Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani da kuma kishi. Ashe alhaji balarabe yana da wani maiyi masa aiki daya fini? Arangama ya tambayi kansa sannan saiya juyo ya kalli alhaji balarabe yace kada ka bata kudinka abanza ka barni naje har asbitin na karasa shi.
Alhaji balarabe yayi murmushi kamar yasan abinda yake wakana azuciyar arangama saiyace kada ka damu arangama kayi aiki mai kyau kuma zan biyaka kudinka yanzun nan kada kuma ka bari kishi ya dame ka domin mutumin da zansa ya karasa shi LIKITA ne asibitin.
Arangama yaji zuciyarsa ta danyi sanyi sannan lokaci guda kuma ya cika da mamaki tayaya likita zai iya karasa shi?
Alhaji balarabe yayi murmushin mugunta sannan yace wannan wani abune da bai shafeka ba.
.
Allah kayi mana tsari da shedanun iyaye laila wacce ke labe a kofar dakin tace cikin zuciyarta duk abinda ya wakana tsakanin Alhaji balarabe da arangama a kunnenta.
*** *** ***
DR. LABARAN dan fari ne siriri mai kama da langa langa na zaune akana daya daga cikin kujeru ukun dake falonsa. Idan ka kwatanta girman kujerar da yake zaune dakuma girman jikinsa to yan kananan yara uku zasu iya zama hardashi acikin kujera batareda kowannensu ya matsu ba.
Dr. Labaran wanda ke sanye da farar riga da wando irin wadanda likitoci ke sawa ya dubi falon dake dayake ciki sannan ya girgiza kansa cikin takaici saboda abinda yagani a falon. Yayi matukar datti rabon da falon yaga shara yau wata daya kenan haka ne ma yasa har yanar gizo gizo ta fara yiwa silin din dakin kawanya duk inda ka duba yanace a mamaye da bandon babu abinda zai iya kamanta dakin dashi sai dakin tattabaru kilishin dake dakin yayi butu butu da kura duk lokacin da Dr. Ya dan motsa kafarsa sai kura tayi sama kamar hayakin taba. Abin yana matukar batawa Dr. Labaran rai musamman ma daya tuna da cewar duk laifin na matarsa ce MARIYA tagama raina shi dadin dadawa kuma tsoronta yake ji.
Ayan kwanakin nan masifar mariya har tafi da sakamakon satar maganinnikan gwamnati da mijinta sukayi na kimanin kudi naira miliyan daya kuma daga karshe sata ta tashi gundun likitocin aka kore su shikuma Labaran da yake duk asibitin babu wanda yafishi kwarewa wajen fidar mutane sai akayi masa ahuwa amma da yarjejeniyar cewa za'a hutar dashi na wata daya sannan kuma za'aci gaba da rike albashinsa duk karshen wata har sai ya biya abinda ake binsa.
To akan wannan dalili sai ya zamanto duk wasu bukatu na yau da kullum da akeyi agidan Mariya matarsa ce take samo musu bashin kudin da zasu batar. Atunanin mariya in karshen wata yazo labaran zai bata kudin ta mayarwa da wadanda ta ranta domin likitan bai nuna mata cewa sai yagama biyan kudin ba za'a fara biyansa albashi. Don haka sabanin yadda take tunani saigashi yau watan ya kare har sabon watan yakai kwana biyar amma babu kudi babu dalilinsu wannan ranar itace ta uku kullum sai anyi fada tsakanin mariya da mijinta dr. Labaran wadanda suka kasance kiristoci hausawa wanda suke da'awar wai Isa Almasihu dan Allah ne.
Tunanin dr. Labaran ya ktse adaidai lokacin da kofar dakin kwanansu ta bude mariya ta fado dakin kamar an jeho ta daga sama sanye take da doguwar riga ruwan madara kanta babu kallabi hakanan babu kitso wannan shi yasa yayi bucaca kamar ciyawar Rago.
Oh Jesus! Labaran yace cikin zuciyarsa domin yasan bala'i yazo kenan.
Mariya ta nufi shi tana muzurai kamar zata rufe shi da duka. Adaidai lokacin ne labaran ya mike tsaye da niyyar ya gudu sai mariya tayi wuf taci kwalarsa ta shake sannan tace ina zaka munafuki? Saika biya mutane kudinsu zaka fita in kasan bazaka biya ba meyasa ka karba?
Dr. Labaran yaji katuwar matarsa tanayi masa kamshin mutuwa.
To ki sakeni mana yace cikin wata shakakkiyar murya don baya iya numfashi.
Anki a sake ka din. Marita takara matse dan siririn mijinta ajikin bango tana zazzare idanu sannan ta fara wata masifar saina fada a coci idan munje wannan lahadin ince musu kana cin bashi baka biya kuma........ Karar talfon din dake dakin itace ta cece labaran wanda shi har ya fara fita daga hayyacinsa.
Mariya ta saki kwalarsa shikuma ya nufi inda talfon din yake ya dauka.
Wanene ke magana? Labaran ya tambaya numfashinsa sama-sama
alhaji balarabe ne wata murya mai dauke da gadara ta amsa masa.
Labaran ya rike numfashinsa cikin kaduwa domin yasan alhaji balarabe baya kiran mutum a banza labaran yadan juyo kadan ya kalli matarsa wacce ke tsaye tanajin duk abinda yake fada sannan yadawo da hankalinsa kan talfon din dake hannunsa. Oh alhaji balarabe ne in ce dai ko lafiya?
Idan babu lafiyarma kasan ai babu abinda zan yi da dan dagajin likita kamar ka.
Alhaji balarabe yafada a fusace saurara da kyau aiki zakayi min ladanka Naira dubu Hamsin ne kudi hannu. Amma aikin nada hadarin gaske zaka iya ko bazaka iya ba?
.
Mariya wacce ke kusa dashi tanajin duk abinda ake cewa tayi wuf ta warce kan talfon din daga hannun mijinta sannan tace
ALHAJI ZAIYI KOMAI HATSARIN SA
KO YANA SO
KO BAYA SO.ME YAFI KUDI ? - 06
.
Mariya wacce ke kusa dashi tanajin duk abinda ake cewa tayi wuf ta kwace kan talfon daga annun mijinta sannan tace.
Zaiyi alhaji ko menene ko yana so ko baya so!
.
Mintuna ashirin dayin wannan magana saiga dakta labaran agaban alhaji balarabe yana tsuma.
So nake ka karasa kashemin majinyacin da aka kawo muku jiya.
Dubu hamsin zan baka da mota me kagani?
Oh Jesus Dr. Labaran ya fada bakinsa na rawa.
** ** **
Mansur na zaune akan kujerar karfe ya zurawa mahaifinsa idanu baya ko kiftawa alhaji abubakar kwance yake akan gadon asibitin yana numfashi da kyar sama sama ga hannunsa daure da wani farin abu mai kamar zunguru wanda akayi masa dorin karaya dashi. Mansur ya shafe kusan sa'o'i hudu kenan awannan hali yana kallon robar ruwa ta hudu da ake durawa mahaifinsa.
** ** **
Mintinu biyu da barin abida sai laila ta dawo tsakiyar fulawowin nan na gidansu data saba zama ta fara tunanin hanyar da zatabi don ganin ta karya zaluncin da mahaifinta keyi. Adaren jiya ta yanke shawara biyu na farko shine ya zama dole ta sami kudi kafin ta fara hambarar da gwamnatin mahaifinta atunaninta kudin zatayi amfani dasu wajen siyan motoci guda uku da kuma daukar nauyin mutanen da zasu taimaka mata.
To tayaya zata sami kudin? Shine tambayar data kasa gane amsarta abu na biyu kuma da yafi damunta shine Arangama dan ta'addar mahaifinta duk da yake akwai ire irensu arangama da dama da sukeyiwa mahaifinta aiki amma ita arangama yafi bata tsoro ita kuma gashi ba namiji ba ballantana ta dauko hayar wanda yafishi rashin imani yayi maganinsa.
Laila tayi murmushi inda zaka dubi fuskar laila alokacin zaka iya tabbatarwa da kanka cewa barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba. Irin murmushin da alhaji balarabe keyi ne aduk lokacin da yake sjirin shirya aikinsa na mugunta irinsa ne ya bayyana a fuskar laila data tuna da cewa itama fa yanzu yazama dole ta fara yin abubuwa irin na mahaifinta dole ne itama tafara yin yan dabarun mahaifinta keyi wajen samun nasarar yiwa mutane kwarjini da kuma samun karfin iko akansu.
Rana tafara zafi domin alokacin sha daya ne da yan mituna laila ta dauke kujerar ta daga hantsin sannan ta koma gindin wata bishiya yar madaidaiciya mai wadatacciyar inuwa iska ta fara kada fulawowi, furanni ganyayen bishiyoyin alfarmar dake zagaye da laila. Lallausan gashin kanta mai santsi da kyalkyali sai kada yake daga kanta zuwa fuskarta ita kuma tana dawo dashi da hannunta.
Ruwan hodar rigar da take sanye da ita da farin zanen boyel din data daura su suka hadu suka dada fito da kyawun laila musamman ma dayake tana tsakiyar furanni ne.
Laila ta dubi farar takardar zanen dake hannunta sannan ta daga kanta ta dubi korayen ganyayyakin bishiyar da take karkashinta. Zuciyarta cike da tunani wanda zata dauko hayarsa don maganin Arangama. Wani koren ganye ya tsinko daga cikin dubban ganyayyakin bishiyar ya fado akan farar takardar dake hannun laila. Laila ta dubi koren ganyen saitaga yayi matukar dacewa da farar takardar kore da fari suna matukar dacewa aduk lokacin da aka hada su koda kuwa a zane ne. Laila tasake duban koren ganyen saita fara tunanin ta dauko kalolin zanenta ta zana ganyen akan farar takardar domin duk lokacin data kalle shi zaike sata farin ciki kuma zaike tuna mata da.......
Kirjin laila ya fara dukan uku uku alokaci guda kuma sai murmushin nan ya bayyana a fuskarta hakika sai yanzu laila ta gano mai maganin Arangama.
KORE DA FARI. Laila tace cikin zuciyarta koren ganyen daya fado akan farar takardar da laila take rike da ita shiya tuna mata da kalar kayan yayan kawarta dake kaduna bashida wani kaya daya wuce koriyar riga da farin wando.
Shekaru biyu da suka wuce tun laila tana karatu a london ta taba kawowa kawarta mai suna BATULA ziyara ita wannan kawa ta laila tana zaune a kaduna kuma sakandire daya suka gama da laila kwanakin laila goma sha biyu a kaduna alokacin ne to tasan yayan batula mai yawan sa koriyar riga da farin wando ko kuma koren wando da farar riga. Saboda shakuwar da batula sukayi da laila sai ya zamanto har wasu lokutan batula tana baiwa laila labarin irin mugayen halayen yayanta. Maganganun da batula ta fadawa laila akan yayanta sun fara bayyana garai garai azuciyar laila waccce ke zaune a tsakiyar farfajiyar gidansu.
Kinga yayan nan nawa. Batula tacewa laila bashida imani ko kadan kinga har hayarsa ake dauka yana kashe mutane ya kwace dukiyoyinsu. Mu kanmu yan gidan nan tsoronsa mukeyi.
Ke hatta babarmu ma tsoron yi masa magana takeyi tunda babanmu ya mutu shikenan saiyaci gaba da abinda yaga dama babu wanda ya isa ya hanashi.
Kwanan laila biyu a kaduna rannan saiga yayan kawarta yashigo gidan sanye da koren wando da farar riga kato ne mai jajayen idanu da kuma tafka tafkan tafukan hannu kamar muhuci aduk lokacin da ransa ya baci sai fuskarsa ta koma ruwan toka toka. Ga mamakin batula lokacin da yayanta ya shigo saitaga yayiwa Laila murmushi.
Yau baki mukayi a gidan ne? Yayanta yace. Abinda yayi matukar baiwa batula mamaki saboda ita a iya saninta takai wata daya wata magana bata hadasu ba amma sabanin haka saigashi yau yanayiwa kawarta murmushi ita kuma tasan yayanta bai damu da kula yan mata ba saboda in ya kulasu ma tsoronsa sukeyi. Hakika abin yabata mamaki. Tun randa Laila suka hadu da yayanta kullum saiyazo gidan har laila tayi kwanakinta goma sha biyu bai daina zuwa gidan ba wanda ada sai yayi wata daya bai leko ba wannan sune abubuwan da laila ta rinka tunani azuciyarta hakika ta samu mai maganin Arangama domin tanada tabbacin cewa tana kiran yayan kawar nan tata zaizo domin shi dama bashida wani aiki sai ta'addanci. Yayan batula kawar laila kuwa ba wani abu bane batacce kowa yasan shi a kaduna tun daga kan mutanen garin kaduna yan ta'adda kai har yan sanda babu wanda baisanshi ba sunansa SALMAN. Wanda ya sanda sukafi saninsa da kore da fari.
Hakika zuwan salman gari kamar annabo ne.
** ** **
Mashayar dake bayan Daba (Durba Hotel) Kaduna ta dinke da yan ta'adda bata gari banza barayi da kuma masu fasa kwaurin miyagun kwayoyi kai harma da samarin garin yan sharholiya.
Katon daki ne mai dauke da kujerun karfe da tebura kowanne tebur bazaka rasa shi da kwalaban giya ba
hayakin sigari dana wiwi yayiwa sararin samaniyar dakin gajimare hayaniyar mashaya ta cika wajen bakajin komai sai karar kwalaban giya da kuma dariyar mashaya. Duk wannan hayani bata hana kidan diskon dake tasowa daga jikin wata boyayyiyar rediyo ba shigowa dakin babu wanda ke jin wani a dakin. Wani katon teburi wanda ke lullube da karan miski shi yafita zakka a dakin sabanin gutun teburin masu dauke da kwalaban giya shi katin wasa ne na karta akansa. Wannan teburi shine akafi sani a mashayar da suna teburin manyan arna domin anan ne manya manyan yan ta'addar kaduna ke caca duk wanda ya samo kudinsa sai yazo ayi ta caca tarihin mashayar ya nuna cewa ba'a taba tashi lafiya ba daga wannan teburin kullum ta Allah sai anyi fada domin duk wanda aka cinye sai ya tashi rigima.
Idan karta masu kula da wajen sun ga za'ayi musu barna su kama mutum suyi waje dashi.
To wannan daren teburin yana dauke da mutane shida cikakkun yan tabargaza ne na kaduna daya daga cikinsu cikakken barawo ne wanda ya kwarance wajen satar motoci. Na biyun kuma ya gwanance ne wajen fasakwaurin miyagun kwayoyi. Na uku kuma ya kwarance wajen yankan aljihu, na hudun kuma shehun malami ne na 419. Sai kuma na biyar wanda shi gwani ne wajen satar mitar wuta to na shidan shine aka dagawa tuta domin shi ya hada duk abinda sauran keyi DON JIN CIKAKKEN LABARIN WANNAN GWANI NA GWANAYE AMMA GWANIN BANZA ADUBA LITTAFIN
*DUBA KIBIYAR AJALI*
(c) Nazir Adam Salih (Nas)
.
Toh na shidan shine aka dagawa tuta domin shi ya hada duk abinda sauran keyi da kuma wanda ma basu isa suyi ba.
Cikakken dan daukeni na kashe ne kato ne kakkaura mai jajayen idanu manya tafukan hannunsa kamar faranti yana sanye da koren wando da farar riga. Salman ne.
Adaidai wannan lokacin kudin salman saura naira ashirin duk an cinye shi fuskarsa harta fara komawa toka toka.
Ka kada ka mana katin mana. Salman yace a fusace daya daga cikinsu yafara kada katin kartan dake hannunsa hannunsa dake kada kartan yana bin sautin kidan diskon dake tashi adakin. Bayan yagama kadawa sai salman ya dauka ya murza kartar sannan ya raba mintuna daya da fara wasan aka cinye guntun naira ashirin din salman nan take salman yaci kwalar wanda ya cinye shi yayita kwasa masa mari har sau uku sannan yace dashi daga yau ka sake yi min coge. Guntun mutanen suna zaune kamar basu da laka saboda tsoro da sukeji salman kamar uba ne agurinsu.
Salman yafito kofar mashayar hannunsa cikin koren wandonsa yana tafiya yana cin cingam
Salman wata siririyar murya ta kira shi ya juya saiyaga ma'aikaciyar hotel din ce keyi masa magana menene? Salman ya tambaya
wata ce take so tayi magana dakai a talfon cikin mamaki sai salman ya juya yabi yarinyar ciki wani dan karamin daki mai dauke da kwawunan talfon biyu yarinyar ta mika masa kan talfon din sannan ta koma gefe guda jikinta na rawa saboda tsoro.
Wane ne? Salman yace cikin wayar talfon din. Laila wata siririyar murya ta amsa masa ko zaka iya tunani? Nice kawar batula wacce natabayin kwana goma sha biyu agidanku.
Oh! Kece? Salman yayi murmushi
lafiya kike son magana dani?
Lafiya lau laila tace dashi sannan taci gaba dacewa Salman bazanyi ma boye boye ba wani aiki ne irin naku nake so kayi min zan kuma biyaka. Laila ta danyi shiru sannan saitayi amfani da kalmar da mahaifinta yake amfani da ita.
ZAKAYI KO BAZAKAYI BA?
In zakayi ladan ka naira dubu hamsin ne. Salman ya rike numfashinsa tunda yake bai taba rike kudi irin wannan ba. Sannan yace haba kanwata laila zanyi mana indai zaki bani su to an gama.
ME YAFI KUDI. LAILA? Ai babu yaushe kike son ganina?
Matakin farko da laila ta dauka ya cimma nasara.
*** **** ****ME YAFI KUDI ? - 07
.
Matakin farko da laila ta dauko ya cimma nasara.
** ** **
Me zaisa na dami kaina wajen tunanin inda zan sami kudin da zan biya masa kudin jirgi? Ga kudi a daki a dankare. Laila tace cikin zuciyarta sannan saita tashi ta nufi dakin mahaifinta tana zuwa saitayi sa'a lokar dayake ajje kudi tana bude nan da nan ta zaro lokar saitaga kudi dami dami aciki na naira hamsin. Bata bata lokaci ba saita fara diba tana zubawa agaban rigarta sai bayan data dau dami koma sha daya ta lura da bakuwar inuwar data lullube ta tajuya cikin kaduwa Alhaji balarabe ne tsaye akanta yana muzurai.
Me kikeyi haka? Ya tambayeta. Laila ta dago kai ta kalle shi sannan tace dashi
Neman Kudi.
Anan ake neman kudin? Alhaji balarabe yace da ita a fusace laila ta sake kallonsa sannan tace to baba tun dagasu agida me zaisa na sha wahalar nemansu? Kaifa kace a nemi kudi kota wace hanya? Toh gashi ina nema saboda nima inason na banbance tsakanina da talakawa laila tayi murmushi sannan tace da mahaifinta kada ka damu baba kudi sune mutum kamar yadda kullum kakeyimin nasiha akai in kuma kaga nayi kuskure baba to ka kara sanar dani.
BABA ME YAFI KUDI? Kafin ya farga ta fice daga dakin.
.
BABI NA HUDU
Abida ta fito daga dakin sanye da zani da riga na jan siliki kanta lullube da farin gyale kafarta tayi caras acikin takalminta (Famours)
HAJIYA GOGGO babar abida na tsakar gida a zaune lokacin da abida ta fito ta dubi abida sama da kasa sannan tace Ke abida wannan kwalliyar kamar wacce zata gurin fati ina ke ina caba kwalle keda zaki duba mara lafiya. Abida tayi murmushi sannan tace Baba ai gani nayi ya dace tunda cikin jama'a zan shiga aganni dan tsaf tsaf.
Goggo ta danyi murmushi sannan tace to shikenan saikin dawo ki gaida Mansur din kice masa nima gani nan zuwa da yamma yanzu ma abindaysa bazani ba saboda yan gaisuwa da suke ta faman zuwa.
To baba abida tace sannan ta nufi garejin motarta.
Abida goggo ta kwala mata kira.
Karki manta kidawo da wuri ki share masa dakin da zai dawo abida ta cika da mamaki da farin cikin jin cewa mansur nan gidansu zai dawo. Baba daman nan zai dawo? Abida ta tambaya don ta tabbatarwa kanta abinda taji. Nan zai dawo mana ya zauna agidan ne shi kadai tunda Allah ya aiko masa da wannan mataici lokaci guda yaya zaiyi kinga ai nice uwarsa nice ubansa.
Abinda tace gaskiyane baba. Sannan ta juya ta tsake nufar garejin motarta tashiga ta tashe ta sannan tayi ribar ta fita ta daya kofar garejin irin garejin nan ne mai kofa biyi daya zai kaika farfajiyar idansu abida daya kuma kofar zata fitar dakai kofar gidan. Wanda ke zagaye da waya da yan furanni da bishiyoyin turare.
Abida na tafiya ahanya zuciyarta cike da tunanin mansur hakika ta dade tana tausayawa mansur irin alin daya shiga na rashin iyaye lokaci guda kuma dadin dadawa gashi duk dukiyoyin mahaifinsa an rasa inda sukayi domin shi daman mutum ne mai zurfin ciki babu wanda yasan iya yawan dukiyarsa. Sunyi maganganu da dama adaren jiya. Tun lokacin da suka sami labarin rasuwar mahaifin mansur sai goggo tafara tunanin halin da mansur zai kasance aciki domin ta san dukiyar da mahaifinsa yabari da kyar mansur zai sami rabi saboda goggo tasan halin mutanen yau duk wanda dukiyar alhaji abubakar ke hannunsa da wuya ya furta cewa akwai ta, tunda sun san Alhaji abubakar bazai fadawa kowa ba irin dukiyar daya baiwa wasu riko abinda kawai goggo ke tununanin mansur zai samu shine gidan da suke ciki dakuma kamfanin da mahaifinsa ya saya kwanan nan. Sai kuma yan kudade da ya ajje agida dakuma wadanda ke banki. Suma wadannan sai an nemi inda alhaji abubakar ya ajje cheak din bankin sannan za'a karbo su.
.
Wadannan sine tunanin da abida keyi lokacin data kama hanyarta zuwa asibitin nassarawa dubo jikin mansur shin me abida zatace datasan adaidai wannan lokaci datake kokarin kaiwa asibiti gidansu mansur nacan natacin wuta?
Kuma yan kwana kwana sun kasa kashe wutar cheak din kudin bankin kimanin milliyan uku da kuma zunzurutun kudi naira dubi dari biyar da kuma motar alhaji abubakar sun zama toka.
Gidan kuma yazama wajen kwanan beraye da maguna Arangama yagama aikinsa.
** ** **
Mansur na kwance akan gadonsa na asibiri yana ta fama da tunanin rashin iyayensa dakuma yadda rayuwa zata kasance agareshi.
Nagaji da zaman asibitin nan mansur yace acikin zuciyarsa abi biyu suka dami mansur na farko shine halin tsoro da fargaba daya gani a fuskar mahaifinsa kafin ya rasu dakuma yarinyar nan datayi masa talfon wai tana son tayi magana dashi. Hakika mansur ya tabbata akwai wani mummunan al'amari dake boye acikin duhu wanda shi kansa baisan shi ba. Wannan abubuwan biyu su suke sa mansur yafara tunanin anya kuwa mahaifinsa mutuwar Allah da Annabi yayi? Lallai ya zama dole yayi dan bincike bayan yabar asibitin nan don ya gano yarinyar datayi masa talfon wata zuciyar tafara raya masa wasu wasin cewa yarinyar datayi masa talfon ita keda dan makullin duk wannan bakin al'amari dake faruwa agare shi.
Idon mansur ya sake karanta duk abubuwan da suka faru zuciyarsa sai yaga cewa babu mafita an hadawa mahaifinsa makarkashiya ne an kuma hallaka shi da farko dai yarinyar daya kasa fahimtar wacece takuma ki fada masa sunanta suna cikin magana wayar ta tsinke na biyu kuma tsoratar da mahaifinsa yayi haka kawai babu dalili na uku kuma maigadin gidansu lallai duk wanda ya daki maigadinsu akai to shine ya turo mahaifinsa daga kan bene.
Wadannan abubuwa su suka taru suka karfafawa mansur gwiwar cewa mahaifinsa kashe shi akayi. Toh shin wane ne mutumin daya kashe mahaifinsa kuma wacece yarinyar datayiyo masa waya. Wannan itace tambayar da mansur yake ta nanatawa azuciyarsa tun sa'o'i hudu da suka wuce. Ya tabbata yarinyar da tayiyo talfon bata da hannu wajen kisan mahaifinsa saidai kuma yana tsammanin tanada masaniyar wani abu dake boye cikin duhun da ya kasa ganewa.
Tunanin mansur ya katse adaidai lokacin dayaji wani daddadan turare ya daki hancinsa ya dago kai ahankali sai yaji ance SALAMU ALAIKUM sukayi ido hudu. Abida na murmushi shikuma mansur na zaune akan gadon cike da mamakin ganin abida ce tazo duba shi rabonsa da ganin abida ya dade.
Sannu mansur yaya jikin?
Da sauki.
Mansur yace gashima har nafara iya motsi sosai da hannun ya dan juya mata hannu tagani.
'Ah lallae ashe dai yan samarin sun sami sauki suka tuntsure da dariya gaba dayansu sannan abida tace dashi hajiya tace zatazo da yamma.
Ai yanzu za'a sallame ni mansur yace da ita. Abinda ta cika da farin ciki dajin cewa yanzu za'a sallami mansur.
Lokuta da dama abida takanyi mamakin kanta saboda duk lokacin da take tareda mansur saitaji wani farin ciki marar misaltuwa. Bata gajiya da son ganinsa muryarsa tana zama kamar wake ne a kunnenta. Menene yasa hakane? Abinda ta tambayi kanta.
Adaidai lokacin data matso kusa da mansur ta zauna akusa dashi hakika duk da yake tana shakar abinda zuciyarta ke raya mata.
Ahalin yanzu tafara tunanin abinda sata farin ciki aduk lokacin da suke tare da mansur ba wani abune ba sai SO.
Abida tayi sauri ta rufe tafin hannayenta kunya ta lullube ta don jin cewa abinda ke zuciyarta yafito fili bata sani ba.
Mansur dake zaune kusa da abida ya juyo cikin mama dayaji tace SO da karfi.
Menene kuma So bida? Cikin tsoro da fargaba sai abida ta gane cewa ashe abinda ta fada mansur yaji.
Yi hakuri mansur wallahi tunani nake yafito fili.
Mansur ya kalleta yayi murmushi sannan yace Lallai abida ashe ke har tunaninki nafitowa fili haka. To wanne tunanin ne ke damun ki haka da har bazaki iya rike shi azuciyarki ba? Ko tunanin samari kike?
Mansur yace da ita yana murmushi wai ma tunanin samari.
Abida tace kai yanzu idan akace ma tunanin samari nake saika yarda? Mansur ya kalleta sannan yace to ai tunanin naki ne naji harda So aciki
don haka nake zaton ko tunanin samari kikeyi.
Lallai mansur kaima kace wani abu.
Abida tace dashi tanayi masa wani irin kallo da mansur ya lura da kallon da take masa to daya gane amsar tunanin abida. Amma sabanin hakan sai ya sami kansa yana mai tunanin anya kuwa zai iya yin kwana daya batareda yaga abida ba? Dan zaman da sukayi na mintuna kadan sai mansur yaji kamar abida tazamo wani bangare na jikinsa.
Abida ta kurawa mansur ido wanda ya nutse cikin kogin tunani maras dalili. Shi kansa baisan abinda yasa zuciyarsa ke raya masa wadannan abubuwa ba. Kuma bayan haka ma ai abida kanwarsa ce kaga kuwa don yaso...... Wani dan motsi abayansa ya katse masa tunaninsa yakuma katsewa abida damarta na kallon kyakkyawan fuskar saurayin da take mutuwar so ta gani a kullum.
Wani dan siririn likita ne yashigo mai kama da langa langa yana sanye da fararen kaya irin na likitoci
Sannu Mansur Yaya Jikin?
Da sauki mansur ya amsa masa.
Likitan ya matso kusa da mansur ya kama karyayyen hannun ya dan dadduba sannan ya zaro wani littafi yayi yan rubuce rubuce bayan yan mintuna ya mika wa mansur wasu magunguna acikin leda sannan yace dashi. An sallame ka allah

Please Login or Register in order to submit comment