Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saro suna rufe motocin dasu. Mintuna bakaiwa da farawar su sai ga motocin sun bace. Bazaka taba cewa akwai mota awurin aboye ba.
Daga cikin hasken farin watan zaka iya ganin farankau farankau din kunnen bazuka zakuma ka iya shaida salman cikin koren wando da farar rigarsa. Bazuka ya kalli salman shima salman ya kalli bazuka sannan salman ya takura ya buga tsalle yafado kan arangama.
Arangama yayi wata kara ta razana kafin yagane abinda ke faruwa salman yakama kwalar rigarsa ya hada kansa da bishiya. Dummm.
Nan take arangama ya baje sumamme. Guntun sauran direbobin sunyi sororo mutuwar tsaye saboda tsabar tsoro. Daya daga cikinsu yafara karanta
AYYATIL KURSIYYU. Domin shi a zatonsa aljani ne ya sauko daga sama. Dayan kuma dayake jahili ne sai tsoro yasa shi fitsari a tsaye.
Salman ya matso kusa dashi tun kafin ya karasa sai direban ya sare anan yafadi sumamme. Ya zurare ya zube akar.
Duk dayake kuwa ba suma yayi ba yanaji yana gani salman ya hadasu ya daure da igiya kamar barayi bayan dan lokaci saigashi salman ya dauresu su duka.
Bazuka na zaune akan bishiya yana kallon abin dake faruwa koda yaga salman yagama daure su sai ya dira.
Kama min nan. Salman yace dashi bazuka ya matsa kusa ya kama kafar arangama shikuma salman yakama kansa suka jefa shi cikin daya daga cikin motocin. Da haka suka jefa su suka kulle su aciki. Abinda bazuka baisani ba shine salman ya lalube takardun dake aljihun arangama wacce alhaji balarabe yabasu amatsayin shaida idan sunje wajen aliyu batala. Ya kuma lalube yar karamar bindigar da alhaji balarabe ya sayawa arangama amatsayin kariya.
Ko kadan su salman basu sha wuya wajen shawo kan aliyu batala ba da farko yaso ya nuna musu shi sam ma baisan zancen ba amma daga karshe saiya amince a sakamakon takardar shaidar da salman ya nuna masa mai dauke da sa hannun alhaji balabare daga karshe yasa yaransa acikin daren suka dauko katan katan din tabar acikin wata motar katako aka kuma rufe katan katan din tabar da ciyawa.
Karfe hudun dare salman na zaune shikuma bazuka nata nasa aikin na loda katan katan din tabar cikin otocin su guda biyun da suka rage ita kuma daya motar su arangama kwance ciki sumammu.
Anan salman yace da bazuka zasu barsu da safe yan sanda sa same su
Idan kuma sun mutu ma to wa ya ragu? Abinda salman kenan yace.
Bazuka yagama shirin tabar tsaf sannan ya juyo ya kalli salman yace. Sai kayi tafiya. Duk inda nayi ka bini. Salman ya kalle shi galala kamar wanda yake tunanin yatabu sannan yace kana jin zamu iya fita da wannan kayan ta gaban kwastan da rana tsaka?
Ai abin da ba zai yu bane.
Bazuka yayi dariya sannan yace da salman agurinka ba. Adaidai lokacin ne bazuka ya zaro wasu tutocin kasar jamhuriyar nijar guda biyu daga aljihunsa yan kananan tutoci ne irin wanda masu mulki ke sawa agaban motocin su in zau kai ziyara wani wajen. Sannan bazuka ya zaro lambobin mota guda hudu daga cikin jakarsa t roba lambobin motar irin wanda gidan gwamnatin nijar ne ke yin amfani dasu ajikin motocinsu.
Salman shidai na zaune yana kallon bazuka yanata faman daura lambobin bayan yagama daurawa sai ya mike tsaye ya sake zaro tutocin daga aljihunsa yaje ya kafa daya agaban motar da zai shiga ya kuma kafa daya agaban motar da salman zai shiga. Sannan ne yace da salman to Bismillah. Zabi daya daga ciki kashiga.
Salman ya dube shi sannan yace in nashiga me za'ayi? Bazuka yace tafiya mana. Ta ina zamu bi? Salman ya sake tambaya ta inda gwamnan maradi zaikai ziyara najeriya ba.
To idan zaikai menene binshi zamuyi? Bazuka ya kalli salman sannan yace kai baka gane magana shin duk inda nake kai baka ganewa? Duba ka gani lambar motar mu irinta motocin dazasu yiwa gwamna rakiya ne kuma tutocin ma irin nasu ne kuma tanan hanyar zasu wuce suna wucewa zan yi gaba nabisu abaya kaikuma kana biye dani kaga idan munje boda sai kwatsam su dauka muma yan rakiyar gwamna ne. Kaga saimu shige cikin kwanciyar hankali batareda wata matsala ba. Suna fitar damu daga kasar sai mu saki hanya mubi ta kanmu. Sauran kuma ya rage nawa. Nasan duk hanyoyin kamar yadda nasan tafin hannuna. Bazuka yayiwa salman murmushi sannan yace ko har yanzu baka gane ba?
** ** **
Da kyau bazuka da kyau salman laila tace cikin farin ciki lokacin dataji su salman sunyi nasara wajen fito da tabar daga nijar sun kawai alhaji sama'ila tabar tun kafin su salman su karaso alhaji sama'ila ya bugo mata waya yace da ita an kawo masa.
Laila ta bude wata karamar akwati ta dauko damin naira hamsin-hamsin na naira dubu hamsin-hamsin ta baiwa su salman da bazuka tana basu ta mike tsaye to ni zan tafi nagode akuma sauka lafiya zan kuma sake bukatar ku in an kwana biyu sannan tafice daga dakin.
Daga karshe salman da bazuka suka baiwa juna hannu sukayi sallama.
Bazuka ya nufi filin jirgin sama shikuma salman yayi nasa wuri.
** ** **
Gidan babu kowa sai laila ita kadai tana hada kayanta acikin wata bakar akwati bayan tagama saitayi sauri ta nufi inda mahaifinta ke ajje na'urar nan mai bude akwatin kudin dake karkashin kujera a boye. Wannan kudi sune wadanda alhaji abubakar sukayi kwangila shi da alhaji balarabe to yanzu alhaji abubakar ya mutu kuma alhaji balarabe ya cinye kudin ga kuma laila nan ta bude kasan kujerar ta dauko akwatin kudin ta kuma nufi inda mahaifinta ya boye dan karamin jirgin nan mai saukar ungulu da niyyar ta gudu gurin kanwar babarta dake jos wato babar bazuka.
Can kuma alokacin da alhaji sama'ila ya sa yaransa su dauki katan katan din tabar daya saya su kai masa gida saboda shagon ya cika lokacin da suka isa gida da tabar sai hajiya goggo ta basu izini dasu shigo da tabar cikin gia takuma ce su kaita can cikin wani daki dake fuskantar wanda mansur ke ciki.
Bayan dan lokaci sun gama lodawa sun bar gidan mansur na kwance a kado saiyaji karar faduwar kwalin tabar da aka shiga dasu yanzun nan yafado. Nan da nan yashiga dakin da niyyar ya gyara kwalin da hannunsa mai lafiyar a zatonsa basu shirya kwalin daidai bane.
Mansur ya bude dakin ya shiga kwalin ya fashe abin dake cikin kwalin ya wartwasu adakin mansur ya cika da mamaki shidayake tsammanin yaga ciyawar taba saiyaga dalar amurka ako ina awarwatse adakin. Wani dan motsi dake bayansa shiyadawo da mansur cikin hankalinsa abida na tsaye akansa idonta akan dalar amurka.
** ** **
Tun kafin bazuka yazo kano saida laila ta sanar dashi duk abinda zai faru don haka yazoa shirye daya daga cikin abinda suka tattauna da yar uwarsa laila shine bayan sun rabu zatayi kamar ta sallame su shida salman amma sun shirya cewa bazuka zai sameta agidan da mahaifinta ya boye jirgin nan ya dauketa su gudu Jos kafin kura ta kwanta.
Karfe biyar da rabi ta isa gidan tana zuwa tayiwa jirgin kallo daya sannan ta zaro salularta daga jakarta ta bugawa mahaifinta.
Lokacin da mahaifinta ya dauko sai ya tambayeta Laila kina ina nake neman ki tun dazun? Laila ta amsa da cewa ina neman kudi awaje baba na sami kudi kuma nayi amfani da nasihar dakayimin na nemi kudin awaje ta kowace hanya kamar yadda kace nayi ka kuma duba akwatin kudin ka mai ruwan gwal itama tabar da Arangama yaje nijar ya dauko ma, itama na nemata kuma na samu. Ka gani ai babu abinda yafi kudi ko baba?
Kafin alhaji balarabe yayi magana laila ta maida salularta jakarta SANNANME YAFI KUDI ? - 11
.
Kafin alhaji balarabe yayi magana laila ta maida salularta jakarta sannan ta nufi jirgin da niyyar ta shiga don ta zauna aciki ta jira bazuka.
Ta bude jirgin da niyyar ta shiga sannan saitaji kamar an soketa da kibiya salman na zaune acikin jirgin bindigar mahaifinta daya sayawa arangama shikuma salman ya kwace tana barazana ga rayuwarta.
Salman yayi dariya sannan yace kin gama naki kanwata saura ni na taka tawa rawar.
Laila ta dubi salman sannan tace dashi haba yaya salman kada kayi min haka mana nifa kanwarka ce ka tuna mutuncin dake tsakaninmu.
Kudi yafi mutunci laila babu abinda yafi in kuma akwai to ki fada min
ME YAFI KUDI ?
gara ki matsa da baya kar raina yabaci na raunata ki kanwata.
Salman yace yana murmushin mugunta laila taja da baya fankar jirgin tafara juyawa laila ta kalli salman ta kuma kalli akwatin data aje acikin jirgin ahannunsa sai hawaye ya fara kwaranyo mata.
Kadawar da iskar fankar jirgin ke yiwa gashinta ita ta tabbatarwa da laila cewa salman yayi sama da dalar amuka miliyan uku yakuma yi sama da yancinta wani motsi dake bayanta shi ya dawowa laila hankalinta ta juya ta dubi inda motsin yake. Duk da yake duhun magariba ya fara shigowa hakan bai hana laila ganin farankau farankau din kunnuwan Bazuka ba. Ka makara sha sha sha Laila tace dashi a fusace.
.
ALHAMDULILLAHI MUNZO KARSHEN KASHI NA DAYA KENAN SAI KUMA MU HADU A KASHI NA BIYU INSHA ALLAHU
.
KASHI NA BIYU
.
BABI NA BAKWAI 7
Arangama yayi dan motsi da kafafunsa sannan yayi gurnani dan tsamirmirin direban dayayi suman karya ya dago kansa ahankali sannan ya dogara ya tashi zaune ta hanyar yin amfani da kafadarsa ajikin makaren kujerun motar dasu salman suka kullesu aciki.
Yayi kokarin kunce igiyar dake hannunsa amma abin yaci tura duk lokacin da yayi kokarin takura igiyar saiyaji kamar hannunsa zai karya to gashi daman hannunsa a bushe kamar itace. Yayi ta mutsu mutsu shi kadai amma ya kasa kunce kansa. Karfe biyar da mintuna arba'in na safe agogon dake jikin motar ne ya nuna adaidai lokacin ne arangama ya farka yatashi zaune da kyar yana gurnani kamar zaki. Sannan ya dubi daya direban na biyu dake kwance baya ko nuna alamar farkowa. Sannan ya juya ya dubi daya direban mai fuskar matsorata wanda ke kwance jikin makaren motar yana haki.
Kai sha shan banza me kakeyi azaune? Arangama yace dashi cikin fushi menene amfaninka kana ganinmu a kwance amma ka kasa kunce kanka balle mu ka taimake mu. Cikin fushi sai arangama ya dago kafafunsa biyu wadanda ke daure da igiya tamau. Ya daki gilashin dake jikin kofar motar bangaren hagu karfin dukan yasa gilashin ya tarwatse kamar an daki kwarya da gora.
Dankareren bakin takalmin dake kafarsa shi ya baiwa kafar tasa kariya daga yankan gilashin.
Arangama ya zare kafarsa ahankali yana muzurai sannan ya dago hannayensa biyu dauraru yafara yanke igiyar dake jikinsu ta hanyar yin amfani da kaifin fasashshen gilashin daya rage bai fadi ba daga jikin mota.
Dakiku arba'in cif saiga igiyar akasa arangama ya yanketa sannan ya kunce waccce ke daure da kafarsa ya dubi daya mutumin wanda har yanzu ke kokarin kune hannunsa amma batareda yaci nasara ba ya kwashe shi da mari har sai da kansa yayi baya sannan arangama ya dauki balgacaccen gilas din dake warwatse ko'ina ko ina cikin motar ya yanke igiyar dake hannun mutumin da kuma kafarsa lokacin da arangama ya bude motar suka fito tuni rana ta fara sadadowa ta bayan tsibirin tarin yashin dake falalen filin saharar.
Sassanyar iska mai ratsa kashi da bargo ta buso. Arangama ya dubi mutumin dka egefe guda yana kokarin tsai da jinin dake kwarorwa daga bakinsa asakamakon marin da arangama yayi masa.
Zan kara ma wani marin idan bakazo nan ka kama min mun fito dashi ba. Arangama yace dashi cikin kakkausar murya da zata iya sa mace mai juna biyu bari. Dan siririn mutumin ya share jinin dake kwarara ta baki ta hancinsa.
Sannan ya matsa jikin motar inda arangama ke ta famar kiciniyar janyo kafar daya mutumin dake cikin motar. Rike nan. Aranagama ya bugawa mutumin tsawa cikin gigita sai mutumin ya rike kafar shi kuma arangama ya shige cikin motar ya tallafo kan mutumin sannan ya turo shi waje.
Bayan sun turo shi waje sai suka kwantar dashi akan sassanyan yashin bayan arangama ya gama yanke igiyoyi da aka daure mutumin dasu sai yafara mirgina mutumin akan sassanyar yashin.
Wai shi a haukansa sanyin yashin na iya farkar dashi tunanin hakan shi ya jefo da wata dabara zuciyar arangama. Kama nan mu tube rigarsa yace da daya direban mutumin ya tallafo dan uwansa sumamme ta baya sannan ya fara kwabe rigar mutumin. Lokacin da hannunsa ya zo daidai kirjin sumammen mutumin sai kamanninsa suka canza guma ya rufe shi duk da yake kuwa har yanzu sassanyar iska na busowa. Fuskarsa ta canza launi lokacin daya daga kirjin mutumin babu alamar numfashi. Sannan kijrin ya daina bugawa.
Arangama ya kira sunansa tsorace. Sautin muryar mutumin ne yasa arangama matsowa da sauri ya ture mutumin sannan ya tallabi sumammen kansa ya langwabe gefe guda. Arangama ya dafa kirjin babu bugun zuciya sam wannan kuma ke nuni da...........
Ya mutu. Arangama yace babu alamar jin tausayi ko nuna imani azuciyarsa.
Daya mutumin ya fashe da kuka kamar mace Allah sarki sabitu allah yasa ma kaji Allah yaji kanka. Sannan ya durkusa ya rungumo mutumin yana kuka yana girgiza shi. Tashi mu tafi sabitu na san da gangan ne ba mutuwa kayi ba. Nasan arangama karya yake baka mutu ba. Baka mutu ba baka mutu ba wayyo Allah na rasa dan uwana abanza shekarun mu ashirin muna aiki tare sabitu amma saika mutu ka barni.
Yayita sambatu arangama na gefe yanayi masa dariya. Domin shi aganinsa wannan wata hanya ce dazata kawo masa kudi don haka menene abin damuwa ciki? Ya tambayi kansa yana murmushi.
Direban yaci gaba da sharbar kuka yana ta juya dan uwansa shikuma arangama tuni zuciyarsa ta fara yi masa sakar gizo-gizo.
Misali yanzu Alhaji yatashi daga bacci ya sami......... Tunaninsa ya katse indai hakane to ya samarwa kansa sabuwar hanya ta kasuwanci. Aranhama yayi murmushi lokacin daya mike tsaye sannan ya sunkuya ya ture direban dake rungume da kawar. Ya ciccibi gawar sannan ya nufi bayan but din motar. Yana zuwa sai yajefa shi ciki ya sake mayarwa ya rufe. Sannan...ME YAFI KUDI ? - 12
.
Yana zuwa saiya jefa shi ciki ya sake mayarwa ya rufe sannan ya dubi mutumin dake zaune akan farin yashin saharar yana kuka murmushin mugunta ya bayyana a fuskarsa lokaci guda kuma ya kalli tsibi tsibin yashin dake sararin sahar fari tas iska tafara kadawa da dan karfi haryanzu kuma ana kwararo sassanyar iskar nan.
Idan har inaso abin ya cimma nasara yace da kansa to dole ne wannan ya tafi..... Ya nuna mutimin dake kuka da dan yatsansa. Wayyo Allah sabitu. Mutumin yaci gaba da sambatu mutuwa mutuwa me yasa kika dauki dan uwana sabitu baki daukeni ba. Wayyo mutuwa kizo ki daukeni na huta.
Kanajin yanzu idan mutuwar ta dauke ka huta?
Kakkausar muryar arangama ta doki kunnensa kamar daga sama sai yaji hannayen arangama sun shaki kwalar rigarsa sunyi sama dashi karfafan hannun arangama suka daga mutumin sama kafarsa ko kasa bata tabawa. Kana son mutuwa ta dauke ka ko? Arangama ya tambaye shi yana murmushin mugunta. Kayi min rai don Allah da gangan nake mutumin yace cikin tsoro yana makyarkyata a sama arangama ya jijjiga shi domin shi ji yake kamar ya dauki yar tsana. Allah ya karbi addu'arka arangama yace dashi yanzu mutuwa zata dauke ka.
Wayyo Allah amsa kuwar kukan mutumin ta ratsa sararin saharar lokacin da arangama ya hada shi da jikin bishiyar dasu salman suka dana musu tarko karar haduwar kan mutumin da jikin bishiyar yabada wani sauti duss! Kamar an jafi jaki da kabewa bai ko shura ba.
Arangama ya saki kwalar mutumin ya fado akan yashi sannan ya kama kafar mutumin ya fara jansa akan yashin saharar kamar mataccen jaki. Saida yayi tafiya dashi mai nisa. Sannan ya yarda shi agindin tsibin wani yashi tun kafin yabar gurin iska ta fara turo yashin kan mataccen mutumin arangama yayi murmushi lokacin dayaga tuni yashi ya rufe rabin mutumin.
.
Bayan ya dawo gindin motar saiya bude bayan but din motar domin ya tabbatarwa da kansa ko gawar daya baro ciki tana nan. Bayan ya tabbatar din sai ya rufe yashiga motar ya tasheta karfe bakwai saura minti uku agogon jikin motar ya nuna arangama ya duba nasa agogon don ya tabbatar da gaskiyar agogon jikin motar. Bakwai saura minti bakwai ya nuna. Hakan shi ya tabbatar masa da cewa agogonsa ya makara da minti biyar. Ya kunna sigari sannan ya fitar da hayaki ta baci ta hanci yayi murmushi sannan yace
ME YAFI KUDI ?
Lokacin dayaja motar kurar yashin saharar ta rufa masa baya. Babu alamar gawar mutumin daya kashe lokacin da yazo giftawa ta wajen yashin ya rufe ta.
** ** ** **
Me yake faruwa ne? Bazuka ya tambaya a rude.
Yatashi da kudin gaba daya laila tace dashi tana sheshshekar kuka. Bazuka yayi shiru na dan lokaci yana sauraron rugugin jirgin mai saukar ungulu da ya tashi hannayensa cikin aljihun wandonsa na leda yayi shiru na dan lokaci sannan ya dago kansa ya dubi laila farankau farankau din kunnuwansa masu kama da alamar Tambaya na nuna takaicinsu ga abinda yafaru.
Menene dabara? Laila ta tambaya cikin sanyin murya kiyi hakuri laila yaci gaba da cewa nasan halin salman bashida kirki ko kadan tun lokacin daman danazo sai danayi mamakin yadda akayi kika hada kanki da wannan dabbar mutumin mai mugun hali. Na san dama haka zata faru.
Laila ta fara kuka ba kuka zakiyi ba.
Bazuka yace da ita yanzu ina zamu mu buya kafin gobe da safe nasan yanzu babanki na nan na shirin baza karnukan farautarsa domin ganin bamu kai labari ba.
Koda yake nasan idan yazo baiga jirgin ba zai iya tunanin tuni mun bar garin bazai taba zaton ke da nine ba ko kuma salman tunda baisan da zuwan mu ba.
Amma nasan dan ta'adda arangama wanda na fada miki salman ya sumar da su a saharar nijar zai iya shaidawa babanki cewar kinada mataimaka don haka abinda nake gani yanzu shine musami inda zamu buya kafin gobe da safe akwai wani kauyen nan kusa da jos inda wani babban abokina yake ina ganin nan yakamata mu tafi gobe a boye ki acan kafin nayitunanin abin yi.
Sannan bazuka ya juyo ya dubeta yace saina dawo miki da kudin mahaifinki da salman ya dauke ni nayi sanyar har abin yafaru don haka kuwa alhakin neman su na kaina. Sannan yayi murmushi yace da laila nafi salman hadari idan raina yabaci saina rama miki cin amanar da salman yayi miki koda kuwa zai zama karshen rayuwata ne.
Abinda laila ta gani a idanunsa shiya tabbatar mata da abinda yafada gaskiya ne. Laila tayi ajiyar zuciya sannan tace dashi mu tafi gidansu kawata abida ina tsammanin zasu sami gurin buya. Suka nufi inda motar take suka shiga. Bazuka yatashi motar sannan suka fice daga gidan.
Adaidai lokacin ne sukaji rugugin jirgi ya sauka afilin saman malam aminu kano wanda ke makwabtaka da gidan gonar da alhaji balarabe ya gina don ajiye jirginsa mai saukar ungulu. Bazuka ya dubi laila yayi murmushi menene? Laila tace dashi haryanzu muryarta a sanyaye.
Ina mamakin irin yadda mutane suke jefa kansu ga halaka ne duniya da lahira akan kudi.
Abinda nake mamaki shine salman baiyi ko tunanin abinda zaiyi da duk kudin nan ba. Baikumayi tunanin inda zaije ya aje jirgin ba. Amma saboda
idonsa ya rufe baiyi tunanin haka ba. Yanzu idan jirgin yafado dashi ya mutu me zaicewa Ubangijinsa?
Kai kenan da kake tunanin Allah inji laila kasan fa kudi yadda suke yanzun nan sa sai imani.
Kudi manya inji bazuka.
Laila ta dubeshi tayi murmushi sannan tace harka tuno min da kalmar da mahaifina ke tambayata da ita ina karama.
Me yake cewa dake? Bazuka yace da ita
Kanason kaji ne?
Ya gyada kai.
Sannan tace kalmar a kullum itace
ME YAFI KUDI?
bazuka yace LAFIYA......sannan yayi shiru yana shakkar abinda yace saboda ganin salman baiyi tunanin lafiyarsa ba sai kudin. Sannan ya karawa motar wuta zuciyarsa tana mai shakkar amsar daya baiwa Laila.
** ** **
Mansur yajada baya cikin tsoro tunda yake bai taba ganin dalar amurka kamar haka ba. Abin yazame masa kamar budin idon aljanu amma ganin abida abayansa tana kallon kudin shiyasa shi wasuwasin hakan.
Abida ta dafa bayan mansur cikin kaduwa da abinda tagani ta bude baki zatayi magana amma abin ya gagara mansur ya dubi fasassun kwalayen tabar (dalar) da suka fashe sannan yayi musu lissafin gaggawa cikin zuciyarsa su biyu ne kawai suka fashe amma sai mansur yaga kamar duk kwalayen ne suka fashe saboda tarin dalar dake tsakar dakin.
Mansur ya dubi abida jikinsa na rawa karyayyan hannunsa amakale akusa da kirjinsa.
Alhaji ne ya aiko dasu? Ya tambayeta a tsorace ta gyada kai sannan tace ina zuwa.
Tafice da sauri ta nufi babban dakin shakatawa bayan yan mintina ta dawo tace dashi nayiwa baban waya gashi nan zuwa mansur ya kasa cewa komai sabioda rikicewar da kwakwalwarsa tayi.
Dirin motar da sukaji a kofar gidan shiya nusar dasu da zuwan alhaji sama'ila sukaji takun alhaji ya nufo dakin tuni daman sun sanar da hajiya goggo don haka su uku alhaji ya tarar adakin ko wannensu na tsuma sun hada gumi kamar masu hadiyar kunama. Alhaji sama'ila yayi turus a kofar dakin kamar wanda yabita cikin fasassun bulan kasa yana kallon kudin sannan ne hajiya goggo tace dashi akaro na farko. A ina ka sai wannan tabar alhaji? Yayi shiru na dan lokaci sannan yace dasu kuzo mu tafi falo.
Bashi yagama tunaninsa ba sai karfe bakwai da rabi na yamma sannan ne ya juyo ya dubesu. Hajiya gaggo tace alhaji meke faruwa ne? Ni ban gane ba awajen wa ka sai wannan tabar? Alhaji sama'ila ya dubeta sannan yace agurin LAILA BALARABE..... Duka dakin akayi ajiyar zuciya alokacin ne kararrawa ta dau kara abida ta tashi da sauri ta bude tace wanene ?
Atsaye a kofar dakin sanye da kayan siliki ruwan hoda Laila ce atsaye kuma abayanta wani saurayi ne sanye da kayan leda. Kunnensa kamar alamar tambaya (?).
.
BABI NA TAKWAS 8
Alhaji balarabe ya ajje salular ahankali cikin takaici manya manyan kumatunsa masu kamar tumfafiya suka motse sannan kirjinsa yayi kuna yafara radadi. Nan da nan ya nufi dakin shakatawarsa da sauri ya bude wata yar karamar akwatinsa fara wacce yake ajje magungunansa don irin wannan rana. Shekaru kusan takwas kenan yanzu da alhaji balarabe yake fama dawannan cuta ta ciwon zuciya. Bacin rai mai tsanani shi yake tayar masa da ciwon yajawo fararen ledodi da kuma kwalabe wadanda ke dauke da kwayoyi iri daban daban sannan ya fara zazzago kwayoyi daidai akan tafin hannunsa bayan ya zaro iri tara sai ya fara jefa kwayoyin abakinsa yana kora su da ruwa.
Bayan duk ya hadiye kwayoyin sai yatafi dakin barcinsa ya kwanta zuciyarsa tana ta tafarfasa da bakin cikin da laila ta tura masa.
Yanzu yar dana haifa ce tayi min haka? Ya lumshe idonsa yana juyi akan gadom. Akwayin gwal dinka ta kudi na dauke ta...... Tabar dakasa arangama ya dauko ma anijar itama na dauketa..... Ka gani baba me yafi kudi?..... Nasihar ka ce nayi amfani da ita.
Maganganun da laila ta fada masa ta cikin salula sukaci gaba da amsa kuwwa acikin kwakwalwarsa wayyo Allah na tsiyace! Yace cikin takaici yana shure shure akan gadon da manyan kafafunsa masu kamar doya.
Yanzu ina zanga laila? Da kudina ya batagara na rasa laila.
Sannan ne to arangama ya fado masa azuciya Ina yake yanzu? Tambayar da tafara darsuwa azuciyarsa kenan.
Haushi ya sake tuke shi zuciyarsa tafara radadi kamar zata fito daga kirjinsa idanunsa sukayi ja kamar gauta.
Wanne sakaci ne yasa arangama yayi masa wasa da dukiyarsa? Sannan ne wani tunani ya fado masa mai tsoratarwa.
Laila ita kadai bazata iya kwace kwalayen taba daga hannun su arangama ba. Idan kuwa abinda laila ta fada gaskiya ne to tabbas ko shakka babu laila tana da matamaka.
Su wanene ? Alhai balarabe ya tambayi kansa tsoro da fargaba suka kara cika zuciyarsa domin yasan indai har da gaske din ta kasance laila nada mataimaka to lallai yanzu dukiyarsa tayi masa nisa don ya tabbata yanzu tsakanin dukiyarsa da kanon dabo me yiwuwa yafi nisan Mil dari biyar.
Abinda ke dagulawa alhaji balarabe lissafi kuma ke matukar bashi mamaki shine wanene da har zaifi karfin arangama ya kwaci dukiyarsa daga hannunsa?ME YAFI KUDI ? - 13
.
Abinda ke dagulawa alhaji balarabe lissafi shine wanene da har zaifi karfin Arangama ya kwaci dukiyarsa daga hannunsa?
Alhaji balarabe ya tuna da irin taurin kan arangama zafin zuciyarsa dakuma yawan son tashin hankalinsa saigashi cikin yan sa'o'i yarsa ta samo wanda yafi shi.
Alhaji balarabe

Please Login or Register in order to submit comment