Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gareshi suka tari juna suka
ruguntsume da
masifaffen yaki mai tsananin ban
tsoro da ban
al'ajabi domi kuwa kowannensu
yana kai sara da
suke ne cikin tsananin zafin
nama,juriya da
bajinta.Da farko sai yakin ya nuna
kamar karfin
damtse yazo daya,domin saida
suke shafe kusan
dakika dari da ashirin sunayin
bakin gumurzu ba
tare da dayansu ya sami nasarar
koda lakutar jikin
daya ba,amma kuma sai kwatsam
akaga Safirat ta
fara yin wata irin gagarumar
jarumtaka taban
al'ajabi ya zamana cewa tana tashi
sama kamar
tsuntsuwa tana shawagi akan
Hidaisu tana kai
masa mugayen hare hare cikin
bakin zafin nama
daya ninka na farko sau uku,wurin
ya dare jini yayi
feshi,Hidairu ya kurma uban ihu
sakamakon
tsananin zafi da zogin da yaji
amma saiya taso a
fusace ya kawai Safirat wani
mugun sara,saura
kiris ya zabtare Mata Allon
kafadarta ta
dama,amma saita goce takobinsa
ta sari iska ita
kuma ta daka tsalle sama ta jera
masa lugudan
naushi da kafarta a fuskarsa da
kirjinsa sau goma
sha biyu,Tun Hidairu na layi daga
tsaye kamar
wanda yasha giya ya bugu sai
kawai akaga ya
bingire kasa sumamme.Koda ganin
abinda ya faru
sai gaba dayan fadawa da dakarun
yakin kasar
suka zube kasa bisa guiwoyinsu
suna masu mika
wuya ga Safirat.Nan fa Farin ciki ya
lullube Safirat
tayi nuni da hannunta izuwa can
inda aka daure
mahaifiyarta dake dirkar da aka
daureta a jiki ta
jijjigo daga cikin kasa gaba dayanta
ta taso a sama
tazo gaban Safirat.Cikin tsananin
farin ciki Safirat
da Mahaifiyarta suka rungume
junansu daga can
sai Safirat ta dubi Dakarun tace a
kirawo likita ya
yiwa Hidairu magani sannan a
kama shi shida
sarki Safwan akai su kurkuku a
kulle.Koda jin
wannan batu sai Gargus ya dubi
Safirat cikin
alamun tsananin damuwa yace
haba ya shugabata
ya zaki bar makiyanki a raye,ba kya
tsoron nan
gaba su cutar
™Abubakar Haleefah Physicist™
dake?Koda jin wannan tambaya sai
Safirat tayi
murmushi tace ai idan na kashe su
ban more
ba,burina shine bakin ciki da
takaicin yadda
rayuwarsu take ya zamo
Ajalinsu.Gama fadin
hakan keda wuya saiga jama'ar
gari mata da maza
suna firfitowa daga cikin
gidajensu,manya da yara
babu wanda ya rage.Koda ganin
haka sai Safirat ta
tashi sama kamar tsuntsuwa taje ta
dira akan
babbar ganuwar dake fuskantar
jama'a akayi tsit
tamkar mutuwa ta gifta.Adaidai
wannan lokaci ne
Safirat tayi gyaran murya tace yaku
jama'ar birnin
Kisra kuyi sani cewa yau ni Safirat
'ya ga marigayi
Boka Saiham na zamo
GAGARABADAU a wannan
nahiya tamu gaba daya kuma da
sannu zan zamo
SARAUNIYAR DUNIYA!Tabbas na
cika burin
mahaifina domin na sami daukakar
da babu wani
mahalukin daya sameta a wannan
zamani ina so
ku sani cewa sarkinmu na da wato
mahaifin sarki
Safwan shine ya kashe mahaifina
saboda kawai
mahaifina ya sana'anta abinda da
babu
kamarsa.Bayan nan kuma sai dansa
Safwan ya
shiga farautar rayuwata domin ya
kashe ni ya
mallaki wannan kwari da
baka.Haka kuma manyan
sarakunan duniya suka hado
dakarun yaki suka fito
farautata domin su mallaki kwari
da bakana bisa
son zuciyarsu,duk wanda ya
mallaki wannan kwari
da baka zai gabatar da mulki ne na
zalunci.Kowa
yasan tsakanina da sarki Safwan
domin tun muna
yara mukeyin SOYAYYA amma sai
gashi yayi mini
butulci saboda son duniya,yayi
kokarin hallakani
da kuma rabani da abinda
mahaifina ya shafe
shekaru kusan arba'in a cikin kogon
tsafi yana
kirkirarsa.Wannan ya tabbatar mini
da cewa maza
azzalumai ne kuma ba yan goyo
bane,saboda haka
daga yau namiji ya daina mulki a
nahiyar nan gaba
daya,a yau dinnan zan hau karagar
mulkin Birnin
Kisra na zama Sarauniyarku.Gaba
daya fadawan
kasar nan zan tuje musu rawaninsu
na baiwa
mata.Duk namijin da yake da
adawa akan wannan
batu to ga fili ga mai doki ya fito
mu fafata.Hatta
dakarun da zasuyi tsaro a birnin
nan daga yau
mata ne.Koda Safirat tazo nan a
jawabinta sai
mata suka rude da shewa gami da
tafi suka kama
yiwa Safirat jinjina da kirari,wuri ya
hautsine,maza
kuwa sai hankalinsu ya
DUGUNZUMA ainun suka
rasa abinda yake musu dadi,nan
take aka cika
umarnin Safirat aka kai sarki
Safwan da wazirinsa
Hidairu izuwa kurkuku aka
kulle.Koda Hidairu yaga
an kulleshi a cikin kurkuku saiya
fara kokarin
amfani da sihirin tsafinsa domin ya
balla kofar
dakin da aka kulle su a ciki amma
sai sihirin yaki
yayi tasiri.Al'amarin da yayi
matukar fusata shi
kenan ya wangame bakinsa ya
kwarara uban ihu
cikin tsananin takaici sannan ya
fashe da kukan
bakin ciki,kawai sai yaji sarki
Safwan ya bushe da
dariya,cikin kaduwa da mamaki
Hidairu ya dubi
Safwan yace menene kuma
amfanin wannan dariya
taka alhalin ni da kai duk tamu ta
kare.Sa'adda
Safwan yaji wannan tambaya sai
yayi shiru ga
barin dariyar ya dubi Hidairu cikin
nutsuwa yace
wannan duniyar da muke ciki ce ta
burgeni saboda
tana nunawa mutum sakamakon
abinda ya aikata
ya gani da ransa da idanunsa.A
hankali mahaifina
ya yaudari Boka Saiham kuma yaci
amanarsa ya
kashe shi don kada ya mallaki
wannan
SIHIRTACCIYAR KWARI DA BAKA
amma a karshe
shima mahaifin nawa ya rasa tasa
rayuwar,kuma
bukatarsa bata biya ba ni ma gashi
na yaudari
Safirat naci amanarta bukatata bata
biya ba,kau ma
kuma gashi kaci amanata
bukatarka bata biya.Yau
dana karbi soyayyar Safirat na
aureta a matsakin
ABOKIYAR RAYUWA ta da yanzu
kuwa na zauna
cikin kwanciyar hankali kuma da
yanzu ban
janyowa sauran sarakunan duniya
bala'in da suke
fuskanta ba.Koda sarki Safwan yazo
nan a
zancensa sai ya fashe da kuka na
bakin ciki da
nadama.Yana cikin wannan hali ne
yaji Waziri
Hidairu ya dafa kafadar a lokacin
daya mike zaune
da kyar sakamakon zogin da
raunikan jikinsa keyi
masa.Sarki Safwan ya juyi ya dubi
Hidairu yace me
kake son ka gaya mini alhalin kaci
amanata kuma
ko alamar nadamar yin haka babu
a tare da
kai.
¶TRIPLE Ŷ
Hidair ya gyada kai yace ai ita
nadama a cikin
zuci take indai ta gaskiya ce ba sai
na nunata a
zahiri ba,abinda zan sanar dakai
shine ka kwantar
da hankalinka ka sani cewa komai
nisafan jifa kasa
zai fadi.Tun farko duniya kawo i
yanzu namiji ne
bisa mace don haka koda Safirat ta
sami nasarar
aiwatar da wannan cin zarafi a
garemu mazan
duniya a yanzu to akwai lokaci da
zaizo
alkadarinta ya karye,ina mai
tabbatar maka da
cewa dole ne wata rana sai ta
dawo karkashin 'da
namiji tunda dai 'ya mace akayi ta
su kuwa mata
sun kasance masu rauni a
kanmu.Yayin da Hidairu
yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki
Safwan yayi
sanyi kuma ya kurawa Hidairu
idanu yana tunanin
da nazari daga can saiya kyalkyale
da dariya yace.
Sai mun hadu a part B.
LIKING AND COMMENTING
NECESSARY. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part B.
SAIYA KYALKYALE DA DARIYA
YACE,yakai abokina
kayi sani cewa na sauya shawara
bisa hukuncin
dana yanke akanka wanda ke cikin
zuciyata da
nayi niyar na kashe ka a nan a cikin
kurkukun
sannan na kashe kaina domin mu
huta da takaicin
wulakancin da Safirat zata cigaba
da yi mana har
izuwa karshen rayuwarmu,amma a
yanzu dakayi
mini wannan jawabi sai na gane
cewa lallai akwai
bukatar muyi hakuri mu jira lokacin
da wani jarumi
zai zo ya share mana hawayen
bakin cikinmu.Koda
gama fadin hakan sai sarki Safwan
ya rungume
Hidairu suke bushe da dariyar
mugunta a lokaci
guda,adaidai wannan loka cine
sukaji birnin ya
kaure da kade kade da bushe bushe
da kuma raye
raye alamar cewar an fara gudanar
da bikin nadin
sarauniya Safirat.Saida aka kwana
ana bidiri a cikin
birnin Kisra mata sukayi ta
sharholiyarsu suna cin
zarafin mazajensu sai yadda sukayi
dasu wato
suka rinka juya su tamkar waina a
kas,Daga
wannan rana maza suka zama
bayin mata mace
batayin komai saidai ta kwanta taci
tasha.Amma
hatta aikin gida mazajensu keyi
musu saidai idan
mijin ya kasance attajiri ne ya debo
maza bayi su
yiwa matarsa aiki.Duk laifin da
mace ta yiwa
mijinta tayi a banza amma da zarar
namiji ya yiwa
matarsa laifi nan take za'a yanke
masa hukunci
mai tsauri.Ko'a ci shi tara mai
yawan gaske ko
kuma a dina masa watanni ko
shekara a gidan
wakafi.Haka dai sarauniya Safirat ta
cigaba da
gudanar da mulki wanda babu
adalci a cikinsa ko
kadan ya zamana cewa rayuwar
maza ta shiga
kunci,takaici da bakin ciki,kai sai
dama takai cewa
sarauniya Safirat na kwace dukiyar
mazaje tana
dankawa matayensu suna juyata
saidai a rinka
sam musu wani abu daga cikin
abinda aka
samu.Duk wani aikin karfi kona
wahala maza ke
yinsa a cikin birnin Kisra,yara da
tsofaffi ne kadai
basa fuskantar wannan wulakanci
na sarauniya
Safirat.Bisa wannan dalili ne
mazajen birnin
wadanda ba zasu iya jure wannan
wulakanci ba
suka fara sulalewa suna yin Hijira a
sirrance ba
tare da an sani ba suka rinka
hakura da
matansu,yayansu da
dukiyarsu.Wadansu matan da
suke matukar kaunar mazajensu sai
suka rinka
binsu suna gudu tare.Koda
sarauniya Safirat ta
gano hakan sai tasa aka datse duk
hanyoyin fita
daga garin ya zamana cewa babu
mai fita sai an
bincike shi an tabbatar da cewar ba
hijira zaiyi
ba.A cikin sati uku kacal sarauniya
Safirat ta sauke
gaba dayan yan majalisar
kasar,hakimai,dakatai da
masu unguwanni akan mukamansu
ta dora mata a
kai.Sannan kuma ta tara dakarun
yaki na mata
gudu dubu dari bakwai da saba'in
da
bakwai,Gargus ne ya baiwa
wadannan mata horon
yaki mai tsananin gaske naban
al'ajabi kuma
sarauniya Safirat ta basu sirrikan
tsafi don kare
kansu gami da zama
jajurtattu.Bayan sarauniya
Safirat ta tabbatar da cewa
wadannan dakarun yaki
nata guda dubu dari bakwai da
saba'in da bakwai
sun sami cikakken horon yaki irin
wanda take so
sai ta tashi manzo da wasika izuwa
birnin
Misra.Da rana tsaka sarkin Misra na
zaune a fada
tare da dukkan fadawansa da
sauran mutanen gari
ana tafiyar da harkokin mulki
kamar yadda aka
saba saiga manzo daga birnin Kisra
wadda ta
kasance mace ce a cikin gagarumar
shigar yaki
bisa wani bakin ingarman
doki.Saboda isa da jin
kai har cikin tsakiyar fadar
badakariyar ta shigo da
dokinta dakaru na kallonta amma
aka rasa wanda
zai taka mata birki har ta iso kusa
da sarki ya
zamana cewa tazarar dake
tsakaninsu bata wuce
taku goma sha ba sannan ta sauko
daga kan
dokinta ta dan risina kadan ga sarki
sannan ta
dago kai ta dubeshi cikin nutsuwa
ba tare da
shakkar komai ba tace sunana
Lubbatu daya daga
cikin dakarun yakin sarauniya
Safirat ta birnin
Kisra,ni manzo ce a gareka ta bani
wasika na kawo
maka kuma tana bukatar amsar
wasikar yanzu
domin na kai mata.Koda jin
wannan batu sai
hankalin kowa a cikin fadar ya
dugunzuma ainun
saboda rashin sanin abinda wasikar
ta kunsa,shi
kuwa sarki sai yayi murmushi
sannan ya dubi
Lubbatu cikin gadara yace fito da
wasikarki ki
karanta a fili kowa yaji abinda ta
kunsa.Ba tare da
gardamar komai ba kuwa sai
Lubbatu ta zura
hannu cikin aljihun sulkenta na yaki
ta dauko
zungureriyar wasika ta warware ta
sannan ta fara
karanta sakon dake cikinta a fili
kamar
haka:Takarda daga hannu
sarauniya Safirat mai
kasar Kisra wacce ke shirin zama
sarauniyar
duniya kaf.Zuwa ga sarkin birnin
MisraIna mai
sanar da kai cewa nan da cikar
kwanaki kadan
zanzo kasarka tare da dakaru na
mutun dubu dari
bakwai da saba'in da bakwai kacal
wadanda gaba
dayansu mata ne zalla da zarar na
iso ina so kazo
kayi mubaya'a a gareni domin na
sauke ka daga
kan karagarka sannan nayi binciken
mace data
dace da matsayinka a cikin birnin ta
maye
gurbinka.kamar yadda ka sauka
daga kan
mukaminka haka nakeson gaba
dayan fadawanka
da duk masu mulkin kasar ka su
sauka su baiwa
mata matsayinsu,idan ka amince da
hakan zaka
tsira da rayuwarka da kuma
mutuncinka idan kuma
kaki zaka rasa komai naka.Koda
Lubbatu tazo nan
a karatun wasikarta tuni jikin
sarkin Misra ya dade
da fara karkarwa,zuciyarsa tana
tafarfasa kamar
zata kone fuskarsa kuwa ta kama
gatsine kamar
zata zazzago kasa saboda tsananin
fishi,kawai
saiya doki kasa da hannayensa biyu
yayi sama
tamkar da majaujawa aka janyeshi
yana saman ya
zare takobinsa ya kaiwa Lubbatu
mummunan sara
a wuya da nufin ya cire mata
kai,cikin bakin zafin
nama taja da baya amma duk da
haka saida kaifin
takobin ya yanketa a saman kirjinta
jini yayi
tsartuwa a lokacin data daka tsalle
can gefe daya
kuma ta mike tsaye zumbur cikin
matukar juriya
tana mai zare takobinta gami da
dafe raunin
nata.Cikin tsawa sarki
™Abubakar Haleefah Physicist™
ya baiwa dakarunsa umarninsu
afka mata su
kasheta.Nanfa fadar ta hargitse aka
ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa
dakaru sama da
dubu uku sun rufarwa Lubbatu ita
kadai suna kai
mata sara da suka ta ko ina domin
su hallakata ita
kuwa ta wanzu tana mai kare
kanta gami da maida
martani da kuma kokarin samarwa
da kanta hanyar
da zata tsere.Saida aka shafe sama
da sa'a guda
anayin wannan bakin gumurzu da
kyar da sidin
goshi Lubbatu ta sami damar fasa
kofar fadar da
karfin sihirin tsafinta ta gudu daga
cikin fadar bisa
dokinta cikin matsanancin gudu na
fitar
hankali.Bayan anyi mata mugayen
raunika guda
uku a jikinta.Jini na zuba a jikinta
kuma jiri na
dibarta ta nausa cikin daji.Duk da
haka saida
sarkin Misra tare da dakarunsa suka
biyo sawunta
suka cigaba da farautarta a cikin
daji.Ba don tana
da karfin sihirin tsafi ba da sai sun
ganta sun
hallakata.Saida Lubbatu tayi jinyar
kwana bakwai a
cikin daji ta boye kanta sannan ta
sami lafiyar data
cigaba da tafiya ta isa birnin Kisra a
matukar
galabaice.Da shigowarta cikin fadar
sai sarauniya
Safirat ta mike zumbur ta ruga
gareta ta rungumeta
cikin tsananin takaici sannan ta
dubeta tace naga
duk abinda ya faru a gareki a can
birnin Misra
kuma inaso ne na zuba ido har kika
kwace kanki
daga sharrinsu domin su gane
cewa ke kadai ma
sun kasa kawar dake bare ni da
kaina naje.Tabbas
kin cika jaruma a bar kwatance don
haka na baki
matsayin mataimakiyar shugaban
dakarun yakina
Gargus kuma na baki dukiya da
dinare miliyan
sittin tare da babbar gona guda
daya daga cikin
manyan gonaki na na bayan
gari.Koda jin wannan
albishir sai Lubbatu ta sulale kasa
sumammiya
saboda tsananin farin ciki saida aka
kawo ruwa aka
yayyafa mata sannan ta farfado
nan take Safirat ta
dubi Gargus tace aje a fara shirin
yaki gobe da safe
zamu tafi izuwa birnin Misra ina
mai bayar da
umarnin cewa muna shiga birnin
mu kashe duk
mazajensu,yara da tsofaffi kadai
za'a bari da
rai.Gargus ya risina yace an gama
ya shugabata.
*Acan birnin Misra kuwa tun daga
ranar da aka bi
sawun Lubbata ta tsere aka nemeta
sama da kasa
aka rasa sai sarkin Misra ya fara
shirye shiryen
yaki don ya tabbatar da cewar
sarauniya Safirat
nanan tafe.Nanfa yasa aka rinka
binne mugayen
tarkuna a cikin dajin da dole sai an
ratsa ta cikinsa
sannan za'a iso birnin nasa sannan
kuma ya aika
da sakon neman agajin dakarun
yaki daga
kasashen dake makwabtaka
dashi,wasu sarakunan
sai suka aika masa da gudunmawar
dakaru wasu
kuma sai suka noke saboda tsoron
kada fishin
Safirat ya shafe su.A wannan lokaci
da yawa daga
cikin sarakunan kasar sun yanke
shawarar suyi
mubaya'a ga sarauniya Safirat
domin su tsira da
rayukansu da mutuncinsa wasu
kuma sai suka
zuba ido domin suga yadda zata
wakana a
tsakaninta da sarkin Misra saboda
shima ansan
cewa ba karamin jarumi bane
kuma babban
takadiri wanda baya gudu ko ja da
baya a filin
daga.Kwanaki goma sha daya na
cika sarauniya
Safirat ta sauko a kofar birnin Misra
tare da
dakarunta na yaki guda dubu dari
bakwai da
saba'in da bakwai da kuma
dodanni guda talatin
da uku dukkaninsu suna karkashin
jagorancin
dodo Gargus.Lokacin da labari ya
riske sarkin
Misra cewa ga sarauniya Safirat can
tare da
dakarunta sun iso kofar birninsa su
duka ba tare
da dayansu ya hallaka ba saiya cika
da tsananin
mamakin yadda akayi suka tsalle
shirin duk
tarkunan da aka binne musu.Nan
take ya dauko
madubin tsafinsa ya shafe shi saiya
ga ashe gaba
dayan tarkunan Safirat ce ta
lalatasu da karfin
sihirin tsafinta.Nan take ransa ya
baci,da yake
zuciyarsa ta kekashe ga barin tsoro
kuma ya cika
zarto mai kishin kansa da kasar sa
sai ya mike
tsaye zumbur ya kirawo gaba
dayan dakarun na
yaki yace ayi shiri aje a tare
sarauniya Safirat a
kofar gari.Duk mayakin daya
tsorata yayi yunkurin
guduwa a bakacin ransa.Nan dai ya
cigaba da
karawa mayakan nasa karfin guiwa
yana mai cewa
ku sani cewa wannan yaki da zamu
fita yaki ne na
kare mutuncinmu,rayukanmu da
darajarmu ta
'ya'ya maza,da dai a wulakantamu
a maishemu
bayin matayenmu gwara mu mutu
a FILIN
DAGA.Ko ba komai zamu bar tarihin
cewa mun
mutu mazaje ba mata ba kuma
jaruman da baza'a
taba mancewa dasu ba.Koda jin
wannan batu sai
gaba dayan dakarun nasa sukaji
dukkan tsoro ya
kau daga cikin zukatansu suka
kama kurma ihu
tamkar ma sun sami nasarar yakin
da zasu fita
suna yiwa sarkin nasu jinjina gami
da kirari.Ba
tare da bata wani lokaci ba aka
daurawa sarkin
Misra damarar yaki yahau dokinsa
ya jagoranci
miliyoyin dakarun yaku suka zaburi
dawakansu da
gudu a lokacin da aka bude
katuwar kofar birnin
suka fice daga dayansu sannan aka
mayar da kofar
aka rufe.Ai kuwa suna fitowa suka
hango sarauniya
Safirat tare da tsirarun dakarunta a
tsaitsaye bisa
dawakai daga can dan nesa
kada.Tazarar da bata
wuce kamu arba'in ba.Nanfa aka
fara kallon kallo
tsakanin rundunar biyu har izuwa
wadansu yan
dakikai.Daga can sai sarkin Misra ya
sakarwa
dokinsa linzami ya taho a hankali
ya fito daga cikin
tasu rundunar alamar cewa so yake
ya tattauna da
sarauniya Safirat kafin a fara
yaki.Koda ganin haka
sai itama Sarauniya Safirat ta
sakarwa nata dokin
linzami ta durfafeshi har saida suka
isa tsakiyar
filin sannan suka tsaya cak suka
sake kallon
juna.Koda Safirat ta karewa sarkin
Misra kallo tsaf
daga irin halittar da Allah yayi
masa ta
sadaukantaka,kwarjini da kirar karfi
sannan ta dubi
miliyoyin dakarun yakin dake
bayansa saida taji
zuciyarta ta dan sosu kuma ta
tabbatar da cewa in
ba don ta sami sirrin wannan kwari
da baka na
mahaifinta ba da bata isa ta iya
tarar wannan
runduna da yaki ba.Bayan anyi
kallon kallo na
™Abubakar Haleefah Physicist™
tsawon yan dakiku kadan tsakanin
sarkin Misra da
sarauniya Safirat saiya dubeta cikin
tsananin fushi
yace yake wannan azzalumar
sarauniya kiyi sani
cewa na sani cewa kece zaki sami
nasara a
wannan yaki da zamu fafata amma
ina alfahari da
zan mutu a matsayin sarki mai
kishin kasarsa da
jama'arsa kuma jarumin da bai
mika wuya ba ga
'ya mace,nayi miki alkawarin cewar
kafin ki kaini
kas a wannan yaki da zamu fafata
sainayi miki
raunin da har abada tabonsa bazai
bace ba a
jikinki saidai akaiki kabarinki
dashi,saboda ba na
son ki manta da takaicina bayan
mutuwata.
¶TRIPLE Ŷ
Koda
sarkin Misra yazo nan a zancensa
sai sarauniya
Safirat ta bushe da dariyar
mugunta sannan ta
murtuke fuskarta tace hakika ka
burgeni daka
kasance jarumi mai kishin
kansa,amma ka sani
cewa baka kishin jama'arka da
kasarka tunda idan
har muka gwabaza wannan yaki
saina kashe gaba
dayan wadannan mayaka naka na
yiwa kasa ado
da jininsu kuma saina kone
dukkanin kyawawan
gidajen nan naku na ruguje su.Idan
har kana
kishin jama'arka da birninka to zan
iya sauya
shawara na baka zabi guda.Zabin
kuwa shine
zamuyi wannan yaki mu biyu rak ni
da kai,idan na
sami nasarar kashe ka nayi
alkawarin bazan kashe
ko mayaki daya ba daga cikin
dakarunka kuma
bazan rushe gida daya ba a cikin
birninka kona
koneshi amma kuma dole ne
alkawarina ya cika a
kan mazajenku wato dole ne na
maishe su bayin
mata.Koda jin wannan zabi sai
sarkin Misra yayi
shiru yana tunani daga can kuma
saiya juya da
baya yayi kuskus da shugaban
dakarunsa na yaki
sannan ya sake dawowa wajen
sarauniya Safirat
yace,na amince da wannan zabi da
kika bani na
muyi wannan yaki a tsakaninmu
mu biyu rak,idan
kin sami nasara a kaina ki idda
nufinki,idan kuma
nine na sami nasara a kanki saina
murkushe
birninki kuma namai da nufinki
akan
matayenku.Dajin haka sai Safirat
tayi murmushi
tace na amince da hakan,nan take
Safirat ta zare
takobinta taja da baya kadan da
dokinta,shima
sarkin Misra saiya zare tasa takobin
yaja da baya
kamar yadda tayi.Lokacin da suka
tasamma juna a
guje suna ruri da kururuwa sa'adda
kofaton
dawakansu ke kartar kasa suna
tayar da kura kai
kace wadansu manyan giwaye ne
biyu zasuyi karo
da juna saboda kasar wajen ce ta
kama girgiza,ai
kuwa suna haduwa suka kacame
da azababben
yaki na gaban kwatance,suna kan
dawakan nasu
suka rinka kaiwa juna sara da suka
cikin bakin
zafin nama,ya zamana cewa
kowannensu na kare
hare haren yana maida
martani.Duk sa'adda
takubbansu suka hadu saidai kaga
tarwatsin wuta
na tashi,saida suka shafe rabin sa'a
suna wannan
bakin gumurzu ba tare da dayansu
ya sami wata
nasara ba.Al'amarin dayayi matukar
baiwa Safirat
mamaki kenan kuma ya daure
mata kai saboda
sanin cewa tunda ta mallaki
wannan kwari da baka
babu wani jarumi da yake iya tare
hare harenta
saboda zafin namanta da kuma
karfin saranta,ya
akayi sarkin Misra yake iya karewa?
Tambayar da
Safirat tayiwa kanta kenan kuma ta
kasa baiwa
kanta amsa. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part C.
KUMA TA KASA BAIWA KANTA
AMSA.KODA
SARKIN MISRA DA SAFIRAT SUKA GA
SUN shafe
kusan sa'a guda suna wannan
bakin artabun ba
tare da dayansu ya sami wata
nasara ba sai duk
su biyun suka fusata ainun suka
soke dawakan
nasu da takubba suka durkushe
kasa dasu suka
zubar da su kasa.Take dawakan
suka mace,nanfa
Safirat da Sarkin Misra suka sake
ruguntsumewa
da sabon azababben yaki mai
tsananin tashin
hankali domin wannan karon sun
sauya salon fada
sun hada da kaiwa junansu naushi
da bugu da
hannu da kafa.Nanfa karfin yazo
daya ya zamana
cewa kowa yana rama abinda ake
masa.Nan da
nan suka hadawa junansu jini da
majina.Amma
duk sa'adda suka sari jikinsu da
takubba saidai
kaji kara na tashi tamkar karfe da
karfe.A sa'a
guda ya zamana cewa duk su biyun
sun jigata
ainun.Gaba daya rundunonin biyu
sun zuba ido
kawai suna mamakin yadda
wannan gumurzu ya
kasance haka.Har saida
kowannensu ya jigata
ainun,bisa dole suka ja da baya
sukayi cirko cirko
suna haki da kallon juna tamkar
zakaru.A wannan
lokaci ne kowannensu ya fara
tunanin abu na
karshe da zai yi ya cutar da abokin
gwaminsa.Kamar hadin baki sai
suka mike tsaye
tare suka juyawa juna baya,sukayi
tafiya taku
bakwai bakwai sannan suka juyo
da sauri suka
rugo da azababben gudu izuwa
kan juna suna ruri
da kururuwa kai da gani kasan
cewa mugun gamo
za'ayi wanda dole ne dayansu ya
bakunci
lahira.Koda ya rage saura baifi taku
uku ba su
hadu sai Safirat tayi wuf ta zare
bakin mayafin
dake lullube jikin kwari da bakanta
dake goye a
gadon bayanta.Shi kuma sarkin
Misra saiya
ambaci wadansu kalmomin tsafi
guda uku,ai kuwa
suna haduwa sai Safirat ta sami
nasarar lumawa
sarkin Misra takobinta a
cikinsa.Take takobin ta
faso gadon bayansa ya kurma uban
ihu,kawai sai
Safirat ta tsaya cak tana
murmushin farin ciki
amma kuma sai taji wani irin
mugun zugi a jikin
karamin dan yatsanta na
hagu.Koda ta dago da
hannunta ta dubeshi sai taga ashe
sarkin Misra ya
sami nasarar guntule danyatsanta
da kaifin
takobinsa jini na zuba.Take bakin
ciki da takaici
suka turnuketa.Sarkin Misra ya
dago kansa da kyar
a lokacin da yake kakarin mutuwa
ya dubi Safirat
kawai saiya bushe da dariyar
mugunta.Al'amarin
da yayi matukar girgiza Safirat
kenan kuma ya bata
mamaki ta dubeshi tace saboda me
kake yi min
dariyar mugunta alhalin mutuwa
zakayi?Koda jin
wannan tambaya sai sarkin Misra
yayi kakin jini ya
tofar a lokacin da idanunsa ke
lumshewa sannan
ya sake bude bakinsa da kyar yace
ina yin dariya
ne bisa dalili biyu,dalili na farko
shine na sami
nasarar cika alkawarina a kanki na
guntule miki
dan yatsan hannunki guda,lallai da
wannan tabo
zaki tafi har can kabarinki.Dalili na
biyu kuwa
shine a cikin binciken danayi a
hallarar tsafina
akwai wadansu jarumai guda biyu
da zasu bayyana
nan bada dadewa ba a wannan
nahiya tamu,sune
kadai jaruman da zasu iya tsayar
dake akan
wannan buri naki na maishe da
maza bayin
mata.Jarumi na farko ana kiransa
da suna Yarima
Musal'Asari daga birnin
Istanbul.Bani da cikakken
tarihinsa amma jarumtakarsa da
karfin addininsa
gami da sa'arsa sun nunka naki sau
biyu.Jarumi
na biyu ana kiransa Samazan kuma
zai fito ne
daga kasar Hindu,Jarumi Samazan
ya taba zuwa
har nan kasar tamu kuma munyi
abota ta tsawon
wata uku,kuma a wajensa na sami
horon yaki
kuma ya bani kaso daya a cikin
kaso uku na
sirrikan tsafinsa.A yanzu haka
tunda mutuwa zanyi
bazan iya baki labarinsa ba amma
ki nemi matata
Gimbiya Ulaimatu zakiji cikakken
tarihin rayuwarsa
a wajenta.Lallai haduwarki da
jarumi Samazan da
Yarima Musal'Asari shine karshen
tasirinki.Gama
fadin hakan keda wuya sai sarkin
misra ya
langwabe kansa ya mutu tsugunne
batare daya fadi
kasa ba.Safirat taci birnin misra da
yaki a saukake
kuma ta zauna da gimbiya Ilaimatu
inda ta fara
bata labarin jarumi Samazan.Kafin
ta fara bata
labarin saida gaba dayan mutanen
birnin maza da
mata suka hadu a babban fili
sannan ta fara basu
labarin kamar haka:-Dajin yayi tsit
tamkar babu
wani abu mai rai a cikinsa,babu
sautin kaduear
iska kuma babu sautin takun
sawaye walau na
mutum kona dabba,babu kukan
tsuntsaye dana
halittun daji.Komai jarumtakar
mutum idan ya
shigo cikin wannan daji sai yaji
tsoro kuma sai
yayi mamaki saboda akwai ni'ima
sosai a
dajin.Tarin bishiyoyi da yayan
itatuwa kuwa ga sun
birjik wasu ma sun gaji da nuna
sun rube,koramai
da fadamomi kuwa gasu nan cike
da ruwa garai
gari mai dadin dandano gwanin
ban shaawa.To
waishin menene ya hana tsuntsaye
da dabbobi
zama a cikinsa ba tare daya
fuskanci wata matsala
ba,wannan itace tambayar da
bakon mafaraucin
yayiwa kansa.Mafarauci Samazan
matashi ne dan
kimanin shekaru talatin da biyu,ya
kasance dogo
mai kirar sadaukai kuma
kyakkyawa ne wanda duk
mace datayi masa KALLO DAYA
saiya burgeta.Idan
ya fita yawon farautarsa yakanyi
shekara uku bai
koma kasarsu ta Hindu ba.Bayan
haka yanayin
tafiya mai nisa ya shiga cikin
dazuzzukan wadansu
kasashen.Tunda Samzan ya fara yin
farauta a
rayuwarsa bai taba yin dogon
zango ba irin
wannan domin yanzu ya shafe
shekara guda da
wata bakwai yana ratsawa ta cikin
dazuzzuka iri
iri.Samazan ya hadu da masifu iri iri
akan
hanyarsa domin ya fafata da
mugayen dabbobin
daji,yanfashi da mugayen aljanu,in
badon yana da
jarumtaka matuka ba kuma yana
da karfin sihiri da
tuni ya hallaka.A wannan doguwar
tafiya da yayi
tunda yana shaida inda ya nufa har
saida kansa ya
juye ya rasa ma inda ya nufa,shidai
a saninsa
bangaren birnin Misra ya durfafa
daga can birnin
Hindu to amma yanzu ya gane
cewa ya kaucewa
hanya ya shiga nahiyar da bai taba
shiga ba ma.
™Abubakar Haleefah Physicist™
Samazan ya kasance dan baiwa
domin tun yana
yaro karami duk abinda yasa a
gabansa yana
samun sanara sannan kuma yana
da basira gami
da hasashen akan abinda zai faru a
gaba,sau tari
ba sai yayi amfani da tsafi ba yake
gano inda
ma'adanan kasa suke ba don haka
yana amfani da
wannan dama tasa ya sami dukiya
mai yawan
gaske,bisa wannan dalili ne ko
kadan Samazan bai
damu da kudin da yake samu ba a
farauta.Wannan
ce tasa Samazan yake son ya
yawata a duniya
domin binciken inda ma'adanan
kasa suke,idan
yayi nazarin wuri yaga cewa bazai
iya hako dukiyar
ba shi kadai saboda sai anyi haka
mai zurfin
gaske,saiya nemi sarkin garin su
yayi yarjejeniya
akan cewa za'a biya shi wani kaso
idan akaga
dukiyar.Duk sa'adda akayi hakan
kuwa sai an
samu dukiyar.Hakance tasa mutane
suke matukar
mamakinsa suke ganin kamar da
aljanu yake
aiki.Ko kadan babu sa hannun
aljanu a cikin
al'amarinsa baiwace kawai da
kuma sanin sirrin
kasa bisa huldar yau da
gobe.Lokacin da Samazan
ya tsinci kansa a cikin wannan daji
mai ban al'ajabi
sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi
kuma yaji kamar
ya juya da baya ya fasa shiga
dajin.Amma daya
tuna doguwar tafiyar daya sha da
irin bakar
wahalar daya fuskanta da kuma
rashin sanin irin
albarkar dake wajen sai yayi
kundunbala ya saida
ransa ya cigaba da kunna kai
ciki,dama kuma yana
da wani babban buri a cikin
zuciyarsa.Saida
Samazan ya shafe sa'a uku yana
tafiya a cikin
wannan daji yana ratsawa ta cikin
kwazazzabai,duhuwoyi da surkuki
iri iri batare daya
hadu da wani mugun abu
ba.Kwatsam sai yayi
kicibus da wani katon rafi wanda
dole saiya ratsa
ta cikinsa sannna zai iya
wucewa.Koda ganin haka
sai Samazan ya karasa daf da rafin
ya tsugunna ya
kara kunnensa akan yashin dake
gabar rafin,take
ya gane cewa rafin yana da zurfi
sosai,kuma babu
mamaki a cikinsa a iya samun
mugayen halittu
duk da cewa bashi da tsawo
mutum zai iya
hayeshi a cikin rabin sa'a.Dan haka
akwai hadari a
shige shi,Kai tsaye ba tare da anyi
amfani da
kwale kwale ba.Nan take tunanin
sassaka kwale
kwale ya fado masa a rai.Daya
tabbatar da cewa
ba aiki bane na rana daya sai ya
sauke katuwar
jakar guzurinsa dake rataye a
bayansa ya kafa tanti
sannan ya dauki gatarinsa ya tafi
neman bishiyar
da zai saro yazo ya sassakata yayi
kwale kwale da
ita.Saida ya bata dan lokaci mai dan
tsawo kafin ya
sami bishiyar data dace.Yana ganin
bishiyar ya
kamu da farin ciki saiya ajiye
gatarinsa sannan ya
kwabe rigarsa.Wohoho kirar jiki irin
ta Samazan
dole ne ta burge mutum saboda
Allah yayi masa
damatsa,kwanji da jijiyoyi iri daban
dana sauran
sadaukai.Kana ganin siffarsa kasan
cewa dole ne
ya kasance GAWURTACCEN
SADAUKI.Batare da
bata lokaci ba Samazan ya dauki
gatarinsa ya
kama saran bishiyar aikuwa nan da
nan ya kaita
kasa a cikin kankanin lokaci saboda
karfinsa da
kuma kwarewarsa.Mafi akasarin
irin wannan
bishiya sai karti mutum biyu sun
far mata suke iya
kaita kasa a cikin sa'a guda,amma
sai gashi shi
Samazan ya kaita kas a cikin
lokacin da bai wuce
dakika dari tara da arba'in ba.Koda
share zufar
dake jikinsa baiyi ba saiya ciccibi
bishiyar ya
dorata a kan kafadarsa ta hagu ya
ruketa da hannu
daya sannan ya ruke gatarinsa da
hannu ya juya
ya nufi can bakin wannan rafi inda
ya kafa
tantinsa.Tun daga nesa mamaki ya
turnuke
Samazan kuma ransa ya baci,ba
komai ne ya
haddasa hakan ba face hango
tantin daya kafa baje
kas an yayyagashi.Koda ya hango
hakan saiya
rugo da gudu a fusace a tunaninsa
zaizo ya iske
wanda yayi masa barnar.Yana
zuwa daf da wajen
tantin sai yayi wurgi da bishiyar
daga kan
kafadarsa ya buda hannunsa mai
ruke da gatarinsa
sannan ya dubi gabas da yamma
kudu da arewa
kuma ya kasa kunne amma baiga
kowa ba kuma
baiji motsin komai ba.Al'amarin
daya fara fusata
shi kenan ya kurma uban ihu
nufinsa ko ma
menene yayi masa wannan barnar
ya jiyo
muryarsa ya dawo gareshi su fafata
amma sai yaji
shiru,koda ya dubi jakar guzurinsa
sai yaga an
fatattakata tamkar zabira aka sa
aka yanyanka
ta.Sai ransa ya kara baci fiye da
koyaushe.Ya
kama muzurai da numfarfashi
kamar zakin daya
fito farautar abinci yana fama da
yunwa.Tsawon
yan dakiku Samazan na tsaye yana
huci kamar
bakin kumurci kwatsam sai ya jiyo
wani irin
gurnani mai karfi daga cikin
karkashin wannan
rafi,nan take ya gane cewa abinda
yayi masa
wannan barna a cikin rafin
yake.Cikin hanzari
Samazan ya matso gaban gabar
rafin kuma ya zare
takobinsa wato ya hada makamai
biyu a hannunsa
ya zuba idanunsa akan cikin rafin
yana jira yaga
abinda zai fito daga ciki amma sai
yaji sautin
gurnanin ya dauke dif!Tamkar bai
taba jin sa
ba.Nanfa Samazan ya tsaya yana
shawara da
zuciyarsa akan ya shiga rafin yayi
nutso kasa
domin yaga ko menene a ciki ya
kashe shi ko
kuwa dai ya bari sai ya gama yin
kwale kwalen
sannan ya shiga.A karshe saiya
yanke shawarar ya
bari saiya gama kwale kwalen don
haka saiya
koma da

Please Login or Register in order to submit comment