Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashirin da bakwai kato ne mai fadin kirji kamar kofar gareji
wanene ya taba ka alhaji? Tambayar kenan da ta fara fitowa daga bakinsa?
Wani marar kunya nake so ka gyarawa zama yadan yi shiru na dakiku.
Me kake so ayi masa alhaji! Akashe shi? Arangama ya tambaya
alhaji ya dago kai ya dubi arangama ido da ido sannan yace
Daka samawa kanka dubu talatin kuwa. Sannan yace Eh A KASHE SHI.
Iska ta dau amsa kuwwar muryar alhaji balarabe ta kaita kunnen laila dake can wani dan daki amakale tana saurare.
A KASHE SHI ?
Allah kayi mana tsari da shedanun iyaye laila wacce ke boye abayan labulan dakin tace Duk abinda akayi a kunnenta.
.
BABI NA BIYU 2
Duk da yake ana fama da matsananciyar zufa hakan bai hana mutane jin dadin rayuwarsu ba saboda iskar dake kadawa mai sanyaya zuciya sakamakon canjin yanayin dake shirin faruwa gajimare yayiwa sararin samaniya kawanya amma jama'a sai yawonsu suke domin sun riga sun camfa cewa wai hadarin bana ruwa bane irin gajimaren nan ne na sauyin yanayi daga zafi zuwa damina wannan lullumi mai dauke da sassanyar iska shi yaba wasu yan kananan yara damar warware jirginsu na leda zuwa sararin samaniya
wani yaro dake cikin yaran yana dauke da danko koda yaga jirgin dan uwansa ya riski can kololuwar samaniya sai yace da dan uwansa Audu idan na harbo jirgin ka nawa zaka bani?
Daya yaron wanda zaren jirgin ledar ke hannunsa yace haba ai baka isa ba in kuma ka isa to ka harbo shi zan baka Kwandala.
Daya yaron yayi dariya yace idan ba tsoro ba kawo kwandalar
ka harbo shi mana ai zan baka yaron mai suna audu yace.
To shikenan daya yaron yace sannan saiya tabe dankonsa ya auna jirgin ledar ya saki dankon tsakuwar ta keta sararin samaniya da wani irin kara sannan ta sami jirgin ledar ji kake cuss jirgin ledar ya fara tawangaririya asama sakamakon iskar dake kada shi aduk lokacin da iskar ta kada shi sai ya yiwo kasa da haka har ya kusan zuwa doron kasa. Amma hakan bata sami damar yiwuwa ba koda ya taho sai ya fado akan cunkoson wayoyin tangaraho.
Yeh! Yaron yayi ihu na harbo shi wallahi saika bani kwandalata
yaro mai jirgi ya fusata don ganin an bata masa jirgi kuma ance ya biya kwandala.
An hanaka ka kwata mana in kanada karfi
jin haka keda wuya sai daya yaron ya kama shi da kokawa yana kokarin kwace zaren jirgin dake hannunsa koda suka ja zaren jirgin ledar da karfi sai wasu biyu daga cikin wayoyin tangarahon suka tsinke suka fado kasa.
Wani katon maigadi dake zaune akofar wani katon gida mai dauke da wani dan karamin lambu yataso ya nufo inda yaran suke a fusace saboda ganin barnar da sukayi musu domin ya gane cewa wayoyin tangarahon biyu da suka tsinke na gidan ubangidansa ne.
Kai dan ubanku bakuda hankali ne?
Maigagin yace a fusace kaga yan iskan yara masara jin magana sun janyowa mutane wahala maigadin yayi kan yaran da bulala sukuma suka watse suna dariya suna cewa
Anyi din dan kulu kafi mai abu zafi.
Maigadin baikoma ta kan yaran ba sai ya kama wayoyin tangarahon yana nannadewa.
.
To adan wannan bata lokacin da maigadin yayi ne Arangama dan ta'addar alhaji balarabe ya sami damar sulalewa zuwa cikin lambun.
Akalla ya shafe sama da sa'o'i uku yana makale awani lungu yana jiran wata dama daga maigadin sai gashi ta samu cikin sauki Arangama yayi sauri ya dane kan wata katuwar bishiyar mangwaro mai yawan ganyayyaki da furanni daga kan bishiyar idan ya zuro kafarsa zai iya taba matattakalar benen da alhaji abubakar kebi wajen saukowa.
Maigadin yagama nannade wayar sannan yadawo ya zauna yana jiran alhaji abubakar ya sauko domin ya fada masa barnar da yaran sukayi.
Arangama wanda ke kan bishiya amakale ya kalli maigadin sannan yayi murmushi ya duba agogonsa saiyaga karfe biyar da rabi da yamma akalla zaiyi jiran sa'o'i uku ko hudu kafin Alhaji abubakar ya sauko.
** ** ** **
Mansur na zaune akan daya daga cikin kujerun falon yana karatun wani littafi mai suna
KIBIYAR AJALI
agabansa wani dan karamin tebur ne dauke da kofi da matsatstsen lemon zaki da abarba acikin kofin
kuma akwai tsine na zukar lemon.
Mansur ya ajje littafin dake hannunsa ya dauko kofin lemon yafara zuka. Adaidai lokacin ne wayar tarfon din dake dakin ta dau kara, ya ajje kofin dake hannun sannan ya dauki kan talfon din.
Wane ne? Yace cikin sassanyar murya.
Alhaji abubakar yana nan? Wata siririyar murya ta tambaya cikin Rada
mansur yayi mamakin jin muryar mace ke tambayar mahaifinsa kuma muryar na dan rawa daga can kamar ma a tsorace ake maganar.
Yana wanka wani abune ?
Kace masa yayi sauri ya....... Siririyar muryar ta katse, wayar tangarahon ta zama gawa a hannunsa Mansur ya ajje wayar ahankali cikin zulumi wacece wannan ke son yin magana da baba? Mansur ya tambayi kansa.
.
Kofar daya daga cikin dakunan dake fuskantar falon ta bude Alhaji abubakar ya shigo falon Ganin mansur a tsaye akan wayar tangarahon cikin damuwa shiyasa shi tambayar ko lafiya? Mansur ya kalle shi sannan yace
wata ce wai take son magana dakai.
Alamun mamaki suka bayyana a fuskar alhaji abubakar sannan yace wacece wannan? Bata fadama sunanta ba?
Mansur ya girgiza kai bata fada ba
kaikuma don shirme baka tambayeta ba ko? Kuma ai da saika bari ma nafito ko ka kirani kafin ka ajje wayar.
Ai mun fara magana wayar ta katse abin kawai danaji tafara cewa shine wai kayi sauri......sainaji wayar ta katse.
Alhaji abubakar ya daga kansa sama yayi tunani na dan lokaci sannan yace toh shikenan Allah ya kyauta ina tsammanin wayar ce ta sami matsala sai gobe a samo ma'aikata su gyara mana hanyar. Kuma ko wacece ma ai ta sake kira.
Kararrawar sallama ta dau kara adaidai lokacin da agogon dake bangon dakin ya buga karfe shida daidai.
Shigo alhaji abubakar yace
Kofar dakin ta bude katon maigadin nan yashigo sanye da riga mai yankakken hannu irin ta farauta. Katuwar hular kabar dake kansa tare da kambuna goma sha biyu dake sanye a kwanjinsa na hannun dama su suka sa shi kama da wani kasurgumin mafaurauci gwanin iya kama kura. Maigadin yafadi yayi gaisuwa sannan yace Alhaji wasu yan iskan yarane suka tsinko mana wayar tarhon gidan nan shine naga ya dace na sanar dakai.
Mansur ya kalli alhaji shima alhaji ya kalle shi sannan alhaji abubakar yace da maigadin to shikenan BARAU na gode gobe In Allah yakaimu a gyara.
To Alhaji madalla ni zan koma Barau ya mike daga durkusonsa ya nufi kofa,
alhaji abubakar ya zaro sababbin kudi yan ashirin ashirin na naira dari biyu ya mikawa maigadinsa Barau.
Nagode Alhaji Allah tsareka daga makiya. Dakin yayi shiru babu wanda yace AMIN. Kaddara tariga fata da mansur yasan abinda ke shirin samun mahaifinsa cikin wannan daren to daya amsa addu'ar Barau da Amin.
.
*** *** ***
Yauhe kake son a kashe shi? Aranagama ya tambayi alhaji balarabe.
Yau nake son yabar duniya alhaji balarabe ya amsa masa domin idan har nabari yakara kwana aduniya yagama dani kuma inason na nuna masa cea nafi karfin wulakanci daga yau yasake yiwa wani rashin kunya.
Arangama ya kyalkyale da dariyar mugunta mai kama da aradu jajayen hakoransa suka bayyana afili hayakin taba da goro duk dafe su. Ko da alhaji balarabe ya kalli hakoran arangama sai suka tuna masa da tsohon doki.
Arangama ya dubi alhaji balarabe yace ni zan tafi saina dawo alhaji balarabe yace to mu hadu karfe goma sha biyun dare ka kuma zo min da shaidar ka kashe shi idan naga shaida saina biyaka.
Arangama yayi dariya sannan yace Alhaji baka taba bani aiki na kasa ba ko ka taba?
Alhaji balarabe ya girgiza kai
sannan ya nuf kofa alhaji balarabe yabishi abaya.
Laila dake make abayan labulen bangon dakin ta sulale ta shige dakinta ta kulle yanzu shawara ta rage ga mai shiga rijiya laila tace cikin zuciyarta yazama dile ta jira har alhaji balarabe yafita.
Abinda yasa kuwa shine tana so ta bugawa alhaji abubakar waya domin ta sanar dashi cewa mahaifinta ya aiko a kashe shi. Laila bata sami damar buga waya ba sai bayan da alhaji balarabe fita harkokinsa bai kuma fita ba sai bayan biyar da rabi alokacin ne laila ta buga wayar shikuma Mansur dan alhaji abubakar ya dauka kaddara tariga fata alokacin ne yara suka tsinke wayar.
.
*** *** ***
Inason zanje na dubo jikin na hajiya, alhaji abubakar yace da dansa Mansur.
Koda mansur ya dago kai suka yi ido hudu da mahaifinsa sai yaji duk tsigar jikinsa ta tashi shi kansa mansur baisan menene dalilin hakan ba to amma yasan akwai wani abu dake damun mahaifinsa wanda yaki ya bayyana masa tun lokacin daya sami mahaifin nasa cikin gumi sharkaf yake ta kokarin ya fahimci abinda ke damunsa amma hakan ya gagara abinda yafi damun mansur shine mahaifinsa baya fadar sirrinsa ga kowa shi mutum ne wanda yayi imani da ajje sirrinsa cikin zuciyarsa batareda yafadawa kowa ba koda kuwa Dansa ne.
Ko bakaji abinda nake fada bane?
Alhaji abubakar ya katsewa dansa tunaninsa. Mansur ya juyo suka hada ido da mahaifiME YAFI KUDI ? - 04
.
Ko bakaji abinda nake fada bane?
Alhaji abubakar ya katsewa dansa tunaninsa.
Mansur ya juyo suk hada ido da mahaifinsa alamun tsoro da fargaba suka bayya afuskar mahaifinsa su suka sa kirjin mansur yafara dakan uku uku adacan mansur baisan mahaifinsa da tsoro ba to amma saigashi yau acikin yan sa'o'i kadan duk ya rikice.
Tun lokacin daya sami mahaifinsa yana rubutu akan dan karamin littafin nan ya lura dacewa al'amuransa sun sauya baki daya.
Naji baba mansur ya amsa masa sannan yakara dacewa idan kaje kayi mata sannu kace mata ni sai da safe zanzo.
Alhaji abubakar ya duba agogonsa saiyaga takwas da kwata nan da nan ya juya ya nufi kofar dakin.
Saina dawo yace da mansur,
haryanzu muryarsa na rawa saboda tunanin abinda ya wakana tsakaninda alhaji balarabe awannan ranar.
Har alhaji abubakar ya nufi kofar dakin saiya juyo yace Af na manta da abincin da zan kaiwa hajiya ina ka ajje shine ko ka sakamin acikin mota? Ya tambayi mansur
Mansur wanda zuciyar ke cike da tunane tunane yayi firgigit sannan yace yana dakin dafa abinci dake kasa acan ramatu tabar shi bari na dauko ma.
Har ya mike tsaye sai alhaji yace a'a bari nayi kiran barau ya daukar min yasa min a mota.
Mansur ya kalli mahaifinsa sai tausayinsa yakama shi saboda ganin irin halin daya shiga na tsoro da fargabar wani abu. Wani abu ne ya tayar da hankalin baba?
Mansur ya tambayi kansa.
Alhaji abubakar ya sakeyiwa dansa murmushi sannan yace saina dawo ya nufi kofa ya bude.
Wata iska mai hada da dumi dumi ta bugi fuskarsa saboda zafin da ake fama dashi.
Barau! Alhaji abubakar ya kwallawa maigadinsa kira
Shiru barau bai amsa ba.
Alhaji blarabe ya juyo kadan ya dubi mansur cikin mamaki yace inajin yana kasa bari na karasa na same shi yana gama fadin haka saiya rufe kofar yataka kafar benen ya nufi kasa.
Arangama dan ta'addar alhaji balarabe n rabe akan bishiya yana jiransa yakaraso.
.
Da alhaji abubakar yasan bazai dawo ba gida da rai ba to daya fadawa dansa mansur cewa akwai kudinsa na wani kasuwanci da sukayi a kasar amurka a kalla dalar amurka miliyan guda wanda sukayi da Alhaji balarabe kuma sukayi yarjejeniya a rubuce cewa alhaji balarabe zai ajje kudin idan shekara ta zagayo zasuyi amfani da kudin wajen gina kamfanoni guda uku.
Shin ahaji abubakar yasan cewa takardar da sukayi yarjejeniyar akai suka kuma dauketa suka kaita banki ajiya amatsayin Tsaro. Alhaji balarabe yayi amfani da mukaminsa dakuma dukiyarsa wajen tsoratar da manajan bankin akan cewa yabashi takardar kokuma ya rasa aikinsa, abinda alhaji abubakar kuma bai sani ba shine Alhaji balarabe ya sami takardar yakuma konata ya zuba tokar acikin ruwa. Dayasan kwanakinsa aduniya sunzo karshe to daya fadawa dansa mansur zancen kudinsu wanda ke akwatin karfe mai ruwan gwal. Kudin sune wanda alhaji balarabe ya dan zaro kadan ya baiwa 'yarsa laila naira dubu goma daga ciki taje wajen Party.
Abinda alhaji balarabe baiyi imani dashi ba shine ajiya a banki tunda ya lura da yawan durkushewar bankuna yasa akayi masa wannan maboyar kudi ta musamman.
.
** ** ** **
Arangama na makaleakan bishiyar dake daf da kafar benen saiyaji an kwallawa barau maigadi kira. Nan da nan sai yaji gabansa yafadi daya tuna dacewa idan fa alhaji abubakar na tare da barau to babu damar aikata abinda yake shirin aikatawa. Arangama yayi kasake yana sauraron takun sawun barau ayayinda yake haurowa kan benen da gudu gudu.
To asannan ne dabara ta fadowa arangama alokacin tsakanin barau da bishiyar dake daf da benen baifi takun kafar bene biyu ba.
Arangama yayi kasa kasa kadan hannunsa daya rike da reshen bishiyar kafarsa mai sanye da wani katon takalmi na reto a sannan ne ya hango Sonkon barau na kyalli acikin farin wata ya kara kasa kasa da takalminsa saidaya bari kan barau yazo daidai gindin katon takalminsa sai ya dubi tsakiyar kansa ya doka da katon takalminsa barau yaji wani abu ya daki kansa kamar aradu kwakwalwarsa tafara juyawa. Alokaci guda kuma ya rike tsakiyar kansa da hannayensa yana kokarin ihu amma hakan bata samu yiwuwa ba wani abu mai kamar guduma ya sake dukan kansa. Atake anan ya sume bayansa ajingine ajikin karfen daya kare matattakar benen hannayensa akankame da kansa.
Ahaka alhaji abubakar ya same shi.
Tsigar jikinsa ta tashi tsoro da fargaba da keta faman razanashi tun rana suka taru suka shafe duk wani tunani dake zuciyarsa da farko yayi niyyar yakoma saman benen ya sanar da dansa abinda ke faruwa amma saiyaji kafarsa bazata iya daukarsa ba. Yayi kokarin yayi ihu domin akawo masa taimako to amma idan ya bude bakinsa saiyaji kamar ansa masa takunkumi tsoro da fargaba duk sun kashe lakar jikinsa zazzafar iskar da akaeyi hasken farin wata dakuma tsoro da fargaba su suka hadu suka sa alhaji abubakar cikin wani mummunan hali cikinsa ya murda yaji kamar zaiyi amai. Alokaci guda kuma saiyaji idonsa ya lumshe kamar zai suma nan da nan ya rike karfen benen domin idan bahaka ba saiya fadi
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN.
Abinda alhaji abubakar kenan yafada cikin zuciyarsa.
.
Arangama wanda ke makale akan bishiyar yayi murmushin mugunta wannan matsoracin da wuri zan gama masa aiki yace cikin zuciyarsa sannan ya sake yo kasa kasa kafarsa na reto kamar zata taba bayan alhaji abubakar mummunar fuskarsa sai kyallin gumi take acikin wadataccen farin watan zaka iya kiran fuskarsa wani abin ban tsoro acikin mummunan mafarki, fuskarsa ce irin wadda ke ba yara tsoro takuma hana su barci domin aduk lokacin da suka rufe idonsu zasu dinga mafarki da ita.
Kwakwalwar alhaji abubakar tafara gargadinsa da cewa akwai wani a saman bishiyar nan a makale don haka sai yayi karfin ya daga kansa domin yaga abinda ke faruwa damar da arangama ke jira kenan alhaji abubakar na daga kansa sai dankareren takalmin arangama ya daki tsakiyar gadon bayansa da karfi duka ne irin wanda zai iya sa giwa tayi taga-taga koda kuwa bazata fadi ba.
Alhaji abubakar yaji kamar mota ta doke shi dukan ya daga shi sama sannan ya fado da baki akan matattakar benen. Alokaci guda kuma ya kwalla wata kara mai ban tausayi irin karar da zakaji a bakin naman dajin da aka ritsa da tarko yana neman hanya ya rasa.
Iska ta dauki amsa kuwwar karar alhaji abubakar ta watsa ko ina cikin farfajiyar gidan karar ta doki dodon kunnen Mansur. Alokaci guda kuma yaji kamar an soka masa allura domin ya tabbata muryar mahaifinsa yaji. Yatashi da gudu ya nufi kofar falon sannan batareda yayi wani tunani ba saiyabi matattakalar benen da gudu ya nufi kasa. Baiyi taku goma ba sai yayi tuntube da barau maigadi wanda ke jingine akafar benen zaune akan hanya magashiyan sumamme ya tuntsura sau uku sannan da taimakon ubangiji sai yasa hannunsa ya rike karfen kafar benen sannan ne yaji kashin hannunsa yayi kara. Baya bukatar dubawa domin ya tabbatar karyewa yayi. Wani radadin zafi ya ratsa mansur tun daga tsakiyar kansa har zuwa babban dan yatsansa na kafa.
Alokacin ne kuma saiyaji kamar numfashin mutum acan kasan benen kallo daya ya tabbatar wa da mansur cewa mahaifinsa ne nan da nan ya yunkura ya mike tsaye ya nufi kasan benen duk da cewa kuwa hannunsa nayi masa radadi yadai daure har ya karasa kasan benen.
Alhaji abubakar na kwance jini na zuba ta baki ta hanci babu alamar rayuwa agare shi idanun mansur suka cicciko da kwalla sannan ya sunkuya kasa ya dafa kirjin mahaifinsa da hannunsa mai kyaun sai yaji zuciyarsa na bugawa sama sama alamace mai nuna cewa da wahala ya dada mintina goma aduniya.
.
Arangama na kallon duk abinda yafaru akan mansur koda yaga mansur ya nufi kasan benen wajen mahaifinsa shi kuma sai ya dirgo daga kan bishiyar ya nufi saman benen da gudu. Yana zuwa ya bude falon yashiga bayan yan mintina ya sami abinda yake nema wato Mitar wutar gidan. Yasa hannu ya lalubo wani siririn karfe daga aljihunsa wanda daga bangarensa hakora ne guda biyu daga bangaren kuma a nade yake da roba. Yadubi mitar wutar na yan dakiku sannan ya tura karfen ciki ta hanyar rike robar dake hade da karfan mitar mutar tayi wani tartsatsi sannan wutar lantarkin gidan duk ta mutu. Arangama ya nufo kofar dakin da sauri ya bude ta sannan ya dan saurara baiji motsin komai ba sai sheshshekar kuka akasan benen Mansur ne. Arangama yace cikin zuciyar da boyayyen murmushi sannan sai ya kama kafar benen ya dira.
Arangama ya saba da dira daga saman gini mai tsawo don haka wannan tsirgar dayayi daga kafar benen ba wani sabon lamari bane agare shi gidan yayi duhu kamar kabari a sakamakon lantarkin da arangama ya lalata.
Arangama yabita cikin lambun gidan ya zagaya can bayan gidan sannan yayi tsalle ya kama katanga ya tsirga cikin wani katon filin kwallon kafa dake bayan gidan. Yana tsirga sai yaji mansur ya kwalla kara mai hade da sheshshekar kuka hakan ne yasa shi zaton cewa Alhaji abubakar ya mutu yayi murmushin mugunta daya tuna da dubu talatin din da Alhaji balarabe yayi masa alkawari
Gobe a otal zamu kwana nida yarinyata SHELIN.
Arangama yace cikin zuciyarsa
cikin sauri arangama ya nufi inda ya boye motarsa acan tsallaken titi har zai tsallaka sai yaga wata mota ta nufo wajen aguje sannan ta wuce da gudu koda ya duba lambar saiyaga motar na daya daga cikin motocin ubangidansa Alhaji Balarabe.
Cikin mamaki yabi motar da kallo sannan ne ya tuno ko shakka bayayi ya gane ko motar wacece.
Me Yakawo Laila nan? Arangama ya tambayi kansa cikin mamaki.
*** *** *** ***
Cikin mamaki da rudewa sai laila ta ajje kan talfon din dake hannunta me kuma ya lalata hanyar talfon din nan? Laila ta tambayi kanta gumi ya fara tsatstsafowa a goshinta da ta tuna da cewa yan mintuna kadan suka rage mata ta tserar da ran wannan bawan Allah Alhaji abubakar. Laila taci gaba da tunani bayan yan dakiku saita yanke shawarar ta shiga motarta tayi gudu idan tayi sa'a ta riga arangama zuwa.
Nan da nan ta mike tsaye ta nufi dakin mahaifinta ta bude wata yar karamar akwati mai dauke da cakin dakin kudi dakuma dan littafin da alhaji balarabe ke rubutaME YAFI KUDI ? - 05
.
Ta bude wata yar karamar akwati mai dauke da cakin din kudi dakuma dan littafin da alhaji balarabe ke rubuta lambobin talfon dakuma sunan abokan harkarsa da unguwar da suke.
Laila ta bude littafin tafara bin sunayen daya bayan daya cikin gaggawa tana karantawa har tazo kan sunan Alhaji abubakar wanda agabansa sunansa ne da lambarsa taga an rubuta Unguwar dila lamba S001 batareda bata lokaci ba saita mayar da littafin cikin jakar ta kulle sannan ta dawo falo ta nufi wani dan karamin teburi mai dauke da fulawowin roba akansa ne ta dauki dan makullin motarta sannan tayi waje da sauri.
Cikin abinda bai gaza mintina goma ba sai gata a unguwar dila.
Ta rage gudu adaidai lokacin ne fitilar motarta ta dauko wani katon fili wasan kwallo ta duba barin arewa da filin saita hangi wani katon gida mai dauke da dan karamin lambu duk da yake bata kai kofar gidan ba balle ta duba lambar amma zuciyarta ta fara raya mata cewa wannan ne gidan alhaji abubakar domin duk fadin wajen babu gidan dayakaishi kyawun fasali bayan tayi dan tunani kadan saita karawa motar giya ta danyi gaba da gudu da niyyar ta zagaya kofar gidan a sannan ne to taji kamar an kwalla ihu alokaci guda kuma saitaga gidan yayi duhu baki kirin.
Zuciyarta na harbawa da karfi ta juyo da fuskarta ta dubi sauran gidajen dake kusa da wurin saitaga har yanzu suna dauke da hasken wutar lantarki kirjinta yafara dakan uku-uku domin abinda ta gani ya tabbatar mata da cewa Arangama ya rigata kuma yagama aikinsa koda laila ta gama tunaninta saita taka birki ta tsaya daga inda take tana iya hangen kofar gidan alhaji abubakar.
Laila tayi mamaki dataga babu maigadi amma kuma ga kujerarsa daram a kofar gidan ko kadan laila bata fatan ta yarda da abinda zuciyarta ke raya mata amma babu abinda zatayi abinda zuciyarta ke gaya mata shine. Arangama ya hada harda maigadin ya doke babu mamaki kuma ya kashe su baki daya. Laila nagama wannan tunanin saitaga zamanta anan yana da matukar hadari don haka saitasa giya ta juya da gudu zuciyarta cike da tunanin matakin farko da zata dauka wajen ruguza azzalumar daular mahaifinta alokacin ne ta wuce Arangama wanda ke tsaye abakin filin nan batareda taganshi ba.
*** *** ***
Hannun agogon mai launin gwal dake makale a bangon dakin alhaji balarabe yayi tsaiwar wata akan karfe bakwai na safe dakikar agogon na bugawa ne lokaci guda da bugun zuciyar alhaji balarabe wanda wanda ke faman kai gwauro yakai mari tun kusan kimanin sa'a guda kenan data gabata.
Sanye yake da wando na farin boyel da rigarsa haka nan hula zanna bukar dinkin tangaran tayi daraf a tsakiyar kansa a saba'in. Ahannunsa na dama akwai salula baka mai doguwar eriya da ke barazanar kamo bayan duniya hannunsa na hagu acikin aljihunsa ahaka yake ta zirga zirga akan tattausan kilishin daya mamaye tsakar dakin yana jiran Arangama yakawo masa cikakken labarin abin daya wakana tsakaninsa da alhaji abubakar.
Alhaji balarabe ya dade jiya baiyi barci ba zuciyarsa nata saka masa abinda zaiyi da kudin nan dayake son handamewa na alhaji abubakar saidai kuma komai ya dogara ne akan ko alhaji abubakar ya mutu ko bai mutu ba. Duk da yake alhaji balarabe ya kona takardun yarjejeniyar da sukayi haryanzu hankalinsa bai kwanta ba domin yasan in dai alhaji abubakar yana raye sai yayi ja in ja kafin ya hakura yabar kudin.
Alhaji balarabe yasan dole ne ma ya cinye kudin saidai kuma abinda ya tsana arayuwarsa shine bata lokaci a kotu kafin rigimar ta kwanta yasan sai anyi a kalla kamar shekara ana gumurzu duk kuwa da cewa duk kusan lauyoyin dake garin na lasar zuma daga hannun Alhaji balarabe.
Kararrawar sallama ta dauki ruri haka shi ya tsayar da alhaji balarabe cak daga safa da marwar da yake. Kofar dakin ta bude Arangama ya shigo dakin sanye da bakaken kaya na jeans yana huci kamar maciji. Kallo daya alhaji balarabe yayi masa ya tabbatarwa da kansa babu lafiya.
Me yafaru? Alhaji balarabe ya tambaya.
Arangama ya zazzare idanu sannan yace da alhaji balarabe naje na gama aikata shi kamar yadda kace tun daga saman benen na turo shege kamar gare gare na kuma tabbata babu wanda za'a turo daga kan benen nan batareda ya karya wuya ba. Amma abin mamaki yanzu ina kan hanya sainaji ana fada atakaitattun labarai wai bai mutu ba yana asibiti kuma wai har likitoci suna tsammanin zasu iya ceto ransa.
Arangama ya dan saurara sa'ar da ya lura da cewa alhajin bashi yake sauraro ba.
Tsawon lokaci suna wannan hali can sai alhaji balarabe yayi ajiyar zuciya sannan ya dago kai a fusace ya kalli arangama
A wanne asibitin aka kwantar dashi?
Asibitin nassarawa. Arangama ya amsa lokaci guda kuma yaji gabansa yafadi duk kuwa da irin dakakkiyar zuciyarsa sa'ar daya lura da murmushin muguntar daya bayyana a fuskar alhaji balarabe murmushi ne irin na marasa imani wadansa basu dauki mutum abakin komai ba. Duk dayake Arangama na tsoron alhaji balarabe bai taba barin Alhaji balarabe ya gane ba.
Alhaji balarabe ya kalli Arangama sannan yace dashi. Kada ka damu ka cika aikinka ka kyaleni dashi akwai wanda zansa ya karasa shi dubu hamsin ta isa.
.
Arangama yayi shiru yana tunani zuciyarsa cike da da

Please Login or Register in order to submit comment