Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka wuce na ta kururwa cikin zuciyarsa ya dubi nafisa yace.
"Ki tafi na sake ki saki biyu" Ya fice daga dakin ya nufi kofar gida, ya barta a nan tsaye saroro cikin kaduwa. Abin da bai sani ba shine duk masifar da NAFISA ke yi bata taɓa tsammanin zai iya sakin nata ba.

Yusif ya ji gabansa ya fadi ras sa ar da ya fito kofar gidan Wanda ke tsaye a kofar gidan tamkar mutumin da ya taɓa zuwa fadar mutuwa ne a gurin Yusif. A tsaye a kofar gidan yana duban Yusif cikin murmushi Saddiq ne.

"Yaya Yusif ina kwana..?" "Lafiya lau! "Yusif ya amsa bakinsa na rawa, domin ganin yaron ya tuno masa tsawon shekaru tara da suka wuce. Duk da yake ya dada girma, amma har yanzu zuciyarsa tana iya tuna kamaninsa a wancan tsahon lokaci.

"...Daman...daman zuwa na yi in fada ma...AUREN YAYA AZIZA YA MUTU" Yusif bai gaskata kunnuwansa ba, ya dubi saurayin lokaci guda ya tuna addu'ar da saurayin ya taɓa yi masa tun yana yaro. Ga mamakin Yusif sai ya ji hawaye ya kwace masa.

"Allah....Allah na gode ma da ka dawomin da matata AZIZA!".

BABI NA HUDU 4

KEBBI
LARABA
JANAIRU 6 5:00am NA SAFE

Kowanne daki mutum bibiyu ne a dadɗaure da sarkoki, suna ta sukur-sukur kamar kaji. Mataki-mataki ne, domin ko a cikin 'yan fursunar, wani ya fi wani 'yanci. Irin 'yan fursuna da suke da dan 'yanci, sune irin wadanda suke da karamin laifi, da kuma wadanda wa'adin futarsu ya kusa.

AMMA AGURIN....... KUMA ASHE BAHAKA BANEAZIZA-13

BABI NA HUDU 4

KEBBI
LARABA
JANAIRU 6 5:00am NA SAFE

Kowanne daki mutum bibiyu ne a dadɗaure da sarkoki, suna ta sukur-sukur kamar kaji. Mataki-mataki ne, domin ko a cikin 'yan fursunar, wani ya fi wani 'yanci. Irin 'yan fursuna da suke da dan 'yanci, sune irin wadanda suke da karamin laifi, da kuma wadanda wa'adin futarsu ya kusa.

Da yawa daga cikin baki idan suka dubi gidan yarin daga waje, sukan yi kuskurensa a matsayin wani gini daban amma bana fursuna ba. Domin kowa yasan ga al'ada an saba ganin katangar gidan yari zungureriya to amma saɓanin hakan wannan bata da tsayi, kuma an yi mata fenti rangadadan kamar wani dandalin shakatawa da iyalai kan kai ziyara ranar sallah.

A can ciki abin babu kyan gani babu dadin ji. Da yawa za kaji takadarai ma'abota kwane-kwane, handuma, murdiya, da masu son kudin gaggawa suna addu'ar Allah raba su da mugun ji da mugun gani, to wannan gidan yarin suke nufi.

Dogayen dakuna ne a jajjere rukuni-rukuni. Akwai rukunin masu dankaramin laifi, wadanda ke hade a ciki a cunkushe kamar kajin gidan gona, kowa akan kirji yake kwana, babban abin alfahari a dakin shine bargo, to amma duk da hakan wani Sa'in yana zama bala'i domin kwarkwata da kudin cizo ne ke kafa sharkwata dinsu a jikin bargon

Kullum ta Allah za'a fito da sababbin shiga cikin hantsi, domin su gasa jiki da mayafinsu su kuma kori kudin cizo da kwarkwata. Sa'a guda ake basu, abinci sau biyu a rana, wani dan fursuna ya taba cewa da ya sake shan miyar fursunan gara a bashi ruwan allura yasha hakanan kuma da ya sake cin shinkafa, ko tuwon fursunan, gara yayi shekara yana cin danyar goba a abincinsa sau uku a rana:

Wadannan rukunin 'yan fursuna kamar 'yan aljanna ne akan rukuni na biyu wadanda ke can ciki a daddaure cikin sarka. kamar kayan kwantaina. Duk wanda ke cikin wannan dakuna an shafe sunansa daga cikin babin wadanda za su sake zama a duniya, ko kuma a sararinta, kayan da ke jikin su bakake ne, kamar yadda zuciyarsu take bakin kirin. Saɓanin sauran 'yan fursuna su sai abin da suke so za'a basu suci, domin da yawa daga cikinsu hukuncin kisa ne a kansu, masu yar dama-damansu ne ke zaman rai-da-rai babu ranar fita, daga nan sai kabari. A cikin daya daga cikin irin wadannan dakuna ne to aka fara wata dirama.

Mutanen biyu dake cikin dakin kafafunsu a dadɗaure da sarka, an kuma hadasu da wani katon turke an daure kamar shanu. Wani sa'in akan bar musu hannayensu ba tare da an daure ba domin su sami damar cin abinci.

Wani dogon saurayi dake can kuryar dakin a dadɗaure da sarka, ya dubi katon biredin dake gefensa a ajiye sannan ya dauke kai gefe guda.
A zahiri Mustapha, ko kuma Musti kamar yadda 'yan duniya kan yi kiransa a lokacin da yake zaman 'yancin yin abin da yaga dama a sararin duniya, bai fi shekara talatin da daya ba a duniya, to amma tarin gemun dake fuskarsa buyu-buyu kamar ciyawa a gonar rago, su suka kara masa shekaru ya zama tamkar dan shekara hamsin a duniya.

A wannan safiyar Musti cikin yunwa ya tashi, dan haka sai ya dubi dan uwansa da ke kwance cikin sarka yace.

"Kai Danko, ni fa yunwa nake ji, in kana iya cin biredin nan da aka kawomin jiya tashi muci, domin bana jin zan iya jurewa har a kawo mana abinci gara na dan tattoshe..."

"Danko, dankareren Kato ne, wanda a zamaninsa in ya barke da gudu baya kamuwa duk kuwa da Ribarsa shekarunsa ashirin dai-dai a gidan yarin. Danko ya dubi Musti yayi huci, Musti yayi sauri ya dauke kansa, domin duk da irin kaunar da Danko ke nuna masa da kuma tausaya masa din da yake, akwai lokuta da Musti kan ji ya tsani Danko, domin kullum cikin tusa yake sai kace bodari, gashi da dan banzan ci kamar gara, idan yayi huci kuwa, sai kace tayar mota ake sacewa.

"Ka ci dai kawai, ni yau a koshe na kwana" Danko yace da Musti.
Musti ya dauki biredin ya yage ledar ba tare da ya damu da ya kunshe ta a hankali ba. Ya gyara kafafunsa da ke cikin sarkokin, sannan ya gutsuri biredin, yana gutsura, sai wata siririyar wuka fara ta azurfa ta fado daga cikin biredin sannan daurin kudi 'yan naira dari biyar ya fadi daga karshe kuma sai wata guntuwar takarda ta fadi. Musti ya dubi biredin cikin kaduwa, cikin biredin kwaroro ne babu nama ko shakka ba ya yi biredin jakada ne ba abinci ba.

Hannunsa na rawa ya dauke kudin da wukar ya boye domin yasan kowani lokaci daga yanzu gandiroban dake kula da su za su shigo kawo musu abinci, sannan sai ya dauki takardar, wacce ke dauke da wani irin sarkakken rubuta tafiyar tsutsa ya fara karantawa.

MUSTI
shekaran jiya muke ta tunanin yadda za a yi mu sanar da kai, muka rasa, domin bai yiyuwa mu sanar da kai gamu ga gandiroba Da Kyar muka tuno wannan dabarar.... Lokaci yayi kamata yayi ka tsero daga wannan wahala shekara tara ba wasa ba ce aina nan bayan kasuwa muna jiran tserowarka, a duk lokacin da ka sami dama, abin kawai da muke so da kai shine ka Kokari ka tsallake katangar. Mun bata layin dake kawo wa gidan yarin wuta, wanda kuma ke kula da injin bada wuta na gidan mun gama dashi zai baka mintuna goma dai-dai ka tsere, daga 6:00am-6:10am na safe daga karshe kuma muna son mu shaida ma cewa mutuniyarka da muka baka labarin tayi aure, a yanzu haka dai aurenta ya mutu... ya rage naka muna nufin AZIZA

Sunan Aziza tamkar sukar mashi ne a zuciyar Musti. Tuntuni, tuntuntuntuni da ya yi niyyar gudu da tuni ya gudu, duk kuwa da katuwar wayar da ta zagaye gidan wacce ke dauke da wutar lantarki... da fa ni na kaika lahira.

Musti bai damu da wannan ba, abin da ya hana shi guduwa shine zamansa a cikin gidan yarin ya fi zamansa a waje... tun ranar da Aziza ta kunce masa zani a kasuwa ya ji duk zaman duniya ya isheshi, dan haka lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai-da ran sai ya yi farin ciki, domin haka din zai zamo masa katanga tsakaninsa da tunanin Aziza.... Tun da farko so ma yayi a yanke masa hukuncin kisa ya huta da azabar zuciya.

"AZIZA!" Ya sake nanata sunan cikin zuciyarsa nan da nan yaji gumi ya fara wanke fuskarsa. Idan badan Aziza ba, da ban san ta ba, da ban taɓa haduwa da ita ba, da yanzu ina waje da 'yancina kamar kowa". Musti ya ce cikin zuciyarsa.

Danko ya tashi zaune a hankali yana duban Musti, ashe tun sa'ar da Musti ke karatun wasikar Danko ke dubansa daga kwance.

"Me... menene?" Danko ya tambaya yana duban fuskar Musti a jike sharkaf da gumi. Musti ya mika masa takardar yace "Mutanen mu ne suke son na tsere...kuma...kaji wai auren Azizan nan da nake baka labari ya mutu...." Musti yai shiru akwai wani sauti da muryarsa ke bayarwa wanda yasa Danko ya tausaya masa domin yasha bashi labarin aziza ba sau daya ba ba sau biyu ba danko ya taba cewa dashi WATARANA...AZIZA-14

Danko ya tausaya masa, domin Musti yasha bashi labarin Aziza ba sau daya ba sau biyu ba. Danko ya taba cewa dashi wata rana.

"Musti, yanzu kuwa da za'a sake ka ka koma gida, kuma ace Aziza ba ta da aure za ka iya aurenta kuwa?" Musti ya dubi Danko cikin farin ciki domin duk wani abu da za'a hadasa da Aziza faranta masa rai yake.

"Me zai hana? Ai duk duniyar nan bani da wadda tafi min Aziza, duk kuwa da cewa ita ce ta yimin sanadiyyar zuwa gidannan. Bari in fada ma Danko, wallahi abu daya ne ya hanani tserewa daga gidan nan, saboda nasan Aziza tayi-min nisa". A yanzu da Danko ke rike da guntuwar wasikar abin da yafara fado masa a rai kenan, duk kuwa da cewa yau shekaru uku
kenan da yin hirar. Danko ya dubi Musti yace.
"To ai sai mu hanzarta ko? Yanzu dai ina tsammanin shida ta kusa ka ji kuma abin da suka ce, mintuna goma kacal kake da su. Musti bai gaskata kunnuwansa ba, ya kalli Danko cikin kaduwa yace muryarsa na rawa yace.
"Kana...nufin kace ka goyi bayan na tsere". Dánko ya fashe da dariya.
"Ai ba kai kadai ba Musti, ni kaina zaman nan ya isheni haka, rabona da in ga abin da ke gudana a sararin duniya yau shekaru ashirin. Idan badan kai ba Musti da tuni na dade a waje, to amma a kullum idan na yi niyyar gudu sai in tausaya maka domin zan tafi in barka kai kadai da tunanin masoyiyarka AZIZA, nasan yadda ciwon so yake, a kullum fatana shine ka kawo shawarar tsira!" Danko ya yi shiru yana maida numfashi sa'annan sai ya mikowa Musti hannu.
"Bani kudin da aka aiko ma" Musti ya dube shi cikin mamaki
"Bani mana kada su karaso ko so kake lokaci ya kure mana. Ai idan kaga an aiko ma da kudi to akwai abin da ake bukatar kayi dasu". Danko ya sake fashewa da dariya.

"Kudin sune tikitin mu na tsira, kasan gumakan zamani ne kowa su yake bautawa". Musti ya miko masa kudin hannunsa na rawa

"Hado min har da wukar mana" Musti ya ji gabansa ya ladi "Wuka "Danko ya daga masa hannu bai karasa ba. "Bai kamata yaro kamarka ya yi kisan kai ba kabar wadanda suka saba su aikata ya dan yi shiru sannan ya dada da cewa
"Kai dai zuba min idanu nan da mintuna goma sha biyu muna waje.

Yan fursunan suka yi shiru na dan lokaci sa'ar da suka ji sautin takun sawu an nufo dakin dakin da suke rufe. Nan da nan suka dubi juna Sannan abin mamaki sai suka ji rurin injin da ke baiwa gidan yarin wutar lantarki ya tsaya hakan shi ya dada sa shirun tayi yawa, ta kuma kara bugun da zuciyar Musti ke yi domin yasan tuni sun shiga cikin mintuna goman da aka basu na tserewa

Gandiroban da ya nufo dakin dogo ne fari bafilatani, yana da tarin suma akai, wanda hular da ke kansa bata rufe koda rabin gashin ba. Zuciyar Musti ta fara har bawa, lokaci guda kuma zuciyar Danko ta yi fari tas kamar nono, domin yasan gandiroba GAMBO ba zai yi wuyar sha'ani ba.

"Barka da zuwa Malam Gambo" Danko yace da shi cikin walwala.

"Danko mai duniya, ina fatan dai lafiya" Gambo yace yana murmushi. Sun dade suna wasa, an riga an saba, tun kafin Gambo ya shiga aikin fursuna Danko yake gidan, Yau kuwa da fara aikin Gambo shi kansa shekaru goma sha daya kenan. Akwai wani abu da ke burge Gambo a tare da Danko. Na farko dai mutumin yana da fara'a da nutsuwa, koda yake dai wani lokacin mafadaci ne na gaske, wanda hakan shi yayi sanadiyar da yasa aka rabasu da sauran mutane ire-irensu wadanda ke da hukuncin daurin rai-da-rai, aka kawo su nan shi da Musti aka daure, saboda tsabar fadansu. To amma duk da haka dai Danko yana burge shi domin mutum ne mai yawan yi masa alheri
musamman ma idan aka aikowa da Danko yan kudade domin gidansu Danko gidan Attajirai ne.

"Lafiya ba lau ba Danko yace da Gambo gandiroba. "Subhanallahi... me ya faru kuma Danko?" Danko ya dubi Gambo cikin fara'a yace.

"Haba Gambo. yanzu ace kana nan kana aiki agidannan amma yau nafi wata uku ban yi wanka ba. Gashi kuma duk kun bi kun daure ni da sasari kamar wanda aka yankewa hukuncin kisa...ai in dan fadan da na yi ne ya kamata a ragamin haka". Gambo ya dube shi cikin murmushi yace.

"Danko ai kasan ni ba laifina bane" Danko yace. "Eh, nasan da haka, amma ko wanka dai ai abar ni nayi, haba Gambo kai fa nake takama dashi a gidannan" Yana fadin haka sai ya saki kudin dake makale a jikinsa suka fadi sannan yace.
"Ina tsammanin dai ai wanda ke waje shi ke bukatar kudi ba daurarre marar 'yanci ba, kai dan Allah Gambo bar bawan Allah Danko yayi wanka mana". Danko yace cikin dariya Gambo ya dubi kudin ya hadiyi yawu, yasan abin da ake nufi domin ba yau aka fara ba. To amma abin da bai sani ba shine nufin na yau ya wuce tunaninsa.

"Ba komai Danko Gambo yace yana murmushi.

"Ai wannan shine amfanin a dade tare, bari in bude ku, amma daya bayan daya Musti ma sai ya dan watsa ruwan amma fa ku yi sauri" Musti ya dubi Gambo sa'ar da yake kokarin bude kofar dakin ta farko, kirjinsa na harbawa yawun bakinsa ya kafe, hakan shi ya hana shi yiwa Gambo godiya.

Gambo ya lalubi aljihunsa ya fito da 'yan mukullaye, sannan ya durkusa ya fara kunce sarkar da ke kafar Danke Danko yana cewa

"Kai amma fa wallahi yau Gambo ka taimakeni, wallahi baka ji ba yadda jikina ke danko, kamar cimgam, wani lokac idan na hada hannayena guri guda da kyar na ke ɓanɓarewa".

"Muje ka yi wankan, sai ka yi sauri idan ka gama.. Maganar ta makale a makwogwaronsa, sa'ar da busassun 'yatsun Danko masu kamar karfe da karfin tsiya kamar talauci suka shaki magoronsa. Danko ya daga shi sama da hannu daya ya buga shi da kasa batareda da ya saki makogoronsa ba saiya maka kokon kansa a daben sumuntin dakin.

WANNAN GANDUROBAN DA ALAMA MAYYAR KUDI CE KAMAR O'OAZIZA-15

ƘARSHEN LITTAFI NA DAYA

Danko ya daga shi sama da hannu daya ya buga shi da kasa, sannan ba tare da ya saki makogwaronsa ba, sai ya maka kokon kansa a daben sumuntin dakin.

Sautin da kokon kan ya bayar sai da yasa zuciyar Musti kusan fitowa daga kirjinsa. Ganduroban ya harba kafa sau biyu daga nan bai ko kara motsi ba. Danko ya nufi inda Musti yake a daure, cikin gaggawa yasa dan mukullin da ya lalubo daga aljihun gandiroban ya bude sasarin dake kafar MUSTI.

Mintuna uku dai-dai duka al'amarin ya dauka, mintuna hudu kuwa Danko da Musti sun bude kansu, sannan suka nufi can bayan gidan yarin da gudu-gudu.
"Kana jin...zai rayu kuwa?" Musti ya tambayeshi muryarsa na rawa. Danko yayi murmushi yace. "Wa ya sam masa, kaga wukar ma ba tayi amfanin komai ba".

A wannan lokaci, ma'aikatan gidan yarin sun yi imani da cewa babu ta yadda za'ayi wani dan fursuna ya iya tserewa, domin sun san ko da ya kunce ma, to wayar da aka zagaye gidan da ita ba ta barin sa ya tsira da rai duk wanda ya taɓa wayar sunansa matacce, gashi kuma tsayin wayar ya fi ma tsayin katangar da ke zagaye da gidan baki daya, wannan shi ya sa mafi yawanncin lokuta za ka sami ɓangaren katangar daga yamma babu kowa, domin ba'a tsammanin akwai dan fursuna da zai yi kokarin tserewa da karfe shida na sassafe. To amma abin da ba Su sani ba shine, ba su taɓa kawowa koda aransu ba, cewa za'a dauke wuta, domin ko da an dauke wuta to akwai in ji lafiyayye sai gashi a wannan safiyar injin ya mutu.

Cikin sauki suka tsallaka katangar kamar birirrika. Dan tsirarin dai-daikun mutanen da suka fara fitowa daga gidajensu domin tafiya neman abinci suka dinga bin 'yan fursunan da kallo cikin kaduwa, suna ta sheka gudu abinsu, suka nufi hanyar da zata kai su bakin kasuwa. A dai-dai lokacin ne to suka ji mota a bayan su tana Hon Musti ya juyo yana gudu yana duban motar dake binsu baya cikin firgici. Lokaci guda kuma ya dubi danko cikin halin kaduwa, domin bai taba tsammanin bayan shekaru ashirin din da jibgegen mutumin ya shafe a gidan maza har zai iya gudu haka ba, domin kai kace akan iska ya ke tafiya kafafunsa ko taɓa kasa sosai ba sa yi. A dai-dai lokacin da Musti ke kokarin kwana ya shige wata 'yar siririyar barauniyar hanya, sai ya ji ance

"TSAYA MUSTI MUNE" wannan murya ita ta fi kowacce murya dadi a wannan lokacin akunnen Musti, ya gane muryar. Danko na cikin tikar gudu sai ya waiwayo cikin mamaki domin jin Musti ya rage gudu.
"Su...ne" Musti yace dashi yana haki. Fijo 504, marar lamba ta tsaya a kusa dasu, a gaban motar direba ne kadai da wani saurayi kakkaura, idanunsu boye a bayan bakaken tabarau kafin kiftawa da bismillah Musti da Danko sun fada bayan motar. Karar cin tayar motar ya cika gurin ayayin da motar ta harba kan titin a guje kamar kibiya wata 'yar karamar yarinya da ke dauke da kwanon shan ruwa a bakin titin ta jefar da kwanon ta koma cikin gida da gudu a tsorace tana ihu ita ta dauka kanta motar ta taho.

"An gaisheku mazaje!" wata kakkausar murya irin ta mafarauta tace da su daga gaban motar. Danko yayi murmushi yana duban Musti

"Mutanen kune ko?" Musti yayi shiru bai amsa ba, akwai wani irin yanayi na ko in kula da Danko ya lura da shi a fuskar Musti

"Tunanin me kake yi?" Danko ya tambaya yana duban Musti

"Kai ma ai ka sani

"Tunanin Aziza?" Musti ya gyada kai kamar kurma. Danko ya sake murmushi yace

"Lallai kaunarka da Aziza sai Allah" ya dan yi shiru sa'ar da motar ta fada cikin wani rami gararam! Sannan yaci gaba. "Har yanzu nasan kana son auren Aziza?"

MUSTI ya dubeshi fuska murtuk yace.
"Duk rayuwata danko, duk jin dadina danko,. Duk farin cikina danko yana hannun Aziza, amma duk saboda ita gashi a yau duk na rasa su" yayi atishawa.
Kasan fa daga yau duk wata kwanciyar hankali ta kare mana, domin kullum zamu kasance ne cikin buya, babu yawon rana sai na dare, domin za'a yi ta yada hotunan mu a jaridu da mujallu ana nemanmu, daga yanzu ko kukan zakara mutum ya ji sai gabansa ya fadi... kaga kuwa idan haka ne to ta yaya kake tsammanin har zan iya auren Aziza?" Danko, ya yi dunkum domin bashi da amsar tambayar.

Tsawon lokaci babu wanda ya sake magana, kowa ya yi shiru zuciyarsa na karatun wasikar jaki, motar na ta sheka gudu dasu tsakanin dazuzzuka kamar za su bar duniya. Can sai Danko ya yi ajiyyar zuciya sannan yace.

"To amma dai nasan har yanzu kaunar Aziza na ranka.." wani tattausan murmushi ya subuce daga fatar bakin Musti sannan sai ya girgiza kai ya ce.

"Da ne wannan, amma duk da haka dai ina bukata mu sake haduwa da Aziza" Danko ya dubi Musti cikin kaduwa "Kana nufin kace ka daina kaunarta?" Musti ya gyada kai.

Danko ya hade fuska yace "To mene ne kuma na son sake ganinta?" Musti ya amsa lokaci guda

"SO NA KE NA KASHE TA!"

WANNAN SHINE KARSHEN LITTAFI NA DAYA

AMMA FA DUKKAN GODIYAR KU KAMATA YAYI TA TAFI KAI TSAYE ZUWA GA MAMALLAKIN LITTAFIN AZIZA WATO Nazir Adam Salih

Domin Shine Kashin Bayan Wannan Aikin Komai Yana Tafiya Ne Bisa Sahalewarsa Gamida Kwarin Gwiwar Dayake Bani Akoda Yaushe.

WATAKILA MU SHIGA LITTAFI NA BIYU IDAN NAGA KUN NUNA BUKATAR YIN HAKAN..AZIZA-16

LITTAFI NA BIYU 2

BABI NA BIYAR 5

KANO

5 JUMA'A JANAIRU

8 3:30PM NA RANA

Ta fada dakinta cikin sauri tana tsaki sa ar da taji shigowarsa dakin shakatawar. Alhaji Ibrahim ya yi tsaye cikin takaici, hannunsa da carbi, Dawowarsa kenan daga masallacin Juma'a, tun- daga can yake lazimi, amma abin da ya gani yanzu ya tsinke zaren laziminsa, ya kuma cinna wutar da ta dade tana ruruwa cikin zuciyarsa. Yau kam ko sama... da kasa zata hade... kai ko hadiye ni za tayi ba masifa ba sai na fada mata gaskiya".

Sa'ar da ya shigo dakin, 'yarsa ya hango tsaye a cikin falon sanye da dogon. wando (Jeans) mai wata irin beza daga kasa,. kamar kafar tattabara, banda wannan kuma rigar dake sanye a jikinta matsatsiyace, mai kamar fata, tana dauke da wadansu dishi-dishin Allah tsine suna daukar idanu... haka nan kuma karin Allah tsine kanta babu dankwali.

Duk wannan lokaci guda Alhaji Ibrahim ya lura da hakan kafin tayi sauri ta fada cikin dakinta gami da tsaki. Alhaji Ibrahim ya ji tsakin.
"Mariya!" ya Kwalawa matarsa kira a fusace. Shiru ba'a amsa ba
"Mariya..."ya sake kwalla kiran a karo na biyu. "Gani nan ina zuwa dan Allah, kai sai shegen kira wallahi kamar tsohon makaho!" Alhaji Ibrahim ya ji kamar wani abu ya tsikari kirjinsa saboda bakin ciki, nan da nan sai yaji kafafunsa sun fara rawa, cikin gaggawa ya nemi daya daga cikin kujeru
sama da arba'in da ke cikin makeken dakin shakatawar ya zauna Asalin Alhaji Ibrahim mutumin Bauchi ne, karatun allo ya kawo shi Kano. Ba'a dace ba ya zama cikakken malamin tsubbu, wanda ya shahara akan aikinsa, kullum baka raba shi da attajirai, mata, samari mutanen kirki da ɓarayi.., sannu ahankali suka dora masa tsanin arziki, malam Ibrahim ya haure abinsa.

Mutane sun sha mamaki sa'ar da aka ji cewa wai Malam Ibrahim ya bar tsibbu, kai bama tsibbun ba kawai ya bari, har garin ma ya bari. Aka yi ta jajensa, daga baya aka sami labarin cewa wai wani mutumin kauye ya ganshi a Makka. Shekarunsa goma sha biyar a kasa mai tsarki.

Don haka sa'ar da ya dawo Kano ya gina dankareren gida a Tarauni ba kowa ne zai taba gane shi ba, domin zamansa na farko ba a Tarauni ya zauna ba To amma duk da haka sai da wasu magulmata suka gano cewa, ashe dai hamshakin attajirin da a yanzu yake kiran kansa da Alhaji Ibrahim, shine dai wannan tsohon malamin tsubbun da suka sani. An dacde ana yada jita-jita cewa, wai damfara ya yi a Makka shi yasa ya gudo da makudan kudade, wasu kuwa suka ce a'a ai har a makkan ma Malamin tsibbu ne.

To koma dai mene ne, sa'ar da Alhaji Ibrahim ya sauka, sai aka ganshi tare da wata kyakkyawar mata mai kamar balarabiya. Mazaje da dama suka yi ta kyashinsa, suna cewa.
"Kai amma fa mutumin nan ya auro mace da kyawu ZINARU!

Duk wannan shirme da suke yi shi akullum Alhaji Ibrahim nadamar aurenta ya ke yi domin rabonsa da wani kwakkwaran farin ciki tun kafin ya auro ta daga Saudiyya. Kudi dai Allah ya hore, to amma sai abin da tace dashi,
ya zama tamkar rakumi da akala sai in da ta ja shi, kai ko riga zai sa sai ta zabar masa wacce take so hakanan ma abinci sai wanda take so za ta sa ma'aikatan gidan su shirya, feleke dai iri-iri, har wata rana la taba cewa dashi "Gaskiya ni daga yau bankara cin abinci tare da kai, yanzu ace mutum taunar abinci ma bai iya ba, sai ka yi ta tauna cakam-cakam kamar mai cin danko! kai subhanalillahi wallahi wannan da ace har yanzu a Saudiyya muke da bazan kara zuwa wata liyafar arziki da kai!".

Shekararsu daya da zuwa Kano ta haifa masa yarinya kyakkyawa mai kamar balarabiya, wacce an dade ana labarin kyawunta a makwabta,

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

1 month ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment