Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunan yarinyar AZIZA. Tun da aka haifi yarinyar har zuwa ranar da ta fara tafiya sau uku ubanta Alhaji Ibrahim ya taba daukarta, ba dan komai ba kuwa sai don ranar da aka haife ta, Alhaji Ibrahim ya dauketa yana tofa mata addu'o'i a fuska, uwar ta Kwaceta cikin fushi tana cewa.

"Bani ita kada ka ɓata min yarinyar da yawu a wofi, kai har wata addu'a ka iya? In gaskiya ne ka yiwa kanka mana, ko a rage maka wannan wangamemen bakin naka!"

Tun daga ranar bai sake kokarin daukar yar karamar yarinya Aziza ba, wani lokacin ko gurinsa Aziza ta tafi, sai matarsa Mariya ta yi sauri ta sure ta kamar wacce ta ke tsoron zata taba wuta.

Sannu a hankali har yarinya ta fara wayo, ba tare da ta saba da Ubanta ba, hakanan bata jin maganar kowa sai ta shaidaniyar uwarta. Wata rana suna karin kumallo da safe sai matarsa Mariya ta dube shi tace.
"Zan mai da Aziza Bauchi gurin 'yar uwata, a can nake son ta yi Sakandire, tun da dai tayi Firamare a nan". Alhaji Ibrahim ya dubeta a tsorace, domin ya gama tsorata da masifarta, shi yasa duk abin da tace masa sai yace TO.

"Ai ba To" kawai za ka ce dani tsohon matsolo, haka zaka bar yarinyar ta tafi, to bari in fada ma bata barin gidan nan sai ka bata naira miliyan guda". Idanun Alhaji Ibrahim suka zazzaro cikin kaduwa yana kallonta.

Yar karamar yarinya kamar wannan, me za ta yi da kudi har.... Mariya ta katse shi cikin Karaji
Kaga... Wallahi duk matsolancinka saika bayar domin yata' dole ta wala ta batar da duk abinda ranta ke so.... Kaidai ace tayi wayo sosai ma da sai ka saya mata mota.
Washegarin ranar tun da asussuba ta tashe shi ya rubuta mata cek din naira miliyan daya

Duk shekarun da suka gabata Alhaji Ibrahim bashi da cikakkiyar masaniya akan al'amuran yarsa. Abin kawai da ya sani shine bayan dawowarta daga Bauchi MARIYA ta yi masa masifa ya sayo mata sabuwar mota, haka nan kuma lokaci lokaci, ya kanga Samari iri-iri ana shiga da su cikin gidansa duk wai da sunan samarin Aziza ne, to amma akwai wani mummunan tunani da ke kai kawo cikin zuciyarsa, tabbas yana Tunanin a cikin samarin har da na matarsa MARIYA. To amma duk da haka bashi da ikon yin koda tambaya ballantana wani kakkausan furuci domin yin shirun shine samun lafiyarsa.
Alhaji Ibrahim bai san da Auran Aziza ba sai da ya rage sati biyu kacal sannan Mariya ta ce dashi.

Yata ta sami miji a Abuja, sai ka yi shirin aure, domin yau saura sati biyu".

"Sati biyu?" Alhaji Ibrahim ya tambayeta cikin kaduwa.
Tace Kwarai kuwa saura sati biyu, to me ye? Maganar kudi kuma kana dashi to ba shikenan ba".

Alhaji Ibrahim bai sake cewa komai ba har zuwa ranar daurin auran, amma duk da haka kullum ya kance a zuciyarsa

Ya tata, kudi namu... shin ni bani da kome kenan?"

Shekarun da suka biyo bayan auren Aziza sun zo wa Alhaji Ibrahim a bazata, domin yayi mamakin ganin sauyin da bai taba tsammani ba a tattare da matarsa. Na farko dai saboda rashin Aziza kusa da ita Alhaji Ibrahim yakan sami lokacin dan zama irin na aure shi da matarsa, hakanan kuma babu tarin tsinannun samarin da ke ta sintiri, wannan abu ya farantawa Alhaji Ibrahim rai, lokaci guda kuma yayi addu'ar Allah sa Aziza ta tafi kenan.

Dan haka mutuwar auren Aziza, shi ya warware dukkan dan sauran farin cikinsa, ya kuma dawo da jiya iyau..

Sati guda da ya shude bashi da kwanciyar hankali, kullum a masifa suke shi da Mariya. Duk dai ya jure, amma karfin hali yake. Tun shekaru kusan ashirin kenan yake fama da masifaffan ciwon wanda ada yasan kafin ya auri Mariya bai taba jin matsanancin ciwon yana tsikarar zuciyarsa ba. Ganin Aziza, a irin yadda take a yammacin ranar shi ya dada dawo masa da masifaffen ciwon a wannan karon ba tsikarar kirjin kawai yake ji ba, akwai wani sashe da yake ji kamar ana rura masa wuta.

Tunaninsa ya katse a dai-dai lokacin da matarsa MARIYA ta fado dakin shakatawar a fusace.
"Me nene ne kake damuna da kira haka kamar tsohon Makaho?

******* ********* ********* ********* **************

Tsahon lokaci yana duban matar dake tsaye a kansa kerere tana muzurai kamar zata haushi da duka.

"Zauna... mariya". Yace da ita muryarsa na rawa. Mariya ta dube shi shekeke, taso ta ki zama, to amma akwai wani abu a cikin kwayar idanunsa da ya gargadeta. Dan haka sai ta zauna.

KUMA KU SAMU GURI KU ZAUNA BARI NIMA NA NEMO IZNI DAGA GURIN TAWA MADDAM DINAZIZA-17

*********** ************ *********** **************

Tsahon lokaci yana duban matar dake tsaye a kansa kerere tana muzurai kamar zata haushi da duka.

"Zauna... mariya". Yace da ita muryarsa na rawa. Mariya ta dube shi shekeke, ta so ta ki zama, to amma akwai wani abu a cikin kwayar idanunsa da ya gargadeta. Dan haka sai ta zauna.

"Mariya, ina son ki sami nutsuwa ki tuna da Ubangiji wanda ya halicceki, domin kin shagala, zamani mai tsawo kina abin da kika ga dama na daga barna, son zuciya ko gezau ba kya yi, kamar ke kika halicci kanki" yayi shiru yana dubanta. Babu wani alamar canji a fitsararriyar fuskarta sai yaci gaba.

"Kin dade kina cuta ta, da takurawa rayuwata, duk kuwa da cewa aljannarki ma a karkashin kafata take... amma kin san ban tabi yi miki korafin komai ba, dan ni ba ta kaina na ke yi ba ta AZIZA 'yarmu nake yi "wannan shine karo na farko tun da aka haifi Aziza, da ya taba cewa da ita 'yarsa. Mariya ta turo baki gaba kamar bakin kifi.

Yarmu fa kace?" Alhaji Ibrahim ya dago carbin dake hannunsa ya dora bisa cinya kana ya yi gyaran murya ya ci gaba.
"Wannan har kullum shine irin jahilcin da ke cutar al'amarinki, yanzu dan nace 'yarmu sai abin ya zama laifi Mariya ta harare shi. "To na ji mai 'ya, ai sai ka yi min gorinta- tun da kai ka sunkuya ka haifeta." Alhaji Ibrahim ya dada yin shiru a karo na biyu wannan masifa ta fara isar sa, to sai dai fa ko me za'a yi ya rigaya yayi rantsuwa sai ya fada mata gaskiya. "Mariya ko fa me za kice Aziza 'yata ce kuma babu ta yadda za'a yi ina ji ina gani da idanuna da lafiyata na bari Aziza ta lalace... ba zan yarda ba". Wani zazzafan gumi ya fara sartu akan goshinsa, wannan shi ne karo na farko da ya taɓa kokarin gayawa matarsa Mariya ba zai yarda da al'amarinta ba. mariya ta dubeshi cikin mamaki a sa'ar da yaci gaba da cewa.

"Daga yau sai yau kada in kara ganin Aziza ta fita... ko da.... "Ba ka isa ba wallahi!!" Mariya ta katse shi cikin hanzari. Lokaci guda kuma ta mike tsaye a fusace.

Ya na yarda yarmu ce bani kadai na haifeta ba, amma zancen wai kada ta kara fita wannan ba zata sabu ba bindiga a ruwa, idan ta zauna a gidan kai za ka nemo mata miji? Ko kai zaka aure ta?" idanun Alhaji Ibrahim suka zazzaro waje yana kallon mariya tana masifa. "Kada ki yi haka Mariya, yarinyar nan ita kadai muke da ita a duniya yanzu idan ta lalace me gari ya waya kuma..." Yayi shiru sa'ar da yaga mariya ta sa shi gaba tana kyalkyala dariya.

"Oh! dan Amina Muhammadu, yanzu kai dan Allah Malam har kana da abin cewa akan tarbiyar Aziza? Ka tuna fa tun tana karama ni nake fama da ita, babu ruwanka da ita, sai yanzu ne kuma bayan har ta yi auren farko sannan ka fara tunanin kada ta lalace to kuma in lalacewar zata yi sau nawa za ta lalace? Sai yanzu da ta fito daga dakin mijinta na farko. Dubi fa yarinyar nan guda a gidan nan amma dai-dai da rana daya baka tafa tambayar abin da ya rabota daga gidan mijinta ba, ko ka taba?" Alhaji Ibrahim ya yi shiru, bai san abin da zai ce da ita ba domin' ta fishi baki bugu da kari kuma bai iya yin wata
KwakKwarar tankiya sakamakon ciwon dake hakarkarinsa
"To ai shikenan, tun da dai kina ganin abin da Azizi ta ke yi a yanzu dai-dai ne sai mu zuba mata idanu ko?" Mariya ta zumburo baki gaba kamar jaba, sannan ta matso dab da mijinta Alhaji Ibrahim tace dashi a tausashe
"Wai shin yaushe basira da tunani za su zowa wannan runtumenien kan naka? Kai ana nuna maka gabas kana yin yamma, gani kake yi kamar wai son bata Aziza nake yi, to amma kaki ka tambayeni dalilin zuwanta gida". Alhaji Ibrahim ya dago kai ya dubeta zuciyarsa na kuna yace

"Me kike nufin da in tambaye ki? Yanzun ke a matsayinki na matata, ita 'yata har sai na tambayeki dalilin da yasa ta zaman gidan? Ni bani da martabar da za ki zo ki sameni a matsayina na mijinki har sai na tambayeki da kaina?" Mariya ta dube shi a raine shekeke akwai wani tattausan murmushin izgilanci dake makale akan latar bakinta.

"Yau dai na fahimci 'yan mazanci kake ji, to bari yau daya dai in rusuna a gabanka". Ta matso dab da shi cikin izgili ta dafa gwiwarsa tace.

**Yarka dai Aziza a yanzu ba ta'da miji' Alhaji Ibrahim yadubeta a rude. "ba ta da miji kamar yaya?" mariya ta jefeshi da murmushin ko in kula. "Mijinta ne ya mutu shi yasa ta dawo gida!" Alhaji Ibrayim ya bude baki cikin kaduwa....

...Daga dakin da take Boye Aziza na iya hange da kuma jin duk irin mahawarar da iyayenta ke tafkawa. Ko da taji sa'ar da mamanta ke cewa "Mijinta ne ya mutu' sai wani tattausan murmushi ya subuce daga kyawawan lebbanta, lokaci guda kuma ta dauki jan baki ta nufi gaban madubi ta fara zezarawa a fatar bakinta, A dai-dai lokacin ne to ta jiyo mahaifinta na cewa.

"Amma har ayi sati guda da mutuwar mijin nata ni ban sani ba.." Tana jin haka sai ta dada sakin wani sabon murmushin kana tace a sanyaye.
"Iya wannan ma ka sani... da ace kasan abin da na aikata...".

Aziza bata kare fadin maganar ba sai taci gaba da nazarin surar jikinta a gaban madubin. Abin da ta gani ya yi matukar burgeta, musamman ma wandon mai beza dake jikinta wanda ya yi mutukar fitowa da kugunta, domin' ya matseta tsam-tsam tamkar fatar jikinta, Aziza tana sane da cewa duk mutumen dake da ra'ayin mutanen da masa duhun kai, kamar yadda ta kirasu, idan yaga shigar da tayi sai yayi tofin ala tsine, to amma ita duk wannan bashi bane a gabanta, domin ita a yanzu ta riga da kuna ba ta tsoron kauri, duk wata gutsuri tsoma da kananan guna-guni na mutanen unguwa bashi da wani tasiri akanta, ita babban burinta a wannan yammacin rana shine Allah sa kwalliyar da tayi ta burge babban masoyinta, abin kaunarta kwaya daya jal a duniya wanda tun da tazo duniya shi kadai ta taba so har zuciyarta ba tare da wata amaja ko murdiya ba
Aziza ta baro gaban madubin kana ta zabi daya daga cikin kujeru masu numfasawa dake dakin ta lume a ciki, lokaci guda kuma ta rufe idanunta, ta zauna zaman sauraro, zama na zuzzurfan tunani, domin ta rigaya ta saba a duk lokacin da ta zauna zaman jiransa, sai tunanin al'amuransa da kuma dabararsa sun fado mata a zuciyarta. DABARA!!, kamar yadda ta kirawo al'amarin, tabbas dabara domin da ita ne kawai tayi amfani ta rabu da tsohon mijinta, wanda ya shiga tsakanin ta da babban masoyin nata da kuma babban-babban abin kaunarta wato kudi..

Shekaru uku da suka wuce, Aziza ta fara tunani idanunta a lumshe. Sa'ar da tana jami'a ta hadu da wani mutum. A ranar tashinta kenan daga darasinta na karshe, ta nufi dakin kwanan dalibai mata, rungume da litattafanta a kirji, domin daman tun da safe suka yi alkawarin cewa in an tashi zata sami kawarta mabaruka domin karbar wasu takardu na lissafi.

ASHE TSAUTSAYI NE DAI YA KAWO......AZIZA-18

Tashinta kenan daga darasinta na Karshe, ta nufi dakin kwanan dalibai mata, rungume da littattafanta a kirji, domin daman tun da safe suka yi alkawarin cewa in an tashi zata sami kawarta mabaruka domin karbar wasu takardu na lissafi.

Ya kasance a ranar Aziza ta tashi cikin kuncin rai domin kafin ta baro gida sai da aka yi ta cacar baki tsakanin mahaifanta akan wasu kudi da take son a bata, wanda daga karshe da kyar ta sami rabi, domin mahaifinta yayi bayanin cewa tunda Mariya ta takura masa akan sai ya saya mata mota, to bai ko kara bata wasu kudin kashewa masu tsoka. Tun da Aziza ta shigo makarantar take ta cika tana batsewa kamar birdidingi, wasu uku daga cikin kawayenta a ranar sun yi kokarin janta da hira, to, amma jin takaitacciyar amsar da ta basu a ranar shi yasa su rufe bakinsu alaikum domin ba tun yau ba suka fahimci cewa in har Aziza tana cikin fushi to a kyaleta ita kadai ya fi.

Dan haka ana gama darasin ranar sai ta fito da sauri dan kada ma wani ya ganta ta nufi dakin kwanan daliban tana rangwada kamar dawisu, daga inda take tsaye tana iya hange dankareriyar marsandinta cikin filin fakin tana sheki da daukar ido kamar fasasshiyar kwalba a cikin rana. Aziza tayi tsaki ta tura baki gaba kamar algaita. Kamata ma yayi ace yanzu a dan karamin jirgin sama ake kawoni makaranta. "Tace cikin zuciyarta. A dai-dai lokacin da ta fara jiyo hayaniyar dalibai mata a dakin kwanan ne to taji kamar daga sama ance da ita.

"Sannu baiwar Allah" Aziza ta danyi turus, bata yi niyyar juya ba, to amma a cikin sautin muryar ta ji wani ingancin sauti da bata taba jinsa ba a bakin wani namiji, sannu a hankali sai ta juyo fuskarta murtuk ta dubi inda ta ji kiran, tana juyowa sai suka yi ido biyu da shi. Aziza taji gabanta ya fadi, ras, ita kanta bata san dalili ba, to amma me yiyuwa hakan bai rasa nasaba da surar saurayin, tun da Aziza take a duniya bata taba ganin mutum da yayi mata kwarjini kamarsa ba.

Saurayin da yayi mata magana zaune yake akan kujerar katako irin ta dalibai, a gindin bishiya yake shi kadai da alamu karatu yake,yi domin akwai tarin takardu da kuma wani katon littali a ajiye akan dan felelen katakon dake makale a daman kujerar wanda aka yi musamman dan ya canji teburi. Saurayin dogo ne wankan tarwada zai yi kimanin shekaru ashirin da tara me yiyuwa kuma talatin da biyu a duniya, yana da kyawawan
yan yatsu kamar mace, kafarsa sanye take cikin takalmi kanbas ballantana ma Aziza ta hangi sawun kafarsa, to sai dai ta lura da cewa fuskarsa doguwace ma'abociyar dogon hanci da madaidaicin baki, mai jan lebba jikakku ba busassu ba murmushinsa shi Aziza ta fi so, to amma babu abin da ya burgeta irin manyan idanunsa masu haske na mamaki, tun d Aziza take ba ta tabi ganin idanun namiji da hasken nasa ba Aziza tayi mamaki a zuciyarta in har ita kanta idanunta sun kai nasa haske

Sa'ar da ta juyo suka dubi juna sai ya yi mata wani tattausan murmushi, nan da nan Aziza ta ji gwiwowinta sun yi sanyi. Na shiga uku, ta ce cikin zuciyarta.

"Ki yi hakuri dan Allah na tsayar da ke..." saurayin yace cikin in'ina. "Daman aron injin lissafi na ke so Allah sa kina da ita" Aziza ta dube shi a dimauce, ga mamakinta sai ta ji duk da cewa ba ta da injin lissafin amma ba zata iyo ce masa bata da ita ba akwai wani kwarjini, da wani boyayyen al'amari a fuskar saurayin da ke burge Aziza.

"Uhm... uhm... bani da kalkuleta wallahi, amma in zaka iya jira bari in shiga (Hostel) sai na karɓo maka a gurin kawata"

Saurayin ya dubeta da tattausan murmushi mai narkar da zuciya "A'a kada ki wahalar da kanki wallahi... idan babu shike nan, ina ma da ita a daki na baro ta ina sauri ni kuma gandar komawa na ke yi shi yasa na tambayeki.. "Aziza ta jefe shi da nata murmushin. "Kai dai bari na dauko ma nan-nan ne fa". Ta nuna ginin dakuman kwanan daliban da dan yatsanta. Tana gama fadi sai ta
nufi ginin da sauri.
Saurayin ya saki wani ɓoyayyen murmushi sa'ar da ya dubi bayan Aziza tana sauri. Batun yau ba, ya dade yana fakon Aziza yana kokarin ya cafki zuciyarta bai sami dama ba sai yau ko shakka ba yayi yasan Aziza ta gama fadawa. Bayan wasu 'yan mintuna, sai ga Aziza ta dawo cikin sauri hannunta na hagun dauke da injin lissafi yayin da hannunta na dama kuma ta dauko robar ruwa mai sanyi da kofin azurfa akan robar

"Ikon Allah" saurayin yace cikin murmushi yana kallon robar ruwan sanyin da ke hannunta

"Kamar kin san abin da ke zuciyata wallahi yanzun nan nake shirin tashi zuwa shan ruwa" Aziza tayi far-far da idanunta, akwai wani farin ciki dake lullube zuciyarta a duk lokacin da ta dubeshi, haka nan muryarsa na yiwa Aziza dadi idan ya fara magana bata son ya bari. Haka nan ga dadin mamakin Aziza sai ta ji duk kuncin da ke ranta a wannan rana ya yaye.

"Ina duban ka daman na san kishirwa kake ji domin naga bakinka kamar ya bushe". Suka fashe da 'yar dariya baki dayansu. Aziza ta bude robar kana ta tsiyaya masa ruwan a kofi da mika masa cikin girmamawa akwai wani irin murmushi mai fassara da yawa a gefan bakinta.

"Na gode, ranki ya dade..." saurayin yace lokaci guda kuma ya dauki kofin. Bayan ya shanye ruwan sai Aziza tayi sauri ta dago robar sama tace "In dada ma". Saurayin ya girgiza kai da 'yar dariya.
Kai! So kike na fashe?" suka sake tuntsurewa da dariya suka dan sunkuyar da kai na dan lokaci kana sai Aziza tace.. "Bari in tafi gara kayi karatunka kada na dameka".

A lokacin a durkushe take a gabansa tana fadin haka sai ta mike tsaye ta dada da cewa.
"Idan ka tashi sai ka mika kwalbar da kofin daki mai lamba talatin da bakwai.

"Ban san iya godiyar da zan yi miki ba gashi kuma har zaki tafi ban san sunan ki ba". Saurayin ya mike tsaye, cikin fara'a. "Kana iya kirana da AZIZA

"Ni kuwa kina iya kirana da USMAN", suka dan yi dariya Sannan sai Usman yace.
"Ina fatan ba mun rabu ke nan ba". Aziza ta dube shi cikin Rausaya tace. "In kana son mu sake haduwar me zai hana ka neme ni?"

Tun daga wannan ranar Aziza ta zama baiwarsa bata da ikon yin komai sai abin da yake so badon komai ba sai don tsabar mutuwar son sa da ta ke yi.

Washegarin ranar da sassafe misalin karfe takwas saura Aziza ta shigo makarantar cikin dankareriyar marsandinta, sanye take da doguwar riga ta siliki da wandonta, rigar tana dauke da wasu fala-falai a gabanta kamar fukafikin Malam buda mana littafi, to sai dai kuma launin rigar ya sha banban da na wandon duk kuwa da cewa yanayin silikin da aka yi su da shi duk iri daya ne. A dai-dai lokacin da ta shigo ta daya daga cikin tagwayen kofofin na jami'ar Bayero ne ta hangi Usman yana ta sauri ya nufi cikin makaranta a kasa. Da farko Aziza bata gane shi ba, me yiyuwa hakan na da nasaba ne da jikewar da bayan rigarsa yayi ne sharkaf da gumi, babu mamaki kuma tsananin kodewa da jemewar kayan da ke jikin Usman ne suka hana ta gane shi. To koma dai mene ne sa'ar da ta zo giftawa sai ta hangi gefen fuskar Usman cikin sauri ta lalubi burki ta tsaya, aka yi sa'a kuwa ba aguje take ba; domin kullum kwanan duniya aguje take shiga a guje take fita kamar kurege duk kuwa da jefi-jefin kabarin mai tatsinen da ya rarraba hanyar.

"Usman ina kwana". Tace dashi cikin murmushi a dai-dai lokacin da tayoyin motar suka gama sauka kasa. Usman ya juye cikin shakka domin bai dauka da shi ake ba. yana juyowa sai suka yi ido biyu da Aziza. Usman yaji zuciyarsa ta harba, Allah gwanin hikima yace cikin zuciyarsa. Hakika nayi sa'a.
"A'a... Hajiya Aziza ina kwana kece haka da sassafe?" Aziza ta harare shi lokaci guda kuma ta bude masa gidan gaba na motar.

"Wa yace da kai sunana Hajiya Aziza?" Usman ya dubeta cikin tattausan murmushinsa, kana ya shiga motar yana rufe kofar sai gilashin ya rufe. Usman yaji sassanyar raɓa ta fara dukan.fuskarsa sa'annan ta ratso tun daga babban dan yatsansa har zawa goshinsa, usman ya yi ajiyar zuciya a zuciyarsa yace. Masu ruwa su ke da kifi. Aziza ta tuka motar a hankali suka nufi cikin makarantar. "Usman kenan... kana da laccar safe ne?" Usman ya girgiza
kai kana ya fara goge fuskarsa da wani jan kyalle. "Laccar karfe tara nake da ita wallahi ke fa?" Aziza ta dube shi da murmushi a dai-dai lokacin da suka kawo filin fakin, cikin gwaninta Aziza ta tura hancin motarta karkashin wata bishiya tsakanin wasu motoci guda biyu, Honda da kuma wata shudiiyar (bus) ta kawo yara makaranta. Aziza ta kashe motar kana ta juyo ta dube shi

"Nima sai karfe tara zan shiga". Wanan zance da ta fadi karya ne, a ka'ida takwas ya kamata ta shiga, domin da tara za ta shiga da babu abin da zai kawo ta makaranta yanzu. Usman ya dubi kyakkyawar fuskar Aziza a zuciyarsa yana mai addu'ar Allah sa kada tace su fita daga motar domin na'urar sanyaya iskar ba karamin aiki ta ke yiwa jikinsa ba, domin yaci uwar tafiya, tun da dai tun daga Rijiyar zaki yake tafe har zuwa kofar makarantar.

Matasan biyu suka dubi juna na dan tsayin lokaci kana suka Sunkuyar da kai cikin murmushi a kunyace. Aziza ce ta fara dago kai ta dube shi, nan da nan sai ta ji zuciyarta ta harba, ashe rigar da Usman ke sanye da ita ba karamar kodewa ta yi ba, Rigar shat ce shudiya, amma saboda masifar duniya ta dadewa da dukan rana ta kode ta koma ita ba fara ba ita ba shudiya ba, hakanan bakin wandon dake jikin Usman shima a koɗe yake ya koma toka-toka, akwai alamu da ke nuni da cewa kowane lokaci daga yanzu idan aka takurawa wandon zai iya fashewa ta gwiwa, Aziza tayi addu'ar Allah sa ba a gabanta wandon zai fashe ba, to amma duk da wannan babban abinda ya fi tayarwa da Aziza hankali shine kwalar rigar Usman, domin daga inda take zaune tana iya hangen gurabe uku inda kwalar rigar ta fara dariya, hakanan hannun riga ya fara zazzarewa. Aziza ta matsa daf da Usman cikin damuwa tace.

"Usman a nan garin kake?" Usman ya dubeta cikin mamakin jin tambayar. "A nan nake da zama rijiyar zaki a gidan wani dan uwan Babana amma sanadin karatunnan da nake yi ne na dawo nan, ni mutumin MALUMFASHI NE". Aziza ta gyada kai cikin gamsuwa kana ta daga kai sama tana duban rufin motar cikin damuwa. Duk da yake dai tun da Aziza ta zo duniya bata taba sanin menene talauci ba, to amma labarin da ta ke samu a game da shi da kuma wadanda take gani a ciki sun isa su tsorata ta Duk da cewa bata taba shiga cikinsa ba, babu abin da ta ki jini irin ta rabi talauci. Dan haka a yanzu da tasa abin da take so Usman a gaba sai ta ga dole ne tayi wani abu akai, dole ne in har zata iya ta tsame shi daga cikin tsananin talaucin da yake ciki. Zuciyarta ta shiga cikin damuwa, ko shakka ba tayi duk duniya babu wanda take kauna kamar Usman duk kuwa da cewa jiya-jiyan nan suka hadu, to amma tambayar da har Aziza ta kasa sanin amsarta shine shin zata iya aurar fakiri kuwa kamar Usman?

"Tunanin me kike yi" Usman ya katseta. Aziza tayi ajiyar zuciya, kana ta dube shi da murmushi, amma duk da haka sai da Usman ya lura da alamun, damuwa karara a fuskarta.

"Oh, wallahi Usman tunaninka na ke yi?" Usman ya yi mamaki. "Tunanina kamar yaya?" Aziza ta dube shi. "A kasa kake zuwa makaranta kullum?" Usman ya gyada kai cikin dariya. "Kin san dalibi... kuma talaka

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

1 month ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment