Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma
masu kwarin gaske ne,cikin zafin
nama ya karyo
rassai guda biyu sirara musu
tsini.Karar rassan ne
yasa kadan ya tsaya cak ya juyo da
baya,ai kuwa
sai Samazan ya mike tsaye zumbur
ya ruga da
gudu izuwa inda kadan yake.Koda
kadan ya jiyo
takun sawun Samazan sai shima ya
rugo da gudu
izuwa gareshi,inda ace mutum
yana nan a lokacin
da wannan kada da Samazan suka
falfalo da
azababben gudu domin suyi
mugun gamo dole ne
yace Samazan ya haukace saboda
in ba mahaukaci
ba babu wanda zai yarda yayi gaba
da gaba da
wannan murgujejen kada.Koda ya
rage saura baifi
taku bakwai ba suyi muguwar
haduwa sai
kowannensu ya daka tsalle
sama,kadan ya
wangame bakinsa yana mai fesar
da wannan
mugun ruwa da nufin ya
hadiyeshi.Koda ruwan ya
zuba a sassan jikin Samazan saiya
kokkonashi
tamkar garwashin wuta aka watsa
masa amma bai
narke ba.Samazan ya kaucewa
hadiyar kadan ya
lafo gadon bayan da hannu daya ya
dane bayansa
sannan ya daga wadannan siraran
rassan bishiya
guda biyu ya caka su a cikin
fasasshen kwayar
idanuwan kadan.Take rassan suka
lume a ciki
idanun suka fasa ta bayan kan
nasa.Take kadan
yayi wani irin ruri da gurnani mai
matukar ban
tsoro a lokacin da jini ya kama tsiri
sama daga
cikin idanun kadan kuma ya fado
kasa tim.Ya
kama birgima wacce ta haifar da
girgizar
kasa,shima Samazan saiya fado
kasa ya mirgina
can gefe daya don kada jelar kadan
ta ragargaza
shi sakamakon jehota da yake
izuwa ko
ina.Sakamakon mirginawar da
Samazan yayi sai
raunin gadon bayansa ya bugu da
jikin wata
bishiya take ya baje a kasa
sumamme.Samazan
bai farfado daga dogon suman da
yayi ba sai
bayan sa'a daya da rabi lokacin da
wata irin iska
mai karfi ta rinka kadawa,tasa
ruwan wannan rafi
ya kama yin ambaliya har ruwan ya
watso kan
Samazan,Samazan na farkawa sai
yaji raunin
gadon bayansa a daure tamkar
igiya akasa ka
zagaye bayan nasa.Koda yakai
hannun nasa ya
shafa raunikan sai yaji an dinke
shi,cikin firgici ya
yunkura zai mike tsaye sai yaji an
danne shi ya
kasa koda motsa ko ina a
jikinsa.Sannan kuma sai
yaji an kece da mahaukaciyar
dariya.Take wani irin
shudin hayaki ya baiyana tsulum a
gabansa kuma
sai hasken ya rikide ya zama wan
dan guntun
aljani wanda baifi a kife shi da
kwando ba,kansa
rantalele ne yafi gangar jikin girma
amma
fukafukansa yan kanana ne tamkar
na dan
tsako,gangar jikinsa siffar jemage
ce ba kyan gani
abin tsoro.Aljanin sai ya risina ga
Samazan ya
gaishe shi cikin girmamawa sannan
yace gaisheka
sarkin sadaukan duniya,hakika ka
ajiye tarihin da
har abada duniya ba zata taba
mancewa da kai
ba.Domin ka kashe kashe dabbar
data gagari
dukkan jaruman aljanu da
bil'adama tsawon
shekara ashirin.Lokacin da Gimbiya
Ulaimatu tazo
daidai nan a labarinta rana ta fadi
gari ya soma yin
duhu don haka sai sarauniya Safirat
ta tari
numfashinta tace dakata haka bana
son kowa yaji
karshen wannan labari face ni,zan
kira ki ki karasa
mini labarin a lokacin da muka
kadaita mu biyu
jal,A cikin daki bayan na nada muku
sabuwar
sarauniyarku.Koda gama fadin
hakan sai sarauniya
Safirat ta mike tsaye nan take gaba
dayan dakarun
yakin birnin suka zube kasa a
gabanta suna masu
mika mubaya'arsu.Nan dai taro ya
watse kowa ya
kama gabansa.Lokacin da
Sarauniya Safirat ta
shiga cikin turakar sarkin misra ta
kwanta akan
gadon da nufin tayi bacci sai ta
kasa saboda
tunanin mutum uku,mutum na
farko shine marigayi
sarkin misra kuma ba komai take
tunowa ba'a
kansa face maganganunsa na
karshe kafin ya
mutu.Mutum na biyu kuwa shine
Yarima
Musal'Asari wanda akace a halin
yanzu ya fito
farautarta,gashi da sa'a da kuma
karfin sihirin
tsafi.To waishin ma ta yaya zata iya
kare kanta
daga sharrin wadannan jarumai
biyu kuma waishin
yaya karshen labarin Jarumi
Samazan zai kasance
kafin ta hadu dashi.Nan take Safirat
ta yanke
hukunci a cikin ranta cewar ba
gudu ba ja da baya
a kan nufinta na maishe da dukkan
mazajen
duniya bayin mata kuma zata
cigaba da bincike a
cikin hallarar tsafinta domin ta
gano hanyar da zata
hallaka Yarima Musal'Asari da
jarumi Samazan tun
kafin su risketa.
SHIN SARAUNIYA SAFIRAT ZATA CIKA
BURINTA NA
SAUKE SARAKUNAN DUNIYA KAF
DAGA KAN
KARAGARSU TA MULKI TA DORA
MATA AKAI?
TSAKANIN YARIMA MUSAL'ASARI DA
JARUMI
SAMAZAN WAI ZAI FARA HADUWA
DA SARAUNIYA
SAFIRAT KUMA IDAN SUN HADU
MENENE ZAI
FARU?
SHIN YAYA KARSHEN SAFIRAT YAKE
KASANCEWA?
Mu Hadu A Kibiya Ratsa Maza Littafi
Na Shida Don
Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen
Kayataccen
Labari.
Alhamdulillah.End Of Kibiya Ratsa
Maza (5).Dama
Kamar Yadda Na Fada Kafin Na fara
Littafin 1-5 ne
ya fito.To kuma gashi Allah yasa
mun kammala
shi.So sai muyi jiran fitowar
cigabansa nan bada
jimawa ba.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment