Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta daure ta shirya cikin lafayya green colour babu laifi tayi kyau tare da Yakura suka shirya abincin gidan sai kamshi yake.Shiru babu su babu dalilin su.
Lamarin daya fusata su sossai,ana haka sukai baki dangin Babansu.Sun tare su babu yabo ba fallasa, nan Anwar abokin wasan su ne yai zumbur ya dauko jug na lemo ya kwankwad'a Yakura tana kai! Kai!! Kai!!! Amma ina saida ya shanye tas yana leme baki dai-dai lokacin Yalfata ta fito ganin abinda ya auku yasata sakin giggitaciyar kara ta zube sumammiya.

Ruwan da Yakura ta watsa mata shi ya farfado da ita, kuka take tamkar ranta zai fita tana danasanin biyewa son zuciya yau gashi tayi asarar kud'inta wakan siyo soyyayar Hamza ta bige ga Ammar. Ammar dan kanwar mahaifinsu Yakura ne, suna zaune a can Askira inda danginsu suke matansa uku kuma kowace da yaranta bashi da kirki tsayayyan namijine a gidansa mace bata kawo masa wargi. Hata Yagana shakarsa take sossai, Yalfata ta saki ajiyar ajiyar zuciya bayan gama tuna waye Ammar a gareta, fuuuu ta bar dakin sun jima suna hira da Yakura duk da rabin hirar umm da eh ne anan Ammar yake tambayarta dalilin suman Yalfata.Ta rasa karyar da zatai masa, can dabara ta fado mata tace masa haka take lokaci zuwa lokaci. Asiri gaskiyar me shi kafin su bar gidan Ammar ya soma nan da nan da Yalfata, Yakura ta tsorata matuka saboda ita ta amso maganin kuma bokan yai mata gargadi kan kaucewa aikata sharudansa dole wanda yaci maganin shi Yalfata zata aura.Tunda Yalfata ta shige daki take gursheken kukan nadama, a haka Yakura ta sameta tana hada kayanta riketa tayi cike da mamaki take dubanta.
Ku biyo ni..
[8/8, 9:59 PM] Sanah S Isma'il Matazu: *YAR KURMA*
*SANAH S MATAZU*
*20*
My editer
Chuchungaye
Dedicate.
Ummu Samhat
Auntyn Kt.

"Lafiyarki ke kuwa? ".
Cikin kunar rai ta dago kai tana hawaye"gidanmu zani kinsan aikin bokanki ci yake kamar yankan wuka, kin riga kin cutar dani da zuciyata dole in yi nisa dake"wani giggitacan mari ta wanka mata.
"Ni zakiyi wa iskanci Yalfata daga taimako? Kinsan yadda nake ji a raina game da wannan al'amarin na fiki son ki auri Hamza saboda burina nasan kassara Fannah. Dalilin Fannah nazamo kaskantaciya a idon Hamza harya kai ga marina. Kinsani sarai hana yafiya auranki ba komai bane face fansa ga muradin raina. Kije gida zan san matakin d'auka dole in kauda Ammar a doron kasa mudin zai bani matsala".
"Kisa!?".
Ta furta a tsorace, "tabbas kuwa"cewar Yakura. "Babu ruwana Yakura walahi babu ruwana,son zuciyarki ya yi yawa ina nadamar biyemiki zanje in auri Ammar domin shi ne kaddarata. "Hmmm! Kije zaki dawomun da kafaffunki".
Bata tanka ba ta hada kayanta ta nufi gida, a kofar gidan su tai kicibus da Ammar da hanzari ya amshi kayanta jikinta yai sanyi tabbatar aikin Yakura saboda kwata-kwata Ammar bame sakin fuska bane.
Har ciki ya kaimata kayan, bambarakwai take duban lamarin namiji da suna Hajara. Mahaifiyarta tana tsaka da aiki taga shigowarta tare da Ammar ta dinga dubanta da kallon tuhuma sai dai babu wata k'ofa data bayar dan hango matsalarta kai tsaye sashinsu ta nufa ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa taji sa'ida. Koda Yagana ta shigo, tsareta tayi da tambayar dalilin dawowarta amsar dayace babu komai. Kada kai tayi ta fice,tun daga lokacin ta koyi zaman dakai babu ruwanta da kowa. Cikin kwana uku maganin Yakura ya gama yiwa Ammar wani irin kamu, kai tsaye mahaifin Yalfata ya sanarwa kudirinsa sossai yaji dadin batun kasancewar kaf sa'aninta sunyi aure Yalta hada haihuwa ita kuma shiru.Ba jinkirtawa ya bashi auranta, lokacin da yajewa Yagana da batun tsalle tayi ta dire atabau bata aminceba, shi kuma yace yaga me musu da umarninsa saidai ta zaba auranta kona diyarta. Hankalinta ya tashi sossai, Yalfata kuwa ko musu batai ba,saboda tasan shukarsu suke girbewa nadamace cike da zuciyarta suna ji suna gani aka soma shirye shiryan biki watanni biyu masu suwa wanda yai dai-dai dana Faanah.

Kwanci tashi Yakura ta haihu lafiya, ta sami d'anta namiji kyakkyawa dashi ranar suna yaci sunan Muhammad.Hamza yafi kowa murna da wannan suna shi da Faanah saboda sunan mahaifinta ne hakan yasa suke kiransa Baana. Shi kenan sunan ya bishi,yaron ya taso da farin jinin jama'a Faanah duk irin hancin da Yakura take mata kan d'aukarsa bata gajiya Hajja taita yi mata fad'a.Faanah itace wankansa, kashinsa fitsarinsa nan da nan sukai sabo dashi ko'ina ya ganta ya wangale baki gashi da fara'a watansa shida aka tayar da maganar auran Faanah da Hamza haka Yalfata da Ammar gadan-gadan.

Sossai Hamza ya gyara gidan Hajja, babban falo da wajan girki da dakin bacci aka fitar sai bandaki da store sai wajan cin abinci Hamza ya k'awata gidan sossai da shukoki Faanah taji dadi sossai, ya zuba mata kayan d'aki masu kyau da matsakaicin kud'i ga labulaye da carfet masu kyau. Hajja tai hidimar turare sossai Bakurama ya yi rawar gani shiya biya sadaki da sissin gwal.Yalfata ma an yi hidima babu laifi duk da babu walwala tare da'ita aka gama biki aka d'auketa zuwa garin Askira zama cikin kishiyoyi.
FATAN ALKHAIRI YALAMMAR.................

Faanah an sadata da gidan masoyinta, masha Allah zamansu gwanin ban sha'awa satin Hamza biyu Alngoburo ya yo masa waya yana yi masa tsiya tilas ya hada kayansa ya koma Maiduguri. Da kuka suka rabu da Faanah, Hajja tai ta lallashi.Kafin tafiyarsa ya gyara mata wajan sakarta ta koma aiki sossai, yanzu har Maiduguri ake kai mata. Kullum Faanah tana aikawa daukar Baana Yakura na hanawa, in taci arziki ne Hajja na kusa take yakana ta bata shi gorin haihuwa kuwa iri-iri kota kanta bata bi.


Bari mu waiwayi amarya Yalfata, zamanta babu laifi akwai kulawa saidai matsin kishiyoyi kishi suke na tashin hankali babu wadda ke ragawa wata.Ringid'i-ringid'i suna zaman dadi rana daya Ammar ya sauya mata lamarin da ya jawo kwantsamewarta duk ta yankwane ta fita hayyacinta. Abin babu kyan gani a haka Yakura ta kawo mata ziyara ta dinga masifa kan ta zauna ta koma borar gida........

BAYAN SHEKARA BIYAR.......
Abubuwa da dama sun faru, garin Biu sun samu cigaba an gina musu babban asibiti Hamza yana cikin wanda aka kawo garin. Yaji dadin hakan sossai koba komai ya samu kusanci da danginsa, hidima yake dasu sossai babu k'yashi abun hannunsa bai rufe masa ido ba ga sadaka da tausayin almajirai, duk ranar lahdi ya kan ware lokaci a gida yana duba masu matsalar kunne da basu shawarwari. Hakan yasa mutanan garin ke alfahari dashi suna kyautatta masa.Hakan na ciwa Yakura tuwo a kwarya,Baana ya girma sossai har an sashi makarantar boko da islamiyya yana primary three(aji uku)kullum yana tare da Faanah Abbagana yana yi masa lesson. Tunda ya girma yai wayau Abbagana yake kiran Hamza wato Abbagana na nufin Uncle.Hamza shi yake d'aukar nauyin komai nasa kama daga sutura makaranta da komai.Batun noman Hamza arziki ya habbaka ya bud'e wajan kiwon kifi ya dankawa Bakura.Hajja najin dadin yadda suka had'a kansu sossai yanzu bata da wata matsala.Kwatsam Allah ya bawa Faanah juna biyu, cikin nata ciki ne mai matukar sa laulayi sossai. Komai taci sai ta amayar dashi hakan ya tayar da hankalin Hamza da Hajja,Yakura kuwa ina wuta ta sasu mita take kullum sai kace kanta aka fara laulayi.Tun Bakura na yi mata shiru har ya kai ga tankawa ya yi mata tas daga nan suka sami sa'ida.
Cikin Faanah nada wata hud'u cif Yalfata tazo gida da ciki wata bakwai.Babu laifi ta dan ciko, zuwanta Yagana ta riketa tace bazata koma ba saita haihu an sha fama amma kiri kiri ta hanata komawa lamarin daya fusata Ammar ya saketa saki biyu.

Sakin ya girgizata amma lokacin da Yakura ta samu labari,wani dadine ya ziyarceta ko babu komai ta samu hanyar kuntatawa Faanah.

Tsaunuka ne masu tsananin santsi da hadari, ga kayoyi a haka take haurasu duk ta hada gumi. Kashirban hakan bai dameta ba burinta ta isa saman tsaunin,da kyar takai tana hucci tana komai kwatsam sai gata gaban wata karamar buka,zubinta kansa abun tsone zagaye take da kawunan kwarangwal na mutum.Ni kaina sai da suka tsoratani, wata giggitaciyar kara aka saki daga cikin bukar take ta tsorata tai taga-taga k'afarta ta hagu ta gice luuuuuuuu ta tafi k'asan tsaunin................
Caraf aka cafketa,tare da ajiyeta a kan tsaunin Yakura ta saki ajiyar zuciya, jikinta duk ya mutu zubewa tayi tana yi masa kirarin nasa na k'a'ida ta bud'e baki zatai magana ya katseta."Nasan abinda ke tafe dake, burinki kawar da facalarki".Kai kawai ta d'aga masa ya yi wata mahaukaciyar dariya"an gama mudin zaki bi sharad'aina mudin kikai kuskure kamar na farko kar ki tunkari inda nake"."Na amince Bokan Bokaye"ta furta da muryar tsoro, rufe idanunsa ya yi ya soma karanta wasu batuttuwa take wajan ya tirnik'e da wani kakkauran hayak'i Yakura ta soma tarin wahala. Wata gugguwa ta sake had'owa ta murtuke bukkar can hayakin ya soma hucewa haske ya bayyana,idanunta sunyi jajjur sai hawaye take. Wata kwatanniyace ta bayyana a gabansa cike da wani koran ruwa mai tsananin yauk'i da hammami a samanta wata cukuikkuyayyiyar leda ce yasa hannu ya d'aukota aikin sihiri ko danshin ruwan babu ajiki bale yauk'in.

Mik'a mata ya yi cikin sauri tasa hannu ta karb'a, jikinta sai rawa yake ta ciro kud'i kimanin dubu goma ta zube masa."Kije ki zuba mata ta sha ko ta ci, zata mutu babu mai gane abinda kika zuba ciki komai k'wak'war mutum".Cikin murna tace "na gode uban Bokaye","ku sauka da ita" aka fad'a da tsawa luuuu! taji an sauketa k'asan tsaunin da sauri ta zari takalminta ta d'auki hanya.

Kwanci tashi cikin Faanah ya shiga wata shida,a lokacin Hamza ya siyi mota suka kuma hada kudi suka kai Hajja saudiyya.Sai dai kwata-kwata hankalin Hamza da Hajja ya tashi ssboda kunburin da kafafunta suka yi. Kullum suna hanyar asbiti tare da bin shawarwarin likita kan bayanan da yai musu.Wasu lokutan Alangoburo ke zuwa hargida ya dubata a wasu shawarwari da ya basu kan cewar:

_"Ana so mai juna biyu ta guji aikata ayyukan da suke bukatar karfi maiyawa.Idan so samu ne mai juna biyu ta samu wanda zai rika taya ta aiki.Ana so mai juna biyu ta rika motsa jiki, hakan zai kara mata lafiya da kuma kuzari.Ya kamata mai juna biyu ta rika kwanciya da wuri, kuma an fi so ta kwanta a rigingine, yin hakan zai sanya jini ya rika zaga jikin jaririn da mai juna biyu take dauke da shi.Idan mai juna biyu tana son samun natsuwa da jin dadi a lokacin da take kwance,to ta sanya karamin matashi a tsakanin k'afafunta da kuma k'ark'ashin cikinta."_

Cikin ikon Allah kumburin ya yi sauk'i.Baana har kuka yake in yaga yadda take shan wahala, duk da k'aracin shekarunsa yana da tausayi sossai shi yake zuwa ya yiwa Faanah shara duk da dukan da yake sha wajan Yakura sai ya koma.Haka k'ananun ayyuka in yaga Hajja na yi shi yake k'ok'arin karb'a yayi Yakura takaicin duniya ya isheta ita dai a rayuwarta tana adawa da cigaban Faanah.Kwata-kwata yanzu tunaninta ya tafi kan yadda zata zubawa Faanah maganinta.Ta rasa mafita, duk lokacin da tayi yunk'urin hakan jikinta sanyi yake saboda ba sa ga miciji bale ta yaudareta.

BABIN 'KADDARA......
Ranar wata littinin da misalin k'arfe hud'u na yamma ciwo ya turnik'e Faanah, abin tausayi gidan babu kowa sai nishi da murk'ususu take ta juya ta sake juyawa babu mataimaki sai ubangijin bayi.Zaune yake a office haka nan gabansa ya tsananta fad'uwa,cikin sanyin jiki yaiwa Alangoburo sallama ya nufo gida yaso karantar yanayinsa dake ba mutum bane me bin k'wak'wafi sai ya share. Kai tsaye makaranta ya biya ya d'auko *Baana*yana kusantar gida gabansa na tsananta bugawa tukinma neman gaggararsa yake da k'yar yakai kansa gida yana parking Baana ya fito ya nufi shiga gidan.Murmushi ya yi yace.
"Baana ba zaka je ka fara kaiwa Hajja da Mamanka ladan ba?".Turo baki ya yi yace"k'yalesu Abbagana Hajjar nan cewa take wai ni ne mijinta, ko me zanyi da tsohuwa? Abbagana ai Hajja k'arama ce zata haifamun mata ko? ".Ya fad'a yana tsareshi da ido,dariya ya yi yace"hakane Baana".Da haka suka shiga gidan, shiru babu motsinta da sauri ya nufi babban falo bata ciki kai tsaye bed room ya nufa (d'akin baccin su) da hanzari ya shiga sakammakon nishin da yake jiyowa yana shiga das! Gabansa ya fad'i......


Cikin kaduwa ya karasa, gaba daya ta hada gumi
tamkar wadda aka zubawa ruwa a jikinta.Jikinsa
ya yi mugun sanyi, ganin ko ina na jikinta rawa
yake.Hannu yasa ya d'agota ta juyo das! K'irjinsa
ya buga ganin hak'oranta na sark'ewa da sauri
ya nufi kitchen (d'akin girki) ya d'auko cibi wato
cokali ya raba hak'oranta ya saka shi tsakanin
harshanta domin bata taimakon gaggawa saboda
yaga alamun tana gab da fara jijjiga.Ya juya
zashi gidan Hajja, carraf ta rik'o hannunsa ya
kasa motsawa.Murya a raunane yace"Please
Faanah ki sake ni in kira Hajja,asibiti zamu kaiki"
sakinsa tayi tana lumshe ido a guje ya kwasa sai
gidan Hajja.
Mintuna uku suka shude sai gashi tare da Hajja,
da taimakonta suka sata a mota cikin sauri suka
nufi asibiti.Da gudu *Baana* ya nufi gida yana
kuka, yana bawa Yakura labari hankadeshi ta yi
tana fatan Allah yasa Faanah ta mutu. Bakura
daya sawo kai gidan yace"ubangiji ya shiryeki
Yakura" hannun Baana ya kama sukai
waje.Barinta sukai tana ta sakin maganganu,
Bakura ya share masa hawayan suka tari abin
hawa zuwa asibitin.Kafin suje Hamza ya yiwa
Alangubro waye, suna zuwa aka karb'esu da
hanzari aka yi emergancy room (dakin taimakon
gaggawa)da Faanah. Gaba d'aya Hamza ya fita
hayyacinsa, Hajja da Yakura ke tausarsa.Ana
haka aka shigo da Yalfata zuwa dakin haihuwa,
nan Yagana suka hadu da Hajja sai jajjantawa
juna suke.Hamza ya kasa zaune bale tsaye,
shud'ewar rabin awa aka nemi ganin Yagana.
Bakinta har kunne Yalfata ta haihu,an samu
mace nan da nan ta cika da farin ciki.
Hajja adu'a kawai take can Dr Hannafi ya fito sai
gumi yake, ya nemi ganin Dr Hamza.Cikin
damuwa ya dubeshi"Dr i'am sorry to say (kayi
hak'uri da abinda zan ce) dole a yiwa Madam
CS".Jiki a sanyayye yasa hannu, Hajja kuka n
zuci kawai take Hamza kuwa kasa jurewa ya yi
saida ya yi kuka. Alangoburo ne yaja shi office
d'insa ya bashi ruwa ya yi alwala,a hankali ya
dinga yi masa nasiha tare da nuna masa komai
nufin Allah ne. Gab da za'a yi mata aikin ubangiji
ya bata ikon haihuwa da kanta sai dai ta jigatu
matuk'a.Tilas aka nemi jini aka k'ara mata,daga
nan akai d'akin hutu da'ita yarinyar kuwa akai
dakin adana yara da'ita kasancewarta bakwaini
'yar firit da ita a nan suka kuma had'uwa da
Yagana da Hajja kowannensu na yi wa kowa san
barka.
Hamza baki yak'i rufuwa,abokan aikinsa sai
tayashi murna suke yi.Kai tsaye ya yi wa Hajja
bayanin zai je gida ya d'aukowa Faanah kayanta
anan Yagana ta nemi alfarmar ya sanarwa
Yakura haihuwar Yalfata badan ransa ya soba ya
amshi sak'on.
Yana fitowa dakin sukai kici6us da Bakura, gaba
daya sukai dariya Bakura yace"angon k'arni"kai
ya sosa yana sunne shi k'asa Baana ya rik'o
hannunsa "Abbagana ina babynmu?"Dafa kansa
ya yi yace"karka damu zaka ganta".Murmushi ya
yi suka wuce gida baki daya, Bakura ne ya amshi
sakon sanar da Yakura haihuwar Yalfata Hamza
ya wuce kasuwa dan siyo kayan buk'ata.
Da murna Bakura ya sanar da ita haihuwar, babu yabo ba fallasa ta nuna murnarta da haihuwar.Lokacin da Hamza ya dawo nik'i-nik'i da kaya dangin cimar masu jego ya nufo asibitin a bakin k'ofa sauki kici6us da Yakura ta kalleshi ta watsar taja Baana suka nufi shiga b'angaran masu haihuwa.

Kar6e hannunsa ya yi ya nufi wajan Hamza"Abbagana muje naga jaririyar Hajja" bai tanka ba yaja hannunsa suka shiga takaici ya kume Yakura tai kwafa a ranta tace "Allah ya kai damo ga harawa"ni kuwa nace"kobai ci ba ya taka Yakura".Ciki suka shiga cikin mutuntawa ya risina ya gaida Yagana ya yi musu barka, tana tsokar Baana "ga matarka" ya turo bako "ni jaririyar Hajja ce matata"kai tsaye wajansu Faanah ya nufa ya iske Hajja na aikin lallashi saboda Faanah taga kowa da jaririyarsa banda ita.Cikin hikima ya dinga lallashinta da k'yar da sid'in goshi ta hak'ura, Yakura tazo taiwa Hajja barka ta koma wajan Yalfata. Cikin takaici tace "kun kira uban yar? "jinkina kai Yalfata tayi ta lumshe ido.

Tsayin kwanaki uku suna asibitin ba'a salami kowaccen su ba, kullum Yakura sai tayowa Yalfata girki sunzo tare da Baana ta kawo mata.Baana na yawan yi mata k'orafi me yasa bata yiwa Hajjansa sai tai masa banza ko ta dake shi. Bakurama ya yi iya yinsa ya zuba ido.

Talatainin dare kowa ya yi bacci, k'ur idonta biyu Yakura ta muskuta ta kali Bakura da yake baccinsa ta sauke ajiyar zuciya.Garin ya yi fayau saboda tasowar hadari,zuciyarta tai wasai ganin ta sami mafitar da ta dad'e tana nema da murmushi ta kwanta Alla-alla take gari ya waye.Washegari da safe da wuri Bakura ya fita saboda gonarsa,Baana yana zaune sai shige da ficenta take hankalinsa na kan karatunsa kasancewar an yi musu hutu yana bita da sun koma sai shiga primary four.K'arar hon d'in Hamza ya jiyo, da gudu ya nufi hanyar waje turus ya tsaya sakammakon kiran da Yakura tai masa cikin daurewa tace"ina zaka? "."Wajan Abbagana zamu ganin baby"ya fada a tsorace tunaninsa fada zatai masa sai yaga akasin hakan saboda lokuta da dama haka take masa.Murmushi tayi ta mika masa kwanon plastic mai kyau"gashi ka kaiwa Auntynka kace ina gaishe da Hajja" cikin hanzari ya karba ya yi gaba har ya kai soro ta gargadeshi in yaci sai ta yanke masa kunne. Yana fita tai shewa"Faanah sunanki matatta",da hanzarinsa ya karasa gurinsa yana shasshekar dariya "Abbagana muje in ga matata yau an budeta? "murmushi ya yi "da saura Baana".Turo baki ya yi yace "ni ni zan koma gida","pls yaron Hajja karka koma, mika rikowa Hajjan?".Dariya ya yi "na Aunty Yalfata ne da Hajjansu in ji Mamana".'Daukarsa ya yi suka tafi, suna zuwa ya kaiwa Yagana ya juyo wajan Faanah rigima yasa musu ina matarsa sai da aka kaishi ya gano ta.

Suna nan zaune Bakura ya shigo ya duba Yalfata da Faanah,daga nan ya wuce gida yana zuwa ya gayawa Bakura Hajjanta na gaisheta cike da mamaki take tambayar ina ya gansu shi ma da mamaki yace"asibiti naje dubasu yanzu Yalfata tace taga aike ta gode".Das! Gabanta ya fad'i cikin inda-inda tace"dama ba'a salamesu jiyan ba?".Cike da ginshira ya bata amsa"ga zahiri kin gani"take jikinta ya dauki rawa ta aro juriya ta yafa ta shige d'aki kawai bata tanka ba. Kafada Bakura ya zunkud'a ya koma gona ko ta kanta bai bi ba.Mintuna biyar da fitarsa ta suri lafaya ta nad'e jikinta cike da sassarfa ta dauki hanyar asibitin.Gudu-gudu sauri-sauri ta karasa tana shiga tai kici6us da Hamza ko kallonsa batai ba ta wuce.Tana shiga d'akin 'yan haihuwar karaf idonta ya gane mata abinda ya razana ta... ....
na barku lfy..
N. W. A
[8/8, 10:06 PM] Sanah S Isma'il Matazu: *YAR KURMA*
Sanah S Matazu
*24*
Hango Yalfata ta yi tana sid'e hannu alamun ta
gama cin abincin, guiwa a sanyaye ta ja jiki zuwa
cikin d'akin cikin zuciyarta ta furta"ta faru ta
k'are".A sanyaye ta zauna, Yagana ta dubeta"ke
kuma lafiyarki kin taho tamkar wadda aka
gayawa mutuwa? ".
Murmushin yak'e ta yi a ranta tana jin ciwo, ta
d'aga idanu ta kali Faanah sai walwalarta take yi
abinta.Bata jima ba ta mik'e taiwa Yagana
salama zuwa gida.Kamar mahaukaciyya haka ta
kama Baana da duka tai masa lillis, mak'ota ne
suka k'wace shi kowa ya tambayeta me yai mata
sai ta haushi da masifa haka suka tattara suka
k'yaleta a daran kasa runtsawa ta yi.Washegari
da sassafe ta tambayi Bakura zuwa asibiti, bai
hanata ba tana zuwa ta samu an salame su jiki a
mace ta nufi hanyar gidan su.Zuwanta ta samu
Ammar ya zo da kayan jaririya da sauran hidimu
nan ta samu labarin an rad'awa jaririya sunan
mahaifiyarsa wato Marwanahtu.Ta dinga yar
masa da maganganu san ranta, shi dai bai tanka
ba yai musu salama ya wuce. Yagana ta
dubeta"ke nifa bani da kud'i ya zamui da hidimar
suna? Kinsani sarai ba zan so in yi abin fad'a ba
Yakura ta numfasa tana tuna al'adarsu wajan
bikin suna sun bambanta da Babur mutan Biu da
kuma hausawa sossai.Su dai a tsarin su, idan
Mace ta haihu idan haihuwar fari ne a al'adar
bare-bari uwa ita take yin abincin suna wato
uwar 'ya.Idan hausawa ne kuma miji shi yake
yi,sai tallafawa da ba'a rasaba daga
dangi.Baburma haka suke, sai fannin sunan yaro
haihuwar farko mahaifin yaro shi ya ke za6ar
sunan yaro cikin danginsa yasa. na biyuma
haka.Na uku kuma mahaifiya ake bawa
zab'i.Ragon suna ranar suna ake yankawa a soya
a rabawa kowa,aci ana nishad'i da farin ciki.
Haihuwar fari Uwa za tayi kyan goyo,mai yawa
mijima zai yi sanan dangin miji zasuyi nasu
akwati guda kayan sossai abin dai sai wanda ya
gani.Ga abinci mai dad'i da sunasur da miyar
kub'ewa ake ci sai wani abu kamoniya shi kuma
da kayan ciki ake ci. Kamar source haka yake
suna yawan yinsa duk taron suna da shida da
basise.
Shi basise da madara ake yi da shinkafa da
mangyad'a ko man shanu.
*DAHUWAR BASISE*
Shi dai basise da farar shinkafa ake yinsa,
shinkafar tuwo idan kika d'ora ruwa ya tafasa sai
ki wanke kizuba kamar zaki yi tuwo.Idan ya dahu
sossai sai ki dama madara d'an kauri sai kizuba
da suga kituk'a yayi d'an ruwa-ruwa idan ya
sulala sai ki sauke sai kid'ansa mangyad'a ko
manshanu sai ci.
Ajiyar zuciya ta yi ta muskuta tace"Hajja su
Ammar sun fita kunya saura mu".Yagana ta
gyara zama tac"ai shi ne nake sanar miki"Yalfata
tai jigum tana jinsu hannunta kan cikinta ita
kad'ai tasan abinda take ji.Kud'i Yakura ta
zubewa Yagana"Hajja gasu nan dubu hamsin ne
kiyi amfani dasu kafin Bakura ya dawo zan je
unguwa".Ta washe baki ya gonar auduga"sai kin
dawo",har ta kai karshen k'ofa ta juyo sukai
kallon k'uda da Yalfata ta kad'a kai tai waje cike
da ginshira.
(((o(**************************)o)))
Tamkar wadda zata tashi sama haka ta nufi
dajin,cikin sauri-sauri take haye tsaunin har
gocewa take duk hannunta ya k'uk'uje saboda
wahalar data sha tana isa k'arshan tsaunin ta
haye tana muzurai.Cikin rawar murya ta soma
kirari,ga Bokanta.Fit! Yayo fitar burgu daga
saman tsaunin yana dariya sai ta zube ta sa
kuka mai cin rai.
"Na yi kuskure Bokan bokaye, kaimin agaji",dariya
ya yi ya buga k'afa k'ura ta tashi fuu! Yai kukan
kura ya yi kirari yace"dama na gaya miki babu
yadda zan gyara wanda ya ci shi zai mutu".'Bat
ya b'acewa ganinta, jikinta a matuk'ar galabai ce
ta rarrafa zuwa k'asan tsaunin hanya ta nufo
tana sak'e-sak'e a ranta tafiya mai nisa ta fito da
ita bakin titi daga nan ta wuce gida.
Tsayin kwana biyu gaba d'aya Yakura ta kasa
sukuni, har zuwa ranar suna komai a d'ararre
take yin sa sun sha suna an yi abubuwan bajinta
sossai dangin biski, sunasur da sauran su.Har
zuwa yamma Yalfata na walwala cikin jama'a
gab da magarba jikinta ya soma rikicewa.Iya
tashin hankali Yakura ta shiga, tana rik'e da
Yalfata wadda ke murk'ususu ta rik'e cikinta sai
hawayen wahala take gaba d'aya ta
galabaita.Yagana taiwa Yakura tsawa"ki tashi mu
kaita asibiti",jiki a sanyayye ta kamata suka wuce
asibiti da hanzari aka karb'eta tsayin lokaci
likitoci na iya k'ok'arin su a kanta an samu ciwon
ya lafa har ta samu bacci nan Yakura suka shiga
suka ganta.Daganan Yakura ta zauna wajanta,
Yagana ta juya gida d'auke da Marwahnatu a
bayanta dan kwantarwa da jama'a hankali.
Tafiyar Yagana da mintuna goma Yalfata ta farka
cikin matsananci ciwo, a guje Yakura ta fito
neman likita sukai kici6us da Hajja da Hamza
gefansu Faanah da Baana da alamu daga
b'angaran kula da bakwaini suka fito cikin
hanzari Hajja ta rik'o Yakura.
"Lafiya Yakura? "
Cikin kuka tace"Yalfata ce....." sai kuka ya
sik'eta gaba d'aya ta basu tausayi da sauri
Hamza ya kira mata likitan dake kula da Yalfata
suka rufawa d'akin baya a tare gaba d'ayan su.
Da sassarfa suka isa,suna shiga suka tsaya turus
sakammakon abinda idanunsu ya gane
musu.Yakura ta saki wata giggitaciyar k'ara sai
kuma lauu! Tayi k'asa a hanzarce Hajja ta
tarota,rinjayarta take gaban Hajja ya yanke ya
fadi a kidime tace.
"Hamza!".Firgigit Yakura ta farka ganinta a kan gadon asibiti ya tsinka zuciyarta, jiki na rawa ta diro tana dube-dube cikin sauri ta bud'e k'ofar tai waje dai-dai lokacin aka turo gawar Yalfata Yagana na kuka Hajja na lallashinta.Yakura ta sunkuyar da kai hawaye taf idonta ni kaina taso bani tausayi amma dana tuna k'udirinta sai naji haushin kaina, dama ita mugunta fitsarin fako ce.

Hajja ce ta kamata suka wuce gida, dangi kowa ya yi jigum na alhinin mutuwar Yalfata nan da nan aka hadata zuwa gidanta na gaskiya, ubangiji yasa mui kyakkyawan karshe.Tsayin kwana uku ana karbar gaisuwa,daga nan aka nad'e shimfid'un zaman makoki.Yakura duk ta rame ta fita hayyacinta.Yakura ta so karb'ar Marwanahtu amma Yagana ta hanata kullum ana bata madarar shanu da wannan yarinyar ta samu kulawa.


Su Faanah masha Allah suna samun kulawa sossai,yarinya taci sunan Benazirahtu lokacin da Hajja tai masa k'orafi kan sunnan da ya saka hai jib'anci sunan wani cikin danginsa ba kawai murmushi

Please Login or Register in order to submit comment