Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damunka?" Kwana biyu na lura dakai bakacikin hankalinka?"
Meke damunka wadda mu mahaifanka bazaka iya fad'a mana shiba,
Tun shekaran jiya nasanya d'an uwanka Fahad yakiramun kai domin mutattauna akan tafiyar da zamuyi a gobe zuwa yola, domin nemawa Fahad auren Bahijja,
Amma dazarar antukari d'akinka sai aji kofa a rufe harka fita."
Ina kake zuwa?"
Meke damunka wadda a matsayinmu na mahaifanka bazaka iya fad'a mana Shiba?"

Adnan yasunkuyar da kansa k'asa yace "ranka ya dad'e tuba nakeyi,
Munkun fara jarabawa karatu ne yake hanani sukuni kwana biyu nan, kayi hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwaba, tuba nakeyi.

Maimartaba yayi murmushin jin dad'i
Yace "meye shawararka na tafiyar da zamuyi yola gobe Neman auren Fahad da Bahijja?"
Banida wani buri a rayuwata illah naga na aurar daku lokaci d'aya dakai da d'an uwanka, amma kai har yanzun ba kasamu matar da kakeso ba,
Mamynka tasha nema maka 'ya'yan k'awayenta amma gaba d'ayansu bbu wace tayi maka a rayuwarka,

Adnan yakuma sunkuyar da kansa k'asa yace Allah ya taimakeka ai nesa tazo kusa,
Murmushi jindad'e yayi, yace "Allah yasa cemun zakayi kasamu matar aure, danafi kowa jin dad'i,
Sai na had'aka da d'an uwanka na aurar daku gaba d'aya.

Adnan yayi murmushin jin kunya, yace "kusan hakan ne ranka ya dad'e,

Maimartaba yace "Alhamdulillah.
'Yar waya?"
A wace unguwa take?"
Waye mahaifinta?"

Adnan yayi murmushi ya sunkuyar da kansa, yace Allah ya taimakeka k'auwar Bahijja ce Bilkisu, tare muke karatu da ita, kuma munfahimci junanmu tana sona Nima inasonta, Abba ka taimakamun karnasa Bilkisu.

Maimartaba yace Alhamdullah abu yazo gida kenan, amma naji dad'i sosai Allah yasa abukanin arzikinkune.

Murmushi yake yana cike da jin kunya ya amsa da Amin Abba,
Mikewa tsaye yayi zaitafi d'akinsa, yace Abba natafi sai da safe,
gobe tafiyar safe zakuyi kuwa?"
Maimartaba yace "tafiyar safe nakeso muyi in Allah ya yarda.

Allah ya tsareku Abba ya kuma kaiku lafiya dawo mana dakai cikin koshin lafiya.

Cike dajin dad'i Abba ya amsa da Amin Adnan.

Yafito yanufi d'akinsa shekad'ai yasan abunda ke cikin zuciyarsa.
Shigarsa d'akin yacire kayansa, yana mai dariyar mugunta yana fad'in gimbiya Bilkisu kenan kinshigo hannuna zanwula k'antaki yanda naga dama, domin ba d'igon sonki a cikin zuciyata ko d'aya,
kuma dole kiyi biyayya saboda kina k'arkashin inuwar aurenah,

Zanyi amfani da wannan damar na aure ki domin nad'auki famsar abunda kika aikatamun a gaban bainar jama'a.

Ya kuma yin murmushin mugunta, yacije baki, yace "nalura da idanunki saikin buk'atar d'a namiji,
da wannan zanyi amfani, na azabtardake azaba mai tsanani, saikinyi danasanin aurenah rayuwarki."

Yayi kwanciyarsa yana tunanin mugunta iri iri a rayuwarsa."

Maimartaba sarki Bashir mahaifinsu Adnan yasauka garin yola lafiya,
Inda yasamu tarba da karramawa a masautar yola,
Yayi farin cikin karramashi da akayi,
Daga nan yashiga fad'awa mai martaba abunda ke tafe dashi."

yazo neman auren Bahijja da Bilkisu,
Sarki Abdulraham yaji dad'i kuma yayi farinciki da zuwan nasa,
yace " aidakayi zamanka ba saikazoba ko aike kayi ya wadatar, kuma Bahijja da Bilkisu 'ya'yankane duk yanda kazartar da hukunci a kansu dai dai ne, ba saika taso tun daga kano zuwa yola nemawa Fahad da Adnan aureba.

Amma wani hanzari ba guduba, 'yarka Bilkisu karatu takeyi bansaniba ko Adnan zai iya jiranta harta kammala karatun nata sannan daga baya sai ayi bikin nasu, a lokacin ta mammals karatun nata.
hakan naga yafi.

Sarki Bashir yayi murmushin jin dad'i yace Bakomai hakan da katsara yayi dai dai zanje na shawarci Adnan idan yanada ra'ayin barinta karatu bayan anyi auren saitaci gaba da karatun dama kuwa makarantarsu d'aya.

Murmushi sarki Abdulraham yayi yace "hakan shine daidai idan ya amince sai ayi auren gaba d'aya,
Nima zankira Bilkisu domin naji ra'ayinta a kan hakan,

A haka sukayi sallama suka rabu cikin farin ciki da kewar juna.

Bilkisu kwana biyu hankalinta ya kwanta ta natsu karatunta tasanya a gaba, domin sunkusan fara exam, tsakaninta da prince sai dai kallo, itama mamaki yakebata domin gata gashi sai dai yarab'ata yawuce itama hakan,
Tana mamakinsa amma a zuciyarta bata yarda dashi ba domin tasan a kwai wata kullanliya dayake kullawa a rayuwarsa,
Ita kuma ta d'auki d'amarar duk abunda yake nufi tafishi jinsa.


TOPHA OHH NI UMMU SAFWAN












Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR......

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page 3⃣2⃣ 3⃣3⃣

A haka suka cikagaba da zama da prince a makaranta babu be kula wani daga cikinsu,
Abu d'aya yake damunta dashi a kullum idan suka had'u sai yayi mata wani kallo nasama da k'asa sannan yacije baki yayi tafiyarsa, abun yana bata mamaki amma bata kulashi."

Seefana tace "sister naga mutumin naki kwana biyu nan ya daina kulaki?" Kodai yaga baya iyawa da fitinarki ne?" Domin kema idan yayimaki bakyaleshi zakiyiba,

Bilkisu tayi dariya tace " nasan bazai barniba domin inaji a rayuwata da kwai abunda yake shiryawa, domin nasan halin Adnan sarai baya barin bashi,

Wayar da kecikin jaka ta d'auki ruri, ita takatse masu maganar da sukeyi da safeenat,
Sauri bud'e jakarta tayi domin tasan Abbantane ke kiranta domin ringing d'insa daban ne tasanya masa,
Takara wayar a kunnenta tare dayin sallama ta gaidashi cikin fara'a dajin dad'i,
Abba shima cike da farin ciki yake amsa gaisuwa gimbiya Bilkisu,

Bayan sunk'are gaisawar Abba yake shaida mata da tashigo mota gobe yana son ganinta akwai maganar da yakeso yayi da ita,

Bilkisu tayi mamaki sosai take tambayarsa Abba lafiya kuwa?"
Ina Ammi nah take?"

Yayi murmushi yace "Ammi ki lafiyarta k'alau gata a kusani, taja wani dogon ajiyar zuciya,
Tace Abba bata wayar mu gaisa naji muryanya,

Abba yamikawa Ammi waya suka gaisa, sannan zuciyar Bilkisu tayimata sanyi,
Tace "insha Allah gobe zamuyi asubanci mutafo tareda fadawa gaba d'aya,

Abba yace "yawwa gimbiya Allah yayi maki albarka, yakawoki lafiya, tace "Amin Abbana sukayi sallama,
Bayan ta k'are waya da Abbanta,
takira fadawa take shaida masu gobe su zama cikin shiri yola zasu tafi, kuma tafiyar safe take buk'ata suyi, su tabbatar da sunwake motocin da zasuyi tafiyar dasu,
Suka amsa mata da angama ranki ya dad'e,
Takashe wayarta tasanya a jaka,

Takai dibanta ga Safeenat tace "sister gobe fa yola zantafi Abba yana nemana amma ina ganin kwana d'aya zanyi saboda munkusan fara jarabawa,
Safeenat tace "sister Allah yakaiku lafiya ya kuma dawo dake lafiya,
Bilkisu ta amsa da "Amin."

Ashe duk maganar da sukeyi a kan kunnen Abdullah da yazo giftawa ta wurin yaji Bilkisu na waya, tana fad'in to Abba insha Allahu gobe da sansafe zamuyi asubanci mutafo tare da fadawa."

Ai kuwa Abdullah yaja gefe d'aya ya tsaya inda bata iya ganinsa saida ta kammala wayar,
Har maganar da sukayi da Safeenat duk a kan kunnensa, ya fahimci gobe yola zata tafi kenan?"
Aikuwa yashiga jin dad'i domin bazai yarda ba dashi za'atafi baza'a barshi garin Kano ba,

Juyawa yayi ta bayanta yayi tafiyarsa gida yashiga harhad'a kayansa gobe sai yola, domin ba zai yardaba k'afarsa k'afar fadawa ko a but ne ya amince a sanyashi a tafi dashi yola,

Wasa wasa Abdullah beyi barciba Allah Allah yake safiya ta waye masa yagansa a mota sunmik'i hanyar yola,.

Dakyar yasamu asuba tayimasa tun kafin mahaifinsa ya fito zuwa masallaci Abdullah yarigashi fitowa rataye da jakar kayansa yayi saurin bud'e gida yanufi masaukin fadawa,

Yana isa k'ofar gidan ya tarar da motoci Jere har basa k'irguwa, sunbi layi alamar ba'a jima da gama wankesu ba,

Yakai dibunsa a gaba d'aya motocin saida gabansa yafad'i,
A zuciyarsa kuma yace "Alhamdulillah Ashe inada Rabin zuwa masarautar su Bilkisu,

Yadiba gabas da gamma gudu da arewa bega alamar mutum ko d'aya ba,
Ya fahimci cewa suna masallaci sallah sukeyi,
A can ya hango wata mota rab'e gefe d'aya ya rataya jakar kayansa yanufi motar yayi tsaye, ya kai dibansa a cikin motar yahango rubar ruwan faro,
Yabud'e murfin motar ya d'auko robar ruwan yayi arwala ya tayarda sallah a bakin motar, domin da zarar yashiga masallaci to kafin yafito suna iya tafiyarsu subarsa,

Bayan ya k'are sallah ya bud'e murfin motar yayi shigewarsa gidan baya rungume da jakar kayansa,
ya d'au minti biyar a motar, saiyaji zafi yayi masa yawa, yashiga zuge glass d'in motar domin iska yashigo masa,

Aikuwa anan take sanyin asuba mai had'e da iska mai dad'i yashiga ratsashi, dama besamuyin barci jiyaba,
Abdullah yasaki baki da hanci sai kwasar barci yakeyi rungume da jakar kayansa."😊

Gimbiya Bilkisu ta shaidawa fadawa cewa da zarar sun kammala sallar asuba zasu wuce,
Haka kuwa suna k'are sallah kowannesu ya shiga motarsa suka nufi gidan Bilkisu domin d'aukarta suwuce.
Koda suka isa gidan Bilkisu tareda jakadiya har sun kammala shirinsu tsaf suka fito sukashiga mota suka d'au hanyar."

Abdullah nacan cikin motar mutane yasaki Baki da hanci sai kwasar barci yake harda yawun barci😊

Saiji yayi ankwankwasa murfin motar a zabure ya farka cikin gigin barci yake fad'in ankawo yolar?"πŸ™ŠπŸ˜‚

Bud'e idonsa da zaiyi yayi arba da wani k'aton soja bak'i sed'ik dashi dawani k'aton ciki idanunsa jajir,sai wani huci yake, ya kai dibansa ga Abdullah yace "ubanwaye yashigo dakai cikin motanah?"

Abdullah sai da cikinsa ya d'uri ruwa, yafito cikin motar ya maida idonsa a k'ofar gidansu fadawan yaga bbu motocin da yagani d'azun har sunyi tafiyarsu yola kenan, yad'ora hannu a kai ya kurma ihu,
Soja narik'e da kwalar rigarsa yana cewa "yakama b'arawo cire belt d'in wandonsa yayi yana neman zugawa Abdullahi shi, Abdullah saibada hakuri yake gashi bayada wuyar sakin fitsari,
Aikuwa soja na d'aga belt daniyar zugawa Abdullah, sai ga fitsari yadinga zuba a wandonsaπŸ˜‚ yarik'e belt d'in, mutane ne suka zagayesu suna tambayar abunda ke faruwa aikuwa Abdullah yanasamun sa'ar soja ya gantsaramasa cizo a hannu soja yakwatsa ihu, yasaki Abdullah ya yana diban hannunsa,
Shikuwa Abdullah ya zuba da gudu yabar jakar kayansa a motar soja😊













Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASAUTAR.....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


Page 3⃣3⃣ 3⃣4⃣

Dedicated to my lovely sister NA'IFA YAHAYA Allah yasauki lafiya mutafo garin Kano mukwashi shokiπŸ˜„πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―





Gudu yake akan titi yana motsa jininsa,
Dama haka al'adarsa take, dazar yayi sallar asuba tunkafin safiya tawaye, kafin mutune sufara firtuwa,
Prince yake gudun a kan titi domin motsa jininsa,

Yauma hakan takasance gudu yake a kan titin, saiji yayi mota ta bangajeshi, tayi sama dashi ta yafar akan titi,
Tundaga lokacin Be kuma sanin inda kansa yakeba,

Mai motar kuwa Yakama gabansa yayi tafiyarsa, yabar prince kwance cikin jini kota ina zubar masa yakeyi,

Gimbiya Bilkisu tareda fadawanta a kan hanyarsu ta barin gari,

Sun iso daidai wurin da abun yafaru,
Ganin mutane sunyi cincirindo a tsaitsaiye yasa ta kai dibanta a wurin taga mutane sun tsaitsaya alamar wani abun suke kallo,

Tayi saurin d'agawa fadawa hannu alamar su tsaya."
tabasu umurni sufita suga meke faruwa?" taga mutane tsaitsaiye a kan titi?"

Wasu daga cikin fadawan suka fito, suka nufi wurin da abunyafaru,
sukaga mutum a kwance cikin jini, anrasa mai taimakamasa."

Sukayi saurin nufo Bilkisu dake cikin mota a zaune, suna shaida mata, da cewa
Hatsarine ne yafaru ranki ya dad'e, wadda kuma abun yafaru a kansa yana buk'atar taimakon gangawa domin duk mutanen dake wurin tsoron tab'asa suke.

Tayi saurin bud'e murfin mota tafito, tana bada umurni da a d'aukeshi a nufi asibity dashi,

Nan take fadawa suka tallebesa a kasanyashi a mota suka nufi asibity dashi,
Asibitin kud'i suka nufadashi,
Bilkisu tabada ATM CARD d'inta akaciro mata kud'i ta dank'awa d'aya daga cikin fadawan kud'in, tabashi umurni duk abunda ake buk'ata yayi amfani da kud'in asaya.
Takoma warta mota tayi zamata tareda jakadiya."

Likitoci suka kawowa prince taimakon gangawa, suka tallabesa suka nufi d'akin da za'a dibashi.

Prince kwance cikin jini kamar bayada rai saiwani numfashin wahala yake fitarwa,
Likitoci tsaitsaye a kansa domin ceto rayuwarsa,

Babban likitan yabada umurni da akiramasa d'aya daga cikin wad'anda suka kawosa,

Fadawa suka nufi ofishin likita yake shaida masu majinyacinsu yana buk'atar asanyamashi jini da gangawa,
Idan ba hakan ba yana iya rasa rayuwarsa a kowane lokaci, domin jininsa yakusan k'arewa ajikinsa,

Dan haka aje cikin 'yan uwansa a nemo wasu daga ciki wad'anda jininsu yayi daidai danasa sai a d'ebeshi a sanya masashi,

Fadawa suka fito suka nufi wurin gimbiya Bilkisu suna shaida mata abunda likita ya fad'amasu, jini ake buk'ata asanyawa mutumin da suka kawo,

A razane tafito a motar tana kallonsu, d'aya bayan d'aya tace, to Ku meye amfaninku da bazaku bada jininku a sanyawa musulmi d'an uwanku domin ceto rayuwarsa ba?"

Kallo suka bita dashi cike da jin tsoro,
Fahimtar haka da tayi daga garesu yasa,
Tarab'asu tawuce cikin sauri tanufi ofishin likita,
Tura k'ofa tayi tashiga tareda yimasa sallama, bata jira amsawarsa ba, ko kuma ya bata umurnin zama ba,
Taja kujera ta zauna,

Likita saibinta yake da kallon mamaki,
Yace malama lafiya?"
Daga ina haka?"

Takai dibanta a wurin likita tace " yi hakuri docter banyi maka bayanin koni wacece ba, wlh duk a rud'e nake,

Marar lafiyar damuka kawo yanzun,
wadda ke buk'tar jini cikin gangawa, shine nazo domin a d'ebi jinina a sanya mashi, domin idan akatsaya Neman 'yan uwansa zai iya rasa rayuwarsa,
Don Allah docter kayi Sauri ka auna jinina idan yayi daidai danasa a sanyamashi.

Likita yatsora mata ido cike da mamaki, yace "idan son samune munfi buk'atar asanya masa jinin namiji a kan na mace,
Saboda mace tana haihuwa kuma tana zubarda jini duk k'arshin wata,

Mik'ewa tsaye tayi cike da b'acin rai, tace "dakata Docter βœ‹πŸΌ kaifa kace yana cikin mawuyacin hali mutuwa ko rayuwa?"
Amma kakeyimun wani dogon zance, magana d'aya nakeso kafad'amun,
Ana iya d'ibar jinin mace a sanyawa wani koba'a d'iba?"

Docter yace ana d'iba amma idan mace ta jima bata haihuba,

Bilkisu tace "toni bantab'ayin aure ba bare na haihu,
Docter sanyamun abun d'ibar jini, kad'iba kak'arawa bawan Allah karya rasa rayuwarsa.

Da Sauri likita ya d'auko kayan aiki ya kwantar da ita kan gado yashiga d'ibar jininta.

Bayan minti talatin ta tashi daga kan gadon, fadawa sai sannu suke jera mata.

Ganin likita tayi a gabanta yana mata sannu had'i dayimata tambayoyi,
Babu abunda kikeji a jikin?"

D'aga masa kai tayi tace "banajin matsalar komai docter.

Yace "Alhamdulillah mund'ebi jininki roba biyu,
Asanya masa wadda insha Allahu munasaran farkawarsa nan da awa d'aya,

Tace "Allah yabashi lafiya."

Likita ya amsa da "Amin."
Ya kuma kallonta yace "amma ke matarsa ce ko?"

Domin a zamanin damuke ciki babu wadda zai iya taimaka maka da jini sai mahaifiyarka, ko kuma matarka, kodai wani d'an uwanka koshi d'an uwanka najini,

Bilkisu tayi murmushi tace niba matar sabace, ba kuma 'yar uwarsa bace,
Asalima bansan koshi wayebane,
Domin har yanzun banga fuskarsaba, tsoho ne, ko yarone, bansaniba, taimako nayimasa saboda Allah domin duk wadda ya taimaki wani Allah zaitaimakesa."












Pls 'yan uwana kutaimakamun da addu'a idanuna ciyo yakemun sosai





Writing by Fareedah bashir
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




Page 3⃣6⃣ 3⃣7⃣

Bilkisu ta sauka garin yola lafiya,
Inda dukkanin wad'anda ke cikin gidan masarautar yayi murna da farin cikin dawowarta.

Bayan tayi wanka tashirya taci abinci, ta sauko k'asa tanufi sashen maimartaba domin taji Neman da yakemata,

Ta Tarar da maimartaba kishin gid'e a kan kujera,
Tayi sallama tashiga.
Tasamu wuri a k'asa gefen k'afarsa ta zauna, ta sunkuyarda kanta k'asa tace "Allah ya taimakeka Allah ya k'ara maka lafiya,
Gani nazo ranka ya dad'e Allah yasa ba laifi tanayiba,

Maimartaba yayi murmushin nan irin nasu na manya,
Yace "aibakya laifi Bilkisu,
Domin kina kiyaye duk wani abuda kikasan zaib'amun rai,
Dan haka nafifitaki a cikin 'ya'yana.

Wato Bilkisu wata shawara nakeso muyidake wadda maganar waya bata isa,
Saikinzo gani gaki.
Bilkisu kinsan d'an sarkin kano,
Fahad shiyakeson Bahijja,
Ta girgiza kai.
To satinda yawuce mahaifin yaron wato sarki Bashir, yazo da kansa ba aike yayiba,
yazo neman aurenku keda Bahhija.
Saida gaban Bilkisu yafad'i

Yaci gaba da cewa Kema d'ansa Adnan yaganki a makaranta, yanunamun dacewa, harkun fahimci junanku, dan hakan nayanki hukunci aurardaku gaba d'ayanku keda Antynki Bahijjah.

maimartaba magana yakeyi amma gaba d'aya hankalinta bayajikinta, musamman dataji ya ambaci yabadasu gaba d'ayansu,
Idanunta ne suka cika da hawaye tasunkuyarda kanta k'asa yadda Abbanta bazai iya ganin hawayentaba,

Maimartaba tunda yafara yin magana yake kallon yanayinta yalurada lokaci d'aya tacanza masa daga k'arshe hawaye take zubarwa,

Yace subahanallahi Bilkisu laifi?"
Meyasanki zubarda hawaye?"

Goge hawayenki kidaina kuka,
Idan maganar aure ce bakyaso daki zubarda hawayenki k'ara afasashi,
Nima abunda yak'arabani kwarin gwaiwar yimasa alk'awalin badake, yazomun da mgnar cewa kunfahimci junanku a makaranta dake da yaron.
Amma wallahi Bilkisu mundun bakyaso to alk'awari ne bazan maki auren dole ba,

Kanta a sunkuye k'asa sai zubarda hawaye take,
Gaba d'aya tausayin mahaifinta duk yagama lunlub'eta, a zuciyarta,
Wato domin ya faranta mata rayuwa yana iya ruguza alkharin dayayiwa sarki Bashir nabayardasu dayayi gaba d'ayansu,
Abba idan yayi haka kuma har abada sarki Bashir bazai kuma yarda da maganarsaba,
Sannan kuma idan yayi hkan, yaya k'auwarsa sarki bashir Amminmu zaji dad'i wadda suke uwa d'aya uba d'aya, da sarki Bashir,
Zai iya zamantuwar rugujewar zumcinsu,

Maimartaba yace "gimbiya Bilkisu kenake saurare, kukan da kikeyi nameye?"

Takuma sunkuyar da kanta k'asa tace"Abba karatuna banaso nayi aure batareda na kammala karatunaba,
Abba inaso nayi karatu sosai domin nataimaka 'yan uwana mata takowace hanya,

Abba yace "nasan kudirinki a kan karatunki, gimbiya Bilkisu,
Nayiwa sarki Bashir bayanin karatunki,
Yace zai tambayi Adnan d'in idan yaji yagani ya amince zaibarki idan akayi auren saikici gaba da karatunki
Idan kuma be aminceba to lallai bazan auran dakeba sai bayan kin kammala karatunki har lokacinda burinki yacika, gimbiya Bilkisu,

Murmushin dole ta k'wakwalo tayi, had'ida kallon mai marmarba,
Tace nagode Abba,

Yace "goge hawayen kitashi kitafi kikwanta kihuta nasan kinsha gajiyar hanya,

Tamik'e tsaye had'ida yimasa sai anjima,
Tafita daga d'akin,
Tafiya takeyi kamar wadda kwai yafashewa a cikin domin gaba d'aya batacikin hankalinta, da kyar tasamu ta isa d'akinta cikin mawuyacin hali.

Akan gadonta tafad'a tasaki wani wahalallen kuka mai tsuma zuciya,
Tana magana ita d'aya kamar wata zaranriya,
Ashe dama Adnan d'an uwanane yake wulak'antani hakan?"
Meyake nufi da turowa Neman aurena?"
Wani sabon salon wulak'anci dacin zarafi zaikuma yimun bayan ya aureni?"
Domin a bakinsa yasha furtamun bayasona, bayason ganina,
Me kama danima idon ya ganta sai ya hukuntata,
Sannan ace da wannan zanyi rayuwar aure?"😭
Takuma b'arkewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya,
Tana danasanin had'uwarta da Adnan a rayuwarta gashi yanzun yana neman ruguzamata rayuwa."



Adnan kuwa gaba d'aya yasusuce baya da maganar kowa sai ta Bilkisu,

Anty Bahijja ke k'ara kwantar masa da hankali akan cewa Bilkisu insha Allahu takusan zama matarsa,

Likita ya turo k'ofa yashigo had'ida yimasu sallama yanufi gadon Adnan domin ya ciremasa rubar jinin da ke hannunsa,
Doctor yakai dibansa ga Adnan yayi murmushi yace " Adnan angon Bilkisu ina fatan ba abunda kemaka ciyo domin munasan ran sallamarka nan da zuwa gobe,

Adnan kwance yake amma jin doctor ya ambaci Bilkisu yayi zumut ya mik'e zaune,
Yana murmushi yace doctor kokasan Bilkisu ne?"
Kaga mundace da juna ko?"
Gata fara kyankyanwar yarinya mai dogon hanci, ga k'aramin baki,


Please Login or Register in order to submit comment