Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kabiyo ta wannan hanyar."?

Betankawa Abdullah ba, sai gudu yake shararawa, Abdullah duk ya tsorata da ganinsa cikin wannan halin.

Sai ganin yayi.
yayi parking a dai dai k'ofar gidansu Bilkisu, waya yad'aga yakira fadawansa, yayi masu kwatancen a inda yake suzo susamesa.

Ya mayarda kallonsa ga Abdullah yace, "yau zannuna mata na i'sa nakoresu a garin nan,kora ta wulak'anci, kuma zan a zabtar dasu har saitayi nadamar marina datayi a gaban bainar jama'a,
Itama zan wulak'antata kamar yanda tayimun a gaban bainar jama'a.

Yana rufe bakinsa saiga fadawa sun iso kowanesu jira yake abashi umurni.
Runsunawa sukayi suna kwasar gaisuwa, kallo yabisu dashi d'aya bayan d'aya, yayi masu nuni da gidansu Bilkisu,
Yace "kushiga gidan nan kufitomun da duk wani abu dake cikin gidan nan, tareda bil adaman dake rywa acikinsa, duk a fitomun dasu yanxun nan."

Fadawa suka afka gidan, suka tararda jakadiya zaune tana yankan a aifa, sai ganin fadawa tayi gabanta, kallonsu tashigayi cike da mamaki, ita dai tasan ba fadawan masarautarsu bane, tomeye had'insu da wad'an nan fadawan? Tashiga yiwa kanta tambayoyi. Saiji tayi anwatso mata a kwatin kayansu a k'afa, cike da mamaki take kallonsu tana fad'in "lfy"? Meyafaru"? Me mukayumaku"? Basu saurare taba sukaci gaba watso masu kayansu a waje."

Bilkisu kuwa na makaranta, batasan abunda ke faruwaba. Kuka takeyi, safeenat sai hakuri take bata, gameda abunda prince yayi mata.
Mekewa tayi tsaye cikin yanayin damuwa tace sis zantafi gida kaina ke yimun ciyo, bazan samu damaryin test d'in nanba domin kona tsaya bazan iya rubuta komaiba.

Safeenat tace "sis Allah ya sauwak'e, idon kikaje gida kisha magani. Ynxun da munfito gani nan zuwa naga jikin naki.

Bilkisu tace "to sis ngd saikin shigo."
Tawuce tatari mai adai2 sahu yakaita gida.
da shigarsu kwanar unguwarsu ta hango mutane, sunyi cincirundo a k'ofar gidansu mamaki tashigayi tana tambayar kanta lfy"? Taka mutane haka a k'ofar gidansu?

K'arasawa tayi domin ganin me kefaruwa, sai ganin kayansu tayi anawatso masu a kofar gida,
Jakadiya sai kuka takeyi tanabada hakuri amma basu saura ra mataba,

Bilkisu nazuwa wurin gaba d'aya kallo yadawo Kanta, ganin fadawan prince tabawa kanta amsar wadda yasanya suyimasu irin wnn wulak'ancin, batabi takan kowaba sai wurin jakadiya tanufa dake durkoshe tanabawa fadawa hakuri,
Durkusawa tayi tad'ago jakadiya tsaye tace "Ammi meye abunbasu hakuri a ciki? Ki kyalesu kawai suyi abunda sukeso.
Tana mgna amma idanunta sun cika da hawayen bak'in ciki.
Yau ita gimbiya Bilkisu itace ake wulak'antawa a gaban bainar jama'a😭
Tana rungume da jakadiya suna kuka."

sai tab'i taji anayi a bayanta, juyawarda zatayi ganin prince tayi tareda Abdullah sunayimata dariyar k'eta.

Kallo tabisu dashi sama da k'asa,
Prince yace " ni nasanya a yimaku hakan, domin bana muradin ganinku a k'asata, bakeba ko mai kama dake nagani saina sanya ankoreta a garin nan, bareke. Na tsaneki banason ganin fuskarki bare mai kama da fuskarki.

Kallon tsana tabisa dashi, tana mai zubarda hawaye, tace "banada niyar mugunta amma kaine mutum na farko da zansanya a axabtar dashi a zaba mai tsanani,
banada niyar amfani da damata domin wata manufa marasa kyau, amma Kaine mutum na farko dazaka sanyani yin hkan,
Kasani na tsaneka tsanawa mai tsanani. Ka wulak'antamu a gaban bainar jama'a kaima ka saurare naka hukunci gobe.
Tana kaiwa nan Safeenat tafito cikin a dai dai sahu, ganin Prince tsaye tabawa kanta amsar tambayar dazatayi,

Bilkusu tayi karfin halin yimata mgba tace sis tsayar mana da mai a daidaita karya tafiyarsa.
Tsaidashi sukayi takama hannun jakadiya tasanyata a ciki, sanan tadawo d'aukar kayansu, ba komai tad'aukaba sai jinkar takardunta, sai kuma a kwatin kayansu, tasanya a bayan adaidai ta.
Mutane sai kallonta suke suna mai tausaya mata.

Dawowa ta kuma kiyi, tanufi gefenda makwanciyarta take tsaye tana zubarda hawayen tausayinsu domin sunyi matuk'ar sabawa da ita

Cikin yanayin kuka ta nufo Bilkisu ta rungumeta tana kuka, Bilkisu tayi k'arfin halin yimata mgna, tace
"Hajjah daina kuka zandawo gareku bada jimawaba, abunda nakeso dake yanxun kisamu yara sukwashe maki duk wani abu dake wurin nan, nabaki shi kyauta, sanan ta Nuna wani k'aton frege tace wanan kuma a kai sa gidan liman nabasashi."
liman dake tsaye cikin yanayin tausayi yanufota yana godiya, domin tun zuwan Bilkisu a unguwar duk ranar juma'a saitasanya ayimasu abincin sadaka duk wanda yazo sallah a masalancin to saiyaci abincin Bilkusu yana mai sanyamata albarka, sannan shima liman d'in duk zai sallar juma'a dasabon d'unki yakeyi wadda Bilkisu take d'unka masa.
Abunda yasa suka saurarawa wadda yayi mata hkan, ganin fadawa dasukayi da kuma Prince da ke tsaye domin sunsan halin prince ba imani ke garesa ba.

Sanan tanuna wasu durum2 na ruwa tace liman a kai wad'an nan masalanci a dinga zuba ruwan alwala."

Tana kaiwa nan tajuya tanufi wurin prince dake tsaye yana kallonta sai a lokacin yafara tausayamata, tanuna masa hannu tace" kasaurare hukuncin da zanyi maka gobe dakai da duk wasu magoya bayanka."

Tabarshi nan a tsaye tashiga a dai2 ta suka nufi gidansu sakeenat."





















Ummu Safwan 😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAURAR..

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




Page1⃣6⃣


Gimbiya Bilkisu ce kwance a kan makeken gadonta, tana xubar da hawaye, tana tuna irin wulak'ancinda prince Adnan yake mata, a bainar jama'a, to ita metamasa? meta taremasa a rayuwarsa?"

To tabbas idan befita rayuwartaba sai yayi nadama, a rayuwarsa."

domin zatayi amfani da mulkinta da sarautarta tasanya a azabtar dashi,axaba mai tsanani."

A haka tak'arasa kukanta har b'arci barawo ya saceta."

Shiri takeyi domin tafiya makaranta, yau Monday, test kegaresu maizafi, domin test d'in darasinda zasuyi malamin ba sauk'i ke garesa.
A gurguje ta kamlla shirinta tafito, domin tayi breakfast.
Safeenat sai wayatakeyi mata da tayi sauri lokaci yakusan k'orewa.
Fitowa tayi tana shedawa jakadiya, tafiyarta.

Jakadiya sai addu'a takeyamata, tareda kirari
Murmushi Bilkisu tayi tace "jakadiya bazaki dainaba kenan. Tayi tafiyarta."

A makaranta tasame safeenat tana jiranta domin saura binti 10 sufara test d'in,
samu wuri tayi tazauna a kusa da safeenat, Bilkisu tace "sis yau makara nasoyi. Allah kawai yatsare danayi loosing din test d'in nan.

Safeenat tace baki kwanta dawuri bane sis, kina can kina tunanin masoyinki da ke yola, tana fad'a mata hakan ne cikin yanayin wasa,

Bilkisu takai mata dukan, wasa tace "Allah yatsareni aini banada saurayi. Ke banma tab'ayin soyayya a rywataba, saboda ni har ynzun banga namijin da yayi dai dai da tsarin rayuwata ba."

Safeena tarik'e bakiπŸ€” tace "keko sis wani namiji ne wannan kikeso ki aura haka?

Bilkisu tace wannan nabarwazuciyata."

tashi mutafi kinga ga uncle can na hango zai shiga class kinsan halinsa idon ya rigamu shikenan munyi loosing d'inta, muyi sauri murigashi k'asarasawa."
Suka mike suka nufi ajin.
Tafiya sukeyi wadda zata sadasu ajin nasu,

Bilkusu saiji tayi ancire mata hijabi daga bayanta, kankame jikinta tayi cikin jin kunya.
tayi tsaye wuri d'aya, juyawa tayi domin ganin waye yacire mata hijabi, sai ganin prince tayi a tsaye tareda k'awayensa, yacije baki yana murmushin mugunta, k'awayesa sai dariya sukeyimata.
Safeenat tasoma yimasu magiya, tace " don Allah prince kayi hakuri kabata mayafinta, idan wani abu takeyimaka wlh daga yau ta daina bazata kuma yimaka shiba, pls PrinceπŸ‘πŸΌ

Tsawa yadaka mata, yace "ina ruwanki"? rufemun baki, kada ki kuma yimun katsalande s al'amunrana".

Shuru tayi taja gefe ta tsaya.
daga k'arshe tacire d'ankwalin kanta, tabawa Bilkusu tarufe jikinta dashi.

Dariya suka dinga yimata suna nunanta da hannu, musamman prince Adnan da Abdullah,
Matsowa yayi kusa da ita, yana mai murnushin mugunta, yace "Bilkisu ne sunanki kowaye? Ashe ke ba kowa bace? Ba kuma 'yar kowabace face 'yar talaka, masu zaman kansu.
Harkike neman fad'awa jinin sarauta. mu samman ni prince Adnan yanuna kansa da hannunsa.
To zakiyi nadamar abunda kikayimun, za kuma kiyi danasani a rayuwarki, domin daga yau, bazaki kuma zama a garin nan ba.
Zanyi amfani da mulkina da kuma sarautana, nasanya akoreku a garin, nan dake da mahaifiyarki. domin nanumaki k'arfin mulkina, kuma kitabbatar da cewa mulki da sarauta, ba abun renawabane, musamma a irinku talakawa matsiyata.

Makure take a bayan Safeenat, sai kuka takeyi, musamman jikinta dake sake kowa sai kallonta yakeyi, sanye take da atamfa riga da siket, sun d'an kama jikinta, amma ba sosai ba gata Allah yahoremata dukiyar Fulani. d'ankwalin da Safeenat tabata shine tarufe k'irjinta dashi.

Kuka takeyi tana kallonsa sama da k'asa, tace " tabbas yau na tambatar da cewa kai jahiline, baka da tausayi.
zuwa makarantar kawai kake, amma baka amfani da abunda ake koyarda kai, nagane zuwa makarantar kawai kakeyi badon kayi karatuba sai domin kanuna cewa kai d'an sarauta ne, kataka talaka wanka, yanda ranka yakeso, kai a tunanin ka shine mulki Ko sarauta?
To ba mulki bane, wannan shi akekira da jahilci wadda yake d'awainiya da kai a yanzun,
Sannan kasani baka i'sa ka koremu a garin nanba, domin bada ku'din masarautarku aka gina garin nan ba, sannan ina mai tabbatar maka da saikayi nadamar abunda ka aikatamun,"

Kuka take mai tsuma zuciya. Shikuwa sai kallonta yake cikin jin dad'i domin yasan daga yau bazata kuma yimasa rashin kunyaba.

Abdullah yace ke 'yar matsiyata duk'a kibawa prince hakuri yabaki hijabinki, domin ransa yab'aci.

Kallo tabi Abdullah dashi, cikin b'acin rai, ta d'aga masa hannu ya isah, sarkin molarsa, tobada kai nakeyiba dashi nakeyi, kabarshi yabud'e kazamin bakinsa yayi magana, bakaiba.
Kuma ina fatan a cikin mgnarka babu kalaman ban hakuri a cikin domin idon zamu shekara hka baka isa nabaka hakuriba.

Prince dake tsaye takawomasa mak'ura, ya kalleta yace "tabbas yau saina bak'antamaki, kuma saina musguna maki, har saikin durk'usa k'asa kinbani hakuri sannan zankyaleki, sai nanuna maki keba kowa bace, face baiwa, ba kuma baiwar kowaba face baiwata wulak'anta tarciyar baiwa."

Yana rufe bakinsa saiji yayi ta d'auke masa fuska da mari, tana wani huci.
k'arya kakeyi nazamar maka baiwa kuma mafi wulak'antar baiwa a wurinka.
Ta kuma matsawa gab dashi, tasanya talkaminta mai tsiniπŸ‘  ta takamasa k'afa, ta Murza, saida prince yasaki k'ara mai sauti wadda tajawo hankalin d'aliban makarantar yadawo kansu, sanan tasa hannu ta k'arbe hijabinta a hannunsa

taja hannu safeenat, suka bar wurin tana mai zubarda hawaye."

Anan tabar prince durk'ushe yana murk'usun k'afarsa, Abokaninsa sai sannu suke jeramasa, idonsa ya rikid'e yayi jajir.

Kallo yabi Abdullah dashi, yace "tabbas yau d'in nan sai sunbar garin nan ita da matsiyaciyar uwarta, mik'ewa yayi tsaye ja hannun Abdullah suka shiga mota suka nufi gidansu bilkisu."











Ummu safwam
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR...

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S



Page 1⃣8⃣


Prince naganin tafiyarsu, Bilkisu, ya shiga motarsa tareda Abdullah suka nufi asibiti domin adiba masa k'afarsa dake xubar da jini."

Likita ya kyaramasa k'afar tareda bashi maganun nuka domin yayi amfani dasu yasha."
A jiye Abdullah gida yayi, shikuwa ya k'arasa gida."

Da shigarsa gida, ya hango Bahijja tareda yarima Fahad a zaune suna hiransu ta masoya."
Ganinda yayiwa Bahijja saida gabansa yafad'i domin ya d'auka Bilkisu ce tabiyosa har gida domin d'aukar fansar abunda yayi mata, dan shi yanzun harga Allah tsoron Bilkisu yakeji, dan muguwace, ta iya mugunta."
ya kai dibansa a k'afarsa, inda ta takasa da talkaminta mai tsini,
har k'afar tafara kunbura, yace "Allah ya i'sarmun muguwa."
Yawuce su Bahijja ko kallon inda suke beyiba ya k'arasa shiga gida."


Tafiya sukeyi a dai2 sahu, Bilkisu sai kuka takeyi, jakadiya da Safeenat sai hakuri sukebata,
Jakadiya tace meyasa kika zab'arwa kanki wanann rayuwar."?
Karki manta kinada gata kinada k'udi, kuma kinada mulki, gimbiya amma kika zab'arwa kanki rayuwar wulak'anci haka."?

Da sauri ta kalli jakadiya, tayimata nuni da tadaina maganar kar Safeenat dakeyin waya ta fahimci abunda take fad'i."

Bakinta taja tayi shuru, domin bin umurnin gimbiya."

Adai dai wani katafaren gida madai daici, mai a dai2 sahu, ya tsayardasu, Safeenat ce tafara fitowa ta biyasa kud'insa, sanan suka soma d'aukar kayan suka nufi cikin gidansu."

Shigarsu gidan kenan, suka tarar da mahaifiyar Safeenat a Zaune tana yankan yakuwa,
Da fara'arta ta tarbesu , tanufi pallonta dasu."

Anan sukaita gai gaisawa, daga k'arshe Safeenat tafad'awa mahaifiyarta abunda ke faruwa,
Momy mahaifiyar Safeenat ta tausayawa Bilkisu tareda mahaifiyarta jakadiya, a cewarsu."

Momy tabawa Safeenat umurni da akwashi kayansu a kaisu d'akin saukar bak'i, hkan kuwa a kayi.
Angyara masu d'akin had'i da kankab'e masu k'ura sannan aka shigar masu da kayan ciki."

Jakadiya ta mai da kallonta a d'akin, sannan ta kalle Bilkisu tace Allah ya taimakeki, a nan zamuci gaba da rayuwa kenan?

Bilkisu ba ta kula Jakadiya ba."

Jakadiya ta kuma fad'in ranki ya dad'e nasan bakyason yawan tambaya, amma naso naji ko meya had'inki da wanda yakoromu a gidan damuke zaune."? naga alamarsa kamar jinin sarauta ne."?

Jinda Bilkisu tayi jakadiya nafad'in ankorosu a gidansu, yasanya idanunta suka kad'e sukayi jajir,
Sai hawaye take zubarwa."

Wayarta tad'aga takira maimartaba sarki Abdulraham yola, mahaifin Bilkisu kenan,
Abba naganin wayar gimbiya Bilkisu yatashi daga kishin gid'en
dayake ya zauna, cikin farin cikin dajin dad'i ganin kiran gimbiya Bilkisu, yayi saurin d'aukar wayar.
Yace gimbiya Bilkisu ina fatan dai lafiya k'alau kike?

Bilkisu tayi kokarin saita muryanta dake cikin yanayin kuka, tace 'Abba lafiya k'alau nake, sai dai kewarku dakai da Ammi da kuma yaya Abdull,

Abba yace "gimbiya Bilkisu ko kina buk'atar trasfar ne kidawo kusa damu."?

Tayi murmushin dole, tace a'a Abba inajin dad'in karatuna anan.
Munkusan samu hutu Abba zanzo na zauna tare daku."

Yace yawwa gimbiya Allah yashigemaki gaba damak'iyanki, tace "Amin Abbanah, sukayi dariya gaba d'ayansu."

Tace Abba kasan dalilin dayasanya nakiraka kuwa."?
Yace " gimbiya ina zansani sai kinfad'amun."

Tace Abba ina buk'atar katuromun fadawa gobe."

Abba yayi murmushi yace gimbiya dama nafad'a maki zaman makaranta irin wannan dole saida basu tsarunki,
Kika kafe ke saida jakadiya kawai zakitafi,

Meke faruwa dakene."?
Babu wani abu dayasame ki ko."?

Tayi murmushi tace Abba babu komai,
Ina dai buk'atarsu a kusadani, nawani d'an lokaci,
Akwai wani taro daza'ayi a makarantar. Abba ina buk'artasu saboda tsaru,

Abba yayi murmushi yace kinyi tunani maikyau gimbiya Bilkisu."
A cikin fadawan wad'anne kike buk'ata a turumaki."

Tace "yawwa Abba nah, don haka nakesonka,
Abba ina buk'atar katuromun sarkin gida, da sarkin hukunci da sarkin gishiri, Abba katurumun fadawa masu hukunci, mota ashirin, sannan Abba ina buk'atar kud'i a accaunt d'ina masu yawa."

Yace "gimbiya Bilkisu duk abunda kike buk'ata zanyimaki shi, saboda nasan bazaki Zubar da mutuncinki da darajarki ta 'ya mace ba,

Yaushe kike buk'atar aturomaki fadawan."?

Tace "Abba gobe nake buk'atarsu k'arfe goma na safe."

Abba yace "gobe zasuyi sammako, su tafo insha Allah."

Gimbiya Bilkusu tace "nagode Abbanah."

A nan sukayi sallama, da Abban nata,
Ta maida kallonta a gun jakadiya dake zaune kan katifa tana saura renta,
murmushin jin dad'i tayi, tace "banason amfani da mulkina domin na musgunawa mutane, amma yazama dole nakwace 'yancina a wurin Prince Adnan
Jakadiya tace "ranki yadad'e meye tsakaninki da Wanda yayi muna wulak'anci, nan."?
ina ganin kamar jinin sarautane."

Bilkisu ta kalli jakadiya tace "dare yayi jakadiya mukwanta muyi barci, gobe idan Allah yakaimu,
insha Allah zanbaki amsar dukan tambayoyinki dakikayi mun."

Jakadiya tace "to Allah yakaimu goben saida safe."

A hka suka kwanta Bilkisu kuwa barci ya ga gareta,
sai tunani take ta yanda zata d'auki fansar wulak'ancin da prince yayi mata a gaban bainar jama'a."











Ummu safwan😘😘😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR..

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF
LIFE WRITER'S



page1⃣9⃣


A haka barci b'arawo yayi awun gaba da ita."

Shiri takeyi domin tafiya makaranta, domin tunda asuba Abba yakirata a waya yake shaida mata, fadawan da yaturo mata sunkunsan k'arasowa ."

Shiri take a gurguje, saiga Safeena takawo masu breakfast dinsu, kallon agogon hannunta tayi, tace "sis kinsan lokacin cin abincina beyiba sai zuwa anjima zanyi breakfast,
Kifito kawai muk'arasa makaranta karmu makara.

Safeena tace "to bara na d'auko mayafina, ta ajiyewa jakadiya abincin tajuya tafita."

Tafiya sukeyi suna fira ita da safeenat, d'alibai sai nunata sukeyi suna magan ganunsu, bata kulasuba, class tanufa domin d'aukar karatu,

Fitowarsu kenan daga class, Bilkisu tasamu wuri tazauna, tare da safeenat a kan wasu fararen kujerun roma,
Suna diba littatafansu, sai ganin prince tayi a gabanta tareda Abdullah sai wani huci yakeyi,
Kallon tsana yabita dashi yace "ke 'yar matsiyata waye yabaki izinin zama a kan wad'an nan kujerun."?

Nakoreki a garin nan ashe bakitafi bako?
To yau zanyimaki kurar kare,
sai anrakamun ke kibar garin nan saboda na tsaneki banason ganin fuskarki mai kama da aljanu, muguwa kawai,
yakai dibansa a k'afarsa data kumbura yace kinyi nasara kinyimun illah to kisani kafin nasanya ayimaki rakiya kibar garin nan kema sainayi maki illah wadda ko mak'iyinki sai ya tausayamaki."
Abdullah yace " bazaki tashi a kan kujerar anamaki magana ko kallon mutane bakyayi,mai sunfar muna fukai,
ya sanya hannu ya zame kujerar da take zaune saida tafad'i k'asa."

Ranta idan yayi dubu ya b'aci idanunta cike da hawaye ta d'aga kai ta kallesu, samada k'asa bata tankamasu ba, saima sunkuyarda kanta ta kumayi k'asa tana zubar da hawaye."
Safeenat ce kejan hannunta, alamar subar wurin, amma tayi tsaye tak'i d'agawa daga inda take."

Sai jiniya suka jiyo a bayansu, da bushe bushe irin na sarakuna, motocine keta shigowa cikin makarantar sunfi talatin, aikuwa kallo yakoma Kansu kowa mamaki yakeyi, ko bak'i sukayi a makarantar ne."? wasunsu na fad'in wanan sarki wane garine yakawo masu ziyartar bazata,
Prince kuwa naganinsu yabisu da kallon burgewa yanda suke busa da jiniya, yasan ko gaba da gabanta a sarauta."

Gimbiya Bilkisu na ganinsu tayi murmushin jin dad'i, sun iso a dai dai lokacinda take da buk'atarsu.

Prince sai kallon motocin yakeyi yaga sunk'i k'arewa sai shigowa sukeyi gwanin ban sha'awa."

Be ankaraba sai ganinsu yayi a gabansa sun tsaitsaya mamaki yashigayi,

Gimbiya Bilkisu tashi tsaye tayi tasamu wuri ta zauna a kan kujera, ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya mulki da sarautar ya motsa, Safeenat sai kallo tabita dashi tana mamaki,

Fadawan kowanensu yafito a mutarda yake a guje suka runsunawa Bilkisu suna kwasar gaisuwa had'i dayimata kirari, "Allah yataimake, Allah ya tsaremana lafiyarki, hak'ika masarauta tayi rashinki, ranki ya dad'e gamu, sarki ya turomu kina buk'atarmu a kusa dake,

Bilkisu dake kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, ta maida kallonta agun prince da duk yawani rud'e sai mamaki yakeyi,yana tunani a ransa to ita wanan wacece?
shi kuwa Abdullah sai goge zufa yake, domin yafita hanyacinsa gaba d'ya.

Ta maida kallonta a fadawan tayimasu nuni da hannu alamar sutashi,
Da Sauri suka mik'e tsaye, Suna mai jiran umurninta.

Shikuwa Prince da Adnan saboda rud'ewa rik'e yake da hannun Abdullah suna k'okarin Barin wurin,
Dalibai da malamai duk sunzagayesu sai kallon mamaki sukeyiwa Bilkisu."

amma banda shugaban makarantar domin yasan ko ita wacece."

K'okarin barin wurin sukeyi Prince da Abdullah tayiwa fadawa nuni da hannu da su tsayar mata dasu,

Aikuwa a guje suka sha gabansu, suna fad'in gimbiya ke buk'atar mgna daku,
Prince ya kalli kansa yace wacece kuma gimbiya?
Kusan kodawa kuke magana kuwa? Yanuna kansa da hannu."

Duk abunda sukeyi akan idon gimbiya, tayi murmushin mugunta."

Gimbiya Bilkisu tace ina sarki hukunci? Yamike tsaye yace gani ranki ya dad'e."

Sanan ta kuma cewa ina sarkin gishiri."?
yace "gani rankin ya dad'e."

"Tayi masu nunu da Prince da Abdullah dake tsaye suna musu da fadawa,

Tace " kud'aukomun wad'ancan yaran masuyimawa mutane gardama."
Suka runsuna sukace angama ranki ya dad'e

Prince da Abdullah na tsaye saiji sukayi and'aukeso sama, ba'a diresu a ko inaba sai a gaban Bilkisu dake zaune a kan kujera."

sarkin hukunci yace ranki ya dad'e gasu."

tayi nuni da hannu alamar subar mata su a nan, 😊

Ta kallesu sama da k'asa tayi murmushin mugunta,
Tace prince Adnan ina mulkinka yake? Ina sarautarka take? Kana amfanida mulkinka da kuma sarautarka kana taka talakawanka yanda kakeso."
bakasan irin baiwar da Allah yayiwa wani a cikin wad'anda kake wulak'antawa ba,
To gani gabanka kana i'k'irarin zakasanya fadawanka suyimun korar kare a garinka,
Kana i'k'irarin zaka wulak'antani, wulak'anci mai tsanani.
Ba dan komai kakeyin haka ba, sai dan kana yarima d'an sarki,
A yanzun zan nunamaka ko a sarautar, gaba da gabanta,
Zan nunamaka mulkin wata masarautar yafi mulkin masarautarku."

Tace "ina sarkin hukunci yace "gani ranki yadad'e, tanuna Abdullah tace " meye hukuncin mekatsalanda a magana."?
sarkin hukunci yace "bulala hamsin,ne gimbiya

tace sarkin hukunci ayimasa bulala d'ari gamida hukunci mai tsanani."

Yace angama rankin ya dad'e."

Abdullah najin anbaci bulala d'ari saida yasaki fitsari a wando d'alibai sai dariya sukemasa, dama addu'a sukeyi Allah yakawo masu k'arshin zaluncin prince a makaranta,

Abdullah ya kalli prince dake durkushe a gaban Bilkisu, yace "aiga irinta nan saida nafad'amaka ka kyale yarinyar nan amma ka kafe saitabar garin nan, yanzun gashinan kadazamun bala'i."

Ya runsuna a gaban Bilkisu yace ranki ya dad'e kiyi hakuri natuba wlh ko kallonki baza kuma yiba, kice a sansautamun hukuncin nan, wlh bazan sakeba."😊

Bilkisu tayi masa wani kallo sama da k'asa
"Tace wai mekuke jira dashine? Kunbarshi yana damuna da suruto." aikuwa aka tungumi Abdullahi akasanyashi a mota, yana kuwa ya komai, duk yajik'e wandonsa da fitsariπŸ™Š

Ta maida kallonta a kan prince, tace "natsaneka kamar yanda kaima kake i'k'irarin ka tsaneni, bana buk'atar ganin fuskarka,
Tace ina sarkin gishiri? yace "gani ranki ya dad'e tace asanyashi a mota a tafi dashi, a horashi a koyamasa yanda ake daraja d'an adam a duk inda yake."















Ummu safwan😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR....

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT
OF LIFE WRITER'S


Page2⃣0⃣

Fadawane rik'e da prince suna k'okarin sanyashi a mota,
Shikuwa Ya sunkuyar da kansa k'asa, idanunsa sunriked'e sunyi jajir." jiyakeyi kamar k'asa

Please Login or Register in order to submit comment