taso da saurinsa yana nuna farin cikinsa da ganin Baana. Da wannan damar Benaziratu ta kufce ta fyala da gudu, yabi bayanta da kallo yana murmushi karaf suka hada ido da Yakura ya sune kai yana shafa k'eya.
Gimtse fuska tayi ta shimfid'a masa tabarma karauni, ya zauna yana gaishe su tare da tambayar yadda ya same su. Cikin murmushi suke amsawa, shigowar Marwanatu tana kuka ne ya katse su. Cikin masifa Yakura tace"kin tsaya ta dake ki ko?" Marwanahtu tai ajiyar zuciya tana lab'e-lab'e saboda ta san mudin Yakura ta kamata duka zata sha. Saboda kullum gargad'inta ta daina bari Benaziratu na dukanta ne. Cikin mamaki Baana yace" wace ce ?" Cikin jin haushi ta numfasa.
"Wacce ce kuwa banda Benaziratu?" Ta fad'a da gurb'ataciyyar hausar ta.
Mumushi yayi a ransa yana fad'in "yaushe Hajja zata sauya?". Shiru na tsayin lokaci, ya yunk'ura zai mik'e " ina zaka"? Cewar Yakura. Kansa a k'asa ya furta "zan je in huta an jima in shiga in gaishe da Abbagana". Murmushi mahaifinsa yayi yace "Allah ya kaimu" k'wafa tayi taja hannun Marwanatu suka bar wajan. Daga shi har mahaifinsa murmushi sukai_.





Washegari da misalin k'arfe bakwai na safe Baana yana zaune a dakalin k'ofar gidansu, ya hango tahowar Benaziratu tunda ta taho ya zuba mata ido. Shi dai rayuwarsa yarinyar tana birgeshi, komai nata cikin nutsuwa take yi duk da cewar tana da son barkwanci. Bai ankara ba harta k'araso ta zo giftawa ta d'aga masa hannu tana murmushi gab da zata shiga gidansu ya d'aga murya da k'arfin gaske, ya k'wala mata kira *"Benah"*. Juyowa tayi ta murgud'a d'an k'aramin bakinta, ta murd'a yatsu suka bada sauti ta shige gidan. Yai murmushi a ransa yana fad'in "hallayar Benah tana nan". Cikin gidan ta shiga da fuskarta d'aure tai salama, duk haushin Baana ya tuk'eta nan duniya ta tsani a kirata da Benah, ganinta kawai iyayine irin na Baana dan yaje birni karatu.

_"Ke! 'Yar kurma" aka fad'a da k'arfi daga gefanta, juyowa tayi tamkar mayunwacin zaki tana huci. Ganin Hajja Yakura sai ta sadda kanta k'asa tana gaisheta cikin gwarancinta irin na Bebaye. Matsowa tayi ta kama kunnanta ta murd'e ai kuwa ta saki k'ara saboda azabar wahala, shar k'wala ta zubo mata. "Dan ubanki me Marwanatu tayi miki jiya, da zaki sata Ku........?" Maganar ta katse sakammakon k'watarta da Bakura yayi yana bambamin fad'a.

"Ke dai Yakura kinji kunya, me yarinyar nan tai miki? Tsabar k'in Allah kin takura mata idan da kara itama 'yar ki ce"._

_"Kai! Kai!! Kai!!! Bakura dai na fad'in wannan, Allah suturi buk'wui ina amfanin sai da rai a nemo suna? Wai kai kana tunani zanso wannan abar? Hmmmm! Allah ya kiyayye had'a iri da kishiya". Wata muguwar harara ta makawa Marwanahtu, tuni ta ja hannun Benaziratu wadda take razgar kuka, kasancewar duk da k'arfi Yakura take maganar tana jinta. Kad'a kai Bakura yayi ya shige d'akinsa.

Suna fita sukai kici6us da Baana, hannun Benahziratu ya kamo yana tambayarta. Ta k'wace hannunta dan tuna abinda yai mata d'azu. Bata kula kowa cikin su ba ta warce hannunta tana kuka, kai tsaye gida ta nufa. Cikin raunin murya ya dubi k'anwarsa"Marwah me ya samu Benah"? Murmushi tayi dan taji dad'in yadda ya kira sunan. Tiryan-tiryan tai masa bayanin abinda Yakura tayi, kansa ya ri'ke yana jinjina hallayar mahaifiyarsa a ransa yana fadar" wai shin yaushe Hajja zata sauya?"............

_Kai tsaye gida ya shiga, alamu da yawa sun nuna tsantsar damuwarsa. Yana shiga da salama ta amsa masa babu yabo ba fallasa, ya samu guri ya zauna. Minti biyar babu wanda yace uffan cikin su, ganin babu fuska ya yunk'ura ya bar gidan. Zuciyarsa na zafi.

Kai tsaye gidansu Benahziratu ya nufa, cikin murmushi yai salama. Mamaki ne ya kamashi ganin Benazirahtu normal (lafiya) tana aikin ta. Mahaifin Benazirahtu ne ya fito da murmushi ya ce "a'a Baana barka da zuwa, saukar yaushe?" Ya shafa k'eya d'abi'ar da ta zamo masa jiki da murmushi yace. "Abbagana jiya da yamma nazo hala Benah bata gaya muku ba? Ta gani a jiyan". Cikin murmushi yace "kasan halin kayar ka", zama sukai suka k'ara gaisawa. Can sai ga Hajja Faanah ta fito, suka gaisa da nuni da hannu. Ruwa mai sanyi Benazirahtu ta ajiye masa cikin a kofin kushi, ta sake dawowa d'auke da babban a kushi ta sunkuya ta ajiye. Murmushi ya yi ya bud'e k'amshin manshanu ya yi masa salama, ya lumshe ido ganin biskin gero da miyar kub'ewa ga manshanu. Ai ba jinkirtawa ya sab'a hannun riga ya soma kwasar loma.
_Can ya d'aga murya yace "Abbagana ina ce Hajja ce tayi girkin nan ba wannan ba?". Tsaf ta kalle bakinsa, ta gane furucinsa ai kuwa ta turo baki ta hau buga k'afaffu alamun shagwab'a. Gaba d'aya suka saki dariya, cikun gurbataciyyar maganarta tace "nafi matarka iyawa". Dariya suka sake yi, Hajja Faanah na tambayar abinda Benazirahtu tace. Mahaifinta yai mata bayani da hannu._

_Bayan ya gama ta d'auke kwanukan, ya dubeta "Benah d'auko jakarki ta school (makaranta) in gani kinji", babu musu ta mik'e sai ga ta ta dawo d'auke da'ita, karb'a yayi yana duddubawa a hankali yake mata tambayoyi tana amsawa . Sossai yaji dadin yadda ta maida hankali tana karatu fiye da Marwah.Bai bar gidan ba sai gefun sallahr azahar, a ransa ya k'udiri kyautar da zai mata.
************
_Washegari kuwa sai gashi da dogayan riguna, dai-dai ita guda uku bayan sun gaisa da Hajja Faanah ya bata. Godiya sossai sukai masa, Banazirahtu baki yak'i rufuwa ya gonar audiga. Da gudu ta suri kayan ta nufi gidan wan mahaifinta, tun a soro take kwad'awa Marwanahtu kira. Tana fitowa ta hau nuna mata kayan, cikin murna tace "waya baki?" Babu komai ranta tace "Baana"........... Kafin ta k'arasa magana taji an warce kayan kai tsaye cikin murhun girki Hajja Yakura ta watsa su, wata giggitaciyar k'ara Benazirahtu tayi ta shid'e ji ka ke yif! Ta fad'i. Hakan yai dai-dai da shigowar Baana cikin kad'uwa ya furta.
"Benah!




Cikin kad'uwa yake girgizata yana kiran sunanta *Banah! Benah!! Benah!!!* amma kash! Shiru Malam yaci shirwa. Hankalinsa ya yi matuk'ar tashi da wani rikitacan kallo yake duban mahaifiyars. Sai dai kawaici irin na d'a da uwa ya kasa tankawa. Surarta yai bai zame ko'ina ba sai d'akinsa, sossai yake zuba mata ruwa ta k'i motsawa. Ya kasa kunne amma bata motsi, k'irjinsa ya dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!. "Kadai ace *Benah* ta rasu"?. Ya fad'i hakan a ransa. Can ya tuno wani bayani da akai musu a wata lecture, yayin da mutum yai dogon suma. Hamdala yayi ga ubangiji, ya toshe hancinta ya bud' e bakinta ya had'a da nasa. Ya soma musayar numfashi kafin minti uku ta soma motsi, cikin sauri ya watsa mata ruwa.

_A hankali ta zuba masa ido, can ta fashe da matsanancin kuka saboda tunawa da kayanta."Baana kayana" , ta fad'a cikin gwaranci. Janta yayi jikinsa yana shafa kanta a hankali tai shiru sai ajiyar zuciya take. Sai da ya tabbatar da ta yi shiru ya d'auko chaculate ya bata, tare da alk'awarin kawo mata wasu sababbun kayan. Da murna tai masa salama ta nufi gida. Tana zuwa ta zauna ta bawa mahaifinta labari, murmushi yayi tare da bata hak'uri ya gargad'eta da kada ta gayawa Hajja Faanah komai, saboda gudun matsala. Koda ta tambayeta cewa tayi "kayan ne sukai yawa canzowa za'ayi".

_Cikin rashin walwala ya shiga gida, Hajja Yakura ta dubeshi "wai kai dan an k'ona kayan waccan nakasshashiyar *'YAR KURMAR* kake ciwa mutane kunu? Meye abun damuwa da lamarin mutanan da suke da nakasa a rayuwar su? Mtssss!" Ta ja tsaki tana gunguni. Cikin taushin murya ya dubeta._

_"Hajja ki fahimce ni koba komai *Benah* 'yar uwata ce, kuma k'abilarmu d'aya nakasa ba zaisa in nuna mata k'yama ba. Bafa laifi sukaiwa ubangiji ya hallice su haka ba, suma mutane ne kamar kowa kuma ubangiji yana kishin su yana sonsu. Haba Hajja". Ya fad'a da sanyin murya, ai kuwa yana direwa ta hau sababi, kai kace zaginta ya yi jikinsa yai sanyi zuciyarsa na radad'i yana takaicin hallayar mahaifiyarsa.

TUSHAN LABARIN*_

_Baana d'a ne ga Alairam Modu kalmar Modu na nufin Muhammad kenan, Modu wanda akafi kira da sunan Bakura,saboda kasantuwarsa babba a gidansu. Kalmar Alairam na d'aukar Alhaji ne a yaran Kanuri ko kuma Aisami wato Alhaji. Hajiya kuma sukan kirata Aisaram, yayin da . Bakura dai haifaffan garin Mai duguri ne, su biyu iyayyansu suka haifa da k'aninsa mai suna Hamza. Sun taso cikin so da k'aunar juna, mahaifinsu fittacan Malamine wanda yake koyar da d'alibai sama da hamsin.Sunansa Aisami Muktar Bunu, wanda da yawan muta ne ke kiransa Malam Bunu. Mahaifiyar su kyakkyawar mace ce mai suna Falmata a salinta shuwa ce._

_Sun taso cikin ingantaciyyar tarbiyar da mahaifinsu ya basu, mahaifinsu mutum ne mai neman na kansa. Saboda sana'a maganin wulak'anci ce, shi kuma Kanurin mutum nan duniya ya tsani raini da wulak'anci. Haka kuma Kanuri ya tsani 'kazanta baya son rashin gaskiya da girman kai uwa uba d'aukar al'adar da ba tasa ba._


_Idan kuwa so kake ka burge Kanuri, to kayi masa kyautar gwal ko hula ko turare mazan su da matansu akwai son k'amshi. Kanuri akwai iya kula da tattalin mace tamkar k'wai, sun tsani rashin iya girki da yawan dariya. Matansu kuwa in kana son burgesu kyautar gwal da mindil. Mindil wani gyala ne na bare-bare, shigar su kuwa mata sunfi yin shigar lafayya, ko riga mai dogon hannu da mindil. Tsofaffun cikin su dama wasu cikin matasa, da yawa suna cin goro.Suna amfani da wani abu mai suna; ingwargo abun yana nan green ne(kore) in suna cin goro suna goge bakin su dashi don hak'orin su ya yi ja.Idan na tsaya yi muku bayanin Kanur sai mu kwana, saboda suna da al'adu daban-daban ababban sha'awa._

_Malam Bunu yana sa'ar d'inkin hula, sai kuma d'an hasafi da yake samu daga masu zuwa ayi musu adu'a. Hakan baisa zuciyarsa ta mutu ba kullum burinsa yaransu sui karatu domin gobansu._

_Yaransu na samun kulawa dai-dai gwargwado, sun tsaya kan tarbiyar su. Kaf d'insu sai da suka hadda ce alk'ur ani mai girma sannan suka saka su a makarantar boko. Lokacin Bakura nada shekaru goma cif, Hamza kuwa nada bakwai, sai dai mahaifinsu na yi musu lesson a gida wata rana kuma Falmata tayi musu, wadda suke kira Hajja.Fanin ilmin boko ma babu dama, sun tsaya tsayin daka da karatun su. Bakura na primary four Hamza na primary two wani muhimmin al'ammari ya tasowa Alairam wanda hakan ya tilasta masa tashi daga Maiduguri zuwa garin biu d'aya daga k'aramar hukumar jahar Maiduguri._


_Al'amarin ya samo asali ne na wata makaranta
da aka bud'e ta islamiyya a garin biu dan
bunk'asa harkar ilmin addini. Aka d'auki Malam
Bunu zuwa wannan sashi, da farko ya soma
zuwa ya dawowa iyalansa duk mako d'aya wato
kwana bakwai. Daga baya yaga rashin dacewar
hakan, saboda yadda sukai sabo da iyalansa
shawarar Falmata ya nema ya samu k'aramin
gida ya sai musu suka koma can da zama gaba
d'aya. Dama ba wani dangi ne da shi sossai ba
duk sun mutu sai k'anin mahaifinsa guda d'aya
shima ya tsufa sossai. Haka suka tattara suka
koma._
************
_*GARIN BIU*_
_Garin Biu na d'aya daga cikin k'anannan
hukumomin jahar Maiduguri.Shi dai k'auyen Biu
k'auye ne babba, wanda Allah ya a zurta su da
noma da kuma karatu.Sun d'auki karatu da
muhimmanci fiye da yadda mai karatu yake
zato.Shiya sa suka samu cigaba a cikin
Maiduguri, dama wasu garuruwan a cikin
Maidugurin. Idan kika cire ma'aikaci d'aya na
biyu zaki ga babur ne wato yaransu. Ilahirin
mutanan biu babur ne.Haka kuma ta b'angaran
noma, Mata suna yi Maza suna yi. Amma duk da
wannan noma, dole yaro sai ya bawa karatu
lokacinsa. Suna noman gyad'a masara da
barkono da kuma gauta._
_Mutanan garin sun iya zaman duniya da kissa,
da kuma wayo sai dai suna da rowa. Sanan kuma
hanyar zuwa biu bata da kyau akwai gargada a
hanyar. Allah ya horewa mutanan Biu iya
soyyaya, sun iya soyayya 'yan garin. Matan garin
kuwa suna da had'in kai tsakanin su.Mai karatu
kar kayi mamaki in nace maka, zaka ga mace ba
abinda take b'oyewa mijinta komai tare
suke.Suna tanadi da tattalin junan su._
_Idan kuwa ka shiga jami'ar Maiduguri zaka riski,
gungun d'alibai 'yan garin har taron su suke duk
k'arshen wata. Sukan yi had'in guiwa wanda ba
shi da kud'i su tara masa.Kishi da jinsin Kanuri
akwai wahala, ballantana kishi da matan garin
Biu.Kishi da su yana da wahala saboda suna da
bala'in kissa da iya kula da Miji uwa uba
biyayya._
_Wannan shi ne bayanin garin Biu a tak'ai ce,
kuma mudin akai hutun makaranta lokacin
damuna to zaki ga d'alibai mazauna Biu na
turruruwar zuwa yin noma garin su._
_Komawar su garin Biu bai kawo nak'asu a
rayuwar su ba, hasalima cigaba suka samu ta
fannoni da dama. Makaranta mai zaman kanta
mahaifinsu ya saka su, sab'anin da da suke zuwa
makarantar gwamnati.Zama suke cike da
walwala da jin dad'i, a jikin gidan su akwai
mak'ota guda biyu d'aya 'yan garin Gwaza ce
yaranta biyu d'aya sunan sa Alangubro d'ayar
kuma Aysa. Aysa na nufin Aysha, Alangubro
kuma ranka ya dad'e.Akwai kyakkyawar alak'a
tsakanin wannan mak'ota. A hanun daman su
akwai wata dattijuwa mai suna Hajja Faanah.
Hajja Faanah mace ce mai yakanah da son yara,
tun tarewar su jininta ya had'u dana Hamza
sossai. In babu makaranta nan yake yini suna
hira tana koya masa yaran su. Hajja Fannah a
salin sunanta Fatima ne, bata da yara d'anta
d'aya hamshak'in mai kud'i ne. Ya wadata ta da
komai, yana zaune a garin Gaidahm shi da mai
d'akin sa da 'yar su guda d'aya mai sunan
Hajja.Amma kash! Kurma ce haka aka haife ta
bata magana sai dai nuni da hannu. Lokaci-
lokaci suna zuwarma Hajja hutu.Kullum Hajja
cikin bawa Hamza labarin Faanah take, hakan ya
dasa masa zumud'in san ganin ta._
_Yawan bawa Hamza labarin Faanah yasa yake yawan yiwa Hajja Faanah maganarta.Tare da tsananin tausayinta a ransa, musamman da ya samu labarin kurma ce. Badan Hajja ce ta gaya masa ba da ba zai yadda ba, saboda yadda yake ganinta a hoto kyakkyawa ce sossai. Ya matsu ya ganta,kullum Hajja cikin bashi baki take saboda basa garin kwata-kwata suna Canada can Faanah take karatunta. Kwanci tashi Bakura ya gama makarantar gaba da primary lokacin Hamza na aji biyar, Malam Bunu ya sama masa admission a jami'ar Maiduguri fanin Islamic. Haka suka cigaba da rayuwarsu abin sha'awa, Hamza na mataki na biyun k'arshe mahaifinsu ya rasu, sakammakon annobar amai da gudawa._

_Mutuwar ta girgiza su sossai, Hamza sai da yayi sati a kwance a asibiti. Cikin k'ank'anin lokaci suka zama abun tausayi, Hajja Faanah ce take taimaka musu da abinci da hidimar yau da kullum.Tilas Bakura ya hak'ura da karatu ya rungumi noma, saboda tallafawa rayuwar su. Kwanci tashi Hamza ya zana jarrabawa, ta fito ranar Hajja har walima ta shirya masa.Bayan watanni biyar sakammakon sa ya fito, sakammako yayi kyau sossai Hajja da kud'inta ta sama masa gurbin karatu, a jami'ar Maiduguri. Lokaci zuwa lokaci yakan ziyarci garin Biu, hakama Maiduguri wajan k'anin Kakansu.Haka ma lokacin noma yakan zuwa sui noma ya koma .Hamza ya dage karatu yake sossai yana karantar fanin kunne.Kullum Falmata na nunawa Bakura da Hamza su rik'i Faanah da muhimmanci ko bayan ranta. Bayan shekara d'aya da rasuwar Malam Bunu lokacin Hamza na level one kwatsam, Hamza na zaune a gidan Hajja Faanah suka ji salama. Hajja ta mik'e tana murna cikin yaransu tana raira wak'a abin gwanin sha'awa ta rungume wata kyakkyawar mace tamkar balarabiya. Cikin kulawa tace._
_"Barka da zuwa, barka da zuwa". "Da alamu dai bak'in na musamman ne", Hamza ya fad'a a ransa. Karaf idonsa ya sauka a kan namijin da yarinyar kusa dashi wadda bata gaza shekaru goma sha hud'u ba. Murmushi ya sub'ucewa Hamza saboda, ganin Faanah yau bayan tsayin lokacin da Hajja tai tana bashi labarin ta._

_Zahiri ya santa a hotunan ta wanda suka cika d'akin Kakarta, cikin murmushi ya dubi Hajja yace"yau dai naga takwarar Hajja". Gaba d'aya hankalinsu ya dawo kansa, cikin murmushi mahaifiyar Faanah tace._
_"Hajja wannan waye"?._
_Hajja tai murmushi, "sunansa Hamza mak'ocin mune d'an wajan Malam Bunu da nake baka labari a waya. Cikin murmushi yace"Masha Allah" bayan komai ya lafa suka zauna, ana ta hirar yau sha gamo. Hamza ya mik'e yana murmushi, yaiwa Hajja salama zuwa gida_

_Cikin walwala ya shiga gida yana bawa Hajja Falmata labari, cikin farin ciki tace "yau dai buri ya cika an ga Fauna", murmushi ya yi shigowar Bakura ya katse musu hirar da fara'a yake tambayar abinda ya faru. Hajja ce take bashi labari, da murmushi yasa hannu a aljihu ya fito da kud'i naira dubu biyu."Maza je kayo cefane a sauki bak'i", dan dad'i rungume Bakura yayi yana murna"karka damu awaana" awaana na nufin d'an uwa._

_Cikin sauri ya nufi kasuwa ya siyo nama, tare da kayan amfani. Nan da nan Hajja ta hau hidimar bak'i, biskin gero da miyar kub'ewa tayi musu yasha manshanu gefe kuma soyyayar kaza ce. Ni kaina sai da nayi sha'awa. Hajja na gamawa, ta had'a masa ya d'auka sai gidan Hajja._

_Kai tsaye gidan Hajja Faanah ya nufa, cikin nutsuwa ya yi salama. Daskarewa ya yi saboda mamaki, ba komai ya haddasa masa hakan ba face ganin Faanah. Durkushe take gaban d'an magen Hajja tana wasa da shi. Bai tab'a zato haka kyanta yake ba, kwata-kwata a hoto munninta ya hango. Gashinta ya rufe mata ido saboda yawansa da santsi, gyaran murya ya yi yai salama daga ciki Hajja ta amsa. Ya shiga yana murmushi ya sauke farantin hannunsa wanda aka jera kayan. Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sannu da k'ok'ari Hamza, hada hidima"?. Cikin murmushi ya sunkuyar da kai, mahaifin Faanah ya bishi da kallo yaron ya birgeshi sossai cikin ransa yana k'udirta wani lamari._

_Murmushi yayi ya fito zuwa tsakar gida, a hankali ya zauna yana fuskantar Faanah yana murmushi. Cikin barbanci ya ce"ba magana k'anwata?", da hannu ta nuna masa alamun bangane ba. Hamza yai murmushi a fili ya furta "kash! Tsutsa baki cin ragon goro", cikin tausayawa ya dinga kallonta. Fitowar Hajja yasa ya mik'e yana dubanta yace, "Hajja ina so mui magana da takwararki ban iya ba". Murmushi tayi "da sannu zaka iya Hamza rai dai" , murmushi yayi ya kad'a kai yayi wa Hajja salama ya wuce._

_Bakura noma yake sossai, Allah yasa masa albarka. Ubangidansa mutum ne mai saki masha Allah cikin ikon Allah, ya had'a shi da wata budurwa a wani aikin gona da ya fita yi mai suna Yakura. Yakura masifaffiyar yarinya ce ta bugawa a jarida, irin matan nan ne gansama-gansama masu suffar k'irar doki doguwa ce mai tsayi kakkaura. Bak'ace ba can ba tana da tsage guda biy-biyu a kumatunta wanda suka fito da fuskarta sossai hancinta mai tsayi sossai. Tana da yalwar gashi. Asalin mahaifanta 'yan garin Gamborun kukawa ne aiki ne ya kawo su garin Biu. Mahaifinta mutum ne mai mata biyu, da yara guda goma sha biyu. Yakura itace babba mahaifiyarta mafad'aciyyar mace ce. Sunanta Yagana, su biyu ne mata a wajanta ita da k'anwarta Yalfata. Sai maza akwai Alanguburo, Barma Hamza da kuma Muktar. Kishiyarta Yawuri yaranta duk mata ne, hakan ya haifar da k'anannun maganganu tsakanin zaman Babbar 'yarta itace Kundum yarinya mai hak'uri sossai, sai mai binta Bintu da Findu sai kuma Yazeyi da autarsu Yalta.Zaman gidan wani irin zamane na ishasshiyar mace hakan yasa mahaifiyar su Kundum bata da sakewa sossai asalinsu 'yan garin Askira ne .Kundum na aure a Gwaza Bintu a nan Biu Findu ce take Maiduguri Yazeyi Askira take sure sai auta Yalta dake karatu._

_Tunda Allah ya had'a Yakura da Bakura, suke wa juna. Yakura ta shiga ta fita ta hana zuciyarsa sukuni. Daga ita har mahaifiyarta, saboda bata son ya kub'uce mata. Dalili duk wanda yazo neman auranta yaji bata da mutunci guduwa yake, hakan yasa su kaiwa Bakura ruk'on talalla ya

Please Login or Register in order to submit comment