Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari asamu kudin. Yace cikin zuciyarsa yayi ribas ya fita da motar daga cikin gareji sannan ya nufi gidan alhaji sama'ila baiko damu ya rufe komar garejin ba. Hannunsa akan hancinsa yana kare warin gawar dake cikin motar.
Alhaji balarabe yaji sa'ar da arangama ke lalube aljihunsa lokaci guda kuma yagane cin amanar da arangama ke shirin yi masa saidai kuma babu yadda ya iya daga lokacin da ruwan allurar nan ya kwarara jijiyoyinsa jikinsa saiyaji kamar an zare masa laka. Hakika kam yasan yanzu rayuwarsa tazo karshe. To amma fa kafin ya mutu din sai ya batawa arangama ruwa. Don haka saiya yunkura amma tashi ya gagara yasake yunkurawa ya daki gefen teburin dake daf da gadon alokacin ne tunanin laila ya fado masa nan da nan saiyaji kamar an kara masa karfi domin yasan idan yabar arangama ya cimma burinsa to wannan na nufin laila ta tashi a tutar babu kenan.
.
Yafara jan ciki akasa har saida yakai ga inda talfon yake sannan hannunsa na rawa ya buga lambar police stations wajen jami'an tsaro cikin rawar baki yace da wanda ya dauki wayar ku duba mota mai lamba..... Yabasu lambar motar
to menen kuma daga ake bugo wayar? Alhaji balarabe yamaida numfashinsa da kyar saura kadan kan talfon din ya kwace daga hannunsa sannan yace muryarsa na rawa ku hanzarta motar bambalasta ce kuma da gawar mutum aciki.
Kan talfon din ya kwace daga hannunsa ya fado kan tattausan kilishin.
Wani duhu mai tsananin baki ya mamaye kwakwalwarsa sannan yaji ya daina tunanin komai yakuma daina ganin komai sai surar mahaifiyar laila wacce ta rasu tun laila tana karama. Gababbuwan jikinsa suka saki sannan mai kasancewa da yanke jin dadi da komai da komai na rayuwar duniya ta dauke shi.
.
*** *** ***
Tun lokacin daya hau babban titi ya lura da bakar motar na binsa amma ko kusa bai taba zaton yansa ne ba don haka saiya kwantar da hankalinsa yaci gaba da tukinsa har zuwa kofar gidan alhaji sama'ila yana zuwa sai mai gadin gidan ya bude kofar cikin gaggawa saboda ganin motar mai tsada ce. Arangama ya wuce kai tsaye cikin babban dakin shakatawar dake gidan sannan yagawa wadanda suke cikin falon tsawa.
Ya Isa haka! Yace dasu cikin kakausar murya hannunsa rikeda da..ME YAFI KUDI ? - 18
.
Ya isa haka! Yace dasu cikin kakkausar murya hannunsa rike da sharbebiyar takobi mai launin garai tsirararta tana kyalli.
Alokacin Alhaji sama'ila na sake tattauna maganar laila da iyalinsa ahaka arangama ya ritsasu alhaji da hajiya goggo na zaune kusa da juna ita kuma abida na zaune kusa da mansur tana sakar tuma kasa. Lokacin da arangama ya fado dakin kamar daga sama yana muzurai alhaji sama'ila ya fara karanta ayatul kursiyu azuciyar domin shi a tunaninsa aljani ne ya bude masa ido. Amma ganin kowa adakin yayi shiru sai alhaji sama'ila yagane cewa lallai ba aljani bane.
Ina bukatar kwalayen tabar daka saya.
Arangama yace dashi kai tsaye inkuma bahaka ba yanzun nan naraba ka biyu cikin alhaji sama'ila ya dauki kara kululu domin yasan arangama yaron alhaji balarabe ne mansur yayi ido hudu da arangama saiyaji shima cikinsa ya kada saboda ganin jajayen idanun arangama.
Inason sa da.... Muryar arangama ta kakare sannan karar bindiga ya mamaye gurin takobin yafadi gefe guda sannan jini yafara bullowa daga hannun arangama inda yansanda suka harbe shi.
Muna bukatar muga hannunka a sama daya daga cikin yansandan guda uku yace dashi. Arangama ya juya ahankali sannan ne to ya fahimci ashe dan sanda daya ne mai bindigar kamar haske don sauri babu wanda uaga zuwan dukan yansandan sai kawai gani sukayi dan sandan yayi sama yafado akasa bindigar kuwa tayi waje guda
Arangama ya nake yansandan sannan yayi waje da gudu yana zuwa saiya fada cikin bambalastar yayi ribas. Sannan ya fizgi motar da gudu zuciyarsa cike da tunanin inda yakamata yaje ya buya kafin kurar nemansa ta lafa. Domin yasan yanzu labarinsa ya isa ga kowanne dansanda dake garin sannan ne to ya tuno da inda yake ganin nan kadai ne zai iya buya batareda an kama shi ba.
.
Dr. Labaran na zaune shi da matarsa mariya tana kallon talabijin shikuma yana nazarin wani littafi dake magana akan haihuwa sai kofar falon ta bude da karfi kamar iska ta dokota. Arangama ne.
Lafiya? Dr labaran ya tambaya lokaci guda kuma idonsa yakai kan sharbebiyar wukar dake hannun arangama. Inason ka boye ni arangama yace dashi cikin kakkausar murya.
Ni bazan boye ka ba babu.....
Bai karasa ba akamakon tsinin wukar daya binne kansa cikin makogoronsa matar dr labaran ta kwala kara Oh jesus! Alokai guda kuma karar harbin bidigogi daga waje ya rufe kukan nata. Arangama ya fadi da fuska akan dr. Labaran wanda ke kwance yana shure shure wanda baya hana mutuwa ba'a dade ba yansanda suka cika gidan kowanne na nasa aikin.
.
** ** **
Kwanan alhaji balarabe biyu da rasuwa laila da bazuka suka sauka agidan alhaji sama'ila anan ne alhaii sama'ila yabasu duk labarin abinda yafaru shima bazuka yabasu nasa labarin sannan bazukan yayi sallama yace da laila idan an kwana biyu ta koma wajen mahaifiyarsa wacce yar uwa ce awajen mahaifiyar laila.
Yau kwanan laila hudu kenan acikin kwanakin datayi tayi ta fama da ziyarar jami'an tsaro wanda daga karshe duk maganar ta shiririce tunda wadanza za'a hukunta duk sun tafi.
.
Wata safiyar juma'a misalin takwas da rabi na safe rana ta fara hidowa daga cikin sararin samaniyar subhanahu wat'ala sai iyalan gidan alhaji sama'ila sukaga laila ta fito da jaka gaba daya suka tashi tsaye suna tambayar ta inda zata. Acikinsu mansur wanda shi tun bayan dawowarta bai taba gajiya da ganintaba. Hakika abin ya tayar masa da hankali.
Me akayi miki laila? Alhaji sama'ila ya tambaye ta.
Laila ta share hawayenta sannan tace babu komai baba inason dai kawai na koma wajen yar uwar mahaifiyata ne jos.
Domin akullum na dubi mansur inajin kunyar hada ido dashi saboda.....
Haba laila....... Hajiya goggo tace da ita. Ai abinda ya wuce ya wuce to ke da zaki zauna dashi har abada yaya zakiyi?
Laila ta juyo ta dubi hajiya goggo a rufe kamar ya ya har abada ni dawa zamu zauna dashi?
Ke laila dubanni nan bana son munafinci kina sonsa ko bakya son ba ko?
Laila ta dago kai suka hada ido da mansur wanda ke murmushi.
Tayi maza ta sunkuyar da kai don kunya tana murmushi.
Ah! Su laila manya harda yi masa irin wannan murmushi wato kwace min fada zakiyi kenan tun kafin a....
Sam abida ta manta da hajiya da alhaji suna wurin nan da nan ta tashi ta ruga ta shige dakinta da gudu.
Yar banza mara kunya. Hajiya goggo tace. Alhaji sama'ila yayi murmushi baice komai ba mansur shima kunya ta rufe shi.
Inason ku hada kanku. Ku yanzu ya'yana ne don haka kuda abida babu wanda yafi wani agurina. Alhaji sama'ila yaci gaba da cewa nan da watan gobe za'ayi bikin ku ke kuma laila saikisan yadda zakiyi da dukiyarki domin yanzu kina daya daga cikin cikon manyan garin nan.
Laila ta dube shi sannan tace dashi
baba kayimin duk abinda kaga ya dace tunda kace in dauke ka amatsayin mahaifi to na dauke ka din. Nakuma danka duk dukiyata ahannunka.
Alhaji sama'ila ya kasa magana don mamaki sannan ya dubi hajiya gwaggo ya kifta mata ido saitabishi suka bar wajen suka nufi dakin kwanansu. Sunyi hakane don su bar yaran su kebe da junansu kuma su fahimci juna.
Laila ta dubi mansur cikin jin kunya sannan tace dashi Yaya Mansur.
Suka tuntsure da dariya bakisan wani abu ba hajiya laila. Mansur yace da ita.
Ina son ki shayar dani madarar soyayyar nan da kikayi min alkawari acikin wasikar ki ta kwanaki kin tuna?
Laila ta dube shi ta kanne ido sannan ta matso kusa dashi ta dafa kafadarsa da siraran yan yatsunta tace dashi. Kai baka mantuwa? Kuma wayace maka sunana hajiya.
Mansur yace ai dole akira ki hajiya domin yanzu duk zagayen nan babu mai dukiyarki kinga kuwa ai dole ne ko don kudin ki akira ki hajiya. Kinsan kuwa kudin na iya sawa ayi komai don haka kullum nake jin tambayar nan azuciyata wai ME YAFI KUDI ?
Laila ta sunkuyo ahankali kanta daf da fuskarsa sannan tace madarar soyayya.
Suka sake kyalkyalewa da dariya. Kishi ya tuke abida wacce ke leken duk abin dake faruwa ta taga. Sannan ta leko tace. In ka gama da ita ka karaso nan nima na baka tawa madarar soyayyar saidai ni tawa harda zuma aciki.
Banda dai kishi yayata. Tun yanzu har an fara? Laila tace da abida cikin wasa. Abida ta harari laila sannan tayi murmushi tace. Daga yau na daina kanwata.
Suka fashe da dariya su duka ukun.
.
KARSHE.
.
NAZIR ADAM SALIH. (Nas)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment