Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an kwana bakwai bata zo ba tun a kwana na hudu hankalin Sunusi yafara tashi kwana na biyar ya kasa barci kwana na shida cin abinci ya fara gagararsa kwana na bakwai yafara ramewa kowacce sa'a cikin zulumi
Shin batada lafiya ne ko wani hadarinne ya same ta ko.... Kuma mahaifinta ne ya hanata fita... Kokuwa.... Gumi ya karyo masa kamar ruwa a zaune yake shi kadai acikin daki yana son ya tashi ya tafi gidansu aziza ya duba amma fargaba ta hana shi.

MAHAIFINA NE BAYA SON GANINA DA SAMARI... kalaman ta suka fado masa ya kwanta domin ya dan runtsa amma abin ya gagara domin ji yake yi kamar ana tsikara masa allura azuciya nan da nan ya Mike dole ne naje gidan kome ta fanjama fanjam yace da kansa.

Karfe takwas da rabi ya isa unguwar TARAUNI.
Tangamemiyar kofar babu kowa sai wata akuya da ya'yan ta guda uku kwance karkashin wani teburi na katako me yiwuwa na maigadin ne Sunusi yace acikin zuciyarsa yanufi kofar gidan zuciyar sa kamar zata tsage ga mamakin sa saiyaji hawaye na neman subucewa daga idanunsa tsananin kauna da begenta suka dada mamaye zuciyar sa hakanan faduwar da gabansa yakeyi shi yafi damunsa domin yasan indai lafiya lau....babu abunda zai hana aziza zuwa gurinsa har sati guda.

Hakanan gabansa na faduwa ya kwankwasa Tangamemiyar kofar batareda shi kansa yasan me zaice ba idan wani ya fito.

Kwankwasawarsa keda wuya sai kofar ta dan bude wani mai gadi dogo fari siriri mai fuskar matsorata da lankwasashshen hanci kamar na aku ya leko sunusi ya dube shi ya kasa cewa da shi komai dogon mai gadin ya dubi Sunusi sama da kasa sannan yace cikin wata siririyar murya.
Kai...ne.... Sunuzi...?
Eh Sunusi. Sunusi ya gyara masa sunan cikin mamaki zuciyarsa na bugawa.

Maigadin ya turo dogon hannunsa ta cikin kofar batareda ya fito da gangar jikinsa gaba daya ba ya mikawa Sunusi wata yar takarda.
Hajiya..... Aziza ce tace idan kazo abaka yana fada saiya turo kofar garam afuskar Sunusi ya rufe.

Sunusi ya dubi yar guntuwar takardar cikin fargaba sannan saiya matsa kusa da hasken wutar sosai yafara karantawa dakyar-dakyar domin ko karatun hausar ma ba sosai ya iya ba.

***MASOYINA SUNUSI***
Da fatan zaka yafeni domin ba laifina bane laifin ka ne domin yana da kyau in zaki dauki kaya ka dauki daidai wuyanka kada ka dauki mai yawa ya karya maka wuya baki daya.
Sunusi duk abinda nakeyima ina bin umarnin mijina ne domin nayi amfani da damar na dan taimaka maka na kuma sha dariya domin Wallahi wani lokacin idan na dube ka na tuna wai kai har soyayya kake yi dani sai in bingire ni kadai a dakina inyi ta dariya.....
Sunusi Wallahi... Ka dan burge ni kuma yau da kullum da nake zaune dakai saida Naji INA DAN KAUNAR KA. To amma har yanzu kana bukatar ka iya diresin, ka kuma karo karatu ka kuma iya magana.
Inafatan zaka manta dani ka koma makaranta ka karo ilmi domin haryanzu kai a kwakwalwa dan yaro ne ƙarami a jiki ne kawai kake babba.
GOBE DAURIN AURENA.
AZIZA-06

Inafatan zaka manta dani ka koma makaranta ka karo ilmi domin haryanzu kai a kwakwalwa dan yaro ne ƙarami a jiki ne kawai kake babba.
GOBE DAURIN AURE NA.

DAGA AZIZA....

Saida Allah yakawo yan kato da gora suna rangadin unguwa suka tsinci Sunusi da asuba a kofar gidan kwance a sume takardar ahannunsa.

Sunusi yayi ajiyar zuciya cikin duhun daren wannan duk wani abu ne da yafaru tun tsawon shekara uku da suka wuce to amma labarin daya samu na mutuwar auren aziza ya warware komai yadawo kuma da dukkan abubuwan da suka faru tsakaninsa da aziza garai-garai acikin zuciyarsa kamar yanzun nan abun yafaru.

Acikin shekaru ukun da suka wuce duk rayuwar sa ta lalace Yakama shaye shaye yan uwansa duk suka kyamace shi suka ma fara jin tsoron sa ya daina kula mata sai Samira da kullum ke ta naci amma abanza wannan ita tasa duk abubuwa sukayi masa zafi ya hada yan kayansa bayan yayi yan buga bugarsa yake son tafiya soja domin ranar da ya tabbata ya rasa aziza sai yaji bai ki ma ya mutu ba to shi dai bai iya kashe kansa to amma hanyar da tafi kusa da mutuwa itace Soja.

Sunusi ya sake lalubar jakar daya zuba duk kayansa aciki ya zuge jakar sannan yafara fito da kayayyakin dake ciki.

A daidai lokacin ne to dakin ya gauraye da haske Sunusi ya dago kai zai fara masifa sai yayi ido biyu da Samira
Tsawon lokaci suna duban juna sannan sannu ahankali sai idanun Samira suka kai ga inda jakar take tayi mamaki sa'ar da taga Sunusi yafara fitar da kayan daga cikin jakar.

Samira.... Ke bakida zuciya ne dan Allah? Na roke ki da ki hakura bana son kullum kiyi ta naci ina muzanta ki ni nafada miki ba tun yanzu ba.... Bazan iya son wata ya'mace ba in ba aziza ba.

Hawaye na zuba a kumatunta ta dube shi tace.
Kullum ina addu'a inafatan Allah ya sauya wannan ra'ayi naka....Kasan Nima na sha fada maka cewa bazan taba iya son wani da' namiji ba in ba kai ba inda zan so ai da tuni nayi aure... Haba ka tuna fa yau shekara uku kenan ina bin ka abaya... Abaya amma kaki tausaya min kuma.... Zuciyarta ta karaya tafara kuka tsawon lokaci ta dago kai ta dube shi tace.
Yanzu gobe zaka tafi sojan? Ga mamakinta sai taga ya girgiza kai.
Nafasa tafiya Samira. Wani digon farin ciki yayi sartu cikin zuciyarta domin ta dauka kukan da tayi ne ya karya zuciyarsa zai fasa tafiyar.

Meyasa kafasa? Samira ta tambaye shi Sunusi ya Mike tsaye ya matsa daf da ita yace saboda wacce zan tafi sojan domin Rashinta
AUREN TA YA MUTU gurin ta zan koma Samira ki gafarce ni domin acikin wasikarta tace TANA SONA
DON NA TABBATA AZIZA NI ZATA AURA YANZU

BABI NA BIYU 2

JIHAR ZARIYA

RANAR LITININ JANAIRU 4 GA WATA
KARFE 12:00PM NA DARE

Kada ka motsa tattausan muryar matar tace dashi a tsorace ta cikin duhun..
Kamar motsi nakeji acikin falo matar ta sake cewa mutumin ya dubi matar wacce ke kwance tsirara akan gadon kusa dashi numfashinta sama sama saboda tsabar kaduwa da motsin da taji.
Motsi kika ce fa... Bakya tsammanin ko kyanw....
Ni bama kiwon kyanwa agidan nan rufa min asiri mijina baya son kyanwa... Matar ta katse shi.
Tsawon lokaci suna kwance lamo akan gadon basa ko motsi suna sauraro shiru shiru basu sake jin motsin komai ba sai wur wur din na'urar sanyaya dakin dake yiwa shirun ado.
Ina tsammanin kunnuwanki ne suke jiye miki karya...
Mutumin yace gamida ajiyar zuciya me yiwa shi baisan da hakan ba amma ita matar dake kwance kusa dashi tsirara taji jikinsa yana rawa kamar mazari hakanan kuma yafara gumi daga inda take kwance tana iya hango shacin katon hoton mijinta DAKTA ALI wanda ke makale ajikin bangon dakin.

Ta godewa duhun dake dakin domin da'ace akwai haske bata tsammanin zata iya hada idanu da hoton.
Lallai kam ni Naji motsi matar ta sake maimaita bayanin ta na farko mutumin ya dubi kyakykyawar fuskar matar ta cikin duhun daren yace.
To wa kike tsammanin zai shigo dakin ayanzu...
Wajen sha biyun dare kuma fa kince dani maigidanki na gurin aiki yau can zai kwana to wanene?

Ni ma abinda kenan nake tambayar kaina kuma nasan masu aikin gidan nan dai tun tara na dare nake sallamar su masu gadi kuwa duk saboda kai na sa ya sallame su... Tayi shiru bata karasa ba sakamakon kwakkwaran motsin data sake ji a falon matar ta rike numfashinta... Na...Shiga uku tace cikin rada.
Mutumin dake kusa da ita ma yaji motsin yi maza ki lalubo min kayana idan nasa saiki kunna wuta ina iya cewa dashi wata matsala ce ta dole ta dawo dani saboda satin daya wuce da muka zo nan tare dashi mun fara zancen kafa sabon asibiti awani kauye dake Jos..

Matar bata ko sauraren shirmen dayake fadi ba abinda take kallo ya isa yasa koda shi dake surutun yayi shiru.

Daga inda take kwance ta cikin duhun daren tana iya hangen kofar dakin tana budewa ahankali.
Uhm Uhm yau asiri ya tonu mutumin yace muryarsa kasa-kasa kuma tana rawa matar dake kwance kusa dashi ta zunguri katon tumbinsa.

Kada ka motsa... Yi shiru kawai kofar dakin ta bude sannu ahankali dogon mutumin ya shigo dakin duk da cewa bata iya ganin fuskarsa ta tabbata mai gidanta ne.

Kada ka kunna min kwan wuta in zaka shigo shigo kawai bana son haske shiru na dan lokaci sannan sai akace daga cikin duhun.
Ashe idanun ki biyu ai da ni na dauka tuni kinyi barci DARLING BALARABA Shiyasa na shigo cikin sanda dan bana son na tashe ki wani abu na manta inafatan zakiyi min afuwa na kunna wutar.
Akwai alamar murmushi a muryarsa wanda acikin dakikar abinda ke faruwa matar tasa ta gane cewa lallai baisan da mutum acikin dakin ba to amma ta makara. Dakin ya gauraye da haske.

Shida matarsa Balaraba suka fara hada idanu tayi sauri ta dauke fuskarta jikinta na bari acikin mayafin da suke lullube sannan kuma sai suka hada idanu da KWARTON matarsa. Dakta Ali yayi tsaye nan sororo hannunsa haryanzu akan makunnan kwan lantarkin yana kallon su kwance irin kallon daya saba yiwa dubban marasa lafiyar dake kwanciya a asibitinsa.
Idan har al'amarin yabashi mamaki ko sa shi kaduwa to bai nuna hakan a fuskar sa ba.

Sai yace Oh.. Da Allah kuyi hakuri wallahi bansan hutawa kuke yi ba shiyasa na kunna wutar (I'm sorry please)
Dakta Ali yace harda murmushi kai kace wanda yayi idanu biyu da wani muhimmin abu mai dauke kewa yasake duban katon kwarton dake kwance akusa da abar kaunarsa Balaraba sai alamun mamaki suka bayyana a fuskarsa.

A'a wannan kamar abokina ALHAJI ISAH... ikon Allah Daman inason ganin ka sai ga ka kuma mun hadu a banza. Akaro na farko tun sa'ar da dakin ya gauraye da haske sai kwarton yace.....
Kayi hakuri don Allah.....Wal.... Wallahi tsautsayi ne.
Dakta Ali yasa alamar mamaki a fuskarsa.
A'a ahh menene kuma na ban hakurin laifin me kayi min? Dan kawai mutum ya tafi aiki abokinsa yazo taya matarsa kwana sai abun yazama laifi?
Ai AMINCIN kenan wannan shi ya tabbatar min da cewa lallai koda mutuwa nayi zaka iya rike min mata ta.

Nidai dan Allah..... Dakta ya daga masa hannu yace..
Menene kuma na daga murya ko so kake kowa yaji wannan abu? Wannan abu fa daga ni sai kai sai ita babu wanda yasani dan haka abunda nake so dakai shine ka tashi bakin ka Alaikun ka shiga bandaki kayi wanka.

Yabaro inda yake tsaye sannan ya kwashe kayan alhaji Isah dake zube a tsakar dakin ya makale su a hammatarsa sannan ya nufi kujera ya zauna.
Tashi kaje kayi wanka kekuma tashi ki leka dakin girke-girke ki samo min dan abunda zanci kafin yafito daga wankan Naji cikina kamar kara yake.

Shiru babu wanda ya motsa.
Kunga dan Allah kada ku bata min lokaci sauri nake zan koma gurin aiki in kuma so kuke na tona asirin to kuci gaba da kwanciyar nan... Waya kawai zan bugawa ofishin yan sanda.....

Alhaji Isah ya Mike zaune sannan ya janye mayafin ya sauko daga kan gadon tiɓi tiɓi kwaryar cikinsa kamar kullin gwanjo daga shi sai gajeren wando jikinsa na rawa kamar kafafunsa bazasu iya daukar sa ba.
Muje na rakaka ban dakin yana nan kusa.

Cikin Yan dakiku ya tura shi cikin bandakin sannan yasa makullin kuba ta baya ya rufe shi aciki yace idan ka gama wankan saika kwankwasa kofar nazo na bude ka saikuma ka hanzarta domin nasa ta shirya mana abinci Dakta Ali yace saidai kuma ashe kashhhhhhh.....AZIZA-07

Aliyu ya koma cikin dakin. Matarsa Balaraba na tsaye a tsakar dakin, mayafinsu lullube da jikinta idanunta sharkaf da hawaye.

"Dan...Allah.. ka yafeni, daga yau ba zan sake yi ba..." Ta fara kuka.

Dakta Ali ya sake komawa kan kujerar ya zauna jagaf kanta, ga mamakinsa sai yaji duk gabobinsa sun gaji kamar wanda aka yiwa duka, domin zuciyarsa ta gama konewa.

Idan ka dubeshi a fuska babu abin da ya dameshi, amma zuciyarsa a badini kamar murhum makera take tuni ya daina jin sautin komai dake dakin, hatta shashshekar kukan matarsa, da rokon da take yi duk ba jinsu yake yi ba, domin ta gama karya zuciyarsa, ta karya katangar karfen da ya sha wuya kafin ya ginawa zuciyarsa, katangar da ta kare kaunar wacce yafi kauna fiye da kowacce mace a fadin duniya, wanda in da ba dan katangar nan ba da ya gina, to da ba zai ma taɓa kaunar Balaraba ko da dai dana dadika daya ba.

Lokacin da ya fara kaunar Balaraba, yayi farin ciki, duk da yake dai daman ba wani jin dadin auren sa da Balaraba yake yi ba, domin sai abin da taga dama ta ke yi, to amma dai a kalla kaunar ta da yake yi, ta taimakawa zuciyarsa, ta tserar dashi daga halakar da yawan tunani kan jefa dan Adam, don in ta mantar da shi Tunanin mace daya a duniya da bai taɓa zaton zai iya daina tunani ko daina kauna ba, wacce in da ba dan katangar nan ba da ya gindaya tsakanin kaunarta da kaunar Balaraba, da tuni tunaninta ya je fa shi a uku, domin yana iya yin sanadiyyar barinsa likita, aikin da yasha wuya shekara da shekaru kafin ya gina kansa akai.

Dan haka koda ya zauna a yanzu ya lumshe idanunsa, kayan kwarton makale a hammatarsa, sai ya ji katangar nan tana rushewa kadan-kadan a cikin zuciyarsa, sannu a hankali sai tekun kaunar matar nan ya sake kwararowa cikin zuciyarsa, wanda 'yan sa'o'i kadan da suka wuce katangar ba ta barinsa ya kwaranya. Dakta Ali, ya fara tunanin, tabbas, duk da abin da tayi masa, yayi imanin cewa abu ne mai wuya in har da ya aureta, in za ta iya kawo masa kwarto cikin gida. Har yanzun nan bai taɓa yarda da cewa wai son sa ne ba ta yi shi yasa taki aurensa ba, kaddarace kawai ta rabasu da ita. Dakta Ali ya dada gyara zama, gami da dada lumshe idanunsa, sannan zuciyarsa ta koma, can wani zamani, a wani lokaci, a kuma wani wuri da ya dade da bari, tun- tun-tuntuni, tun kusan shekaru takwas da suka shude.

Idan ba tsautsayi ba, me zai dauki mutumen dake zariya, bayan gashi ga jami'ar Ahmadu Bello, ya mai da shi Kano jami'ar Bayero? Wannan ita ce tambayar da a kullum Dakta Ali yake yiwa kansa. Abin ya fara ne a jami'ar bayaro tun kusan shekaru takwas da suka wuce a lokacin yana shekararsa ta karshe a makarantar. Yadda abin ya faru kuwa shine shigowa makarantar ya yi da sassafe domin ya sami damar baiwa wani Malami wasu takardu da yake son asa masa hannu. Daga wannan shekarar ya kammala karatunsa kenan.

Lokacin da yayi fakin da motarsa Hajiya ba duwawu a karkashin wata bishiya dake farfajiyar makarantar, ya yi mamakin ganin tuni har dalibai sababbin dauka sun cika makaranta. Duk inda ka hanga suke ta bulbulowa kowannensu rike da babbar ambulan launin kasa-kasa, wacce mafi yawanci takardun kammala karatunsu na sakandire ne a ciki.

Dakta Ali ya dubi agogonsa, sannan yayi murmushi sa'ar da yaga kusan du sababbin daliban dake shigowa sai sun yi tambayar inda za su. Gashi tun takwas na safe har sun hallara.

"Za su gaji su daina, domin doki kawai suke kafin su gaji" Dakta Ali yace da kansa yana murmushi sa'ar da ya bude kofa motar ya fito sannan ya rufe. Ya juya kenan zai tafi sai ya ji motsi a bayansa.

"Salamu Alaikum...." Wata zazzakar murya ta yi masa sallama. Tun kafin ya gama juyawa tayi sallamar hakanan kuma tun kafin yaga mai sallamar Dakta Ali ya yi imanin cewa ko wacece mai muryan nan ba zata taɓa zama mummuna ba. Ya juya a hankali sannan ya yi ido biyu da ita tana haskake shi da murmushi wannan shine farkon afkuwar tsautsayin.

"Ameen wa'alaikumussalam". Aliyu ya amsa yana dan in ina.

"Yar budurwar dake tsaye gabansa bai ko taba tsammanin a cikin bakaken fata na Najeriya za a iya samun kyakkyawa kamarta ba. Gashi dai, yau kusan shekarunsa shida kenan a makarantar nan in aka hada da matsalolin yajin aiki, amma tunda ya zo jami'ar Bayero bai taɓa ganin mace mai cikar halitta irin ta yarinyar da ke tsaye a gabansa ba

Dakta Ali ya sake kura mata idanu yana kokarin ganin makusa, amma abin ya gagara. Tsarki ya tabbata ga Sarki gwanin dai-daita nama, kashi, jini da bargo. Dakta Ali yace cikin zuciyarsa sannan sai ya dubi ambulan din da ke hannunta

Ikon Allah, ashe sabuwar shiga ce ma", yace cikin zuciyarsa, sannan sai yace a fili yana mai yi mata murmushi.

Yammata sannu da zuwa, ko akwai abin da zan iya yi miki?"

Budurwar ta gyada kai, ta dada haske shi da murmushi tace. "Dan Allah "CHEMISTRY" aka bani zan karanta, to na karbi takardar daukan nawa, kuma gashi nazo... ban san... abin da ya kamata na yi ba... kuma ban san inda ya dace na je ba.." Tayi shiru tana dubansa da dara-daran fararan idanunta.

"Subhanallahi, in ta yi murmushi ma tafi kyau" yace cikin zuciyarsa.

"Ka da ki damu, zo mu je sai in kaiki duk in da ya kamata..." "Kai da na gode kuwa wallahi.." Tace dashi cikin murmushi.

"Bari to in je in sanar da direbana cewa ya jirani zan dan dade.." sai a lokacinne to Dakta Ali ya lura da falleliyar motar dake can gefe guda tana sheki. Daga inda yake tsaye yana iya hangen zungureriyar hular direban mai kamar shantu. Dakta Ali yayi mamakin abin da ya hana direban lankwasar da hular domin har taɓa saman motar hular take yi.

Ya bita da kallo sa'ar da ta nufi motar tana rausaya tamkar reshen bishiya a lokacin iskar damina. Dakta Ali ya dubi falleliyar motar sannan ya juyo ya dubi tasa motar mai kamar akurki, nan da nan sai yaji dariya ta kamashi, ada can ya dauka a mota yake tafiya, amma a yanzu ya fara tunanin lallai ba'a iya kiran motarsa da suna mota ba sai dai ko Amalanke.

"Sannu.. na dawo ko.. gashi zan saka wahala.." Tace dashi.

"A'a babu komai wallahi, ai farin cikina ne na taimakawa kyakkyawa kamarki.." yarinyar ta fashe da wata irin 'yar marayar dariya mai kamar sarewa..

Kusan sa'o'i biyu suka shafe suna yawace-yawace, daga wannan ofis zuwa wancan, bayan sun gama ne, Dakta Ali ya sake rakata har jikin motar da aka kawota lokacin da suka zo direban ya dade da ɓingirewa barci, doguwar hularsa ta fada bayan motar kamar shantu. "Ban san da irin kalmar da zan gode maka ba" yarinyar tace dashi tana dubansa, siraran 'yan yatsun hannunta akan madai-daicin bakinta. "Murmushinki ma kawai godiya ne a gareni" suka fashe da dariya gaba dayansu. Iskar dake busawa, taci gaba da busa sassanyar iska atsakaninsu, lokacin yana daya daga cikin lokutan da Dakta Ali ba zai taba mantawa ba har iya rayuwarsa. "Me kake karantawa ne kai?" Ta tambaye shi a kunyace.

"Likita ne"

"A'a, babbar magana, ashe ni da babana ma nake tsaye "Ina fatan dai in mun fara karatun za ake dan taimaka mana?" suka sake bushewa da dariya

"Jin dadi na ne na taimaka miki" Dakta Ali yace. "Gashi kuma har zan tafi ko sunanka ban sani ba..."

"Sunana Ali.... Abubakar" Yarinyar tayi dan murmushi, lokaci guda kuma ta bude bayan motar ta shiga sannan sai Ali ya dan rankwafa a jikin kofar motar yace "Yaushe zaki fara zuwa lakca" Ta dan yi tunani sannan tace. "Sai litinin mai zuwa" Dakta Ali ya sake tura kansa ta cikin kofar
motar yace da ita. "Kin san sunana, ni ban san naki ba, gashi kuma har mun kusan kaiwa sa'a biyu da sanin juna.

"Oh! Dan Allah ka yi hakuri wallahi sunan nawa ne na 'yan kauye ni kaina ba jin dadin fada sunan nake ba" Ta yi shiru tana dariya,

Sannan sai tace.

"SUNANA AZIZA"

Tun daga wannan rana ya zama bawanta, domin a kullum bashi da wani aiki da ya wuce na hidimar Aziza... koyamin wannan.. bangane wannan ba...wancan yaya yake..

Haka nan yayi ta fama da ita tun bata ganewa sosai, har dai Allah ya fara fahimtar da ita sannu a hankali dangantakarsu tabar kawance ta rikide izuwa soyayya, kusan ko yaushe suna tare, ba dare ba rana. Mahaifan Aziza sun yi mutukar yabawa da halin Dakta Ali,
domin mutum ne mai yawan abin kunya da mutunci da girmama magabata.

Shekara ta gushe, dakta Ali ya kammala karatunsa ya tafi bautawa kasa, amma duk da haka kusan kullum sai sun shafe kusan sa'o'i biyu suna hira.

Dukkan tunanin wata 'ya mace dake doron kasa, sai da Aziza ta kankare shi daga zuciyar Dakta Ali, ya zamanto ba shi da wani tunani sai nata. Idan zai kwanta bai iya barci, ba har sai......AZIZA-08

Dukkan tunanin wata 'ya mace dake doron kasa, sai da Aziza ta kankare shi daga zuciyar Dakta Ali, ya zamanto ba shi da wani tunani sai nata. Idan zai kwanta bai iya barci, har sai ya bijiro da tunanin kyakkyawar fuskarta ma'abociyar tattausan murmushi sannan yake iya yin barci, wani lokacin shi kadai sai kaga yana murmushi. Domin muryar Aziza yake ji tana yi masa wasa cikin raha Ya gama batawa Kasa lokacin Aziza tana aji biyu. Wata rana ya tambayeta cikin raha suna hira. "Aziza zaki ko iya aure na?" Ta haske shi da murmushi tace. "Haba Ali, sanin kanka ne duk duniya bani da wanda nake burin zama da shi har iya rayuwata da ya wuce kai, ka tuna fa da sunanka kawaye na ke kirana a makaranta, har wasun su na cewa da ni matar Dakta. Ta dan yi shiru tana kashe masa idanu.

"Kasa ranka a inuwa, in Allah yaso kaine maigidana Ta rufe idanu cikin kunya.

"Shekara biyu dai yanzu ya rage min, sai ka fara shiri domin aurena da shagali " suka fashe da dariya cikin farin ciki. Dakta Ali bai taba farin ciki irin na ranar ba, domin yana tunani in har ya rasa Aziza, to bai jin zai iya yin aure har abada.

To amma a gidan su Aziza mahaifiyarta ta taba tambayarta "Shin ko Dakta Aliyu...dinne zai zama sirikinnamu?" Aziza dubi mahaifiyarta ta fashe da dariya tace.

"Kin ji Momi, da wani irin zance, ai Dakta Ali mutunci ne kawai tsakanina da shi".

Sannu a hankali, kwanaki da watanni suka yi ta shudewa, har shekarar fitar Aziza daga makaranta ta zo, lokacin da aka yi bikin yaye dalibai a Jami'ar Bayero, Dakta Ali baya kasar ma baki daya yana kasar Rasha wani kwas da ya shafi aikinsa na likita, sai bayan shekara da kammala karatun Aziza Dakta Ali ya dawo a lokacin ma har ta gama bautawa kasa.

Ko wanka bai yi ba a yammacin ranar da ya sauka a gidansu da ke Zariya. abin da ake bukata na aure ya sayo shi tun daga can, dan haka da zuwansa sai ya bude manya-manyan akwatunan da ya sako kayan Aziza a ciki, yana nazarinsu, lokaci guda kuma yana ayyana irin yadda Aziza zata kara kyawu cikin kayan sanan sai yayi murmushi, ya dauki kan tarho. A zuciyarsa yana cewa bari in buga mata waya, in ji ko ta dawo, domin duk satin duniya sai ya bugo mata waya daga kasar rasha sun yi hira, to amma yau kusan wata guda kenan idan ya bugo baya samun hanya, can sai yaji an dauki kan tarho din a can daya bangaren.

"Halo..." muryar mahaifiyar Aziza ce Dakta Ali yayi ladab da muryarsa yace.

"Baba ina wuni?"

"Lafiya lau..." Aka dan yi shiru

"Baba nine Ali..."

"Lah Aliyu kaine, wallahi ban gane muryarka ba, yaya aiki, ina fatan dai kun kusa kammala kwas din naku ?" Ali ya ji zuciyarsa ta harba, farin ciki ya lullubeshi. Ni suke saurare na dawo yace cikin zuciyarsa.

"Ai har mun gama, yanzu ina nan Zariya daga can nake bugo wannan wayar". "Ah! Barkanku Aliyu Allah ya taimaka". Shiru a daya bangaren na dan lokaci. Can Aliyu sai yace. "In... Aziza din tana kusa, sai a bani ita mu gaisa.
shiru a can daya ɓangaren, kusan dakika talatin ba amsa. "Baba.... Kina nan?" Aliyu ya tambaya cikin mamaki.

"Ina..... nan Aliyu, mamaki nake yi, ai na dauka ta fada maka'

Gaban Aliyu ya fadi.

"Ta fadamin me?" Aliyu ya tambaya akwai alamar tsoro a muryarsa. Aka sake yin shiru a can bangaren, sannan sai muryar matar ta daki dodon kunnensa kamar sautin aradu.

"Ai yau Aziza watan ta daya A ƊAKIN MIJINTA....

Ni na..." Aliyu ya fadi sumamme.

Hakika al'amura da dama sun

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

5 months ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

4 months ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment