Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kullum sai Fannah ta lek'a musamman in Bakura yana bawa shuka ruwa, a rayuwarta tana son koran ganye.Tun Bakura na korarta har sukai wani irin sabo, har gona take zuwa noman gona.Sossai Bakura ya dawo tausayin Fannah, masu irin lallurarta nasan kusancin 'yan'uwa yau ga Faanah babu uwa babu uba bale Hajja. Ana saura kwana bakwai bikin Bakura Hamza ya dawo, ya yi murna da yadda Bakura ya ware sashin su saboda baya son Yakura ta raina masa Hajjansa. Sai dai ya kad'u sossai da yadda Bakura yai musu, karan tsaye wajan sai da gonarsu lamarin da har sai da sukai musayar yawu kan batun.


ku daka ce ni.
[8/8, 9:57 PM] Sanah S Isma'il Matazu: *'YAR KURMA*
©
*SANAH S MATAZU*
®
*N.W.A*
*13*
Kwanci tashi suka cinye samister d'aya, suna
shirin fara jarrabawa kullum adu'arsa ubangiji
yasa ya haye matakin karatunsa.
Faanah na samun kulawa dai-dai gwargwado
wajan Hajja,tun bayar tafiyar Hamza ta fahimci
kad'aici ya yi wa Faanah yawa, ana haka aka
bud'e wajan koyon sak'ar hannu kusa da su.
Batai wani jinkiri ba ta yankar mata form ta
soma zuwa.
Tana jin dad'in zuwa sossai, nan da nan ta maida
hankali akai ta soma yin safa da abun goge
gumi.
Tun bayan komawar su Yakura gida, Yelfata ta
kasa nutsuwa. Kwata-kwata zuciyarta na wajan
Hamza ya burgeta matuk'a amma data tuna
Faanah sai gabanta ya yanke ya fad'i ta tabbatar
akwai wata alak'a irin ta zuciya tsakaninsu.
Saboda yadda taga yana nuna mata kulawa a
zahiri, da kuma yadda ya taso mata tamkar
mayunwacin zakin da ya shekara be ci ba.
Zaune take tayi nisa cikin tunanin, Yakura ta jima
a tsaye a kanta bata san tana kanta ba har saida
ta d'an tab'ota. A jiyar zuciya ta saki tana
dubanta"lafiya Yalfata, meya sameki ?"Hmmm!
Babu komai Yakura". "Ke! Dakata ni zaki b'oyewa
damuwarki?", tayi jigum tana tunani ta nisa tace
"Yakura inason Hamza". Cikin tashin hankali ta
zaro ido "awaana Bakura? ('Dan uwan Bakura).
Kai ta d'aga mata tana jinjinawa. Yakura ta
jinjina, ta sake jinjinawa taja fasali ta dubeta.
Kinsan dai bisa dukkan alamu wannan Kurman
budurwar sace, dan haka ki sake dabara sai kace
wata mara masoya". "Ni dai shi nake so Yakura
wa nake dashi? Bayan duk sun gudu, kema ki
hanzarta rik'e Bakuran da kike homa a kansa
kafin ya sub'uce miki". Duka ta kai mata tare da
cewa"ni zaki yiwa iskanci?". Da gudu tayi ciki,
karaf sukai karo da Yalta k'anwar Kundum. A
zafaffe ta kwad'awa Yelta marin daya gigitata
har ta saki jakar islamiyarta, da sauri ta taro
abarta saboda muhimman littatafan da suke ciki.
Bata tanka ba ta sa kai zuwa sashinsu, fuskarta
tayi red'u-rud'u abinka da farar fata cikin kunar
rai ta ajiye jakarta tana taya Mamansu aiki da
take bakacan tsakin biski. Da kulawa ta
dubeta"Yalta lafiya?" Share hawayanta tayi, tana
yi mata bayanin abinda Yalfata tayi mata.
Murmushi tayi ta jinjina kai, "karki sake ki kulata
ko me zatai miki na gayamiki, share hawayanki
komai lokacine. Fatan dai kinyi karatu sossai?".
Tausayin mahaifiyarsu ya cikata, saboda tasan
ko kara ta kaiwa mahaifinsu babu matakin d'auka
Yagana itace mace mai kwalli a gidan.
Kwanci tashi aka soma gudanar da maganar
bikin Yakura da Bakura, rawar jikin da Bakura
yake har mamaki yake bawa Hajja. Ta dai tattara
ta zuba masa ido,tayi juyin duniya yai al'adun
mutan garin Biu a wajan bikin ya kaffe al'adun
Kanuri zai yi lamarin daya haifar musu da sab'ani
sossai. Gonarsu guda biyu yasa d'aya a kasuwa
ya siyar duk sabo da hid
Cikin kwanciyar hankali Bakura ya soma neman
auran Yakura.Hajja ta tattara ta zuba ido kan
lamarin, kullum cikin yimasa adu'a take.
BIKIN KANURI
Al'adar Kanuri wajan gudanar da auransu, ya
bambamta sossai da sauran mutane. Misali. Su
dai a bikin bare-bari da farko idan kaga yarinya
kana so, idan kuka shak'u kai da ita kuka aminta
to zaka fad'awa iyayenka itama ta fad'awa nata
iyayen akan cewa za'azo tambaya. To tambayar
gidan mazane zasu sayi alewa da goro da minti
da cingam, masu yawa da kuma kud'i karshe shi
ne dubu ishirin ba'abada k'asa da haka sai sama.
Akwai masu bada dubu hamsin, tamanin harma
d'ari kawai dai-dai k'arfinka amma kar a gaza
ashirin shi ne a talauce. Wannan bayani dana ke
muku duk kayan nagani inasone shi ne su ke
cewa tambaya.
Daganan kuma sai kayan toshi, shi kayan toshi
yadda kukasan kayan aure haka ake had'asu
wasu saitin akwati mai biyar wasu mai hud'u
wasu mai uku. Harda masu dozin musamman
fanin gidan sarauta. Za'azuba kayan duniya ciki
k'awaye da 'yan uwa aita zuwa kallo. Idan an
gama kallo kamar sati biyu sai a rabawa k'awaye
da 'yan uwa rabin kayan kamarsu fant su
mayuka su powder (hoda).Hada masu saka gwal
da kujerar makka.Abin sai wanda ya gani, hakan
al'ada ce wanda bai yi ba da wanda ba ayi wa ba
ya zama abun tsegumi.Da wuya ma a kasa yi,
tunda suna girma al'adunsu sai dai wata bata kai
wata ba.
Fanin danginki uwa da uba kuma, akan basu
turame mayafai ke kuma saiki d'inka sauran.Idan
aka kwana biyu sai a shirya kayan sa rana.Aje a
yanke rana amma basu fiye yanke ranar dayawa
ba.Yayin da ya rage saura sati biyu biki zaki
amso anko.Miji shi zai wa k'awayenki anko.Ko
sun kai ashirin shi kuma zai bada kudin turare da
gyaran jiki.Dakuma kudin shiga kasuwa na
k'unshi kuma duk ba kudi kadan ake bayarwa ba.
'Bangaran sadaki kuwa mafi yawa da sisin gwal
suke biya, hakan al'adarsu ce.
Sossai Bakura ya yi hidimar auran Yakura, duk
wata al'ada da ake yi sai da ya yi ta.Arzik'insa
d'aya Yakura bata da k'awaye da yawa saboda
masifarta.Haka ya zage ya yi hidima sossai,
b'angaran gidan su daga dama ya bige ya yi
sabon gini.'Daki biyu da babban fallo da kitchen
da band'aki sai yai doguwar katanga a kai musu
tsakani da Hajja.Wajan yasha gyara da siminti,
ya dasa fulawowi koraye wanda suka k'awata
tsakar gida.
Tunda aka gama ginin kullum sai Fannah ta lek'a
musamman in Bakura yana bawa shuka ruwa, a
rayuwarta tana son koran ganye.Tun Bakura na
korarta har sukai wani irin sabo, har gona take
zuwa noman gona.Sossai Bakura ya dawo
tausayin Fannah, masu irin lallurarta nasan
kusancin 'yan'uwa yau ga Faanah babu uwa babu
uba bale Hajja. Ana saura kwana bakwai bikin
Bakura Hamza ya dawo, ya yi murna da yadda
Bakura ya ware sashin su saboda baya son
Yakura ta raina masa Hajjansa. Sai dai ya kad'u
sossai da yadda Bakura yai musu, karan tsaye
wajan sai da gonarsu lamarin da har sai da sukai
musayar yawu kan batun.

Cikin ikon Allah aka soma gudanar da bikin Yakura,shagali ake sossai abin sai wanda ya gani.Yagana ta fito da amarya ras,sai k'amshi take tasha gwala-gwalai.

Anyi biki an kare aka kai amarya d'akinta, masha Allah hada gararta turare kuwa ya yi b'ari kamar kamfani.Tunda aka kawo amarya tsayin kwana biyar, bata tako ta gaishe da Hajja ba.Sabo da zuwa yasa Fannah kullum tana sashin Yakura da wannan damar take galaza mata ta fannonni da dama.

Itace sata wankin kwanuka,girki hada wanki, lamarin na ciwa Hajja tuwo a kwarya,tayi-tayi ta hanata zuwa ta ki dainawa haka ma Hamza.

Kwanan amarya goma yaran gidansu sukai k'ungiya suka kawo mata ziyara.Sun barraraje suna shafta Fannah nata hidimar gida banda Yelfata da ta koma gefe tai tagumi zuciyarta taf damuwa,burinta kawai san ganin Hamza Yakura ce ta kula da yanayinta ta jata suka shiga d'aki.Suna shiga da sauri Yelta tai waje takamawa Faanah aiki,ita dai tana burgeta.

Dubanta Yakura tayi tace.
"Lafiyarki kuwa Yalfata?"ta fada tana dubanta.
"Lafiya ba lau ba Yakura zuciyata na neman fashewa kin sani sarai ina kaunar Hamza amma na lura hankalinsa kaf naga waccan kurmar".Tak'arasa maganar da alamun rauni.

"Mtsss! Kin cika abun haushi walahi Yalfata,du du nawa yaron yake da zai dameki muka bi da Bakura ma bale Hamza?".
"Hmmm!Yakura walahi na buga iya bugawata kafin in tunkareki gazawata yasa na fito miki da maitata fili.Gaskiya zan fito in gaya masa abinda yake raina kawai in huta".
"Shikenan ki gwada ki gani".

Kamar an jeho shi ya shigo sashin ransa a b'ace kwata-kwata ya manta da bata ji"Fannah!Fannah!!Fannah!!!".Hannu yasa ya fincikota daga dakin girkin,ganin yanayinsa yasa tai saurin hada hannuwa alamun ban hak'uri.Harara ya jefa mata da gudu tayi sashin Hajja tana numfarfashi.Da sauri suka fito gaba dayansu, ransa a bacce ya nunata da yatsa"Yakura ya soma isarki ban shiga sabgarki ba karki takuramun. Banda rashin imani me wannan baiwar Allah ta tsaremiki?Kurumta fa ba rashin 'yanci ba ne,kurumta ba rashin gata bane........"bai k'arasa ba ta tareshi a zafaffe.


"Har wani gata ne da mai nakasa irin wannan?" Ta fad'a tana nunata da baki,ta cigaba "Wacce ce ita?Wanne gata ne da'ita?Wadda ba'asan asalin nata ba kake hankoro a kanta?Banda kai din wazai kwasa?Kaima dan kana lallab'awa cikin dare ne kana lalubeta shiyasa meye bamu sani ba?Bonono kawai.......a dai bi sanu shi ramin k'arya k'urarre ne........"bata k'arasa ba ya zabga mata mari kyawawwa guda uku,daga bayansa a ga zabga masa.Cikin zafin rai ya juya ganin wanda sukai masa hukunci yasa jikinsa mugun sanyi. Bakura ne da Hajja,cikin fushi yake dubansa"matar tawa zaka mara?".

"Hamza meyasa kake da zafin zuciya?Hakan ba hallayarka bace".Cewar Hajja.Cike da fitsara Yakura tace"haka zaki ce mana,ai ba karya nayi ba tsohuwar banza ba d'akinki yake turata ba".Cikin zafin rai Hamza ya rarumi muciyar da Yelta take hada biski ya kwadawa Yakura a goshinta.Wani wawan ihu ta saki,Bakura yayi kansa cikin kid'ima. Tsawa Hajja tai masa ya juyo jikinsa na rawa "walahi Hajja sai na d’auki mataki bazan yadda ba".

"Zo ka rama a kaina".
Jin furucinta yasa jikinsa yin sanyi.

Sauke hannu ya yi yana huci,ransa in ya yi dubu ya b'aci zuciyarsa taf k'unci ya ja Yakura suka shiga sashinsu tana ta kwarma ihu.Hajja ma taja Hamza suka koma nata sashin.Sun jima babu wanda ya tanka daga can Hamza ya dago idanunsa jajjur ya fesar da iska me zafi yace"Hajja ki amince min in auri Fannah".

Tai murmushi irin na manya zuciyarta k'war cike da tausayins"zaka auri Fannah Hamza,amma kaga yanzu akwai tarin abubuwan dake gabanka ka bari mubi komai a hankali".

"Shikenan zanyi yadda kike so",murmushi tayi nan ya dinga jan Fannah da hira rai banza ya had'a hannayansa alamun ban hak'uri ta juya kai.Saukowa ya yi ya sunkuya tare da kama kunansa,murmushi ta yi ta sauke hannuwan suka cigaba da hirarsu.A ransa tausayinta yake,kudin wajan Hajja ya karba ya wuce gona aka dan yin aikin daya dace.


'Bangaran Yakura da k'yar Bakura ya lallasheta tayi shiru,yana fita Yelfata ta turo baki "gaskiya Bakura kin cucceni yanzu Hamza zai kara tsanar ahalinmu".Cikin masifa ta tureta gefe"baki da mutunci Yelfata baki dubi iskancin da yai munba wato ke soyayya ko?".Yelta ta k'unshe dariyar da take cinta, banda Allah ya kara babu abinda take musu a ranta.
A ranar Hamza ya siyowa Faanah shukoki ya dasa a gidan Hajja,shikenan ta janyewa zuwa gidan Yakura.



Yelfata tayi gum da bakinta,koda wasa bata gayawa Yagana abinda ya faruba.Fanin sakarta abun ya girmama nan da nan tai suna a garin gata da k'wak'k'alwar fitar da kala-kalan saka.Har abun goyo take da abun rufe televission sossai Hamza ya ji dadi dakin soro da yake sauka in ya dawo ya kashe ya fito mata da kofa.Anayin girbin gauta nan ya zuba mata jari sossai,in ta saka set riga da wando da safa da zanin goyo na yara sai asaka a leda.Nan da nan makarantun nursery suka soma bata aikin huluna da riguna.

Hankalin Yakura ya tashi bak'in ciki murarran duk lokacin da Hamza ya dawo hutu tare suke aikin.A haka ya gama karatunsa ya zauna jiran sakammako,saidai bai zauna zaman kashe wando ba noma ya dirafafa sossai.



Kwanci tashi result d'in (sakammako) Hamza ya fito,babu jinkiri ya samu aiki wani asibi mai zaman kansa cikin garin Maiduguri.Hajja tayi murna sossai,haka ma Fannah da Bakura duk da babu jituwa tsakaninsu.Zaman Yakura da su Hajja abin sai wanda ya gani rashin mutunci take shimfidawa san ranta,babu wanda ya isa ya hana ta gama da Bakura sai abinda tace.

BAYAN SHEKARA BIYU.
Abubuwa da dama sun faru,ciki hada auran Yelta kanwar Yakura yar dakin su Kundum.Kwatsam sai ga bayyanar ciki a jikin Yakura babu wanda bai yi murna da hakan ba.Hajja tamkar ta goyata duk iskancin da take mata bata dubashi ba tausayinta take sossai saboda cikin me laulayi ne.


Yakura ta bijiro da san abata Fannah dan taimakawa wajan aiki,atabau Hamza ya nuna rashin amincewarsa a wata ziyara da ya kawo musu ranar hutun k'arshan mako.Har saida sukai hatsaniya da Bakura.Yakura tace ta hakura Yalfata zata d'auko,dama da gaya ta tayar da maganar Hamza yana nan dan tasan bazai amince ba saita bijiro da Yalfata don cimma burin su.


Hamza aiki yake sossai da gaskiya,gidan su na Maiduguri ya gyara ya zauna yana kulawa da Hajja da kanin kakansu sossai uwa uba Fannah.Duk wata yana zuwa dubasu ya kawo musu kayan arziki.Cikin Yakura nada wata uku aka kawo Yalfata, adaidai lokacin Hamza ya bijiro da batun auran Fannah ya turo kanin kakansa ya nema masa auranta wajan Bakura.


An yi komai cikin mutuntawa,sai bayan an gama komai sannan Bakura ya ke bawa Yakura labari lokacin Yalfata ta kwashe biski tana hada miyarsa tsabar kaduwa batasan lokacin da ta saki tukunyar miyar ba ta kwaro a.............

Cikin ikon Allah ya zuba a kasa bai taba kafaffunta ba.Bakura ya bita da kallon mamaki,bai tanka ba sai sanu da yayi mata Yakura kuwa takaici ya hanata magantuwa.Bakura ne ya fita saboda kiransa da aka yi a waje,tamkar jira Yalfata take ta dora hannu a ka ta saki kuka mai cin rai.Yakura tana kallonta sai da tayi mai isarta sannan ta tanka.
"Kitashi ki had'amana miyar kizo musamu mafita".
Bata jira cewarta ba ta shige d'aki,kwafa Yelfata tayi a ranta tana ayyana muguntar da zataiwa Fannah.Cikin mintuna shabiyar ta kammala komai,ta nufo wajanta ta dinga binta da kallo tamkar sabuwar makanta harta zauna.

"Hmm! Majanuniyar Hamza har kin gama?".
"Kome zaki kirani bai dameni ba,burina samun mafita ke nake sauraro".Cewar Yelfata.

"Hmmm!Sanin kanki ne baki da gurbi a zuciyar Hamza,saboda yasan wacece ke ta fanin hallaya duk da bai zauna dake ba yana ji ana fada.Dan haka samunsa zai miki wuya sossai.Mafi a'ala mubi kansa da Malamai.Saidai gaskiya zaki sha wuya Hamza yafi Bakura rikon addinni shiyasa kikaga nayi nasara kan Bakura farat daya".

"Nifa Yakura ba gane wannan batun naki nake ba.Mafita kawai nake nema,haka kawai kin tsaya yimun dogon sharhi babu fashin bak'i kawai ki fito kicemun ga mafita".

"Yelfata har yanzu ke yarinya ce,nafi ki son ki auri Hamza walahi sai yanzu nake takaicin auran Bakura Hamza namiji har namiji abin tunk'aho.Ki dubi yadda ya zama abin kallo".


"Hahhahaha!". Yelfata ta kwashe da wata shu'umar dariya,ta cigaba."Ke yanzu Yakura ko kunya baki ji ba gotai-gotai dake ki auri Hamza kinfa girmeshi kai alla sitiri buk'ui".

Duka ta kaimata a zafaffe ta kaucewa dukan tana gimtse dariyarta.Gimtse fuska tayi"kinga Yakura kibamu mafita mubar shirme dan Allah zuciyata zata fashe".

Rada tai mata a kunnuwanta suka kyalkkyale da dariya,tare da tafawa."Shawara mai kyau babbar yaya".Cewar Yalfata.

Ana kiran la'asar Yalfata tai wanka ta shirya cikin lafaya.Sky blue abinka da farar mace tayi kyau sossai.Hoda ta shafa ta kawo kwali ta tisa biy-biyunta tar ya fito ta hade gashin kanta ta saka barimar hanci blue dark.Sak Kanuri,wasu turarruka ta dinga bin jikinta dasu masu matukar kamshi kai Kanuri kunyi inji Sanah.Cas ta fito bayan ta yanne jikinta da lafayar.Tana fitowa Yakura tasa shewa "kai gaskiya dole ki rud'a Hamza autar Yagana".Murmushi tayi bata tankaba ta nufi hanyar fita zuciyarta na dukan uku-uku.

Kai tsaye hanyar shagon Fannah ta nufa,duk agama tasan yana can gabanta ya tsananta bugawa lokacin data nufi shagon.Zaune ta hangoshi cikin shigar manyan kaya kansa yasha hula yar Maiduguri gefansa Fannah ce sanye cikin lafaya 'yar ubansu mai tsadar.Zuciyarta tai zafi,bata raba d'ayan biyu Hamza ya yi mata ita.Takai idonta kan hannunta tasha warwarayenta guda uku masu tsada,cikin mutuwar jiki taji kamar ta koma tayi ta maza ta karasa.

Da salama ta shiga,dai-dai lokacin Hamza ya dago kai kallon da yai mata yasa gabanta tsananta bugawa........
Cikin sanyin jiki ta karasa ciki, muryarta a raunanne tace"Hamza wajanka nazo"ya d'ago yai mata diban karan mahaukaciya ya kauda kai can kuma ya gimtse fuska ya dubeta"lafiya?".
Haushi ya kasheta ta aro juriya "magana nake so muyi"gyara zamansa ya yi saboda yanayinta ya bashi tausayi sossai zatonsa ko wani ne babu lafiya ya numfasa yace"ke nake sauraro".Wani k'ududu ya tokare mata zuciya"a gaban wannan banzar zamui magana?"Ta fad'a a ranta, can ta saki murmushi"koda yake ai kurma ce duk a ranta tayi maganar.Karasawa tayi ta samu guri kusa dashi dab da dab ta zauna, cikin sauri ya muskuta yana duban fuskar Faanah da ta sauya yajayi da alamun damuwa tattare da ita.

"Ina saurarranki"ya furta fuska babu walwala, ta rausayar da kai gefe tai fari da idonta har yai ta maza ya d'auke kansa.

"Dr zakayi mamakin abinda yake tafe dani, amma ba abin mamaki bane in har zakaimun uzuri. Zuciyata ta dad'e tana k'aunarka,ganin babu mafitar da yafi sanar dakai yasa na yanke shawarar aikata hakan, ina fatan zakai maraba dani cikin zuciyarka".Galala yake kallonta,yaro da wayau harta dire batunta,tsabar takaici da mamaki kasa magana ya yi can ya nisa a ransa yana tunanin mai zaice mata. Murmushi ya yi ya dubeta.

"Gaskiya naji dadin kalamanki Yalfata, amma wani hanzari kiyi hakuri zahirin gaskiya kinsan an yi maganar aurena da Fannah. Kuma ko babu batun Fannah bazan iya auranki ba,saboda bakya cikin tsarin matan da nake burin aura ta kowane fanni".

Cikin zafin rai ta dubeshi"duk wani rashin tsarina har nakai wadda take da nakasa tare da'ita? Kurma fa Hamza, Kurma ce ta yaya zaka had'ani da'ita bayan tana da tawaya a rayuwarta? "Ransa yai mummunar b'acci a harzuk'e ya tashi"Yalfata Kurmar da kika raina ta fiyemin ke koran juji".
"Koran kuji? ".
Ta furta da alamun tambaya"Eh koran juji, mace kyakkyawa a gidan da babu tarbiya".Ya bata amsa kai tsaye ya cigaba."Fannah Kurma ce amma ta fiye mun ke sau dubun dubata, na tsaneki na tsani ahalinku masu tarin son zuciya kanku kad'ai kuka sani. Biyan buk'atunku kuke buri in kuka samu kowa ma ya rasa, inaso ki fita harkarta da ahalina as from today (daga yau).Ya fad'a da tsananin b'accin rai, cikin takaici ta dubeshi "walahi Hamza saina d'auki fansar abinda ka shukamun".Da gudu tabar wajan tana kuka, zama yayi yana numfarfashi zuciyarsa na zafi.
Da kuka ta isa gida tana bawa Yakura labari, hankalinta ya tashi tasan dama za'a rina an saci zanin mahaukaciya zuciyarta tai zafi sossai da kyar ta lallashi Yalfata. Hamza cikin sauri ya hadawa Fannah kayanta yanai mata nuni da su tafi gida. K'yam ta tsaya ta kafeshi da ido tana tambayarsa dalili, bai boyemata abinda ya kawo Yalfataba saboda yana so tayi nisa dasu. Aikuwa ta shak'a hada kukanta nikaina naci dariya Kurma da kishi. Koda suka koma gida saida ya bawa Hajja labari, yana ta dariya abinsa, hankalin Hajja ya tashi dannewa kawai take zahirin gaskiya tana tsoron sharin Yakura da danginta.


'Bangaran Bakura abin ya girmama ko zuwa gaishe da Hajja sai ya gadama. Ahaka Hamza ya koma hutunsa, ransa fes cike da kewar Fannah tunda ya koma ya dirfafi aikinsa sossai, hata noman ya dora masu kulawa da fanninsa saboda Bakura gauta yake yi shikuma barkono.Lokaci zuwa lokaci yana aiko da kudin aiki. Tafiyar Hamza da sati biyu suka soma fuskantar wata gaggarumar matsala.Da farko duk sanda Fannah tai aiki ta gama a shago take barin kayanta, sai lamarin ya zamo mata barazana a gareta.

Da zarar tayi aikin ta gama in ta dawo gida, washegari zata iske an b'ale mukulin shagon an lallata kayan, haka in ta kwshe ta gyara wanshekare ma haka zata iske anyi. Tun tana boyewa Hajja harta kai ga furta mata abinda yake damunta, hanlakilta ya tashi, kafin cikar wata guda duk wani abu mai amfani na shagon an lallatashi kaf.Lamarin daya haifar musu da nakasu sossai, saboda kudin dasu suke hidimar gida kafin Hamza ya yo aike tunda Bakura baya ta tasu. Haka suka tattara suka rufe shagon,hakan ya haifarwa da Fannah kad'aici da damuwa Hajja na kokarin kauda hakan abun yaci tura. Wata sabuwa kuma duk lokacin da Fannah ta fita yara saita zame musu abar tsokana, da jifa suna kiranta kurma Yalfata kuwa yar gida take zuwa kamar abin arzik'i tacewa Hajja tazo taya Fannah hira, tun Hajja ja kaucewa hakan harta amince da wannan damar takewa Fannah kisan mimmik'e ta faki idon Hajja taita mintsinin Fannah.

Fannah babu baki sai dai in tagaji da azaba ta bar wajan ta shige daki.Hamza kuwa kulum hankalinsa yana gida,burinsa kawai yanzu auran Fannah kwatsam ranar wata Lahdi aka zo musu da batun zuwa garin Biu dan yin allurar rigafin kunne saboda kusantowar damuna.A ranar yaja abokinsa Alangoburo wanda shi gynean ne suka had'o kayan toshi akwati hud'u washegari suka nufi garin Biu.

Ranar littinin da safe tawagarsu sukaiwa garin tsinke, a masaukin ma'aika aka ajiyesu Hamza yaja Alanguburo suka nufi gidan Hajja. Hajja na zaune taji shigowar yara da kaya, ta mike tana tambayarsu shigowar Hamza yasa ta mik'e tana mamakin ganinsa ranar aiki.
Ranar littinin da safe tawagarsu sukaiwa garin tsinke, a masaukin ma'aika aka ajiyesu Hamza yaja Alanguburo suka nufi gidan Hajja. Hajja na zaune taji shigowar yara da kaya, ta mike tana tambayarsu shigowar Hamza yasa ta mik'e tana mamakin ganinsa ranar aiki.

Da murna ta tareshi aka shigar da kayan ciki,ta kawo musu ruwan sanyi dan saukar bak'i sun jima sossai baiga wucwar Fannah ba tun yana jiriya harya kai ga furtawa.

"Hajja ina Fannah? ".
Alangoburo ya yi dariya yana tsokanarsa.
"To majnunu Fannah"duka ya kai masa suna dariya. Nan da nan Hajja ta hau dube-dube "aikuwa shigowarku tana tsakar gida kodai tana fanin Yakura? ".

"Yakura? "
Ya fad'a fuskarsa a d'aure, bata bashi amsaba tai masa nuni da takalmanta da suke gaban k'ofar d'akinta. Bai tanka ba yaja hannun Alangoburo suka nufi d'akin, da sallama suka shiga das! Gabansa ya fad'i saboda hango yanayin da take ciki.


Cikin hanzari ya k'arasa ta d'ago kai suka ido gabansa ya tsananta fad'uwa.
Kuka take sossai,hada hawaye jikinsa yayi sanyi ya zauna kusa da ita tai saurin janyewa ta matsa ya kali Alanguburo ya kada kai.Cikin nutsuwa yai mata nunu da "menene? " kai ta kada masa alamun babu komai, kansa yai zafi sossai. A zafaffe ya bar dakin idonsa jajjir Alangubro ya rufa masa baya Hajja ya samu murya a tausashe "Hajja miya sami Fannah? ""Meka gani"?.Ta bashi amsa"kuka take"ya fad'a cike da raunin murya.
"Kuka?".
"Eh! Hajjah".
"Taf babban lamari", ta furta jiki a sanyaye take bashi labarin matsalar da suke fuskanta, kansa ya daure ya raunana muryansa"Hajja zanje in dawo ki lallasheta tayi fushi taki saurarona ina tsoron ubangiji ya kamani da alhakinta".
"Kaje Hamza zan ki da komai".
Kai ya kad'a suka nufi masaukinsu a hanya sukai kicibus da Bakura da murna ya taresu,sun jima suna magana nan yai masa batun auransa da Fannah harma da kayan toshin daya had'a yaji dadi sossai karshe ya gayyacesu cin abincin rana zuwa anjima sun ji dadi sossai Hamza ya dinga ayyana ansamu sassauci duk da baiga hakan a tare dasu Hajjah ba.

Da sallama suka wuce, koda isarsu kasa komai yayi, abokinsa ne ke tausarsa har yaji dama-dama.Karfe uku suka nufi gidansu sashin Hajja suka nufa, zuwa lokacin ansamu sasauci Fannah ta fito tana taya Hajja aiki. Da sallama suka shiga,Fannah ce tai musu shimfida ta kawo musu ruwan farau-farau.Hamza na kula da yanayin Fannah tun tana shan kamshi harta sake.

Anan Hajja take basu labarin matsalar Faanah, cikin takaici Hamza yace"yanzu Hajja aka rasa wanda zaibi mata kadin lamarin ina Bakura? "Murmushi kawai tayi tace"Yaro yaro ne".Babu wanda ya sake tankawa ciikinsu. Sunci abinci sossai suka zauna tattauna batun auran, Hajja ta dage Fannah nan zata zauna shi kuma Hamza ya dage Maiduguri k'arshe suka ajiye magana zata zauna anan saboda lallurarta Hamza bai soba dandai kawai kowa yaki bin bayansa har abokinsa da yayansa.Bakura abin nasa yayi sauki dama duk tsiyar asiri kwana arba'in ne balle ga jikin musulmi mummuni me bautar ubangiji.Sun ajiye maganar bikin zuwa wata d'aya, lokacin Hamza ya samu gidan dazai ajiyeta bayan sun gama ya zauna dala-dala yai mata bayani,sai da ta gama fahimtarta atabau ta nuna tafison ya gyara gidan Hajjanta su zauna a can, sossai Hajja taji dadin hakan dama hassashanta kenan dan dai kawai abinka da hakin maraya,gudun fadawa hakinta yanzu kuwa tunda ita ta amince Hajja ma ta goya mata baya. Hamza yaso kaucewa amma babu hali, Bakurama yaji dadin hakan.Dole aka kara bikin zuwa wata uku saboda yana son yaiwa gidan gyara sossai.

Tunda Bakura yajewa Yakura da batun zuwan cin abincin su Hamza take d'auki saboda ta samu damar iddar da nufinta.Sarai kan idonta aka wuce da akwatunan daya shigo dasu, zuciyarta ta tsinke sossai ta tabbatar auran Fannah na gab hakan na nufin kuncin kanwarta. Yalfata kuwa zazzabi me zafine ya rufeta, saboda takaici da bakin cikin abinda idanunta suka gani. A hakan

Please Login or Register in order to submit comment