Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kintsenta kuma ta sanya
wadannan takalma
da Bandaru ya bata sannan ta fice
da sauri daga
cikin tantin.Tana fitowa tayi arba
da wadannan
dodanni guda arba'in.Kowannensu
ya goya jakar
guzurinsa a gadon bayansa sai kace
sun kasance
mutane ba dodanni ba.Al'amarin
daya baiwa
Safirat dariya kenan yayi
murmushi,kawai sai ta
juya ta nufi arewacin dajin ta
dagawa dodannin
arba'in hannu tana mai yi musu
inkiyar su biyo
bayanta.Nan fa Safirat ta falfala da
azababben gudu
izuwa cikin dajin dodannin arba'in
na rufa mata
baya suma sunayin gudu na ban
al'ajabi don har
tashi sama sukeyi saboda karfin
gudun
nasu.Amma duk da haka Safirat ta
basu yar tazara.
*** A*H*P ***
Sarki Safwan na zaune akan kujera
ya zuba idanu
izuwa cikin dajin Tsaunin Lauhul
Farras a lokacin
da alfijir ya keto sai ya fara
gyangyadi.Nai ankara
ba sai baccin ya kwashe shi gaba
daya har da
minshari.Ashe suma sauran
rundunonin da suka
fito farautar Safirat basuyi bacci ba
da
daddare.Abin kamar hadin baki sai
suma suka
kama gyangyadi a wannan lokaci
da alfijir ya
keto.A sansanin sarki Safwan barde
Barha ne kadai
baya yin bacci a wannan lokaci
saboda a daren
jiya kwanciya yayi ya hantse
abinsa,amma gaba
dayan sauran dakaru da hadimansa
da kuyanginsa
duk bacci sukeyi.Koda Barde Barha
yaga kowa
bacci yakeyi hatta sarki safwan
kuma shi kadai ne
idonsa biyu sai hankalinsa ya
DUGUNZUMA
saboda tsoron kada jaruma Safirat
ta fito a daidai
wannan lokaci daga cikin dajin
Lauhul Farras
saboda yasan cewa shi kadai bazai
iya cimmata ba
ya tare ta.Sannan kuma sai yaji
tsoron kada ya
tashi sarki Safwan daga bacci ya
zamo ya aikata
lafin katse masa baccinsa.A karon
banza ya
fuskanci hukunci mai tsananin.Nan
fa barde Barha
ya kama kai kawo a gaban sarki
Safwan wanda ke
fama sharar bacci akan kujera yana
tunanin abinda
zai fishshe shi.Kwatsam sai barde
Barha yaga
giftawar wani abu shuu!Ta
gabansu tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya.Kafin ya
juyo yaga ko mene
ne tuni Jaruma Safirat da
dodanninta guda arba'in
sun bazu tazara mai yawan
gaske.Barde Barha ya
wangame bakinsa ya kuma ya
takarkare ya kurma
wani uban ihu mai tsananin kara
da firgitarwa.Take
sarki Safwan da sauran dukkanin
jama'arsa suka
farka firgigit a dimauce.Sarki
Safwan ya zare
takobinsa koda ya kallo gabansa
sai ya hango jelar
daya daga cikin dodannin kan
tsaunin Lauhul
Farras ta kule izuwa cikin
daji.Kawai sai sarki
Safwan ya falfala da masifaffen
gudu izuwa
arewacin dajin domin ya gane
cewa Safirat ce tazo
ta giftasu yana bacci.Nan yake
kuwa Barde Barha
da sauran dakaru suka ruga suka
hau dawakansu
suka bi sawun sarki,su kuwa
hadimai da kuyanci a
firgice suka shiga hada kaya sannan
suma suka bi
sawu.Kamar yadda su Jaruma
Safirat suka gifta su
sarki Safwan suna bacci haka suka
gifta sauran
sansanin na sarakai,jarumi da
matsafa,sai bayan
sun wuce sannan ake farga dasu a
bi
bayansu.Nanfa aka kasa uban tsere
a tsakaninsu
ba sassauci.Amma aka rasa wanda
ma zai kusanci
su jaruma Safirat.Sai gashi mutum
daya jal yazo
yana ta wuce jarumai,matsafa da
sarakai rike da
zabgegiyar takobi a hannunsa.Nan
da nan ya
baiwa kowace runduna tazara mai
yawan gaske har
ya bace musu bat da gani saboda
masifaffen
gudun da yakeyi amma duk da
haka shima da
kyar yake iya hango dodo na
karshen baya daga
cikin dakarun Jaruma Safirat masu
tsaronta.Haka
dai aka cigaba da tseran gudu
tsakanin su jaruma
Safirat da sarki Safwan tun daga
fitowar alfijir har
rana ta take a sannan ne kowa ya
gaji
ainun.Tsananin yunwa da kishirwa
suka
addabesu.Amma saboda naci anki a
daina
gudu.Safirat da dakarun nata har
tangadi sukeyi
kamar zasu fadi kasa.Shima sarki
Safwan
haka,wani lokacin ma har faduwa
yakeyi amma
kuma har a san
™Abubakar Haleefah Physicist™
nan takobinsa na hannunsa bata
subuce masa
ba.Ana cikin wannan hali ne Safirat
taga uku daga
cikin dodanninta sun sare sun fadi
kasa suna haki
kamar ransu zai fita,kawai sai ta
sharesu ta cigaba
da gudunta abinta suna kara yin
dan gaba sai
dodannu biyar suka sake sarewa
suma suka zube
kasa.Faruwar hakan keda wuya sai
hankalin
Jaruma Safirat ya dugunzuma
domin ta fahimci
cewar indai aka cigaba da gudun a
haka to za'a
kai munzalin da zata rasa gaba
dayan
dodanni,alhalin kuma tasan cewa
akwai lokacin da
zasuyi mata matukar amfani.Bisa
sa'a kuwa sai
Safirat ta hango wata fadama
(korama) a gabansu
kadan.Cikin farin ciki ta karasa
gaban koramar ta
tsuguna ta jika kanta ta sha ruwa.Ai
kuwa sai
suma sauran dodannin suka rugo
izuwa cikin
fadamar suna murna suka kama
shan
ruwan.Adaidai wannan lokaci ne
Safira taji takun
sawu da gudu an tsaya a bayansu.A
nutse Jaruma
Safirat ta mike tsaye ta juyo a
hankali saboda
dama tasan wanda ke biye dasu
din.Ai kuwa tana
waigowa tayi arba da sarki Safwan
a tsaye rike da
sharbebiyar takobinsa yana haki
kamar ransa zai
fita.Ga tsananin kishirwa na
damunsa,lebansa ya
bushe sai kallon wannan ruwa na
cikin fadamar
yake.Nan fa aka fara kallon kallo
tsakanin sarki
Safwan da jaruma Safirat.Kawai sai
dodannin suka
yunkura zasu kaiwa sarki Safwan
farmaki amma sai
jaruma Safirat ta daka musu tsawa
tace wannan
yaki ba naku bane shi kadai ya iso
nan don haka
mutum daya ne zai yakeshi kum NI
CE!Koda gama
fadin hakan sai jaruma Safirat ta
cire battar
ruwanta daga kwankwasonta ta
tsomata cikin
fadamar ta cikata da ruwa sannan
ta tsuke bakinta
ta cillawa sarki Safwan ya
cafe.Dama tazarar dake
tsakaninsu bata wuce taku ashirin
ba.Safira ta dubi
sarki Safwan a lokacin da hawaye
ya subuto mata
cikin tsananin takaici tace bazan
yaki masoyina a
lokacin da yake jigace ba,kasha
ruwa ka gusar da
kishinka.Koda jin haka sai sarki
Safwan ya bude
battar ruwan ya kafata a bakinsa
ya kama
kwankwada har saida ya koshi
sannan yayi jifa da
ita.Ya dubi Safirat fuskarsa a
murtuke tamkar yana
kallon kumurcin maciji mai shirin
saransa.Har ya
budi baki zaice wani abu sai ta tari
numfashinsa
muryarta tana rawa tace ashe zaka
iya sayar da
soyayyarmu saboda abin duniya?
Ina kaunarmu da
amanar dake tsakaninu?Shin laifin
mahaifina ne ya
shafeni har da kakeson ganin
bayana?Koda sarki
Safwan yaji wadannan tambayoyi
sai zuciyarsa ta
karaya kuma kunya ta kamashi
sannan hawaye ya
zubo masa shima ya budi baki cikin
rawar murya
yace,yake Safirat ki dauki
soyayyarmu,kaunarmu,­
shakuwarmu da kuma amanar
dake tsakaninmu
tamkar wani abu daya faru a
mafarkin daya shude
tuntuni a baya.Ki sani cewa a halin
yanzi bani da
wani abokin gaba wanda ya fiki
domin mahaifinki
ne ya kashe ubana kinga dole ne na
dauki fansa
akanki.Abu na biyu dole ne na
rabaki da wannan
KWARI DA BAKA naki domin ceto
Rayuwar kasata
da jama'ar da kuma mulkina.Idan
harna barki kika
mallaki wannan kwari da baka tofa
sai duniya gaba
daya ta koma hannun mata.Sai
maza su koma
hannun bayin mata.Kinga kuwa
duk ranar da
mulkin duniya ya koma hannun
mata sai komai ya
lalace.Zaman lafiya da kwanciyar
hankali sun rushe
kenan.Saboda haka yanzu bani da
wani zabi
wanda yafi na kashe ki na dauke
wannan baka
tunda gaba daya sarakai,jarumai da
matsafan
duniya hankalinsu na kan
baka.Kafin sarki Safwan
ya gama rufe bakinsa tuni Jaruma
Safirat ta daka
masa tsawa tace kaje ka binciki
mahaifiyarka kace
kana son ta gaya maka ko wanene
ya kashe
ubana.To ka sani cewa ubanka ne
ya siye
amintacciyar baiwar ubana ta zuba
masa guba a
shayinsa.Shin rama cuta ga macuci
laifi ne?Hatta
uwata bata san nasan wannan sirri
ba.Koda jin
wannan batu sai jikin sarki Safwan
ya sakeyin
sanyi a karo na biyu.Amma sai
zuciyarsa ta
kekashe ya sake murtuke fuskarsa
yana mai gyara
tsayuwa alamar cewa a shirye yake
a gabza
yakin.Koda ganin haka sai Hawaye
ya sake
subutowa Safirat tace tabbas yau
ne na tabbatar
da cewa NAMIJI BA DAN GOYO
bane,kuma namiji
butulu ne!Idan har nayi nasara
kanka kuma na
sami nasarar dauko tuttun kwari
na,na rantse da
jini ubana saina sa gaba dayan
mazajen duniya
sun zubar da hawaye.Sai na sauke
gaba dayan
sarakunan duniya daga kan
karagarsu ta mulki na
dora mataye akai.Sai kowace matar
aure ta daina
kwanciya a kasan mijinta,sai dai a
samansa.Sannan sai kowace mace
ta daina dafawa
mijinta abinci tare da yi masa
sauran hidima,saidai
shi yayi mata ya zamo
bawanta.Saina maishe da
dukkan mazajen duniya tamkar
karnukan farautan
mata sai yadda suka so zasu
sarrafasu.Safirat na
gama fadin haka sai ta dubi
dakarun dodanninta
tace dasu ko sarki Safwan zai samu
nasarar
kasheni kada ku tayani yakarsa.Duk
wanda ya
tayani yakarsa zan kasheshi da
hannuna.Nan take
Jaruma Safirat ta zare takobinta ta
ruga izuwa kan
sarki Safwan tana mai kwarara
uban ihu da
kururuwa,takobinta na kartar kasa
tana tashin
kura.Suna haduwa suka kacame da
wani masifaffen
yaki mai tsananin ban tsoro da ban
al'ajabi.Nanfa
suka rinka kaiwa junansu sara da
suka cikin bakin
zafin nama,juriya da bajinta.Su
kuwa wadannan
dodanni sai suka zuba musu idanu
kawai suka
zama yan kallo saboda tsoron saba
umarnin
jaruma Safirat.
Toofah!!Nima ganin ana wannan
masifaffen yaki
yasa na tsaya domin na more kallo.
Don't just read and
pass,Commenting and Liking
Necessary.
A yanzu ne labari ya fara dadi fiye
da da. KIBIYA RATSA MAZA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part B
Saboda tsoron saba umarnin
Jaruma
Safirat.Wohoho!Idan jarumtaka ta
hadu da
takwaranta,naci da juriya suka
game tofa dole ne
yayi yayi tsamari ainun.Saida Safira
da Sarki
Safwan suka shafe dakiku masu
yawa suna wannan
artabu amma dayansu bai samu
nasarar koda
lakutar jikin daya ba.Al'amarin daya
dugunzuma
hankalin kowannensu kenan.Shidai
sarki Safwan
burinsa shine ya kashe Safirat kafin
ragowar
rundunonin makiyanta su karaso
wajen ya dauke
bakan dake goye a bayanta ya
gudu.Itama Safirat
kokarinta shine ta gama da sarki
Safwan kafin
sauran makiyan nata su karaso
domin ta isa cikin
dajin Sharkif in yaso su sameta a
can.Koda
kowannensu yaga wankin hula zai
kaishi dare sai
suka sauya salon fada a lokaci guda
suka hada da
kaiwa juna NAUSHI DA BUGU.Nan
take kuwa labari
yasha bambam ya zamana cewa
sun fara hadawa
kansu JINI da MAJINA.Nanfa suka
fara
galabaita.Lokaci guda kowannensu
ya fara ja da
baya cikin tsananin fushi sukayi
nazarin juna suna
mamakin yadda karfin damtsensu
yazo daya gami
da iya yakinsu.Kamar hadin baki sai
kuma suka
sake rugowa da gudu izuwa kan
juna a karo na
biyu suna masu kwala ihu.Koda ya
rage saura taku
uku kacal su hadu sai kowannensu
ya daka tsalle
sama ya kaiwa dan uwansa mugun
sara.Duk da
cewa kowannensu yayi yunkurin
kaucewa harin da
aka kawo masa,amma sai da hakan
ya faskara
domin sarki Safwan ya sami
nasarar saranta a
gadon bayanta,ita kuma ta samu
nasarar saransa a
kirjinsa.Lokaci guda duk su biyu
suka rusa ihu
sakamakon tsnanin zafi da zogin da
sukaji a
lokacin da jini yai tsartuwa daga
jikinsu suka fado
kasa a matukar galabaice suka kasa
koda mikewa
tsaye.Adaidai wannan lokaci ne
suka jiyo sukuwar
dawakai a bayansu.Suna waigawa
suka hango
rundunonin daruruwan mahaya
sun tunkaro su
daga can nesa sai kara yiwa
dawakansu kaimi
suke domin su riskesu cikin
kankanin
lokaci.Sawayen dawakan nasu na
tashin
gagarumar kura.Koda ganin haka
sai daya daga
cikin dodannin ya suri jaruma
Safirat ya dorata a
gadon bayansa,ya falfala da wani
azababben gudu
irin nasu.Ai kuwa sai sauran yan
uwansu suka rufa
masa baya.Kafin rundunonin
abokan gabar Safirat
su iso wajen tuni dodannin sun
kule a cikin dajin
tamkar basu taba wanzuwa ba a
wajen.Koda sarki
Safwan yaga Safirat ta tsere saiya
kurma uban ihu
na bakin ciki kuma ya dafe
raunikan kirjinsa mai
bulbulo da jini.Adaidai wannan
lokaci ne ya bingire
kasa sumamme.Koda dakarun sarki
Safwan suka
iso sukaga halin da yake ciki sai
suka
dimauce.Nan tahe aka kafa tanti
aka shigar dashi
ciki,likitansa ya kama
aikinsa.Sauran sarakuna da
jarumai da mayakan da suka iso
kuwa suka cika
da tsananin bakin ciki saboda sun
san cewa koda
ma sunbi bayan Safirat a yanzu ba
lallai bane su
risketa kafin ta isa cikin dajin
Sarkif.Dajin da babu
wani mahaluki da baya tsoransa a
duk fadin duniya
walau MUTUM ko ALJAN.Nan take
gaba daya
sarakunan kimanin su arba'in gami
da manyan
bokaye su ashirin da takwas da
kuma
zakwakwaran jaruman da suka fito
daga manyan
birane na duniya su talatin da biyu
suka shirya
taro na gaggawa aka zauna ana
tattaunawa.Sarkin
Misra ne ya fara da fadin cewa a
halin yanzu babu
abinda ya kamata muyi face mu jira
farfadowar
sarki Safwan na birnin Kisra tunda
shi kadai ne a
cikinmu ya sami nasarar cimam
wannan
takadariyar yarinya har suka
fafata.Kuma dama
shine mafi sanin siriinta tunda tun
suna yara suke
tare.Shine kadai zai iya bamu
shawara da wannan
baka kafin ta dauko kuttun
kwarinsa.Koda sarkin
Misra yazo nan a jabawabinsa sai
wani shahararren
boka na kasar Yemen ya tari
numfashinsa yace kai
bazai yiyu ba,domin a bari ya huce
shike kawo
rabon wani.Kuma da zafi zafi akan
bugi karfe.Ba
muki ta shawararka ba amma ga
wata
shawarar.Kowacce runduna ta zabo
wakilanta guda
goma goma a turasu subi bayan
jaruma Safirat da
dakarun dodanninta,su cimma
kafin su shiga cikin
dajin Sarkif.Tunda dai itama Safirat
akwai rauni
babba a jikinta yanzu,nasan ba
zasu shiga cikin
dajin Sarkif da ita a wannan hali
ba.Dole ne su
tsaya suyi jinyarta ta farfado kuma
ta dawo cikin
haiyacinta.Boka Inzuba ne yayi
wannan
jawabi.Koda jin haka sai sansanin
ya rude da
shewa kowa na cewa ya amince da
shawarar boka
Inzuba.Nan take kowace runduna
ta zabo dakaru
goma daga cikin mayakanta wanda
take takama
dasu.Kuma ganin cewa ta yarda
dasu,zasu iya yin
duk abinda ake ganin ba zai yiyu
ba,kowane
badakare kallo daya zakayi masa
ka tabbatar da
cewa ya cika gwarzon mayaki abin
kwatance
saboda suna da kwarjini,haiba da
cikar zati gami
da sura irin na manyan
jarumai.Kuma kowannensu
na dauke da mahaukacin
makami.Har wadannan
zababbun dakaru sun yunkura zasu
bi bayan su
jaruma Safirat sai sarkin birnin
Farisa ya tsaida su
yana mai daga hannu sannan ya
dubi gaba daya
jama'ar dake wajen yace yanzu a
misali idan
wadannan wakilan dakaru namu
suka sami nasarar
karbo wannan baka a hannun
Safirat wa za'a barwa
Bakan?Koda jin wannan tambaya
sai kowa ya
shiga taitayinsa aka kama muzurai
ana kallon
juna.Aka rasa wanda zaice kala.Da
ganin haka sai
sarkin Farisa yace tunda an rasa
mai bada amsar
tambayata ni zan baiwa kaina
amsa.Amsar itace da
zarar an zo da bakan,sai a shirya
GASAR
JARUMTAKA a tsakanin dakarun
jaruman
namu,wanda suka yi nasara su za'a
barwa
bakan.koda jin haka sai aka dada
rudewa da
shewa kowa na cewa ya amince da
wannan
tsari.Nan take dakarun wakilcin
suka zaburi
dawakansu da gudu izuwa cikin
daji domin su
riske su jaruma Safirat kafin su isa
dajin Sarkif.
*** * * * ***
Bayan tafiyar wadannan dakarun
wakilci da kamar
kimanin
™Abubakar Haleefah Physicist™
rabin sa'a ne sarki Safwan ya
farfado daga dogon
suma da yayi.Yana bude idanunsa
yaga raunin
kirjinsa a dinke kuma ya tsinci
kansa kwance a
cikin tanti.Take ya gane cewa
dakarunsa ne sualka
iso suka ceci rayuwarsa.Kawai sai
ya tuno da
yadda Safirat ta kubuce masa,nan
fa bakin ciki ya
turnuke shi ya rasa abinda ke masa
dadi a
duniya.Cikin tsananin karfin hali
sarki Safwan ya
yunkura domin ya mike zaune
daga kwance amma
saiya kasa bisa tsananin zafi da
zogin da yaji
tamkar kasusuwan kirjin nasa zasu
kakkarye.Bisa
dole ne ya koma ya
kwanta.Faruwar hakan keda
wuya saiga likitansa ya shigo cikin
tantin da sauri
saboda dama yi kiyasta iya tsawon
lokacin da
sarki Safwan zaiyi ya farka daga
bacci.Da shigowar
likitan yana duban sarki ya gane
cewa yayi
yunkurin mikewa zaune don haka
saiya dubeshi
cikin alamun tsananin damuwa da
fargaba yace ya
shugabana ka sake yunkurin zauna
zaka iya rasa
rayuwarka gaba daya domin kuwa
dukkan
kasusuwan jikinka ne zasu
kakkarye saboda
jijiyoyin dake rike da kirjin naka ne
zasu
tsintsinke.Kayi sani cewa ka auna
arziki daya
zamana cewa saran da jaruma
Safirat tayi maka
baikai ga datsa kasusuwanka
ba,naman wajen ya
dare kuma ya dan taba kashin
kadan.Dole ne a
kallah ka sami kwana tara a
kwance kana jinya
kafin kashin ya hade ka iya motsi
sosai ko ci gaba
da tafiya.Koda jin wannan batu sai
zuciyar sarki
Safwan ta kama tafarfasa kamar
zata kone saboda
bakin ciki domin yasan cewa kafin
cikar kwanakin
tara jaruma Safirat zata iya dauko
kurtun
kwarinta.Idan kuwa har haka ta
kasance tofa babu
wani mahalukin da ya isa ya tare
da yaki don ko
mutanen duniya ne da aljanunta
zasu hadu a kanta
sai ta karar dasu.Koda sarki Safwan
ya gama
aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai
sabon bakin ciki
ya turnukeshi har kwallar takaici ta
cika masa
idanu yayi sauri ya kauda kansa ga
barin kallon
likitan nasa don kada ya gane
damuwarsa.
*** * * * ***
Al'amarin Jaruma Safirat kuwa
itama tun sa'adda
ta fadi kasa sumammiya daya daga
cikin dodannin
ya sureta ya aza a bayansa suka
ruga izuwa cikin
daji bata farka ba sai bayan sa'a
uku da rabi,tana
bude idanunta ta tsinci kanta
kwance akan wata
bishiya mai yawan duhuwar
ganyaye kuma a cikin
wani irin daji wanda ko a labari
bata taba jinsa
ba.Da farko saida Safirat ta shafa
gadon bayanta
taji an dinke rauninta kuma an
shafa mata wani
magani a kansa me maiko.Koda ta
dubi gabas da
yammanta sai taga ashe akwai
wadannan dodannin
kimanin su goma akan bishiyar sun
yi mata
KAWANYA suna gadinta.Bisa
mamaki sai jaruma
Safirat taga ta iya mikewa zaune
alhalin a zatonta
ba zata iya mikewa ba zaune sai
bayan yan
kwanaki.Koda taga ta mike zaune
daram ba tare
da taji wani ciwo ko wani zogi ba a
bayanta sai ta
dubi dodannin tace,maza kuzo mu
wuce izuwa
cikin dajin sarkif saboda na
tabbatar da cewar
makiya suna biye damu,kuma idan
suka riskemu
anan ban san yadda karshen
gumurzunmu zai
kasance ba.Koda jin wannan batu
sai wannan dodo
wanda ya goyata a bayansa ya
dubeta yace,ya
shugabata ai dama ba wani abu
bane yasa muka
yada zango ba anan face ganin
halin da kike ciki
na suma da wannan rauni dake
jikinki.In badon
mun kware akan ILMIN LIKITANCI
ba da ba zamu
iya ceto rayuwarki ba har ma ki iya
mikewa
zaune.Kuma gani mukayi idan ma
muka shiga
cikin dajin Sarkif dake a cikin
wannan mugun hali
babu abinda zaki iya bisa batun
dauko kuttun
kwarinki.Kinga kenan shigar tamu
bata da wani
amfani.Koda jin haka sai Safirat tayi
murna kuma
ta yiwa dodannin godiya bisa ceto
rayuwarta da
sukayi.Nan take ta duro kasa daga
kan bishiyar
suma sai suka duro.Nan take taga
ragowar
dodannin suna fitowa daga inda
suka lallabe don
tabbatar da TSARO.KAfin Jaruma
Safirat tayi
yunkurin cigaba da tafiya sai kawai
sukaga
wadannan dakarun wakilci sun
durfafo su a guje
bisa dawakai su da yawa suna
masu zare
takubbansu suna kwarara uban ihu
mai tsananin
firgitarwa.Kuma tazarar dake
tsakaninsu bata wuce
taku goma ba.Har jaruma Safirat ta
yunkura zata
zare takobinta sai wannan dodo
daya goyata yai
wuf ya sureta ya sake° goyata a
bayansa yace ya
shugabata bai kamata kiyi yaki ba
yanzu domin
raunin gadon bayanki bai gama
hadewa ba da
warkewa.Dinkin raunin zai iya
warewa idan kikayi
kyakkyawan motsi.Ki kyalemu da
wadannan dakaru
zamu iya dasu.Kafin wannan dodo
ya gama rufe
bakinsa tuni sauran yan uwan nasa
sun ruga izuwa
inda dakarun wakilcin suke suka
tare su.Nanfa aka
ruguntsume da azababben yaki sai
gashi dodannin
suna daka tsalle sama suna
shawagi akan dakarun
wakilcin suna kai musu
yakushi,sara da suka da
miyagun faratan hannayensu.Su
kuma suka wanzu
suna karewa gami da maida
martani.Nanfa kowa
ya zamewa kowa alakakai domin
babu bangaren
dake samun wata nasara.Duk
saadda makaman
dakarun ya hadu da jikin dodannin
saikaga
tarwatsin wuta na tashi.Da yake
suma wadannan
dakarun wakilci sun cika jarumai
masu karfin
sihirin tsafi gami da matukar juriya
da tsagwaron
iya yaki sai karfi ya kusan zama
daya.Koda
donannin suka ga haka sai suka
rinka huda cikin
dawakansu suka rinka faduwa kasa
matattu suna
kayar da mahayansu.Nanfa aka
bude kasuwar
KASUWAR YAKI ta gaba da
gaba.Abinda ya
dugunzuma hankalin dakarun
wakilcin shine ganin
yadda KAIFI da TSINI baya tasiri a
jikinsu.Duk
wannan abu dake faruwa dodon
dake goye da
Safirat yana ta kokarin samun
hanyar da zai tsere
da ita ne ya nausa cikin dajin Sarkif
amma ya kasa
saboda dakarun wakilcin sunyi
musu kawanya
ne.Saida aka shafe sa'a daya da rabi
ana yin
wannan bakin artabu ba tare da
kowane bangare
sun sami wata nasara ba.Kwatsam
bisa tsautsayi
sai tsinin takobin
™Abubakar Haleefah Physicist™
daya daga cikin dakarun wakilcin
ya soki idon daya
daga cikin dodanni.Faruwar hakan
keda wuya
dodon yayi wani uban ruri a
lokacin da jini ya
kama feshi yai tsalle ya runtuma da
kasa ya kama
kakarin mutuwa.Koda dakarun
wakilcin suka ga
haka sai suka cika da murna saboda
sun gano
lagon dodanni ai kuwa sai suka
kara kaimi wajen
yakarsu.Sai gashi sun cigaba da
soke musu idanu
suna zubewa kasa matattu tamkar
ana sassabe a
gona.Nan da nan cikin kankanin
lokaci suka kashe
kimanin dodanni ashirin da bakwai
su kuwa
dodanni da kyar suka iya kashe
ashirin da daya na
dakarun wakilcin.Koda Safirat taga
irin mummunar
barnar da dakarun sukayi musu
saita fusata ainun
bata san sa'adda ta daka tsalle
sama ba daga kan
gadon bayan dodon daya
goyata.Tana saman iska
ta zare takobinta ta afka cikin
dakarun wakilcin ta
hausu da sara da suka ba
kakkautawa.Take salon
yaki ya sauya domin a cikin dakika
arba'in ta
shaftare makogwaron dakaru
kusan hamsin suka
zube kasa matattu.Ana cikin haka
ne wani
badakare mai mugun naci ya
sadado ta bayan
Safirat ya doki gadon bayan nata
da kafarsa guda
da dukkan karfinsa.Jaruma Safirat
tayi tsalle sama
tamkar an janyeta da majaujawa a
lokacin data
kurma uban ihu sakamakon mugun
zafin da taji a
gadon bayanta kuma sai fuskarta
ta gwaru da jikin
wata bishiya ta fado kasa
sumammiya.Kafin daya
daga cikinsu ya sami damar
cafkarta tuni wannan
dodo ma'abocin goya Safirat ya
dauketa daga
wajen ya sake goyata ya falfala da
azababben gudu
ta tsakiyar dakarun wakilcin yana
tarwatsasu da
karfin tsiya su kuma suna yi masa
lugudan sara da
suka suna kokarin hallaka Safirat da
dauke
bakanta.Amma sai suka kasa
saboda dodon yafi
gaba dayansu zafin nama da karfin
gudu da kuma
tsananin karfin damtse.Kafin su
ankara tuni ya fice
fit ta tsakiyar tasu ya basu tazara
mai yawa.Nanfa
suka bi bayansa da gudu a lokacin
da tsirarun
dodannin ma suka rufa masa
baya.Haka dai
dakarun wakilcin suka cigaba da
bin wannan dodo
mai goye da Safirat suna karawa
dawakansu
kaimin gudu wanda gudun nasu
gudu ne na SIHIRI
amma har dodon ya iso bakin dajin
Sarkif basu
sami damar riskarsu ba.Koda
sukaga dodon ya
fada cikin dajin Sarkif da kafafunsa
sai suka ja
linzamin dawakansu sukayi turjiya
da haniniya.Jin
turjiyar dawakan nasu ne yasa
dodon ya tsaya cak
ya waigo yana yiwa dakarun
wakilcin murmushin
muhunta sannan ya yafutosu da
hannu yana maiyi
musu nuni da cewar idan sun isa su
biyoshi cikin
dajin sarkif din.Amma dukkaninsu
sai suka noke
aka rasa wanda zai saida ransa.Ta
gaban dakarun
wakilcin sauran dodannin suka zo
suka wuce da
gudu suka fada cikin dajin Sarkif
suka bi
dan'uwansu a baya lokacin daya
juya ya cigaba da
tafiya a hankali cikin Izza,Kasaita da
kwanciyar
hankali.
*** * * * ***
Bayan Kulewar Dodannin ne a Cikin
dajin Sai.....
Tab su Safeerat sun shigo DAJIN
SARKIF dajin da kowa ke shakka.Sai
gobe maji yadda zata kasance
Insha Allah. KIBIYA RATSA MAZA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part C
BAYAN KULEWAR Dodannin ne a
cikin dajin sai
dakarun wakilcin suka dubi junansu
cikin tsananin
takaici.Daya daga cikinsu ya dubi
sauran cikin
alamun matukar damuwa yace
bamu da ilimin
komai akan dajin Sarkif,duk wanda
yayi gangancin
shigarsa a cikinmu tabbas mutuwa
zaiyi.Yanzu
kuzo mu koma sansaninmu wajen
shugabanninmu
mu sanar dasu duk abinda ya
faru,amma dole ne
mu dauki gawar dodo ko guda
daya ne domin su
gasgata zancenmu su tabbatar da
cewar munyi
iyakar kokarinmu.Gama fadin
hakan keda wuya sai
dakarun wakilcin suka juya da baya
da gudu izuwa
cikin dajin da suka baro,wato can
inda suka fara
yin gumurzun farko dasu jaruma
Safeerat.
*** * * * ***
Al'amarin su jaruma Safirat kuwa
lokacin da aka
shigar da ita cikin dajin sarkif
sa'adda take cikin
suma na biyu goye a bayan
wannan dodo,tafiyar
dakika dari biyu da sittin kacal
akayi ta farfado
daga suman da tayi.Amma sai taji
gadon bayanta
yana yi mata mugun radadi da zogi
sakamakon
naushin da akayi mata wanda ya
zama ya fama
mata raunin,amma sai taji cewa
zata iya yin tafiya
da kafafunta,Sai ta budi baki tace
ka ajiyeni na taka
da kafafuna.Koda jin muryar Safiray
sai farin ciki ya
kama dodon ya tsaya cak ya sauke
ta saboda
tsawonsa.Koda ya direta kasa a
gabansa yaga ta
fara kallon dajin Sarkif tana
murmushi saboda
ganin irin ni'imar dake cikinsa ta
korayen
ganyaye,ruwan duwatsu dake
kwaranya wanda ya
kasance garai garai gwanin ban
sha'awa da kuma
yayan itatuwa irinsu inibi,baure da
sauransu sai
yace ya shugabata kyawun wannan
daji ya daina
birgeki domin kyan dan maciji
ne.Idan kinsan
masifun dake cikinsa da bakiyi
sha'awar shigarsa
ba.Mu kanmu a yanzu ba karamin
ganganci mu
kayi ba da muka biyo dake izuwa
nan kawai,don
bamu da yadda zamuyi mu kawo
kanmu GIDAN
MUTUWA,kuma ako yaushe a ko ina
ajali zai iya
zuwa ya shammacemu a cikin
wannan daji.Koda
jin wannan batu sai mamaki ya
kama jaruma
Safirat tace to wai shin menene
abin tsoro a cikin
wannan daji?Ni tun da muka shigo
cikinsa ko
mugun kwaro guda daya ban gani
ba.Gama fadin
haka keda wuya sai safirat taji wani
irin huci a
bayanta mai dumi kamar an kunna
gagarumar
wuta sannan kuma taji wani irin
gurnani mai
matukar ban tsoro.A firgice ta
waiga bayanta da
sauri,koda tayi arba da abinda ke
bayanta sai taji
kamar ta saki fitsari a tsaye saboda
tsananin
razanar da tayi duk da jarumtaka
irin tata kuwa.Ba
komai jaruma Safirat ta gani ba
face wata irin
katuwar macijiya mai girman
gaske,amma kuma
kanta irin na macen bil'adama ne
rafkeke tamkar
tunkuyar girki irin ta mutanen
da.Tna da idanuwa
manya manya kamar tulu,hancinta
wawakeke za'a
iya zura mutum a cikin kowane
kofar
hancin.Bakinta kuwa kamar kofar
shiga wani
gari.Hakoranta gabza gabza ne
kamar hauren giwa
ne aka jera sama da kasa kuma
guda dari ba daya
ne.Saboda girman jelarta da
nauyinta ko yaya ta
motsa sai dajin gaba daya yayi
girgiza.Tunda
Jaruma Safirat tazo duniya ko a
mafarki bata taba
tunanin cewa akwai wata halitta
mai mummunar
siffa irin wannan ba.Nan take sai
jikin Safirat ya
kama karkarwa.Su kuwa wadannan
dodanni
abokan tafiyar Safirat tuni sun arce
daga wajen sun
shige cikin kogunan duwatsu da
cikin ramuka sun
buya suka bar Safirat ita kadai a
tsakiyar dajin a
gaban wannan muguwar
Macijiya.Lokacin da
macijiyar taga yadda jaruma Safirat
ta firgice kuma
ta dimauce sakamakon yin arba da
ita sai ta bushe
da wata irin mahaukaciyar dariya
mai kama da
saukar kwaran kwatsa sannan ta
hade bakin a
lokacin da wani irin turirin dafi ke
fita ta dakawa
Safirat tsawa tace ke karamar
kwaruwa wane irin
taurin kai gareki gami da ganganci
da rayuwa har
da zakiyi tunanin shigowa cikin
wannan daji domin
ki dauki wani abu?To ki sani cewa
ko shi kansa
mahaifin naki boka Saiham daya
tabbata shugaban
bokayen duniya bai taba shigowa
nan ba,saidai ya
aiko da abu ta hanyar sihiri shi
kansa yasan ya
turoki ne izuwa AJALINki.Kafin
macijiyar ta gana
rufe bakinta tuni jaruma Safirat ta
tari numfashinta
tana mai cewa ke tsohuwar
azzaluma,ki sani cewa
koma girman halitta,komai jin
kanta da karfinta sai
an sami wadda ta fita
komai.Tabbas na firgita da
ganinki saboda shi tsoro wajibi
ne,amma dana
gane cewa ke azzalima ce sai naji
duk tsoronki ya
gushe daga cikin zuciyata.Duk
abinda yai farko a
cikin wannan duniya yana da
karshe,babu mamaki
zuwana nan ya zama sanadin
karshen
zaluncinki.Nayi imani cewa sai na
sami abinda
nazo nema a cikin dajin nan kuma
sai na fita a
raye don haka ke baki isa ki hanani
daukar abinda
nazo dauka ba.Koda Safirat tazo
nan a zancenta
sai Macijiyar ta wangame katon
bakinta ta bushe
da dariya a karo na biyu,iskar bakin
nata ta daga
Safirat sama har saida ta daina
dariyar tsuke
bakinta sannan Safirat ta fado kasa
tim.macijiyar ta
dubeta cikin kallon raini tace
hakika yaro bai san
wuta ba sai ya taka ta.Tunda kikayi
mini rashin
kunya yau saidai uwarki ta haifi
wata amma dai ke
taki ta kare.Idan kina da wasiya ta
karshen rayuwa
ki fadi kafin ki sheka
barzahu.Kuttun kwari da
bakan da kika zo nema bama ke ba
wasunki ma
basu isa susan inda yake ba a cikin
wannan daji
bare su dauka daga nan har izuwa
rayuwa idan
akwaita.Kafin Safirat ta bude baki
tace wani abu ko
kuma tayi wani yunkuri tuni
majiyar ta shammaceta
ta wangame bakinta.Take wata irin
iska mai karfi ta
fito daga cikin bakin ta zuke Safirat
ta
hadiyeta.Kawai sai macijiyar ta rufe
bakin nata
sannan ta daka tsalle ta tsunduma
cikin wani
tafkeken kogi tayi nutso izuwa
karkashinsa.A
ka'idar wannan macijiya duk
abinda ta hadiye a
cikin dakika
™Abubakar Haleefah Physicist™
biyar kacal yake narkewa ya
zagwanye saboda
tsananin zafin dake cikin
cikinta,amma sai gashi
Safirat bata narke ba kuma bata
mutu ba amma
tsananin zafin cikin macijiyar yasa
jikinta yayi luguf
kuma numfashinta ya fara sarkewa
saboda rashin
shakar iska.Koda Safirat taji zata
hallaka saita
mike tsaye a cikin cikin macijiyar ta
zare wata
wuka dake daure a jikin cinyarta ta
hagu ta kama
saran hanjin cikin macijiyar.Ai kuwa
sai macijiyar
ta rinka jin kamar zata mutu don
haka bata san
sa'adda ta wangame bakinta ba
tayi wata irin
muguwar kara wacce tasa gaba
dayan halittun
dake cikin karkashin tekun suka
mace nan
take,wadanda ke saman kogin suka
sume,wadanda
ke cikin dajin bisa turba dole suka
toshe
kunnuwansu,wasu kuwa suka rinka
tona kasa suna
binne kansu da kansu a karkashin
kasa.Safirat ta
cigaba da saran hanjin cikin
macijiyar duk da cewa
kuwa hanjin baya katsewa amma
macijiyar bata
daina mutsu mutsu da juye juye ba
tana ruri da
ihu tana gwara jikinta a jikin
duwatsun dake cikin
karkashin kogin.Sakamakon haka
ne Safirat ma ta
rinka faduwa tana gwara kanta da
jikin macijiyar
amma saboda tsananin naci da
juriya sai ta cigaba
da mikewa tsaye zumbur tana ci
gaba da saran
hanjin macijiyar,nanfa ya zamana
cewa da ita da
macijiyar duk sun wahala sun jigata
ainun.nan da
nan idanun macijiyar suka kada
sukayi jawur,suka
fara zubar da hawayen wuya,kai da
bala'i yai bala'i
macijiyar taji cewa tabbas hallaka
zatayi sai ta taso
sama daga karkashin kogin ta fito
bakin gabar
kogin ta fito bakin kogin ta kama
kakarin amai
domin ta watso Safirat waje daga
cikinta ta huta da
azabar da take ji.koda Safirat taji an
zukota za'a
wastota waje daga cikin macijiyar
don haka saita
saki jikinta ta taho da gudu tana
fitowa bakin
macijiyar saita wurkila jikinta ta
haye saman kan
macijiyar ta zauna daram.Kafin
macijiyar ta wurkila
jikinta ta jeho Safirat kasa tuni ta
daga wannan
wuka dake hannunta ta caka mata
ita a tsakiyar
madigarta.Nan take jini ya kama
tsiri sama a
lokacin da macijiyar tayi wani irin
uban ruri wanda
bata taba yin kamarsa ba.Kawai sai
ta langwabe
kasa tayi wanwar ko shurawa
batayi ba.Ashe ruhin
wannan macijiyar a cikin tsakiyar
kanta yake cikin
madiga.Ita kanta jaruma Safirat da
taga ta sami
nasarar kashe macijiyar tayi
matukar mamaki
domin bata san cewa ruhinta a
tsakiyar kanta yake
ba kawai dai tsananin sa'a ne da
rabo ya kaita ga
samun wannan nasara.Saboda jikin
Jaruma Safiray
ya hadu yayi lugub sakamakon
tsananin zafin da
cikin macijyar yake dashi saita
yanke jiki ta fadi
kasa sumammiya.Adaidai wannan
lokaci ne
wadannan dodanni suka fito daga
cikin ramuka da
kogunan duwatsun da suke boya
da gudu suka
rugo izuwa inda take kwance.Nan
dai suka fara
kokarin ceto rayuwarta.Saida suka
shafe kusan
rabin sa'a suna yi mata fifta da dan
yayafa mata
ruwa amma bata farka ba.Al'amarin
dayai matukar
dugunzuma hankalinsu kenan suka
fara tunanin
cewa lallai ta mutu saboda babu
alamar inda yake
motsi a jikinta.Nan fa dodannun
suka kama kuka
suna zubar da hawaye na takaici da
bakin ciki
saboda a ganinsa bai

Please Login or Register in order to submit comment