Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa koda motsi balle guduwa. Komai ya rarrumo to Yakura ce mutum ta farko, hatta da Hajja da Hamza ya tsaya da hidima da su hakan ya soma kawo nak'asu a karatun Hamza._

_Kwanci tashi kwannan su Faanah uku a garin Biu, zuwa lokacin sun yi wata irin shak'uwa da Hamza sossai, in basu ga juna ba kamar sa yi zazzab'i tun Hamza bai iya maganar kurame ba har ya koya.Faanah gidan su Hamza take yini suna hira abinda ya bashi mamaki har rubutu ta'iya in ya fad'a Hajja ta kanyi murnushi tace "nakasa bata hana bawa zama managarcin mutum"._

_Kwatsam ranar wata Asabar ana saura kwana hud'u su Faanah su koma Canada, tana gidan su Hamza suna hira suka samu bak'uncin Yakura da Yelta. Lamarin da ya haifar da rud'ani cikin zamantakewa............_
_Tunda sukai salama suka shigo Yakura ta kasa d'auke ido akan Fannah, zuciyarta na wani irin suya tsananin kishi ya kasheta. Bakura ya kasa tsaye sai nan da nan yake yi da su. Zama sukai suka gaishe da Hajja ta amsa da fara' a. Hamza kwata-kwata yak'i kallonsu ko d'aya Yakura bata birgeshi, sai da Bakura ya yi masa magana sannan ya juyo ya gaishe su. K' ur! Idanun Yalta a kan Hamza, zuciyarta ta shiga bugawa nan da nan so yai mata dabaibayi. Fuska a d'aure ya juyar da kai ya cigaba da yiwa Faanah hirarsu irin ta ma'abota kurumta sai dariya take wani lokacin tayi murmushi. Yakura ta nisa tace"Bakura dama kana da k'anwa?" Murmushi ya yi yai mata bayanin Fannah a wajan su.Dai-dai lokacin Hajja ta basu waje, kamar jira take tana barin wajan ai kuwa Yalfata ta kwashe da wata shu'umar dariya"hhh! Nida durum kace bata ji?". A zuciye Hamza yayo kanta bai wata wata ba ya kwasheta da mari, cikin takaici ya nunata da yatsa zuciyarsa na zafi_.

_Bai an karaba yaji saukar mari a kuncinsa, cikin kad'uwa ya juya saboda ganin wanda ya mareshi abin mamaki Bakura ne. Ransa ya yi zafi ya dinga dubansa a wani irin yanayi kawai sai ya girgiza kai ya wuce. Hannun Fannah ya kama suka wuce zuwa gidan Kakarta. Tunda ya fita ya kasa magana, sai ajiyar zuciya yake. Faanah ta kama hannunsa ya zuba mata ido, sai ta girgiza kai shar hawaye ya zubo mata. Rikicewa yayi yana girgiza kansa bai taba ganin kukanta ba sai yau "shin me hakan yake nufi? Kodai Faanah najin abunda nake ji a raina?" Hannu yasa ya share mata hawayan suka nufi gidan Hajja da fara'arsu suka shiga. Hajja da mahaifiyar Faanah da mahaifinta na zaune suna fira, cikin murmushi suka zauna. Faanah nasan yiwa Hajja bayanin abinda ya faru ta kasa. Fahimtar hakan yasa Hamza yai mata bayani gudun zargi. A hargitse mahaifinta ya mike yana masifa" sun san kuwa yadda nakeson 'yata? Kurumta baisa ta zama wofintaciyya ba mutum ce mai cikakken yanci kamar kowa". Hajja ce ta dinga tausarsa haka ma Hamza bayan komai ya lafa Hamza ya dubi Hajja yace "Hajja wai haka aka haifi takwararki ko lallura ce?". Ta bud'e baki zatai magana sai gani nayi ta mik'e zumbur!. Ku biyo ni_

_Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sarkin tsoro naga randa zaka daina tsoron nan naka"dariya ya yi yana soka kai ta cigaba "yau dai zaka ji wacce ce Faanah?"..........._

_*WACCE CE FAANAH*_
_Kamar yadda ka sani ni na haifi mahaifin Faanah, shi kad'ai na haifa a salin mahaifinsa d'an Damaturu ne tsakanin Damaturu da Maiduguri tafiyar 177km ne ya taso cikin taskun 'yan uba su goma ne. Shi kad'aine waraki a cikinsu saboda mahaifiyarsa Bahaushiya ce 'yar Kano. Tsangwama da hantara babu wadda mahaifiyarsa bata gani ba, harta rasu sai tsangwama ta dawo kansa. Saboda Kanuri bayason auran wanda ba k'abilarsa ba sai rantsattsan rabo. Haka ya taso cikin gararin rayuwa, har girmansa Allah ya taimake shi mahaifinsa ya tsaya masa kan karatu. Allah ya had'amu da shi ne a wata ziyara da ya kai garin mu Gaidahm gidan marayu cikin k'ank'anin lokaci mukai sabo dashi._

_Kasancewata marainiya bani da kowa kawai na taso ne na tsinci kaina a gidan marayu. Bayan dogon bincike aka bawa mahaifinsa aurena, zaman wata biyu mukai a Damaturu akai masa sauyin aiki zuwa Biu. Zamanmu a Damaturu zamane na hantara da hancini, dawowarmu Biu sai muka samu kwanciyar hankali a haka Allah ya bani juna biyu harna haifi d'a namji wanda yaci sunan Muhammad. Dangin mahaifinsa babu wanda yazo mana har ranar suna, kwanci tashi mahaifinsa ya soma sana'ar gwal nan da nan Allah ya bud'a masa ya zama shahararran mai kud'i. Lokaci zuwa lokaci muna zuwa ziyara gidan marayu da kuma Damaturu duk da bama samun wata tarbar kirki.Muhammad nada shekaru uku Kakansa ya rasu, mutuwar ta girgizamu dama shi kad'ai ne wanda ya rage mana. Bayan rasuwarsa sukai raban dukiyarsu kowa akabashi tasa suka watse. Kwanci tashi akasa Muhammad a makaranta kulawa yake samu sossai, harya gama makarantar primary ya shiga secondary. Yana jss two wata masifa ta samemu, barazana da yake samu daga abokan kasuwanci. Saboda ya tara dukiya da yawa duk garin Biu ansanshi, kwatsam wata ranar Lahdi da dare muna bacci aka hauro aka kashe shi. Lamarin daya girgizamu, sunyi bincike basu samu komai ba, saboda duk wata ajiya tasa tana banki wala kud'i wala kaddara._

_Haka muka sha kukanmu muka more, haka na cigaba da rainon d'ana na ingantashi da karatu da tarbiya har ya kammala makarantarsa. Na sama masa gurbi a makarantar kud'i nan yai karatunsa na shekaru shida na gaba da secondary daga nan ya samu admission a jami'ar Maiduguri bayan gama karatun sa na master yai aure, ya auyi Maryam 'yar a salin garin Maiduguri cikakkiyar Kanuri kyakkyawa gaba da baya. Zamansu shekara d'aya ya nemi gurbin k'aro karatu a k'asar Canada. Naso hanashi amma daya gayamun k'udirinsa saina hak'ura suka tafi. Shekarar su daya da tafiya aka haifi Fannah wadda taci sunana. Naji dad'in yimin takwara da akai sossai, daga can ya aiko abokinsa ya tafi dani akai suna na dawo. Sai da suka shekara uku sannan suka zo wajena lokacin Faanah ta girma, abinka da rainon turawa tayi girma sossai kamar 'yar shekara shida gata kyakkyawa. Abinda ya bani mamaki tunda suka zo banga tayi magana ba, tun ina kawaici har na furta. Cikin jimami sukai mun bayanin *KURMA CE* da farko hankalina ya tashi amma daga baya na fawwalawa ubangiji domin shiya hallice ta ya fimu santa._


_*Haka suka gama hutun su suka koma, tun ban iya hira da'ita ba harna koya nayi kewarta sossai. Bayan gama karatun mahaifinta Canada suka d'aukeshi aiki hakan ya tilasta musu zama a can. Zamowar Faanah Kurma baisa ta samu rashin kulawa daga iyayye ba hasalima tsananin sonta suke yi sossai, makaranta mai tsada suka sata abinka da kasasshen ketare sossai Malamai suke bata kulawa. Yanzu Faanah nada shekaru goma sha biyar tana matakin karshe a makarantar gaba da primary, ta iya rubutu sossai saidai bata ji kwata-kwata haka ubangiji ya hallici baiwarsa...........wannan shi ne tarihin Faanah._

_Ajiyar zuciya Hamza ya yi yace "kin san me Hajja?" "Saika fad'a Hamza". "Walahi banyi zaton haka aka haifi Faanah ba kin san akwai........_
shi, ya dauko ya daga.Sun jima suna magana sannan ya katse ya soma bayani._

_"K'ananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira Otitis media, shi otitis media ciwo ne wanda yake ciwo a tsakiyar kunne._

_Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzab'i wani lokaci mai tsanani,sai dai sau da dama bai cika zama abun damuwa ba._

_Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa otitis external, wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara basu cika kamuwa da shi ba kamar na farkon ba._

_Yawanci k'ananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne, musamman k'ananan yara daga cikin wannan jerin:-_ _Yaran da aka haifa basu kai lokacin haihuwa ba.Akwai yaran da suke yawan jin sanyi sosai.Sannan akwai yara wad'anda basa son wari, kamar hayak'in taba da sauran su.Ko kuma yaran da ba’a basu nono ba.Da kuma yaran da aka baiwa abincin gwan gwani._

_Wasu k'wayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne.K'wayoyin cutar na tafiya daga bayan mak'ogoro yayin da Eustachian tube ta lalace,wannan ke kawo ciwon tsakiyar kunne.Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon mak'ogoro ke kamuwa da ciwon kunne.Otitis external shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da k'wayar bacteria._
_Cikin murmushi Mahaifin Faanah ya dubeshi"shin ya alamomin ciwon suke Dr Hamza?". Dariya Hamza ya yi yace"haba Baana ban kai ga zama ba just one level fa". Gaba d'aya sukai dariya, banda Faanah da tai zuru tana kallon su, tausayinta ya cika Hamza ji yake tamkar ya bata kunnuwansa. Kad'a kai ya yi yaci gaba._

_Alamun ciwon:-Ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da k'aik'ayin kunne da zafi.K'ananan yara basa iya Magana,amma zasu kasance da zazzab'i marar misali._

_Haka nan zasu kasa yin barci, su rik'a sosa kunnen su har yayi jinni, kuma suna kasa iya sauraron k'ara ko amo.Za’a iya samun fitar ruwa mai k'wayoyin cuta daga kunnuwan.Ciwon bayan kunne shima yana da zafi sosai, yana sa k'uraje sossai a bayan kunnuwa._

_Ana iya ba yara 'yan k'asa da wata shida maganin kashe k'wayoyin cuta (Antibiotics).Shan maganin rage zafin ciwon.Yara suna jin sauk'i yayin da suka fara amfani da maganin kashe k'wayoyin cuta.A nan yana da muhimmanci ga Iyaye su kiayye umurnin likita har k'arshe.Shan Topical antibiotics da man shafawa suna maganin otitis external.Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sossai.Idan kuma yana da zazzab'i fiye da sa’a 48, da kumburi bayan kunne, idan yana barci sosai, kuraje a kunne, baya ji sossai ko gaba daya._

_Kunne yana d'aya daga cikin sassa masu muhimmanci sosai a jikin d'an Adam.Wanda ba kasafai ake gane muhimmancinsa ba, sai ya kamu da wata matsala._
_Kuma amfaninsa ba wai kawai a jin magana ya tsaya ba, a’a yakan kuma taimaka wajen sa dai-daito idan mutum ya mik'e tsaye ta yadda ba zai fadi kasa ba._

_Kunne na da b'angarori uku, na waje da tsakiya da kuma can ciki.Fatar kunne da k'ofar kunne ta waje su ne bangare na waje d'in.Amfanin wannan sashe shi ne tare iska da amo ya saita su zuwa cikin kunnen. Wannan b'angare bai cika samun ciwo sosai ba, sai dai akan iya yanke shi a hadari, ko kuma da abubuwa masu kaifi idan wata tarzoma ta tashi misali.Ita kuwa k'ofar kunne ana iya ganin dattin kunne a ciki a fitar ta wannan bangare._



_B'angare na tsakiyar hade yake da mak'ogwaro ta yadda kwayoyin cuta daga makogwaron kan yi saurin shiga kunne, musamman ga yara tunda hanyar da ta had'asu gajeriya ce.Ruwa ma kan iya shiga wannan b'angare na kunne a yayin wanka ya hana mutum sakat._

_Daga can ciki kuma akwai wani b'angaren,inda dodon kunne wato cochlear (da kike tambaya akai) suke, da wasu kasusuwa kanana guda uku.Jijiyar da ke da alhakin sa mutum jin magana a jikin dodon kunnen ta ke.Wato ke nan dodon kunne shi ne ke da alhakin jin magana.Su kuma kasusuwan sukan taimaka wa jiki wajen daidaito._

_Abubuwa da dama kan taba lafiyar dodon kunne har a rasashi ta hanyar hujewa;abubuwan su ne kwayoyin cuta (kamar sankarau) ko wasu magunguna, na nasara ne (kamar gentamicin) ko na gargajiya, ko kuma a hud'a shi ta hanyar susa da abu mai tsini, ko kuma ta hanyar fad'awa ruwa da karfi, ko buguwa ta hadai,ko ta yawan shan kara fiye da kima, ko ma abin ya faru tun a ciki, a haifi mutum haka ba ya ji.Akan iya yin dashen wani dodon kunnen idan bukatar hakan ta taso._ _Idan ruwa ya shiga kunne, misali kamar a lokutan wanka, za a iya sa tsinke mai auduga a goge.Idan bai fita ba a bari bayan kamar kwana biyu zai tsane da kansa.Sai idan ba a ji ya tsane da kansa ba ne ya kamata a je asibiti._ _Masu aiki a kamfanin da suke da injina masu kara ko filin tashin jirgin sama, dole su rika toshe kunnensu a kullum, domin kiyaye lafiyar dodon kunne.Irin wannan kara ma takan iya fasa dodon kunne.Masu aiki a irin wad'annan wurare yana da kyau su rik'a zuwa wurin likitocin kunne a kalla sau d'aya a shekara don kula da lafiyar kunnensu.Hak'k'insu ne su nemi kamfanin ya samar musu abin rufe kunne da kuma likitoci domin kula da lafiyar kunnensu.A kasashen da suka ci gaba, idan babu irin wannan a kamfanin,ma’aikata za su iya kai kamfani k'ara kotu don a tabbatar an samu yanayin aiki wanda ba zai taba lafiya ba._
_Wad'annan su ne hanyoyin da za su iya sa a kamu da ciwon kunne, dama wasu hanyoyin daban-daban.Ga hanyoyin kariya daga ciwukan kunnen;-A mafi yawan lokuta ba sai an fitar da dattin kunne ba, dattin da kansa yake fita.Wato kunne shi ke wanke dattinsa da kansa.Yakan wanko shi ya turo shi k'ofa kunne.Za a ga dattin launin ruwan kasa a nad'e a jikin wani abu mai dank'o.Idan har ta kama sai an cire wannan abu mai danko, to kada a yi amfani da abu mai tsini.A sa irin abin goge kunnen nan mai auduga a bakin kunnen a fito da shi a hankali._

KARIYA

_Wanke hannuwanka da na yaro.Shayar da yara da nonon uwa.Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance.Daina amfani da kayan susa.Daina shan taba a d'akin da k'ananan yara suke.Yiwa yaro rigakafi da yana rage wannan ciwon.Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Fluvaccine) kowacce shekara.A k'arshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne:Kada ayi amfani da auduga a kunnen,domin zata iya k'ara girman k'wayar cutar.Kada a diga maganin kashe k'wayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne.Kada a share kunne da auduga domin kauda dank'o kunne."_

_Gaba d'aya suka saki ajiyar zuciya, Hajja ta dinga murmushi tana jinjinawa Hamza. Haka ma Mahmmad, a ransa yana ji ina ma Hamza zai yarda ya zama yaron shi saboda yana da burin bud'e shaguna a garin Biu dan hab'aka garin. Kasa hak'ura yayi sai da ya furta sossai Hajja taji dad'in k'udin d'anta. Hamza kuwa murmushi ya yi yace su bashi lokaci ya yi shawara da Bakura da Hajjansu. Sun amince da batunsa saboda yana da na gaba dashi. To nima bari in je in huta kafin in d'ora nagaji da yawa Lo
_Washegari Hamza bai yi k'asa a guiwa ba, ya sanar da Hajja k'udirinsa. Hajja ta nuna masa rashin amincewarta ta nuna masa karatunsa yafi komai muhimmanci a gareshi. Bai jinkirta ba ya sanarwa da mahaifin Faanah shima baiga laifinsa ba saboda yasan muhimmancin karatun._

_Kwanci tashi kwanaki na shud'ewa, harzuwa lokacin babu jituwa tsakanin Bakura da Hamza. Hamza da Faanah sunyi wata irin shak'uwa sosai. Ranar da mahaifanta suka saka zasu koma Canada, Faanah ta dinga ihu tana kuka kan bazata bisu ba. Hankalinsu ya tashi sossai, a rayuwarsu basasan b'acin ranta saboda yarinya ce mara son hayaniyya duk da kassncewarta Kurma. Tilas suka hak'ura suka barwa Hajja ita da sharad'in zata koma in hutun Hamza ya k'are ya koma makaranta. Haka suka rabu suna ta jimamin rabuwa da juna.

_Ashe tafiyar ajali ce a ranar jirginsu ya samu accident (had'ari), babu wanda ya rasu a cikin su. Lokacin da labari ya samu Hajja fad'uwa tayi sumammiya lamarin daya haifar mata da cutar shanyewar b'arin jiki. Al'ammarin daya d'aga hankalin Hamza da Hajja Falmata Allah sarki Faanah kuka ma gagararta ya yi sai zubar hawaye.

_Kwananta goma a asibiti babu abinda take iya yi, kwata-kwata jikinta baya motsi.Hamza ya shiga faffutukar neman kud'in magani, abun yaci tura. Aikin yi ya gaggara kasancewar damuna tayi nisa, hakan yasa ya shiga mawuyacin hali saboda tausayin Faanah. Cikin ikon Allah ya samu aikin kwaso wani barkono daga wata gona zuwa gidan maigari. Yana kammalawa aka biyashi naira dubu goma, ya juya kud'in ya jinjina a ransa yana tunanin ko zasu isheshi hidimar kulawa da Hajja.Kwana uku yana tunanin lamarin, ya dauki kud'in ya dank'awa likita dan bata kulawar data dace. A haka yaci gaba da neman wani aikin, Hajja Falmata ita take kawo abinci kullum yayin da Faanah da Hamza ke jinya.Ranar kwana na sha hud'u ta amsa kiran mahallicinta. Haka rayuwar take (KULLU NAFSEEN ZA'IKATTUL MAUT),haka aka tattara Hajja zuwa gida akai mata sallah aka sadata da makwancinta na gaskiya. Ubangiji kasa mui kyakkyawan k'arshe amin.

Kacokan Hamza ya tattaro kayan Faanah zuwa gidansu, babu uwa babu uba babu kaka. Rayuwa ta yi mata k'unci Hamza da Hakka ne kad'ai take kallo taji dad'i a ranta. Hutu ya k'are Hamza babu kud'in komawa makaranta, duk yadda yaso abun ya gaggara ya tirza ya tirza abu ya gaggara, Hajja ce ta tunkari Bakura da batun, atabau yace bazai bayar ba shi yana so ne ya k'arasa had'a kud'insa ya siyi sissin gwal wanda zai kaiwa dangin Yakura na neman auranta. Sossai Hajja taji haushin abinda Bakura ya yi, amma bata nuna masa ba. Lamarin ya sha kansu sossai, Hamza ya shiga damuwa abokansa duk sun koma makaranta banda shi.
Ranar wata Asabar suna zaune jigum, Hamza yana yiwa Hajja bayanin aikin daya samu na gonar mak'ocinsu mahaifin su Alangubro. Faanah ce ta fito ta ratso tsakar gidan tana murmushi, wani abun hannu mai kauri ta ciro a hannunta guda hud'u ne ta bashi guda biyu, batai magana ba ta tamke fuska ta koma d'akin Hajja yasan ni sarai, koda ya kirata bazata juyoba. Cikin murmushi ya dubi Hajja yace"Hajja 'yarki rigimammiya ce, kwana uku kennan ina fama da'ita wai saina saida abun hannunta na koma makaranta. Hajja bawai siyarwa ne bana son yi ba, asalin abun hannun na mahaifiyarta ne kinga a yanzu Faanah bata da komai data samu daga mahaifanta inba awarwaron nan ba sai gidan Hajja." Ajiyar zuciya ta yi "lallai kayi gaskiya Hamza dad'ina da kai hankali amma tunda ta dage ka karb'a saika siyar da biyun ka ajiyemata biyun. Intaga babu su a hannunta gaba ai banga abunda zata ce a siyar ba".
"To! Shikenan Hajja", da haka suka kashe maganar. Cikin satin aka kai abun hannun kasuwa, abinda ya bashi mamaki dubu d'ari da hamsin aka siyi kowane d'aya, hakan yasa ya saida d'aya ya dawo da d'ayan ya karb'i biyun ya had'a ya ajiyemata. Dubu hamsin ya karb'a ya bawa Hajja dubu hamsin taimusu siyyayar kayan masarufi na dubu ashirin, dubu ashirin yace asiyawa Faanah kayan dangin turare da lafayya da mindil ai kuwa tayi murna sossai. Dubu hamsin ya ajiyeta zai yi noman gyad'a da barkono. A satin ya koma makaranta.

Tun komawarsa makaranta ya kasa sukuni, kwata-kwata tunanin Faanah ya hanashi walwala. Da farko ya d'auka sabo ne, turken wawa daga baya sai salon ya sauya. Lokuta da dama muryarta har gizo take yi masa a kunnuwansa. Lamarin ya d'aga masa hankali ya kan yawar tambayar kansa "ina ni ina soyyaya da kurma?" Amsar da take bashi wuyar samu a koda yaushe. Ba lallurarta yake gudu ba, yadda Hajja zata karb'i lamarin, zahirin gaskiya da farko tausayinta yake ji daga baya ya gama amincewa zuciyarsa san Faanah yake.Kwanci tashi suka cinye samister d'aya, suna shirin fara jarrabawa kullum adu'arsa ubangiji yasa ya haye matakin karatunsa.
Faanah na samun kulawa dai-dai gwargwado wajan Hajja,tun bayar tafiyar Hamza ta fahimci kad'aici ya yi wa Faanah yawa, ana haka aka bud'e wajan koyon sak'ar hannu kusa da su. Batai wani jinkiri ba ta yankar mata form ta soma zuwa.

Tana jin dad'in zuwa sossai, nan da nan ta maida hankali akai ta soma yin safa da abun goge gumi.

Tun bayan komawar su Yakura gida, Yelfata ta kasa nutsuwa. Kwata-kwata zuciyarta na wajan Hamza ya burgeta matuk'a amma data tuna Faanah sai gabanta ya yanke ya fad'i ta tabbatar akwai wata alak'a irin ta zuciya tsakaninsu. Saboda yadda taga yana nuna mata kulawa a zahiri, da kuma yadda ya taso mata tamkar mayunwacin zakin da ya shekara be ci ba.
Zaune take tayi nisa cikin tunanin, Yakura ta jima a tsaye a kanta bata san tana kanta ba har saida ta d'an tab'ota. A jiyar zuciya ta saki tana dubanta"lafiya Yalfata, meya sameki ?"Hmmm! Babu komai Yakura". "Ke! Dakata ni zaki b'oyewa damuwarki?", tayi jigum tana tunani ta nisa tace "Yakura inason Hamza". Cikin tashin hankali ta zaro ido "awaana Bakura? ('Dan uwan Bakura). Kai ta d'aga mata tana jinjinawa. Yakura ta jinjina, ta sake jinjinawa taja fasali ta dubeta.

Kinsan dai bisa dukkan alamu wannan Kurman budurwar sace, dan haka ki sake dabara sai kace wata mara masoya". "Ni dai shi nake so Yakura wa nake dashi? Bayan duk sun gudu, kema ki hanzarta rik'e Bakuran da kike homa a kansa kafin ya sub'uce miki". Duka ta kai mata tare da cewa"ni zaki yiwa iskanci?". Da gudu tayi ciki, karaf sukai karo da Yalta k'anwar Kundum. A zafaffe ta kwad'awa Yelta marin daya gigitata har ta saki jakar islamiyarta, da sauri ta taro abarta saboda muhimman littatafan da suke ciki.

Bata tanka ba ta sa kai zuwa sashinsu, fuskarta tayi red'u-rud'u abinka da farar fata cikin kunar rai ta ajiye jakarta tana taya Mamansu aiki da take bakacan tsakin biski. Da kulawa ta dubeta"Yalta lafiya?" Share hawayanta tayi, tana yi mata bayanin abinda Yalfata tayi mata. Murmushi tayi ta jinjina kai, "karki sake ki kulata ko me zatai miki na gayamiki, share hawayanki komai lokacine. Fatan dai kinyi karatu sossai?". Tausayin mahaifiyarsu ya cikata, saboda tasan ko kara ta kaiwa mahaifinsu babu matakin d'auka Yagana itace mace mai kwalli a gidan.

Kwanci tashi aka soma gudanar da maganar bikin Yakura da Bakura, rawar jikin da Bakura yake har mamaki yake bawa Hajja. Ta dai tattara ta zuba masa ido,tayi juyin duniya yai al'adun mutan garin Biu a wajan bikin ya kaffe al'adun Kanuri zai yi lamarin daya haifar musu da sab'ani sossai. Gonarsu guda biyu yasa d'aya a kasuwa ya siyar duk sabo da hidimar bikin.
Cikin kwanciyar hankali Bakura ya soma neman auran Yakura.Hajja ta tattara ta zuba ido kan lamarin, kullum cikin yimasa adu'a take.

BIKIN KANURI
Al'adar Kanuri wajan gudanar da auransu, ya bambamta sossai da sauran mutane. Misali. Su dai a bikin bare-bari da farko idan kaga yarinya kana so, idan kuka shak'u kai da ita kuka aminta to zaka fad'awa iyayenka itama ta fad'awa nata iyayen akan cewa za'azo tambaya. To tambayar gidan mazane zasu sayi alewa da goro da minti da cingam, masu yawa da kuma kud'i karshe shi ne dubu ishirin ba'abada k'asa da haka sai sama. Akwai masu bada dubu hamsin, tamanin harma d'ari kawai dai-dai k'arfinka amma kar a gaza ashirin shi ne a talauce. Wannan bayani dana ke muku duk kayan nagani inasone shi ne su ke cewa tambaya.

Daganan kuma sai kayan toshi, shi kayan toshi yadda kukasan kayan aure haka ake had'asu wasu saitin akwati mai biyar wasu mai hud'u wasu mai uku. Harda masu dozin musamman fanin gidan sarauta. Za'azuba kayan duniya ciki k'awaye da 'yan uwa aita zuwa kallo. Idan an gama kallo kamar sati biyu sai a rabawa k'awaye da 'yan uwa rabin kayan kamarsu fant su mayuka su powder (hoda).Hada masu saka gwal da kujerar makka.Abin sai wanda ya gani, hakan al'ada ce wanda bai yi ba da wanda ba ayi wa ba ya zama abun tsegumi.Da wuya ma a kasa yi, tunda suna girma al'adunsu sai dai wata bata kai wata ba.


Fanin danginki uwa da uba kuma, akan basu turame mayafai ke kuma saiki d'inka sauran.Idan aka kwana biyu sai a shirya kayan sa rana.Aje a yanke rana amma basu fiye yanke ranar dayawa ba.Yayin da ya rage saura sati biyu biki zaki amso anko.Miji shi zai wa k'awayenki anko.Ko sun kai ashirin shi kuma zai bada kudin turare da gyaran jiki.Dakuma kudin shiga kasuwa na k'unshi kuma duk ba kudi kadan ake bayarwa ba.

'Bangaran sadaki kuwa mafi yawa da sisin gwal suke biya, hakan al'adarsu ce.

Sossai Bakura ya yi hidimar auran Yakura, duk wata al'ada da ake yi sai da ya yi ta.Arzik'insa d'aya Yakura bata da k'awaye da yawa saboda masifarta.Haka ya zage ya yi hidima sossai, b'angaran gidan su daga dama ya bige ya yi sabon gini.'Daki biyu da babban fallo da kitchen da band'aki sai yai doguwar katanga a kai musu tsakani da Hajja.Wajan yasha gyara da siminti, ya dasa fulawowi koraye wanda suka k'awata tsakar gida.
Tunda aka gama ginin

Please Login or Register in order to submit comment