Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farko ga yaro,a kwana a tashi._

_Ilmin d'iya mace zai iya kasuwa fanni daban-daban wato boko da addini.Ilmin addini shi ne mafi kyautuwar ilmi awajan kowane mahaluk'i mai neman dacewa ba wai ga d'iya mace kawai ba amma da yake akan d'iya mace nake magana shi yasa zanfi bada muhimmanci akanta._

_Yayin da kika riski kanki a b'igiran da basa b'ukatar karatun d'iya mace mai tsayi, karki zafaffawa kanki wajan cewa sai kinyi, maida hankali wajan neman ilmin addinni wanda zai zamo miki abin alfahari anan duniya da kuma gobe k'iyama.Dashi ne zakisan yadda zaki bautawa ubangijinki cikin tsarkakewa da nutsuwa,dashi ne zakisan kanki da abinda zai amfaneki.Gwar-gwardon ilmin da kika samu koda iya makarantar gaba da primary ne zai amfaneki ya amfani iyalanki muddun kinyi mai inganci.Ilimin boko bai zama koma baya idan mukai duba da yanayin zamani, saboda a yanzu anci gaba sosai komai saida ilimi.Ilmi baya zama b'atanci saidai akwai hanyoyin da suka dace abi wajan nemansa.Wasu lamuran da suka shiga cikinsa ne sukai katutu suka haifar da rud'ani a zukatan al'ummah da iyayyanmu Maza da Mata.Amma banda hakan babban abin alfahari ne ace yau mace ta taka wani matsayi na taimakon al'ummah musamman a harkar lafiya.Abin takaici zaka shiga asibitoci da dama kaga bamu da manyan likitoci mata sai maza, wanda wannan babban abun kaicone a garemu ace Namijine zai duba mace sab'anin mace yar'uwarta,kuma hakan ya samo asaline sakammakon k'arancin mata a wannan fannin,wasu suna so suyi amma babu damar hakan saboda rashin wadata yayin da wasu kuma da wadatar amma iyayensu basu basu goyon baya akan hakan ba._

Haqiqa ilmin 'ya mace nada matuqar muhimmanci,saboda muhimmancinsa nema wasu ke ganin a ilmantar da ita yafi a ilmantar da d'a namiji,hujjarsu ita ce:
"Ita mace Ita ce uwa kuma makarantar farko ga kowanne dan adam,haqqin kula da tarbiyyan yaro yafi yawa ga uwa ko kuma nace gabadaya ma ya ta'allaqa ne akan ita uwa,toh idan bata samu tayi ilmi ya za'ai taba yaronta ingantacciyar tarbiyya?" Wannan shine ra'ayin masu kafa hujjja kan cewa ilimin mace yafi na da namiji.

Annabi(s.a.w) yana cewa"Neman ilimi farilla ne(wajibi) ne akan duk wani musulmi da musulma"
Idan muka duba anan zamuga cewa Annabi bai ware maza zalla kan maganar neman ilimi ba,a'a sai yace" Musulmi da Musulma" Sannan ilimin nan ba wai ana nufin na addini bane kawai a'a harda na zaminin,mu duba hadisin nan na Harijata bn Zaid bn Thabith zamu fahimci hakan,Zaid bn Thabith ya koyi yaren Yahudawa ya kuma yi amfani dashi wajen karanta wasiqa yayinda Yahudawa suka aiko ma Manzon Allah(s.a.w) ko kuma rubuta wasiqa yayin aika musu,shin Idan har akwai wani aibu ko abin tir acikin haka Annabi ya tura shi(Zaid) musamman domin yaje ya koyo wannan ilimi a wajen wadanda suka kasance ba musulmai ne ba?

"Ina tsoron in umarci bayahude ya rubuta min wasiqa yayi qari ko ragi acikina hakanan kuma ina tsoron in wasiqa tazo daga yahudawa ace bayahude ne zai karanta sai yayi qari ko ragi" Inji Ma'aiki(s.a.w)
(Tuhufatul Ahwazee)

Duba da wannan hadisin ya kamata iyaaye su riqa barin 'ya'yansu suna shiga wannan fage na ilimin zamani ana damawa dasu domin ta haka zamu iya ciyar da addininmu gaba, idan kuwa bamu hankalta ba lallai watarana zamu wayi gari muga kafirai sun zamo jagaba akan komai na al'amuran rayuwarmu( Allah ya sawwaqa).

Ya ishi mai ilimi daraja saboda fadinsa madaukakin sarki"Allah ya shaida cewa lallai ne babu abin bautawa da gaskiya face Shi,kuma mala'iku da ma'abota ILIMI sun shiada"
Kuma dai da ilimi ne zaki sauqe abinda ke kankk na bauta ko ibada,da shine zaki zama 'ya mai tsari kuma abar yabo,da ilimi ne zaki kubutar da kanki daga rayuwa ta kaskanci izuwa ga rayuwa mai enci.

Ma'abota Hikima na cewa "Shi ilimi haske ne,shi yake maida bawa d'a sannan ya maida d'an da bashi dashi bawa" Sannan wasu ma'abota hikiman suka kara da cewa"Ilimi yafi dukiya,domin kuwa shi ilimi shi yake tsaron mai shi kuma duk inda yaje tare yake tafiya da abinsa acikin kansa,acikin qwaqwalwarsa yayinda dukiya kuma mai ita ne ke bata tsaro,idan yayi tafiya ba tare da ita ba toh fa bashi da bambanci da wanda bashi da ita"

Sannan idan mukai nazari da kyau zamu ga babu wani mai ilimi daya tab'a mutuwa da aka rabawa magada iliminsa amma mai dukiya kuwa munji mun kuma gani sau ba adadi,Don haka yan'uwa mu tashi mu nemi ilimin addini dana zamani(boko) don gujewa kunci da kuma dana sanin da kan riski marasa su"


Jikin iyaye da dama yayi sanyi,Hajja kuwa tuni taji tana burin karfaffawa Beenah guiwa wajan yin karatu.Baana babu abinda yake sai murmushi tare da yabawa kwazanta gwamnan Maiduguri yai mata kyautar kudi naira dubu dari biyu tasha kyaututtuka sossai da haka taro ya watse.

A gajiye suka koma gida, Hajja sai data kwakkwame Beenah take saboda tsantsar farinciki ji take inama mai gidanta nada yai yau da yayi alfahsri da ahlinsa.
..
*36*
Bayan komawarsu gida mahaifanta sukaita yabawa kokarinta,Baana banda murmushi babu abida yake yi zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.Marwa da Yakura kuwa bakin ciki babu magana musamman da Marwa ta zo da creadit uku pass shida hakan ya konawa Bakura rai.Beenah ce ta silalle zuwa sashin Baana dai dai lokacin ta sameshi yana waya, dam gabanta ya fadi musamman data fahimci da mace yake waya idonsa a kanta harya sauke wayar yana karantar yanayinta.

Yana dire wayar yace "Beenah yadai?" Firgigit! Ta juyo tana murmushin yake"Yaya waya gayama taron yau? " "Hmm! Beenah my unique abinda ya shafeki ai ya shafi Yayanki Abbune ya fad'amun" kai kawai ta girgiza "ok" ta furta tai masa sallama ta wuce.Ya rakata da idanu, haka kawai ta tsinci kanta wani abu na mintsinar mata zuciya game dashi das! Gabanta ya fadi saboda tunawa da kalaman Marwa yau ta sawa ranta sai taiwa Hajjansu tambayar dake adabarta.Dan haka tun yamma ta tsiri kwana gidan Hajjan.

Ta gama aikinta tayi komai,shiru Baana bai shigo ba har suka kwanta jin bacci na shirin kawomata farmaki yasa ta mitsuke ta dubi Hajja."Hajja dama mutum na auran awaanansa? dam! Gaban Hajja ya fadi"ina kika tabajin wannan kwabar Beenah? Ko bokonku da kuke tunkaho da ita basu da wannan tsarin ina kika jiyo kuma?". Ajiyar zuciya ta saki ta kwashe yadda sukai da Marwa ta gaya mata dif! Tai shiru tana jinjina lamarin a hankali ta warwarewa Beenah alakar Baana da Marwa ta kuma ja kunanta kada tagayawa kowa ta san batun.Jinkinta ya yi sanyi sossai ta dade tana jinjina lamarin a haka bacci barawo ya saceta.

Washegari haka ta yini zungur bataga Baana ba, haka kawai abin ya dunga cimata rai ko wajan aiki bata da wani sukuni.Sai magarba tana shirin tashi daga shago ta sunkuya hada wasu zarurruwa taga inuwar mutum sannu a hankali kamshin turaransa ya gauraye wajan ta dago suka kali juna wani abu ya tsinka zuciyarta mai nauyin gaske.Idanunsa masu zaiba-zaiba suka kafeta.

Cikin zuciyarta ta dinga wassafa tsarinsa, dogone mai faffadan kirji yana da tsayin fuska mai cikar kasumba baka sidik kwantaciya luf-luf hakama gashin kansa hancinsa ziyat dogo yana da manyan idanu da yalwar gashin gira miskiline da wuya kaga dariyarsa yafi yawaita murmushi...... tai saraf ta kauda tunanin daya ziyarci zuciyarta tana murnushin yake"broth have a sit" ba musu ya zauna yana karewa shagon kallo nan da nan ta sallami dalibanta ta dawo gurinsa.


Cikin murmushin k'asaita ya zubawa hannunta ido wanda yasha kan lalle, karaf suka hada ido ta sunne kai kasa tana wasa da yatsun.

"Beenah nazo ne kan maganar karatunki, tunda naga Hajja ta sassauto kan ra'ayinta zan karbi takardun yanzu in tafi dasu.Zan nema miki gurbin karatu a Maiduguri sai ki koma gidan Kaka(kanin mahaifin su Dr) domin su Abbu sun aminta da karatunki banda zaman hostel.Hajja ce taso bamu matsala itama ta sauko, tunda tace dama tunaninta aure kuma baki da mashinshini bale a kai ga batun aure". Ya karasa furucin yana murmushi, batun ya taba zuciyarta ta kanne tana murmushin tura haushi"share Kakus waya ce mata banda samari?Ina dasu kawai ina son fara karatune sai mu dora daga inda muka tsaya..".Kallon da ya jefa mata ya sanya maganar makalewa a fatar bakinta.

"Wato kina da samari? Ya fad'a da kaushin murya,kai ta gyada masa ya sha mur kome ya tuna ya saki murmushi yace " ok Allah ya taimaka" "amin ta fada da dakakkiyar murya ya wuce be tanka ba.Jiki a sanyaye ta rufe shagon ta wuce gidan Hajja, yinin ranar babu wata maganar kirki data had'asu nan da nan ta hada yanata-yanata ta koma gidansu. Da magarba aka aikata kai masa abinci, lokacin da tai sallama dakinsa ya jima bai amsaba ganin babu alamun amsawar Mansur abokinsa ya amsa mata cike da nutsuwa tai salama bai amsaba bai kalleta ba sai lumshe ido da yayi ya fada bandaki.

Mansur da Muzabil ta gaisar, ta wuce jiki a sanyaye kwata-kwata ya sauya mata.Tana fita ya fito ya sauke ajiyar zuciya, Mansur ya kwashe da dariya"zaka kashe kanka dalilin b'oyayyan so" "hmmm! K'yaleni Mansur Beenah (is my life) rayuwata ce karaf! A kunnuwan Marwa da tazo giftawa,ranta ya dugunzuma da gudunta ta bar wajan ta nufi gida tana hawaye.

Hankalin Yakura yai matukar tashi ta dinga tambayarta abinda ya faru, sai da ta gama kukanta samnan ta bata lamari ta jinjina kai tare da lallashinta.

Washegari da sassafe cikin shirinsa na kananun kaya,shigar tai masa kyau yai karo da Beenah gab da shiga gida kowa ya daukewa kowa kai.A ranta tana mitar ya dauki al'adar saka kaya kanana,kai tsaye ya shiga yiwa Yakura sallama.Fuskarta babu yabo babu fallasa har ya mike zai bar d'akin ta kada baki ta kira sunansa.

"Muhammad". Kafaffunsa ne sukai sanyi matuk'a bai ta6a jin ta kira sunansa kai tsaye ba.

"Dawo ka zauna zamui magana".

Ba musu ya nemi waje ya zauna ta kalleshi.
"Inaso mui magana da kai umarni nake baka ba shawaraba,ka auri Marwah".

Kansa ya yi nauyi, jim ya d'ago idanunsa jajjur ya sunkuyar da kai "Hajja.." kafin ya dire ta tare"bana buk'atar komai tashi ka tafi Allah ya kiyaye".

Bashi da zabi face bin umarninta, jiki a mace ya fito karaf yai kici6us da Marwa alamun labe tai musu wata muguwar harara ya jefa mata sum-sum ta wuce tana murmushin mugunta.Mak'alk'k'ale Yakura ta yi tana dariyar jin dadi,ta tureta tana fadin ja'ira.

Baana zabar tashin hankali ko sallama baiwa Hajjan Beenah ba daga gidan Hajjansu kai tsaye wucewa ya yi.Hakan yasa basui sallama da Beenah ba Marwa na lekensa ta soro dadi taji sossai ta koma gida.

Bangaran Beenah tunda taga babu shigowar Baana jikinta ya soma sanyi,bayan fitar Faanah shago ta zari mendil d'inta tai gidan Hajjansu cike da murmushi ta shiga gidan.Turus ta tsaya ganin babu Baana ta d'aure ta shiga tana tsokanar Hajjansu.
"Ja'ira burinki dai ya cika dazu Yayanki ya shigo yi mun sallama yake gayamun ya tafi da takardunki ashe gidan Kakanki zaki zauna?". Tuni guiwoyinta sukai sanyi zarginta ya tabbata Baana ya yi fushi ya tafi. Tun tana fuskantar batun Hajjansu, harta gaji tai mata sallama ta koma gida.Yini tayi tana tunani.

A rikice Baana ya nufi gidansu Mansur, yanayin daya ganshi ya bashi mamaki.Baana nnutsatsan mutum ne ba komai yake daga masa hankaliba.Bai b'oyewa Mansur komai ba yai jim yana tunani ya numfasa.

"Baana ka fawalawa ubangiji komai, domin baza kaja da umarinin mahaifiyarka ba uwa uwa ce tafi karfin komai kabita sannu".

"Hmm! Na gode Mansur, amma kasan inason Beenah nasota tun bata isa abar sha'awa ba yanzu baka ganin auran Marwa zai min shamaki da Beenah"?.

"Tabbas shamakine domin ba kowa keda fahimta ba, amma auran Marwa ko a addinni bazai haramtama auran Beenah ba".

"Na yadda da batunka, amma zan cigaba da boye son Beenah domin bayyana shi fitinane ga ahalina.Inason Beenah fiye da kaina, bazanso shigarta matsala ba zan cigaba da yi mata b'oyyayan so".

"B'oyyayen so?".
"Tabbas Mansur".
"To! Nikam ina ganin da kamar wuya, domin so duk inda yake baya b'uya".
"Ka zuba ido zakai mamaki".
A ranar suka bar garin Biu, kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji.Baana har yai sati biyu da tafiya zuwa lokacin Beenah ta kai makura wajan dane abinda take ji a ranta har ya soma sata rama.





Tunda aka soma batun zuwan Beenah karatu Dr ya nemi shawarar Bakura kan gyara ainihin gidansu na Maiduguri.Hajja kad'ai suka sanarwa,sossai tayi farin ciki da hakan koba komai zumunci zai k'ara k'arfi.Kudi ya tanada sossai aka bige gidan kanin mahaifinsu da nasu ya dawo garin Biu kafin a gama aikin a d'akin Baana akai masa masauki.

Dake filayene d'iban da sai aka samu wadatar guri sossai, fanni hudu aka fitar kowane d'auke da falo da bedroom biyu a ciki tare da wadatar tsakar gida da band'aki.Duk da hakan akwai ragowar guri wanda zai kai ayi part biyu a ciki kawai sai Bakura ya bada shawarar ayi k'aramin lambu a tsakiya ayi shuke-shuke saboda Faanah.
Hakan kuwa ba k'aramin k'awata gidan ya yi ba.Cikin wata d'aya aka gama ginin gidajan.Aka rufe ana jiran lokacin tarewa,ko Baana bai san da batun ba.

Kwanci tashi aka shiga gudanar da shirin saukar su Beenah, an yi shagali sossai hankalin Beenah yai matuk'ar tashi ganin har aka gama bai hallata ba.Kuma taji lokacin da Abbunta ya sanar dashi a waya, haka tai taron sukuku da ita.Falmata ta kula da sauyawarta, tun tana yi mata kawaici harta kai ga tambayarta a hanyarta ta yi mata rakiya bayan gama taron.


Beenah ta kanne kawai tace"babu komai Falmat (just pray for me) ki dai tayani addu'a tunanin rabuwa da gida ne kawai.
"Hmm! Beenah unique kenan".
"Au! Kema?".
Dariya sukai daga nan sukai sallama.Cikin ikon Allah aka soma shirye-shiryen graduate din Baana, Dr ya dage kan kowa sai ya je saboda akwai abokinsa dake Kano a gidansa zasu sauka.

Beenah taso togewa taga babu dama saboda babu wanda zai zauna.Tun saura kwana hudu tafiya Marwa ke gid'imi itace gyaran jiki kunshi gyaran gashi saboda zasu ganin Baana.
Yakura kuwa sossai take tsumata da tsubace-tsubace turare kwalli da sauransu,tun Beenah na maida hankali wajan sha'anin harta watsar saboda ta lura babu nutsuwa a batun.
Ranar Littinin taro ya kama su kuma tun Asabar sukaiwa garin Kano tsinke, a unguwar Nassarawa G.R.A gidan aminin Dr wato Barrister Mustapha Muhammad Kurfi.

Mutum mai karamci da kyautattawa, yana da mace biyu da yara takwas.Kawunan matansa a hade yake sossai, babu bambanci tsakanin wance da wance ko 'ya'yan wance.Babban d'ansa na zaune a Abuja da iyakinsa mai suna justice Aliyu.Sai mai bimasa sojane yana Fatakol da iyalansa shi ne Genaral Faisal.Sai Barrister Husnah tana aure a Minna sune yaran uwargida Hajiya Hauwa.Sai Aunty Amarya itace Zainab nada yara biyar Dr Shukura ce babba na aure a Kano sai Juwaira acconter ce tana Dubai da mijinta sai Ammar shi ne yayi aure sai matasan samarin da suka rage wato Samar da Samir duk sun kammala karatunsu.

Samar Bussiness ya karanta hakan yasa shi yake juya ragamar dukiyar mahaifinsu.
Samir kuwa ma'aikacin jarida ne.Akwai yarinyar Justice babbar dake karatu a nan Kano mai suna Asalamiyya matan nada fahimtar juna da kyautattawa tsakanin su.Sun had'u da Dr ne a sanadin karatu tare sukai jami'ar Maiduguri.

Tunda suka sauka ake haba-haba dasu,an musu saukar karamci sossai.Beenah dai bata walwala sosssi,tun zuwansu Aslamiyya take nan nan da Beenah hakan yasa ta saki jiki suketa wasa da dariya juna.
Marwah kuwa sai shisshigewa,Samar take dan ta lura Samir miskiline.Hajiya Hauwa sossai nutsuwar Beenah ta burgeta hartana d'arsa wani abu a ranta.Dadare suka hallara wajan cin abinci,kowa naci banda Beenah datake shan ruwan lipton da meatpie.

Hajiya Hauwa ta kalleta tana murmushi"Benazirahtu kin huta wato bakyacin girkin tsofaffi ko?" ta fad'a da salon tsokana.
Murmushi tayi tana wasa da yatsunta Yakura tai karaf tace"wannan uwar kinibibin na gado".Kowa ya yi sak alamun bai ji dad'in kalamanta ba, maigadi yai salama yana sanarwa akwai bak'o a waje babu tantama Dr yasan Baana ne dan haka yasa Samar ya shigo da shi.

Tunda Beenah taji ance Baana ne,gabanta ya dinga fad'uwa zuciyarta ta shiga rud'u sossai.Sautin muryarsa ya katsemata tunani gaba daya kamshinsa ya cika wajan,ta dago sukai kalon-kalo ya lumshe ido tare tsare gida.Asalamiyya na kula da yanayinsu sai suka burgeta, saurin dauke idonta ta yi ya rissina yana gaishe da mahaifansu cike da ladabi. Bayan an gaggaisa iyayyan suka basu waje sui hirar zumunci, Mazan sukai bangaran maigidan hakama matan.

A hankali Baana yake hira da samarin suna kara fahimtar juna yana sako Asalamiyya itama dake akwai nutsuwa bata cika magana ba Marwa ce dai keta azarb'ab'i Beenah kuwa ko kanzil tanata wasa da wayar Asalamiyya.Lokaci zuwa lokaci suna satar kallon juna, abun yaso bawa Aslam dariya ta kanne.Can Baana ya numfasa yace.

"Beeeeeeenah!".

Cikin nutsuwa ta dago sukaiwa juna wani irin kalo, ta dauke kai tana dubansa.

"Beenah babu magana ko?".

Murmushi tayi amma data tuno abinda ya yi mata, sai ta turo baki ta shagwab'e fuska.

"Bayan ma ka manta dani,kai tahowarka ko sallama".

Salonta ya bireshi sossai tare da haifar masa nishad'i, ya langab'ar da kai yana kwaikkwayonta.

"Bakece kikai mun laifi ba".

Aikuwa gaba d'aya wajan suka kwashe da dariya, yaiwa fuskarta tsuru yana kallon jerrarun fararan hak'oranta da suketa haske.Fuuu!Marwa ta bar wajan, ya tabe baki ko minti biyar batai ba saiga fitowar Yakura fuska a gimtse ta dubeshi.
"Baana ka wuce gida sai zuwa gobe".

Jiki a sanyaye ya amsa, bata tankaba ta banko k'ofar ya mike yai musu sallama harya kai bakin k'ofa ya juyo yaiwa Beenah murmushi.Yana fita Marwa tazo ta wuce tabi bayansa, a tsaye ta sameshi sunkai mintuna shida babu wanda ya tanka ya shiga motarsa ya wuce a zafaffe.Cike da sanyin jiki ta dawo babu kowa a falon sai Aslam nan ta zauna suna hira, jefi-jefi anan take bawa Aslam labarin Baana zata aura.Mamaki ya kasheta, ita dai bataga alamun so a tare dashi ba amma fahimtar da taiwa lamarin yasata gum.Tafi-tafi har dangantarku da Beenah da Baana sai da ta warwarewa Aslam tai jim tace.

"Sis (i'am sorry to say) anya Yayanki ba Beenah yake so ba?". Marwah tai murmushi tace"(iknow) nasani (but) amma walahi mudin ina numfashi saina wargaza tafiyar Baana nawa ne nikad'ai kisa a ranki".

"Amma Marwah hakan da zaki akwai cutarwa.... ".

"Ke! Dillacan dakatamun, nafa fahimci tun zuwanmu bakya haba-haba dani tamkar Beenah walahi zan nuna miki kalata ta zahiri".

"Hmm! Marwah kenan".
Mikewa tai ta barmata wajan ta koma wajan, Hajjansu da Beenah suna hira duniya yaran Kanuri suna birge Aslam sossai.

Sai dare sukai mata salama suka nufi makwncinsu, har shadaya Marwah bata dawoba tana sashin su Samar lamarin daya daurewa Aslam kai sossai ta bude bbaki zatai korafi aka turo kofa........

Gaba daya suka maida hankali kan k'ofar, zatonsu Marwah ce sai suka ga akasin hakan.Copy din Aslam ne Hauwa mai aiki ta kawomata ta karba tai mata godiya ta wuce.

Aslam ta dubi Beenah tana murmushi"ashe Marwa matar yayanki ce?" Murmushi kawai tayi ta amsa da "hakane".Marwah ta shigo tana fizge-fizge babu wanda ya damu da shirginta.
Washegari da wuri suka tashi, ta taya Aslam shiga kichen ta dinga mamaki yadda bata da girman kai irin na wayayyun matan da suka d'auki shiga kitchen gidadanci.A hankali ta dinga kalon yadda take komai,girki kala hudu ta shirya.
Kunun gyada ta shirya da k'osan nama wanda yasha had'i da _peak milk_sai funkaso da miyar agushi sai suka soya plantain da dankali.Beenah tace"badan ba zamu dadeba da nayi koyi na girki""kibari zan baki books in dai kinbisu a hankali zaki fahimta nima zaki rubutamun girkin Kanuri kafin ku tafi ki koyamun turarruka". Dariya sukai a tare, kafin takwas da rabi sun shirya wajan cin abincin yadda ya kamata.Kowa ya hallara suka ci abinci da yamma Samar ya zaga dasu shoprite jufatu sahad sune har hills and villy sun zaga gari sossai.A gajiye suka dawo suna parking dai-dai lokacin Baana da Mansur suka shigo gidan.Idonsa a kanta ya tsare gida, cike da nutsuwa suka gaishesu idon Mansur akan Aslam yanayinta ya burgeshi sossai.
Wucewa sukai suka barsu da samarin gidan.

Suna shiga Aslam ta wuce bandaki, Beenah ta kwanta tare da lumshe ido zuciyarta na zafi.Tunnanin Baana nasan nakasa mata zuciya, kanta ya sara ta dafe idonta yai jajjur.
"Baana ina sonka".
Ta furta hakan, wand labbanta ne kawai suka motsa,tai juyi ta mike Aslam na fitowa ta fada bandaki ta dauro alwala. Ta jima tana addu'a kan darduma daga nan ta dora da sallahr isha'i ta wuce wajan Hajjansu tana zolayarta.

Beenah doguwa ce wankan tarwad'a,mai gashi bak'i sid'ik da shek'i wanda har ya kwanta a kan kafad'unta.Sanye take da lifayar data dace da tsarin fatarta, kalar _pink colour_ ta nade jikinta tas. Fuskarta doguwa mai kyan tsari mai dauke da, idanu dara-dara hancinan siyat da bakinta madaidaici mai dauke da jerrarun hakora fararre tas da hushiryarta tsayayyayiya a tsakiya cas.

Beenah tana da wani irin kyau mai cike da kwarjini, kalo daya in kai mata baka gane hakan sai ka jima.Tana da cikakkiyar hallita kasanta a cike yake dam! Hakama daga sama cikinta ne kawai a shafe tamkar zata karye.Tunda ta fito kamshi yaiwa falon salama Samar kasa dauke idonsa yai a kanta.Aslam kuwa tafi ta shiga yi "yayi Kanurian wannan kamshi haka?" Dariya tayi tana murda yatsu alamun jan kunne.

"Karki fasamun kai fa?".
"Ba wani fasa kai Beenah kin had'u sunan ya dace dake, ga mutumin naki kin watso shi".

"Wafa?".
"K'amshi mana walahi shiyasa jinsin Kanuri kuke burgeni.Inason al'adunku".

"Karki damu insha Allah can zaki aure".

Marwah dan takaici kasa zaman falon tayi.
Gaba d'aya suka dunguma zuwa waje, motocine a zube yan ubansu Alhaji Mustapha da Bakura da Dr a mota d'aya.Hajjansu Hajja Faanah da Yakura da Hajiya Hauwa da Aunty Zainab a mota daya wadda Samir keja.Beenah da Aslam da Marwah a mota daya Samar ne ke jansu suka dauki hanyi reras.
Harabar taron ta cika makil, kowa sai murna yake a haka sukaiwa wajan tsinke.Tunda suka shigo idon Baana na kanta hakan ya sakwarkkwatar da nutsuwata.

Tasowa ya yi ya taresu suka gaisa, a haka aka soma gudanar da taron.Masha Allahu taron ya kayatar sossai kafin biyu aka tashi Baana yasamu point fiye da kowane dalibi hakan yasa akaita daukarsa hotuna.

Dakyar ya faki idon mamansa akai masa hoto daya shida Beenah inda ta dan dora kanta a kafadarsa tai murmushi dimful mata ya lotsa(beauty point) sai hotan yai tsari kasancewar yafita tsayi ya dan rankwafa kansa a saman fuskarta tamkar yana mata rada.A haka taro ya watse suka jiyo zuwa gida, Aslam da Mansur dai bisa alamu sun yi na'am da juna.

Ranar Laraba sukai shirin komawa gida har Baana, ansha kewar juna Alhaji Mustapha yaiwa Baana kyautar mota sabuwa dal.Su Beena kuma sarkokin gwal suda iyayansu mata Samar ne ya siya musu wayoyi su duka ukun ita da Marwa da Aslam kirar iphone mai matsakaicin kud'i. Sossai Dr ya dinga yi masa godiya suka rakasu tasha motarsa ta daga zuwa Maiduguri.
Motar Baana ta rigasu zuwa gida, a Maiduguri suka sauka kowa mamaki yake yadda aka gyara gidan tsarin ya birgesu sai lokacin Dr yai musu bayanin dalilinsa nayin haka.Nan fa Yakura ta dinga bala'i shin Beenah yar gwal ce a saboda ita za'a rabosu da garin Biu.Babu wanda ya tanka mata kwanan su biyu suka wuce Biu cike da walwala.

Tunda suka dawo babu jituwa tsakanin Yakura dasu Beenah musamman yanzu da Baana bashi da wajan zuwa fiye da gidan Faanah.Karfi da yaji sotake ta rabasu lamarin daya fusta Hamza tun yana kawaici harya fito yaiwa Yakura tas.Maimakon a samu sauki sai lamarin ya ta'azara sossai wanda ya haifar da tsana mai tsanani tsakakaninsu.Shi Hamza yana gani bata isaba ita kuma tanai masa kallon a tafin hannuna kake.Beenah an yi registration an gama komai tuni ta tattara kayanta ta koma Maiduguri ita da Hajja,a sashin Hajjan suke ita da Baba Isah sossai tana jin dadin zamanta.Duk weak end Baana na kawomata ziyara tare da siyayya kala-kala lamarin da ya haifar da karin tsananin shakuwa tsakaninsu.

Zumunci tsakanin Beenah da Aslam sai abinda yai gaba, bale yanzu da Mansur ke son d'auko Aslam a matsayin mata lamarin da kowa yaji dadinsa.
Kwatsam Alhaji Mustapha ya nemi shawarar Dr suka soma

Please Login or Register in order to submit comment