Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sawu a
bayansa.Cikin
kaduwa da mamaki ya juya
bayansa da
sauri.Kawai sai yaga ashe Jaruma
Safirat ce ta
durfafo shi rike da makamanta tana
tafiya da kyar
kamar zata fadi.Al'amarin dayayi
mutukar daure
masa kai kenan domin bai taba
nashin wani
mahaluki ba ya iya tashi
tsaye.Kodai mutum ya
mutu nan take ko kuma ya
kwantar cutar ajalin da
zata iya zama sanadin ajalinsa.A
takaice dai har
abada mutm bazai mike ba saidai
ya mutu yana
jinya koda kuwa zai shekara dubu a
duniya.Jaruma Safirat ta cigaba da
tunkarar
Bandaru ba tare da shakkar komai
ba.Tana isowa
dab dashi ta rinka kawo masa sara
da suka cikin
mugun zafin nama na zato.Koda ya
fara kaucewa
hare haren nata yaga tana neman
taba jikinsa
domin wannan karin da karfi na
musamman tazo
masa dashi.Ba shiri ya zare
takobinsa mai
tsananin girman gaske ya shiga
karewa duk daya
san cewa ko ta sami nasarar saran
jikinsa ko sukar
jikinsa bazai ko karcewa ba.Nan fa
suka cigaba da
kaiwa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin
nama,juriya da bajinta ta ban
al'ajani.Suka tayar da
kura akan tsaunin.Haduwar
makamansu ta haifar
da tarwatsin wuta gami da wata
irin kara tamkar
ana kwasa tsawa,sannan wani irin
tururin hayaki ya
rinka tashi,kai kace wuta ce keci
akan
tsaunin.Tabbas Bandaru yayi
mamakin yadda akayi
Safirat ta samu wannan gagarumin
karfi alhalin
yana ganin cewa yama gama da
ita,babu wani
sauran tasiri da zata iya yi.Saida
aka shafe kusan
ranin sa'a ana yi wannan dauki ba
dadi tsakanin
Jaruma Safirat da Bandaru amma
dayansu bai
sami nasarar koda lakutar jikin
daya ba.Koda
Bandaru yaga wankin hula zai
kaishi dare saiya
sauya salon fada ya hada dakai
mata naushi da
bugu.Ai kuwa sai ta rinka gocewa
tana karewa
kuma tana maida martani,amma fa
duk sa'adda
suka hannaye sai taji kamr karfe
take duka tamkar
hannunta zai karye,amma saboda
tsananin naci
gami da tsananin juriya taki ja da
baya ko ta daina
kai hari.Duk sa'adda ta samu
nasarar naushin jikin
Bandaru sai taga ya shanye dukan
koda kuwa akan
fuskarsa ne.Kuma sai taki yarda ya
samu jikinta da
naushi ko bugu.Koda Bandaru yaga
haka saiya
shammaceta ya jeho mata jelarsa
ya kanannade
kugunta da nufin ya dagata sama
ya rotsa da kasa
don ta ratattake kamar yadda
yayiwa wannan
bishiya.Koda Jaruma Safirat ta gane
nufinsa sai
tayi wuf ta cilla addarta cikin katon
bakinsa,al'amarin da yasa ya kasa
dagata sama
kenan ya makata a kas.Kafin ya
zura hannunsa
cikin bakin ya zaro addar saboda
tatokare masa
numfashi da hadiyar miyau sai
Jaruma Safirat ta
rugo da gudu ta daka tsalla sama
ta doki kotar
addar tata data leko wajen
bakinsa.Take addar ta
wuce izuwa cikin makogwaronsa ta
tsaya cak ita
bata wuce ciki ba,kuma bata fito
waje ba.Ba shiri
Bandaru ya warware jelarsa daga
cikin kugun
Safirat ya durkusa kasa ya fara
kokarin amai.Damar
da Safirat ta smu kenan ta rufe shi
da sara da
suka gami da naushi da bugu ta
ko'ina domin ta
gano lagonsa.Amma sai taga kamar
ko'ina a
jikinsa baya jin sara da suka ko
naushi da
bugu.Ko kallon Safirat Bandaru
baiyiba kawai
kokari yake ta amayo addar data
shuge masa
baki.Nan take Safirat ta gano cewa
ai bakinsa
shine lagonsa,don haka sai ta
shammaci Bandaru
a lokacin daya wangame bakinsa
ya zura hannunsa
guda nufin ya zaro addar,cikin zafin
nama ta sake
soka takobinta cikin bakin,itama
rabinta ya shige
makogwaronsa.Ai kuwa sai
Bandaru ya kurma
uban ihu ya fadi kasa yana birgima
da ihu ya fadi
kasa yana birgima da ihu
sakamakon tsananin zafi
da zogin dayake ji yana mai ci gaba
da kakarin
mutuwa.Wannan itace babbar
damar da Safirat ta
samu ta wuce izuwa inda aka ajiye
wannan
baka.Tana isa tasa hannunta guda
ta dauki
bakan.Bakan na barin kan karfen da
aka dorata sai
gaba daya wajen ya haskake da
wani irin haske na
musamman.Ihun aljanun dake
dajin gaba daya ya
cika dodon kunne.Ashe aljanu ne
suka rinka
kumbura suna yin bindiga suna
tarwatsewa izuwa
kwayoyin zarra saboda an karya
tasirin sihirinsu
na tsafi wanda ba'a taba karyashi
ba tsawon
shekaru dari uku da daoriya,tun
daga lokacin da
aka kirkiki wannan tsaunin aka
zuba abubuwan
dake kansa.Saida Jaruma Safirat ta
ratata wannan
baka a kafadarta sannan wannan
haske na
musamman ya bace bat.Ihun
aljanun ya dauke dif
tamkar daukewar ruwan sama.A
daidai wannan
lokacine Safirat ta juya da baya
cikin tsananin farin
cikin samun nasarar dauko
bakan.tana dingishi
gami da dafe kirjinta kuma tana yin
kakin jini tana
tofarwa saboda tsananin zogin da
take ji akan
kirjin nata sakamakin naushin da
Bandaru yayi
mata.Har Safirat ta wuce ta gaba
Badaru wanda ke
kwance a kas magashiyan cikin
gigtar mutuwa.Sai
ta dawo ta baya ta sunkuya a
kansa ta zura
hannayenta biyu cikin bakinsa ta
zaro takobinta da
addarta daga cikin makoshinsa.Faru
war hakan ke
da wuya Bandaru ya furzar da
ruwan dafi daga
cikin bakin nasa a lokacin da
numfashinsa ya
dawo daidai.Ya bude idanunsa da
kyar wadanda
tuni sunrune sun zama farare
kal.Sannan a hankali
idanun suka dawo yadda suke
da,sannan ya tashi
zaune da kyar ya budi bak ya
kirawo sunan
Safirat.Maimakon ta waigo ta
dubeshi sai ta tsaya
cak a inda take sannan tace shin
kana da wani
abin fadi ne a gareni?Koda jin
wannan tanbaya Sai
Bandaru ya kawo gwauron
numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Safirat yace,saboda
me kika ceci
rayuwata?Koda Safirat taji wannan
tambaya daga
gareshi sai ta juya ta dubeshi tayi
masa dan
guntun murmushi tace,tace saboda
kafin mu fara
yin gumurzun yaki ni da kai kayi
min alfarma guda
biyu.Alfarma ta farko itace ka
shawarceni da kada
nayi yunkurin daukar wannan baka
na hakura na
sauka kan tsaunin saboda baka son
ka cutar
dani.Alfarma ta biyu kuwa itace ka
nuna mini
zahirin karfinka domin na tsorata
dakai na fasa
yakarka domin na tsira da
rayuwata.Wannan duk
alamun ne na tausayi da jin
kai.Nagode amma na
biyaka tunda ba ceci rayuwarka a
yanzu,amma ka
sani cewa kai ne namijin karshe da
zan yiwa
taimako ko jin kai a rayuwata.Koda
gama fadin
hakan sai Safirat ta yunkura da
nufin ta sauko daga
kan tsaunin amma sai Bandaru ya
sake kiran
Safirat yace zan sake yi miki
alfarma ta karshe a
rayuwata.Idan kika sauka daga kan
wannan tsaunin
kiyi matukar taka tsantsan da
wannan Baka taki
kuma kada ki yarda da kowa
domin masu son su
rabaki da ita suna da yawa.Ke hatta
sarkinku a
haukace da farautar wannan Baka
na hannunki
kuma zai iya kashe ki domin ya
mallaketa!.Banda
shi a yanzu haka akwai jarumai
guda dari biyu da
arba'in gami da matsafa dari uku
da sittin da kuma
manyan sarakai tara wadanda suka
biyoki izuwa
cikin wannan daji suka yi lamfo
suna jiran ki gama
shan wahala ki dauko bakan
sannan su
shammaceki su rabaki da shi,domin
su karasa can
dajin Sarkuf su isa kogon mutuwa
su dauko kurtun
kwarinsa.Shawarar farko da zan
baki itace ki
lullube wannan baka naki cikin
mayafi domin
haskensa ne zai tona asirinki duk
inda
kike.Shawara ta biyu ki daureshi
tamau a jikinki ko
barci zakiyi ya kasance akansa zaki
kwanta yadda
ko yaya aka tabashi zaki ji.Shawara
ta uku itace
kada ki kuskura kiyi gaba da gaba
da wadannan
jarumai,matsafa da sarakan da suka
biyoki izuwa
cikin wannan daji.Kiyi iya kokarinki
wajen boye
musu har ki fice basu ganki ba,idan
kuma suka
farmaki kar ki yadda ki shafe sama
da rabin sa'a
kina yaki dasu.Ki tsere ki barsu ki
bace mus da
gani.Na sani cewa babu wanda
zakiyi mamakin cin
amanarsa a gareki sama da
sarkinku wato Safwan
wanda tun baki fi shekara tara ba a
duniya kuke
yin gagarumar soyayya.To kada
kiyi mamaki
domin tun sa'adda ya gano batun
kwari da bakan
da mahaifinki ya sana'anta a cikin
shekaru talatin
yaji ya tsaneki kuma ya zamana
cewa bashi da
wani buri da yafi ya hallaka ki ya
rabaki da kwari
da bakan.Koda Bandaru yazo nan a
zancensa sai
Jaruma Safirat ta kamu da tsananin
bakin ciki har
hawayen takaici ya zubo mata
saboda tsananin son
sarki Safwan.A yanzu haka akwai
alkawarin aure a
tsakaninsu,itace ta dakatar da
batun auren bisa
cewa sai bayan ta dauko kwari da
bakanta a inda
mahaifinta ya adana mata sannan
za'a daura musu
auren.Boka Saiham wato Mahaifin
Jaruma Safirat
ya kasance aminin mahaifin Sarki
Safwan,domin
Saiham ne mai bashi tsaro da
kariya daga dukkan
abin ki da makiyansa.Kauna da
amanar dake
tsakaninsu tafi gaban kwatance
don haka tun sarki
Safwan da Safira suna yara kanana
suka shaku
ainun har suka fara girma soyayya
ta kullu.Daga
ranar da mahaifin Sarki Safwan ya
gano cewa boka
Saiham ya fara sana'anta wannan
kwari da baka
wacce in ya kammalata zai iya
mallakar duniya
gaba,ya mulki kowa da komai.Sai
kishi ya
turnukeshi,yaji babu abinda ya
tsana sama da
boka Saiham din.Da farko kafin ya
tsane shin babu
irin shawarar da bai bashi ba cikin
hikima da
basira akan ya tsayar da sana'anta
wannan kwari
da baka amma sai Boka Saiham
yaki har shima ya
fusata ya daka masa tsawa
yace,saboda me zaka
tsayar dani akan sana'anta abinda
babu wani
matsafi daya taba yin kamarsa tun
daga farkon
wanzuwar duniya kawo izuwa
yanzu?Shin kana
ganin cewa idan na kammaka hada
wannan kwari
da baka zanyi amfani da ita ne
wajen cutar da
sarakai irinka?To ka sauya tunani ni
na kirkiri
wannan kwari da baka ne domin
na kare kasata
kawai daga sharrin abokan
gaba.Burina 'yata ta
gajeni akan wannan kuduri ko a
bayan raina.Kga
kenan idan danka ya auri 'yata zata
zamo mai
baiwa sarautarsa da kasarsa kariya
ta zamo tamkar
sarkin yakinsa.Koda jin wannan
batu sai Mahaifn
Sarki Safwan ya tari numfashin
Boka Saiham ya
daka masa tsawa yace,yakai tsohon
aminina kayi
sani cewa masu iko da isa basa
zama waje
daya,idan har ka mallaki wannan
kwari da baka
tamkar ka zamo sarki ne,kaga
kuwa ba'ayin sarki
biyu a cikin gari guda.Ko mutuwa
kayi idan 'yarka
ta gaji wannan baka ta zama
sarauniya,domin dole
ne jama'ar gari su rinka tsoronta
suna girmamata
kamar yadda za'aji tsoron dana a
girmamashi.Saboda haka dole ne
cikin abu biyu ka
zabi daya,kodai ka fasa sana'anta
wannan kwari da
baka ko kuma ka dauki alkawarin
cewa idan ka
kammalata niko daya ne zasu
mallaketa.Idan kuma
ba haka ba kuwa zumuncin dake
tsakaninmu zai
rushe mu zama abokan gaba na
har abada.Idan
kuma har hakan ta faru na rantse
da girman
karagata sai ka fini nadama da
bakin ciki kuma
burinka bazai taba cika ba bare na
'yarka ya
cika.Koda mahaifin sarki Safwan
yazo nan a
jawabinsa sai hawayen takaici da
bakin ciki ya
zubowa Boka Saiham yace,na sani
cewa duk irin
sihirin tsafin danake takama dashi
kaima kana
dashi.Haka kuma duk irin
jarumtakar da nake da
ita ta karfin damtse da iya yaki
kana dasu,danka
ma uana dasu kamar yadda tawa
'yar take dasu.To
amma ka sani cewa mu zuri'armu
muna da
tsananin sa'a da rabo bisa duk
abinda muka sa a
gabanmu.Saboda haka ina mai
shawartarka da
kada ka kuskura ka bari mu zamo
abokan
gaba,zaifi kyau mu ruke
zumuncinmu gami da
kaunar juna izuwa kan 'ya'yanmu
da
jikokinmu.Koda gama fadin haka
sai Boka Saiham
ya mike tsaye ya fice daga cikin
fadar ba tare da
yayiwa mahaifin sarki Safwan
cikakkiyar sallama
ba.Ai kuwa daga wannan ranan
mahaifin sarki
Safwan ya shiga shirye shiryen
yadda zaiyi ya
hana Boka Saiham cigaba da
sana'anta wannan
kwari da baka amma sai ya kasa
samun nasara.A
karshe ne ya yanke shawarar kashe
boka Saiham
ya hada baki da wata amintacciyar
baiwarsa aka
zuba masa guba a shayinsa
yasha.Boka Saiham ya
sani cewa na zuba masa guba a
shayinsa kuma
yasan cewa sarki Ne yasa aka zuba
masa amma
saiya dauki kofin shayin a lokacin
da hawaye ya
subuto masa yasa a bakinsa ya
shanye
shayin.Yana gama shanye shayin
sai ya danki
makoshin baiwar tasa da hannun
guda ya shaketa
ta fara kakarin mutuwa tana
kokarin cire hannunsa
daga kan wuyan nata amma ta
kasa.Boka Saiham
ya kurawa baiwar idanu yana mai
cigaba da zubar
da hawaye yace,yake wannan
baiwa tawa
amintacciya,yau shekara arba'in da
daya kenan
kece ke yimin bauta.Tun kina da
kuruciyarki na
siyoki a matsayin baiwa na rene ki
harkika
girma.Daidai da rana daya ban taba
sabanin ba ko
cin amanata,amma yau gashi
saboda kwadayin
matsayin da sarki zai baki gami da
dukiya,kin
yarda kisa mini guba a shayi na
nasha na
mutu.Kin manta da duk halaccin
danayi miki a
baya.To ki sani cewa nasha gubar
kuma zan
mutu,amma bazan mutu ni kadai
ba,kema zaki
mutu kuma shima sarkin tabbas
mutuwa zaiyi
kuma nine zan kashe shi.Wannan
guba daku ka
zuba mini a cikin shayina bazata
zamo sandain
ajalina ba,sai nan da cikar kwana
ashirin da
daya,kuma a halin yanzu saura
kwana takwas
kacal na kammala sana'anta Kwari
da Bakan
nawa.Gama fadin haka ke da wuya
sai hawayen
nadama ya zubowa wannan baiwa
ta boka saiham
sannan farar dafara ta zubo daga
bakinta kuma
idanunta suka kafe jikinta ya
sandare ta zama
gawa.Take Boka Saiham ya
rungume gawar baiwar
ya fashe da matsanancin kuka na
bakin ciki.Saida
ya shafe sa'a uku rungume da
gawar yana ta
gunjin kuka sannan matarsa
Zaituna ta shigo cikin
falon gidan.koda taganshi rungume
ta gawar
baiwarsu yana ta faman rusa kuka
sai itama ta
kama kuka.Tazo ta cireshi daga
cikin jikin gawar ta
dubeshi cikin tsananin kaduwa da
bakin ciki tace
wane ne ya kashe mana baiwarmu
ta amana,wacce
muka raineta tun kuruciya tamkar
'yar cikinmu?
Koda jin wannan tambaya sai Boka
Saiham ya
rungume Zaituna a kirjinsa ya
kankameta har sai
da yaga ta sami yar nutsuwa
sannan ya bata
labarin duk abinda ya faru
tsakaninsa da sarki da
kuma gubar da sarki yasa wannan
baiwa tasu ta
zuba masa a cikin shayi ya sha.Ya
tabbatar mata
da cewa nan da cikar kwanaki
ashirin da daya zai
mutu kuma tare da sarki zasu mutu
tare.Yayi wani
kakari sannan ya zubar da kumfar
gubar,daga
bisani ya cigaba dacewa,amma
idan Safirat ta cika
shekaru sha takwas a duniya ki...
KIBIYA RATSA MAZA
Littafina na daya(1)
Part C
Amma idan safirat ta cika shekaru
goma sha takwas
a duniya ki bude akwatina ta karfe
ki dauko mata
kundina ki bata ta karanta.Bayanin
duk abinda zatayi
ta gajeni yana ciki kuma ki gaya
mata cewa ta adana
wannan kundin da kyau cikin
sirri.Kuma ta tabbatar
da cewar dare da rana tana tare
dashi.Koda gama
fadin haka sai Zaituna ta sake
rungume Boka Saiham
ta fashe da sabon kuka.Al'amarin
daya karya
zuciyarsa kenan shima yaci gaba da
kukan.Kamar
yadda Boka Saiham ya fada haka
al'amari ya
kasance sai da ya kammala
sana'anta kwari da
bakansa sannan kwanakinsa daya
diba na ajalinsa
suka cika yace ga garinku.Shima
Mahaifin Sarki
Safwan a wannan rana ya mutu ba
tare da wata cuta
ba domin lafiyarsa kalau yaje fada
ya dawo
gida.Koda ya shiga turakarsa ya
kwanta akan gado
domin ya huta shi kenan sai fito da
gawarsa
akayi.Amma kafin ya mutu ya
barwa dansa Safwan
wasikar cewa yayi taka tsan tsan
da Safirat 'yar
boka Saiham ya cire sonta daga
cikin zuciyarsa a
asirrance ba tare da ya nuna mata
ba a
zahiri.Wannan batu ba karamin
girgiza tunanin
Safwan yayi ba,bisa wannan dalili
ne ya tsananta
bincike a cikin hallarar tsafinsa har
ya gano cewa a
mutuwar mahaifin nasa akwai sa
hannun boka
Saiham kuma dama yasan da batun
kwari da bakan
da boka Saiham ya sana'anta kuma
ya baiwar 'yarsa
Safira gadonta.Tun daga wannan
rana ne sarki
Safwan ya dauki alkawarin cewa
saiya kashe Safira
ya rabata da wannan kwari da
baka.ko dan ya dauki
fansar ran mahaifinsa.Abinda bai
sani ba shine
mahaifin nasa ne ya fara zubawa
Boka Saiham guba
a shayi yasa aka bashi ya sha.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Jaruma Safira na kuka cikin
tsananin bakin ciki ta
sauko daga kan wannan Tsaunin
Lauhul Farras,tana
saukowa rataye da wannan baka
sai taga ragowar
dodannin nan sun kura mata ido
suna kallonta cikin
tsananin mamaki kuma suka kamu
da tsananin
tsoronta.Ba shiri suka rika darewa
suna bata
hanya.Ta rika kutsawa ta tsakiyarsu
tana tafiya cikin
tangadi saboda tsananin gajiya
kuma ga hawaye na
zuba a idonta a lokacin da take
tuno da duk
abubuwan da suka far a baya
tsakaninta da sarki
Safwan.Safira ta tuno da irin
shakuwarsu da kuma
soyayyarsu tun suna yara kawo
izuwa girmansu da
yadda suka kasance kullum a tare
dare da rana babu
abinda yake raba su face kwanciyar
bacci.Ta tuno
da alkawarin dake tsakaninsu na
aure kuma ta tuno
irin amincin dake tsakanin
iyayensu.Koda tazo nan a
tunaninta sai tace kai bazai yiyu ba
ace yanzu
Safwan ne ya zamo makiyinta
ba.Safwan ba zai taba
yunkurin kasheta ba ko yaci
amanarta saboda kawai
ya rabata da wannan kwari da
baka.Wata zuciyar
kuma sai tace da ita ke dai kiyi taka
tsan tsan dashi
domin masu iya magana sunce
namiji ba dan goyi
bane kuma akan mulki ko dukiya
mutum na iya
sauya halinsa.Haka dai Safira ta
tsaya cak a kusa da
bakin tsaunin Lauhuk Farras tana
tayin tunani.Koda
taga tunanin nata yaki karewa
kuma gashi ba zata
iya ci gaba da tafiya ba,domin
raunukan dake jikinta
sai damunta suke da zogi da radadi
saita zauna a
kasa ta bude jakar guzurinta ta
dauko zare da allura
ta dinke raunikan da yayi dan zurfi
sannan ta shafa
magani akan sauran.Tana cikin
yiwa kanta magani
ne taga Bandaru tsulum a bayanta
yana kallonta
cikin murmushi.Kawai sai ya
tsuguna bisa gwiwarsa
ya dubeta cikin girmamawa
yace,Ya shugabata nazo
ne gareki domin na baki wata
shawara gami da
taimako guda daya.Zaifi kyau ki
kwana nan tunda
rana ta fadi gari ya soma duhu
domin idan kika ce
zaki fita daga cikin wannan daji a
cikin wannan dare
sai makiyanki sunfi samun damar
cimmaki tunda ko
yaya kika motsa zasu ji sautin
tafiyar tunda
darene.Kuma na gaya miki cewa
suna nan a lallabe
a gaba kadan sunyi lambo,kawai
jira suke suga
fitowarki tunda su bazasu iya
karasowa ba
nan.Taimakon da nake son na miki
kuwa shine ina
son na baki yara na guda arba'in
wadanda zasu
taimaka miki wajen yakar
makiyanki duk da cewa
bazasu iya da makiyan naki ba
saboda tsananin
yawansu,karfinsu da shirinsu,amma
zasu rage miki
masifarsu.Inda ace ina da ikon
barin wannan tsauni
dana biki na zama babban mai
tsaron lafiyarki ko
don rabani da wannan bauta da
nake ciki ba har ta
tsawon shekaru dari uku da doriya
face bayan kin
hada kwari da bakanki.Ina son kiyi
min alkawarin
cewa idan kin kai ga wannan gaci
zaki kizo ki rabani
da wannan tsauni na zamo
shugaban dakarunki
tunda kaf duniya babu jarumi mai
karfin damtsena
da iya yakina.Da jin wannan batu
sai Jaruma Safirat
tayi murmushi tace shi kenan nayi
alkawari indai na
cika nawa burin zanzo na tserar
daka daga wannan
bauta kuma na baka shugabancin
dakaruna.Koda jin
haka sai farin ciki ya lullube
Bandaru yayi
godiya.Nan take ya umarci dodanni
biyu suka hau
kan tsaunin Lauhul Farras suka
dauko tanti,shimfida
ta alfarma gami da kayan abinci na
alfarma suka zo
suka shiryawa Jaruma Safirat.Bayan
sun gama kafa
mata tantin ne ta shiga ciki ta
zauna ta ci ta sha tayi
hani'an.Koda ta hau kan shimfidar
da ka yi mata taji
taushinta sannan ta dubi kayan
alatun da aka shirya
mata a cikin tantin sai ta gyada kai
cikin murmushi
tace,hakika dole ne mutane su so
mulki da dukiya a
cikin wannan duniya.Nikuwa idan
na gama hada
wannan kwari da baka nawa zan
dandana dadin
mulki naji yadda sarakai keji.Tana
gama fadin hakan
sai ta kwanta akan shimfidar ta
mikar da
kafafunta.Abinka da gajiyayye
wanda yaci ya
koshi,nan danan barci ya saceta
bata sani ba.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Rundanace ta manyan jaruman da
duniya ke takama
da ita,tun daga nesa idan ka hango
wannan runduna
zaka yi zaton gaba dayan mutane
da aljanun duniya
ne suka fito yaki.A gaban wannan
runduna wani
hatsabibin sarki ne mai tsananin
mummunar kama
da girman jiki ga manyan
damatsa.Kakkarfa ne na
gaske haye akan toron giwa.Sarki
Haimarul Dainun
ya kasance daya daga cikin manyan
sarakunan
duniya wanda yake mulkin daular
kasashen nahiyar
Habasha gaba daya.Wannan fitowa
da Sarki
Haimarul Dainun yayi tane da nufin
cewa bazai koma
gida ba har sai ya mallaki kwari da
bakan da boka
saiham ya sana'anta a bisa
kudurinsa na ya mallaki
duniya.Sarki Haimarul Dainun ya
sha alwashin kawar
da dukkan wani mahaluki dayake
da irin
kudirinsa.Akan wannan dalili ne ma
yasa ya debo
gaba dauan rundunarsa ta yaki
izuwa dajin Lauhul
Farrasa.Lokacin da Sarki Haimarul
Dainun yayi
wannan fitowa baya barin duk
wani karamin kauye
damanyan birane face ya yakesu ya
hallakasu gaba
dayan masu rauni daga cikinsu
kamar mata,tsofaffi
da kananan yara,sannan ya kona
gidajensu gami da
rushe sauran ginin garin.Jarumai
dake cikinsu kuwa
ya kamasu su zama daga cikin
rundunarsa ta yaki
bisa tilas.Abinda sarki Haimarul
Dainun bai sani ba
kuwa shine gaba dayan manyan
sarakunan duniya
suma sunyo tattaki izuwa dajin
Lauhul Farras domin
mallakar kwari da baka.Lokacin da
sarki Haimarul
Dainun da rundanarsa suka zo wani
katon fili
ma'abocin dogayen itatuwa tun
daga can nesa suka
hango wani jarumi da takubba
guda ya juya
bansa.Jarumin yana sanye da wani
kwalkwali ne ba
bakin karfe wanda a dalilinsa ne
babu mai iya gabe
kowaye shi.Koda ganin wannan
jarumi sai Sarki
Haimarul Dainun ya daka masa
tsawa yace,yakai
wannan dan matashin jarumi
ma'abocin boye
fuskarsa wane dalili ne yasa kazo
ka tare min
hanya?Ko ka gaji ne da rayuwarka
ta duniya?
Sa'adda sarki Haimaruk Dainun
yazo nan a
zancensa sai wannan jarumi
ma'abocin boyayyiyar
fuska ya bushe da wata
mahaukaciyar dariya sannan
ya juyo ya fuskanci sarkin gaba da
gaba sannan ya
maida masa martani da cewa.Ya
kai sarki Haimarul
Dainun kayi sani cewa nazo gareka
ne domin na
gargadeka bisa wannan kudiri naka
Ina mai
shawartarla da ka koma gida kai da
jama'arka
domin kuwa har abda ba zaka iya
jurewa tarin
masifu da bala'in dake tattare da
mallakar kwari da
bakan nan ba.Idan kuwa kaki
yanzun nan zan yake
ka na tarwatsa wannan aniyar
taka.Ka sani cewa ni
Jaruma Safirat 'yar boka Saiham
wadda mahaifina ya
sana'anta wannan kwari da baka
dominta.Nasha
alwashin bazan bar kowane
mahaluki darai ba
muddin yace zai mallaki wannan
kwari da baka dana
fito dominsu.Koda Sarki Haimarul
Dainun yaji
wannan batu take ya kamu da
mamakin kasancewar
wannan jarumi ba namij bane ashe
mace ce.Kuma
ya kamu da tsananin farin ciki
hadauwa da safira
cikin sauki haka domin kuwa a
dalilinta ne ya fito
daga masarautar kasarsa.Takeyi
duba izuwa safira
yace,yake safira ki sani cewa na
kasance a gaba
dayan rayuwa komai na tunkara
ina mai samun
nasara a cikinsa don haka naek baki
shawara da kiyi
gaggawar miko mun wannan
kwari dake dake tare
dake domin ki samu ki tsira da
rayuwa.Yayinda
Sarki Haimarul Dainun yazo nan a
zancensa sai ran
safira ya baci ainun take sai safira
ya zare takobinta
ta afka cikin kakkautawa koda
ganin haka sai Sarki
Haimarul Dainin yayiwa dakarunsa
tsawa yace me
kuke jira da ita maza ku ciro min
kanta ku kawomini
nan,ai kuwa fadar hakan keda
wuya sai gaba dayan
dakarun suka yi mata rufdugu.Nan
ga wuri ya
hargitse aka kaceme da masiffaen
yaki ya zamana
cewa duk inda safira ta kai sara
saidai kaga maza na
zubewa kasa tamajar ana sassabe a
gona.Wohoho!
Aika ga mai kareka lokaci guda
safira ta bazar da
gaba daya dakarun dake gabanta
ta falfala da
azababben gudu ta tunkari inda
sarki Haimarul
Dainun yake bisa toron
giwarsa.Kafin yayi wani
yunkuri ta daka uban tsalle sama
kamar daga cikin
baka aka harbota kawai sai gani
akayi ta fille masa
kai.Koda sauran dakarun nasa suka
ga kan sarkinsu
a sama cikin iska sai suka dimauce
suka zubar da
makanmansu suka cika wandonsu
da iska suka
bazama izuwa cikin daji,taje safira
ta koma inda ta
baro Bandaru da sauran Yaransa.
SHIN SAFIRA ZATA SAMI NASARAR
HADA KWARI DA
BAKAN HAR TAYI AMFANI DA ITA?
INA LABARIN SARKI SAFWAN,WANE
TANADI YAKEYI
AKAN FUSKANTAR JARUMA SAFIRA?
YAYA SAURAN MANYAN SARAKUNA
DA BOKAYE
ZASU FUSKANCI SAFIRA.
Muhadu a littadi na biyu domin jin
cigaba wannan
kasaitaccen labari.
KIBIYA RATSA MAZA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A
A CAN BAKIN DAJIN TSAUNIN
LAUHUL-FARRAS
kuwa runduna ce ta
sarakai,matsafa,jarumai da
manyan bokayen duniya suka
kakkafa sansani
tsubi tsubi a wurare dabn
daban.Kowace runduna
ta fito ne domin farautar Jaruma
Safirat ta kasheta
sannan ta rabata da wannan baka
data dauko a
kan tsaunin Lauhul Farras.Wannan
shine kura da
shan bugu gardi da kwashe
kudi.Daga cikin
rundunar sarakan da suka zo har da
sarki Safwan
tare da dakarunsa na yaki mutum
dubu goma
kuma suma sun kafa sansaninsu
wanda shine mafi
kusanci da tsibirin Lauhul
Farras.Lokacin da rana
ta fadi ne sarki Safwan tare da
shugaban
dakarunsa wani barde da ake kira
Barha na tsaye a
bakin tantin sai sarki Safwan ya
dubi Barha yace
amma nayi mamakin abinda yasa
har yanzu Safirat
bata fito ba daga cikin wannan daji
na tsibirin
Lauhul Farras.Koda jin haka sai
Barha yayi gyaran
murya yace haba ya shugabana ai
bai kamata kayi
mamaki ba tunda ka sani cewa
babu wani
mahaluki daya taba hawa kan
tsaunin Lauhul
Farras ya sauko kasa a raye.Babu
mamaki itama ta
mutu ne a lokacin hakan.Sarki
Safwan ya girgiza
kai yace Safirat bata mutu ba kuma
nayi bincike a
cikin madubi tsafina naga cewa
zata rayu bisa duk
irin gumurzun da zatayi da dakarun
dake kan
tsibirin har ta sami nasarar dauko
wannan
sihirtaccen baka na mahaifinta.Sa'a
dda barde
Barha yaji wannan batu sai yayi
ajiyar numfashi
sannan ya dubi sarki Safwan cikin
alamun tsananin
damuwa da karayar zuciya yace ya
shugabana
yanzu dai da idanunka kaga
runduna sama da
guda arba'in a bayanmu ta manyan
sarakan
duniya,matsafa da jarumai masu ji
da kansu.Yanzu
koda ka sami nasarar kashe Safirat
ka dauko
wannan baka dake hannunta ta
yaya zamu iya
ficewa daga cikin dajin nan da
bakan ta gaba
wadannan miyagun rundunoni
alhalin suma abinda
suka zo farauta kenan?Dajin
wannan batu sai sarki
Safwan ya bushe da dariya.Al'amari
n daya kara
baiwa barde Barha mamaki
kenan.Daga can sai
sarki Safwan ya hade fuskarsa yace
ai raba Safira
da wannan baka yafi tsare bakan
wahala.Duk
wadannan rundunoni da kake gani
na banza ne
muddin daya daga cikinsu bata
rigamu karbar
bakan ba.Bisa wannan dalili ne
yasa kaga ni nayi
kundunbala nazo daf da bakin dajin
tsaunin Lauhul
Farras saboda ya zama nawa da
zarar Safira ta fito
ya kasance nine mutum na farko da
zatayi arba
dashi.Ninasan cewa indai zamuyi
GABA DA GABA
da ita to saina rabata da bakan
tunda bata finin
KARFIN DAMTSE ba dana tsafi kuma
bata fini iya
yakio ba.Duk abinda take takama
dashi nima ina
dashi ko mafiyinsa.Kuma muna
haduwa zan shaida
mata cewa ubanta ne ya kashe
mahaifina don haka
ina son na dauki fansa a kanta,kaga
bata da ikon
cewa naci amanar soyayyarta.Kao
bari na gaya
maka gaskiya,koda Mahaifinta bai
kashe nawa ba
zan iya zuba idanu ba ina kallonta
ta fini matsayi
ba da daukaka tunda nine
sarkinta.Dole ne ka
kawar da batun soyayya na ceci
mulkina da kasata
tare da duk al'ummata.Babu sani
ba sabo a
tsakanina da Safira saidai KAIFIN
TAKOBI ya
rabamu.A yanzu haka ina zargin
cewa Safirat zata
iya fakar numfashinmu ta fito daga
cikin dajin
Lauhul Farras a cikin wannan dare
ta sulale ta
gudu ba tare da wani ya
gantaba.Koda jin wannan
batu sai Barde Barha ya gyada kai
cikin alamun
shakku yace haba ya shugabana ta
yaya Safirat
zata iya wucewa ta gabanmu ba
tare da ka ganta
ba tunda bata da wani sihiri na
bata wanda baka
da shi.Nidai kawai shawarar da zan
baka itace
kada ka kuskura kace zakayi bacci a
cikin daren
nan domin ta bakin kane a ko
yaushe zata iya
fakar numfashi ta fito din.Koda jin
haka sai sarki
Safwan yayi murmushi yace tabbas
maganarka
dutse ce.Dole ne hakura da bacci
gaba daya a
daren yau.Ai kuwa sarki Safwan bai
yarda ya kara
shiga cikin tantinsa ba.Kujera aka
kawo masa ya
hau ya zauna a waje yana mai
fuskantar cikin dajin
tsaunin Lauhul Farrs kuma
takobinsa nakan
cinyarsa ya dafeta da hannunsa
guda sannan kuma
yasa wata kuyangarsa ta dafa masa
shayi aka zuba
masa sinadaron hana bacci a ciki
yasha.Har gefen
asuba idanun sarki Safwan a bushe
suke ko
alamar bacci babu a tare dashi.
*Al'amarin Jarum Safirat kuwa
tunda ta kwanata a
cikin tantinta ta kama bacci ko
kyakkyawan motsi
bata sakeyi ba har asuba tayi.Kawai
sai ji tayi ana
tashinta kamar a mafarki.Safirat ta
mike tsaye
Zumbur a dan firgice.Tana bude
idanunta sai taga
ashe Bandaru ne tsugune a
gabanta kansa
sunkuye don biyayya.Ba tare daya
dago kansa ba
ya dubeta yace ya shugabata yanzu
ne daidai
lokacin daya kamata ki shirya ki
fice daga cikin
dajin nan ki durfafi hanyar da zata
kaiki can Dajin
Sarkif domin ki isa kogon mutuwa
don dauko
kuttun kwarinki.Kamar yadda na
gaya miki a baya
cewa masifar dake cikin dajin Sarkif
ta ninka wacce
ke cikin wannan daji namu sau
goma don haka
saiki jajurce kuma kiyi matukar
juriya da
hakuri.Duk tarin rundunonin
makiyan da suka
biyoki izuwa nan ba zasu iya binki
ba izuwa dajin
Sarkif amma ina zargin cewa
mutum daya zai iya
binki.Koda Bandaru yazo nan a
zancensa sai
Jaruma Safirat ta tari numfashinsa
tace nasan
kowane ne ba wani bane face sarki
Safwan babban
masoyina a da yanzu kuma babban
makiyina.Koda
jin haka sai Bandaru yayi
murmushin murna yace
ina farin ciki da kika fahimci hakan
duk da cewa
har iyanzu nasan zuciyarki tana
miki wasu wasi
akan hakan.Amma dai na san cewa
lokaci zai
tabbatar miki da gaskiyar alamari.A
yanzu haka
tuni dakaru arba'in da nayi miki
alkawari sun gama
shirin tafiya ke suke jira.Kamar
yadda na gaya miki
a baya,kada ki fita daga cikin dajin
nan goye da
bakanki tsirara face kin lullubeshi
cikin mayafi
saboda hasken sane zai fara
™Abubakar Haleefah Physicist™
tona miki asiri.Yanzu ga mayafin da
zaki lullube
bakan na kawo miki.Nan take
Bandaru ya daga
hannunsa sama saiga wani bakin
mayafi ua
bayyana tsulum a hannun nasa
kawai sai ya mika
mata ta karba yace wannan ne
kadai mayafin da
zai iya boye hasken wannan kwarin
naki.Maza ki
lullubeshi yanzu.Ba tare da wata
gardama ba kuwa
sai Safirata ta mike tsaye ta ciro
Bakan daga
bayanta wanda ta daureshi tamau
kuma ta kwanta
a kansa tayi bacci tun a daren
jiyaSafirat na ciro
bakan sai ta lullubeshi da wannan
mayafi.Nan take
kuwa taga hasken nasa ya bace
bat.Cikin sauri ta
mayar da bakan bayanta ta goyashi
kuma ta
daureshi tamau.Faruwar hakan
keda wuya sai
Bandaru ya sake daga hannunsa
guda sama saiga
wani takalmi fade na fatar damisa
ya baiyana
tsulum akan hannun nasa.Kawai sai
ya mika mata
yace ungo wannan ki sanya a
kafafunki.Indai har
da wannan takalmin a kafarki babu
yadda za'ayi
wani yaji sautin tafiyarki ko
gudunki.Abinda nakeso
dake shine daga nan ke da dakarun
dana baki
guda arba'in zaku fice da gudun
tsiya ku nufi
arewa nan ne hanyar da zata kaiku
izuwa dajin
Sarkif.Kiyi gudu iya karfinki da
iyawarki.Ta gaban
makiya zaku wuce amma babu mai
iya cimmaku
saidai a riskeku a can dajin Sarkif
inda kowa zai
shiga cikin tararrabin rayuwarsa.Ni
kaina ba zan
baku tabbacin cewa zaku tsira da
rayuwarku ba
acan.Da wannan furuci nake yi miki
bankwana
yake sarauniyar Duniya ta
gobe.Kuma inayi miki
fatan sa'a da nasara bisa wannan
gagarumin aiki
dake gabanki.Ina fatan zaki zamo
mai cika alkawari
a gareni bayan bukatarki ta
biya.Bandaru na gama
fadin hakan saiya juya domin ya
fice daga cikin
tantin amma sai Safirat ta kira
sunansa da sauri
tace nagode bisa duk irin wannan
taimako da ka
bani kuma lallai zan zamo mai cika
alkawari a
gareka.Koda jin haka sai Bandaru
yayi murmushi
ya fice.Fitarsa keda wuya sai itama
Safirat tayi yan
kintse

Please Login or Register in order to submit comment