Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

business kan shiga da barkono kasar Chine nan da nan suka samu hanya.
Kasuwancin daya haifarsu da cigaba sossai, Baana shi ne mai kula da harkar sossai.Kafin watanni Dr ya samu kudi sossai,ya canja mota mai kyau da tsada ya siyawa Bakura mota mai saukin farashi.Cikin ransa ya kudiri kai Baba Isah Hajja da Bakura saudiyya habu wanda ya tuntuba cikinsu saida ya gama komai.Hajjansu atabau tace sai dai yakai Faanah ita ta hakura aka kada aka raya tilas aka kyaleta.

Lokacin da Yakura ta samu labarin tafiyar,rushewa tai da kuka tana Hamza baya kaunarta ya rasa wazai kai Makka sai kurma, me Kurma zata iya a saudiyya?.Baana takaici ya isheshi ya rasa yaushe mahaifiyarsa zatasan Annabi ya faku.Har gida Hamza yazo ya bata hakuri tare da alkawarin kujerar Hajji.

Kwanci tashi su Beenah karatu ya mika har sunci samister daya, a dai-dai lokacin su Hajja suka dawo Saudiyya suka sauka a Maiduguri.Dama an zuba komai a kowanne sashi dangin AC carpet kayan kallo kujeru da kwabar turare da sauran kayan bukatu.Washegari su Bakura da Yakura da Marwa suka nufo garin Maiduguri.Shi kenan sukaiwa garin Biu hijira,makota an rabu cike da muruntawa.Gidan Hajjan Faanah Hamza yasa aka rushe da nasu aka gida makaranta babba hade da masallaci mai suna.
_HAJJA FAANAH ISLAMIC COLLAGE OF QUR'AN_,makarantar ta ginu sossai Dr ya saki kud'i aka k'awata makarantar aka zuba litattafai d'alibai kyauta.

Baana da mahaifinsa su suka cigaba da ziyartar Biu suna kulawa lamarin noma da kiwon kifi.Tafi-tafi ragamar ta koma hannun Bakura kacokan saboda yanayin aikin Baana da kuma Dr shi Dr na kula da shige da ficen kayansu zuwa China.

Dawowarsu Maiduguri ya samawa Beenah walwala, wani sashin kuma takaici saboda yadda kaunar Baana take mata barazana.

Toshima nasa fannin abun sai addu'duk yadda yaso bayyana mata kudirinsa in ya tuna Hajjansa lamarin dagula masa lissafi yake. Akwai ranar da Marwah ta shigo dakinsa ta tarar yana kallon hotansa a guje taje ta kaiwa Yakura gulma ai kuwa sai gata tana bambamin fada zahiri hotan ta gani hannunsa lamarin daya girgizata ta shiga fada babu ji babu gani.

Bai tanka ba sai hakuri daya bata, abin takaici kwatsam yana fitowa ya hangi Beenah da Samar ya hango suna hira da kyalkkyala dariya wani abu ya tokare masa zuciya kallon da yai mata ya sanyayyar mata da jiki tana gaisheshi ko kulata bai ba yana tambayar Samar ysushe yazo yace masa dazu ya shigo sunzo claring din kaya ne a sanyaye ta bar wajan zuwa cikin gida Samar ya wuce sashin baki.

Cikin sauri ya cimmata a corridor ya tsareta da mayan kallonshi, "wato karatu yasa kin soma zama mara kamun kai ko?" Ji tayi tamkar ya dab'a mata wuk'a a makoshi ta kanne kawai ta sunkuyar dakai tsawa ya daka mata ta dago a rikice"wato dariyar takima kowa kike yiwa ko? Uban me yake cemiki?". Ta turo baki kamar zatai kuka "kawaifa cewa yayi ina burgeshi...." bata karsaba ya kaiwa bakinta bugu hada jini aikuwa shar sai hawaye ya murza yatsu.
"In kara ganin dariyar nan wajan kowane gardi saina mazgeki, kauce bani gu".

Da gudu ta wuce tana shasshekar kuka, aikuwa da yamma Samar daya shigo babu kowa sai Baana a falo dai-dai lokacin ta kawowa Baana copy da cake, yana murmushi yace "nima zanci". Tsare gida tayi babu ko digon murmushi Baana yai murmushi yace "kawo masa saida tai jim sannan ta kawo.Shima Baana ta mikawa ya bashi jiki a sanyayye ya amsa nan da nan Baana ya saki jiki dashi suna hira. Bai jimaba yai masa rakiya ya wuce.
[

Yana shigowa ta sake shan mur, ya gimtse dariyarsa yana dubanta.
"Beenah Hajja na ciki?".
"Bacci take".
Ta bashi amsa a takaice yace.
"Da kyau ta gidana, kin burgeni walahi yanzu ki gayamun wa kike so?".
Murmushin takaici ta yi ta ce, "Babu kowa".Ya ce "ki fad'amun gaskiya bana son karya".Mamaki ya cikata da wannan salon na Baana tace "ka kyale ni nace babu kowa,na lura yanai mun maganar aure ne ni kuma ko'ina sonsa...... "
"Ke!!!".
Ya daka mata tsawa ya murza yatsu "ki kiyayeni" yai waje fuuu!.

Kanta ta sunkuyar k'asa tana jin-jina lamarin Baana a ranta, ta goge hawaye da kyar ta shige dakinta.Cike da tunani kala-kala a zuciyarta.Wani abu ya lullub'e zuciyarta,ta kasa tantance ko miye.Tana ji bata da wani amfani in babu Baana a rayuwarta, saidai kasancewarsu tare tanajin (impossible) abune mara yiwuwa.

Baana kuwa yana fita ya saki ajiyar zuciya, zuciyarsa cike da tashin hankali.Tabbas yasan ba zai taba boye son nata a zuciyarsa ba idon ko zai cigaba da boyewa to zai illatashi.A filli ya furta.
"Allah ka bani Beenah my unique".

Kwanci tashi aka soma gudanar da lamarin bikin Mansu da Aslam lokacin suna second samister, sun shiryawa bikin sossai fannin ango da amarya kowa murna yake sunyi kamu ranar Juma'a,aka daura aure aka taho da amarya Maiduguri.
Tunda aka daura aure a Kano a ka taho da Aslam Maiduguri,nan aka fara sabon biki.Sossai Faanah ke kulawa da ita da irin kayansu na Maiduguri.
Haka kawayan amarya dakin Beenah sukaiwa tsinke duk cikinsu jinin Beenah da Mufida yafi haduwa sosai komai tare suke yi.

Asabar zasui dinner da dare hakan yasa tun safe Beenah da Mufeedah suka je akai musu kunshi ja da baki, yai musu kyau das! Su ka wuce akai musu gyaran kai da jiki suka fito chas tamkar amare.A hanzarce suka koma gida lokacin an yi la'asar gashi Aslam ta takura musu da kira.A hanzarce suka karaso suka kama aikace-aikace daganan suka amso d'unkunansa.

Shigar doguwar riga sukai su biyun gown, ta materil kalan _golden with yellow_dinkin ya zauna das, daga kasa an masa baza ta bude sossai fuskarsu tasha kwaliya sossai sukai ado da white gold takalminsu hills mai tsanin tsini zaiba da jaka karama sai wani mafici karama shima kalar.Kansu head ne blue ya yi musu kyau sossai sun kammala shirinsu cas.Mufeedah sai bin Beenah take da kallo tana tasbihi kaf wajan bata ga wadda tai kyanta ba.

Huremata ido tai tana murmushi tace.
"Yadai?".
"Kinyi kyau Beenah".
Dariya tayi "kema haka".
Kai tsaye suka fito harabar gidan duhu yayi sai hasken inji,kowa ya hau motar zuwa dinner banda su sabida Munzali ne zai kai Mufeedah ita kuma Beenah duk da bata so hakan ba.Cikin nutsuwa suka ratso harabar gidan yuuu!Idanu suka dawo kansu, cike da salon yanga suke tafiya.Karaf idonta ya sauka a kansa,zaune yake shida abokansa sunata fira shi kuwa yayi gum.Cikin takunta wanda ba kowacce mace ta iya ba, ta taho da nutsuwa gaba daya kamshinta ya cika wajan Mufeedah ce tai baya ta koma gida tilas ta tsaya jiranta.Idonsa a kanta yana tasbihi ga Allah suna hada ido ta lumshe yai saurin daukewa.

"An yi dan kai kuma ka yaba".
Ta fada a ranta, kasa kasa ta zaro wayarta tana amsawa tana satar kallonsa.Ta cigaba da amsa wayar, batai auneba sai jinsa tayi kusa da ita ya wuce.
"Kisameni a ciki".
Dam! gabanta yai mummunar faduwa, ta jima tana,wasikar jaki tai shahada tabi bayansa.


A dakinsu babu kowa yan matan sun wuce, tana shiga ta sameshi zaune kallon daya wurga mata yasa jikinta mutuwa ta zube a kan gado kanta a kasa.

"A hakan zaki fita ko? Wato kema kina biyewa yan iskan kawaye ko? Walahi kikaje dinner din nan saina mummunan bata miki"?

"Awaana..... "
"Enough!".
Ya fada da tsawa yai waje,cikin takaici ta tuge head din ta fashe da kuka,tana man zaune Mufeeda ta shigo ta kada ta raya Beenah ba magana sai kuka saida tayi me isarta ta dubeta.

"kije bazani ba".

Ta kaleta da sharin fahimta"da kin tabbata mara kirki".

"Allah kima tafi bani zuwa".

Mikewa tai a fusace tabar dakin, tana nan zaune wayarta nata ring kiran Samar taki dagawa ya shigo ya dauki wayar ya zare sim din ya tauneshi ya watsar ya bude wayarsa ya ciri wani layin special da baya amfani dashi ya saka mata ya zauna.

************************.
Cikin k'unar rai ta d'ago amma ga mamakinta yai mata wani kwarjini ta sadda kanta k'asa zuciyarta na zafi.
"Beenah kina jin zafina ko?"
"A'a awaana".
"Hmm! Nasani Beenah zafina kike ji, tashi ki gyara fusksrki mu je wajan dinner".
Jin batunsa yas wani farin ciki ya ziyarci zuciyarta, cikin bazata amma gudun b'arar da aji yasata kannewa.

"A'a awaana ka barshi an kusa tashi ma".

"Kitashi nace!".
Ya fada da kakkausar murya, tuni ya koma mata ainihin Baana d'insa nan da nan ta mik'e jiki na rawa ta kafa gwaggwaronta ta mik'e.Dariya ta kamashi ganin yadda ta tsorata,a ransa yace "Allah sarki my unique".
"Gyara fuskarki tukun, ko so kike asan naci zalinki?".

Ba musu ta gyara fuskarta, tsaf ta fito kamar ma tafi farko kyau ji ya yi kamar ya rungumeta saboda yadda zuciyarsa ke harbawa".

Cikin nutsuwa ta dinga bin bayansa, harzuwa bakin motarsa sabuwa dal gidan baya ta shiga yai murmushi.
"Dawo gaba koni drivernki ne wannan sai Samar?".

Ras! Gabanta ya fad'i,"karfa Samar ya jamun sallalar tsiya ina amfanin badi ba rai?".

Lumshe ido tayi lokacin da ta samu mazauni a gaban motar, saboda sassanyan k'amshin tsadaddan turarransa had'e dana jikinta da kuma sanyin Ac da suka had'e suka zama ababbe masu kwantar da zuciya.Cikin shauk'i ya tada motar, suka soma tafiya cike da nutsuwa ya ware volm wak'ar na tashi a hankali.

"Love me! Love me!! Say that you love,Kiss me! Kiss me!! who you do you miss me".

Wata kasala ce ta ziyarci gab'an jikinta, duk ta takura sautin wakar na mintsinar zuciyarta gashi data dago saita riski idanunsa cikin nata.Kwata-kwata ya haifar mata da mutuwar jiki can ta aro juriya ta yafa.

"Awaana yaushe zamu je Biu?".

Yabasar kamar bazai amsaba,sai taji haushin kanta dan haka taja bakinta ta tsuke.
"Me zaki yo?".
Bata kalleshi ba ba kuma ta amsaba, yai murmushi kawai ya cigaba da tuk'in wucewar mintuna goma.

"Beenah dake nake".
Ya sake magana karo na biyu, ta muskuta kawai ta motsa bakinta wanda yasha lipstick yai kyau sossai.

"Au! Ban ji ba,kasan kunnuwan sai a hankali.Ganin Falmaht zani".

Dai-dai lokacin suka k'araso yai murmushi ya lakaci hancinta".

Harabar wajan shake take da mata da maza, kowa yana wane wannan a hankali Baana ya fito daga motar yasha kunu hakan ya kara fito da kyansa tsayyayan dirarran namiji kasumbar nan luf.Beenah ta lumshe ido tana san tsayuwa gefansa tana shaka, fahimtar hakan yasa ya dawo baya ya rankwafa saitin kunnuwanta yai mata rada.

"Madam ki saki jikinki".
Jitai kamar ta suma saboda jin dadi, karaf Mufeeda tai saurin daukarsu hoto batare da sun ankareba jerawa sukai zuwa cikin hall din tun a bakin kofa kallo ya dawo kansu tamkar wasu taurari.Tashin hankali Marwa na shirin kai kofin lemo bakinta tuni ya subuce zuwa jikinta, farin ashobe dinta ya wanke da ruwan lemo.Kwata-kwata rasa matakin dauka tayi har Baana yai mata rakiya zuwa wajan su Mufeedah yai musu sallama.Nan da nan 'yan mata suka hau lankwashe murya suna amsawa, Beenah ta tsare gida murmushi ya yi.

"Muffy ga amanar kanwata nan, zan shiga cikin taro Madam na jiran".

Bai jira cewarta ba ya wuce yana gimtse dariyarsa, ganin yadda ta hade fuska kwata-kwata ya gama fuskantar sirrin zuciyarta.A ransa dadi yake ji da ba shikadai yake kidi ya yi rawarba.
Nan da nan hankalin matan wajan ya dawo kan Beenah"gaskiya kin mori yaya mudai muna kafun kafa" aranta haushin su take tana fadin.

"Na mori yaya kona more miji?".

Bata an kara ba sunanta dana Baana ya fito cikin wanda zasu bada takaitacan tarihin amarya da ango mintuna biyar suka shude sannan suka fita.Cikin harshan Kanuri Baana yake bayani, cike da nutsuwa da haiba yana ajiye abin magana waje ya dauki tafi.Beenah ta fiti cikin salon jan hankali take tafiya, harta hau step din Baana ya lumshe ido bayanta kawai abin kallo ne duk sai ya ji haushin kansa daya bari tazo wajan.Murya mai cike da dadin sauti ta soma bata labarin amarya harta gangaro in da Aslam ke burin auran kabilarsu ta Kanuri sabanin nata kabilar.Ta jinjina mata tare da cewa"Aslam yau buri ya cika gaki cikin kabilarmu kuma muna sonki, muna maraba dake duk da kasancewarki jiri ba jirinde ba". Aslam tai murmushi tana jinjinawa Beenah.Cikin nutsuwa ta dawo ta zauna, illahirin wajan ta burgesu.Take jerin yara suka soma shigowa shida mata shida maza cikin shigar Kanuri suna rike da wasu kaskwaye masu fida sassanyan kamshi suka zagaye amarya da ango nan fa aka fara kida.

Bayan komai ya lafa aka soma serving din mutane, Baana na gefe hankalinsa na kan Beenah haka ma Samar itama Beenah da Marwa hankalinsu naga Baana gwarzon maza.


Can Marwa tai nasarar zuwa ta zauna wajan Baana, a hankali ta dinga jansa da fira tun yana basarwa harya biyemata yana murmusawa.Sai dai rabin nutsuwarsa naga Beenah saboda yadda ya lura Samar na bibbiyarta da kuma wani a gefanta shima Kanuri ne ya gane hakan ne da tsagensa.Kafin ya ankara ya hangoshi kusa da ita, itama takaicin kula Marwa data hango yana yi ya haifarmata da son kula Marwan, wanda a lokacin yai mata bayanin kansa soka ne dan Maiduguri iyayansa da kowa nasa na garin Askira aikine y kai shi Abuja.Biye masa tayi suna hira, koba komai ta lura besan mu'amalarta da wasu mazan tana jin dadin hakan dan haka ta saki jiki sa Samar dariya take masa sossai fararran hakoranta yar-yar na haskawa amma kasan zuciyarta kamar garwashi.

Marwa sai zuba take ya kanyar da babu dadin sha, ta juyo taga Baana idonsa na kan Beenah sai huci yake idonsa jajjur aikuwa tsabar takaici kasa magantuwa tayi.Cikin sassarfa ya mike, Beenah da rabin nutsuwarta na kansa tana hangoshi tai saurin cewa"Marwan tashi ga Awaana na nan ya hanani kula kowa kar yaima rashin mutunci". Marwan ya hadiye wani abu mukut"aidama kema hankalinsa na kanki ba inda zani ya kashe ni" "Marwan ka tashi!". Ta fada da tsawa dai-dai lokacin ya iso bai wata-wata ba yai mata wata wawar fincika tai lau zata fadi Marwan yakai hannu zai tareta Baana ma haka bisa akasi hannun Marwan ya riga nasa rikota aikuwa bai auneba ya sauke masa kyawawan mari guda uku rigis wani irin figa yai mata ta kasa katabus sai janta yake tamkar rakumi da akala har cikin mota ya jefata yasa mukuli ji kake kum.Cikin masifa ya koma hall din hankalinta ya tashi da ganin yanayinsa.Yana shiga ya damki wuyan Marwan da kyar aka bambareshi ya fito yana hucci.Wani mugun birki yaiwa motar ya jata ya soma sharara gudu.


Tunda ya soma gudu take kuka mai cin rai, Baana kuwa tsabar takaici ya kasa magana kukanta na taba zuciyarsa.Suna gab da shiga gida ya dubeta"yi mun shiru kona babbalaki in kuma in saukeki ki koma wajan dan iskan saurayin naki to ki bude baki kimun magana.Wato kema ina yabanki sallah zaki kasa alwala ko? To walahi bari Abbagana ya dawo seminer cewa zan masa ya cire ki makarantar ya miki aure tunda auren kike so". Gum tayi zuciyarta cike da tashin hankali, suna shiga harabar gidan ya dubeta "ki biyo ni daki" bai jira cewarta ba ya buga murfin motar ya wuce

42
Cikin hanzari ta gyara kwabarta, "suma ta yi" da gudu sukai sashin da taimakon Hamza ta dawo hayyacinta zata soma surutai Baana yasa akai mata allurar bacci.Kafin ta farfado an sada Bakura da makwancinsa.Yakura ta shiga tashin hankali sossai, danginta duk sunzo hada mahaifin Marwah.

Baana ya rame matuka ko abinci baya ci sossai, saboda zuciyarsa kwata kwata na zargin da hannun mahaifiyarsa a lamarin.Ranar kwana na uku na nesa sun soma komawa gidajansu amma banda mahaifin Marwa da mahaifiyar Yakura sai an yi bakwai.Beenah ce ta hango Baana ya yi tagumi duk ya fita hayyacinsa can ya mike ya koma sashinsa.Mikewa tai ta hada masa lafiyayyan abinci ta shirya a faranti ta nufi sashin babu kowa a ciki sai shi kadai tana shiga gabanta ya fadi ganinsa yana kuka cikin hanzari ta tareshi.
"Haba Awaana kowa ne mai rai mamaci ne, addu'ace ta kamaci Abbu kadai nai masa kuka babu kyau".

Hannunta ya rike yana rawar sanyi, "Beenah kaine ciwo kamar zai tsage". Taba kan tai zafi rau kamar wuta ta mike ta dauko ruwa da tawul tana daddana masa harya sauka ta matsa yaci abinci yasha magani.Sannan ta koma sashinsu taiwa Hajjansu bayani, haka ya kasance tsayin kwana biyu tana kula da Baana harzuwa lokacin Yakura nata iya magana.Ranar kwana na biyar suka tashi da tashin hankali Yakura barin jikinta ya shanye,ranar Baana yai kuka kamar bazai rayu ba tilas aka wuce babban asibiti da'ita.

Har akai bakwai batasan wanda yake kanta ba, tilas mahaifin Marwa ya juya zuwa Askira ya bar Yagana tare dasu.Kwanci tashi watan Yakura biyu a asibiti aka gaji aka dawo gida da ita duk wata hidima tata Faanah da Beenah ne suke yi Baana kullum cikin gode musu yake haka Hamza baya gajiya wajan nema mata magani.

Marwa kuwa kota kanta bata bi, Beenah kullum da safe ita take wanke mata jikinta ta wanke kayan data bata ta feshe dakin da turare ko ina kal-kal yaita kamshi haka abinci mai ruwa-ruwa take girka mata ta kawo mata ta zauna ta bata bata damu da zubowar da yake yi ba zata goge ta kwantar da ita sannan ta tafi school.A hankali ta soma daukar zam-zam kullum tana karanta bisimillah kafa goma shatara ta toma ta shafemata jikinta cikin kwana uku bakinta ya dawo daidai maimakon karkacewar da ya yi. Ta soma magana, amma babu wanda taiwa magana tunda taiwa Beenah so daya ta roki alfarmar tai shiru karta gayawa kowa.


*************************
A gajiye Beenah ta shigo saboda test, tana shiga wajan Yakura ta wuce ganin Baana ta saki murmushi tana tsokanarsa "Barrister dazu Abbu yace mun aiki ya samu masha Allah saura amarya". Wani kallo yai mata cikin sanyin jiki yace"Beenah wadda nake so bata sona, dam gabanta ya tadi ta maze.

"Wa kake so zan nemama amincewarta".

"Beenah kece ke nake so".

Tamkar saukar aradu maganar ra dira a kunnuwanta, ta dago kai tana girgiza kai"a'a Baana bani bace Marwah ce,Marwah kake so kuma Hajja ma ita take so".Da gudu ta juya zata bar sashin cak ta tsaya dalilin jin sautin daya ratsa kunnuwanta.

"Beenah kema ina sonki, walahi kin fiyemun Marwah so dubu yau ina alfahari da abinda na tsana shiya nunamun soyyaya ta gaskiya.Shi yasa ake so bawa ya kyautatta zato zo Benahzirahtu yar albarka".

Muryar Yakura kenan cikin sautin kuka mai cike da nadama, zubewa Baana yai yana sajjada shukuriyya ya rarrafo gabanta. "Hajjana yaushe kika soma magana?" "Beenahnka ce sila Baana ita tai mun addu'a ka tambayeta".

Ya kafeta da ido"wai haka?" kai kawai ra daga masa, dai dai lokacin Dr ya shigo yana murmushi hannunsa rike da magunguna ya karaso duk yaji abinda suka fada ya dubi Yakura.

"Masha Allah sauranmu kafafunki ubangiji ya tashi kafadunki".

"Dr na zalunce ku, kuya femun,dan Allah ku kiramun Hajja da Faanah da sauri Beenah ta juya ta kirasu tana jin farin ciki mamaki da al'ajabi a zuciyarta. Tare suka dawo.Suna shigowa tasa kuka tare da riko hannun Faanah.

A hankali ta dinga labarta musu komai, kafin ta gama gumi ya mamaye kowanansu ba kamar Dr Faanah kuwa tayi zuru Hamza ke mata bayanin wasu abubuwan da hannu wani lokacin ta dubi Yakura ta zare ido wani lokacin ta share hawaye.Tana gamawa ta fashe da kuka ga mamakinta Dr ne yai murmushi tare da Hajja.

"Kaddarar Allah kenan Yakura, ajalinsu ne yazo a hakan kece sila mudai mun yafe miki ubangiji ya kyauta gaba sauranki neman afuwar yan uwanki da ubangijinki.

"Bazan yafe jinin mahaifina ba".

Muryar Baana kenan,kyakkyawan mafi Dr ya zabga masa cikin fada ya soma magana kamar zai shid'e. "Kana da hankali kuwa? Mahaifiyarka ce fa ko kamanta matsayinta a wajanka?. Kana da abin biyanta kuwa a rayuwa? Kamanta cewar.
Ubangiji ya yi gargadi kan mutumin dake daga murya a sama data mahaifansa musamman mahaifiya.Dan kana takama matsayinka na barrister ribar me zaka ci in ka tozarta mahaifiyarka?".

"Yanzu Abbagana sai mu take gaskiya, kan son zuciya?".

Beenah ta dubeshi.

_Awaana kana tare da nutsuwarka kuwa?Hakika iyaye suna da babban matsayi a musulunci domin Allah mad'aukakin sarki ya yi gargad'i da kuma wasiya ga ‘ya’ya maza da mata akan su kyautatawa iyayensu, tare da yi musu duk abin da suke bukata matukar bai sabawa fadar Allah da kuma fadar manzo{ S.A.W } Ba. Allah mai girma da daukaka ya yi gargadi da kuma kwadaitarwa a cikin wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma kuma ya yi bayanin rahama da baiwa tare da samun yardarsa ga duk wanda ya bi iyayensa kuma, ya yi tanadin azaba ga ukuba ga wanda duk ya fandare kuma ya kuntatawa iyayensa, tare da yi masa mumunan sakamako a ranar tonan asiri wato ranar alkiyama._

_Allah mad'aukakin sarki yana cewa a cikin alkur’ani ma girma: mun yi wasiya ga d'an adam game da mahaifansa biyu da kyautata musu, Mahaifiya ta d'auki cikin ka/ki a wahale kuma ta haife ka/ki a wahale, cikinka da yayenka wata talatin ne duk cikin wahala.To acikin wannan aya Allah mad'aukakin sarki yayi mana wasiya wato mu ‘ya’ya akan mu kyautatawa iyayenmu musamman mahaifiya wato uwa, wacce saboda irin tsanance tsanance da ta shiga tun farkon samun ciki har zuwa ranar haihuwa wanda yake ita ce rana mafi shiga tsanani a gareta domin lokacin da mace ta gurfana zata haihu, inda zaka dauko allura ka soki idonta da ita to bazataji komai ba"._


Jikinsa ya yi sanyi ya zube yana kuka yana neman afuwar mahaifiyarsa,Yakura tana share hawaye ta kasa cewa komai.Marwa ta shigo babu sallama babu wanda ta tankawa Dr ya daka mata tsawa take jikinta ya kama rawa ta nemi waje ta zauna nasiha yai musu sossai ya kafa dokar Beenah da Marwah ne zasu ke kula da Yakura daga yau Faanah ta huta Baana yaji dadin hakan nan ya jamata kunne kan saura yaji wani zance.



Kwanci tashi Beenah na bawa Yakura kulawa sossai haka Dr cikin wata biyu ta yi bul-bul da ita Marwa dai tattara kayanta tai ta koma wajan Yagana ta kwashe labarin komai ta gaya musu aikuwa mota guda suka yo suka kare mata zagi tare da cewar babu su babu ita.Ranar Yakura tasha kuka wadda ta raina ta ci kashinta ta ci fitsarinta ita ta tona mata asiri sabanin mutanan da taiwa muguwar tsana.

Kwanci tashi asarar mai rai ras Yakura ta warke ranar sun sha murna da farin ciki,saukar alkur'ani Beenah da Baana sukai bayan wata daya Dr ya sata a mota har Biu suka je tare da su Baana ta nemi a fuwarsu suka yafe mata Dr yai musu alkhairi anan suka samu ana shirin aurar da Marwa zata auri dan wan Babanta.Sun ji dadi sossai tare da alkawarin zuwa taron bikin.


Bayan dawowarsu da sati biyu komai ya yi dai-dai Yakura da Faanah in ka gansu sai ka dauka ya da kanwa ne sossai take taimaka mata wajan ayyukan gida.


Beenah da Baana soyyaya babu kama hannun yaro, dama Hajja Yakura ce matsalarsu kuma ta bada kai bori ya hau nan da nan suka mane Aslam tafi kowa murna lokacin tana laulayin cikinta dan wata hud'u.

Kwanci tashi aka tsaida maganar auran Beenah da Baana, dangi kowa murna yake ya rage saura wata daya bikin akai bikin Marwa aka kaita garin Gwaza mijinta dan sanda ne mai kirki babu laifi.Dai-dai lokacin Yakura ta fita takaba, duk ta yi sanyi yanzu har makarantar islamiyya tasa Dr ya yanko mata form take zuwa.Ganin nutsuwarta yasa Hajja ta yanke Dr ya aureta kota kara samun jikoki,Faanah ta soma tuntuba babu jinkirtawa ta amince hakan yasa ta tunkari Dr.

Sun sha fama kafin ya yarda,su Beenah basu san abinda ke faruwa ba kawai sai wayar gari sukai an daura aure aikuwa sunyi murna sossai babu kamar Baana dan bayasan yai nisa da Yakuransa yanzu wani ji yake da ita yo dama yaji da ita balle yanzu data sauya hali.

Beenah na shiga level two aka soma hidimar biki, dangi daga Gwaza Damaturu Askira Biu Kano ko'ina gidan nan babu masaka tsinke Beenah ji take kamar almara yau zata auri burin ranta.

Ranar Larabar sukai kamu, tare da Kanuri day salo mai nishadantarwa shigar Kanuri akai zala an yi barin turare sossai an ci biskin gero da miyar kuka ko kubewa ko taushe ko agushi da man shanu da kakide sai wanda ka zaba. Daga nan sai dinner ita kuma ranar Alhamis. Juma'a daurin aure da yamma aka kai amarya.

Gidanta ya kayatu masha Allah ta lumshe ido

Please Login or Register in order to submit comment