Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafita hanyacinta,

Zaharaddin ya lurada sauyawa da tayi,
yace "gimbiya yanaga kinbata rai kamar kina kishi daganinsu a tare,?"
Tayi saurin zaro ido tace what?"
No Allah yatsare inyi kishin wancan abun,
nijin haushina da "bataraina,
bewuce ganin safeenat danayi ta tsaya tareda wancan mugun har take magana da shi,
sai Zaharaddin yayi murmushi yace 'harnaji sanyi a raina,

daganan sukayi sallama akan saisun hadu ranar fatin masoya,

Saboda jin haushi safeenat da takeyi batabi takantaba, Bilkisu tayi tafiyarta gida, tabar safeenat tareda Prince

Safeenat tadiba ko ina a makarantar amma bata ga Bilkisuba,
Sai wata Zainab take shaidamata da taga wucewar Bilkisu tanufi gida,
Safeenat tayi mamaki sosai,
Tamik'i hanyar gidansu Bilkisu,
tana Shiga gidan d'akin gimbiya tanufa tareda sallama
Kwance ta tarar da ita tana kallon sillin alamar tunani takeyi,
Safeenat ta kalleta tace "sis shine kika tafo warki kikabarni ina ta nemanki?"
Wai meke faruwa?"

Bilkisu tace "babu abunda ke faruwa, ganin nayi kina tareda masoyinki ne, kuna cikin farin ciki gani nayi karnayi maki magana nakatsemaku jin dad'i, shiyasa nayi tafowata,
Yanzun da kuka k'are firarku bagashi ya d'aukoki a mota ya dawo dake gidaba?"

safeenat tayi murmushi Dan tasan kishine kedamunta, kuma tasan gimbiya da prince suna son junansu ita daice har yanzun bata yarda da hakanba,har k'ara adnan ya fayyace tashi salon soyayyar saura gimbiy bilkisu














Luv u All
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR.....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page4⃣7⃣ 4⃣8⃣

Tafiya suke yana biye dasu a baya,
Safeenat ce a kafara ajiyewa domin gidansune na farko, sannan yawuce domin ya ajiye Bilkisu,

Adnan yayi parking a daidai k'ofar gidansu safeenat,
Yasamu yaro ya aikashi domin akira mashi safeenat,

Safeenat tayi mmki sosai dataga yaro yashigo wai ana sallama da ita a waje,
Cike da mamaki tacewa yaron kaje kace ganinan zuwa,

Hijabinta ta d'auko tasanya tafito dan ganin kowaye ke sallama da ita,

Arba tayi da prince tsaye a k"ofar gidansu tareda Abdullah,

Kallon mmki tabisu dasu tare da yunkurin komawa gida,

Prince yayi saurin shigabanta yana fad'in "pls safeenat kitsaya ki saurareni, kisan abunda ke tafedamu,

Tayimasa wata kalar hararaπŸ™„, tace "meke tafe daku, bayan mugunta,
Ai kobaka fad'i abunda yakawokaba ninasani, kabiyini gida ne domin nima kayimun wulak'ancin da da kaga dama,

Prince yace "pls safeenat ba wannan ne yakawoni wurinkiba,
Hasalima Nazo wurinkine domin nabaki hakurin abunda yafaru a baya wanda naimaku da keda k'awarki,

Ya koma kalar tausayi yace "Pls safeenat kuyi hukuri kuskureni, kuma nagane kuskurena, dan Allah safeenat komai yawuce,
Kuma kitayani bawa k'awarki hakuri, domin har gobe idan mukayi ido biyu da ita ina hango tsanata a cikin idonta, wadda ni kuma banajin dad'in hakan a rayuwata."

Safeenat Allah yajarabeni da mutuwar son Bilkisu wadda nakeji a yanzun idan bansamu Bilkisuba zan iya rasa rayuwata,
Yakai duk kushe a gaban safeenat yana mai zubarda hawaye a fuskarsa,
Yaci gaba da cewa safeenat kitaimakamun kishawomun kan Bilkisu ta amince dani tasoni ta k'aunace ni, koda zanji dd'i a rayuwata,

Safeenat ta tausayawa prince sosai,
Domin ta fahimci yafad'a matsananciyar soyayyar Bilkisu, Prince wadda yakeji da kud'i, da mulki da kuma sarauta, yaugashi a tsunne a gabanta yana zubarda hawaye domin Neman soyayyar Bilkisu,

Takai kallonta a wurinsa, fuskarta cike da tausayinsa,
tace "mik'e tsaye prince kadaina tsugunnawa a gaba na,
Nayarda dakai kuma nayarda da soyayyarda kakeyiwa Bilkisu,
Kuma insha Allah zantaimaka maka Bilkisu tasoka ta kuma k'aunaceka daga k'arshe ta zama matarka

Yayi murmushin jin dad'i, yace nagode safeenat, idan kikayimun hakan komai zan iya mallakamaki a rayuwa,

Ita ma tayi murmushi tace "ba wannan a tsakaninmu zantaimakeka ne, ina kuma taimake K'awata Bilkisu domin kundace da juna,

Sai a lokacin Abdullah yayi magana,
Yace muna godiya k'awarmu da wannan taimako naki, saidai karki manta ranar Monday ne ake bikin ranar masoya wadda kikasani a duk k'arshen shekara muna had'ashi a cikin makaranta, pls safeenat ki taimakemu kishawo mana kan k'awarki ta harci Bikin,

Safeenat tayi dariya ta kalli prince,
tace "prince na Bilkisu lallai kakamu da yawa, insha Allahu zanmu halarci bikin da yardar Allah,

Anan sukayi sallama kowannesu yakama gabansa cikeda farin ciki.

Abdallah ne gaban motar prince sundawo daga gadina wajen dauko kayanyakin daza'ayi amfanidasu wajen bikin dazasuyi na ranar masaya,
Group d'insune, Mazaje group sune shuwa gabannin bikin, sai kaida kamowa sukeyi, suna tsara abubuwan dazasuyi yanda wurin zai k'ayatar,

Suna shigowa harabar makarantar prince yahango motar Zaharaddin kuma ga'alama kamar bilkisu ce acikinta, nan take yaji gabansa yafadi rayuwarsa tab'aci,
Dakarfi adnan yaja wani irin burki ya tsayar da motarsa, wadda saida yafirgita Abdullah, yakai dibansa ga Abdullah daya runtse idonsa saboda tsoro, yace "
wallahi abdallah Bilkisu sotake takasheni darayuwata,Ita ba taga yadda nake sontabane, amma take min walak'anci Rana wani kula wacan jakin mekama da sillan kara amma zanyi maganinta,
Kuma bazan sake kulataba Dan duk abunta yau saura one month bikinmu,amma kamin lokacin saina saitama zahaddin bankali Dan sai yasan yata"ba jinin sarauta

Yana zaune cikin mota yana sakin surutu yahango safeenat zaune tana karatu, saiya bude marfin mota yafita yayi wurin safeenat

Shidai abdallah baicemai komiba kuma baicemai ina zakaba don yasan wahalar dayasha akan shiga hurumin da banasaba don yawahala sosai,Dan haka bemace ina zakaba bare yakallesa

Yarima yazo wucewa hankalinsa yakai wajen Bilkisu sake kwasar dariya,ita harga allah bata lura dashiba shikuma yayi tamaza ya gitta tawajen yayi kamar bai gantaba,don ko motar bai kallaba,

Yana zuwa wajen safeenat yazauna yace kawarmu yakike mikikeyi anan kedaya tace toh yazanyi inanan ina Mazarin karatuna yace wane topic ne idan na,iya intamaki race biology ne reproducthon system OK bara ingani nafa yashiga koya mata saida yatabbatar data iya sosai kana yarabu da ita, suna gamawa yace ina tukueci race gaya photon Bilkisu me har yamiko hannu ya,ansa ta hanamai ta tashi zata tsere aikonan suka kama yar tsere
Gimbiyace tafuto cikin motar Zaharaddin tana bidar safeenat can ta hangota itada yarima suna dariya, batasan miyasa taji gabanta yafadiba tareda bacinrai duk hankalinta taji yatashi duk abundant takeyi Zaharaddin nakallonta yace gimbiya yanaga kinbata rai kamar kina kishi daganinsu tare, race was no Allah yatsare inyi kishin wa nihaushina da "batarai baiwuce safeenat data tsaya tana magana da wancan azzalumin muguba, sai Zaharaddin yayi murm ushi yace wait harnaji sanyi araina, daganan sukayi sallama akan saisun hadu ranar masoya

Saboda jin haushi irin na gimbiya ko bid"ar safeenat batayiba tawuce wata gida saide side suka hadu a can gida

Safeenat nakomawa ta Shiga wajen gimbiya tace shine kika tafo warki kikabarni
Bilkisu tace yo ganin nayi kina tareda masoyinki ina nake miki magana safeenat tayi murmushi Dan tasan kishine kuma tasan gimbiya da prince suna son junansu babu de Wanda yasan dahaka cikinsu musamman Bilkisu harma kara adnan yasan annabi yafaku side bilkisu
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR......

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writteng by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page4⃣9⃣ 5⃣0⃣


Safeenat tayi murmushi, dan ta fahimci kishine fal a idon Bilkisu,
ta kuma kallon Bilkisu don ta kuma k'ara mata haushe, tace
"Tokefa kintafi wurin masoyinki kuna fira kinbarni nikad'aya,
Sannan kuma ni sai ki hanani zuwa wurin bugun zuciyata,

Wata zabura tayi, daga kwance saida tamik'e zaune,
Had'ida zaro ido waje, cikeda kishi,
Tace "lallai safeenat yanzun prince d'inne bugun zuciyarki?"
Mutumin da bed'auki mugunta a bakin komaiba,
Mutuminda bed'auki talaka abun tausayiba sai abun wulak'antawarsa,
Lallai idan ko hakane tabbas bakiyi dacen miji nagariba,

Safeenat tayi murmushin mugunta domin tagano k'awarta kishine ke d'awainiya da ita,
Tace "a yanda ke kika d'aukeshi, kuma kika fassarashi,
Amma prince Adnan ba haka yakeba,
Rayuwar prince social kuma funny ce, amma gawanda yasan hakan, kuma ya fahimceshi,
Prince ba mugo bane, ba kuma azzalumi bane,
Mutum ne mai jink'ai, da kuma tausayi talakawansa,
Kamar ke,
Kenan

Saboda tausayinsa da jink'ansa,
Abbansa yakeson yayi murabus, ya mik'amasa sarautar garin nan, har ya nad'amasa yarima mai jiran gado,
Ba dan komaiba zaiyi hakan ba, saboda prince yadace da sarautar domin babu masarautar da takeson sarkin da beda kwarjini a idon jama'a,
Prince Adnan ya cancanci yazama sarki,

Safeenat ta kuma kyara zama, ta k'ara fuskantar Bilkisu,
Tace yo bakwara Adnan Ba,
Da wannan saurayin naki mai jajayen ido,
Gashi siriri da k'aton kai,
Sai tsinannen kallon mata,
Amma kingani duk abunda prince yakeyi baya neman mata,
Shikuma zaharaddin kamar bunsuru yake,idan yaga mace,
sai fama yakeyi da muni,
Kuma a hakan ke harkinga abunso a wurinsa,

Prince Adnan kuma handsome,
Wadda 'yan mata ke yayi, ba irinsu waneba,
Tana kaiwa nan tamik'e tsaye tayimata sallama tayi safiyarta,
Tabar Bilkisu kwance akan gado, kamar tafashe akan jin haushi,

Duk abunda sukeyi jakadiya na saurarensu sai dariya take masu,
tareda shiwa safeenat albarka,
Domin a halin yanzun itama jakadiya ta fahimci irin son da prince yakewa Bilkisu,
Kuma shine wadda zata aure taji dad'in rayuwarta domin Sundace da juna,
Taji dad'i sosai da safeenat tayimata wankin babba bargo."

Yau takasance ranar masoya ta duniya,
Bilkisu tayi shigar pink&blue,
Tayi kyau iya kyau ta d'auko alkinbarta tasanya, tayi shiga irinta 'ya'yan sarauta,
Domin yau mulki da sarauta Takeji,

Bugu da k'ari yaune kowane d'alibi keyin kwanliya, iya yawarsa domin halarta fatinda za'ayi na ranar masoya a makaranta,

Safeenat tashigo gidan taci karo da Bilkisu tayi wannan kwaliyar bak'aramin burgeta tayiba, tayi kyau sosai kamar wata sarauniyar kyawawa,

Safeenat tafito da wayarta tashiga d'aukarta photo
Dama sunyi da prince akancewa da zarar Bilkisu tashirya, ta d'auko masa kwanliyar da tayi yagani,
aikowa nan take takaikaici idon Bilkisu takirashi tace ya hau online ga photo nan zata turo masa,
Nan take tayi mai sending d'insu gaba d'aya,
Sannan ta rufe data, itama tashiga shiryawa,

Mazaje group duk sun hanlara wurin fatin amma bbu Prince Adnan shugaban biki,
Bisa a canda idan suka sherya bikin bbu wadda zai riganshi halarta bikin,
Kowa mamaki yakeyi lafiya ba'aga Prince yatafoba, musamman 'yan matansa wad'anda suka mutu a kan sonshi,

Shi dai Abdullah yana gefe zaune kuma yasan komai a kan abunda ya hana Prince zuwa, amma be d'umaba domin yasan wuyarda yaci a baya akan sakin magana,

Prince ya gama shirinsa tsaf,
Zaune yake yana jiran kiran safeenat,
Domin sunyi da ita akan cewa ida harsun shirya zasu fito,
Tayimasa magana domin soyake sushiga wurin a tareda Bilkisu,

Saiga kiran safeenat yayi saurin d'auka, take shaidamasa sunshirya yanzun zasu fito su had'u a makarantar

Sauri yayi ya d'auki key d'in motarsa yashiga yanufi makaranta,

Yana shiga makarantar suma suna shigowa,
Yakai kallonsa ga Bilkisu yace "masha Allah, saboda kyawon da yaga tayimasa,
Saima yafarajin wani sabon kishinta yataso masa, jiyakeyi kamar kartashiga saboda kar mazanda ke wurin su kallemasa ita,

Hangosu yayi sunnufi wurin da akeyin fatin,
Saiyaturawa safeenat message akan cewa tayi gaba tabarmasa Bilkisu a baya,

Safeenat na ganin sakon Prince, sai tajuya ta Ganshi a bayansu yana biyedasu,
Tacewa Bilkisu sis bari nayi sauri na samarmuna wurin zama kamun ki iyar da k'arasowa tayi gaba tabarta nan,
Bilkisu tayi murmushi tace aikuwa kinkyauta sis,

Prince nabiye da ita a baya duk bata luradashi ba,
Saida sukazo shiga hole d'in dama kowa yashigo sukad'aine sukayi latti shigowa,
Prince yayi sauri matsawa kusa gareta suka jera a tare suka shiga holle d'in,
Binsa tayi da kallon mamaki,
Ganin yasanya kalar kayanta sak,

Rigarsa pink, wandonsa blue, alkinbarsa ita blue, yanda gimbiya Bilkisu tayi shigarta shima hakan yayi banbancinsu shine ita yadine tasanya, shi kuma k'ananan kaya, Riga da wando,yasanya sai alkinbarsu ita ta mace shi kuma alkinbar namiji,
Gaba d'ayansu sunyi kyau wanda baya misaltuwa,

Ana ganin shuguwarsu gaba d'aya aka d'au kuwa, saboda sun burge mutane sosai,
Zaharaddin jiyayi kamar ya fashe saboda jin haushe,

Bilkisu kallon mamaki tabishi dashi ganin yasanya sak kalar kayanta yasanya, tashiga danasanin da bata sanya wad'an nan kayanba,

Shikuma yana mata kallon kin burgeni,tare da tsura mata ido,yana daga mata gira,

Data lura da hakan kawai saita d'aure fuska,tayi kamar bata ganshiba sukaci gaba da tafiya,

Subahanalillah kuzo kuga yadda sunkayi kyau,Suna tafiya mazaje group namasu photona batare da tasaninsuba, dak'er tasamu tak'arasa kusada safeenat tasamu wuri ta zauna

A Nan m.c yafara gudanar da bayaninsa,
yana fadin duk Wanda yayarda da wankansa to yafito anan,
A nanfa kowa yatsaya ana kallon kallo mazaje group ne suka fita tare da wasu mazaje, amma banda adnan

Can shima Zaharaddin yafito saiga prince ma yafito nan fa kowa yashiga tab'amasu,

M.C yace cikin mata duk wadda ta yarda da kanta tafito,
kokuma subada wadda sukasan tadace,
nanfa kowanensu sai kallon kallo sukeyi wannan takali wanan suna shawara amma gimbiya ko Inda suke bata kallaba bare tace fita zatayi,

Can Ashanti tafita tana yauki nanfa suka had'a baki sukace basu yardaba subasa sonta,

Mc yayi kyaran murya yace " sufitarda wadda sukeso,
sai suka had'a baki gaba d'ayansu sukace bilkisu mukeso,
Bilkisu dake zaune tasunkuyar da kanta k'asa sai dannar wayarta takeyi batamasan wai nar dasuke tuyaba,

Saide taji ana kiran sunanta dasauri tadago kanta sama tana kallon mai kiran nata fuskarta cikeda mamaki,
nanfa safeenat tadinga lallab'ata akan ta tashi tatafi k'in zuwanta wurin ba girmanta bane,

Ahankali tamike ta isa wajen tatsaya, a tsakiyar filin, ido yayo kanta kowa kallonta yakeyi,
Sannan M.C yacigaba da magana,
Yace "muna da sharadin duk wadda yafito Wurin nan to munsan tabbas ya yarda da kansa,

don haka munada sharad'i?

Sharadin shine duk abunda akkace mutum yayi saiyayi ko kuma acishi tarar (70, 000 N)
Ya maida kallonsa a Bilkisu Yace "gimbiya kinyarda,?
Ta maida kallota ga safeenat,
Safeenat tad'aga mata kai alamar tace ta yarda,
Bilkisu ta kalli mc tace "nayar da Dan kudi bama tsalata bane, nan fa aka d'auki kuwa,

yace
sharadi na biyu, programs nafarko dole sai kinyi abunda akkace kiyi, idan bakiyiba zaki biya Tara,
Ko kuma a fansheki, ma'ana kuma wani daga cikin masoyanki subiya maki,

Tana tsaye ankabawa safeenat wani farin kyalle,

akkace ta daure mata fusaka da farin kyallen,

Ya kuma bada umurni akkan cewa duk namijin da yafito tsakar fili,
yacire ta kalmensa ya ajiye a kusa da ita,

bayan sun kammala ajiyewar,

Sai MC ya kalli Bilkisu dake tsaye d'aure da fuska,
Yabata umurni dataduk' ta d'auki talkami d'aya cikin tallakamin da aka ajiywmata a gefenta,

Nanfa tashiga gewaye tana lalaben inda talkaman suke,
can ta canki wani takalme,
tamik'awa MC sannan aka bude mata fuskarta,

MC yashiga diban k'afafun mutanen dake tsaye tsakar filin dan ganin ko takallemen waye ta cinka, Nan aka kasoma dibon k'afa ashe na yarima adnan ne tadauka, aikuwa mutane na fahimtar hakan suka suma kuwa,

M.C yayi gyaran murya yace, "Bilkisu da Adnan kawai yakeso ya gani a tsakar filin,
Zaharaddin yyi bak'in cikin rashin d'aukar takalmensa dabatayiba

MC yace a saurara, za'a sanyawa Bilkisu da Adnan wak'a domin sutaka rawa,

Adnan yaji dad'in hakan,
Ita kuma tad'auki niyar cewa Adnan bazai tab'a kada itaba,

bata iya rawaba amma takawa takeyi cikeda k'asaita saida ta tabawa kowa sha'awa amma banda zaharaddinka,

Sai programs na k'arshe,

M.C yace anason Adnan yayiwa Bilkisu kiss harna tsayin 30minut,
nanfa hall yayi tsit don kowa sonyakai yaga yanda hakan zata kasance

adnan yyi murmushin jin dad'i,
Yasoma lasar baki da gyaram kwalar Rigarsa za,asha banza,

Adnan yasoma matso Bilkisu naja baya, MC yace "wait Prince bara nak'irga goma idan bata yardaba zamu cita tara,
idan kuma akwai mai fan sarta toh am waiting, nanfa yafara k'irga d'aya Bilkisu naja baya prince nabiye da ita har da ta kai karshen bango, Prince nabiye da ita,

Datagade ba sarki sai Allah sai tayi tsaye, ta kulle idonta tana jiran taji saka mako abunda prince zaimata,
Shi kuma har yaruk'o hannunta, yaji ance na nafansheta, nan take prince yayi saurin waigowa domin ganin waye ya katse masajin dad'i, sai yayi arba da Zaharaddin a tsaye yana murmushi, nanfa yaji kamar yamutu amma sai ya yamutsa fuska alamun ko ajikinsa

Amma taciki naciki nan dai akaci gaba da programs daga bisani aka tashi kowa yawatse.

safeenat ce takeyiwa Bilkisu dariya tana fad'in "yau wata datasha lebo,
Bade ta kulataba sai harara databita da ita, tareda fad'in " Allah yafishi,
safeenat tace bawani anaso ana kaiwa kasuwa, ai koke bakiji dadiba itade batace mata uffanba

Suna fitowa Zaharaddin yabiyo bayan bilkisu suna tsaye yanamata k'orafi akan cewa danmi bata dau takalmensaba?"

Magana yaji anayi a bayansa yaji anafad'in "akanmi zata d'auki takalmenka tabar na mijinta?'

Nan suka juya gaba d'ayansu dan ganin mai yin magana,

Zaharandin ya kallesa yace 'toh kai kuma miye naka nabiyomu a Nan Adnan?"

Prince yayi murmushi yace "nabiyoka ne domin inyimaka kashedi a kan karabu da Bilkisu domin nikad'ai nakeda ita, banason inason abu naga wani na Sonsa, Dan haka kakiyayi kanka,
ko nasanya a b'atar min da kai, b'acewa ta har abada,

Domin kadaina ganin kanka wai d'an minister ne,
kod'anda shugaban k'asane kai zan iya sanyawa a b'atarmun da kai.

Bilkisu tayiwa prince kallon sama da k'asa "tace kai malam yimun shiru,
wacece matarka?'
Allah yatsareni danazama matarka,
Tanuna xaharandin tace, "kaga wannan shine mijina,
Wanda ya amsheni a hannun azzalumi irinka,


Tun Kamin ta iyar da maganarda takeyi saiji tayi an watsamata mari,

Ta dafe kunci
Tace "kamareni?" akan nace bana sonka?" toh nafad'a nace bana Sonka Adnan,

shikuma abunda yatsana a rayuwarsa kenan ta duniya,
bilkisu tace bata sonsa.

Nan Yadinga kallonta idonsa yarik'ed'e yayi jajir,
ya hango shatin hannusa,
a inda yamareta ya kwanta mata akan kyakkyawar fuskarta,

Ta kuma kallonsa ido cike da hawayeTace "nace bana sonka zata kuma yin magana yad'aga mata hannu alamar tayishuru yajuya zaitafi idanunsa surikid'e, sunyi jajir sai zubar da hawaye yakeyi,
Zai wuce kenan saiganin sukayi ya yanke jiki ya fad'i k'asa a some,
nan take Abdullah yayo Kansa suka tallabesa aka sanyashi a mota suka nufi asibiti dashi,

Hankalin Bilkisu duk yatashi sai zubarda hawaye takeyi,

zaharaddin yace akan wannan jakin zaki tada hankalinki?"
yama mutu mana,
shiyasa lokacin dayayi hadari naso yamutu,

kenifa saboda kiyayyar da nake masa yasan, natura akad'eshi a mota mufuta, Domin tun farko bana sonsa,

Bilkisu tabishi dawani kallo wadda saida ya firgitashi, sannan ta d'aga masa hannu tace
Ya i'sa zaharandin, dama kai azzalumine maci amana?"
Ashe zaka iya kashe rayuwa?"
kuma d'an uwana?", toh bara kaji daga yau kada ka kuma yimun magana natsaneka, bana sonka banason ganinka azzalumi kawai, nan ta tohfa masa yawu tawuce.

Koda aka i'sa asibitin prince besan inda kansa yakeba,

Likitoci tai makon gaggawa suka basa,sannan akakira sarki yazo han kalinsa a tashe yashigo asibitin,yana tambayar ba,asin abunda ke faruwa ga prince, nan sunkace suma basu saniba gani kawai sukayi ankawosa,

Nan likita yayi sarki magana, akan cewa yana son ganinsa, suna shiga yafayiwa sarki bayani kamar haka,
"zuciyar Adnan ce yake keson bugawa saka makon wani abu dayake so baisameshiba Don haka ayi saurin basa abunda yakeso, idan bahaka

Please Login or Register in order to submit comment