Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamata ace
jaruma kamar
Safirat ta mutu ba wacce tasha
wannan bakar
gwagwarmaya tayi bajintar da ba'a
taba samun
mahalukin da yayi taba a nahiyar
gaba
daya,sannan kuma suna matukar
bakin ciki bisa
ganin cewa duk wahalar da suka
sha a baya ta
raka Safirat izuwa cikin dazuzzukan
biyu da kuma
yan uwansu da suka rasa duk sun
zamo a banza
kenan.Dodannin na cikin wannan
tsananin bakin
ciki ne ma'abocin goyata a bayansa
ya lura da
yadda jikin Safirat ya hadu yayi
lugub har a sannan
tururin zafi bai daina fita ba daga
cikin kofofin
gashin jikinta.Koda ganin haka sai
yayi wuf ya
sureta ya azata a bayansa ya
runtuma da gudu
izuwa wani bangare daban na dajin
wanda shi
kansa bai san inda hanyar zata
kaishi ba.A
dimauce sauran yan uwan nasa
suka rufa masa
baya domin suga inda zai
kaita.Haka dai dodon ya
cigaba da gudu dauke da Safira
yana waige waige
da dube dube ko zai ga abinda
yake nema wanda
yake ganin cewar shine kadai zai
iya ceto rayuwar
Safirat.Duk da cewar wannan dodo
da sauran yan
uwan nasa suna matukar tsoron
wannan daji na
Sarkif sai gashi sunfi jin tsoron
mutuwar Safirat
akan dajin.Burinsu kawai shine su
ceto rayuwar
tata koda kuwa zasu rasa tasu
rayuwar.Saidai
wadannan dodanni suka shafe
sama da sa'a guda
suna guje guje a cikin wannan dajin
Sarkif suna
fadawa cikin tsaunuka suna jin
raunika a jikinsu
saboda komai na dajin daban yake
basa iya kare
jikinsu.Nan da nan suka jigata
ainun suka sha
bakar wahala.Duk wanda ya kalli
wadannan
dodanni a lokacin da suke cikin
wannan hali dole
ya tausaya musu kuma babu
abinda zai burge
mutum face yadda suka nuna
tsananin tausayinsu
da kaunarsu akan jaruma Safirat.Sai
bayan sun sha
wannan muguwar wahala ne
kwatsam suka hango
dusar kankara a gabansu a bakin
wani kogi.A guje
suka karasa wajen wannan dodo
dake goye da
Safirat ya sauketa daga kan gadon
bayansa ya
turbutsata a cikin dusar kankarar
ya binneta a ciki
yabar iya fuskarta a waje sannan
suka ja da baya
suka tsuguna suka tsurawa gangar
jikin Safirat
idanu suna jiran tsammani,ba don
komai ba kuwa
sai saboda sunsan cewa idan Safirat
ta shafe
kamar rabin sa'a a cikin Dusar
kankarar bata
farfado ba to ta mutu kenan ba
zata taba tashi
ba.Koda rabin sa'a ta shafe kuwa
sai zuciyoyinsu
suka karaya suka fashe da
matsanancin kuka kai
kace mutane ne su ba dodanni
ba.Cikin tsananin
bakin ciki suka mike tsaye tamkar
wadanda suka
tashi daga zaman makoki suka nufi
inda Safirat ke
kwance da nufin su cirota daga
cikin kankarar su
haka kabari su binneta.Da isarsu
gabanta
™Abubakar Haleefah Physicist™
wannan dodo ma'abocin goyonta
yakai hannu da
nufin ya zarota sai kawai yaga
idanunta sun bude
nan take ta yunkura ta taso zaune
daga cikin dusar
kankarar.Koda dodannin sukaga
haka sai suka
kaure da shewar farin ciki suka
kama tsalle
tsalle.Koda Safirat taga yadda
wadannan dodanni
ke murnar ganin ta rayu bata mutu
ba sai itama ta
kamu da tsananin farin ciki,nan
take ta mike tsaye
ta daka tsalle ta fada kan kirjin
wannan dodo
ma'abocin goyata suka rungume
juna kuma sai
suka fashe da kukan farin ciki.Saida
suka dan jima
a kankame da juna sannan dodon
ya ajiyeta kasa
tamkar ya ajiye yar tsana saboda
kankantarta akan
girmansa.Kawai sai Safirat ta
dubeshi cikin
murmushi tace waishin menene
sunanka ne?Koda
jin wannan tambaya sai mamaki ya
kama dodon
ya maida mata martani da
murmushi yace,ke kuwa
menene dalilin da yasa tuntuni baki
san suna ba
tun a farkon haduwarmu sai a yau?
Sa'adda Safirat
taji wannan tambaya sai ta sake
yin murmushi tace
saboda ayau ne na tabbatar da
cewa kai masoyina
ne na kwarai domin kuwa ban taba
haduwa da
mahalukin daya taba nuna mini
tsantar kauna ba
kamarka hatta masoyina sarki
Safwan kuwa.Domin
shi ya kasa hakuri da komai na
duniya a kaina.kai
kuwa gashi ka sallama rayuwarka
don ceton
tawa,kayi kuka ka zubar da hawaye
saboda ganina
a cikin mugun yanayi.Inda ace kai
mutum ne
kamarni da babu abinda zai hanani
aurenka face
mutuwa.Amma duk da haka zan
nemi alfarma daya
a wajenka inaso idan har na sami
nasarar dauko
kuttin kwarina zan fara karbar
karagar mulkin
Safwan na zama sarauniyar Birnin
Kisra.A sannan
ne nake son ka zama shugaban
dakaruna ma'ana
ka zama sarkin yakina amma lallai
ka koma can
mazauninku ka dauko matarka
idan kana da
ita.Idan kuma baka da mata to
lallai kayi sabon
aure.Koda Safirat tazo nan a
zancenta sai dodon
ya bushe da dariya yace suna nan
Gargus kuma
dama can nine mataimakon
shugabanmu
Bandaru,Ban taba aure ba amma
saboda na faranta
miki rai bayan kin cimma burinki
zan koma can
dajin tsaunin Lauhul Farras na auri
daya daga cikin
irin matayenmu.Ya shugabata ina
ganin zaifi kyau
mu nemi inda zamu kwana a cikin
wannan daji
tunda yanzu dare ya soma yi gashi
babu hasken
FARIN WATA.Kin sani cewa wannan
daji na Sarkif
yana da tsananin hadari kuma
babu wanda yasan
iyakar mugayen abubuwan dake
cikinsa.Koda
Gargus yazo nan a zancensa sai
Safirat tayi
murmushi tace na aminta da
wannan shawara taka
dari bisa dari.Nan take suka
dunguma gaba
dayansu suka kama neman inda
zasu kwanta su
huta kuma suyi bacci.Cikin sa'a
kuwa basu dade
ba suna nema suka sami wani
kogon dutse.Saida
suka shiga cikin kogon suka cajeshi
tsaf suka
tabbatar da cewar babu wani
mugun abu a
cikinsa.Sannan suka yiwa Safirat
shimfida ta
kishingida.A sannan ne Gargus ya
shiga duba ko
ina a jikin Safirat domin yaga yadda
raunikan
jikinta suke yayi mata
magani.Bayan ya gama
nazarin raunukan ne ya kwanto
jakar guzurinsa ya
ajiye a gabanta ya shiga yi mata
magani a lokacin
ne ta kura masa idanu ta shiga
zancen zuci.Ba
komai bane ya fado mata a rai face
tunowa da
cewar Gargus shine kadai namiji
daya taba jikinta
itama ta hada jikinta da nasa hatta
sarki Safwan
kuwa.Waishin yaushe ne zatayi
aure ta sami mijin
da zai iya sallama rayuwarsa domin
tata kuma ta
sami magaji tare dashi?Koda Safirat
tazo nan a
tunaninta sai hawaye ya zubo
mata,takaici ya
turnuketa ta sami irin wannan
masoyi.Haka dai
Safirat ta cigaba da wannan tunani
har Gargus ya
gama aikinsa bacci ya saceta bata
sani ba.Safirat
bata farka ba daga bacci saboda
tsananin gajiya
da jigata saida gari ya waye har
rana ta
kwalle.Tana farkawa taga tuni su
Gargus sun nemo
mata abin kalaci na yayan itatuwa
kuma ga wani
gasasshen tsuntsu a gefe daya a
gabanta.Al'amarin daya bata
mamaki kenan kuma
ya burgeta ainun.Ba tare da wani
bata lokaci ba sai
Safirat ta mike tsaye taje ta wanke
fuskarta da
bakinta da hannayenta sannan tazo
ta zauna ta
kama cin abincin a lokacin da su
Gargus suka
koma gefe daya suka zazzauna
kuma suka kau
dakai ga barin kallonta saboda
kawaici da
girmamawa.Al'amarin daya kara
bata mamaki
kenan bisa ganin yadda wadannan
dodanni sukeyin
abubuwa na hankali,tunani da
sanin ya kamata
tamkar sun kasance
bil'adama.Bayan Safirat ta
kammala lakacinta ne ta dubi
Gargus tace ina
bukatar naje nayi wanka.Koda jin
wannan batu sai
idanun Gargus suka zazzago ya
kamu da matukar
tsoro ya dubeta cikin alamun firgita
yace haba ya
shugabata shin kin manta ne da
irin tsananin
wuyar da kika sha a yayin da
mummunar macijiyar
nan ta hadiyeki?Shin bakya tunanin
cewa za'a iya
samun wadansu mugayen halittun
a cikin
karkashin kogunan dake cikin
wannan daji har da
kike tunanin kije jiyi wanka a
cikinsa?Sa'adda
Safirat taji wadannan tambayoyi
sai tayi murmushi
tace kada ka damu yakai
amintaccen sarkin yaki
na na nan gaba.Kayi sani cewa ina ji
a jikina
cewar tunda har na sami nasarar
shigowa cikin
dajin nan kuma har na kawo i
yanzu a raye to
akwai alamun tabbacin samun
nasara sai burina ya
cika.Zo muje kayi mini rakiya izuwa
bakin kogin da
zanyi wanka.Koda gama fadin haka
sai Safirat ta
fice daga cikin wannan kogon
dutse tana rataye da
bakanta.Cikin hanzari Gargus ya
take mata baya
har saida suka iso bakin wata
katuwar korama!!! KIBIYA RATSA MAZA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part D
Har saida suka iso bakin wata
katuwar
Korama.Kawai sai Gargus yaga
Safirat ta yunkura
zata cire tufafin jikinta sannan ta
shiga cikin
koramar.Cikin hanzari Gargus ya
dakatar da ita
yace haba ya shugabata ai komai
saurinki dai kya
bari na fara tabbatar da lafiyar cikin
koramar
tukunna.Ki kula da kanki kafin na
fito daga cikin
karkashin wannan korama.Yana
gama fadin hakan
sai ya fada cikin wannan koramar
yayi nutsu izuwa
karkashinta.Saida ya kure nisan
koramar gabas da
yamma kudu da arewa ya tabbatar
da cewa babu
wani halitta mai numfashi a
karkashin wannan
korama sannan ya fito a jike
sharkaf yana yarfe
ruwan dake jikinsa sannan ya dubi
Safirat yace ya
shugabata babu komai a cikin
wannan korama zaki
iya shiga kiyi wankanki.Tana gama
cire kayan
jikinta ta fada cikin koramar ta fara
wankanta cikin
kwanciyar hankali da nutsuwa
tamkar a cikin
gidansu na birnin Kisra take.A
lokacin da Safirat ta
fara wannan wanke hankalin
Gargus yakai kan
wannan baka wacce ke lullube cikin
mayafi,kawai
saiya kurawa bakan idanu yace a
cikin ransa.Oh!
Yanzu akan wannan abin ne
hankalin kowa a
duniya ya tashi,mu kanmu da mu
kayi gadin
wannan baka tun daga lokacin da
Boka Saiham ya
kawota kan Tsaunin Lauhul Farras
dayanmu bai
taba taba ta ba.Ai kuwa kamata
yayi na tabata ko
don na barwa kaina tarihi.Tunda
dai shekaruna sun
kai talatin da bakwai ko Safirat
taga ina tabata ba
zata zargeni bisa komai ba tunda
tasan cewa ban
isa na sarrafata ba.Gama fadar haka
keda wuya sai
dodo Gargus yaje gaban bakan ya
yaye mayafin da
aka lullubeta.Faruwar hakan keda
wuya sai hasken
bakan ya dallare wajen gaba daya
kuma yayi tsiri
yana mai nuni izuwa wata
hanya.Baiyanar hasken
ne ya janyo hankalin Safirat wacce
ke a cikin
korama ta juyo da sauri izuwa inda
Gargus
yake.Koda taga bakanta a
hannunsa kuma hasken
jikin bakan yayi nuni izuwa wani
waje,sai tayi sauri
ta fito daga cikin koramar ta sanya
kayanta ta karbi
bakan daga hannun Gargus sannan
ta zare
takobinta ta nufi inda hasken
bakan keyi mata
nuni.Cikin hanzari Gargus da sauran
dodanni yan
uwansa suka bita a baya suna
mamakin yadda
bakan yake yiwa Safirat
jagora.Nanfa suka rinka
shiga cikin sakuna na duwatsu da
tsaunuka masu
tsananin tsawo da duhu.In badon
ma hasken jikin
bakan ba da ba zasu iya bin hanyar
ba.Duk inda
suka shiga sai suga miliyoyin
dakarun yaki masu
tsananin kwarjini da ban tsoro na
aljanu da
dodanni masu wata irin siffar da
kansu su Gargus
basu taba sanin cewa akwai irinsu
a doron kasa
ba.Komai jarumtakar mutum idan
yayi arba da
wadannan miliyoyin dakaru dole
ne ya firgita kuma
yasan cewa komai hatsabibancinsa
bai isa ya
ratsasu ya wuce ba amma sai gashi
Jaruma Safirat
dasu Gargus na ratsawa a
tsakiyarsu.Dakarun na
gudu suna buya.Ba komai bane
yake tarwatsa
dakarun ba face wannan haske na
jikin bakan
Safirat domin konasu yakeyi suna
narkewa su
zama ruwa.Haka dai Safirat dasu
Gargus suka
cigaba da kutsawa a cikin wani
makeken kogon
dutse wanda girmansa yakai na
birnin Kisra gaba
dayansa.Duk inda mutum ya duba
a cikin kogon
babu abinda zai gani face
kwarangwal na kawunan
bil'adama da kafafuwansu da
hannayensu,sai kuma
beraye suna ta guje guje suna shige
da fice a cikin
ramuka alamar cewa sune suka
cinye naman
mutanen da suka rube a cikin
kogon.Koda Safirat
ta dubi Gabas da yamma kudu da
arewa na cikin
kogon wanda kamar bashi da
karshe kuma taga ko
ina kwarangwal ne tsubi tsubi har
suna tsiri sama
sai tayi ajiyar zuciya ta jiyo ta dubi
Gargus
tace,tabbas nan ne KOGON
MUTUWA,Tana gama
fadin hakan sai ta cigaba da bin
hanyar da hasken
bakanta keyi mata nuni tana bi ta
kan kwarangwal
tana takasu suna ruburbushewa.Su
ma su Gargus
suka cigaba da binta a baya suna
tunkarar can
saman kwarangwal tamkar suna
hawan saman
tsauni.Suna isa karshen tudun
kwarangwalolin ne
sukayi arba da wani dogon teburi
wanda akayi da
zallan shudin lu'u lu'u.A kasan sane
suka ga an
ajiye MAKAMAN YAKI iri iri wadanda
gaba dayansu
anyi su ne da karafa kala kala kuma
kana ganinsu
kasan cewa SIHIRTATTUN MAKAMAI
ne.A tsakiyar
wadannan makamai ne aka dora
wani dogon tebur
na zinare,akan teburin kuma aka
aza kuttun KWARI
na Bakan Safirat alamar cewa an
fifitashi akan
gaba dayan wadannan makaman
yaki.Shi kansa
wannan kuttun kwari wani irin
sheki da walwali
yakeyi yana kashe idanu.Koda
Safirat tayi arba da
wannan kuttun kwarin sai farin ciki
ya lullubeta
domin tasan cewa KARSHEN
WAHALArta yazo.Cikin
sauri ta tunkari inda aka ajiye
kuttun kwarin domin
ta dauka.Koda ya rage saura baifi
taku goma ba
kacal tsakaninta da kuttun kwarin
sai kawai taga
sarki Safwan ya baiyana tsulum a
gabanta tamkar
daga sama aka jehoshi.Fuskarsa a
murtuke tana
gatsinewa tamkar naman fuskar zai
zazzago kasa
saboda tsananin fushi.Hannunsa na
dama na rike
da wata azabgegiyar
takobi,hannun hagu kuma na
ruke da garkuwa.Kawai sai ya dubi
Safirat ya daka
mata tsawa yace yake babbar
abokiyar gabata kiyi
sani cewa a can dajin tsaunin
Lauhul Farras munyi
RAGAS,har kika sami damar
guduwa bayan kin
dauki bakanki.To ki sani cewa anan
kogon mutuwa
dole ne dayanmu ya sami nasarar
kashe daya.Idan
nine na samu nasarar kasheki na
rantse da kabarin
ubana saina wulakanta MATAN
DUNIYA fiye da
yadda kika yi niyar wulakanta
maza saina sa mata
sun rinka kashe kansu saboda
bakin cikin da zan
rinka cusa musu wanda zasu
gwammace
mutuwarsu fiye da rayuwarsu.Idan
kuma kece kika
sami nasarar halaka ni saiki aiwatar
da abinda
kikayi niyya akan MAZAJEN
DUNIYA.Koda jin
wannan batu sai su Gargus suka
taso da gudu da
nufin su afkawa sarki Safwan
™Abubakar Haleefah Physicist™
amma sai ya nunasu da
garkuwarsa take suka
kame a inda suke suka zama
gumaka!Koda ganin
haka sai Safirat ta fusata ainun ta
kurma uban ihu
kuma ta ruga izuwa kan sarki
Safwan suka
ruguntsume da masifaffen,azab
abben yaki mai
tsananin ban tsoro da ban al'ajabi.
WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN
YAKI
TSAKANIN JARUMA SAFIRAT DA
SARKI SAFWAN
HAR YA MALLAKI KWARI DA BAKAN
YA CIMMA
BURINSA?
SHIN SU DODO GARGUS SUN
HALLAKA KENAN KO
KUWA ZASU RAYU?
INA LABARIN SAURAN
SARAKUNA,MATSAFA DA
JARUMAN DAKE FARAUTAR WANNAN
KWARI DA
BAKA NA SAFIRAT?
SHIN SUMA SUNA NAN BIYE DA
SAFIRA A CIKIN
DAJIN MUTUWA?
YAUSHE NE SAFIRAT ZATA CIKA
BURINTA NA
MAISHE DA MAZA BAYIN MATA A
DUNIYA?
Mu Hadu A "KIBIYA RATSA MAZA
Littafi Na Uku
Don Jin Cigaban Wannan
Kasaitaccen Kayataccen
Labari.
Don't Just Read And Pass,Liking And
Commenting Necessary.
End Of Book 2.Sai Mun Hadu A Book
3 Insha Allah.
°KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Uku (3)
via nasir shehu teerlow
Part A
LOKACIN DA AKA RUNGUNTSUME
DA AZABABBEN
YAKI mai matukar ban tsoro da
ban al'ajabi
tsakanin jaruma Safirat da sarki
Safwan sai gaba
dayan dajin na kogon mutuwa
ya kama
girgiza.Kasa ta rinka tsagewa
bishiyoyi suka rinka
kakkaryewa suna zubewa
kasa,duwatsu kuwa suka
rinka mirginawa suna
murkushe yan uwansu da
sauran bishiyoyi.Duk wani abu
mai rai dake cikin
wannan daji na sarkif saida ya
dimauce ya fita
daga haiyacinsa a wannan rana
amma su manyan
giwayen biyu wato jaruma
Safirat da sarki Safwan
ko kadan basu damu da halin da
dajin ke ciki
ba,kowannensu idanunsa sun
rufe bai ma san
yanayin da dajin ke ciki ba
kawai kokari yake yaga
ya kashe abokin fadansa domin
ya kare
martabarsa kuma ya cika
burinsa.Bisa wannan
dalili ne suka rinka kaiwa
junansu sara da suka
cikin bakin zafin nama kuma da
dukkan
karfinsu.Duk wanda yaga yadda
wadannan abokan
gaba ke kawai junansu
mugayen hare hare dole ne
ya firgita saboda kuskure
kankani gaba dayansu na
nufin Ajalinsa.Saida Safirat da
Safwan suka shafe
sa'a daya da dakika dari bakwai
da sittin suna
fafatawa wannan masifaffen
yaki ba tare da
dayansu ya sami nasarar lakutar
jikin daya
ba.Wani lokacin sai kaga faduwa
suke kasa amma
sai suyi wuf su sake mikewa su
cigaba da
gumurzu,a hakane suka jigata
ainun babu shiri
suka ja da baya sukayi cirko
cirko suna kallon juna
suna haki a wannan lokaci ne
kowannensu ya
tabbatar da cewa lallai karfin
damtsensu,iya
yakinsu da karfin sihirinsu yazo
daya,don haka sai
kowannensu ya fara tunanin
hanyar da zaibi ya
sami nasarar kashe abokin
fadan nasa.Bayan sunyi
kallon kallo gami da tunani da
nazari na tsawon
yan dakiku sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna
a lokaci guda tamkar hadin baki
suka kacame da
yakin suka hada da kaiwa
junansu naushi da
bugu,faruwar hakan keda wuya
labari yasha
bambam domin a sannan ne
kowannensu ya fara
samun nasarar cutar da abokin
gwaminsa.Da zarar
Safwan ya sami nasarar
gabzawa Safirat Naushi a
fuskarta ta furzar da jini daga
cikin bakinta,kafin ya
sake kara mata wani naushi ko
yakai mata sara sai
kaga tuni itama ta rama naushin
da yayi mata jini
na feshi daga bakinsa.A hakane
kowannensu ya
sami nasarar yankar dan
uwansa har sau bakwai
bakwai.Sai gashi jini na zuba a
sassan jikinsu,jiri
na dibarsu,suna maye daga
tsaye tamkar sun sha
giya sun bugu,duk wanda ya
dubesu a wannan
lokaci dole ne ya tausaya musu
domin gani zaiyi
kamar gawace taki rami domin
a koyaushe zasu
iya rasa rayukansu.Har izuwa
wannan lokaci dodo
Gargus da sauran yan'uwans
dodanni a kame suke
cikin matsayin gumaka dayansu
bai kara motsawa
ba.Ana cikin wannan bakin
yamutsi ne Safwan ya
Shammaci Safirat ya gabza mata
wawan naushi a
ciki take ta sunkoyo da kanta
kas a lokacin da taji
cikinta yayi muguwar
kullewa.Safwan yasa kafarsa
ya doki habarta saboda karfin
dukan saida tayi
tsalle sama ta fado kasa tim ta
baje kasa
magashiyan a cikin wani irin
mugun yanayi mai
kama da suma.Koda Safwan
yaga ya sami wannan
nasara sai ya sake dako tsalle a
sama ya dira a
gabanta yana mai raba
kafafunsa kuma ya dubeta
cikin murmushi irin na mugunta
da farincikin
samun nasara.Kawai saiya daga
takobinsa sama
da hannayensa biyu da nufin ya
caka mata
takobinsa a cikinta.Ba zato ba
tsammani sai kawai
yaji Safirat ta doki fuskarsa da
tafin kafarta ta dama
da dukkan karfinta,saboda
karfin dukan saida
shima yayi sama bayansa ya je
ya gwaru da wani
dutse kuma ya fado kasa bisa
fuskarsa.Take fuskar
tasa ta daddauje tayi face face
da jini,da kyar ya
mirgina gefe daya yana
numfashi sama sama kuma
ya kasa yunkurin mikewa domin
ji yayi kamar
kasusuwan bayan nasa sun
kakkarye sakamakon
muguwar buguwar da yayi da
dutsen.Cikin
tsananin juriya Safirat ta
yunkura ta mike tsaye taje
har izuwa kan sarki Safwan tasa
hannunta ta lakuci
jini dake kan fuskarsa taje ta
shafa a jikin Gargus
wanda ya kasance
gunki.Faruwar hakan keda
wuya
sai Gargus ya dawo cikin
ruhinsa ya juya da sauri
ya rinka shafar yan uwansa
suma sai ruhinsa ya
dawo.Koda Gargus ya gama
shafar dukkanin yan
uwansa sai ya ruga da gudu
izuwa inda sarki
Safwan yake kwance da nufin ya
karasa kashe
shi,amma sai Safirat ta daka
masa tsawa ya tsaya
cak kuma ya juyo ya dubeta
cikin mamaki yace
haba ya shugabata ya zaki
hanani kashe wannan
babban makiyi naki?Ki dubi irin
mugayen raunikan
da yayi miki kuma ki tuna cewa
barinsa a raye
hadari ne babba domin a
koyaushe karfin jikinsa
zai iya dawowa ya cutar
damu.Maimakon Safirat
tace wani abu sai ta taka
kafafunta da kyau ta nufi
inda kuttun kibiyoyin yake tana
tangadi kamar zata
fadi.Tana isa wajen sai ta dauki
kuttun ta ratayashi
a bayanta.Faruwar hakan a bayanta.Faruwar hakan keda
wuya sai wani irin
haske mai karfin gaske ya
haskake kogon gaba
daya yadda ko allura ce ta fadi
kasa sai idanu sun
gani kuma nan take Safirat taga
duk raunikan
jikinta sun dinke kansu sun
daina zubar da
jini,wasu ma sun zama sai tabo
tamkar tafi wata
uku da samunsu.Safirat
taji
wani irin gagarumin
karfi ya shiga jikinta irin wanda
bata taba jinsa ba
a rayuwarta domin ji tayi kamar
ko duniyar gaba
daya aka aza mata a ka zata iya
dakonta.Kawai sai
ta daka tsalle sama sai gani tayi
tayi sama sosai
tamkar fikafikai ne a jikinta har
tana wani irin
shawagi a saman kogon cikin
matsanancin karfin
gudu tamkar tauraruwa mai
wutsiya domin a cikin
dakika biyu ta kewaye kogon
gaba daya sau goma
sha biyu.Hatta sarki Safwan bai
san sa'adda ya
wangame baki ba yana kallonta
a saman cikin
tsananin al'ajabi duk da cewar
yana cikin mugun
yanayi,kawai sai yaga Safirat ta
dira a
gabansa,karfins
a saukarta ya
haddasa
™Abubakar Haleefah Physicist™
karamar girgizar kasa tamkar
giwace ta diro.Safirat
ta dubi Safwan cikin murmushi
zuciyarta cike da
dumbin farinciki tace na cika
burina na mallakan
KWARI DA BAKAn mahaifina,ka
daina tunanin cewa
kasheka zanyi,ina amfanin
rayuwa idan babu
abokin gaba?Ta yaya zan iya
cusa maka bakin ciki
idan baka raye?Koda gama fadin
hakan sai tayi
nuni da hannunta izuwa kan
sarki Safwan take
wata murtukekiyar sarkar tsafi
ta daure hannayensa
da kafafunsa.Safwa
n yayi iya
kokarinsa ya kwance
kansa da karfin nasa na sihiri
amma saiya
kasa.Koda ganin haka sai Safirat
ta bushe da
dariyar mugunta tace ai yanzu a
duk fadin duniya
babu wani sihirin tsafi daya kai
nawa babu wani
jarumi da zai kaini
jarumtaka.Babu wani aljani da
zai fini karfin gudu ko sauri
daga yau duniyar nan
kaf zata zamo tamkar kwayar
hatsi a kan tafin
hannuna sai yadda naso zanyi
da mutane da
aljanu,kai sarki Safwan yanzu
zansa ayi maka
magani domin ka warke sosai
sannan na sanyaka
a cikin keji tamkar dabbar dawa
na tafi dakai izuwa
birnin Kisra a wulakance domin
ya zamo izina ga
kowa.Zan haye karagar
mulkinka na sauke
dukkanin fadawanka na sanya
mata madadinsu,zan
kafa sababbin dokoki ga
ma'aurata yadda maza su
zamo bayin mata,sauran
sarakuna,jaruma
i da
matsafa kuwa wadanda suka
biyo mu izuwa cikin
wannan daji domin su rabani da
wannan kwari da
baka nawa zakaga yadda zanyi
dasu.Koda gama
fadin hakan sai Safirat ta dubi
Gargus tace dashi
maza a yiwa sarki Safwan
magani.Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya baibaye
Gargus da sauran yan
uwansa dodanni suka rude da
shewar gurnani irin
tasu ta dodanni cikin matukar
farin ciki suna yiwa
Safirat jinjina suna cewa tabbas
kin cika burinki
kin zama SARAUNIYAR DUNIYA!!!
Ba tare da bata
wani lokaci ba Gargus yaje ya
dinke raunikan jikin
sarki Safwan yasa masa magani
a lokacin da sarki
Safwan ya kamu da mugun
bakin ciki hawayen
takaici suka zubo masa a lokacin
da zuciyarsa ta
kama tafarfasa kamar zata
kone,aikuwa Gargus na
gama yi masa magani sai yayi
amfani da sarkar
dake hannunsa ya shake kansa
da kansa domin ya
mutu ya huta da bakin ciki.Koda
ganin haka sai
Safirat ta sake nunashi da
hannunta na hafu take
ya saki wuyan nasa wato ya
daina shake kansa a
lokacin dayaji an zare gaba
dayan lakar jikinsa
hannayensa sukayi kasa sharaf
yaji ko dagasu
bazai iya karawa ba bare ya
sake yunkurin kashe
kansa.Take Safirat ta sake yin
tsafi saiga sarki
Safwan a cikin wani keji bisa
keken doki,Gargus da
sauran yan uwansa dodanni
basu san sa'adda
suka bushe da dariya ba,bisa
ganin yadda sarki
Guda mai daraja kamar Safwan
ya zamo tamkar
dabbar daji.(Hmm Gaskiya
Safeerat taci mutuñcin
Safwañ).Safirat
ta dubi Gargus
cikin murmushi
tace kamar yadda nayi alkawari
daga yau ka zama
shugaban dakaruna na
yaki,wadannan sauran yan
uwanka kuwa wadanda muka
sha bakar wahala
tare da sun zama
mataimakanka,ya
nzu zamu fita
daga cikin wannan daji muje
mu fuskanci dubunan
jama'ar dake jiranmu a
wajensa.Kada dayanku yayi
yunkurin yakarsu ba zamu yake
su ba da kansu
zasu gudu su barmu kuma
akwai sakon da nake
son na basu.Koda gama fadin
hakan sai Safirat ta
hau keken dokin da kejin sarki
Safwan ke kai ta
sakarwa dokin linzami sukayi
gaba.Cikin hanzari
su Gargus suka take mata baya
a guje shi kuwa
sarki Safwan dake cikin keji a
wulakance babu
abinda ya iyayi face cigaba da
zubar da hawayen
takaici.Kafin su nufi wajen
wannan daji na sarkif
Safirat ta goya kwari da bakanta
a bayanta kuma ta
lullube su da wannan bakin
mayafin har saida ta
fara hango DANDAZOn masu
farautarta sannan ta
yaye mayafin data lullube kwari
da bakan ta ajiye
shi a kusa da ita.Koda sauran
sarakuna,matsaf
a da
manyan jaruman duniya suka
hango jaruma Safirat
daga can nesa ga hasken kwari
da bakanta na
dallare musu idanu sai
hankalinsu ya dugunzuma
kuma tsoro ya baibayesu,sarki n
Misra ya dubi
sauran sarakunan yana mai rike
kansa da
hannayensa biyu yace shikenan
ta faru ta kare
Safirat ta sami nasarar hada
kwari da bakanta
gwara ma kuzu mu gudu tun
kafin ta karaso nan
domin mu tsira da
rayukanmu.Gama fadin hakan
keda wuya sai sarkin Misra ya
yunkura da nufin ya
kada linzamin dokinsa amma sai
bokan birnin
Yemen yayi sauri ya riko
dokinnasa yace yakai
wannan sarki menene amfanin
gudun da babu
tsira,to ka sani cewa koda ka
tserewa Safirat a
yanzu to nan gaba zata riskeka
har birninka ta
sauke ka daga kan karagarka ta
wulakantaka ta
maisheka bawa,shin ka zabi ka
zama hakan ko
kuwa zaka tsaya yanzu mu hada
kai mu kwatarwa
kanmu yancinmu?Koda jin
wannan tambayoyi sai
jikin sarkin Misra yayi sanyi ya
fasa guduwa suka
cigaba da zuba idanu suna jiran
isowar
Safirat.Koda Safirat ta matso
kusa kowa yaga sarki
Safwan daure a cikin keji kuma
da Safirat rataye da
kwari da bakanta a bayanta sai
aka dada firgicewa
aka tsorata da al'amarin Safirat
ainun.Koda ya rage
baifi taku bakwai ba tazarar
dake tsakanin Su
Safirat da wadannan
sarakuna,jaruma
n da matsafa
masu farautarta sai taja linzamin
dawakan keken
dokin.Take dawakan suka yi
turjiya suka tayar da
kura aka tsaya ana kallon kallo
tsakanin Safirat
dasu har izuwa yan dakiku.Daga
can sai Safirat ta
dube su cikin nutsuwa tace
yaku wadannan
sarakai,matsafa
da manyan
jarumai kuyi sani cewa
zakaran da Allah ya nufa da cara
tofa ko ana
muzuru ana shaho sai yayi
abinda kuke ta
farautarsa kukeson ku rigani
mallakarsa gashi na
riga ku mallakar abina,idan a
cikinku nan akwai
wanda yake ganin cewa zai iya
yakata a yanzu
domin ya rabani da kwari da
bakana to ya
jarraba,amma fa ya sani cewa
HUKUNCINsa KISA
ne.Idan kuma babu wanda zai
jarraba yakata a
cikinku to ina da shawara gami
da sako a gareku
gaba daya.Shawarata itace
™Abubakar Haleefah Physicist™
dukkanin sarakunan cikinku da
zarar sun koma
gida suyi murabus su baiwa
matayensu
karagarsu,daga sannan kuma su
zamo sune masu
yin aikin gida kamar yadda mata
keyi kuma ko a
kan shimfidar ne duk namijin
daya zamo bisa
matarsa hukuncin kisa ya
tabbata a kansa.Kafin
Safirat ta gama rufe bakinta tuni
sarkin kasar
Yamen ya tari numfashinta yana
mai daka mata
tsawa yace ke yarinya karyarki
tasha karya,na
rantse da darajar iyayena da
kakannina baki isa ki
sauya yanayin da duniya ke ciki
ba tunfarkon
wanzuwarta kawo iyanzu,ina
mai tabbatar miki da
cewa dole ne maza su zamo
gaba da mata don
haka ko a yanzu kin sami
nasarar aiwatar da
nufinki da karfin wannan kwari
da baka na
mahaifinki,ina mai tabbatar miki
da cewa nan gaba
sai an sami jarumin da zai
dakatar dake koma ya
kawar dake gaba daya.A yanzu
da ranmu da
lafiyarmu ba zamu zuba ido ba
muna ji muna gami
ki zubar mana da kimarmu da
mutuncinmu
ba,gama fadin hakan keda wuya
sai sarkin Yemen
ya umarci dakarunsa na yaki
dasu afkawa Safirat
su kasheta su dauko masa
kwari da bakan
nata.Kafin Sarkin Yemein ya
gama rufe bakinsa
tuni dakarun nasa kimanin su
dubu uku sun zare
takubba sun sakarawa
dawakansu kaimi suna
masu kwarara ihu gami da
kururuwa sukayi kan
jaruma Safirat,ita kuwa saita
zaro kibiya guda daya
jal daga cikin kuttun kibiyoyin
nata ta dana shi a
kan bakan ta jashi ta tabe
sannan ta saki
harbi.Take kibiyar ta fita daga
cikin bakan a wani
irin azababben gudu da
karfi.Kafin daya daga cikin
dakarun su dubu uku ya riski
Safirat a inda take
tsaye tuni kibiyar ta fasa
kirazansu su duka sun
zubo kasa daga kan dawakansu
matattu.Wannan
abu ya faru ne a cikin abinda bai
wuce dakika
biyar ba kuma nan take kibiyar
ta dawo da kanta
izuwa jikin bakan Safirat ta sake
dana kanta.Koda
sauran sarakuna,matsaf
a da
jarumai sukaga abinda
ya faru sai dukkaninsu suka
firgice basu san
sa'adda suka zube kasa ba daga
kan dawakansu
suna masu yin mubaya'a shi
kuwa sarkin Yemen
tuba ya kamayi bisa kuskuren
da yayi na tura mata
dakarunsa su kasheta.Shi kuwa
Sarkin Misra saiya
mike tsaye ya matsa kusa da
Safirat ya risina cikin
girmamawa sannan yace yake
wannan JARUMAR
JARUMAI ki tuna cewa
mahaifinki 'da namiji ne
don haka bai kamata ki
wulakanta maza ba,ina mai
rokonki daki janye nufinki na
mayar da maza bayin
mata.Koda kuwa zaki raba mu
da matsayinmu na
mulki.Koda sarkin Misra yazo
nan a zancensa sai
Safirat ta bushe da dariya
sannan tace tabbas ina
girmama mahaifina amma ka
sani cewa sarki dan
uwanka ne ya zama sanadin
mutuwar ubana,kuma
shine namiji na farko wanda na
baiwa zuciyata
amana,amma sai gashi yaci
amanar tawa yayi mini
butulci kamar yadda ubansa ya
yiwa ubana
butulci,bisa wannan dalili ne
nayi rantsuwa akan
cewa saina dauki fansa akan
mazajen
duniya,rantsuwa
bata tashi
face na cikata don haka
babu wata alfarma da zan iyayi
muku akan wannan
al'amari.Kuje ku isar da sakon
dana gaya muku ga
sauran yan uwanku sarakunan
duniya,idan kuma
har yanzu akwai wanda yake
ganin zai sake jarraba
sa'arsa akaina toga fili ga mai
doki.Koda jin haka
sai gaba dayan jama'ar suka
sake zubewa kasa
suna masu nuna
mubaya'arsu.Saf
irat na ganin
haka sai ta bushe da dariya ta
sakarwa dokinta
linzami tayi gaba su Gargus na
take mata baya har
saida suka kule a cikin dajin
sannan kowa ya
kama hanya don tafiya garinsa
cikin tsananin bakin
ciki da sanyin jiki.Lokacin dasu
Jaruma Safirat
suka iso wata mararrabar hanya
sai suka tsaya
Safirat ta dubi Gargus tace
yanzu ka tafi izuwa can
inda jama'arku suke ka auro
mace da zamu tafi da
ita izuwa can birnin Kisra inda
zamu ci gaba da
rayuwa.Koda jin wannan batu
sai farin ciki ya kama
Gargus ya zube kasa yayi godiya
sannan yace ya
shugabata kafin naje na dawo
nan zai iya daukata
kwana uku Shin zaku ci gaba da
jirana ne a nan
ko kuwa zaku wuce izuwa can
birnin Kisra na
riske ku a can?Koda jin haka sai
Safirat tayi
murmushi tace matsayinka a
wajena ya wuce na
tafi na barka dole ne na jiraka
idan ma kana so
zan iya raka can din.Gargus yace
ai ke yanzu kin
zama sarauniyar duniya don
haka idan kikayi gaba
baza zakiyi baya ba,na yarda
zaku iya yada
sansani anan din kuma zan
gaggauta tafiya can
wajen jama'ar tamu na auro
mata,na barki lafiya
sarauniyar duniya.Koda gama
fadin hakan sai
Gargus ya yiwa Safirat sallama
ya juya da sauri ya
falfala da azababben gudu
izuwa cikin daji.Kafin
kiftawar ido ya kule.Nan take
Safirat ta dubi sauran
dodanni ta basu umarnin a kafa
tanti.
Liking an °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Uku (3)
Part B
TA BADA UMARNIN A KAFA
TANTI.Nan take
kuwa
aka kafa mata tanti akayi mata
shimfida a ciki
tayi
kwanciyarta ta kama bacci ba tare
da fargabar
komai ba a lokacin da dodannin
suka kewaye
tantin don tabbatar da tsaro.
*Al'amarin sarki Safwan kuwa a
cikin wannan keji
aka barshi a kulle kuma a
daure,dare yayi ko
ruwa
ba'a bashi yasha ba saida Safirat ta
farka daga
dogon baccin data sha bayan
ankawo mata
abinci
da abin sha tayi hani'an sannan ta
tuno da batun
sarki Safwan.Nan take Safirat ta
dauki Ayaba
guda
ta tafi izuwa wajen tantin ta isa
inda sarki
Safwan
yake,da isarta bakin kejin da sarki
Safwan ke ciki
ta ganshi a kwance ya takure
jikinsa yana
karkarwar dari sai taji ta kamu da
tausayinsa
amma data tuna cewa ranta fa
yake nema sai
zuciyarta ta kekashe ta doki kejin
da
hannunta.Safwan ya mike a firgice
zumbur kawai
sai yaga Safirat tsaye a gabansa
ruke da ayaba
tanayi masa wani irin murmushi na
mugunta.Kawai
sai ta cire ayabar guda daya ta cilla
masa ita
cikin
kejin

Please Login or Register in order to submit comment