Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace nasan kana jin yunwa sai
ka fara cin
wannan ko..?Da jin haka sai takaici
ya turnuke
sarki Safwan ya tuna cewa shifa
sarki ne mai
isasshen iko amma wai shi za'a
wulakanta
haka.Safwan ya dubi Safirat cikin
tsananin fishi
yace zaifi kyau ki kashe ni domin
bazan yarda
kici
gaba da muzanta ni ba haka sai
kace wata
dabbar
daji,kin kulleni a cikin keji kina bani
dan
itaciya.Dana cigaba da rayuwa a
haka gwara ma
na
kashe kaina.Koda jin haka sai
Safirat ta bushe da
dariya lokaci guda kuma ta turbune
fuskarta,tace
bazan kashe ka ba kuma kaima ba
zaka iya
kashe
kanka ba saboda rayuwarka da
komai naka yanzu
a hannuna yake.A nan nan cikin
wannan keji
zaka
kwana duk sanyin nan da akeyi a
kanka zai kare
kuma babu wani abinci da za'a
sake baka face
wannan ayaba,idan ka cinyeta za'a
baka ruwa
makurwa hudu kasha saida
safe.Koda gama
fadin
hakan sai safirat ta juya ta koma
cikin tantinta
taje
tayi kwanciyarta.Fitarta keda wuya
sai Sarki
Safwan
ya fusata ainun zuciyarsa ta kama
tafarfasa
kamar
zata kone saboda bakin ciki don
haka sai ya
yunkura domin ya kama kansa da
hannayensa
biyu
da nufin ya murdewa kansa wuya
amma sai yaji
hannayen nasa sun daskare ya kasa
matsa su
kuma yaji wani irin mugun zugi da
radadi ya
shigeshi bai san sa'adda ya kwalla
ihu ba.Kawai
saiya bingire kasa.A haka Sarki
Safwan ya
kasnace
yana shan azaba ta radadi har gari
ya waye,saida
Safirat ta farka daga bacci taci
abinci tayi wanka
kuma ta gama kintsawa sannan
tazo tayi nuni da
hannunta izuwa kan Safwan
sannan ya daina jin
zafin da yake ji.Kuma ya iya sauke
hannayensa
kasa daga jikin kansa.A wannan
lokaci zazzabi
ya
rufe sarki Safwan sakamakon
kwanan da yayi a
cikin sanyin.Nan take Safirat tasa
aka bude kejin
a
ka fito da Safwan a matukar
galabaice ga yunwa
kuma ga rashin lafiya.Nan take tasa
aka bashi
abinci mai rai da lafiya yaci ya koshi
kuma aka
bashi magani yasha,gama hakan
keda wuya sai
aka mayar da sarki Safwan cikin
kejinsa aka
kulle.Haka dai Jaruma Safirat ta
cigaba da
wulakanta Sarki Safwan har tsawon
kwanaki uku
kuma sau bakwai sarki Safwan
yana yunkurin
kashe kansa yana kasawa.A ranar
kwana na
ukunne da farko yammaci saiga
dodo Gargus ya
dawo tare da amayarsa.Koda
ganinsu sai Safirat
ta
ruga garesu cikin matukar farin ciki
ta
rungumesu
kuma nan take tasa akayi shiri aka
cigaba da
tafiya
aka durfafi birnin kisra.Wannan
shine Abinda ya
faru ga jaruma Safirat bayan ta
sami nasarar
mallakar Kwari Da Bakanta wanda
mahaifinta
Boka
Saiham ya sana'anta.Kwari Da
Bakan da duk
wanda ya mallakeshi tamkar ya
mallaki duniya
ne.
*Al'amarin ragowar manyan
sarakai kuwa da
manyan matsafa da jarumai
wadanda suka zo
yakar Jaruma Safirat domin su
rabata da kwari
da
bakanta sai kowannensu ya koma
izuwa garinsu
cikin rashin kwarin guiwa,tashin
hankali da
matukar damuwa don haka sai
sukayita yada
labarin rashin nasarar da
sukayi.Nan da nan
kuwa
labarin ya bazu ko ina cikin
kasashen
duniya.Koda
sarakuna sukaji wannan labari sai
cikinsu ya fara
durar ruwa saboda babu wanda
yake son a
rabashi
da karagarsa ta mulki a maishe shi
bawa.Wasu
sarakuna kuwa sai suka rinka yin
dariya suna
karyata wannan labari domin basu
ma yarda da
cewa akwai wannan kwari da
bakan ba a duniya
wadda ake cewa jaruma Safirat ta
mallake
shi.Wadanda bokayensu sukayi
bincike suka
tabbatar musu da cewa lallai
wannan labari
gaskiya
ne sai suka fara shirya taro na
musamman domin
susan hanyar da zasu bullowa
al'amarin tun kafin
abin yazo ya riskesu har gida.Nan
da nan sunan
jaruma Safirat ya tumbatsa a
duniya ya
zamanacewa ana kodata fiye da
yadda ma take.
*A CAN BIRNIN ISTANBUL kuwa
wacce ta
kasance
DAULAR MUSULUNCI,Sarkin dake
mulkinsu ya
kasance wani dattijon mutum
wanda shekarunsa
sun haura casa'in,tsufa ta riske shi
amma yana
da
'da guda daya jal wanda ake kira
da suna Musal
Asari.Yarima Musal'Asari ya kasance
sadaukin
jarumi kuma zarto mai tarwatsa
maza a filin
daga,baya ga haka ya kasance
jarumi mai
tsananin
saa bisa duk abinda yasa a
gabansa.Domin tunda
ya zama cikakken saurayi duk gasar
da aka
shirya
a nahiyar shike zama zakaranta
walau a cikin
biranensu na musulmai ko a
biranen ma'abota
bautar wanin Allah.Bisa wannan
dalili ne Yarima
Musal'Asari ya zama sananne kuma
mai matukar
farin jini a wajen yan mata amma
ko kadan
hankalin Musal'Asari baya kan
SOYAYYA da
AURE.Burinsa guda daya ne jal a
duniya kuma
tun
yana yaro karami yaso ya cika
wannan buri
amma
sai mahafinsa yaki ya bashi damar
hakan.Ba
komai
bane burin Yarima Musal'Asari face
ya zagaye
gaba dayan kasashen dake cikin
daular larabawa
™ Prince Auwal Auwzab ™
yaga kowacce irin kabila gami da
al'adunsu da
addininsu kuma ya rubuce shi
domin ya zamo
abin tarihi.Mahaifin Musal'Asari
bashi da kowa a
duniya face shi,Mahaifiyarsa ma tun
yana da
shekara hudu a duniya ta rasu
sakamakon wata
rashin lafiya.Bisa wannan dalili ne
sarki yake
mutuwar son Musal'Asari fiye da
komai a
rayuwarsa kuma ko kadan baya
yarda ya nisanta
dashi.Ana cikin wannan hali ne
fatake suka kawo
labarin baiyanar jaruma Safirat
izuwa cikin birnin
Istanbul inda akayi ta yada jita jitar
cewa sai
wannan jaruma ta mulki duniya
gaba dayanta,a
hankali kuma saita maishe da
mazan duniya
bayin
mata.Lokacin da wannan jita jita ta
yawaita a
gari
saisarki Suleman wato mahaifin
yarima
Musal'Asari ya tara gaba dayan
fadawansa a
cikinsu harda sarkin Yaki
Musal'Asari.Sarki
Suleman ya rufe su da fada yana
mai cewa yaya
za'ayi a bari ana ta watsa wannan
jita jita a cikin
birninsu na musulmai.Nan take aka
kafa doka
akan
cewa duk wanda aka kama yana
wannan magana
ma za'a sa dakaru su kamashi a
kawo shi fada
ayi
masa hukunci tunda dai wannan
al'amari ne na
matsafa da masu hasashen
banza.Hakane tasa
dole bakin da suke shigowa birnin
da wannan
zance suka tsuke bakunansu amma
duk da haka
ba'a fasa yin maganar ba.A boye
cikin gidaje ana
gulma,ba komai bane ya haddasa
hakan ba face
a
wannan lokaci akwai Ahalilkitabi a
cikin birnin na
Istanbul kuma sunayin addininsu
na lumana tare
dasu bisa yarjejeniya.Bayan cikar
kwana uku
dayin
taro sarki Suleman da yan
majalisarsa sai
sarki
Suleman yayi wani mafarki wanda
ya girgiza shi
kuma ya firgita shi ainun ya
zamana cewa
hankalinsa ya dugunzuma ainun
fiye da koyaushe
a rayuwarsa.Ba komai ne ya jefashi
cikin hali ba
face tun yana yaro karami dan
kimanin shekara
shida duk abinda yayi mafarki
akansa to sai
wannan abu ya faru a gaske.A Cikin
mafarkin
nasa
aka nuna masa baiyanar jaruma
inda ta ci
manyan kasashen labarawa guda
hudu da yaki ta
sauke sarakunansu daga kan mulki
ta sanya
mata
a madadinsu.Sannan ta nausa wani
bangaren
daban na duniya inda ta cigaba da
cin kasashe
da
yaki.Sannan kuma ta sake shirin
afkawa sauran
kasashen larabawan data bari a
baya.A daidai
nanne sarki Suleman ya farka daga
baccinsa a
razane yana mai rafka salati.A
wannan rana dai
jikin sarki Suleman yayi sanyi sosai
matuka,kuma
ya kasa cin abincin kirki saida kyar
aka
tursasashi
yaci abincin kadan.Bisa wannan
dalili ne yasa
aka
yi
taron gaggawa inda ya baiyana
musu labarin
mafarkin da yayi.A hakane akai ta
kawo hujjoji
akan dole a tashi a kare kai.Yarima
Musal'Asari
ya
dubi mahaifinsa yace,Ya Abbana ka
bani dama
domin na fita izuwa sauran
kasashen duniya
domin naje na daukaka kalmar
Allah.bisa babu
yadda za'ayi Sarki Suleman ya
amince da
maganar
dansa duk da cewa yana matukar
kaunarsa baya
son rabuwa dashi koda ta dakika
daya ce.Sarki
Suleman ya ce da Yarima
Musal'Asari idan har
ya
dawo gida zai zaba masa matar
data dace dashi
muddin ya dawo ya iskeshi a raye
kuma a
sannane zaiyi murabus ya bashi
Karagarsa.Koda
Sarki Suleman yazo nan a
jawabinsa sai hawaye
ya
subuto masa kawai sai ji yayi
Musal'Asari ya
rungumeshi ta baya shima ya fashe
da kuka,ba
komai ne yasasu yin kukan ba face
wannan shine
karo na farko da zasu taba rabuwa
arayuwarsu ta
tsawon kwanaki ko watanni tun
daga haihuwar
Yarima Musal'Asari kawo
iyanzu.Kashe gari kuwa
da sassafe sarki yasa akayi
shela.Fada ta cika ta
batse da mutanen gari gami da
fadawa,bayan
kowa ya hallara sai sarki ya mike
yayi bayanin
cewa Yarima tare da dakaru dari
uku zasu tafi
izuwa gabashin kasashen labarawa
domin
daukaka
kalmar Allah.Koda jin wannan batu
sai jama'a
aka
rude da kabbara kuma aka kamu
da tsananin
mamakin yadda sarki ya sallama
rayuwar yarima
don tafiya wannan JIHADI.Kuma
kowa ya sani
cewa
daidai da rana daya sarki baya son
rabuwa da
yarima.Ba tare da bata lokaci ba
Yarima da
dakarunsa su dari uku suka gama
kintsawa
dukkaninsu sukayi bankwana da
iyayensu da yan
uwansu dama gaba dayansu
samari ne matasa
babu mutum daya mai aure a
cikinsu don haka
sunaji da samartaka,karfi iya yaki
da kuma
jajurcewa bisa duk abinda suka sa a
gaba.Saida
aka rako wannan runduna har
izuwa bayan
gari,yawancin wadanda suka rako
su din yan
mata
ne masoyansu,wasu ma ansa ranar
bikinsu,lokacin
da bai wuce shekara daya ba.Kowa
ka gani da
budurwarsa amma banda Yarima
Musal'Asari
wanda shi koda wasa ma bai taba
cewa yana son
wata budurwa ba Kamar ni Prince
Auwal Auwzab
Auwzab hmmmmm saura wani
yace ba haka
bane, kuma duk waccce ma tace
tana
sonsa fa to ta yankawa kanta kazar
wahalar da
bazata iya figeta ba.Nan dai
masoya suka kama
kuka da alhinin rabuwa sunajin
kamar su fasa
wannan tafiya har al'amarin ya
fusata yarima
Musal'Asari ya dakawa dakarun
nasa tsawa,kowa
tsoron fishin yarima Musal'Asari
yake dan haka
dakarun suka haye dawakansu
sukayi gaba suna
waigen masoyan nasu har saida
sukayi nisa a
cikin daji suka bace musu da
gani.Mafi akasarin
wadannan zakwakurun jarumai
guda dari uku
sa'annin yarima Musal'asari ne
kuma abokansa
ne
domin tare suka taso,tare sukayi
wasa don haka
akwai shakuwa gami da fahimtar
juna a
tsakaninsu.Wani lokacin ma idan
suna hira da
wasa da
dariya mutum bazai iya ganewa
cewa ko 'ya'yan
talakawa bane shi kuma dan
sarki.Yarima
Musal'asari yana da matukar saukin
kai,kawaici,kunya,jinkai da sanin ya
kamata,amma
kuma baya son zalunci,rainin
hankali,girman kai
da
wulakanci.Sai da wannan runduna
ta shafe sa'a
bakwai da rabi tana ketawa ta cikin
dazuzzuka
har
yazamana cewa sun fita daga
yankin cikin kasar
su ta Istanbul sun nausa nahiyar
birnin Yemen ba
tare da sun yada zango ba ko sun
hadu da wani
mugun abu ba.Adaidai wannan
lokaci sallar
Azahar
Tayi don haka
™ Prince Auwal AUW.ZAB ™
sai Yarima ya bayar da umarnin a
yada zango
domin ayi sallah.Nan take kuwa
aka tsaya aka
kafa
tantuna sannan akayi alwala
yarima ya shige
gaba
yayi limanci akayi sallah.Bayan anyi
addu'a an
shafa ne sai kowa ya fiddo abincin
kalacinsa ya
kama kimtsa cikinsa,shi kuwa
yarima sai ya
koma
gefe daya ya zuba musu idanu
kawai yana lazimi
yana murmushi.Koda ganin haka
sai shugaban
dakarun wanda ake kira da Samhar
ya taso daga
inda yake zaune dauke da
gasasshen nama yazo
daf da yarima ya zauna kuma yayi
masa tayin
naman,yarima ya girgiza kai yace ai
ni ma inada
irin wannan nama da kake ci amma
bana
sha'awar
cinsa ne.Samhar ya dubi Musal'asari
cikin
mamaki
yace haba ya shugabana rabonka
da abinci fa
tunda asuba da mukayi kalaci kafin
mu baro gida
kuma na tabbata cewa kana jin
yunwa ko kuwa
baka da lafiya ne?Koda jin wannan
tambaya sai
yarima ya dafa kafadar Samhar ya
dubeshi cikin
murmushi yace tabbas ina jin
yunwa amma bana
sha'awar cin komai face sabon
nama wanda aka
yanka yau ko tsuntsun da aka
harbo a yau don
haka yanzu ni zan shiga daji na
farauto abinda
zanci.Gama fadin hakan keda wuya
sai yarima
ya
mike tsaye ya dauko kwari da
bakansa ya rataya
su a gadon bayansa kuma ya daure
takobinsa a
kugunsa.Take shima Samhar ya
mike ya kama
shirinsa bisa ganin hakan sai
yarima ya dubi
Samhar yace ka sani cewa babu
sama dani dakai
a
cikin dakarun nan,idan babu ni
babu kai waye zai
basu umarni idan wani bala'in ya
taso ba zato?
Samhar ya gyada kai yace nasan da
haka amma
ka
sani cewa ba zamu bari ka shiga
daji kai kadai
ba
dole ne mu baka kariya duk da
cewa mun san
zaka
iya kare kanka kuma Allah zai
kareka daga
dukkan
abinki,bisa wanann dalili zan hada
ka da mutum
hudu ni kuma zan zauna na kula da
sansanin.Koda
jin haka sai yarima yayi murmushi
ya sake dafa
kafadar Samhar a karo na biyu yace
da kyau
abokina,hakika kana da basira gami
da hangen
nesa shi yasa nake matukar son
zama tare
dakai.Nan take Samhar ya zabo
mutum hudu
wadanda suka san sirrin daji kuma
manyan
barade
sha gwagwarmaya a filin daga ya
hadasu da
yarima suka sashi a tsakiya don
tabbatar da
tsaro
suka nausa izuwa cikin daji.Yarima
da dakarun
nasa mutum hudu sukayita
kutsawa a cikin daji
suna dube dube da hange hange
amma saida
suka
shafe kusan rabin sa'a ko dan
karamin tsuntsu
basu ga giftawarsa ba bare wata
dabba.Al'amarin
daya basu mamaki kenan,Yarima
ya yiwa sauran
dakarun nasa hudu inkiyar su
tsaya.Take
kowannensu ya tsaya a inda
yake.Yarima ya dubi
gabas da yamma,kudu da arewa da
kuma sama
da
kasan dajin yayi nazarin komai
dake wajen,kawai
sai yayi murmushi yace akwai
mugayen yanfashi
a
wannan daji kuma mugayen
dabbobin da suka
hana kananun tsuntsaye da halittu
shi yasa muka
kasa farauto koda zomo guda
daya.Gama fadin
hakan keda wuya sai Yarima ya
bude bakinsa
yana
mai cewa idan mutane ne yan
uwanmu labe a
wannan wuri ku baiyana kanku in
ba so kuke
taku ta kare ba,ai kuwa kafin
yarima ya gama
rufe
bakinsa sai sukaji an bushe da
mahaukaciyar
dariya a cikin wata murya mai
kauri da kaushi
daga sama.Kafin su yarima su daga
kawunansu
sama suga maiyin wannan dariya
tuni dakaru
sama da mutum dubu sun sauko
daga saman
bishiya a cikin shigar bakaken
tufafi,fuskokinsu a
rufe,idanunsu kadai ake gani kuma
kowannensu
na
ruke da muggan makamai.Nan da
nan suka yiwa
su Yarima Musal'asari kawanya
daga can sai ga
shugaban dakarun wani narkeken
kato mai siffar
mutanen farko ya ratso ta cikin
duhuwar ciyayi
yana safe da wata sharbebiyar
adda bisa
kafadarsa
babu riga a jikinsa kuma babu
takalmi a
kafarsa.Dogon wando ne na fatar
jimina kacal a
jikinsa sai kuma tarin guraye na
tsafi a jikin
hannayensa da kugunsa,kallo daya
zakayiwa
wannan narkeken kato ka gane
cewa rikakken
dan
fashi ne wanda bai san wani abu
waishi tausayi
ba,da ganin kura kasan zata ci
mutu.Allah ne
kadai
yasan iya adadin rayukan da
wannan shirgegen
mutum ya salwantar.Koda wannan
kato yayi arba
da yarima Musal'asari sai ya kare
masa kallo
sama
da kasa,daidai ya ganshi a cikin
suturu mai kyau
mai tsada kuma ya dubi dakarunsa
ya gansu a
cikin shigar dakarun gidan sarauta
saiya bushe
da
dariyar farin ciki mai kama da
kukan jaki bisa
ganin karensa ya kama
zomo.Lokaci guda kuma
saiya turbune fuskarsa tamkar an
aiko masa da
sakon mutuwa ya dakawa yarima
tsawa yace
yakai
wannan kyakkyawan matashi ina
mai umartarka
daka gaggauta baiwa yaranka
umarni da su
zubar
da makamansu,kuma su tattaro
duk abinda kuka
mallaka ku zube su anan gabana
idan kuna son
ku
wuce wannan daji a raye,in ba haka
ba kuwa
yanzun nan zamuyi muku kisan
gilla gaba
dayanku
sannan mu kwashe dukiyar taku da
ababan
hawanku
a matsayin ganima.Koda jin
wannan batu sai
Yarima ya jiyo ya dubi gaba dayan
dakarun nasa
yace dasu su zubar da
makamansu.Cikin
tsananin
mamaki da kaduwa dakarun sukayi
tsuru tsuru
suka rasa abinda zasuyi saboda
sunsan cewa
indai
za'a fafata zasu iya kawar da
wadannan
yanfashi
duk da cewa sun ninkasu sau uku a
yawa.Har
Hamsar ya bude baki zaice wani
abu ga yarika
sai
ya tari numfashinsa ya daka masa
tsawa yace
zakubi umarni nane ko kuwa a'a?
Dajin haka sai
Hamsar da sauran dukkanin
dakarun suka cire
takubbansu da sauran makamansu
na yaki suka
zube kasa.Koda ganin haka sai
Yarima
Musal'asari
ya dubi shugaban yanfashin yace
yanzu zan baka
zabi guda biyu kamar yadda ka
bani.Ka umarci
dakarunka su duka su yakeni ni
kadai ko kuma
mu
fafata ni dakai kawai.Idan ni da
dakarunka ne
zamu
fafata nayi maka alkawarin cewar
da izinin
ubangijina dayansu bazai tsira da
rauwarsa
ba.Idan kuma ni dakaine to zan
kasheka kuma
ranka fansar na yaranka ne......... °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Uku (3)
Part C
Kuma ranka ne fansar na yaranka
ma'ana zan
kyale su su rayu a matsayin bayina
kuma dole ne
su karbi addini na.Koda Yarima
Musal'asari yazo
nan a zancensa sai shugaban yan
fashin da yaran
nasa gaba dayansu suka bushe da
dariyar
mugunta sukayi ta kyalkyala
dariyar kamar bazasu
daina ba har saida shugaban nasu
ya tsuke
bakinsa sannan suma kowannensu
yayi
tsit.Shugaban yanfashin ya sauke
lafceciyar addar
tasa kas daga kan kafadarsa yana
mai gyar
tsayuwarsa sannan ya dubi Yarima
Musal'asari
cikin tsananin fushi gami da
kakkausar murya yace
ni zan yake ka kuma idan na kashe
ka zan kama
dukkanin wadannan yara naka
nayita gana musu
azaba mai radadi,daya bayan daya
har sai
kowannensu ya riski ajalinsa.Kafin
shugaban yan
fashin ya gama rufe bakinsa tuni
yarima ya zare
takobinsa ya ruga izuwa kansa sun
runguntsume
da azababben yaki,sauran
yanfashin da dakarun
yarima kuwa sai suka zama yan
kallo suka zubawa
SARAUTAR ALLAH ido.Yarima da
shugaban
yanfashin suka wanzu suna kaiwa
junansu sara da
suka cikin bakin zafin nama juriya
da jarumtaka
taban al'ajabi.Ana fara wannan
gumurzu ne
shugaban yanfashin ya cika da
mamaki kuma ya
gane cewa lallai ya hadu da jarumi
abin kwatance
saboda wannan ne karo na farko
daya hadu da
jarumin daya iya tare dukkan hare
harensa harma
yake iya maida martani.A tarihin
gumurzunsa a
cikin dakika ashirin yake bazar da
mayaki komai
karfinsa girmsa da iya yakinsa
amma sai gashi sun
shafe kusan dakika dari uku da
ashirin suna bakina
artabu shi da yarima Musal'asari
amma ya kasa
koda lakutar jikinsa.Idan kuwa ya
naushi mutum a
mukamukin fuska saidai kaji karar
karyewar kashin
mukamukin amma sai gashi yarima
yana shanye
duk naushin nasa kuma yana
maida martanin
dashi baya ma iya shanye shi
domin duk sa'adda
Yarima ya gabzawa katon naushi
sai yayi taga taga
da baya kamar zai fadi,tsananin
juriyace take sawa
yaki faduwa.Nan da nan suka
hadawa junansu jini
da majina amma cikin kankanin
lokacin shugaban
yanfashin ya fara jigata.Al'amarin
daya baiwa kowa
mamaki kenan a wajen saboda
gashi dai a zahiri
shugaban yanfashin yafi yarima
girma,kaurin
gwanji da kwarjini amma sai gashi
yarima ya fara
luguiguitashi.Har saida takai cewa
takobin katon ta
subuce daga hannunsa ta fadi
kasa,koda ganin
haka sai shima yarima ya jefar da
tasa takobin ya
tsaya suka kama kallon kallo
tsakaninsa da
shugaban yanfashin sukayi cirko
cirko suna kallon
juna a lokacin da jini ke diga a
hancinsu da
bakinsu.Duk wanda ya kallesu a
wannan lokaci
yasan cewa nazari da tunani sukeyi
akan yadda
zasu sami nasarar hallaka
juna,saida suka shafe
yan dakiku kadan suna tunani da
nazarin juna
cikin mugun nufi kai da gani kasan
mugun gamo
za'ayi wanda dole ne abu daya
cikin biyu ya
faru.Kodai ayi ragas ko kuma daya
ya kashe
daya.Koda ya rage saura baifi taku
biyar ba su
hadu sai kowannensu ya daka
tsalle sama,ashe
akwai wata karamar wuka a soke a
bayan
shugaban yanfashin don haka yana
saman sai yayi
wuf ya zaro wuka cikin zafin nama
ya kirbawa
yarima ita a gefan kirjinsa na
hagu.Take wukar ta
lume a gefan kirjin nasa,yarima ya
kwala kabbara
da karfin gaske sakamakon mugun
zafin daya ji a
lokacin da jini yayi tsartuwa daga
cikin ramin
wukar inda tayi masa rauni,amma
saiya daure ya
sakalo wuyan katon da kafafunsa
biyu suka fado
kasa tare.Yarima ya shake wuyan
shugaban
yanfashin da kafafun nasa a lokacin
da jini ke zuba
a kirjinsa,nanfa shugaban yanfashin
yasa
hannayensa biyu ya fara kokarin
banbare kafafun
yarima daga cikin wuyansa.A
lokacin ne
kowannensu ya dage iya
karfinsa,kwanjin
shugaban yanfashin ya kumbura
kuma jijiyoyin
hannunsa suka tashi sukayi burdin
burdin ya kama
ruri da ihu irin na manyan mazaje
sai yayi kamar
zai sami nasarar banbare kafafun
na yarima saiya
kasa.A haka dai yana ji yana gani
Yarima ya
cigaba da shake masa wuya har
numfashinsa ya
fara sarkewa yana karkarwa ya
rinka wutsil wutsil
da kafafunsa.Yaransa suka yunkuro
da nufin kawo
masa dauki sai dakarun yarima
sukayi wuf suka
dauki makamansu suka sha
gabansu.A haka dai
yarima ya sami nasarar kashe
shugaban yanfashin
ya zamana cewa jikinsa gaba daya
ya sandare ya
daina motsi,shi kuwa yarima saiya
mike tsaye
amma yana tangadi jiri na dibarsa
dauke da
takobinsa ya nuna yanfashin da ita
yace kun yarda
ku zama bayina ko kuwa kuma
zaku yakemu?Koda
jin wannan tambaya sai gaba
dayan yanfashin suka
zubar da makamansu suka durkusa
kasa bisa
guiwoyinsu suna masu yin
mubaya'a,faruwar
hakan keda wuya sai dakarun
yarima sukayi sauri
suka kwashe makaman yanfashin
kuma sukayi
musu kawanya suka ritsa
su,adaidai wannan lokaci
yarima Musal'asari ya yanke jiki ya
fadi kasa
sumamme,cikin dimauta Hamsar ya
rugo izuwa
gareshi ya shiga duba raunin nasa
kuma ya bayar
da umarnin a gaggauta kafa tantin
Yarima.Bayan
an kafa tantin ne an shimfidar da
yarima a ciki
kamar gawa,an cire wukar dake
lume a cikin
kirjinsa aka gano cewa akwai
mugun dafi a jikin
wukar.Nan take wani badakare
masanin dafi ya
duba raunin da kyau,nan take gumi
ya karyi masa
ya dubi Hamsar cikin alamun firgici
yace ya
shugaban dafin dake jikin wannan
wuka daga jikin
wani irin maciji na birnin Kisra aka
samo shi,dole
sai an samo irin macijin sannan za'a
sami
makarinsa,abin da zan iyayi kawai
a yanzu shine
na dakatar da dafin daga yaduwa
izuwa dukkan
jijiyoyin jikin yarima kuma zan iya
yin hakanne
kawai tsawon kwanaki uku,idan
aka wuce wannan
lokaci yarima zai iya rasa
rayuwarsa saidai kuma
wani ikon na Allah.Koda jin wannan
batu sai
hankalin Hamsar dana sauran
dakarun ya
dugunzuma ainun cikin alamun
™Abubakar Haleefah Physicist™
tsananin damuwa Hamsar ya dubi
masanin dafin
yace yanzu daga nan zuwa birnin
Kisra tafiyar
kwana nawa ce?Masanin dafin daya
ji haka sai
yace a kalla sai mun shafe kwani
hudu da
rabi.Koda jin haka sai Hamsar ya
mike tsaye
zumbur ya dubeshi yace da izinin
Allah zamu isa
can din kafin cikar kwanaki uku
daka
ambata.Hamsar ya dubi gaba
dayan yanfashin yace
yanzu kun zama bayinmu gaba
dayanku amma
zaku iya zama yantattu bisa
sharadi guda,sharadin
kuwa shine zaku tuba daga yau
kun daina wannan
muguwar sana'a taku ta fashi har
abada kuma
zaku karbi Addinin Musulunci yanzu
take,inba haka
ba kuwa zamu kashe ku a yanzu
take.Koda jin
wannan batu sai gaba dayan
yanfashin sukace sun
amince su karbi Addinin
Musulunci.Ba tare da bata
lokaci ba Hamsar ya biya musu
kalmar shahada
suka maimata gaba dayansu.Nan
da nan akayi
shirin tafiya aka dora Yarima akan
dokin Hamsar
aka cigaba da tafiya ba sassauci
domin a isa
birnin kisra kafin cikar kwanaki
uku.Yarima yana
cikin wani irin yanayi mai kama da
dogon suma
domin bain san a halin da yake ciki
ba kuma bai
san wanda ke kusa dashi ba.
End Of Book 3.
TURKASHI!!!
Sai Muje Zuwa Ga Littafin Kibiya
Ratsa Maza Littafi
Na Hudu (4). °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part Â
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU
GASU YARIMA
MUSAL'ASARI BAYAN SUN BARO
KASARSU TA
ISTANBUL da nufin yin farautar
Jaruma Safirat
domin tsayar da ita akan nufinta na
kaskantar da
dukkan mazajen duniya ta fifita
mata a kansu.
*Al'amarin Jaruma Safirat kuwa a
cikin matukar
farin ciki da kwanciyar hankali ta
durfafi birninsu
na Kisra.Duk sa'adda ta waigo
bayanta taga sarki
Safwan a cikin keji kuma a
wulakance kamar
dabbar daji saitaji dumbin farin ciki
ya sake rufeta
tunda gashi ta sami nasara akan
babban
makiyinta,kuma tana daf da cika
burinta.Haka dai
Safirat da dakarunta su dodo
Gargus suka cigaba
da tafiya tsawon yan kwanaki ba
tare da sun
fuskanci wata matsala ba har suka
iso birnin
Kisra.Tun daga nesa suka hango
kofar birnin a
bude wanwar kuma ko mai gadi
guda daya babu a
bakin kofar.Koda ganin haka sai
Gargus yayi sauri
yasha gaban Safirat ya tsaida keken
dokinta ya
dubeta yace ya shugabata akwai
tuggun da aka
shirya mana a cikin wannan birnin
naku,a ina kika
taba ganin an bar kofar gari a
wanwar haka babu
masu gadi?Koda jin wannan batu
sai Jaruma
Safirat tayi murmushi sannan ta
dubi Gargus cikin
nutsuwa tace yanzu mu da muka
ratsa cikin dajin
Sarkif muka tsallake duk masifun
dake cikinsa
sannan muka shiga dajin mutuwa
muka dauko
kuttun baka ashe har akwai wani
abu wanda zai iya
razana mu?Koda Safirat tazo nan a
zancenta sai
Gargus yaji babu shakka a cikin
zuciyarsa don
haka saiya ruga da gudu ya durfafi
kofar birnin
Kisra.Itama Safirat sai ta karawa
keken dokinta
kaimi.Ragowar dakarun
dodanninta ma suka take
mata baya.Saida su Jaruma Safirat
suka gama
shigewa cikin birnin sai kawai
sukaji an rufe kofar
garin ta waje an kulle su,Safirat tayi
murmushi ta
cigaba da tafiya abinta,babban
abinda ya daure
musu kai shine har suka iso
tsakiyar birnin basu
ga koda mutum daya ba,garin yayi
tsit tamkar
babu wani mai rai a cikinsa.Kai ko
gilmawar
dabbar gida guda daya basu gani
ba amma suna
isowa tsakiyar garin ne Safirat ta
hango
mahaifiyarta a daure a can saman
jikin wata
doguwar dirka tana zubar da
hawaye.Nan take
saiga gaba dayan dakarun yakin
birnin Kisra sun
fito da gudu daga cikin maboya sun
kewaye su
Safirat.Wasun suma sun dana
kibiyoyi wasu kuma
takubbai da adduna da sauran
makamai ne a
hannunsu.Sarki Safwan dake cikin
keji a daure
koda ya hango abinda ke faruwa
saiya bushe da
dariyar farin ciki gami da mugunta
ya dubi Safirat
yace kina zaton cewa kada mage
yanka ne?To ki
sani cewa faduwar zaki a cikin
dajinsu ba wasa
bane,koda kin kashe ni tamkar kin
kashe maciji ne
baki sare kansa ba,saboda da akwai
wanda ya fiki
son wannan karaga tawa kuma ba
wani bane face
wazirina Hidaisu bin Alkas.Gama
fadin hakan keda
wuya sai ga waziri Hidaisu ya fito
daga cikin wani
babban gida a cikin gagarumar
shigar yaki gaba
dayan yan majalisar kasar na take
masa baya.Kai
tsaye ba tare da fargabar komai ba
waziri Hidaisu
ya tunkaro inda Safirat take bisa
keken dokinta
dauke da sarki Safwan a cikin
keji.Saida ya rage
saura baifi taku goma ba a
tsakaninsu sannan
Hidaisu ya tsaya cak ya dubi Jaruma
Safirat cikin
murmushi yace una godiya a gareki
da kika bani
dama ta zartar da abinda ya
gagareni aiwatarwa
tsawon shekaru talatin da
biyar.Babu abinda bayi
ba akan ganin na kawar da sarki
Safwan daga kan
wannan karagar mulki na daneta
amma na kasa
saboda dama can sarautar ta
gidanmu ce
kakaninsa suka kwaceta,ina da
sadaukantaka da
jarumtaka irin na sarkiSafwan
kuma inda da karfin
sihirin tsafi duk irin nasa amma ya
zame mini
alakakai,yau gashi rana daya kin
bani dama nayi
masa juyin mulki,kece kadai zaki
iya taka mini birki
a cikin nasarata,kema kuma gashi
inada garkuwar
da zata kareni daga dukkan
sharrinki,yanzu zan
baki zabi guda biyu,zabi na farko
shine ki bani
sihirtacciyar kwari da bakanki ni
kuma na baki
mahaifiyarki ki juya ki fice daga
birnina kada ki
sake dawowa ko kuma na kashe
mahaifiyartaki,sannan kema na
kasheki kinga dai
ko kin hau kan wannan karagar
mulki zaki karasa
rayuwarki ne a cikin bakin cikin
rashin mahaifiyarki
har abada,ba zaki taba mancewa
da makashinta
ba.Koda Waziri Hidaisu yazo nan a
jawabinsa sai
kawai akaji Jaruma Safirat ta bushe
da
dariya.Al'amarin daya bawa kowa
mamaki
kenan,Safirat ta cigaba da kyalkyala
dariya kamar
bazata daina ba har saida ta fado
kasa daga kan
keken dokin ta zauna a kasa
dirshan tana ta
kyakyatawa,idanunta suka ciko da
kwallar dariya
suma dakarunta su Gargus sai suka
kama yin
dariya irin tasu ta dodanni mara
dadin sautin
tamkar saukar arada.Koda ganin
haka sai waziri
Hidaisu da gaba dayam dakarun
yakin birnin Suka
firgita cikinsu ya duri ruwa sukaji
kamar su watse
kowa ya cika wandonsa da iska
amma saboda ganin
Hidaisu tsaye sai kowa ya tsaya
cak.Lokaci guda
sai akaji Safirat ta tsuke bakinta
tayi shiru ga barin
yin dariyar sannan ta mike tsaye ta
fuskanci waziri
Hidaisu tace ina mai shawartarka
daka gaggauta
sawa a kwance mahaifiyata daga
jikin waccan dirka
(Pillar) a sauko da ita kasa kai kuma
kazo ka bude
wannan keji da sarki Safwan ke ciki
ka sanya
kanka saboda ba zaka iya kashe
mahaifiyata
ba,kayi kuskura babba daka bari
nazo na risketa a
raye,tabbas na raina wayonka da
tunaninka,in
dama boyeta kayi a wani wurin da
zaka iya cutar
dani,idan kana shakka a kan cewa
zaka iya kashe
tan to ka jarraba ka gani.Koda
waziri Hidaisu yaji
wannan batu sai ransa ya baci nan
take ya dubi
dakarun da suka dora kwari da
baka yayi musu
inkiya,nan take dakarun kimanin su
miliyan daya
da rabi suka juya da saitin
kibiyoyinsu suka saita
mahaifiyar Safirat suka sake jan
™Abubakar Haleefah Physicist™
zaren bakan suka tabe.Koda ganin
haka sai idanun
Safirat suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo
mata a zaton Hidaisu wannan
hawaye da Safirat ta
zubar na bakin cikin mutuwar
mahaifiyarta ne don
haka saiya bayar da umarnin a
sakarwa
mahaifiyarta ta harbi.Kaico hakika
masu iya
magana sunyi gaskiya da suka ce
rashin sani yafi
dare duhu domin inda maharban
nan sunsan
abinda zai biyo baya da dayansu
baibi umarnin
Waziri Hidaisu ba.Koda Hidaisu ya
bayar da
umarnin aka saki miliyoyin
kibiyoyin suka tafi da
gudu domin suje su cake
mahaifiyar Safirat a inda
take daure jikin Dirka a can saman
gini sai akaga
kibiyoyin sun dawo da baya da
gudu sun cake
wadanda suka harbo su suka rinka
zubewa kasa
matattu.Nanfa garin gaba daya ya
hautsine mutane
suka kama guje guje da iface
iface.Gaba dayan
sauran dakarun yakin ma sai suka
dimauce suka
zubar da makamansu suka kama
gudu suna
neman maboya.Suma gaba dayan
yan majalisar
kasar wadanda suka baiwa Hidaisu
goyan baya sai
sukayi masa tawaye suka tarwatse
kowannensu ya
sami wuri ya labe ya zuba ido yaga
yadda karshen
al'amarin zai kasance.Kafin kace
wani abu filin
wajen ya zama wayam babu kowa
face Safirat a
tsaye tare da dakarunta dodanni
sai gawarwakin
dakarun da sukayi yunkurin kashe
mahaifiyarta.Kuma sai Waziri
Hidaisu wanda ke
fuskantarsu sai kuma sarki Safwan
wanda ke daure
cikin sarka a cikin keji.Tsawon yan
dakiku ana
kallon kallo tsakanin jaruma Safirat
da waziri
Hidaisu cikin tsananin fushi da
kiyayyar juna har
fuskar Hidaisu nayin gatsine saboda
tsabar
fushi,sai kawai yayi wuf yayi jifa da
alkabbar jikinsa
sannan ya zare takobin jikinsa ashe
dama a shirye
yake ko riga babu a jikinsa sai wani
dogon wando
na almiski irin nasu na
sarakai.Waziri Hidaisu ya
cika murjejen kato mai kirar
sadaukai domin gaba
dayan jikinsa cike yake da tarin
tsoka,kwanji da
jijiyoyi,a gaba daya mazajen dake
filin ma babu
mai girmansa da kwarjininsa.Kawai
sai ya nuna
Safirat da tsinin takobinsa ya budi
baki cikin
kakkyausar murya yace ke yarinya
idan duk fadin
garin nan babu wani da namiji
dayai saura saini ba
zaki firgita ni ba na kasa tunkararki
da yaki,ina mai
tabbatar miki da cewa ni zaki ne
uban dawa don
haka faduwata sai anyi da
gaske,kibar ganin cewa
kin sami nasara akan sarki Safwan
kiyi zaton cewa
nima zaki iya samu a kaina,kuma
idan kin kisa ki
ajiye kwari da bakan naki na sihiri
mu yaki juna da
zallan karfin damtsen,u da iya
yakinmu ba tare da
karfin sihiri ba ki yadda zanyi fata
fata dake a nan
wurin,ai komai lalacewar namiji
yana gaba da
mace har abada.Koda Hidaisu yazo
nan a
jawabinsa sai zuciyar Safirat ta
kama tafarfasa
kamar zata kone don haka sai ta
cire kwari da
bakan dake rataye a bayanta kuma
a lullube cikin
bakin mayafi ta mikawa Gargus ya
rike mata.Koda
ganin haka sai idanun Gargus suka
zazzrao
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya
dubeta cikin
alamun tsananin firgici yace haba
ya shugabata
saboda me zakiyi wannan ganganci
shin kin manta
ne da bakar wahalar da muka sha a
baya kafin mu
sami nasarar hada wannan kwari
da bakansa ko
kuwa so kike ki mutu a banza ki
tarwatsa duk
mafarkin mahaifinki?Koda jin
wadannan tambayoyi
guda biyu sai Safirat tayi murmushi
sannan ta
matso daf da Gargus tayi masa rada
a kunne tace
ai abinda baku sani ba shine daga
ranar dana
dana kwarin wannan baka da
hannuna gaba daya
sihirin dake jikinta ya shiga jikina
don haka babu
wani makami da zai iya tasiri a
kaina.Koda kuw
kuwa zamu kwana arba'in muna
yin wannan yki
domin bazan taba gajiya ba,koda
gama fadin
hakan sai jaruma Safirat ta zare
takobinta ta juya ta
fuskanci inda waziri Hidaisu ke
tsaye.Koda ganin
haka sai Hidaisu ya takarkare ya
kwarara uban ihu
mai tsananin firgitarwa ya rugo da
gudu izuwa
kanta,aikuwa itama Safirat saita
ruga da gudu
izuwa

Please Login or Register in order to submit comment