Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yai musu ya nufi cikin gida dan gaida Hajjansu.Yana shiga ya tsaya cak sakammakon abinda kunnuwansa ya jiye masa.
Karaf kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Marwa"walahi Hajja ta baya na bugata ta doku, shegiya ni so nayi kunnuwan su k'arasa d'aukewa.Sannan na yaga littafin da take matuk'ar so, ai walahi shswararki ce abin bi kisan mummuk'e zan dinga yi mata saina nakasa nakassashiya".Hajja ta saki dariyar jin radad'i, tare da dafa kafad'un Marwa ta cigaba"lallai Marwa kece makami mai linzami dazai zamo abin tunk'ahona a da na d'auka cewa burina na wargaza Faanah bazai cika ba tunda mahaifiyarki ta kasa cika shi sanadin hakan na rasa ki yau na tabbatar ba haka hane.Yanzu ne salon wasan zai soma".Cikin alamun mamaki Marwa ta dubeta, "bangane ba Hajja?"."Zaki gane Marwa yau zan bayyana miki abinda baki sani ba, zaki k'ara rik'e makaminki wajan yak'ar Benah".A hankali ta labarta mata asalin wacce ce ita, tun daga farko har k'arshe.

Kansa ya sara ya dafe kan, duniyar ta soma juya masa ya shirya tsaf ji yake kamar yau za'a tashi duniyar zuciysrsa ta tsinke yaja jiki yana mirgina kai tamkar marayan zaki.Kai tsaye sashin Hajjansu ya nufa, anan ya riski Benah tana taya Hajja had'a biskin gero idonsa jajjur yai salam karaf suka had'a ido k'ur suna kallon juna wani abu ya daki zuk'atansu Baana yau ya kasa d'auke ido a kanta ya lumshe ido gashin idonsa gazar-gazar suka rufe ruf har suna tabo saman idonsa tar ya budesu a kan fuskarta.Tai saurin dauke ido"awaana me ya sameka?" tai furucin da ci da zuci."Benah d'auko mindil d'inki muje asibiti a duba ciwonki" dafe kan ta yi saboda sarawa da ya yi Hajja tai murmushi tace.
"Ai bata ji Benah nan da kake ganinta, tunda ta shigo nake fama taje Abbunta ya kaita asibiti tak'i".Turo baki tayi"kinji ki kakus dake wai Benah,bakinki ya yi sabo da kuka ki bari masu oral English sui iyayin da suka saba".Baana ya kwashe da dariya "yes my unique ga yawa Kakus ta tsufa".Dariya ta yi had'i da cewa"shakiyai ku barmun gidana".Da gudunsu suka fita suna dariya, kai tsaye Baana motar Dr ya karb'a ya d'auki Benah suka nufi *BIU SPECIALIST HOSPITAL*.Dake suna da fayal babu jinkirtawa aka karb'eta, an mata dressing wajan sauranta allura nan take idonta yai k'wal zatai kuka tillas akai kiran Baana.

Cikin tausayawa ya dubeta, "my unique ki tsaya mana" a shagwab'e tace "Yah Baana bana son alura zafi walahi" ya rasa yadda zai mata dabara ta fad'omasa yace "Benah kali can".

Tana juyawa yai saurin kama hannayanta yaiwa Dr inkiya cikin sauri yai mata allurar, ta saki k'ara tare da kwanciya a jikinsa yar! Tsigar jikinsa ta zuba tare da wani shock a hankali ya sauke wata sasanyar ajiyar zuciya kukanta yadinga taba mashi zuciya. Dagewa ya yi yana lallashinta har tai shiru ya karbi magungunan da alluran yace shi zai dinga yi mata ko Dr haka suka fito asibitin yana ta aikin lallashi.

A mota rafe suke tamkar kurame, babu wanda ke tankawa kowa da abinda yake sakawa cikin ransa, ta nufasa tace.

"Yah Baana kai da ka sauya couse kake cewa zakai mun allura Abbuna dai zai mun".

"Hmmm! Walahi Beenah bada son raina na sauya ba nafison in zama kamar Abbagana dan dai Abbagana yace karmutare wajan abu d'aya ne, na amshi zama barrister amma kefa?".

Yai tambayar yana tsareta da idanu,kanta a k'asa tana wasa da farcanta tace"Yah Baana nifa nafison kammala hadata saura izzuf biyar, sannan inaso in taimakawa 'yan uwana mata matasa domin su dogara da kansu. Amma inason in karanci gynea ganin kamar Hajja bazata amince ba,shiyasa da Abbu yai min maganar ban bada goyon baya ba amma inaso in yi zurfin karatu kodan 'yan uwana mata.Shi yasa na fara da koyawa matasa kamata sak'ar hannu".

Tunda ta soma magana yake kallon bakinta d'an k'arami kowa ne harafi cike da nutsuwa take furta shi harta dasa aya.Yayi murmushi.

"Beenah zaki karatu insha Allahu, karki damu duk burikanki zasu cika mudin ina raye, fatana ki tsaya wajan kyautatta karatunki babu ruwanki da shasshashun abokai bale samari".

"Insha Allah Yayana" a haka suka karaso gida yana janta da fira gab da zasu shiga gida sukai kici6us da Marwa wani mugun kallo ya watsa mata Beenah ta kallesu ta murda yatsu murmushi ya yi ya jinjina kai sukai sallama.
Ya dubi Marwa "ki sameni a daki" bai jira cewarta ba ya wuce sitroom dinsa na gidansu Beenah ta kofar ciki ya bata umarnin ta kawo masa abun sha.
Kanta a k'asa tana juye-juye ya dubeta zuciyarsa kamar ta fashe, ya hadiyi wani kakkauran miyau tamkar makogwaransa zai yake ya kalleta. "Yanzu Marwa kin kyauta kenan? Cikin mamaki tace"menayi kuma Baana? Ya shak'a sauka kad'an ya kaimata duka.
"Rainamun hankali zakiyi!?" Tuni tayi saranda tana rarrabe tsakanin k'arya da gaskiya zuciyarta ta shiga rud'u ina yaji labarin nan? Ko dai Beenah ce ta fada'? Kai ba Beenah bace ita kanta batasan waye ba. To kodai yaji hirarmu d'as! Gabanta ya fad'i ta numfasa tare da jan ajiyar zuciya."Nifa gaskiya ba Beenah bace, kadai namun iko irin naka walahi ba yadda zan yiba wana munafikin ne yace nice? Ko ita nakassashiyar ce ta tad'a?" Wani kyakkyawan mari ya zabgamata dai-dai lokacin Beenah ta shigo da hanzari ta ajiye ruwan duk da bata ji abinda suke tattaunawa ba jikinta ya bata Marwah ce bata da gaskiya tana rik'e da hannunsa tace"a kullum ina tunasar dakai kadaina nuna k'wanji a kan mace domin ita d'in mai rauni ce karka dinga biyewa zuciya wajan tunzuraka harta kaika ga yanke bahagon hukunci.

Ta sassauta murya tana dubansa tace.
_"Haba Yah Baana Musulunci bai yarda a muzgunawa ‘ya mace ba ta kowane irin hali.Mata wasu halittu ne na dabam, wadanda suka zama dole a girmama su.Addinin musulunci bai yarda a nuna bambanci a sha’anin da ya shafi ‘ya mace ba._
_Annabi Muhammadu (Tsira ya tabbata gareshi) ya fad'a mana cewa: Mata kamar k'asusuwan hak'ark'ari suke, idan har ka yi k'ok'arin lank'wasar da su da yawa, sai su karye, idan kuma ka bar su, su malkwade.Ya zama dole ka dai-daita tsakani wajen kula da mata.Zafaffawarka bashi zaisa fa ta bi umarnin ka ba musamman a wannan tsakanin shekarun tana ganin takai kabi komai a hankali zaifi alfanu._

Sakin hannunsa tayi tana murmushin da ya kara mata kyau, jiki a sanyaye ya zauna yana dubansu su duka Beenah ta zauna ya dubu Marwa "ke bazaki zauna ba ne?" Zama tai tana gun-guni takaicinta zuwan Beenah wajan ta faki idonsa ta zabgamata harara d'auke idonta tayi kamar bata gani ba ya numfasa yana dubansu.

"Naji dad'in tunatarwarki Beenah harga Allah bani da burin wulak'anta dan Adam musulmi balle Mace da nakewa duban kashin bayan al'ummah.Amma Marwa ki sani abinda kikai kwata-kwata baki kyauta ba domin dai kisan cewa.


_'Dan Adam shi ne mafi d'aukakar halittar Allah Ta'ala.Ubangiji subahanahu wataala ya kimsa masa hankali da tunani, ya kuma sanar da wannan zab'ab'b'en halitta tasa kyawawan sunayensa wato asmaul husna.Shima d'an Adam d'in wata babbar aya ce daga cikin ayoyin Allah. Alkur'ani mai girma yana cewa:"Kuma Allah ya sanar d'an Adamu dukkanin sunaye sannan ya kawo su gaban mala'iku yace: 'Ku ba Ni labarin sunayen wad'annan abubuwa in kun kasance masu gaskiya' " Suratul Bakara : aya ta 31Allah ya ba wa mutum daukaka tunda ya halicce shi cikin mafi kyan sura, kana ya hura masa ruhi daga gare shi.Allah subhanahu wa taala yana cewa: "Hak'ik'a mun halicci mutum cikin kyakkyawar halitta."Dad'in dad'awa, Ubangiji ya nad'a mutum a matsayin khalifansa a bayan k'asa.Duk bawan da zaki gani a doron k'asa akwai hikimar ubangiji na hallitarsa ba wai dan baya sansa bane a'a ikonsa ne ya nuna._
_Wad'annan darajoji da Allah ya bawa d'an Adam suna nuna irin matsayi da d"aukaka da Allah ya yi masa.Bisa la'akari da wannan matsayi d'an Adam yana iya kama hanyar aikin k'warai da kamala. Amma idan ya fand'are ya k'i amfani da hankali da daraja da kuma zab'in da Allah ya yi masa, yana iya tab'ewa ya fad'a cikin k'ask'anci.Saboda haka wajibi ne d'an Adam yayi iya k'ok'arinsa domin kaiwa ga k'ololuwar daraja, wacce ta dace da muk'amin Khalifan Allah a doron k'asa, ta yadda duniya zata tsarkaka ta yi kawa.Sai dai cimma wannan zai yiwu ne kawai idan dan Adam d'in ya san hak'k'okinsa da buk'atunsa, sannan ya zage damtse domin kaiwa ga rayuwa ta kamala da sa'ada da kuma kwanciyar hankali.Samun wadannan kuwa yana dogara ne ga yin hob'b'asa da aiki tuk'uru kamar yadda sak'on Ubangiji na k'arshe, wato Alkur'ani mai girma yake cewa: "Ko kuna tsammani cewa Mun halicce ku ne da wasa, kuma ba zaa dawo da ku gare mu ba?".Suratul Mumina, aya ta115.'Daya daga sifofin d'an Adam shi ne yana iya sarrafa mazauninsa wato wannan duniya, ya kawo sauye-sauye cikinta, sab'anin sauran halittu.Wannan sarrafawa ta dogara ne da nau'in tunani da tsare-tsaren da mutum yake sakawa a cikin zuciyarsa.Idan zuciyarsa mai tsarki ce, kuma an zayyana ta da dan Adamtaka da manufofi madaukaka, to duniyar da mutum zai gina zata kasance mai kyau mai armashi.Idan kuwa zuciyar mutum da lamirinsa masu daud'a ne, duniyar da zai gina ma haka zata kasance. Don haka ne matukar sifar dan Adamtaka bata sami kafuwa a zuciyar mutum ba, ba zai iya gina rayuwa mai nagarta kuma abar alfahari ba.Dole ne dan Adam ya fara da tsarkake zuciyarsa,domin zuciyar mutum birninsa da haka har ya sami daman isa ga matsera._
_Dole ne sai tushen dan Adamtaka da take cikin ran mutum, ta tsiro ta yi tofo, kafin sakonnin wahayi masu haskaka zuciya su sami gindin zama su yi masa tasiri.Wannan kuwa ba zai yiwu ba har sai mutum ya san kansa da kuma mahaliccinsa,kuma ya dauki salon rayuwa mai ma'ana.Sakonnin Annabawan Allah masu cike da annuri, suna fadakar da mutane domin su kiyaye mutuncinsu, su tsare hakkokinsu, su kuma more rayuwa ta saada karkashin inuwar dan Adamtaka.Hakkin bil Adama batu ne wanda al'ummomin duniya suke kira gareshi. Tun fil'azal, addinin Musulunci ya bawa mutum hakkoki,kamar yadda na fad'a a baya, a lokaci guda kuma ya dora masa wajibobi, wato akwai hakkokin wasu da ke kansa. Manzon Allah da Imaman Ahlulbaiti sun yi kokari wajen warware matsalolin da al'umma take fuskanta, amma ko wane daya daga cikinsu yana bin salon na musamman wajen shiyarda mutane.Imam Ali ibn Hussaini al-Sajjad (a.s.) ya bayyana koyarwar addinin Musulunci ta hanyar amfani da salon addu'a, wato a cikin addu'o'in da yake koyawa mutane akwai bayanin manufofin addini. Baccin haka Imamus Sajjad ya wallafa littafin da aka fi sani da Risalatul Hukuk, wato Littafin Hakkoki,inda a ciki ya yake koyarda dan Adam hakkokinsa da hakkokin da suka rataya a wuyansa.Wannan littafi, ya kunshi kakkoki hamsin da daya, wadanda hakkokin ne da dan Adam yake da su bisa laakari da dabi'arsa,kuma babu wata doka ko iko da zai iya soke wadannan hakkoki. Idan dan Adam ya kula da wadannan hakkoki ya kiyayesu, zai yi rayuwa mai kyau, mai cike da dan Adamtaka da mutunci.Ga yadda Imamus Sajjad (a.s.) ya fara bayanin hakkokin: "Ka sani cewa Allah Mai Girma da Daukaka yana da hakkoki wadanda suka kewayeka, a duk motsawar da ka ke yi, ko natsuwar da ka yi, ko halin da ka shiga, ko wurin da da ka sauka, ko gabar da ka juyata.." Da haka kuma ya cigaba da bayanin hakkokin Ubangiji kan bawansa, da kuma hakkokin dake tsakanin mutane.Tsara alakokin zamantakewa ta hanyar aiyana hakkoki filla-filla, shi ne tushen farko na tsarin zamantakewar Musulunci".

Beenah ta girgiza kai tana murmushi, tana jinjinawa Baana Marwa kuwa ta shak'a iya shak'a ji take tamkar ta hadiye Baana in zata iya ta huta.Ta sunkuyar da kai tana gun-guni cikin zafin rai yace"me kika ce?".Ta sake kaskantar da kai "cemaka akai ina neman shiriyar da zaka tasani kanaimun wa'az?".Mamaki ya kashe shi Beenah kuwa kasa tankawa tayi yai murmushi yace "Marwa babu abinda zai tayar da sandarki face nacin daddanawa, ko yanzu baki makaraba hanyoyin shiriya yawa gare su in kinso zaki iya zama mai kirki".Kafin ya dire ta tareshi "yaushe nace inason zama mutuniyar kirki? Mtss mai bunu a gindi dai.....waima yaushe ake kud'in k'asa gari ya tashi? ".Ya yunkura zai yi magana ya maida kayarsa"Marwa banason zamanki da Beenah" "saika kashe ni" ya kad'a kai da sauri "tarbiyarki ce bata gamsheni ba" ya fada cike da son tura haushi. Aikuwa ta shak'a ta mike tana kada jiki "kace in shirya sarkin musulmi zai mak'wabceni".

Fuuu! Tabar d'akin tana mita, bangare guda kuma tana ganin wautarta saboda sarai tasan halin Baana.Beenah ta saki ajiyar zuciya tana kallon Baana sukai murmushi mai cike da manufofi.....
Cikin kwanakin babu jituwa tsakanin Beenah da Marwa, haka ma Marwa da Baana a haka ya kammala hutunsa ya koma makaranta cike da kudirin dake bibbiyar zuciyarsa amma wani nannauyan lamari na neman yi masa katanga da hakan.Kwanci tashi su Beenah suka kammala karatunsu, zuwa lokacin ta yayye d'alibai a kala hamsin kowace ta iya ta k'ware hakan ya rage mata nauyin koyawa saboda samun matai maka.

Cikin nutsuwa take tafiya, hannunta rungume da alk'ur'ani ji tayi an banganjeta.Cikin sauri ta d'ago kai, batai mamaki ba ganin Marwah ba cikin jin haushi ta dubeta. "Marwa me nai miki banason jan masifa fa,kawai ina tafiyata kawai ina ruwana dake bana son raini kin sani sarai ba kanwar lassa bace bana tsokana amma karya ne kimun ban maida martani ba ki shiga hankalinki". "Da kyau Beenah 'yar kurma, cikar Kanuri kenan kin birgeni amma fa wani b'angaran haushinki naji ina me karancin ji ina rigima? Bakya tsoron a karasa kunnuwan kizamo tamkar waccan kurmar ta gida?Kema wasa kike kinsan nafi k'arfinki zamanmu bazai tab'a zuwa a muhalli guda ba tunda mai iyayine ya tarad da mai kinibibi shawara nazo baki kifita harkar awaana Baana domin Baana na Marwah ne ita kad'ai".Beenah tazo iya wuya, takaici mak'ara a zuciyarta ji take kamar ta shak'eta ta huta ta kanne tana dubanta."Walahi kin bani dariya Marwah me akai akai Baana, da zan tada jijjiyoyin wuya a kansa? Abu daya nasani bazai sauya ba yadda yake awaananki nima awaana nane saidai wata kusan tafi wata.Kin fini kusanci dashi kasancewarsa uwa daya uba daya a gareki, kinga shi ne Bakura a gidanku dan haka kisani Baana awaananki nima haka".Rab'awa tai zata wuceta ta fincikota suka fuskanci juna, suna jin numfashin juna sossai idanun Beenah farare tas manya da kwaya baka sidik suka sauya kala zuwa ja tana dubanta."Kusanci dake tsakanina da Baana haka yake, bai kai nakiba sai dai na fahimci bayan nakasar kunne kina da nakasar kwanya ina nuna miki ne kan Baana shi zan aura dan haka ki fita a rayuwarsa kusancinki gareshi barazanane ga rayuwata!". Cikin jin zafi ta tankada Beenah tai gaba"lallai Marwa kin tabu awaanan naki zaki aura" ta fadi hakan a ranta ta wuce gida saidai wani abu na cin zuciyarta wani bangare nasan gasgata batun Marwa da hakan ta karasa gidan duk ranta a jagule.

Jiki a sanyaye tai salama gida ganin mahaifiyarta a dakin girki da sauri ta ajiye jakarta ta shiga tayata, suna aikin suna hirarsu irin ta diya da mahaifiya can Faanah ta nisa da hannu take mata alamun"meke daminki yanayinki ya sauya?"murmushi tayi ta girgiza kai alamun babu komai.Bata sake magana ba amma tasan ba yadda tai ba, suna gab da gamawa mahaifinta ya dawo aiki nan mahaifiyarta ta barmata aikin ta karbi kayansa zuwa sashinsa.Da murmushi ya nufo kichen din yace"Dr Beenah Baana Biu" ta turo baki"kaga Abbuna kadaina cemun bana so".Cikin murmushi ya shafi gemunsa"ku kasance cikin shiri graduation d'in Yayanku k'arshan wata daku za'a Kano".Tsale tai tana murna"naji dadi Abbu Yaya zai dawo nasamu me lesson din tajweed a gida, dama kai aiki yana yi maka yawa.Noma asibiti ga kiwon kifi, dan ma kana da masu kulawa.Allah Abbu tausayinka nake wasu lokutan"."Beenah diyar Abbunta, kema kike karfafun guiwa kan dogaro da kai Alhamdullilahi kuma gashi an samu,murna zaki yi shima Baana karki manta gwanine kan harkar noma koda ya dawo zai d'orana kan inda ya tsaya.Kedai ki juri yimana addu'a.Batun takardunu gobe ku shirya ku amso keda Marwa result ya fito,sai muga in an dace amema muku gurbin karatu.Har yanzu kina kan bakanki akan likitan mata ko?".Cikin murmushi ta daga kai hadi da furta"eh! Abbuna Baana ne ya zab'amun" "Allah yasa kin ci couse din da zai baki damar hakan" "amin Abbu".
Sashinsa ya wuce ta bishi da ido tana murmushi tare da jin-jinawa mahaifinta.Kafin magarba ta gama ta shirya musu wajan cin abinci, ana kiran magarba mahaifinta yaja su jam'i sukai sallah suka dora da karatun umdatul ahakam, ya biya mata ta maimaita ya jiye mata hadda suka dora da sallahr isha'i da kuma shafa'i da wutri daga nan sukaci abinci.Suna gamawa mahaifinta ya mike yace zaije wajan Dr Hannafi,bai jima da fita ba Hajja Faanah ta umarceta ta kaiwa Hajjansu abinci cikin nutsuwa ta dauka ta tafi.Da sallama ta shiga soron gidan, duhu sossai kasancewar babu nefa gabanta ya fad'i jin motsi ta daure ta shiga tana gab da wuce soron wal! Aka kawo nefa ta dago idonta a sukwane hankalinta yai mummunan tashi ganin Marwa da Muhuyyideen cikin wani irin yanayi.Take ta dafe kanta dake barazanar fashewa ta wuce su a galabaice, kai tsaye sashin Hajja ta nufa ta kai mata abincin nan ta zauna suna taba hira tsoron futowa take kartai mugun gamo.Anan take bawa Hajja labarin graduation din Baana da batun result dinta da zasu amso gobe.Ta jin-jina kai tace "Beenahzirahtu kema karatun yahudancin zaki yi? Bazaki aure ba kinaganin Marwa tana kula samari ke ko mashinshini babu kodai saina samomiki maganin farin jini? Gaki kyakkyawa rubarkallah amma shiru kake ji Malam yaci shirwa, wato kina biyewa hudubar ubanki da Baana ko? ".

Beenah ta tamke fuska, cikin zuciyarta tana alawadarai da samari irin na Marwa ta muskuta tace"Kijumun tsohuwar nan, watoma banda farin jinin samari? Toni samarin ne bazan kulaba saboda banda lokacin su karatuna shi ne gatana su kansu mazan basusan auran jahila.Kuma ma kike cewa karatun yahudanci zanyi zuwa fa zanyi in koyo yadda ake amsar haihuwa baki ji dadiba ace jikarki zata koyo hakan? Babu ruwan Baana dama can inason karatu, ke kike cusamun kinsa gara na addini to Hajja kowane nada muhimmanci kin gani neman ilmi yanzu na soma tunda ina dame tsayamun.Kajimun Kakus kawai tsohuwa dake zaki hanani karatu.Ita Marwan aidama bata son karatun run fil'azal".

"La'ilaha illalah walahi yarinyar nan rokiya za'ayimiki auran ne bakya so?" "Hahaha! Kai Kakus rukiya ake cewa bafa rokiya ba".Tai waje da gudunta tana dariya,karaf sukai karo da Marwa cikin sauri ta warce jikinta tana binta da kallon kin bani mamaki.Jikin Marwa yayi sanyi ta sassuta murya"Dan Allah Beenah ki rufamun asiri, walahi bazan sake ba".Ta girgiza kai tana mamaki yau ita Marwa take yiwa magiya lallai duniya juyi-juyi inda ranka kasha kallo. Murmushi tayi tace.
Tace"Me zan miki Marwah?Rayuwa ce fa ke kika zab'awa kanki,kowa da kiwon daya amshesa makocin mai akuya ya sai kura nidai iyakacina nasiha.In kin d'auka kanki, in baki dauka ba kanki wallahi kiji tsoron Allah ki taimaki kanki da rayuwarki kisani in kin b'uya a idon duniya toh fa baza ki b'oyewa mahallicin kiba komai zaki yi yana kallonki.

Kuma wallahi sai kinyi nadama, domin shi Namiji bashi da tabbas ko gobe wata zai sake ya barki da k'uncin zuciya.Waima meye riba a rayuwar da kika d'auka......?".

"Ke dila ya isheni dan kinga nai miki sakwa-sakwa? Ina ruwanki da rayuwata?Kabarinmu d'aya?Aikin banza gayar na ayyaro".
Jikin Beenah ya yi sanyi tai murmushi"kishirya inji Abbu gobe k'arbo result d'in mu"
"Ke ya dama ni nakama dahir".Bata tankaba ta wuce,jiki a sanyaye Beenah ta wuce gida tana mamakin Marwah.

Da sanyin jiki ta shiga gida gudun kar Hajja ta ramfota yasa tai gum.Ta nemi wajen kwanciya ta kwanta,sai dai data rufe ido hotan Marwa ke mata gizo hakan yasa ta mike ta d'auro alwala ta soma jera nafifili har goshin asuba.Washegari da wuri ta gama aikinta, ta sallami d'alibanta ta wuce karbar result d'inta.

Tunda ta nufi office d'in exam officer d'in su gabanta ke fad'uwa, da Uncle Tunde ta soma karo ya washemata baki ya gonar auduga, cikin girmamawa ta gaishe shi ta wuce ciki da sallama.Saida ya gama rubuce-rubucensa sannan ya d'ago yana dubanta fuskarsa d'auke da murmushi."A'a Beenah yar baiwa yau kece?"
"Eh! Malam nice" ta amsa tana sadda kai k'asa"."Hmm! Beenah kirkinki ya yi yawa, tunda kika tafi babu ziyara kodayake Baby tacemun kina fama da d'alibai ko?"
"Eh! Malam". "To! Ubangiji ya taimaka yai jagora ai dogaro da kai abune mai kyau ki dage kinji".
"Na gode Malam".

Wasu fayal ya janyo yai rubutu na tsayin mintuna biyar, ya dubeta yai murmushi ya saka sitamfin a d'ayar,d'ayar kuwa sai da ya girgiza kai ya numfasa ya dubeta."Beenah result ba yau ba sai ranar Monday zamuyi taron sallamar d'alibai, taron harda iyayyen yara ko wakilai,ga takardar gayyata kikaiwa Abbunki dana Marwah".

Jiki a sanyaye ta baro makarantar, kasancewar Juma'a ce bata samu Dr a gida ba sai Bakura, bayani tai masa ya karbi takardun ta wuce gidan Hajja tana mata tsiya.

Tsayin kwanaki biyu, Asabar da Lahdi Beenah cikin damuwa ta yi su saboda tunanin result d'inta,sosai mahaifinta ya lura da yanayinta,nasiha ya zaunar da ita yai mata mai ratsa jiki sosai,nan da nan ta ware ta saki jikinta.

RANAR LITTININ
Shiri sukai sosai Hajja Faanah,Dr da kuma Beenah sai Bakura da Marwah,fir Yakura tace babu inda zata je aka kad'a aka raya tak'i,tilas suka tafi babu ita.

Harabar makarantar d'inke take da manyan gwamnati da malamai yan boko, kowace d'aliba sanye take da (uniform) bai d'aya sun zauna cike da nutsuwa,nan da nan aka soma gudanar da taron.Beenah aka kira ta bude taro da addu'a matsayinta na shugabar d'alibai, cikin nutsuwa ta taso ta karbi sifikar nan da nan muryarta ta karad'e ko'ina da daddad'ar sautin muryarta, da yawa daga cikin mahalarta taron fuskarsu d'auke take da murmushi a dalilin nutsuwar da suka samu,wasu kuwa tasbihi suke ga ubangiji (S.W.T) haka ta k'arasa karatun ta dawo ta zauna,wajan ya d'auki kabbara, nan da nan masu bidiyo sukaita d'auka.

Shugaban makaranta ya mik'e yai jawabin godiya ga iyayen yara,Malamai da kuma Beenah,ya mik'a sifik'a ga mai gabatarwa,aka cigaba da gudanar da taron cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.


Rukunin farko na d'aliban da sukai kokari aka soma gabatarwa,sune masu credit tara, bakwai takwas sai mai creadit sha d'aya.Kowace d'aliba burinta ace itace ta farko,a hankali aka soma kiran sunayensu kamar haka;
Falmata Mustapha nada creadit takwas,Kundum Aliyu creadit bakwai,Aysa Bunu creadit tara sai Beenah Dr Hamza creadit goma shad'aya.Take wajen ya d'auki tafi raf-raf ana jin-jinamata.Bayan hayaniyar ta lafa ne aka cigaba da kiran d'alibai suna karb'ar kyautuka daban-daban.

Babu kyautar da Beenah bata karb'a ba,kama daga kan tarbiyya,tsabta da kuma wacce tafi kowa k'okari.Idan ka dubi fuskar mahaifanta babu abinda zaka gani sai murmushin farinciki da suke yi,bayan komai ya lafa akai kiranta don ta tofa albarkacin bakinta.

Cikin nutsuwa ta taso,kanta a k'asa tana d'ago kai sukai ido biyu da Baana ya sakarmata k'ayataccen murmushi,ta sadda kai k'asa zuciyarta cike da tarin tambayoyi. "Yaushe yazo? Waya gaya masa?". Tambayoyin da ta kasa samun amsarsu ta hak'urewa kanta,ta hau step ta amshi abin magana ta d'ago ta saki murmushi saboda ta samu hanyar cusawa Hajja ra'ayinta na son karatu.

"Assalamu alaikum, ina godiya ga ubangijin hallita daya bani ikon ganin wannan rana mai matuk'ar muhimmanci a rayuwata,godiyata ga Malamaina da kuma iyayena tare da.....ta dago ta kalleshi ta juya ta kali kowa sannan ta sake sakin murmushi a karo na biyu wanda hakan ya burge kafin taci gaba da bayaninta.
"Awana Baana Bakura bisa jajjurcewarsu wajan ganin na samu nagartaccen ilmi, Alhamdulillah yau gani a mataki na biyu a fanin karatu,hakan na nuni da cewa mafarkina yana gab da cika. Kirana gareku 'yan uwana d'alibai,iyaye mata iyayena maza shi ne ilmin 'ya'ya mata...D'if wajan ya d'auki shiru saboda gagarumin aikin da kowa ke ganin Beenah ta d'auko mai matuk'ar tsauri.Bata damu da sauyawar jama'ar dake wurin ba ta cigaba.
_Mata!Mata!!Mata!!! Mata sune k'ashin bayan kowace al'ummah,domin idan mace d'aya ta samu wadatacan ilmi tamkar an ilmantar da al'umma ne bakid'aya kasancewarta makaranta ta

Please Login or Register in order to submit comment