Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tsage ya shige saboda kallon da d'alibai suke masa."

Gimbiya Bilkisu na zaune a kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya,
tana kallon yanda za'a sanya shi a mota a tafi dashi."

za'ayi sanyashi Mota kenan, tayiwa fadawa magana tace " kudakata."βœ‹πŸΌ

Suka tsaitsaya suna masu jiran umurninta."

Tace "kusakesa, kurabu dashi."
Nasan yayi nadama domin Daga nadama a idanunsa."
Ta matso kusa dashi taimasa kallon sama da k'asa tace "ko yanzun, kafahimci gaba da gabonta."
Tajuya ta kalli d'aliban dake kallonsu, ta kuma maida kallonta gareshi, tace "diba canπŸ‘‰πŸ» taiyi masa nunida d'aliban dake kallonsu."
tace 'duk kai suke kallo."
"Adnan ina k'asaitarka da kuma sauratarka."?
Adnan ina mulkinka yake? Wadda kake tak'ama dashi kake wulak'anta talakawanka yanda kaga dama."
Duka babu ko d'aya a yanzun."
domin yanzun kana k'arkashin mulkina da sarautata."
Na fad'amaka zansanya ayimaka hukunci mai tsanani da kaida duk wani magoya bayanka."

zan sansauta maka ne yanzun, domin halinda naganka ciki, a yanzun yayi mun dad'i a rayuwata."

Tace "sarkin hukunci,
Yace " Allah ya taimakeki." tace "kusakesa, kurabu dashi yayi tafiyarsa."

Amma, Kutafimun da wancan πŸ‘‰πŸ»tanuna Abdullah."
kuyi masa hukunci mai tsanani, wanda gobe idon yaji manyansa na magana baya kuma yimasu katsalandan a magana."

Abdullah yanajin anbanci atafidashi."
saida yabud'e murfin mota yafito a guje, yana kuwa yanakiran ya tuba bazai sakeba."
Fadawa suka tugumesa suka sanyashi a mota suka tafi dashi."


Ta maida kallonta a Safeena datayi mutuwar tsaye cike da mamaki."
Tace "sister mutafi gida lokacin cin abincina yayi, ta kalli agogon dake hannunta."

Safeenat tace to rankin ya dad'e."
ta kalli Safeenat tayi dariya, tace "nasan yau akwai magana a bakin nan naki."
Safeenat tace kusan hakan ne gimbiya tarunsuna kamar yanda taga fadawa nayi mata."😊
Bilkisu tayi dariya takaimata dukan wasa, tace "to mutafi gida ki furta abunda ke cikin ranki."

Suka nufi mota suka shiga sai jiniya akemasu suka bar makarantar suka nufi gida.'
d'alibai kowane fad'in albarkacin bakinsa yakeyi."


Prince yana samun fadawa nan sakesa, bebi takan kowaba, yanufi motarsa yabata wuta, saida ya bad'e mutane dake wurin tsaiye da k'ora."
sanan ya bar makarantar."
Gudu yakeyi a kan titi Allah ne kawai yakaishi gida lfy."
Da isarsa gida Bebi takan kowaba, kai tsaye d'akinsa yanufa, dashigarsa d'akin nasa. yayi wurgi da key d'in motarsa gefe, ya cire rigarsa yayi wurgi da ita, ya kaiwa bango nushi, idanunsa sukad'e sunyi jajir sai magana yakeyi, ni Adnan yau nine wata banza ke tuzartawa a gaban bainar jama'a."?
Domin tana tak'ama dawata sarauta can tata."
To Ita wacece a cikin gidan sarautar."?
'Yar wace masauta ce?
Idon ita 'yar sarkice ubanta shine nanawa a hawa kujerar sautar?

To tabbas zansanya ayimun bincike a ganomun ko 'yar wace masarautace."? tana matsiyin 'yar sarki, take yawo a k'asa batareda da fadawaba."? take wulak'antarda kanta haka."
Tabbas akwai wani b'oyanye sirri a tareda ita, wadda zan banyak'oshi domin tunuwar asirinta."

Ya kai hannu ya d'auko wayarsa domin kiran Abdullah."
Sai a lokacin yatuna da Abdullah a can yabarshi dasu."
Toko mesukai masa Abdullah."?

Zumur ya mik'e tsaye, yana safa da marwa, daga k'arshe zama ya gagaresa ya d'auko key d'in motarsa yanufi bid'ar Inda Abdullah yake."

Tafiya sukeyi anayimasu jiniya, har suka shiga unguwarsu Safeenat."
Jakadiya dake zaune, tajiyo jiniyar masautarsu, tayi murmushin jin dadi, tace
"Alhamdulillah, tanufosu tanayiwa gimbiya Bilkisu kirari."

Mahaifiyar Safeenat mamaki tashigayi, tabiyo bayan jakadiya domin ganin meke faruwa."?

Sai ganin Bilkisu tayi tafito a mota fadawa nata zuba mata kirari."

hannu ta d'aga fadawan alamar ya i'sa."
Sannan tabud'i baki tai magana tace "kuyi tafiyarku masaukinku idon natashi buk'atarku zan nemeku."
Suka runsuna k'asa sukace "angama ranki ya dad'e."
Sukayi tafiyarsu

Ta maida Hankalinta a ummie mahaifiyar Safeenat, dake tsaye tabita da kallon mamaki."
Bilkisu tayimata murmushi, suka d'unguma sukayi cikin gida gaba d'ayansu."

pallon ummie sukayi masauki, kowa sai kallon Bilkisu yakeyi sunajiran suji k'arin bayani daga bakinta."

Bilkisu ta maida kallonta akansu,taga jira kawai suke tabud'i baki tayi mgna, musamman Sakeenat da mahaifiyarta."
Tayi murmushi, tafara fad'amasu ko ita wacece da masarautar da take, harzuwa ynzun had'uwarta da prince Adnan."

Sun jinjina mata kuma sunyabawa kyawanwan halayyata, suka rufe zancen dayimata fatan alkhairi."













WRITING
BY
FAREEDA
BASHEER✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF
LIFE WRITER'S


page2⃣1⃣

Gidansu Abdullah yanufa, yaci kiran number wayarsa amma a kashe, aika yaro yayi domin yakira masa shi."

Yaron yafito yake shedamasa ance yana makaranta bedawoba."

Godiya yayiwa yaron, yashiga motarsa, yanufi makarantar."

Shigarsa makarantar d'alibai sai nunashi akeyi suna fad'in gashi nan yadawo."

Bedamu da hakanba shidai burinsa yayi ido biyu da Abdullah." ya tabbatar da lafiya k'alau yake basuyimasa illah ba."

Kai tsaye group d'insu yanufa mazaje group suna ganinsa sukashiga yimasa dariya suna fad'in sai mazaje."

Ya d'aure fuska, kamar betab'ayin dariya ba."
Yace ina Abdullah."?

Suka had'a baki gaba d'ayansu sukace, "Abdullah Bilkisu tasanya an tafidashi."

What."? Tasanya antafi dashi."? Wai Metake nufine?
To wlh duk tasanya akayimasa illah,
Itama bazan bartaba."

Yakoma Yashiga motarsa yafigeta da k'arfi, ya bar makarantar."


Gimbiya Bilkisu yanzun hankalinta ya kwanta, sunshiga weekend, gaba d'aya ta manta da wani Prince can."

Hidimar komawarsu samun gidansu sukeyi, ita da jakadiya."

Wadda Abbanta ya turomata kud'i a account d'inta tasaya."

Wancan tsohun
gidan nata kuwa, tayiwa liman magana tana buk'atar a mayardashi makarantar islamiya."

liman yashiga yimata godeya da sanyamata albarka."

Gida yayi kyau dai dai gwargwado, Wadda Abbansu Safeenat ne, yazab'armata shi."

Abban Safeenat yaso ta zauna taredasu, domin a d'an zamanda sukayi tareda ita, ya fahimci yarinyace mai natsuwa da hankali." kuma batada girman kai kamar ba jinin saurataba."

Ita kuma Tayi tunanin idan prince ya fahimci a nan gidan tadawo da zama, to tabbas bazai barsuba zaisanya ayimasu wulak'anci, mai tsanani wadda ita bazataji dad'in hkanba."

Shiyasa takafe ita bazata iya zama dasuba sai dai asayamata gidanta ita da jakadiya su zauna a tare." tafi buk'atar hkan."

Sunkoma gidansu, wadda tareda ummie mahaifiyar Safeenat, da kuma Safeenat, sukaimasu rakiya, sukadinga yimasu fatan alkhairi."
Suka rabu da Safeenat acewa sai ranar monday idon sunhad'u a makaranta."


Kwana biyu kenan babu labarin Abdullah, prince duk inda yasan zaiji labarin babban Abunkin nasa kalmar d'ayace ba'a ganshiba."

Ga mahaifan Abdullah kullum sai damunsa sukeyi da yataimakesu yasanya adibo masu Abdullah wlh shikad'ai suka mallaka a duniya."

Prince bayada kwanciyar hankali, kullum tunaninsa d'aya wace hanya zaibi yadawo da Abdullah gida."

Domin ba iyayen Abdullah kad'ai sukayi rashinsaba, hardashi kansa yayi rashinsa damin bayada abokin ko amini da yawuce masa Abdullah."

kuma gashi duk halinda yahiga a sanadinsa yashigeshi."

Duk hanyarda yasan zaibi yaga Bilkisu ya bita." amma har yanzun besamu ganintaba."
Kuma yarasa a wace unguwa takoma da zama yanzun."

Har unguwarda yasanya aka karesu yatafi, amma zancen d'aya ne basusan Inda takomaba."

Sai dai yatsinci labarin tama bada gidan gabad'aya a mayardashi islamiya."

Hakan yajuya yakuma gida cikin bak'in ciki da b'acin rai."

Sai a can wani tunani yafad'o masa a rai." to ai gobe Monday
kuma yasan Bilkisu da son karatu duk inda take gobe Monday zatazo makaranta."

Yayi dariya jindad'i Yakoma gida cike da tunanin, wace hanya zaibi da ita wadda zata dawo masa da Abdullah."

Abdullah kuwa bayan fadawa sun yankemsa hukuncin da gimbiya ta umurcesu."

Sai da yayi jinya ta kwana d'aya yana mai tsinewa prince domin duk shine sillar sanyashi a wannan masifar."

Haka yacigaba da zama da fadawa tun suna azabtardashi harsuka koma tausayamashi."

shima ya kuma bayarda kansa kalar tausayin biyarsu yakeyi sauda k'afa."

ganin hakan dayake masu, yasanya suka jashi a jikinsu." sukasaki jiki dashi.'

Shi kuwa ya kwantarda hankalinsa yakashe kunne ya kwashe sirrin gimbiya
Bilkisu a bakin fadawanta."

Sabda dasun zauna basada wata fira saita gimbiya Bilkisu da irin kyawawan halayanta."

A nan Abdullah yasan ko 'yar wace masarautarce yakuma fahimci matsayinta awurin sarki."

Yau Monday Bilkisu tak'are shirinta tsaf."
Domin zuwa makaranta."
afterdress ce sanye a jikinta, ta yafa mayafinta, tayi kyau sosai kamar balarabiya."

Wayarta tad'auka takira Safeenat tace "hello sister kinshirya nabiyo tanan mutafi."
Safeenat dake kwance cikin yanayin ciyo, tace "sister banasamun zuwa makarantar nan banada lfy daciyon ciki nagwana jiya."

Bilkisu ce "subhanallah, sister Allah yabaki lfy idon nadawo zanbiyo nadiba jikin naki, sukayi sallama Bilkisu tafito tanufi makaranta."

Prince zaune a kan motarsa, yasha bak'in glass a fuskarsa."

kallon duk wadda keshigowa yake d'aya bayan d'aya."
duk wadda keshigowa makarantar a kan fuskarsa yake." fatansa Allah yahad'ashi da Bilkisu, shikad'ai yasan irin abunda yashirya mata a rayuwarsa."

A can ya hango shigowarta.'
tafiya takeyi cikin natsuwa da k'asaita da littafai rik'e a hannu ta."
Yana hangota ya duru a kan motar, ya zagaya, yashiga mortar, yafige motar da k'arfi yayi cikin Bilkisu , saida yazo gaf da ita sannan ya faka motar yafito."
Bilkisu tsaye tayi takasa tafiya sai kallo tabisa dashi."
bata ankaraba saiji tayi and'aure mata baki anturata a mota."















Writing✍🏻by
Fareeda
Bashir😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MARAUTAR..

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page2⃣2⃣


Tafiya sukeyi, bakinta a d'aure, idanunta sai zubarda hawaye sukeyi."
Saida suka shiga wata unguwa wadda babu hayaniyar mutune a cikinta." Unguwar tsit kakeji kamar babu bel'adamar dake rayuwa a cikinta."

Parking yayi a dai dai wani katafaren gida, wadda babu kowa a cikinsa."fitowa yayi ya bud'e get dakansa sannan Yashigar da motarsa a ciki."

A guje yanufi wurin ajiye motoci."
Tsayawa yayi yabud'e murfin mota ya fito."
Ya zagaya wurin zaman Bilkisu sai zubarda hawaye takeyi."
Ya finciko hannuta da k'arfi yafito da ita, jaye yake da hannunta, harsuka k'arasa shiga cikin gidan."

Wani d'aki yanufa da ita, wadda yake ya motse.
kaya ne ko'ina a watse."
A ranta tace turk'ashi yau dai Allah kad'ai zai fissheni a hannun mugun mutumin nan."
Gashi k'azamin banza, duk k'asaitarsa, dawani kwalliya tasa, ashema gidansa babu komai a cikinsa sai k'azanta."

Ya katsemata tuninta dayace zaki fad'amin inda Abdullah yake ko saina aikata abinda nayi niya a kanki."?

Inkasheki inkashe banza." Domin babu wadda yaga a lokacinda na d'aukoki, bare kiturowa mutane banzayen fadawanki masu kama da samudawa."

Magana yakeyi idanunsa sunkad'e sunyi jajir, cikin b'acin rai yace bazaki bud'i baki kiyi magana ba bare kifad'amun a 'inda kika kaimun Abdullah."

Bilkisu sai kallonsa take sama da k'asa, domin ita a yanzun Allah ya ciremata jin tsoransa a rayuwarta."

Shima ita yake kallo cikin mamaki,
Tace "karyane wlh baka isa kakashiniba sai dai idan lokacina ne yayi."
Abdullah bazan fad'i inda yakeba harsai ka d'an d'anni bak'in cikin daka sanyani na tsawon wani lokaci."

don hka kabani hananya nafita nayi tafiyata, tunkafin warin wannan d'akin yayimun illah."

Cikin b'acin rai yanufuta a fusace, ya had'a bayanta da bango hannunsa a kwalar rigarta ya matseta yana ce mata.
"Ina Abdullah? Iyee ina Abdullah nace?"

Tafita hanyacinta don tsabar tsoro da firgitar abunda yayimata a rayuwarta babu namijin daya tab'ayi mata abinda yayi mata yanzun."
Ta runtse idanunta hawaye na fita daga idanunta,
Ya k'ara matseta ya kuma matso da fuskarsa daidai tata yana wani huci, zakifad'amun inda Abdullah yake ko saina kasheki?"

Ta katse shi dacewa, "hannunka a k'irjina!" Ta fad'i hakan cikeda shagwab'a kuma cikin sanyin murya wadda ke k'unshe da wahala."

Besan lokacinda ya saketaba, dashima ya gano hannunsa a kan k'irjinta yake."
Ya ciji leb'ensa na k'asa a ransa kuwa haushinta ya k'ara kamashi so take tayi suducing d'inshi?"
Tambayar da yakeyiwa kansa kenan,
Lallai yarinyar nan tayi nisa, ganinta zata iya jan hanlinsa ne kome take nufi?"

Duk Kansa yakeyiwa wad'an tambayoyin, a zahiri kuma yanunata da yatsa yana Jamata kunne kokifad'i inda kikai Abdullah ko na d'aukar maki kwankwaran mataki a kanki yanzun nan."

Karfin hali tayi domin ta tsorata da ganinsa cikin wannan yanayin, idanunsa sunkad'e sunyi jajir
Tace "malam kabud'emun k'ofa nafita bana iya k'ara minti d'aya a cikin wannan k'azamin d'akin.
Tanufi wurin k'ofar da niyar tabud'e tafita, saiji tayi ya fisgota ya had'ata a bango ya matseta gam ajikinsa, saiwani numfashi yake fitarwa kamar wani zaki."

Tuni hankalin Bilkisu yatashi, tarufe idonta, tana fad'in SUBHANALLAHI!"

Ina kikasanta? Ashe kinsan Allah?"
To wlh duk Baki fad'i Inda kika kai Abdullah ba zakiyita zama a nan gidan,
Har sai ranar da kikafito da Abdullah sannan kema nasakeki,
Muguwa kawai, aibashi yayi maki laifiba, ni ne nayaki laifin, meyasa bazaki d'auki mataki a kaina ba sai a kansa?" Kina tunin ninafi k'arfinki kenan shiyasa zaki sanya samudawan fadawanki sutafi da Abdullah

Kisakesa mana, ni sai kisanya a kamani."

Magana yakeyi amma bata tankashi,
Ya kuma kuluwa, yajaye a bakin k'ofar d'akin yaturata a kan katifa,
Yabud'e k'ofar d'akin yafita, yasanyawa k'ofar key yayi tafiyarsa ya barta nan."

Bahijja da Fahad soyayya tayi nisa domin har ansanya ranar da maimartaba zaitafi yola neman auren Bahijja k'arshen watan nan."











writing
By
Fareeda
Bashir✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR.......

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page2⃣3⃣

Kwana d'aya babu labarin gimbiya Bilkisu hankalin jakadiya duk yatashi,
Tanufi gidansu Safeenat domin duk a tunaninta suna tareda Safeenat,
Saima taji labarin Safeenat batasamu zuwa makarantaba saboda bata da lafiya,
Ba jakadiya k'adaiba gaba d'aya hankalin iyayen Safeenat saida yashi ,
Domin abbansu Safeenat fitowa yayi daga gida yana salati yashiga motarsa nufi neman Bilkisu."

Safeenat kuwa kuka tashigayi kwana d'aya babu Bilkisu babu labarinta,
Saitafara tunanin ko prince Adnan ne yasanya a d'auketa, domin d'aukar fansar abunda taimasa,
Wata zuciyar kuwa na gargad'inta da bazai iya sanyawa a d'auke ta ba."

Bilkisu kuwa ya kulleta a d'aki yayi tafiyarsa, sai dai duk bayan a'wa biyu zaizo domin ganin koda tayi nadama tafad'a masa inda Abdullah yake,

Amma babu alamar nadama a fuskarta, sai dai ya tarar da ita tana games a wayarta hankalinta a kwance babu damuwa a tareda ita,

haushinta ya lunlub'eshi yace "wato ita wannan yarinyar batada niyar nadama tafad'i inda takai Abdullah kenan?"

Ya kai hannunsa zai fisge yawar dake hannunta k'irar 1phone tayi saurin b'oye wayar a bayanta,
Ganin zai iya murd'eta ya kwace wayar a hannunta , tatura wayar cikin rigarta,
shi kuma ganin ta tura wayar a rigarta, yayi mata wani kallo,
Yace "shed'aniya ni babu abunda zanyi dake, kidaina wani tura waya a riga, wato d'azun kinji dad'in nahad'a jikina da nake shine yanzun kike Neman nasanya hannuna a cikin rigarki, saboda kina jarabanbiya, to Allah yakiyayeni babu abunda nake iyayi dake, kitafi can kinemi dai dai dake, ninafi k'arfinki babu abunda zanyi dake,
Yaja wani dogon tsaki malama kifito mun da Abdullah nasakeki kikama gabanki ."

Ta kallesa taja wani dogon tsaki, tayimasa kallon sama da k'asa,
Tace "mezanyi dakai, dibeka, me gareka wadda harnake sha'awar had'a jikina da kai,
tanuna masa d'akinsa dayi wani kaca kaca da kaya tace " k'azami kawai."πŸ™„

Tace Abdullah bazan fad'i a inda yakeba domin har yanzun bangaji da ganinka cikin k'unci da bak'in cikin rashin ganin Abdullah ba."

Yace "a she kema zama bek'aremaki a gidan nan ba kenan,
Domin mundun bakibada umurnin a sake Abdullah ba nima kisani bazan tab'a sakinki ki koma gida ba,
Kuma kisani abincin da nake kawomaki daga yau na daina,
Sai dai kizauna da yunwa idon kikaji wuya zakiyi bayani da bakinki inda kikai Abdullah,

Ganin yanda yake magana sai wani cincira yake cike da b'acin rai da bak'in ciki, kamar ba Adnan d'in da tasani ba,
Dariya tashiga yimasa tana nunasa da hannu tana dariya harda rik'e ciki,

Haushi da bak'in ciki ya kuma lunlub'esa,
Ya d'aga hannu alamar zai daketa meya tuna oho sai ya sauke hannun yana cizon yatsa,
Sai yafita d'akin a fusace yaja k'ofar d'akin da k'arfi yasanya makulli ya kulleta yayi tafiyarsa."

Ganin ya kuma kulleta bayada niyar sakinta bare takoma gida,
Duk hankalinta yatashi tana tunanin jakadiya, tasan yanzun duk inda take tana cikin tashin hankalin rashin ganinta kwana d'aya dabatayiba
Idon kuma tayi yunkurin shedawa maimartaba to Tabbas hukuncine zai hau kanta watak'ila harta rasa rayuwarta, wadda idan hakan yafaru bazataji dad'i a rayuwarta ba."

zubur tamik'e tsaye da tuna da Safeenat tasan yanzun labari ya kai a kunnesu na b'atanta
Suma tasan tabbas basa cikin kwanciyar hankali a wannan lokacin."

Wayarta ta d'auka takira fadawanta tace tana buk'atar a sakar mata Abdullah yanzun nan,

Suka amsa mata da to angama ranki ya dad'e,

Suka sakesa, suna kewar juna domin d'an zamanda sukayi da Abdullah sunshak'u dashi sosai,
Wadda shi kuma Abdullah beso aka sakesaba ko dan saboda kalar abincin dayakeci irin na masarauta,

Sai yashiga tunani a zuciyarsa, gaskya betab'a ganin masarautar da fadawa suke daula haka, sai a wannan masarautar,

inama shima a maidashi cikin fadawan yaci gaba da rayuwasu,
da ya bautawa masarautarsu Bilkisu,
Domin zama taredasu ya fahimci me'ake nufi da sarauta,
Kuma ya fahimci k'aramci da daraja d'an Adam irin na masarautarsu Bilkisu

A haka dai yabar wurin fadawan,
yana kewarsu,
yana mai tsinewa Adnan a rayuwarsa domin yasan shine silar sanyawa a sakesa, domin yaga kwana biyu beganshiba, saikace a tare a ka haifemu."πŸ™„ Yaja wani dogon tsaki😏 yayi tafiyarsa."


Adnan yana k'ofar gidansu Abdullah yana kwantarwa da mahaifan Abdullah hankali a kan cewa insha Allahu gobe Abdullah zaidawo gida, ba b'acewa yayi ba yanan cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali,

Begama rufe bakinsaba sai ganin Abdullah yayi a gabannsu yana dariya, yayi kyau yayi k'iba har wani shek'i yake, yana masu dariya, yanufi mahaifansa ya rungumesu cikin jin dad'i, suma sai murna sukeyi naganin tilon d'ansu,

Prince baki yasaki yana kallon Abdullah yana mamakin kwana biyu, yaga yayi kyau kuma yayi k'iba.

Gefe yajanyeshe yana kallonsa cike da mamaki,πŸ€”

yace "Abdullah wai meke faruwa ne?" ina fatan muguwar yarinyar bata sanya anyimaka illah ba?"

Yakaiwa Adnan hararaπŸ™„ yace gaskiya ka daina cewa gimbiya Bilkisu muguwa, domin ita ba muguwa bace, illah maison alkhairi da daraja d'an adam,
Ni wlh a baya d'aukar da nake mata wata wuk'antanciyar 'yar talaka marasa galihu a she ba haka abun yakeba,

Adnan yasaki baki da hanci yana kallon Abdullah cike da mamaki,
Yace "gimbiya kana nufin Bilkisu 'yar sarki ce?"

Abdullah yace kwarai kuwa, 'yar sarki ce, wadda mahaifinta da masarauta gaba d'aya suke alfahari da ita saboda kyawawan halayennta da kuma daraja d'an adam."

Adnan yace " 'yar wace masarautarce?" Waye ubanta?" Kuma A wane gari suke gudanar da mulkunsu?"
Duk a jere yajerawa Abdullah wad'an nan tambayoyi,

Abdullah ya wurgamasa harara, yace " kobaka tambaye niba nad'aukoma labarai da d'umi d'uminsu,

Zakasan kowacece Bulkisu amma kabarni nashiga gida nahuta zuwa anjima sai muhad'u kasha labari."


Please Login or Register in order to submit comment