Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yabaci zuciyar ta sosu donjin cewa nace masoyina ka gafarce ni idan nayi ba daidai ba. Mansur nasan yanzun ka gama tsanata tsana mai tsanani musamman ma idan akayi la'akari da irin bakin cikin da mahaifina ya jefa ka shine yayi sanadiyar rasuwar naka mahaifin don haka nasan yanzu banida wata kima a idon ka koda daidai da kwayar zarra. Nasan bazaka taba amincewa dani ba mansur domin aduk lokacin daka ganni nasan zaka ga kamar mahaifina ka gani wanda yayi sanadiyar rasuwar mahaifanka gaba daya.
Inama hannun agogo zai koma baya mansur to dana shayar dakai madarar kauna tsantsan irin wacce baka taba sha ba. To amma ina.. Bakin alkalami ya bushe koda ace yanzu nabaka madarar kaunar bakikkirin zaka ganta bazakaga farinta ba koda kuwa ace tafi takarda fari ne.
Nidai laila na godewa Allah daya cika min burina na ambata abinda ke zuciyata
Mansur zuciyata ta dade tana dafewa kan dokin begenka kamar yadda kayar karangiya ke dake tsumma. Hakika mansur naso ka so matuka wanda banajin akwai abinda zai iya kankare shi me yiwa ka tambayi kanka inda nake ahalin yanzu in har kana son sanin hakan yanzun ina cikin tsakiyar kungurmin daji ne inda nake fatan dama wani naman daji ya hallaka ni na huta da zabar rayuwa.
Dakuma radadin begen ka marar amfani.
Nasan abida ta zarce ni azuciyarka nesa ba kusa ba saidai kuma inason ka sani cewa kai kanka masoyina ka zarce kowa azuciyata banajin kuma son da abida keyi ma yayi koda kashi biyu cikin darin nawa idan bata same ka ba mansur. To saidai na kasance bani ba aure abadan abadina.
Ina tausayin kainsa baosa yin abinda bashida amfani nasan shirme ne ma yanzu na sanar dakai amatsayin ka azuciyata. Mahaifina ya rura komai dakomai kamar yadda ruwa ke rusa tubalin yashi. Ina rokon alfarma daya mansur abin begena ko bayan ka auri abida kada ka manta da cewa akwai wata wai ita laila mai kaunar ka a kullum wacce ta kasance ma'abociyiyar rashin sa'a sakamakon........ Nasan na makara. Na makara.!! Alkalami ya bushe. Mansur abin begena sai watarana.
Nice laila mai begen ka.
Ka gafarce ni in fadin hakan laifin ne.
Laifin wani ai baya shafar wani laila. Mansur yace cikin zuciyara.
Dandanon gishirin dayaji abakinsa shiya tabbatar masa da kuka yake. Tausayin laila ya kama shi domin yasan allah ne mai kaddara abinda yaso daman Allah ya rubuta hakan zata faru. Kuma ai laila ma ba abar ki bace saboda tayi iya kokarinta wajen ganin tuggun da aka shirya bai cimma nasara ba. Amma babu yadda aka iya da ikon Allah.
Abu daya mansur ya barwa zuciyarsa ita kadai shne bazai bar kowa agidan yaga wasikar ba. Sannan ne kuma yaji hankalinsa yatashi daya tuna abinda laila tace. Wane daji ne take magana akai? Ya tambayi kansa. Cikin dan kankanin lokaci saiyaji ya matsu ya sake ganin laila badon karayar dake hannunsa ba to dayabi sahun laila. Haka ya kwanta akan gadon daya saba kwanciya dare da rana yana jinyar karyayyen hannunsa.
Ya lumshe idonsa ga mamakinsa sai yaga surar laila lokacin data tsaya akansa farkon haduwarsu da ita inda take cewa (Mansur Allah Ya Sauwake.)
Amin. Yace ahankali
daya tuna abinda tace dashi kamar alokacin tayi masa sannun shin shin wannan na nufin shima yafara kamuwa da sonta ne daga kawai wasika?
** ** **
Arangama ya matso jikin motar sannan ya ciccibi gawar mutumin ya maida ita ciki.
Kada ka mai da min shi ciki mahaukaci. Alhaji balarabe ya buga masa tsawa cikin karaji.
In kana ganin ya dameka to ka fitar dashi da kanka. Arangama yace dashi yana murmushi lokaci guda kuma ya rufe kofar motar. Yasan alhaji bazai iya koda kusantar motar ba ballantana har ya taba gawar.
Arangama yayi murmushi sannan yace haryanzu kana kan bakan naka alhaji? Zo mu koma cikin falon. Kafin alhaji balarabe yace wani abu tuni arangama yakai falon. Ya zabi kujera daya ya nutse sannan ya juyo ya dubi alhaji balarabe wanda ke tsaye ajikin na'urar sanyaya ruwa yana makyarkyata kamar wanda akeyi masa kidan gangi.
Me kake nufi da kawo min gawa har cikin gidana?
Kana nufin nima dan iskane kamar ka? To wallahi......
Arangama ya katse shi ta hanyar daga hannunsa.
Alhaji me yakawo kuma maganar iskanci aciki? Wannan harka ta yanzu ai babu zancen wani iskanci harkar kawai itace a samu kudi kota wace hanya ko?
Ya dubi alhaji ya kyalkyale da dariyaya buga kafa sannan ya juyo yace dashi.
Dazu ka bani mamaki alhaji wallahi bantaba zato zakaci amanata ba da Allah yasa ka tausaya min lokacin dana dawo maka da abinda yafaru to da nima na tausaya ma. To amma sabanin hakan sai naga ko ajikin ka ka manta rayuwata nake sayarwa wajen ganin na biya bukatar ka. Ba sau daya ba ba sau biyu ba nasha jefa kaina cikin laifin kisan kai kuma duk aikin ka ne ba wani ba. In banda kanada lalatattun lauyoyi kamar ka da yanzu ni tawa ta kare to naji ka ceci rayuwata saidai kuma alhaji anyi rashin sa'a ko kusa ban taba godema ba baka kuma birgeni ba. Saboda nasan ka ceci rayuwar tawa ne don biyan bukatarka. Kasan babu wanda zaiyi irin wadannan muggan ayyuka idan bani ba.
Arangama yayi shiru na dan lokaci sannan yaci gaba da cewa Lokaci yayi nima da zanyi nawa arzikin na daina farautar banza. Amma kamar yadda ka bukata zan nemo ma inda dukiyar ka take zan kuma dawo da ita. Saidai wannan karon akwai sauyi acikin lamarin.
Ya dubi alhaji balarabe kallon raini sannan yace idan na dawo da kudin zan dauki kashi hamsin ka dauki hamsin........
.
Na Ubanka ne kudin? Alhaji balarabe ya fada cikin karaji. Arangama ya daga masa hannunsa sama a fuskar alhaji balarabe kamar yadda malami ke yiwa dalibai idan yana son suyi shiru su saurare shi. Me yayi zafi haka hardasu zagi? Naji bana ubana bane kaima kuma bana uban ka bane na talakawa ne da kuma sauran masu hannu da shunin da kake zalunta.
Kaga kenan babu mai shi acikinmu...ME YAFI KUDI ? -16
.
Naji bana ubana bane kaima kuma bana ubanka bane na talakawa ne da kuma sauran masu hannu da shunin da kake zalunta.
Kaga kenan babu mai shi acikinmu.
Kagodewa Allah ma Alhaji kasan yanzu inada ikon da zan iya yin gaba da kudin idan na samo shi babu yadda zakayi ko kana da ja alhaji ? Yace yana murmushi.
Daidai nake da in bugawa yan sanda waya yanzu me kake tsammanin idan suka sami gawa a motarka? Kanajin zasuyi bakin ciki da hakan ? Nasan yan sandan garin nan zasuyi farin ciki su kama ka da gawa sanin kanka ne an dade ana zargin ka amma an rasa hanyar da za'abi don gurfananr dakai agaban kotu.
Arangama ya tsaya yayi yar atishawa gamida murmushin jin dadin lakcar da yake yiwa alhaji balarabe yasan yasame shi a inda yake. Babu kuma yadda zaiyi dashi. Abu daya arangama zaiyi caca akai shine barin gawar mutumin da ya kashe cikin motar. Cacar da zaiyi itace. Shin alhaji balarabe zai iya taba gawar ko kuwa bazai iya ba?
Yakamata ka samu motar da zakafita yanzu tunda Allah ya hore ma yawan motoci. Arangama yace dashi lokaci guda kuma ya mike tsaye.
A'a fita da ita! Alhaji yace cikin karaji. Haba alhaji ace babban mutum kamar ka yana yiwa yaronsa ihu a kunne kayi ahankali karka kashe min dodon kunne.
Sannan yaci gaba da cewa anan zan bar motar da gawar zan maida motar cikin gareji ka dauki wata motar. Amma kada ka damu nan da kwana biyu zanzo ma da kudin ka idan nadawo kayi yadda nake so ma'ana kabani kashi hamsin dina to babu sauran damuwa agareka. Zan dauki motar da gawar alhakina ne na batar da gawar koma a inane. Kada kuma kayi kuskuren fitar da gawar daga gidan nan ka sanni da yan yarana akwai kuma daya akusa da gidan nan nace dashi dayaga ka hau motar ya sanar da yansanda cewa da gawa acikinta sannan kuma sauran kaidasu kayi bayanin abinda ya hadaka da gawa.
.
Duniya ta taru ta rincabewa alhaji balarabe fuskarsa ta tattauye kamanninsa suka canza tsufansa aduniya yafito fili ya zaro kyalle daga aljihunsa ya goge gumin dake zuba kamar ruwa daga fuskarsa. Alokacin ne arangama ya kunna zungureriyar karan tabarsa ya busa hayaki sama sannan ya dubi alhaji ta cikin hayakin tabar.
Kada ka damu kanka da leken taga ba zakaga yaron ba. Sai bayan kwana biyun idan mun hadu.
Acan wani bangare na makwabta agogonsu yabada wani irin sauti karfe goma na safe kenan. Yanzu ne ma ranar ta fara.
.
.
BABI NA GOMA SHA DAYA 11
Gadon yayi kara kukuu! Lokacin da salman yayi mika hasken ranar dake ratsowa ta cikin tagar dakin ya dallare masa ido salman ya shafa akwatin kudin dake daf da kansa sanan yayi kokarin tashi zaune saiyaji kansa ya sara ciwo ga mamakinsa kuma saiyaji yawun bakinsa yayi kauri alamu ne dake nuni da cewa bashida cikakkiyar lafiya.
Cikin faduwar gaba sai salman ya rungume kwatin kudin ya yiwo waje da ita yaji hajijiya na daukarsa sannan jikin ya dauki zafi kau da farko ya dauka zafin yanayin gurin ne amma daga baya sai ya gane cewa zazzabi ne yake neman rufe shi.
Wani mummunan tunani ya darsu azuciyarsa yanzu idan rashin lafiya ta rufeshi anan me zai faru dashi kenan? Babu mamakin ma wani naman daji ya cinye shi. Tunanin hakan shiya kara tsorata shi nan da nan salman ya yanke shawarar yatafi cikin jirgin ya kwanta yasan indai yana cikin jirgin ne da wahala wani naman daji ya rabe shi domin jirgin na iya tsorata shi.
Salman ya nufi jirgin rungume da akwatin kudin kafarsa ta dabaibate kamar wanda aka daurawa takunkumi yayi gaba kadan saiyaji cikinsa ya murda ba'a dade ba sai amai ya barko masa yayita sheka amai daga tsaye. Bayan dan lokaci sai juwa ta dauke shi yafadi da fuska akan koren ciyayin da suke gurin adaidai lokacin ne wasu bareyi suka wice ta jejin da gudu dajin yayi shiru bakajin motsin komai sai kukan namun daji da kuma wakokin tsuntsaye.
Koda yake ta dade tana yawon neman abinda zataci itada ya'yanta amma hakan baisa ta fidda rai ba. Rabon ta da cin naman mutum har ta manta tun jiya da yamma take yawo har tagaji ita da 'yan kanan 'ya'yanta kyawawa saigashi yau kwatsam ta hango abin da ta dade bataji ko labarin wanda ya ganshi ba MUTUM.
Rabo na Minallahi. Tsuntsu daga sama gasashshe. Zakanyar ta lababo daga cikin duhuwar dajin ya'yanta uku daya mace biyu maza suna biye da ita kowannensu na tafiyar takama irinta manyan dawa masu fada aji yauga wata sabuwar halitta a lardinsu.
Salman yayi kokarin tashi koda zaune ne amma abin yaci tura ga kuma akwatin kudin kankame da kirjinsa adaidai lokacin e to yaji zafin zazzabin ya buge shi bugu mai tsanani. Ashe dai LAFIYA TAFI KUDI? Salman yace cikin zuciyarsa ko da yake wahalace tasa shi fadin hakan domin haryanzu akwatin na kankame da kirjinsa.
Dan motsin ganyen dayaji abayansa shiyasa tsigar jikinsa tashi yayi mamakin jin irin yadda tsigar jikinsa ta tashi da farko ya dauka zazzabin dake damunsa ne yakawo hakan amma daga baya sai jikinsa yabace cewa wani Mummunan abu na shirin faruwa ya juya ahankali yayi rigingine akwatin kudin akan kirjinsa a makale kamar ganga sannan ne to sukayi ido hudu da zakanyar wacce ta fito da harshenta sannan ta mayar dashi jajayen idanunta akan gangar jikin salman. Sukayi ido hudu da jan ido ya kalli jan ido. Yawun bakin salman ya kafe yau na gamu da gamona. Yace cikin zuciyarsa tuni har ya fara tsammanin kansa cikin makara anye wajen makabarta dashi.
*** *** ***
Tambayi abinda kike so mana. Bazuka yace da ita lokacin da ya dauke kan motar don kaucewa wani garken kuraye wadanda suka watsi cikin daji da gudu
shin zan iya sanin inda muka nufa?
Kwarai kuwa.. Bazuka yace da laila inda nake tsammanin salman na nan zamu.
Suna tafiya ne acikin wata yar karamar kota (Landrover) irin wacce yashi baya damunta ko kuma yi mata takunkumi gilashinta kuma masu kwari ne. Lokacin da suka iso jos ne yake ajjeta awani dan karamin hotel dake gefen hanya laila ba ta sake ganinsa ba sai bayan hudu na yamma anan ne to ya shaida mata labarin dan dakin nan da yan fasakwauri ke ajje kayansu. Sannan yabata labarin yadda akayi yayi yasan da zaman dakin daga karshe ya baiwa laila minti biyar kawai su gama shirinsu domin yace wai shigar dare yake son suyi. Biyar da minti ashirin suka bar jos.
Mintinan su talatin kenan yanzu da barin jos. Zaki ita tafiyar kasa? Bazuka ya tambayi laila.
Me yakawo tafiyar kasa kuma mu da muke cikin mota? Laila tace dashi tana dan murmushi.
Kina tsammanin salman zai shamatu ne kai tsaye. Ai dole ne mu ajje motar idan ya rage kilomita biyar saimu karasa a kafa kinga ta haka da wuya yaji motsin mu saboda zaiyi zaton ko naman daji ne ya danyi shiru yana tuki da hannu daya. Dayan kuma yana sosa farankau-farankau din kunnuwansa dashi.
Ina tsammanin an da sa'o'i biyu zamu sa don ma hanyar kasace amma da hanyar kwalta ce da baifi tafiyar rabin awa ba.
Duhu yafarayi don haka sai Bazuka ya kunna fitila hasken fitilar ya hasko wasu zakuna guda biyi agefen hanyar laila ma ta gansu ta rike hannun abba bazuka cikin tsoro bazuka ya kyalkyale da dariya saboda ganin laila taji tsoro.
Kada wannan su dame ki ai sun saba ganin motocin mu bari ki gani da mun kusa gurin zakiga sun gudu suna karasawa kuwa sai zakunan suka watse bazuka ya dan rage gudu don bin hanyar ahankali dakyar yake gane hanyar saboda dadewan da akayi ba'a binta tun bayan rushewar gwamnatin Alhaji bade.
Sai duk dogayen ciyaye suka tsiro akan hanyar inda ada sawun tayar motocin yan fasakwaurin ne.
Kamar salman shima bazuka na tafiya yana kwatanta gurin da yadda yasanshi ada. Babu wani cikakken sauyi bazuka ya gare gudu lokacin da wasu garken kerkeci sukayi sama laila ta rufe idonta da tafin hannunta. Ko yanzu na sami abinda zan bai jikokina labari. Tace da bazuka suka tuntsure da dariya.
*** *** ***
FITO. Ya nufi kofar dakin ya budeta arangama na tsaye akofar dakin sanye da bakin wando na farat shat kafarsa cikin bakin takalmi sau ciki. Abokan biyu suka dubi juna sannan suka tafa. FITO da arangama abokan juna ne tun suna yara Yanayin sana'a ne ya rabasu. Shi fito hakal dinsa yake nema aikinsa shine dakon kwalayen taba anan cikinkasuwa. Duk da yake fito yana da masaniyar irin ta'addancin da arangama ke tafkawa hakan bai shafi abotarsu ba. Shi aganinsa duk ba komai bane kowa tasa ta fishshe shi.
Shegen sama! Kura taga biri Fito yace da arangama suka sake tafawa daman ana ganinka arangama?
Gashi kuwa ka ganni fito ya turawa arangama kujera daya tak din dake dakin sannan shi ya zauna bakin gadi
Fito. Arangama ya kira sunansa neman wani taimako nazo ko kuma ince tambaya.
Kamar yaya fa ? Fito ya tambya.
Shine nazo na tambaye ka don Allah daga shekaranjiya zuwa yau ko wata taba katan ashirin da biyar tazo hannun ubangidanku? Fito yayi shiru yana tunani sannan yace kwalayen suna alamar jan fenti ajiki?
Kwarai kuwa arangama yace.
Sannan fito ya dubi arangama yace Alhaji sama'ila ne ya saya. Makwabcin uban gidanmu mu ya aika muka kai masa ita gida jiya da rana.
Kaga wadansuka suka tabar?
Arangama ya tambaya. Fito ya kame ido sannan yace to nidai bana na gani ba amma naga wani suna magana da alhaji sama'ila din kunnensa fala falla kamar funkaso. Suka kyalkyale da dariya sannan ranagma ya mike yace zan tafi Fito.
Sai yaushe kenan?
Saikuma wani abin ya taso Arangama yace har ya juya zai fita sai fito yace dashi ko nayi tambaya? Arangama ya hade fuska sannan ya girgiza kai kafin fito yasake cewa wani abu tuni Arangama yayi waje.
Yanzu kam nasan inda kudin suke arangama yace cikin zuciyarsa. Tun lokacin daya bar gidan alhaji balarabe yafara tunanin ta inda zai fara neman dukiyar alhaji balarabe waccce daga baya arangama ya fahimci ashe kudi ne aciki.
Kwatsam sai wani tunani ya fado masa yasan ko shakka babu laila batasan kudi ne aciki ba kuma yasan laila bazata gudu da kayan taba niki niki ba wannan shi yasashi zuwa gurin fito domin yasan dole ne laila ta sayar da tabar kafin ta tafi. Saikuma gashi cikin sa'a fito yace masa wai su suka kaiwa alhaji..ME YAFI KUDI ? - 17
.
Sai kuma gashi cikin sa'a fito yace masa wai su suka kaiwa alhaji sama'ila gida.
.
Arangama yayi murmushi hakika sa'a a bangarensa take. Yafara tunanin abinda zaiyi da kudin idan ya dauka tuni har yafara tsammaninsa cikin manyan riguna mutanen unguwarsu suna faduwa suna barka dai alhaji. Ya sake murmushi akaro na biyu sannan yace
ME YAFI KUDI ?
** ** ** **
Zakanyan tayi gurnani shikuma salman yayita yan maza ya yunkura zaune akwatin kudin kankame da kirjinsa. Tsoro da fargaba da kuma zafin zazzabi suka taru suka rikita salman zakanyar ta kalli 'ya'yanta sai kowannensu ya zagaya bayan salman ita kuma ta tsaya daga gabansa sukayi masa zobe salman ya gigice saboda ganin irin yadda ake neman yi masa kisan gilla yanaji yana gani.
Sannan ne ya tuno da bindigar dake boye a aljihun wandonsa to amma anan ake yinta ya saki akwatin kudin yake ganin asara. Domin gani yake kamar in ya aje zakanyar zata dauke da haka kuwa ta faru gara ya rasa rayuwarsa gaba daya. ME YAFI KUDI? Yace cikin zuciyarsa gurnanin zakanyar da ya'yanta ya cika ko ina cikin dajin bakakjin komai sai kukansu.
Can kuma wani bangare na dajin yana amsa kuwwar kukan namun dajin.
Kan salman yafara juyawa saboda azabar radadin zazzabi dakuma kukan zakanyar daya daga cikin dan zakanyar ya yiwo kan salman gadan gadan cikin takama zuciyar salman ta buga baisan lokacin daya zaro bindigar dake aljihunsa ba ya auna kan dan zakin hannunsa na rawa yaja kunamar bindigar. Karar bindigar ya cika ko ina cikin dajin sauran 'ya'yan zakanyar suka tsorata suka watsu cikin dajin da gudu.
Amma ga mamakin salman saiyaga uwar zakunan tsaye akan danta daya harba tana sunsuna shi. Ganin haka sai salman ya sake yunkurawa ya daga bindigar da niyyar harbe uwar. Kunamar bindigar tayi wata yar kara kass. Daga nan batayi komai ba harsashi ya kare.
Zakanyar ta yi wani tashi kamar kibiya salman baiga tashin zakanyar ba sai dirarta yaji aruwan cikinsa. Ya kwalla kara mai tsanani. Karfin dukan da zakanyar tayi masa shiyasa ya saki akwatin kudin wacce tayi sama sannan ta fado gefe guda daf da kofar shiga jirgi mai saukar ungulu dake tsaye.
Sau daya tak salman ya shura kafarsa daga nan bai ko kara shurawa ba. An mutu a banza.
.
Yan mintuna kadan da faruwar hakan ya'yan zakanyar suka sake taruwa sukayi yar kwarya kwaryar walima da naman salman. Daya daga cikin ya'yan zakanyar ya dan yakushi akwatin kudin da kafa ya sansuna sannan ya daga kansa sama yayi mika shi agurinsa NAMAN YAFI KUDI. Wata gajeriyar kura ta leko kanta ta cikin surkukin dajin tana jiran zakunan su gama itama ta sami rabonta.
** ** **
Ga gidan can. Bazuka yace da laila tsaya ni anan naje nadawo karki bar nan gurin duk....... Bazuka yayi shiru lokacin da tunanin irin mugayen namun dajin ya fado masa. Zo mutafi. Yace da ita amma kiyi sanda. Laila tabishi gabanta na faduwa da kyar take jan kafarta don gajiya.
Kusan sa'o'insu biyu kenan suna tafiya akasa. Hasken farin wata ne yake basu damar hangen farin ginin saida ya rage tsakaninsu da gidan baifi taku talatin ba sannan suka hango jirgin mai saukar ungulun yana nan. Laila tace cikin doki. Bazuka ya daga mata hannu sannan yace cikin rada biyoni mu fara duba cikin jirgin me yiwuwa ya ajje jakar ciki nasan yanzu barci yake. Basufi taku shida shida ba sai bazuka yayi tuntube da wani abu. Nan da nan ya haska cocila gurin.
Akwatin kudin laila ce in banda dan alamar an kwarzaneta babu wani sauyi ajikinta. Jakar ce laila tace. Ta dafe kirjinta sannan ne to hasken fitilar bazuka ya dauko wani abu daban. Gaba dayansu suka maida hankalinsu gurin. Bawani abu bane kokon kan salman ne. Laila ta sulale kasa sumammiya bazuka yakai hannunsa aljihunsa amma saiya dauke hannun domin kuwa baya bukatar hannun domin kuwa bayar yin amfani da makami.
.
.
BABI NA GOMA SHA BIYU
Bayan da duk wannan rikicin ke faruwa acikin daji acan kuma cikin gari wata na faruwa.
Alhaji balarabe dafe da kirjinsa wanda ke barazanar tsagewa biyu kowanne lokaci daga yanzu don zafi idanunsa sunyi jajur kama garwashin wuta numfashinsa sama sama. Ya nufi kan gado da sauri ya kwanta yana murkususun azaba. Can jimawa kadan sai likitansa Dr. Labaran yafado masa arai.
Yatashi dakyar ya nufi teburin talfon bayan ya danna yan lambobi sai muryar dr. Labaran tace dashi Oh Jesus wane ne kuma ?
Kayi sauri kazo da kayan aikin ku maza maza nine alhaji balarabe sannan ya mayar da kan wayar akan uwar goyonta.
Alhaji balarabe yaci gaba da murkususun azaba sannan kamar daga sama sai tunanin laila ya fado masa arai.
Ina zanga laila? Ya tambayi kansa. Allah sarki laila ni tawa ta kare ke kadai kika rage min aduniyar nan. Kwalla ta kwararo kan manya manyan kumatunsa sannan yaci gaba da cewa cikin rada
Allah ka dawo min da laila na ganta kafin ka dauki raina. Rayuwar duniya dai abar banza ce yanzu gashi akan abin duniya na janyowa kaina cutar ajali na kuma saka ya'ta daya aduniyar nan cikin Masifa.
Allah sarki laila Allah shiryeta shiriya ta gari. Allah karkasa tayi irin irin halina allah ka kare ta daga sharrin mutanen duniya masu sharri.
Wayyo Allah laila kizo na ganki kafin na mutu kada ki bari na mutu banganki ba kinji laila? Kizo kiji da kunnenki duk abinda kikayi min na yafe miki domin bayin kanki bane nine na janyo komi.
.
Alhaji balarabe yaci gaba da murkususu yana kukan azaba kamar wani karamin yaro. Akaro na farko tun da uwarsa ta haife shi sai yau ne yazama abin tausayi. Sannan kuma abin tausayawa ga duk wanda yaji kalaman dake fitowa daga bakinsa.
Dr. Labaran dogo siriri mai kamar langa langa ya ajje wayar sannan ya nufi dakin da yake ajje magunguna don irin wannan kira na gaggawa cikin sauri ya fara zukar ruwan alhaji yana hadawa da garin allurar saida yajika sirinjin uku sannan ya zuba wasu kwayoyin magunguna a aljihunsa yafito da sauri ya shige motarsa sai gidan alhaji balarabe.
Abinda bai sani ba shine acikin ruwan allurar daya hada harda sauran ruwan nan mai guba (Poison) wacce alhaji balarabe yasa shi yayiwa alhaji abubakar garin sauri ya hada da ita cikin allurar da zaiyiwa alhaji balarabe yanzu.
Agogon bangon dakin yana buga karfe goma na dare dr labaran ya isa gidan yana zuwa yayi fakin da motar tasa ya wuce gidan kai tsaye yana shiga falon sai yayi turus arangama na tsaye akan alhaji balarabe wanda keta watsalniya kamar kifi arangama yana daddanne shi.
Kar katsaya anan kana kallona kamar wani danam dawa. Arangama ya bugawa dr labaran tsawa cikin rawar jiki dr labaran ya zaro allura daga aljihunsa sannan arangama ya danne masa alhaji balarabe dr labaran ya kwarara masa ruwan alluran duka uku cikin jikinsa acikinsu harda allurar nan mai guba. Jikin alhaji balarabe yayi lakwas lokaci guda bai sake motsi ba in banda numfashi dake fita sama sama da saika rantse da Allah matacce ne.
Zai warke nan da safiya. Dr. Labaran yace da arangama to anji san inda dare yayi ma uban surutun tsiya. Dr. Labaran ya fice simi simi kamar yadda yashigo.
Arangama ya duba agogonsa sannan yayiwa alhaji duban karshe yanzu kam yasan da wuya alhaji balarabe ya sake tashi in ba safiya ba. To me zai hana ya dauko motar mai gawa aciki inyaso idan yaje gidan alhaji ya kwace kudaden dake cikin kwalayen tabar ya loda ciki yayi nasa guri. Yasan dai koda alhaji balarabe ya wartsake bai isa yayi masa wani abu ba saboda shidai ba zai kuskura ya sanar da hukuma ba domin idan yayi haka to shima yasa kansa ciki.
.
Mintuna biyu ke yanke shawarar sai arangama ya lalube aljihun alhaji balarabe ya dauki dan makullin bambalastar da gawar ke ciki sannan ya fice daga dakin. Akwai wani abu ajikinsa dake bashi cewar shida dawowa gidan har abada. Arangama yatashi motar sannan yayi murmushi daya tuna da irin talakawan da zasuyita zuwa gurinsa fadanci.
Amma da farko

Please Login or Register in order to submit comment