Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauwake kafin mansur suce amin har likitan yafice daga dakin shin mansur yasan wannan likitan shiya kashe mahaifinsa kuwa? Bai sani ba likitan daya shigo ya duba mansur
Dr. Labaran ne.
.
Mintuna biyar da sallamar mansur saiga su acikin motar abida sun nufi kwandila unguwar su mansur da niyyar dauko kayansa dake gidan domin abida ta sanar dashi hajiya tace agiansu zai ci gaba da zama. Abida ta rage wuta ayayinda suka karaso katon filin wasan nan dake bayan gidansu mansur. Tun kafin su karaso suka hangi taron yara da manya a kofar gidan ana ta ihu motar yan kwana kwana tana fesa ruwa acikin gidan amma a banza kamar ma kara rura wutar akeyi.
Arangama na kallon lokacin da motar su abida tazo kofar gidan lokaci guda kuma yagane mansur amma yarinyar bauganeta ba.
Mansur ya dubi gidansu yaga yazama kamar karmami wuta sai ci take abinda ya bakanta masa rai shine...ME YAFI KUDI ? - 08
.
Mansur yadubi gidansu yaga ya zama kamar karmami wuta saici take abinda ya bakanta masa rai shine hotunansa dana mahaifinsa duk sun kone shida ganin sa saidai a darussalam kenan.
Abida ta dafa kafadar mansur sannan tace dashi kayi hakuri mansur wannan jarrabta ce daga Allah.
Mansur baiko ji abinda take fadi ba wannan ma wani yunkuri ne na lalata rayuwata. Yace cikin rada amma duk da haka saida abida taji abinda yafada ta juyo ta kalle shi cikin mamaki sannan tace
Wanene ke shirin ruguza rayuwarka Mansur?
Kada ki damu. Mansur yace da ita
zan sanar dake idan munje gida.
Awa daya da kashe gobarar saiga mansur da abida agaban hajiya goggo suna bata labarin abinda yafaru hawayen takaici na kwarara a idanunta.
** ** **
Alhaji balarabe na zaune a katon falonsa yana tunanin abinda yafaru a tsakaninsa da Laila hakika barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba domin yau laila ta nuna masa cewa duk mugayen hudubobin dayakeyi mata ta haddace su kuma bayan haka ma saigashi abinda bai taba zaton laila zata fara gwajin darasin dayake koya mata akansa ba. Ya lissafa kudin da laila ta dauka suin kai naira dubu saba'in yayi mamakin abinda laila zatayi da kudi haka. Kuma bayan haka ma ai ita ba wani waje take zuwa ba to me zatayi da kudi haka?
Alhaji balarabe ya yanke shawarar cewa zaiyi iya kokarinsa wajen lallamin laila domin shawo kanta wajen daina satar masa kudi saboda idan taci gaba da haka to bazaiyi kyau ba. Musamman ma dayake yana mutuwar son 'yarsa kuma bazai iya sa Arangama ya tsorata ta ba.
Adaidai lokacin da alhaji ke wannan tunani ita kuma laila na dakin ta tana shirye shiryen mataki nagaba da zata dauka.
Kan talfon ne ahannunta tana yiwa kannen babarta waya wanda suke zaune a jos.
Wa kike son gani? Kanwar babarta ta tambaye ta daga can daya bangaren. Baba nice laila.
Oho laila ce kina lafiya? Yaya su alhaji? Suna nan lafiya laila ta amsa sannan batareda bata lokaci ba tace da kanwar babarta hajiya inaso nayi magana ne da BAZUKA. Ko yana nan? Laila ta tambaya
Eh yana nan. Kanwar babarta ta amsa. Sannan tace bari na kirawo shi mintuna biyu laila ta shawo kansa yakuma yarda zaiyi mata aikin datake so ta sashi.
Bazuka na daya daga cikin kwararrun dirbobin dake simogar din taba daga kasashen waje zuwa najeriya awani lokaci kuma da dan direban jirgi mai saukar ungulu ne. Suna amfani da jirgin wajen safarar miyagun kwayoyi daga kasa zuwa wata kasar. Amma duk wannan wani tarihi ne nada can. Tun lokacin da iyayen bazuka suka sami labarin cewa wani Inyamuri ya koya masa tukin jirgi mai saukar ungulu kuma suka sami labarin abinda yake aikatawa sai mahaifinsa yasashi agaba yayita yi masa nasiha yakuma ce idan bai daina wannan harka ba to zai tsine masa tun daga rannan sai bazuka ya daina tukin fasa kwaurin miyagun kwayoyi yakuma daina tuka motar simogal din taba.
To amma saiga shi yau laila ta dawo dashi ruwa a inda take cewa
Saurara da kyau Abba wata tabace na sami labarin babana yanaso ya fita da ita daga najeriya ya kasa saboda kwastan sun tsananta.
Ita nake so ka fitar min da ita ko tayaya.
Sannan tace dashi
ZAKA IYA KO BAZAKA IYA BA?
In zakayi ladan naira dubu hamsin ce.
Abba Bazuka yace na yarda sannan laila tace to ina tsammaninka gobe da rana.
Abba shine ainihin sunansa amma yan simogal sun fi saninsa da bazuka saboda wai in ya gudu kamar harsashin dake fita daga bakin bindigar nan mai suna Bazuka yake.
MATAKIN KARSHE NA LAILA YA CIMMA NASARA DAGA NAN SAI RIGIMA TA FARA......
.
BABI NA BIYAR 5
Karfe bakwai na safe daidai laila taji mahaifinta ya kwala mata kira. Laila tayi tsaki sannan ta nufi dakin ga mamakinta saitaji ko tsoron mahaifinta bataji yanzu. Ta buda dakin ta shiga. Alhaji balarabe na zaune akan tebur yana sanye da wando da riga na kufta ya dora jar dara akansa ahannunsa na dama kuma yana wasa da biro.
.
Laila abinda nake so dake shine in kudi kike so saiki tambaye ni in bakisu ba sai kin dauka da kanki ba. Sannan yaci gaba da cewa ai da kikaji ina cewa ki nemi kudi kota wacce hanya ai ba ina nufin kifara ta gida bane abinda nake nufi shine ki fara ta waje ko ke haryanzu bakya fhimtar magana ne?
Bakya ganin kin batar da kudin kamar naki kika batar? Kinga ai anyi ba ayi ba kenan ke da zaki shigo da wasu ciki saikuma ki fara diban naki kina kaiwa waje. Laila tayi shiru tana sauraren zantuttukan mahaifinta nason zuciya sannan saita dago kai ta dube shi tace. To baba ai daman kaine baka banbance min din ba daka fahimtar dani da wuri cewa kudin waje ake daukowa akawo gida to ai da ta wajen zan fara. Amma tunda yanzu ka sanar dani shikenan zan fara. Tayi shiru. Alhaji balarabe yayi murmushi sannan yace Jeki ki shirya zaki rakani unguwa.
To baba laila ta fice daga dakin cike da mamaki domin rabon da mahaifinta yace ta rakashi wani waje tun tana yar karamar yarinya. Ko ina zan rakashi bansani ba. Laila tace cikin zuciyarta adaidai lokacin da take kokarin canza kaya.
Laila na zaune agaban motar mahaifinta saitaga ya karya kwana ya nufi (Airpor Road) ita dai bata tambaya ba suna tafiya suna hira kamar da gaske. Mintina goma ta kawo su filin jirgin saman Aminu kano laila tayi tsammanin filin jirgin saman zasu shiga amma sabanin haka saitaga mahaifinta ya zagaya ya nufi wani katon gida dake bayan filin jirgin saman. Gidan zagaye yake da manyan bishiyoyi da furanni gidan tsarinsa irin tsarin ginin turawa ne tun kafin su karaso wani dan siririn mai gadi sanye da kaya ruwan kasa kasa yabude musu kofa suka shiga gida.
To a sannan ne laila taga abinda taji mahaifinta na maganar ya saya jiya a talfon dan karamin jirgi ne mai saukar ungulu jikinsa mulmul yana sheki acikin hasken rana dan jirgin yana tsaye akan koriyar ciyawar data mamaye tsakar gidan.
.
Allah nagode ma daka nuna min inda jirgin nan ke boye laila tace cikin zuciyarta. Tun lokacin dataji alhaji balarabe na fadawa wani abokinsa cewa ya sayi jirgi mai saukar ungulu sai tunani yafadowa laila atake anan taga ya dace ta samo wanda ya iya tukin jirgin sama. To wannan shine dalilin kiran Bazuka kuma laila ta tanadi wannnan jirgin ne amatsayin kafar gudu idan tagama karya gwamnatin zaluncin ta mahaifinta.
Alhaji balarabe yayiwa laila magana har sau uku bataji ba ta zurfafa cikin tunani ya sake kwala mata kira sannan ta juyo firgigit tunanin me kikeyi ne? Alhaji balarabe ya tambayeta.
Ke jirgin yabaki sha'awa ne?
Atake anan laila taga damat da take jira saitayi murmushinta na yaudara kwarai kuwa baba ko zaka kaini inga cikinsa.
Haba laila kwantar da hankalinki ai wannan jirgin har tashi acikinsa saikinyi.
Laila ta dubi jirgin a nutse saitaga mutane hudu zai iya ci harda direba sannan sai tafara tunanin inda zata boye akwatin kudin nan idan ta dauko acikin abubuwan da laile ke shirin yi ya hada da sace akwatin mahaifinta wacce ke cike da dalar amurka. Domin tasan idan ta dauke wannan akwatin toi tagama dashi. Domin ta tabbata duk arzikin dayake takama dashi yana cikin akwatin nan.
** ** **
Jirgin dan karbo yayi kasa kasa asannu sannu har yataba kasa mintuna kadan da saukarsa saiga fasinjojin jirgin sun fara fitowa daya daga cikin fasinjojin wani dan gajerem saurayi ne fari kaukkara mai fadin fuska yana da manyan kunnuwa wadanda suka mike tsaye farankau farankau kamar alamar tambaya (?) saurayin mai manyan kunnuwa Bazuka ne dan kanwar babar laila. Yana sanye da bakar shat da farin wando da kuma takalmi (kito) ahannunsa na dama yana rike da bakar akwatin roba.
Saurayin ya gangaro kasa daga kan matattakar benen jirgin sannan yabi jerin gwanon jama'a zuwa wajen filin jirgin saman. Saurayin ya dagawa wata tasi hannu yace da direban tasi din CITY GUEST HOUSE. Wannan shine inda laila ta zaba amatsayin waje don saukar bakinta. Adaidai lokacin da bazuka ya sauka akano ne su kuma laila da mahaifinta suka baro gida suka nufo filin jirgin saman.
Mintiuna biyu bayan saukar jirgin su bazuka sai kuma wani jirgin ya sauka.
.
Mutumin farko daya fara fitowa daga jirgin wani katone mai jajayen idanu tafin hannunsa manya manya kamar mahuci da karan taba abakinsa yana sanye da Koren wando da farar riga
SALMAN NE
Annoba tazo kano.
Adaidai lokacin da salman yazo kofar da zata fitar dashi daga filin jirgin saman sai ya hangi wata bakar LEDUS. Acikinta akwai wani mutum fari kakkaura mai katon wuya yarinyar dake gaban motar Laila ce. Salman bai bata lokaci saiya tsaida dan kabu kabu yace dashi Yi ta bin motar can duk inda tayi kabita. Dan kabu kabun ya tada babur dinsa sannan ya rufawa motar baya.
Basu dade ba sai sukaga motar ta nufi wani katon gida mai dauke da shuke shuken bishiyoyi, adan dan kabu kabun yabar salman wanda ke labe acikin fulawowin dake gidan cike da mamakin ganin laila da wani wanda yake tsammanin mahaifinta ne agaban jirgi mai saukar ungulu.
Tun lokacin da laila tace zata bashi dubu hamsin salman yake tunanin lallai laila ta hada wani hadadden dil ne. Inda kuma salman ya rantsewa kansa cewa sai ya gano ko menene.
Har su laila suka fito suka bar gidan Salman na labe yana kallon jirgin mai saukar ungulu bayan daya tabbatar sun fice sai ya zagaya ta baya inda ya tabbata maigadin bazai ganshi ba ya haura ya fada cikin gidan cikin sanda salman ya nufi inda jirgin mai saukar ungulun yake.
Salman ya dubi jirgin da kyau sai yaga ashe ma bashida wuyar tasho. Murmushin mugunta ya bayyana a mummunar fuskarsa.
Ko me laila ke shirinyi to wani ya rigata bari naga iya gudun ruwanta da kokarinta kafin na fara nawa.
.
Abinda laila bata sani ba shine Salman da shine shugaban masu safarar miyagun kwayoyin daga sararin samaniyar kamaru zuwa najerya. Tayin amfani da jirgi mai saukar ungulu.
** ** **
Katon falon ya cika da samari da yan mata anata shagalin bikin zagayowar shekarar da aka haifi Abida, mansur na kwance a sabon dakin da aka bashi agidansu abida yana sauraron hayaniyar mutane lokaci lokaci abida takan shigo da kawayenta suyi masa sannu sukumayi masa gaisuwar iyayensa.ME YAFI KUDI ? - 09
.
Lokaci-lokaci abida takan shigo da kawayenta suyi masa sannu su kuma yi masa gaisuwar iyayensa daya rasa.
.
Daya daga cikin bakin da suka taya abida murna akwai LAILA BALARABE wacce tazo yiwa babar abida gaisuwa takuma amsa gayyatar fatin da akayi mata.
Bayan wasu yan awowi fatin yazama tarihi kowa yakama gabansa sai laila da abida ne suka rage suna hira. Abida ta dubi laila tace zo muje ku gaisa da yayana.
Dama kinada yaya namiji? Laila ta tambaya sannan abida tace da ita ai dan kanwar babarmu ce data rasu wallahi laila ina tausayinsa yanzu ace mutum ya rasa iyayensa lokaci guda kuma gidansu ya kone abin saikace hau. Ni wallahi abin har tsoro ma yabani laila ta girgida kai cikin tausayi. Sannan tace zo muje to na dubo shi.
Abida tashige gaba laila na binta abaya har suka isa dakin. Abida ta tura kofar suka shiga dakin. Mansur na kwance akan gado ya kwantar da karyayyaen hannunsa akan filo daya hannun kuma yana rike da jarida yana karatu. Sallamar da abida sukayi da ita ta dauki hankalin mansur daga kan abin da yake karantawa. Sai bayan da abida ta shigo cikin dakin sosai sannan mansur ya lura ashe su biyu ne. Yarinyar da mansur ya gani yar sirirya ce amma ba can ba tafi Badura tsawo da kadan kyakkyawa ce kamar Abida tana sanye da bakaken kaya na boyel.
Dakin yayi shiru sannan abida tace da shi mansur wata babbar kawata ce na kawo ku gaisa.
Mansur ya jiyo kansa suka yi ido hudu da laila wacce keyi masa murmushi amma fa kyakkyawa ne laila tace cikin zuciyarta sannan tace dashi sannu mansur yaya jikin naka yaya kuma akaji da karin hakuri?
Mungodewa Allah mansur yace muryarsa na rawa gumi ya karyo masa tsigar jikinsa ta tashi nan da nan ya yunkuta ya mike zaune su kansu su abida saida suka ga sabon canjin daya bayya a fuskarsa mansur yafara tunanin sassanyar muryar dayaji ta cikin talfon.
Alhaji Abubakar ne?
A'a bashi bane.
To kace masa yayi ya.........
Hanyar wayar ta katse. Irin wannan tunani shiyasa mansur tunanin cewa duk da yake ta wayar talfon yaji maganar hakan bai hana zuciyarsa wasuwasin cewa muryar yarinyar dake gabansa tayi kama da ta yarinyar datayiwa mahaifinsa talfon awa daya kafin a turo shi daga kan benen.
.
Sassanyar muryar ta sake ratsa shirun dake dakin. Allah sauwake mansur laila tace ni zan tafi sai gobe in sha Allah zan dawo na duba ka. Sannan sai murmushi ya bayyana a kyakkyawan labbanta gaban mansur ya fadi daya tuna da cewa irin murmushin da laila keyi masa ahalin yanzu iri daya ne da wanda abida tayi masa a asibiti lokacin da take kokarin nuna soyayya agare shi in dai har laila tana nufin abinda abida ke nufi to lallai al'amura sun zama abinda suka zama kenan domin zuciyarsa ta kara tabbatar masa cewa wannan yarinyar dake gabansa itace yarinyar data bugawa mahaifinsa waya.
Sai anjima laila tace da mansur haryanzu tattausan murmushinta na bayyane a lebbanta. Laila ta wuce gaba abida nabinta abaya. Bayan yan mituna da fitarsu sai kofar dakin mansur ta sake budewa abida ta shigo ciki fuskarta a turbune. Mansur ya dubeta sannan yace menene kuma ya sameki naga duk ranki yabaci? Abida bata ko kalle shi ba saita matso kusa dashi ta zauna abakin gadon kanta a sunkuye sannan tace dashi mansur kiran yayi matukar razana shi saboda kira ne me hade da sheshshekar kuka. Mansur ya dubeta yace haba kanwata. Abida yanzu ko wani abune ya sameki ai bai kamata ki boye min ba kuma.........
Ni ba kanwarka bace abida ta katse shi to mecece in ba kanwata ba?
Mansur ya tambayeta. Abida ta kalle shi kallo ne mai tattare da bege da nuna kauna sannan tayi murmushi kallo daya mansur yayiwa fararen idanunta ya gane abinda take nufi.
Sukayi shiru na yan dakiku sannan abida tace mansur amatsayina na kanwarka don ka kirani masoyiyarka akwai laifi aciki? Mansur yace a'a ina fa. Ai dole mutum yaso kanwarsa abida tace to daga yau ka rinka kirana masoyiyarka sannan tace abu daya kuma in laila tazo gobe zance baka nan. Meyasa? Mansur ya tambaya. Kallon da takeyi maka ne ban yarda dashi ba. Abida ta amsa.
** ** **
Acan kuma daya daga cikin manyan dakunan saukar baki na Tahir Gues palace laila na zaune acikin daya daga cikin kujerun dake fuskantar tagar dakin acan kuma kujerun dake jikin bangon dakin kusa da inda tagar dakin take Bazuka na zaune sanye da bakaken kaya na leda kunnuwansa a tsaitsaye farankau farankau kamar alamar tambaya (?) yana sakatar hakoransa da tsinke akusa dashi kuma a zaune manyan tafukan hannunsa masu kama da faranti akan cinyarsa Salman ne sanye da kayansa na kure akwati koren wando da farar riga zungureren karan sigarin kwarori abakinsa na turiri sararin samaniyar dakin ya hada gajimaren hayakin sigarin da salman ke zuka yana fesarwa.
Da misalin karfe biyun dare na yau zasu isa maradi laila tace dashi. Don haka nake son ku bi jirgin da zai tashi hudun yammacin yau ku riga su zuwa. Salman ya zare karan sigarin dake bakinsa sannan ya dago kai yace.
Laila idan kuma basuzo karfe biyun ba yaya zamuyi?
Laila ta dubi salman sannan tace dashi
haba yaya salman ai kasan bazan fada ma abu da ka ba yau kwana uku kenan kullum saina saurari baba suna magana da mutanen ta wayar talfon. Sunan mutumin ALHAJI BATALA MARADI abin kawai da zakuyi shine kuje cikin dajin ku labe zaku gansu sunzo cikin sababbin fijo uku kuma kamar yadda naji baba na fadi acikin dajin zasu boye motocin ta hanyar rufe su da ganyen bishiyoyi kamar yadda aka tsara zasu karasa cikin garin maradi a kasa idan sunje zasu nemi gidan Aliyu batala shine wanda baba ya ajje kwalayen tabar agidan kuma zatona kwalayen tabar zasukai dari biyar saboda motoci uku ne naji baba nacewa zasu tafi kuna ganewa aiba wanin nawa laila ta tambaya.
Bazuka da salman suka gyada kai sannan laila taci gaba da cewa idan kunje kun buya suna zuwa kai salman aikin ka ne ka tashe su daga aiki amma kayi ahankali kar ka kashe su saiku lalube aljihunsu aciki zaku tsinci takardun shaidar da alhaji yabasu saiku tafi dasu ku kaiwa Aliyu batala.
.
Laila ta danyi shiru sannan ta kalli bazuka tace nan kuma saura aikin ka ne inason ka fitar da tabar daga jamhuriyar nijar ka kuma kawota nan najeriya. Kana zuwa ka wuce sabon gari ka nemi rumfar alhaji sama'ila taba nan ne zaku ajje min ita kuna ajjewa to kunci kudin ku dubu hamsin hamsin ku same ni anan gobe karfe biyar na yamma zan sallame ku sannan laila ta mike tsaye Allah bada sa'a tace dasu. Kafin salman ya tuno wata tambayar har tabar dakin.
Abinda babu wanda yasani daga cikinsu shine kwalayen nan da laila ta aike su su dauko amatsayin sigari to ba taba bace dalar amurka ce yar jabu amma irin wacce babu wanda ya isa ya gane jabunce. Tun daga kasar iran alhaji balarabe yayiwa fasakwarinta yakawota maradi jamhuriyar nijar. Ita kanta laila batasan kudine aciki ba ita wai a zaton ta in ta saida wannan taba ta mahaifinta takuma sace jakar kudin dake boye a kasan kujerar nan dake dakin to ta karya lagon arzikinsa duk da haka laila tayi canke acikin duhu ta kumayi babbar illa batareda tasani ba shin da salman yasan cewa kudi ne acikin kwalayen nan me zakae zaton zai faru ?
.
.
BABI NA SHIDA 6
Mansir na zaune akan gadon dayake jinyar hannunsa sai yaji ana kwankwasa kofa kafin yayi magana kuma saiyaji ance Salamun Alaikum kofar dakin ta bude wani magidancin mutum yashigo sanye da doguwar riga fara kansa babu hula akafarsa kuma yana sanye da takalmi dan madina agashin kansa kuma akwai jefi jefin furfura nan da can.
Nan da nan mansur ya sauko daga kan gadon ya durkusa yace baba ina kwana?
Mutumin ya amsa lafiya lau mansur yaya aka karaji da hakuri? Allah yabaka hakuri kaji. Mansur wannan ka dauke shi amatsayin jarrabawa daga ubangiji duk abinda Allah ya kadda haka zai faru wallahi jiya ko barci banyi ba don tausaya ma da nake kasan jiya na dawo daga fakistan harkar ciniki ina zuwa na sami wannan mummunan labari.
Wannnan mutum dakeyiwa mansur jajen rasuwar mahaifansa ba wani bane illa baban abida sunansa Alhaji Sama'ila kuma sana'arsa itace saida taba akasuwar sabon garin kano akwai jita jirar dake cewa duk kasuwar sabon gari babu dilan taba kamar sa. Wannan mutum shine wanda laila tace akai masa tabar idan sun dauko.
Yan mituna kadan bayan baban abida alhaji sama'ila sun gama gaisawa da mansur sai ya shirya yafita kasuwa harkar ciniki. Yana zuwa ya taradda rumfarsa ta cika makil da yaransa anata harkar ciniki ko da suka kyalla ido suka hango shi sai suka dau sowa suna zuwa suna gaisuwa gama gaishe gaishen keda wuya sai karar talfon din dake dakin ya ratsa katon shagon dake cike da kwalayen taba. Alhaji isma'il ya matsa kusa ya dau wayar sannan yace Hello wanene?
Nice laila aka amsa masa.
Ah to laila ce.
Eh nice baba ina kwana?
Lafiya.
Baba daman wasu katan din taba ne nake son na tambaye ka inzaka saya.
Alhaji isma'il yayi shiru yana tunani wannan yarinya ina ta samu taba? Ya tambayi kansa can dai ya nisa sannan yace da laila guda nawa ne? Sun kai dariya uku zuwa hudu indai zaka saua to zan kawo su gobe wajen karfe hudu.
Saboda sanin da alhaji isma'il yayiwa baban laila wato alhaji balarabe amatsayin biloniya sai ya kawar da tunanin da zuciyarsa ke raya masa na sayen taba daga gurin laila domin yasan yadda alhaji balarabe ya tara dukiya to laila na iya mallakar abinda yafi katan din taba dubu ma. Kuma dadin dadawa ma ai alhaji balarabe bashida wata yarinya sai laila don haka babu mamaki don laila tafara harkar kasuwanci.
Na yarda zan saya. Alhaji isma'il yace da laila idan an kawo goben zanbada kudin atake anan. Laila tace a'a kabari zan karbi kudin da kaina sannan alhaji isma'il ya ajje wayar.
.
Alokaci guda kuma alhaji balarabe nacan nayiwa wani babban abokin harkarsa waya shi wannan aboki na alhaji balarabe sunansa Alhaji Ahmad yana daya daga cikin manya manyan yan canjin kudi dake legas sun dade suna harka da alhaji balarabe shekara goma sha biyar da suka wuce tun laila tana yar shekara daya. A ka'ida duk karshen shekaME YAFI KUDI ? - 10
.
Sun dade suna harka da alhaji balarabe. Shekara goma sha biyar da suka wuce tun laila tana yar shekara daya. A ka'ida duk karshen shekara sai alhaji balarabe ya yiwo fasakwaurin yar jabun dalar amurka daga iran zuwa najeriya shi kuma alhaji ahmad shine mai batar da ita a lagos.
.
To awannan yammacin sai alhaji balarabe ya buga masa waya. Mutumina alhaji balarabe yace dashi cikin wayar talfon din ka shirya gobe warhaka dalar amurka ta cika dakin ka har saman dakin.
Kai mutumina banda karfi fa? Alhaji ahmad kenan acan daya bangaren dake legas.
Allah ba zancen wasa ba kaidai ka shirya wallahi duk dukiyata na tattara na saro dalar amurkan da ita kudina da suke ciki sun kai naira billiyan goma sha biyar saboda haka kayi ahankali karkayi wasa da dukiyata idan kuma ka sake kayi wasa da ita to kamar kana wasa da rayuwarka ne. Alhaji balarabe ya gargade shi.
** ** **
Taurari masu hasken gaske sun yiwa sararin samaniya kawanya sun kuma kawata ta babu alamar gajimare asararin samaniyar saidai tsabagen sanyin da ake kwararawa kamar jaura zata wuce.
In ka dauke dan zagayen dasu Bazuka da salman ke boye duk sararin dajin babu wata bishiyar kirki sai tarin yashi nan da can. Wannan ba wani bakwan abu bane sau dayawa ko daman akan sami karancin bishiyoyi da kuma matsanancin sanyi awaje mai sahara kamar jamhuriyar nijar.
Salman ya kunna karan sigarinsa na goma sha shida a ranar cikin hasken ashanar da salman ya kunna sai bazuka ya kula da agogonsa karfe biyu saura minti biyar na dare tun suka iso dajin babu wanda yace da wani uffan tun karfe takwas na dare suka iso nijar suna zuwa suka shiga motar da zataje wata kauye anan kusa da inda suke boye bayan motar ta sauke su sai suka sayi dan abincin da zasuci suka nufi cikin dajin. Salman ya sayi kwalin taba daya amma daya duba kwalin yanzu saura guda hudu duk dayake bazuka direban simogal din taba ne amma shi allah baisa yana sha ba.
Bayan mintuna takwas sai suka hango hasken fitilun motoci ya haskaken dajin nan da nan salman da bazuka suka dare kan bishiyoyin da suke karkashinsu basufi minti daya da hawa ba motocin da laila ta siffanta musu suka ja birki awajen Arangama ne yafara fitowa sannan sauran direbobin suka fito yan sirara ne bakake masu fuskar matsorata.
Anan zamu boye su arangama yace dasu sannan yace da dayan dauko min addar nan. Direban yakoma cikin motarsa ya zaro wata sharbebiyar adda.
Arangama ya karbi addar yafara saro ganyen bishiyoyin dake zagayen wajen dan lokaci kankani saigashi yatara tulin ganyayyaki. Direbobin suka sake shiga sannan suka matso dasu cikin lungun bishiyoyin sannan suka fita suka fara daukar ganyayyakin da arangama ya

Please Login or Register in order to submit comment