Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya izuwa inda
fatattakakken tantinsa
yake ya shiga kukkullashi yana
gyara shi cikin
matukar takaici da bakin ciki.Hakika
inda ace yayi
arba da wanda yayi masa wannan
barna da sai
yayi masa muguwar azaba ko
KISAN
WULAKANCI.Samazan ya hado
itatuwa ya kunna
wuta sannan ya zauna a gaban
wutar ya dauko
zare da allura ya kama dinke jakar
guzurinsa
wacce aka fatattakata.Gama dinke
jakar keda wuya
saiya fara gyangyadi kawai saiya
bingire kasa ya
kama bacci mai nauyi harda
munshari saboda
tsananin gajiyar dake jikinsa
sakamakon doguwar
tafiyar daya sha da kuma aikin sare
bishiyar da
yayi,tabbas jiki da jini akwai gajiya.
MAI ZAI FARU DA WANNAN JARUMI?
Sai Mu Hadu
a Cikin Littafi Na Biyar Don jin
cigaban wannan
labari. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part Â.
BAYAN BACCI YA SACE SAMAZAN DA
KAMAR
DAKIKA ARBA'IN SAI GA WANI
MURTUKEKEN KADA
YA TASO SAMA DAGA KARKASHIN
WANNAN
RAFI.Masana tarihi da masu bincike
a doron kasa
sun tabbatar da cewa a duk fadin
duniya babu
wani kada mai girmansa.Wannan
daji da Samazan
ya shigo ana kiransa da suna
Mautul Inzag.Fiye da
shekaru dari daya da ashirin baya
mutane da
dabbobi,tsuntsaye da aljanu basa
shigowa cikin
wannan daji na Mautul Inzag
saboda masifar
wannan kada wanda ya kasance
sihirtacce.Shi dai
wannan kada asalinsa wani boka
ne ya taba zama
a gefen birnin dake daf da dajin
Mautul Inzag ya
samar dashi ya barwa mutane
annoba.Ba komai ne
yasa bokan yayi wannan kada ba
sai saboda yar
sarkin garin yake mutuwar so
bayan ya shafe
shekaru goma yana yi mata wahala
kuma yana
taimakon mahaifinta da birnin
gaba daya bisa
alkawarin za'a aura masa ita.Sai
akayi masa
butulci aka aurar da ita ga sarkin
wani gari
daban.Bakin cikin hakan ne yasa
bokan ya kamu
da ciwon zuciya.Koda ya tabbatar
da cewa wannan
shine ajalinsa saiya dauki alkawari
cewa saiya
haifarwa da birnin mai suna
Kaldusa masifar da
zatayi ta addabarsu har
abada.Bayan kwana bakwai
da mutuwar bokan ne kadan mai
lakabi da Inzag
ya baiyana a cikin wannan katon
rafi.Baiyanarsa
keda wuya sai duk dabbobi da
tsuntsaye da
aljanun dake cikinsa suka rinka
ratsa ta cikin dajin
basa isa birnin Kaldusa face sun
zama
gawarwaki,komai yawan rundunar
mayaka da karfin
sihirin su da suke zuwa musamman
domin yakar
kadan dayansu baya tsira da
rayuwarsa.Idan kadan
ya taka kasa girman takun sawunsa
yana kaiwa
fadin zira'i ashirin da kuma zurfin
kamu
goma.Tsawon Inzag kuwa daga
kansa zuwa
karshen jelarsa yakai kamu dari da
sittin don haka
yana iya kanannade jelarsa yayi
gammo da
ita.Gaba daya jikin nasa kaifi ne
dashi tamkar
zabira don haka duk abinda ya
doka da jelar tasa
koda kuwa dutse ne ko karfe saiya
rabashi gida
biyu ko ya ragargaza shi.Duk
abinda Kada Inzag
ya ciza da hakoransa indai mai
raine take yake
rubewa ya rinka fitar da
tsutsotsi.Idan ya wangame
bakinsa ya feso wani irin ruwa
saikaga kamar
ruwan sama ne ya sauko kuma duk
abinda ruwan
ya taba saiya narke ya
zagwanye.Daga ranar da
kada Inzag ya baiyana sai fari da
talauci ya kama
birni na Kaldusa ya zamana cewa
duk shekara sai
anyi mummunan fari,yunwa da
cututtuka iri iri suka
addabi mutane duk wanda yayi
yunkurin yin Hijira
kuwa saidai a tsinto gawarsa a
bayan gari.Wani
abin mamaki shine duk irin cutar
da ta kama
mutum ba zata kashe shi ba amma
kuma baza'a
taba warkewa ba koda likitocin
duniya zasu taru a
kansa.Bisa wannan dalili ne
kasashen dake
makwabtaka da kasar Kaldusa suke
kyamatarsu
aka hana su yin huldar komai da
kowace kasa ya
zamana cewa ba'a shigo musu
suma basa shiga
wata kasar.Bisa wannan dalili ne
harkokin
kasuwanci suka dakushe,abincin da
ake nomawa a
kasar ya daina isar talakawa,ya
zamana cewa
kowane gida sau daya akeyin
abinci,komai rashin
imanin mutum idan ya shiga cikin
birnin Kaldusa
yaga yadda mutane ke fama da
rama da bakin
talauci dole ne ya tausaya
musu.Musamman idan
ya dubi kananan yara yaga cewa
zai iya kirga
kasusuwan jikinsu.Haka ake fama
da wannan
masifa a birnin Kaldusa tsawon
shekaru dari da
ashirin kuma a dalilin hakanne
kowa ya rungumi
kaddara tun mutane na shiga dakin
bautar garin
suna rokon abin bautarsu akan ya
magance musu
wannan matsala har saida sukayi
fishi suka daina
bautawa gunkin nasu aka rufe
dakin bautar gaba
daya.Lokacin da Kada Inzag ya taso
sama daga
karkashin wannan rafi ya hango
Samazan kwance a
can gefe daya yana ta fama shara
bacci sannan
kuma yaga tantin daya rusge an
sake kafashi.Nanfa
mamaki ya kama Kada Inzag domin
tsawon
zamansa a cikin wannan daji
shekaru dari da
ashirin wannan ne karon farko
dayaga bil'adaman
daya iya shigowa har yazo bakin
gabar rafin da
yake ciki,cikin sanda Kadan ya fito
daga cikin rafin
ya zagaye Samazan har sau biyu
yana kallonsa
kawai yana nazarinsa.Maimakon ya
hallakashi
saiya sake ragargaza tantin nasa
sannan ya koma
cikin wannan rafi yayi nutso izuwa
karkashinsa.Duk
karfin sautin takun kadan da kuma
karar rugujewar
tantin bata sa Samazan ya farka
daga baccin da
yakeyi mai nauyi ba.Har saida gari
ya waye,koda
rana ta fito da dallare kan fuskar
Samazan saiya
farka daga bacci a firgice yana bude
idanunsa yayi
arba da wawakeken takun
sawayen kadan kewaye
dashi.Tunda Samazan ya fara
yawon farauta a cikin
dazuzzuka bai taba ganin sawun
kafar dabba mai
girma kamar wannan ba,abinda ya
tsora tashi ma
shine ganin zurfin takun
sawun,ganin sawun ya nufi
cikin wannan kogi ne ya tabbatar
masa da cewa
halittar ruwa ce.Abinda ya kara
fadowa Samazan a
rai shine me yasa wannan halitta
bata kashe shi ba
kuma ya akayi ta fito har ta
zagayeshi amma baiji
motsinta ba ya farka?Amsar da
Samazan ya kasa
baiwa kansa kenan.Kawai sai yace a
ransa idan ma
tsorona dabbar taji ai zamu hadu
ne kafin nabar
wannan daji(Kunji Gwarzon
Namiji).Koda gama
fadin hakan saiya dauko jakar
guzurinsa ya fiddo
da kalaci yaci sannan ya kama aikin
sassaka kwale
kwalensa.Saida Samazan ya yini
yana wannan aiki
har doshin magriba saadda gari ya
fara duhu
sannan ya dakata ya huta.Samazan
bai kammala
aikin kwala kwalensa ba sai bayan
cikar kwanaki
uku,kuma a tsawon wannan lokaci
kullum saiya
jiyo gurnanin wannan kada a cikin
rafi amma ko
kadan bai fito ba sunyi arba.Abinda
bai sani ba
shine kadan baya fitowa bakin
gabar rafin face sai
bayan kwanaki bakwai ko kuma
idan wani abu ya
fada cikin rafin bisa tsautsayi.A cikin
wadannan
kwanaki ukun ne kuma Samazan
ya sami
™Abubakar Haleefah Physicist™
damar yin yawo sosai a cikin
wannan daji har ya
gano abinda yayi matukar bashi
mamaki kuma ya
jefashi cikin tsananin farin ciki.Ba
komai ya gano
ba face akwai dumbin dukiya mai
tsananin yawan
da babu kamarta a ko ina cikin
duniya.Samazan ya
gano cewa akwai tarin lu'u lu'u da
zinare a cikin
kogunan dajin wadanda za'a iya
shafe shekara dari
ana hakosu basu kare ba.Lallai idan
da akwai
kasar dake mallakin wannan daji
kuma inda tasan
da wannan dukiya da babu kasar
da zata kaita
arziki.Nan take Samazan yace a
ransa ya zama
dole na bincika na gani ko da akwai
masarauta a
kusa da wannan daji domin na
nemi hadin kan
sarkinsu mu hako wannan dukiya
tare.Nikam Allah
ya kawo mini karshen wannan
rayuwa daga nan na
daina yawon duniya don cika
burina.Shidai
Samazan ya baro kasarsu ne don
neman arzikin
da zai huce takaicin da dan sarkin
garinsu ya
kunsa masa kuma bisa alwashin
hakanne yayi
bankwana da iyayensa abin ya faru
ne kimanin
shekaru uku baya.Samazan ya
kasance haifaffen
birnin Hindu kuma mahaifinsa ne
sarkin mafarauta
na kasar gaba daya amma ya tsufa
ainun don haka
bashi da wani buri wanda yafi
dansa Samazan ya
gaje shi,amma inda matsalar take
dan kanin sarkin
Hindu wanda ake kira Balwan bashi
da burin da
yafi ya sami wannan sarauta ta
sarkin mafarauta
saboda da can asalin sarautar a
gidansu take
amma da akayi wata gasa sai
mahaifin Samazan
ya lashe gasar ya karbe kambun
sarautar daga
hannun mahaifin Balwan.Mahaifin
Balwan ya
kasance kasurgumin attajiri kuma a
cikin harkar
farauta tasa Allah yayi masa arziki
na ban
al'ajabi.Shi kuwa mahaifin Samazan
bai tara wata
dukiya ba ta'azo a gani ba amma
yana da rufin
asiri.Lokacin da mahaifin Balwan
yaga mahaifin
Samazan ya kwace sarautarsa
sunansa nata
daukaka shi kuma nasa na
dakushewa sai yayi
amfani da dukiyarsa ya rinka gine
gine na kasaita
a kasar Hindu kuma ya rinka
taimakon talakawa da
kuma duk wanda yake da wata
matsala,ada ko
sadaka bayayi bare kyauta.Duk
inda aka nemi agaji
kafin sarkin Hindu yakai nasa tuni
mafarauci
Hashmar yakai nasa..Nan da nan
Hashmar ya
zamo babban mutum a kasar Hindu
sunansa ya
daukaka ainun,darajarsa ta
girmama ya zamana
cewa ana girmamashi fiye da
yadda ma ake
girmama Sarki har takai cewa bisa
dole sarkin ke
jansa a jikinsa don shima kada tasa
darajar ta
zube.Nanfa Hashmar ya sami shiga
ainun a wajen
sarki har takai cewa shima babban
mai baiwa sarki
shawara ne akan dukkan al'amura
kuma duk
abinda ya zartar dashi ake
zartarwa.Dama tun
daga ranar da Imsar mahaifin
Samazan ya kwace
kambun sarautar a hannun
Hashmar sai gaba mai
tsananin ta kullu a tsakanin su don
haka sai
Hashmar yayi amfani da damarsa
ta wajen sarki
yasa aka hana yin farauta a cikin
gaba daya
dazuzzukan dake cikin kasar kuma
ya hana hako
ma'adanan kasa.Dama shima Imsar
yana da
wannan baiwa irin ta Samazan
wato baiwar gano
inda ma'adanan kasa suke,koda
sarkin Hindu ya
hana farauta da hako dukiya ta
karkashin kasa,sai
tattalin arzikin mafarauci Imsar ya
dakushe ya
zamana cewa babu wata hanya da
yake samun
kudi bisa dole ya koma harkar
noma,noman ma
sai yaki karbarsa,hakkane ya janyo
sanadin talauci
a gidansa ya zamana cewa da kyar
ma suke tsira
da abincin da suke ci.Tun Samazan
baifi shekara
tara ba a duniya suka tsinci kansu a
cikin wannan
matsala kuma a lokacin ne gaba
mai tsananin ta
yawaita tsakaninsa da Balwan.Tun
suna yaran
shida Balwan sun taso da
sadaukantaka da iya
yaki da farauta.Don haka duk inda
suka hadu sai
fada da yaki ya kamasu kuma duk
sa'adda suka
fafata kare jini biri jini sukeyi.Saidai
tsananin wuya
tasa su rabu bisa dole.Amma
dayansu ya kasa
hallaka dayan saboda karfin
damtsensu dana
sihirin tsafinsu yazo daya.Har suka
girma a haka
suke don hama ma sai suka daina
yakar juna aka
koma yin kiyayyar zuci,harara da
kuma
ba'a,sannan duk bala'in da daya
yaga dayan a ciki
bazai taimaka masa ba.Lokacin da
Samazan ya
zama cikakken saurayi ne dan
shekara ashirin da
biyar sai mahaifinsa Imsar ya matsa
masa akan ya
nemo matar aure saboda shi kadai
ne dansa a
duniya kuma yanason yaga
jikansa.Koda jin
wannan batu sai hankalin Samazan
ya dugunzuma
ya dubi Imsar cikin alamun
tsananin damuwa yace
haba yakai Abbana ya zaka ce nayi
aure alhalin
muna cikin wannan hali na
rashi,wani lokacin ma
abinda zamu ci a gidan nan ni da
kai da
mahaifiyata wahala yake yi
mana,sau tari sai naje
kasuwa nayi aikin karfi sannan
nake samo mana
abinci.Ka sani cewa a cikin zuciyata
na dauki wani
alkawari guda daya,alkawarin
kuwa shine inason
na shiga duniya na bazama cikin
wadansu
kasashen neman arziki.Burina shine
na samo
dukiyar da tafi ta Hashmar,ya
zamana cewa
gidanmu ya danne gidansa domin
sai nayi
abubuwan da suka ninka nasa sau
dari.Bakin cikin
daya kunsa maka ya dakusar da
sunanka ya jefaka
a cikin talauci da izinin abin
bautarmu Kirishna sai
shima ya fada ciki da dukkan
zuri'arsa.Lallai saina
daukar mana fansa,abinda nake
bukata kawai a
wajenka shine ka bani izini nayin
wannan
tafiya.Koda jin wannan batu sai
hawaye ya zubowa
Imsar yace haba yakai dana shin ka
manta ne
cewa kai ne kadai 'da na a
duniya,ta yaya kake
zaton cewa zan barka kayi wannan
tafiya wacce
bansan ranar dawowarka ba,kuma
babu tabbacin
cewa zaka dawo a raye,gashi na
tsufa karfina ya
kare kuma ko yaushe rai zai iya
halinsa duk da
cewa tsufa ba mutuwa bane.Koda
tsoho Imsar
yazo nan a zancensa sai jikin
Samazan yayi sanyi
kuma shima yaji ya kamu da
tsananin tausayinsa
bai san sa'adda shima ya kamu da
tausayinsa ba
har idanunsa suka ciko da kwallah
nan take suka
rungume junansu suka kama kukan
zuci.Daga
wannan rana Samazan ya cire
™Abubakar Haleefah Physicist™
burin daukar fansa akan sarkin
mafarauta Hashmar
da iyalansa ya maida hankalinsa
akan kokarin ruke
gidansu da kyautatawa iyayensa da
kuma tsare
mutuncinsu har tsawon wata
uku,ya zamana cewa
shida iyayen nasa suna cikin zaman
lafiya da
kwanciyar hankali saboda a
wannan lokaci
Samazan ya zage damtse yayi aikin
karfi mai yawa
ya samo yan kudade masu yawa
don haka sai ya
siyo musu abinci mai yawa wanda
zai ishesu har
tsawon shekara guda kuma ya
baiwa mahaifiyarsa
yan kudi masu yawa yace ta adana
su saboda
amfanin yau da kullum.Saboda jin
dadin wannan
abu ne da yayi musu ya zamana
cewa kullum a
cikin sa masa albarka suke.Ana cikin
wannan hali
ne wata rana kwatsam cikin
tsakiyar dare Samazan
da iyayensa na cikin dakuna suna
bacci sai sukaji
mutanen unguwar sun rude da
ihu.A firgice suka
farka daga bacci suka rugo waje
suna fitowa
sukaga ashe rumbunansu ne suka
kama da wuta
tuni ma sun gama konewa kurmus
babu kwayar
abinci guda daya da za'a mora.Koda
ganin wannan
al'amari sai mahaifiyar Samazan ta
fashe da
kuka,shi kuwa mahaifin nasa
durkushewa yayi a
kasa ya durfafi kasa da kansa
saboda tsananin
takaici,jarumi Samazan kuwa
jikinsa ne ya kama
karkarwa zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata
kone a lokacin da makwabtansu
keyi musu jajen
wannan masifa suna tattaunawa
ana mamakin
abinda ya haddasa wannan wuta
saboda ba'a san
yadda akayi ba ta tashi.Kawai sai
Samazan ya juya
da baya ya ruga da gudu izuwa
cikin dakinsa yayi
damarar yaki ya dauko makamansa
ya sake fitowa
da gudu ya ruga izuwa inda
dokinsa yake ya
kwanceshi ya hau yana shirin
sakarwa dokin
linzamin kenan sai yaga mahaifinsa
tsaye a
gabansa fuskarsa a murtuke ya
dubeshi yace ina
zaka je?Samazan yace yakai
abbana ka yi sani
cewa ba wani bane ya turo aka
kona mana
rumbunanmu ba face Hashmar ko
kuma dansa
Balwan.Na rantse da darajarka
yanzu zanje na
yakesu har cikin gidan nasu na
kashe su gaba
daya daga matansa har yayansa
koda kuwa bazan
dawo a raye ba.Koda jin wannan
batu sai Imsar ya
matso gaban Samazan ya zabga
masa mari mai
karfi.Samazan ya tsaya yana kallon
mahaifinsa
cikin mamaki domin ko tsawa
mahaifin nasa bai
taba yi masa ba tun da aka
haifeshiSamazan ya
tsaya yana kallon mahaifinsa cikin
mamaki.Take
alamar mamaki ya baiyana karara a
kan fuskar
Imsar bisa marin da yayiwa
Samazan ya zamana
cewa shi kansa yayi mamakin
yadda akayi ya
mareshi.Take idanunsa suka ciko da
kwallah ya
dubeshi yace yana da kyau ka iya
sarrafa zuciyarka
a duk lokacin data fusata domin
tsalle daya ke jefa
mutum cikin rijiya.Kaman tane
cewa duk abinda
kake takama dashi walau karfi ko
tsafi duk
Hashmar da dansa Balwan suna
dashi,bazaka iya
kawar dasu ba kuma baka da
cikakkiyar hujja akan
cewa sune suka zo suka kona mana
rumbunanmu,baya ga wannan
sarkin yawa yafi
sarkin karfi zasu iya sawa dakarun
sarki su
kamaka akan ka kai musu hari
kuma kasan cewa
sarki nasu ne zai iya yanke maka
hukuncin daurin
rai da rai a kurkuku,idan kuma
hakan ta sameka
bakin ciki ne zai zamo sanadin
ajalina.
Uhm Littafi yafa zo karshe.kamar
yadda nace 1-5 ne ya fito. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part B
ZAI ZAMO SANADIN AJALINA.KODA
YAZO NAN A
ZANCENSA SAI HAWAYE YA ZUBOWA
SAMAZAN
YACE YAKAI ABBANA YANZU KANA
NUFIN SHIKE
NAN SAIDAI NA CIGABA da zuba
ido,ina ganin
makiyanmu na dakusar
damu,tunda har takai azo
a kone abincinmu to tabbas wata
rana kuma mu
za'a kone.Dajin wannan batu sai
Imsar ya gyada
kai yace baza'ayi haka ba,abinda
nake so dakai
shine kayi shiri a yau dinnan ka
nausa cikin duniya
domin cika burinka.Koda jin
wannan batu sai
Samazan ya kamu da tsananin
mamaki yace yakai
Abbana ina dalilin da yasa ka sauya
shawara,shin
tafiyartawa ba zata haddasa maka
wani ciwon ba?
Sa'adda Imsar yaji wannan batu sai
yayi ajiyar
numfashi sannan ya dago kai ya
dubi Samazan
yace ai tuni makiya sun dade da
samini wannan
ciwo kuma babu mai cire mini
shi,ka sani cewa da
ciwon nan har abada gwara wanda
za'a rabu dashi
watarana.Abinda nake nufi shine
idan har na
hanaka tafiya neman daukar fansa
to dani da kai
da mahaifiyar taka duk a cikin
bakin ciki zamu
mutu amma idan ka tafi muna sa
ran cewa
watarana zaka cika mana
burinmu.Koda ba zaka
dawo ka same mu ba raye.Nasa
maka albarka da
cewa komai wuya komai tsanani
zaka sami nasara
ko dakuwa zaka kusan rasa
rayuwarka.Koda
Nazirat mahaifiyar Samazan taji
cewa Samazan
zaiyi wannan tafiya sai ta rugo da
gudu ta fada kan
kirjinsa ta rungume shi tana mai
fashewa da
kuka.Al'amarin daya karya
zuciyarsa kenan shima
ya kama kuka yace yake ummina
bai kamata ki
rinka zubar da hawayenki ba
saboda tunda kika
haifebi daga kuruciyata kawo
izuwa girmana bamu
taba rabuwa ba sai yanzu.Wannan
tafiya da zanyi
tana dauke da manyan burika
namu,yana daga
cikin burin na dawo da sarautar
sarkin mafarauta a
garin nan tunda yanzu ma gashi an
hana yin
farautar gaba daya kuma an hana
hako ma'adanan
kasa.Koda jin wannan batu sai
Nazirat ta janye
jikinta daga cikin na Samazan da
sauri ta dubeshi
cikin firgici tace ta yaya zaka dawo
da farauta gami
da hako ma'adanan kasa agarin
nan alhalin
masarauta ce ta hana?Sa'adda
Samazan yaji
wannan tambaya saiya goge
hawayen dake cikin
idanunsa yace yake ummina idan
har na cika
burina na samo arzikin dazan fita
nema nayi miki
alkawarin cewa saina dawo mana
da sarautarmu ta
gidan nan koda kuwa saita kaini da
sauya sarki
tunda sarki na yanzu azzalumi
ne,lallai saina sake
shi daga kan karagarsa na dora
kaninsa Ikmal
tunda kowa yasan cewa shi adali
ne.A gaban
dimbin jama'ar dake tare a kofar
gidan nasu
Samazan yayi wannan furuci a
lokacin da ake ta
kokarin kashe kudurinsa,jama'a
suka tarwatse don
gudu kada Samazan ya shafa musu
kashin kaji,Ita
kuwa Nazirat saita firgita ainun ta
dubi Imsar tace
yaya kana jinsa yanayin irin
wannan ganganci
amma ba zaka hana shi ba,Imsar
yace ai an wuce
lokacin da zan hanashi aiwatar da
duk abinda yayi
akan makiyanmu tunda sun kaimu
makura,ki gane
cewa wanda duk baya sonka to
baya son ka
rayu.Samazan jeka ka gama hado
kayanka yanzun
nan nake son muyi bakwana ka tafi
izuwa cika
burinka mahaifinsa yace.Koda jin
haka sai
Samazan ya sauko daga kan
dokinsa da sauri cikin
farin ciki ya ruga izuwa cikin gidan
ya dauko
jakarsa ta guzuri ya budeta ya zuba
yan
kayayyakin da yake bukata sannan
ya sake rugowa
waje.Ba tare da bata lokaci ba yayi
sallama da
iyayensa suna masu sa masa
albarka suna kuka
shima yanayi,da kyar Samazan ya
janye jikinsa
daga cikin nasu ya sake kama
dokinsa ya hau ya
zabureshi da gudu.Su kuwa suka
bishi da kallo
kawai,a lokacin da Nazirat ta dora
kanta a kan
kirjin Imsar duk su biyun suna
zubar da
hawaye.Idanunsu,zukatansu cike
da dimbin bakin
ciki da alhinin rabuwa da dansu
wanda basu da
tabbacin sake ganinsa a rayuwa
kafin su bar
duniya.
*Al'amarin Jarumi Samazan kuwa
maimakon ya
fice daga cikin birnin nasu na Hindu
sai ya wuce
kai tsaye izuwa gidan Attajari
Hashmar.Gidan
Attajiri Hashmar ya kasance katon
gida kuma
kawataccen gaske domin a gaba
daya birnin Na
Hindu a wannan lokaci banda gidan
sarkinsu
wanda ake kira Nagur Bin Hunzal
babu wani gida
kamarsa.Sama da dakaru dubu biyu
neke gidan
kuma kafin mutum ya isa falon
Hashmar na gidan
inda ake saukar baki saiya ratsa ta
cikin kofofi
tara.Tafiyar dakika dari shida.Ba
tare da shakkar
komai ba Jarumi Samazan ya
durfafo wannan gida
na attajiri Hashmar.Tun daga nesa
da dakarun
tsaro suka hango shi sai suka zare
makamai suka
taso masa,masu takubba da masu
masu suka sha
gabansa domin a zatonsu yazo ne
da nufin yaki,ko
gezau Samazan baiyi ba,yana isowa
daf da kofar
godan sai yaja linzamin dokinsa ya
tsaya
caki.Sannan ya dubi dakarun tsaron
yace banzo
nan ba domin na zubar da jinin
dayanku,nazo ne
domin nayi magana kawai da mai
gidanku kuje ku
shaida masa cewa gani nan ina
jiransa.Koda jin
wannan batu sai shugaban dakarun
ya mayar da
takobinsa cikin kufe sannan ya dubi
Samazan cikin
alamun girmamawa yace yakai
babban jarumi ina
mai shawartarka da kayi maganar
da kazo da ita a
cikin cikinka don nasan cewa
shugabana Hashmar
dashi da dansa Balwan ba zasu
saurareka ba
tunda ka sami irin muguwar
kiyayyar dake
tsakaninku.Ni kaina nayi mamakin
abinda yasa ka
kawo kanka nan.Kafin Shugaban
Dakarun ya gama
rufe bakinsa tuni Samazan ya tari
numfashinsa
yana mai daka masa tsawa yace
kaje ka isar da
sakona ko kuma na tarwatsaku da
karfin tsiya na
shigar da kaina har cikin fadar
shugaban
naku.Koda jin wannan batu sai
shugaban dakarun
ya juya da sauri ya ruga izuwa can
cikin gidan.Jim
kadan saiga shugaban dakarun tare
da Hashmar
da Balwan a cikin shirin yaki a
fusace sun fito da
sauri.Koda sukaga Samazan a tsaye
bisa dokinsa
fuskarsa cike da murmushi babu
™Abubakar Haleefah Physicist™
wata alamar damuwa sai
murmushi akan fuskar sai
suka cika da matukar mamaki.Koda
Samazan yaga
Hashmar da Balwan tsaye a
gabansa sai ya dubesu
a nutse yace yaku manyan abokan
gaba,kuyi sani
cewa nazo ne nan domin naja
kunnenku bisa abu
daya,yanzun nan zanbar garin nan
domin yin wata
muhimmiyar tafiya.Bansan ranar da
zan dawo ba
amma kada ku kuskura ku taba
iyayena domin duk
ranar dana dawo na iske wani abu
ya samesu na
rantse da darajarsu mutum daya a
cikin zuri'arku
kaf ba zai tsita da rayuwarsa
ba,rumbunanmu na
abinci da kuka tura aka kone ya
isheku.Kada a
sakeyi mana wani abun.Da wannan
furuci nakeyi
muku sallama sai sun sake
saduwa.Koda gama
fadin hakan sai Balwan ya fusata
ainun ya yunkura
zai zare takobinsa amma sai
Hashmar yayi sauri
ya rukeshi yana mai kyalkyala
dariyar mugunta
sannan ya dubi Samazan yace yakai
yaro idan
takamarka sa'a to nima ban taba sa
wani abu a
gabana ba ya gagareni.Kaje ka
shiga duniyar ka
yawata duk inda ka so,duk abinda
zaka samo kaje
ja samo shi muna nan madakata
muna
jiranka.Tsakaninmu dakai zamuga
wanda zaiga
bayan wani.Nayi ma alkawari daga
yau bama mu
ba wani ma bai isa ya iya cutar da
iyayenka ba
muddin ina numfashi a cikin garin
nan.Domin bani
da burin da yafi iyayenka suga irin
mummunan
karshen da zakayi.Fatana shine
bakin ciki da
takaicin lalacewar rayuwarka ya
zamo sanandin
ajalinka.Sa'adda Samazan yaji
wannan batu sai
shima ya kyalkyale da dariyar
mugunta sannan
yacr lokaci ne kadai zai warware
wannan gardama
dake tsakaninmu,yana gama fadin
hakan saiya
kada linzamin dokin ya juya da
baya ya zabureshi
da gudu.Cikin kankanin lokaci ya
bacewa su
Hashmar da gani sai kurarsa.A
sannan ne Balwan
ya ciza yatsa kuma ya dubi
Hashmar cikin alamun
tsananin takaici yace haba ya Abba
me yasa ka
hanani na yaki wannan babban
makiya namu
yanzu na kashe shi domin mu
cusawa ubansa
bakin cikin dazai kaishi
kushewarsa?Koda jin
wannan tambaya sai Hashmar yayi
murmushin
mugunta irin na manyan azzalumai
marasa imani
sannan ya dafa kafadar Balwan
yace kai yaro ne
'dana,ai shi kisan mummuke yafi
kisan farat daya
takaici,yana da kyau ka ganawa
makiyinka azaba
mai radadi kuma ka cusa masa
takaici da bakin
ciki mai radadin gaske kafin ya
gama dashi.Ta
haka ne kadai zaka zamo
gagarabadau kuma
babban dodo ga dukkan
makiyanka,muje zuwa
mahaukaci ya hau kura zamuga
wanda zai
gaji.Wannan shine asalin tarihin
rayuwar Jarumi
Samazan da kuma dalilin da yasa
ya baro kasarsu
ta Hindu ya shiga duniya.Bayan
Samazan ya
kammala aikinsa na hada kwale
kwale kuma yaci
abinci ya koshi a lokacin da dare ya
soma saiya
shigo cikin tantinsa ya kwanta
kamar yana bacci
abinsa a cikin gidansu na birnin
Hindu.Bai farka ba
saida gari ya waye hasken rana ya
doki
fuskarsa.Cikin hanzari Samazan ya
mike tsaye yaje
yayi wanka a bakin gabar wannan
rafi sannan yayi
kalaci ya shiga kimtsawa yana
diban kayansa yana
zubawa a cikin wannan kwale
kwale.Koda ya gama
shirinsa tsam saiya janyo kwale
kwale izuwa cikin
rafin ya shiga ciki ya zauna ya
kama tukashi ya
nufi cikin rafin kai tsaye,Ba tare da
shakkar komai
ba.Abinda ya daurewa Samazan kai
shine tunda ya
fara wannan tafiya a cikin wannan
rafi sai yaji
gurnanin dabbar dake karkashinsa
ta dauke dif
tamkar bai taba jinsa ba.Koda jin
haka sai shima
ya basar ya cigaba da tuka kwale
kwalensa cikin
kwanciyar hankali da nutsuwa ba
tare da fargabar
komai ba.Saida Samazan yayi tafiya
mai tsawo a
cikin rafin ya iso daidai tsakiyar
kwatsam sai
wannan kada ya faso tsakiyar
kwale kwalen da
kansa.Take kwale kwale ya dare
biyu Samazan yayi
sama a dimauce ya fado ruwan
tsundum ya lume
kasa.Take yayi arba da narkaken
kadan a
karkashin ruwa.Sa'adda ya waigo
gareshi kuma ya
durfofoshi.Koda Samazan yayi arba
da wannan
kada sai ya firgita ainun saboda bai
taba ganin
kada irinsa ba mai tsananin girma
da ban tsoro.A
karon farko Sai Samazan ta juya da
sauri cikin iyo
tamkar kifi da nufin ya gudu ai
kuwa sai kadan ya
kara karfin gudun nasa a karkashin
ruwan domin
ya cim masa.Koda Samazan ya
waigo bayansa
yaga saura kiris kadan ya cimmasa
kuma ya
ganewa bai isa yakai bakin gabar
kogon ba batare
da kadan ya cimmasa ba.Gashi a
wannan lokaci
ransa ya baci matuka bisa ganin
yadda wannan
kada ya tarwatsa masa kwale
kwalensa bayan
yasha wahalar sassakashi.Nan take
Samazan yaji
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar
zata kone don
haka sai yayi kundunbala ya juya
ya tari
kadan.Aikuwa sai kadan ya
wangame bakinsa da
nufin ya hadiyeshi.Wohoho!Karfi da
zafin nama
suna da rana domin ba don
Samazan yana da
tsananin zafin nama ba da bai isa
ya iya kaucewa
hadiyar da kadan ya kawo masa
ba.Kawai sai ya
kaucewa kadan ya hadiyi
iska,Kadan ya wurkila
jikinsa ya juyo da baya gareshi,tuni
Samazan ya
dunkule hannunsa na dama ya
gabzawa kadan
wannan naushi akan idon na hugu
da kukan
karfinsa.Nan take idon Kadan ya
gwallatse ya
tsiyaye.Kadan yayi wani irin mugun
ruri
sakamakon tsananin zafi da zogin
da yaji,ai kuwa
saiya makawa Samazan jelarsa a
gadon
bayansa.Take gadon bayan nasa ya
dare jini yayi
tsartuwa shima ya kurma uban ihu
a lokacin da
kadan ya sake daga katuwar jelar
tasa domin ya
maka masa,cikin bakin zafin nama
Samazan ya
zare takobinsa ya kare bugun da
kadan ya kawo
masa.Koda jelar kadan ta hadu da
takobinsa sai
tarwatsin wuta ya tashi,karfin
bugun jelar akan
takobin da nauyinsa ya rinjayi
Samazan ya juya
sau uku kamar katantanwa.Adaidai
wannan lokaci
ne Samazan yaji numfashinsa na
neman karewa
tunda a karkashin ruwa suke don
haka babu shiri
ya dago sama daga cikin ruwa.Ai
kumwa sai
shima kadan ya dago sama ya sake
wangame
bakinsa.
™Abubakar Haleefah Physicist™
Ya kawo masa hadiya,Samazan ya
goce ya daka
tsalle ya fada kan gadon bayan
kadan ya datse
bakin nasa da hannayensa biyu.Ai
kuwa sai kadan
ya kama wurkila jikinsa yana
katantanwa da
Samazan a cikin ruwa.Wani lokacin
ma sai yayi
nutso dashi kasa kuma ya taso
sama.Nan
Samazan yaji ya fara fita daga
haiyacinsa
sakamakon ruwan dake shiga
bakinsa da
hancinsa.Duk wannan bakin
gumurzu da sukeyi
Samazan bai yarda ya yarda
takobin hannunsa
ba.Domin duk sa'adda kadan ya
wurkila jelarsa ya
kawo masa duka da ita da takobin
yake karewa.Ba
don haka ba da tuni kadan ya
ragargaza jikin
nasa.Koda Samazan ya fuskanci
kanshi a mutuwa
da rayuwa a wannan gumurzu da
sukeyi sai yayi
sauri ya murza wani gurin tsafi
dake jikin
hannunsa na hagu take ya rikide ya
zama kifi suka
kasa tsere da kadan a karkashin
ruwan suka nufi
karshen rafin inda gabar take.Nanfa
kadan ya dage
iya karfinsa domin ya cimmasa
amma sai ya kasa
duk da cewar tazarar dake
tsakaninsu bata wuce
kamu uku haka ba,suka iso har
bakin gabar rafin
sai kifin yayi tsalle ya fito daga
cikin koramar
aikuwa shima kadan saiya dako
tsalle ya biyo shi
a saman.Kifin na sama ya rikide ya
zama Samazan
ya juyo da sauri yasa kafarsa ya
doki kan
kadan,saboda karfin dukan saida
kadan ya fado
kasa tim a kusa da gabar rafin
tamkar giwa ta
fadi,karfin buguwarsa da kasa gami
da nauyinsa ya
haifar da girgizar kasa,amma sai ya
shanye dukan
tamkar susa akayi masa kuma ya
fusata ainun ya
jefo doguwar jelar tasa ta
kanannade Samazan tun
daga kafafunsa har izuwa
kafadarsa ta matse
shi.Saboda tsananin zafin da
Samazan yaji kamar
gaba dayan kasusuwan jikinsa zasu
kakkarye bai
san sa'adda ya kurma uban ihu
ba,don haka sai
shima ya takarkare iya karfinsa ya
fara buda jelar
kadan,a hakne kaifin jelar ya fara
yankar jikinsa,jini
na zuba amma duk da haka saiya
nace kuma ya
daure ya cigaba da buda jelar har
ya samu ya zaro
hannunsa guda daya daga jelar
yayi wuf ya zaro
wata wuka a kugunsa ya cakawa
kadan akan daya
lafiyayyen idon nasa.Take shima
wannan idon ya
gwallatse kadan ya kurma uban
ruri wanda yafi na
farko kuma ya warware jelarsa
babu shiri daga jikin
Samazan kuma ya fusata ainun ya
rinka jefa jelar
izuwa gabas da yamma,kudu da
arewa,sama da
kasa yana kaiwa Samazan mugun
hare hare,bisa
dole Samazan ya rinka guje guje da
tsalle tsalee
yana kaucewa harin nasa.Tabbas in
badon kadan
ya makance ba da abune mayuwaci
a wannan
karon ya tsira daga sharrinsa.Ahaka
ne Samazan
ya samu da dan nisanta daga kusa
da kadan ya
fadi kasa sakamakon jirin dake
dibarsa da kuma
jinin dake zuba daga raunikan dake
jikinsa.Babu
raunin da yafi addabarsa sama da
wanda ke bisa
gadon bayansa domin mugun
radadi da zugi yake
masa tamkar ana zuba masa
barkono a cikinsa
kuma bai daina zubar da jini ba.Duk
sa'adda
Samazan ya shago bayan nasa da
hannunsa jini
yake gani tamkar a sannan akayi
masa wannan
rauni.Nan take hankalin Samazan
ya dugunzuma
ainun ya rasa abinda ke masa dadi
ya tambayi
kansa a cikin zuciyarsa yace,Ta yaya
zan dinke
wannan rauni dake bisa gadon
bayana?Tabbas
idan ban tsaida jinin ba nan da
zuwa wani lokaci
zan iya rasa rayuwata gaba
daya.Adaidai wannan
lokacin ne mugun kadan ya durfafo
inda Samazan
ke zaune kuma a lokacin ne
Samazan ya fara ganin
dishi dishi wato idanunsa suka fara
lumshewa.Ashe kdan yana amfani
ne da kamshin
bil'adama amma bada idanunsa ba
tunda ya
makance,kamar Samazan yasan da
hakan sai yayi
sauri ya dauke numfashinsa domin
a wannan
lokaci baisan abinda zai yi ba ya
kare kansa.Shidai
yasan cewa sara da suka basa tasiri
a ko ina a
jikin kadan,to wai shin wace dabara
zanyi amfani
da ita na sami nasarar kashe
wannan kada?
Lokacin da kadan ya iso daf da
Samazan saiya
daga kansa sama ya shinshina
gabas da
yamma,kudu da arewa,da yaji babu
sautin mutum
saiya wuce gaba a lokacin da
kafarsa ta hagu ta
gaba ta take hannun Samazan na
dama.Take
yatsun hannun nasa guda uku suka
karye Samazan
yayi sauri ya toshe bakinsa da daya
hannunsa
domin ji yayi kamar zai rusa ihu
sakamakon zafin
da yaji.Koda kadan yayi dan nisa
kadan ga barin
inda Samazan ke zaune sai
hankalin Samazan ya
sake dugunzuma fiye da ko yaushe
bisa ganin
yadda kadan ya fusata ya
wangame bakinsa yana
furzar da wani irin ruwa mai yawan
gaske.Koda
ruwan ya zuba akan bishiyoyi sai
suka kama
narkewa.Take Samazan ya aiyana a
ransa cewa
wannan cefa damarsa ta karshe da
zaiyi amfani da
ita ya kashe wannan kada amma
idan ya bari
kadan yaje ya dawo tofa ajalinsa ne
yazo.Inda
matsalar take shine ta yaya zai iya
kashe kadan?
Waishin inane lagon kadan ne? KIBIYA RATSA MAZA!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part C
WAISHIN INANE LAGON KADAN NE?
Koda Samazan
yayi wannan tambaya a cikin
zuciyarsa sai nan
take wata dabara ta fado masa
amma kuma bashi
da yakinin cewa dabar zata
fisheshi,saidai kuma
bashi da wani zabi wanda yafi
hakan.Gama aiyana
hakan keda wuya saiya waiga
bayansa yaga wata
yar karamar bishiya mai siraran
sassa,amma

Please Login or Register in order to submit comment