Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rufe idonsa yana tunanin abinda zaice da arangama idan ya dawo domin ya tabbata arangama zai dawo gareshi tare da labarin abinda ya faru idan ya kuskura yadawo min babu wata kwakkwaran hujja saina sa wanda yafishi ya kashe shi. Yace cikin zuciyarsa.
.
Alokaci guda kuma yafara tunanin idan har arangama yadawo gareshi to shi ya dace yasa ya nemo laila da mataimakan ta domin shi yasan su. Abinda yaka tabbatarwa kansa shine shin zai iya sa arangama ya kashe laila kuwa saboda kudinsa? Yafara wasu wasin da laila da kudin wanne yafi wani? Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa.
Daga karshe zuciyarsa tace dashi.
In har laila ta nunawa arangama taurin kai to zai bashi izini kawai ya kasheta ita da mataimakanta. Domin kuwa da yarasa dukiyarsa gara ya rasa laila. Shin to kudi yafi laila ne? Ya tambayi kansa. Ko shakka babu kudi yafi komai harma da laila. In har bance kudi yafi laila ba ai kuwa bazance laila tafi kudi ba.
Tunanin hakan shiyasa shi manta radadin da kirjinsa keyi murmushin yake ya bayyana a lebbansa sannan ya dafe kirjinsa yace
ME YAFI KUDI?.
** ** **
SALMAN ya karkata kan jirgin mai saukar ungulun ya nufi tafkeken dajin nan ihunka banza wanda ke kusa da jos tsakaninsa da jos kilomita chasa'in da uku ne.
Tun sa'adda laila ta sanar dasu dabararta sai shima tasa dabarar ta fado masa nan da nan yakuma dana nasa tarkon na dade ina shuka dusa yace zuciyarsa na dade ina taya masu hannu da shuni cika manya manya aljifansu da naira nida mummunan aiki su kuma da kudin amma ni haryanzu banyi arziki ba. Babu shakka nayi wauta da tun tsawon lokacin da masu hannu da shuni suke daukata hayar ta'addanci wannan dabararsa bata fado min ba.
Salman ya goge gumin dake barkowa daga goshinsa lokacin daya karkata linzamin jirgin ya saita shi abangaren kudu maso yamma duk da yake ya dade rabonsa da tukin jirgi mai saukar ungulu hakan baiyiwa tukin nasa illa ba ahalin yanzu abin yayi matukar burge shi.
Irin yadda yaga yana sarrafa jirgin ya dada burgeshi akaro na biyu. Karfe takwas da rabi na dare agogon dake tsakiyar tarkacen sarrafa jirgin ya nuna. Wata jar na'ura ta haska agaban jirgin salman yayi sauri ya danna wani farin madanni mai shan kwallon kafa jirgin yayi kasa kasa ya kaucewa gajimaren da jirgin ke shirin shiga sannan ya dawo daidai yaci gaba da tafiya a inda yake sannan yayi murmushi hakika haryanzu yana nan bai zube ba rabonsa da tukin jirgin mai saukar ungulu tun sunayiwa Alhaji bade safarar miyagun kwayoyi. Salman ya yakune fuskarsa saboda wautar dayayi abaya lokacin daya tuna da wata rana ana ruwa kamar da bakin kwarya wani mutum ya bugowa alhaji bade waya yace yana son abashi aron daya daga cikin yaransa. A lokacin alhaji bade ya tura salman.
Karfe biyar da rabi na yamma salman ya isa gurin mutumin a legas ne kuma mutumin yace dashi yana son yabi wani dan kasuwa daya fita yanzun nan ya nufi tashar jirgin ruwa dake legas yana son salman ya karbo masa kudin dake tare da mutumin. Salman ya dubeshi sannan har zaiyi magana sai mutumin ya daga masa hannu yace dashi bazaiyi wuyar ganewa ba. Sannan yayi murmushi yace dashi balaraben kasar masar ne yakawo min wasu kaya irin namu na saya na biya shi shine to nake son ka karbo min kudin domin inada bukatarsu.
Salman yace Angama.
Ana cikin ruwan ne yake samun balaraben sanye da rigar ruwa ta leda a bakin tekun. Alokacin ne salman yayita binsa harsaida yaga sun bar idan mutane sannan salman yayi masa barin makauniya ya kwashe kudin yabar balaraben sumamme abakin ruwa.
Abinda ke baiwa salman haushi shine maimakon ya koma yacewa mutumin baiga balaraben ba sai kawai yakaiwa mutumin kudin. Hakika abin yakan baiwa salman haushi aduk lokacin daya tuna da irin wautar dayayi abaya. Adacan dai sun nemarwa masu kudi yanzu kuwa sun gane zasu samarwa kansu kudi ta hannun masu kudin.
Salman ya dubi na'ura mai kwakwalwa dake gaban jirgin sannan yayi nazarin hoton dake dajin da take nuna masa yayi murmushi dajin kore shar acikin farin wata da ya haske wajen. Nan da dan lokaci kankani zai karasa inda yayiwa tsinke mw yiwuwa nan da mintuna biyar. Ya danna mulmulalliyar na'urar nan. Sannan jirgin ya fara yiwowa kasa kasa salman ya taba akwatin kudin daya kwace daga hannun laila sannan yayi murmushi.
Mun daina wahalar banza lokaci yayi daya kamata muma muyi kudi kota halin kaka.
Hasken farin watan ya huda gilashin jirgin ya kuma haskake ko ina acikin jirgin salman ya shafi koren wandonsa sannan ya gyara kwalar farar rigarsa ya sake murmushin dadi daya tuna abinda zaiyi da kudin daya sata sannan yace cikin Nishadi ME YAFI KUDI ? ** ** **
.
Kararrawar agogon dake jikin bangon dakin ita ta tashi alhaji balarabe daga nannauyen barcin daya tsinci kansa ciki tunda yake bai taba barci mai nauyi da kuma mugayen mafarke mafarke kamar wannan ba.
.
Ya tashi zaune akan gadon sannan ya dafe kansa wanda kamar zai cire saboda ciwo zuciyarsa kamar zata tsaga kirjinsa ta fito don zafi ya tashi tsaye ya nufi katon madubin dake jingine ajikin bangon dakin ya dubi surarsa ajiki.
Abinda yagani yayi matukar girgiza shi yakuma bashi tsoro. Bai yarda surarsa yagani ba sai bayan daya daga hannu sannan yaga abin dake jikin madubin ya daga hannu sa'illin ya yarda shine. Kaico yace cikin zuciyarsa.
Yanzu alhaji balarabe ne ya zama haka biloniya uban miloniya?
Kumatunsa duk sun zube sun zama kamar hujajjiyar tumfafiya idanunsa sun fada ciki kamar idon yartsana alokacin ne kuma mummunan mafarkin da yayi jiya yafado masa.
Acikin mafarkin ne yaganshi wai yana bin laila da gudu abakin wani ruwa ita kuma tana gudu hannunta rike da akwatin kudin da take dauke. Lokacin daya kusan kamata sai wasu samari guda biyu suka fado daga sama suka dauke laila sukayi cikin ruwan da ita. Shikuma yaci gaba da binsu har sai da yajishi tsindum yafada cikin ruwa sannan ne ya hango laila itada samarin nan akan ruwa a tsaye.
Ya gane daya saurayin amatsayin arangama amma dayan baigane shi ba.
Abin kawai da zai iya cewa shine daya saurayin baigane din ba yana sanye da koren wando da farar riga.
Alokacin ne wasu siraran hannaye suka fito daga cikin ruwan suka kama alhaji balarabe yana ihu amma babu wanda yazo cetonsa. Alokacin daya nutse akasan ruwan saiyaga kayan jikinsa sun zama farare tas. Kuma agabansa a tsaye labaran likita ne yana murmushi ahannunsa na hagu yana rike da alhaji abubakar na damar kuma ya mikawa alhaji balarabe. Daga karshe ba tareda son alhaji ba sai yayi wani abu mai karfi ya tura hannunsa cikin hannun labaran likita alhaji abubakar yana murmushi. Alokacin ne to alhaji balarabe ya farka firgigit. A sakamakon kararrawar agogon bangon dakin.
Alhaji balarabe yayi ajiyar zuciya ya sake duban kansa ajikin madubin dakin sannan ya tashi ya nufi bandaki. Bayan ya watsa ruwa saiya fito ya wuce dakinsa kai tsaye. Yana zuwa saiya duba ma'ajiyar kayansa ya zabo jamfa da wando marasa nauyi na danyen boyel bayan yagama shirinsa tsaf sai ya dauki dan makullin motarsa ya nufi cikin babban falon gidan.
Lokacin ne yo yayi turus ya tsaya kamar wanda aka nausa a zaune akan daya daga cikin kujerun alfarmar shakatawar dake dakin idonsa wuri wuri yana sakatar kunnensa da gashin kaza kafarsa ta dama akan ta hagun. Atangama ne.
** ** **
Dakin yayi shiru na dan lokaci sannan muryar alhaji balarabe ta ratsa shirun da cewa daga ina kake?
Daga inda ka aikeni. Arangama yabashi amsa kai tsaye.
Da wacce kazo? Alhaji balarabe yasake tambaya.
Da abinda baka taba tunanin zaifaru ba.
Arangama ya sake bashi amsa kai tsaye akaro na biyu.
Haushi ya kama alhaji balarabe lokaci daya lura da irin amsar rainin da arangama ke bashi. Ni kake fadawa magana haka kai tsaye arangama? Alhaji balarabe yace dashi cikin fushi.
Sannan ua daga dan yatsansa na hadu ya nuna goshin arangama yace in kana tsammanin dukiyata dakayi sakaci ta bata tasha ruwa to kana bukatar a saka ka a turu.
Arangama ya dubi alhaji balarabe cikin mamaki domin bai zaci alhaji balarabe zai fada masa irin wannan maganar ba.
Kuma abinda yafi bashi mamaki shine yadda akayi alhaji balarabe yasan dukiyarsa ta bata. Ya dubi alhaji balarabe cikin mamaki sannan yace yaya akayi kasani?
Alhaji balarabe yayi murmushin yake sannan yace a fusace kaidai kaji kunya wallahi ashe duk yadda na dauke ka baka kai nan ba.
Yanzu awai wai duk ikirarin nan naka da taurin kanka dakuma dabaci irin naka ace wai Laila ce ta samo mai tausasa kanka. Sakaran banza mai kurin wofi.
Alhaji balarabe yayi shiru yamada numfashinsa sannan yaci gaba da cewa Arangama banga amfanin zamanka agurin nan ba in kana son mu daidai dakai to ka tashi tsam daga nan ka shiga duniya ko zaka samo min labarin inda laila take. Idan ka samota to zaka nuna min kai namiji ne amma ni yanzu dan daudu na dauke ka. Kuma kada kayi tsammanin zaka sake samun kwabo awajena bani bakai daga yau har sai randa ka dawo min da dukiyata. Kada kuma ka saurarawa kowa.
Alhaji balarabe yayi shiru idanunsa akan fuskar arangama baya ko kiftawa. Arangama ne yafara kawar da fuskarsa
kada ka saurarawa kowa koda kuwa Laila ce. In kuma zata kawo matsala...... Ka kasheta domin dukiya tafi min fiye da yar banza kamar ta. Ka tabbata ka fice daga gidan nan kafin nadawo.
Alhaji balarabe yaci gaba da cewa nakuma baka sati guda ko kazo min da labarin kokuma ka gwammace ba'a haife ka ba ka sanni ka kuma san halina da kuma karfina agarin nan karfin nairata ya isa yasa yan sanda su saye min kai har abada sanin kanka ne badon ana tsorona ba da yanzu an cafke ka. Shin ko ka manta mutumin nan daka banke da mota lauyoyina suka ceto ka da kyar?
Da yanzu bakai. Tafi ka fice sakaran banzaME YAFI KUDI ? - 14
.
Tashi ka fice sakaran banza!
Kafin arangama ya motsa tuni alhaji balarabe ya fice daga dakin yana kada dan makullin banbalastar sa hularsa dinkin damanga agaban goshinsa karin hular shi ya mai da ita kamar mangalar jaki,
.
BABI NA TARA 9
Ku shigo mana ku zauna
muryar alhaji sama'ila ce ta katse shirun dake dakin laila ta nufi kujerar dake bangaren yamma na dakin ta zauna shikuma bazuka ya nufi inda mansur ke zaune ya zauna gamida ajiyar zuciya bayan duk sun zauna sai alhaji sama'ila ya dubi laila yace da ita Laila meke faruwa ne? Na fahimci akwai wasu abubuwan mamaki dake kulle acikin akwatin karfe wanda kuma nake tsammanin dan makullin budeta tana wajenki.
Yayi shiru na dan lokaci yana kada yan makullan motar dake hannunsa. Muna son musan abinda ke cikin akwatin mamakin da dan makullanta ke hannunki.
Laila ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na sartatowa kan kumatunta sannan ta dago kai ta dube su tace
labarin nada tsayi. Babu mamaki kuma in na fada muku ma bazaku yarda ba amma tunda baba ya bukaci hakan to zan sanar daku koda kuwa bazaku yarda ba.
.
Sannan ne tafara basu labarin tun daga inda mahaifinta ya buga mata waya har zuwa inda akayi taggum kashe mahaifin mansur da kuma niyyar data kudura na yanzu. Lokacin data kawo karshe duk dakin kuka ke don tausayi. Alhaji sama'ila ne da bazuka basuyi kuka ba mansur na kukan takaicin tuggun da aka hadawa mahaifinsa sukuma su abida da hajiya goggo na kukan tausayin mansur dakuma Laila.
Alhaji sama'ila yayi shiru zuciyarsa cike da tunanin abinda yakamata yayi na farko dai yanzu ya tabbata laila bata san kudi ta sayar masa ba a maimakon taba shikuma yana tsoron alhaji balarabe ada kadan kadan to amma irin jin gaskiyar al'amarin alhaji abubakar sai abin ya tsorata shi domin yasan idan ya kuskura alhaji balarabe yasan shine ya sai kayan daga hannun laila to sunansa matacce ita kanta laila na cikin hadari domin a irin yadda yake jin rashin imanin alhaji balarabe yana iya kashe koda uwarsa ne akan Kudi.
Al'amura suka taru suka cushewa alhaji sama'ila na farko dai yasan laila mafaka take nema agidansu itada mataimakinta bazuka. Na biyu kuma shine dolene ya tsuke bakinsa akan maganar kwalayen tbar nan dake cike da tsagwaron kudi bazai fadawa laila ba har sai ya yanke cikakkiyar shawara da farko dai yayi niyyar ya mika komai ahannun yan sanda to amma sai yayi tunanin kwana kwanar kasar nan in ya sake ya tura kudin hannun yan sanda to suda kudin har abada yasan dai daman kudin nan tabbas fasakwaurinsu akayi domin yasha jin labarin irin haka idan ya mika maganar ga yansada to alhaji balarabe tasa ta kare domin shekaru kusan goma sha tara da suka wuce hukumomin jihar nan suka baza ragarsu ko Allah zaisa yayi wani motsin ba daidai ba ya fada amma har yau sun kasa cimma nasara.
Alhaji balarabe uasan yadda yake aikata ta'addacinsa don haka idan hukuma ta sami wannan damar to alhaji balarabe yagama. Saidai shi alhaji sama'ila ba damuwa da halin da alhaji balarabe zai shiga yayi ba. Shi laila yake tausayi musamman ma dayayi la'akari da cewa bata dogara da komai ba sai Allah. Alhaji balarabe da kuma dukiyarsa don haka idan ya mika dukiyar ga yansa to kamar ya mika dukiyar laila ne domin ita kadaice. Mai gadon dukiyar.
Alhaji sama'ila ya dubi laila da mansur yace kiyi hakuri wannan abun Allah ne ya aiko don haka babu yadda aka iya. Ku dauki wannan abu amatsayin jarraba. Sannan ya karkato hankalinsa zuwa fuskar laila yace da ita hakika laila kin yi kuskure ko kuma in kinyi yarinta saboda tsammanin da kikayi na zaki iya tankwara mahaifinki ya daina abinda yake. Kinsan fa ko naman mutum yakeci danye in kika kuskura kika saba masa sai ubangiji yabi masa hakki amatsayinsa na mahaifinki. Hakika kinyi kuskure domin salwantar da dukiyarsa kike shirin yi bashi zaisa ya shiryu izuwa hanya tagari ba. Allah ne mai shiryawa laila ba mutum ba.
Don haka tsakaninki dashi sai addu'a duk dayake kuwa an riga an makara ta riga ta afku babu wanda ya isa ya maida hannun agogo baya. Domin Allah ne yasan irin bacin ran da mahaifinki ke ciki. Sannan yayi shiru na dan lokaci.
Ina son ku bani lokaci na danyi tunani daga yanzu zuwa safe in yaso gobe sai mu kara tattaunawa muga yadda zamu bullowa matsalar. Ya juya ya dubi mansur yace dashi kai saiku kwana tareda bazuka ke kuma abida ki kwana tareda laila sannan ya mike tsaye yace dasu gashi har anyi sallar magariba isha ma ta wuce bamuyi ko daya ba ku tashikuje kuyi sallah yace dasu.
.
Suka mike gaba dayansu harda hajiya goggo sannan ne alhaji sama'ila ya juya yace da mansur ku tafi babban daki ku kwana domin ina tsammanin yayi muku kadan. Nan da nan mansur yagane abinda alhaji sama'ila ke nufi baya son su laila da bazuka su gane ga kwalayen tabar da suka fashe ne amaimakon taba kuma suke tsammani amma dalar amurka.
Abinda duk basu sani ba shi adaidai lokacin da suke shirin yin ramakon sallar magariba da isha Shi kuma salman nacan tsakiyar dajin ihunka banza yana kokarin sauka da jirgin mai saukar ungulu dayayiwa Laila fashi.** ** **
.
Bayan yayi kamar mintuna hudu yana tafiya ahankali a saman tafkeken dajin wanda yake cike da manyan bishiyoyi gamida mugayen namun daji masu cin mutane danye ba gashi. Sai yafara hango kyallin saman kwanon dan karamin farin dakin dake tsakiyar dajin ishashshen hasken farin wata ya wadati ko ina. Salman yayi murmushi lokacin daya hango dakin haryanzu dai yana nan kamar yadda yake babu wani sauyi inka dauke yan kananan ciyayi da suka tsutsturo ajikin bangon dakin babu wani kwakkwaran sauyi. Sannan ne salman yafara tunanin lokutan da suka shude ada can wani zamani. Dakin shine ya zama kamar tasha ko kuma wajen cin zango na kwararrun yan fasakwaurin miyagun kwayoyi dakuma duk wani abu dake yiwa dokar kasa karan tsaye acikinsu harda fasakwaurin taba sigari dakuma jabun dalar amurka wannan itace matattarar duk wani cikakken dan fasakwaurin alhaji bade. Wanda shine uban gidan salman awancan zamani. Anan ne kuma suka sauke kayan da suka yiyo fassakwaurinsu daga kasashen ketare shikuma alhaji bade saiya tura kanan motoci su dauki duk abinda aka sauke yashiga dashi cikin garin. Inda za'a batar dashi ta hanyar bada cin hanci ga wasu gurbatattun mahaukatan na kasa.
Ba karamar dabara salman yayi ba da ya taho gurin domin salman yana da labarin tuni an daina amfani da gurin tun shekaru biyu da suka wuce. Wato alokacin shekarunsa uku kenan da yin murabus. Daina amfani kuma da akayi da wajen ya samo asali ne da bacewar rana inda hukuma ta cafke alhaji bade aka kumayi masa daurin rai da rai agidan maza.
Salman yayi kasa kasa da jirgin tuni kasan jirgin yafara sharar ganyayyakin bishiyar dake wajen. Bayan yan dakika jirgin ya sauka adab da ginin dakin Jif!
.
Yan mituna kadan da saukar sa sai salman ya rungumo akwatin kudin ya nufi dakin bayan yayi yar kokawa da dan makullin dakin na dan lokaci sai yayi nasarar budewa gamida ajiyar zuciya sannan ya dallara hasken cocila cikin tangamemen dakin wanda bazaka yi tsammanin zaikai girman haka ba daga waje. Har yanzu yana nan kamar yadda yake gidajen kwana uku ne adakin haryanzu ba'a dauke su ba bakuma ranar dauke su domin ko yan sanda basusan da maboyar ba.
Saman ya jefa jakar kan gado kura ta tashi bai damu da kurar ba sai kawai yabi jakar kan gadon ya kwanta akansa yayi matashin kai da akwatin kudin zuciyarsa cike da tunanin abinda zaiyi da kudin. Da kuma inda zai nufa bayan kwana uku. Iya kwanakin daya yanke shawara kenan zaiyi azuciyarsa. Salman ya sake mimmikewa zuciyarsa a bushe baya ko tunanin wani naman daji yashigo saboda tabbacin bindigar dake kugunsa yasan kuma babu wanda yasan da maboyar.
.
Tabbas yayi kuskure domin kuwa abinda bai sani ba shine bayan yayi murabus daga fasakwaurin an sami magajinsa agurin. Wanda kuwa alhaji bade ya dauka amadadin salman alokacin shine BAZUKA.
Don haka ne babu wanda yasan wani tsakaninsuda salman. Sai gashi yanzu kaddara ya hada su koda ace babu wanda yasan da maboyar to Bazuka ya sani. Salman bai san da hakan ba.
** ** **
Laila tayi firgigit ta tashine zaune akan gadon gabanta na fdaduwa domin azatonta gari ya waye. Amma sabanin hakan saitaji garin shiru. Abida na daya gadon a kwance sanye da doguwar shima mai shara shara ta dubi abida saitaji tausayinta yakamata hakika ta dade tana begen mansur tun daga ranar datayi ido hudu dashi. To amma kaddara fa?
Tayi shiru tana tunanin irin katangar karfen da kaddara ta gindaya tsakaninda da mansur ta sake duban abida da kyau ko shakka babu abida ma kyakkyawa ce kuma abin bakin ciki shine duk da yake laila tasan ta dan dara abida d kyan kira to abida kuma tafita kusa da mansur.
Domin kullum suna tare dole ne kuma tayi nasarar janyo hankalinsa gareta kuma ko banza dai ita abida batada wani tabon da zaisa mansur yaki ta. To amma ita fa?
Laila ta juya maganar cikin zuciyarta mahaifinta ne yayi sanadiyyar hallaka mahaifinsa hawaye suka kwaranyo zuwa kumatunta alokaci guda kuma ta janyo jakarta gefe guda ta budeta sannan ta dauko biro da takarda ta zauna cikin sauri ta rubutawa mansur wasika sannan ta sauya kayan dake jikinta. Ta zuge jakar cikin sanda ta rataya jakar abayanta wasika data rubuta a rike a hannun ta ta bude kofar dakin ahankali sannan ta juyo ta dubi abida ganin karshe sannan ta juya ta fice daga dakin zuwa falon shakatawar dake tsakiyar gidan.
Ta wuce kai tsaye zuwa dakin su bazuka tun kafin ta karasa kofar dakin ta bude bazuka na tsaye abakin kofar jakar ledarsa rataye abayansa. Ayadda taga yanayin fuskarsa tana tsammanin ko runtsawa baiyi ba. Yayi mata alama da hannu yana nufin ta shirya? Ta gyada kai. Kafin bazuka ya rufe kofar dakin sai laila ta jefa wasikar data rubutawa mansur tsakar dakin sannan bazuka ya karasa rufe kofar ahankali kamar mai rufawa a bayan kwai.
Karfe hudu saura minti goma sha shida laila suka kama hanyarsu ta zuwa kauyen da bazuka ya shawarce su dasu biya acan...ME YAFI KUDI ? - 15
.
Laila suka kama hanyar su ta zuwa kauyen da bazuka ya shawarcesu dasu buya acan laila ta tsere daga gidan alhaji sama'ila ne badon komai ba sai don tunanin alkawarin da bazuka yayi mata na cewa zai dawo mata da dukiyar mahaifinta.
Rashin sani datasan abin dake gidan alhaji sama'ila da bata batawa kanta lokaci ba wajen nemo dan kalilan din kudin da zasu iya jefata ga halaka.
.
Bazuka ya sosa farankau farankau din kunnuwansa masu kama da alamar tambaya (?) sannan ya karawa motar wuta.
Ina tsammanin nasan inda salman ya nufa yace da laila. Adaidai lokacin ne wani dan sanda yafara daga musu hannu amma bazuka baiko dube shi ba balle ya tsaya.
** ** **
Ya nuf kofar a fusace yana kukkumbura kamar wani biddidigi yasan dole ne arangama yayi abinda ya umarce shi dashi. Saboda ya same shi a inda yake so arangama bashida zabi dole ne yayi abinda nasa shi alhaji balarabe yace cikin zuciyarsa.
Ya bude kofar motar ahankali sannan yayi kikam kamar wanda aka soka da kibiya ya kasa karasa bude motar shikuma bai maida ita ya rufe ba. A zaune akujerar banbalastar mutum ne kansa akwance agaban kirjinsa sanye da bakaken kaya alhaji balarabe ya bude baki zai bugawa mutumin tsawa saiyaga ya sulale yafado waje kafarsa aciki knsa awaje. Alhaji balarabe yayi tsalle gefe guda cikin kaduwa sannan yaji wani dan motsi abayansa.
ARANGAMA ne.
Haryanzu kana kan bakanka nasa yan sanda su saye ni? Arangama yace dashi yana murmushi.
.
BABI NA GOMA 10
Abida tayi mika sannan ta mutsutstsuke idanunta ta duba bataga laila ba saitayi tsammanin ko bandaki ta shiga. Amma ga mamakinta saitaga jakar laila bata gurin data ajiye ta ajiya da daddare. Nan da nan abida ta diro daga kan gadon ta nufi dakin hajiya kanta ko dankwali babu. Ta kwankwasa kofar hajiya ta fito tana jan tasbaha ta lillebe jikinta fa farin gyale irin na larabawa. Kallo daya tayiwa fuskar abida ta tabbatarwa kanta wani mummunan abun yafaru.
Lafiya? Hajiya goggo ta tambaya.
Laila tace ban.... Banganta ba. Abida tace cikin In-Ina
kamar yaya baki ganta ba? Ba daki daya kuka kwanta ba? Hajiya ta tambaya mw yiwuwa ko bandaki tashiga
aina duba jakarta ba ban......
Motsin mansur dake bayansu shiya katse maganar abida.
Me yafaru mansur? Goggo ta tambaya akaro na biyu
ina Laila?
Muma ita muke nema. Hajiya goggo tace dashi.
Mansur ya sunkuyar da kansa kasa sannan ya dago yace da wanda sukazo tare ma jiya baya nan na farka banganshi ba kuma na duba bandaki babu kowa babu alamarsa. Jakar kayansa ma bata nan. Sannan ya danyi shiru na dan lokaci.
Ina tsammanin sun gudu yace a sanyaye.
Mintuna biyar da faruwar hakan saiga alhaji sama'ila ya hada taron gaggawa a babban dakin shakatawar gidan.
Menene dalilin gudun? Yace ahankali kamar wanda ke tambayar kansa.
Hajiya goggo ta dube shi tace muma abinda muka gasa ganewa kenan ko kuwa tsoron kada mahaifinta yayi zaton tana nan ne shiyasa ta gudu.
Eh to alhaji sama'ila yace. Saidai kuma idan mukayi amfani da abinda lila ta bamu labari banajin mahaifinta zaiyi tsammanin tana nan domin shi a zaton shi tabar garin.
Sunyi kimanin sa'o'i biyu suna cece kuce da baiyi musu amfani ba saboda sun kasa yanke cikakkiyar shawarar abindaya kamaa suyi. Daga karshe sai alhaji sama'ila yasa yaransa suka sauyawa kwalayen kudin nan matsugunni. Awani asirtaccen dakin karkashin kasa dake gidan aka saka su.
Bayan an gama taron sai mansur ya nufi dakinsa da nufin ya danyi tunani akan abubuwan dake faruwa. Lokacin daya shiga dakin ne to yake ganin farar takarda a yashe a tsakar dakin cikin rawar jiki ya dauki takardar da hannu mai kyan sannan ya warware ta. Tun kafin ya warware wasikar jikinsa yabashi cewa shi aka rubutawa. Sannan ne to yafara karanta wasikar wacce aka rubuta cikin siraran rubutu kyawawa. Tun kafin yafara karantawa yagane rubutun mace ne.
.
Dga Laila Mai Bege:
Zuwa ga Wanda take bege.
Wayyo allah rayuwa inama ace akullum na tare dakai mansur to da duk bakin cikin dake tattare da zuciyata ma'abociyar kaunar ta yaye.
Ka sani ya masoyina na rubuto ma wannan takarda ne cikin bakin cikin rayuwa dakuma takaicin rabuwa dakai akan dole badon naso ba masoyina.
Me yiwuwa ranka

Please Login or Register in order to submit comment