Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya faru ne cikin abin da bai fi dakiku uku ba, don haka sai Aziza tayi mutuwar tsohuwa ta kurawa mutumin idanu cikin kaduwa.

"Baki gane ni ba ko Aziza" Mutumin yace cikin wata busasshiyar murya. Aziza ta dubi mutumin mai tarin gemu biyu-biyu kamar ciyawa, tabbas bata gane shi ba...
mahaukaci ne. Tace a ranta. "Baki gane ni ba?" ya maimaita tambayar. Aziza ta girgiza kai a tsorace. Mutumin yayi murmushi yace "Nine MUSTY..............AZIZA-23

"Baki gane ni ba ko Aziza" Mutumen yace cikin wata busasshiyar murya. Aziza ta dubi mutumen mai tarin gemu biyu- biyu kamar ciyawa, tabbas bata gane shi ba... mahaukaci ne Tace a ranta. "Baki gane ni ba?" Ya maimaita tambayar. Aziza ta girgiza kai a tsorace. Mutumin yayi murmushi yace "NINE MUSTY!".

BABI NA BAKWAI 7

KANO JUMA'A

JANAIRU 8 6:30 NA YAMMA

Kamar dai Dakta Ali, shima Sunusi tun da sassafe yaso ya sauka agidan su Aziza, to amma shi da yake a gari yake sai yaga kamata yayi ya bari har sai rana tayi sanyi ko kuma ma da daddare. Akwai abin da ya sashi tunanin hakan.

Shekarar da Aziza ta yaudare shi babu irin zagin da abokansa basu yi masa ba. "Ai ga irinta nan, daman sai da nace ka rabu da shegiyar yarinyar nan, in banda abinka 'yan bokon kirki ma ya suka kare da ita ballantana kai huhun ma'ahu" wani ne Basiru ke cewa da shi haka, wani abokinsa kuwa mai suna habu cewa ya yi.
"Kabi a hankali Sunusi, kada ka mutu a banza akan mace, sanin kanka ne yan matan zamanin nan ba imani ne da su ba, imaninsu daya shine kawai idan suna kaunarka". Sunusi dai yaji irin wadannan batutuwa hakanan tamkar busar sarewa ya dauke su. Da yake dai kuma abokansa ne, sai Sunusi yaga bai kamata ba ace ya kware musu baya, kamata ya yi a wannan karon ya Boye mu'amularsa da Aziza har sai abubuwa sun yi karfi tsakaninta dashi.

Karfe shida da rabi dai-dai na yamma Sunusi ya gama shiryawa, sanye yake da doguwar riga da wandonta da farin yadi dan Madina, sannan ya dora bakar dara, kafarsa sanye cikin wani shanyayyen bakin takalmi mai kamar kwale-kwale. Sunusi bai so ya tafi da takalmin ba, to amma babu yadda zai yi domin shi kadai yake da shi na fita kunya. Sunusi ya dada jaddadawa zuciyarsa cewa Aziza shi take so ba suturar dake jikinsa ba, domin in dan ta sutura ne tun farko ma da ba zata taba kallonsa ba ballantana har wata mu'amala ta shiga tsakaninsa da ita.

Kafin ya fita daga gida sai da Sunusi ya dauko tsohon hoton da suka dauka shida Aziza a ranar bikin yaye daliban da suka fara haduwa. Sunusi ya Kurawa hoton idanu baya ko kiftawa, ba'a jima ba sai hawaye ya fara sartu akan kumatun Sunusi. Cikin sauri yasa gefen hannun rigarsa ya goge idanunsa, koda ya dubi gefen hannun rigar sai yaga ya dauki datti, Sunusi bai damu
ba. Karfe bakwai saura 'yan muntuna ya isa tarauni, kai tsaye ya wuce zuwa gidan su Aziza, a zuciyarsa yana cewa oh! Allah mai iko shekaru bakwai kenan da 'yan kato da gora suka tsince shi a kofar gidan su Aziza a sume kaga kamar kwana bakwai.

A dai-dai lokacin da Sunusi ya shawo kwana layin gidan su Aziza ne to yaji gabansa ya fadi. Daga inda yake tsaye yana iya hango kofar gidan su Aziza a cike dankam da mutane. Cikin sauri Sunusi ya karasa kofar gidan, sannan ce to yaji mata suna ta kururuwa a cikin gidan, a kofar gidan kuwa wata kakkaurar mata ce mai fuska irin ta Aziza, tana 'ta kururuwa, wasu magidanta guda biyar suna kokarin mayar da ita cikin gida, matar ta kwalla ihu tana cewa.

"Na shiga uku... na shiga uku wayyo Aziza ta!" Sunusi ya fada a kasa ragwaf ya zauna a kasa domin gwiwowinsa ba za su iya daukarsa ba.

***** ******* ******** ********* ****************

Musty! Sunan ya fara kururuwa a cikin kwakwalwar Aziza. Ba dai Mustin da na sani ba tun kusan shekaru tara da suka wuce. Aziza tayi sauri ta shige da duk jikinta cikin komin wankan domin tik! Take tsirara haihuwar uwarta ga kuma wannan katon tsaye a kanta, Aziza ta zura masa idanu na tsawon lokaci Kiri-kirin Kananan idanun da kuma faffadan bakinsa su
suka tuna mata shi tabbas shi ne. "Musti!" Aziza ta kirawo sunansa rabi a fusace sabi kuma a tsorace. Musty ya saki wani busasshen murmushi idanunsa a tsaye kyam ko kiftawa ba sa yi kamar idanun gawa.

Ashe dai zaki iya gane ni, kinga na tsufa ko, na tara gemu ko, duk wahala ce Aziza, shekaru tara a kurkuku ba karamar masifa bace, kuma duk ke kika janyomin". Jikin Aziza ya dauki rawa, "akwai wani abu a tattare da irin kallon da yake mata wanda ke sa 'yar autar hantar cikinta ke kadawa. Aziza ta dora hannunta biyu akan kirjinta tana kokarin boye tsiraicinta.

"Musti fita daga waje kayi jirana me ye haka me ya shigo da kai kuma bandaki". Musti ya kyalkyale da wata siririyar dariya.

"Af, yanzun ma sharrin fyaden zaki yimin Aziza? Bismillah to kina iya sake ihu kamar wancan lokacin idan kinso, sai dai kuma ina mai dada tabbatar miki da cewa a wannan karon abin da zan yi miki ma yafi fyade.
Aziza taji tsigar jikinta ta yi wani yarrr sannan kamar a faifan majigi sai hoton ranar da ta fara ganinsa ya hasko akan zuciyar Aziza kusan shekaru goma sha biyu kenan da suka wuce.

..... Shekaru goma sha biyu da suka wuce, Musti yana daya daga cikin manya-manyan takadarai dake birnin Kano. Al'amarin Musti ya kai girman da sai dai a zuba masa idanu kawai ayi ta yi masa addu'a amma zancen nasiha kam baima taso ba.

Tun yana karami ya fara da 'yan kananan dauke-dauke, daga karshe ya fara bin kananan barayi suna bin gidajen jama'a cikin dare, sannu a hankali har Musti ya dada samun babban mukami a cikin wasu gungun 'yan fashin unguwa dake bin gidajen masu hannu da shuni suna bugewa su karbi abin hannunsu

Wani abin ban mamami shine, mahaifin Musti babban allajiri ne, hakanan yana mutukar son Musti, domin duk abin da yake so zai bashi, to sai dai kuma sata a jinin Musti take, dan haka duk kudin da mahaifinsa zai bashi bai fiye jin dadinsu ba in har ba ya hadasu da na sata ba.

Ana nan a haka rannan sai su Musti rana ta baci, suka shiga gidan wani tsohon soja suka yiwa matarsa fyade, basu sani ba ashe yana da bindiga, mutumin ya bude wuta, a take a gurin ya bindige mutum uku, Musti ne kadai ya daga hannu sama mutumin ya kamashi ya mikawa jami'an tsaro.

Da yake mahaifin Musti yana da tarin abin duniya kuma yasan manya a sama, Musty ko sati guda bai yi ba aka sako shi sauran kuwa bayan wata guda aka harbesu. Sannu a hankali Musty yana aikata laifuka mahaifinsa na fito dashi har sai da ya aikata irin laifukan guda biyar. A laifi na karshe ne to aka so a harbe Musti. Da kyar-da-kyar mahaifin nasa ya fito da shi. Kafin a fito dashi din sai da aka sa Musti ya sa hannu akan wata takarda a ofishin 'yan sandan ciki cewa daga yanzu idan aka kara kamashi da wani laifi babu sauran afuwa. A wannan shekarar ne to Allah ya yiwa mahaifin Musti rasuwa, sannu a hankali Musti ya shiga barna da abin da ya gada ta hanyar shaye-shaye da nemar mata har dai aka wayi gari Musti bashi da komai.

Wata rana da yamma an dauke ruwan sama kenan, Alhaji Ibrahim ya fito kofar gida sanye da babbar riga domin ya sha iska, yana fitowa sai suka yi ido biyu da Musti, ya jike sharkaf da ruwa, duk ya rame ya sirance akwai alamun yunwa karara jikinsa.

"Barka da yamma Alhaji dan Allah a taimaka min da na abinci wallahi yunwa na ke ji". Alhaji Ibrahim ya dubi Musti na tsawon lokaci, ya dade da samun labarin yaron da takadarancinsa, koda ya sashi gaba yana kallo sai shima ya tuna da sa'ar da yake saurayi kamarsa, ya tuna da irin kahon zukar da shima jama'ar gari suka kafa masa suna cewa dan damfara ne shi, Malamin tsibbune, barawo ne shi, kai akwai ma lokacin da aka taba cewa dashi maye ne. Dan haka duk da ya tababta da cewa duk abin da ake surutu akan Musti gaskiya ne, sai yaga ya kamata ya taimaki yaron me yiyuwa yanzu tun da duniya ta hore kamar yadda suma ta hore su yana iya yin hankali."Zo mu shiga gida kaci abinci". Tun daga wannan rana Musti ya zama dan gida, kafin ya zama dan gidan sai da aka kai gwauro aka kai mari tsakanin Alhaji Ibrahim da matarsa Mariya. "Wacce masifa kuma ka debo ka kawo mana gida! Ka rasa wanda zaka debo sai danfashi barawo, wanda duk unguwa aka yi Allah wadai da shi".

"Baki fahimci abin da nake nufi ba Mariya, irin wadannan yara sau da yawa rashin masu yi musu nasiha ne cikin hikima da kuma rashin kulawa shi yake jefa su a cikin irin wadannan al'amura kinga...."

"Kaga ni dai wallahi ko dunkulen magi idan ya bata a gidan nan shine, haka kawai ka dauko mana wani tsinanne!".

Sannu a hankali Musty ya gama warwarewa, Alhaji Ibrahim ya bashi suturu kulum kuma yasa a ringa bashi abinci. Da yake in yi sa'a ya iya mota, duk inda Alhaji Ibrahim za shi shi yake kai shi. Duk wasu ayyuka a gidan shi ke yinsu. Mutanen unguwar da dama suka yi mamakin wannan sauyi na Musti, to amma duk da haka dai basu sha mamakin sauyinsa baki daya ba bar sai da ya fara haduwa da Aziza.

Ranar wata juma'a da safe Alhaji Ibrahim ya kira Musti da "Je ka dauki mota, Bauchi za muje mu dauko 'yata Aziza yace nan zata yi hutu". Musti ya dube shi cikin mamaki yace. "Daman kana da 'ya?" Alhaji Ibrahim ya yi murmushi yace.

"Ina da 'ya mana, a Bauchi take karatu shi yasa baka santa ba".

"Musti shine mutum na farko da Aziza ta fara kauna a duniya, kauna kuma har zuci, domin bayan Musti bata kara wani mutum da gaske ba sai Usman. Ya kasance tun lokacin da Aziza ta kyalla ido ta ga Musti sai taji yana bala'in burgeta. A lokacin kan ta wayene, domin
ajinta biyu kawai a sakandire. Lokacin da Aziza ta dawo gida hutu kullum bata da abokin hira da ya wuce Musti, musamman ma da yake mutum ne mai ya bada labari. Mahaifiyar Aziza ta lura da abin da ke shirin faruwa, dan haka rannan da yamma Aziza da Musti na zaune a
gindin bishiyar dorawar turawa dake farfajiyar gidan suna hira sai mariya ta kwalla mata kira "Aziza!" cikin shagwaba Aziza ta zo. "Gani Mama mene ne?" Mariya ta dubeta a fusace. "Me kuke yi ke da wannan dan iskan yaron!" Aziza ta dubi mahaifiyarta cikin kaduwa, domin ita bata ga wani abin iskanci ba a tattare da Musti, ita a duk lokacin da ta dube shi burge ta ya ke yi musamman ma faffadan bakinsa idan ya yi murmushi da kuma mici-micin idanunsa.

"Mama---hira fa kawai muke yi". Mariya ta harare ta "Ka da na kara ganin ki kin zauna da shi hira wannan dan iskan yaron ina ke ina shi"
Aziza tayi kunnen uwar shegu da maganar mahaifiyarta, kullum suna tare da Musti dare ne kawai ke rabasu, sannu a hankali Aziza ta fara nunawa Musti kauna, irin ta 'yan mata "yan makarantar gaba da firamare. Alal misali akwai sa'ar da zata sami dakarda ta rubuta ( I LOVE YOU MUSTI) sai ta bashi tace kada ya karanta sai yazo kwanciya, wani sa'in kuwa sai ta kama hanunsa ta rubuta (Abin kaunata) sai tace dashi kada ya bude hannupsa har sai ta bar gurin. Haka dai tayi ta yi masa, har dai Musti ya tsunduma iya wuya, kullum bashi da wani tunani sai na Aziza, idan hutu ya kare ta koma Bauchi har ramewa ya ke yi
kafin ta dawo. Musti shine ya fara koyawa Aziza mota a duniya. Domin lokacin da mahaifiyar ta ta fara mitar sai an koya mata mota an kuma saya mata, sai mahaifinta yace da Musti ya koya mata.

Shekaru biyu suka wuce kamar wasa, Aziza ta dada girma kyawunta ya bayyana, gashi kuma ta fara zama (clean). Dan haka rannan tana zaune gaban madubi bayan tazo wani hutu a lokacin tana aji hudu a sakandire, sai ta fara tunanin lallai fa yanzu ta wuce ajin Musti. Ta lura akwai mazaje masu aji da kima dake ta kawo mata bara, amma tana wulakantasu, saboda Musti, Waye Musti ne? Ta tambayi kanta shin ba mahaifiyarta ta taba cewa da ita dan iska bane. Duk dai da cewa hai taba yi mata iskancin ba, a yanzu ta fuskanci cewa ba ajinta bane....

DATA ƊINA YA KARE JAMA'A MU TARA WANI JIƘON IDAN NA SAKA DATA DIN.AZIZA-24

Waye Musti ne? Ta tambayi kanta shin ba mahaifiyarta ta taba cewa da ita dan iska bane. Duk dai da cewa bai taba yi mata iskancin ba, a yanzu ta fuskanci cewa ba ajinta bane....

Washegarin ranar Aziza taci kwalliya ta fito da safe zata tafi unguwa, sai Musti ya hangota nan da nan ya nufo inda take cikin fara'a "Hajiya Aziza ina zuwa ne?" Aziza ta bata fuska unguwa
zani Musti ya dada dubanta cikin murmushi. "Zo to mu tafi in kai ki" Aziza ta girgiza kai". Ba zani da kai ba menene amfanin motar da na koya. Ta mika masa hanu
fuskarta babu alamun fara'a tace. "Bani dan mukullin motar" cikin kaduwa da tsananin mamaki Musti ya yi mika mata mukullin motar.

A ranar wuni yayi a kwance yana zazzabi. Aziza kuwa bata tashi dawowa ba sai bayan Azahar. Sa'ar da ta dawo Musti na zaune karkashin bishiyar da suka saba zama a farfajiyar gidan suna hira. Da farko sa'ar da ya hangota bai yi kokarin tashi daga gindin bishiyar ba domin ya dauka za tazo kamar yadda ta saba idan ta hangoshi Amma sabanin tunaninsa Aziza ko kallon inda yake bata yi ba sai kawai tayi sanɗa. Cikin sauri Musti ya mike ya tari gabanta.
"Aziza sannu da zuwa, tun dazu nake nan ina jiranki, wallahi wuni nayi bani da lafiya". Yayi mata murmushin karfin hali. Aziza ta tsaya cak tana kallon wagegen bakinsa gami da mici-micin idanunsa, lokaci guda kuma tana mai mamakin dalilin da yasa ma har ta fara son wannan mutumin mai kama da zane. Aziza ta kalleshi sama da kasa ta tabe baki tace "Oh ni kake jira ai gani na dawo". Musti yayi shiru a rude yana dubanta.

"Kaga in babu abin da zaka ce dani zan shiga daga ciki na gaji Musti ya dubeta.
"Aziza, bakice dani komai ba, nace dake yau wuni nayi ina zazzabi". Aziza ta daga girar idanunta ta sama.
"Ayya, kaje kasha magani Allah sauwake" Tana gama fadi sai ta juya da sauri ta shige cikin ginin gidan.

Mako guda ya wuce kamar wasa, a tsahon kwana bakwai nan sau uku kadai Musti ya hangi Aziza, ba ma ta fitowa sai ta fuskanci babanta ya aikeshi, shi kuma ba abin ya tambayi
mahaifiyarta ba yasan ba son sa take ba. Al'amura suka cabewa Musti, ya kasa cin abinci rabonsa kuwa da barci ya fi kwana takwas. Wani abin karin bakin ciki kuma ga Musti, a cikin kwanaki bakwai nan kullum sai wani sabon saurayin Aziza-yazo mata hira, wani dan siriri ne fari mai dogon wuya, yana da mota kirar (Honda Prelude) acikinta suke hira. Kullum haka Musti zai shige dan dakinsa dake kusa da na maigadi yayi bakam! Cikin bakin ciki, yayin da kuma yake jiyo shewar Aziza da sabon saurayinta a waje.

A daren wata laraba ne Musti ya gama kaiwa karshe. hakurinsa ya kare. Dan haka sai yayi abinda rabonsa da yi kusan shekara biyu kenan, tun karfe hudu na yamma ya wuce kai tsaye zuwa sabon gari, yaje ya sha giya yayi tatul kana ya yi bushe-bushe son ransa, bai tashi dawowa ba sai karfe tara na dare. Tun daga nesa ya hango farar motar saurayin Aziza. Musti yayi murmushi kana ya shafi zabirar dake aljihunsa.

Aziza da saurayinta sun shagala da hira, basu aune ba sai suka ji an bude kofar motar bangaren direba, suka juya a firgice, a tunanin Aziza ma ta dauka mahaifinta ne. Sannan ne to suka yi ido biyu da Musti.

"Musti me ye haka!" Aziza tace a fusace. Musti bai ko kalleta ba sai ya damki wuyan saurayin ya kwada masa mari, saurayin ya bude baki zai yi ihu sai Musti ya bude wukar askar akan fuskarsa sannan yace cikin kakkausar murya.
"Kai dan uwarka mene ne hadinka da wannan bebi din!" saurayin ya yi shiru tuni har ya saki fitsari a wando domin duk fadin unguwar babu wanda baya tsoron Musti kowa kuma ya sanshi ya kuma san tarihin tabargazarsa. "Wanan yarinyar Musti ce kaji ko!" saurayin ya gyada kai atsorace

"Daga yau idan na kara ganin ka da ita sai na sassaba kamanninka kaji ko!" Musti ya girgiza shi da karfi saurayin yaji kamar wuyarsa zai balle "Bazan sake gaya ma ba, nan gaba idan na ganka da ita sai dai jikin ka ya gaya ma.
Bace min daga nan kafin nan da minti daya! Musti ya daki bakinsa da karfi. Aziza tayi kara a tsorace sa'ar da jini ya fallatsa akan fuskarta. Musti ya wuce kai tsaye zuwa farfajiyar gidan, ya jingina bayansa da jikin bishiyar da suka saba zama da Aziza. Nayi maganin shege. Yace cikin zuciyarsa, sai dai kuma yana cikin damuwa domin yasan ya gama batawa Aziza rai.

Ba'a yi ko minti guda ba, sai Musti yaji sautin injin motar saurayin ya tuka ya tafi. Bayan wasu 'yan dakiku Aziza ta shigo cikin farfajiyar gidan, kai tsaye ta nufi gaban Musti ta tsaya cikin shasshekar kuka tace

"Ka kyauta abin da kayi min Musty! Yadda ka bakantamin ka sani kuka, kaima sai nayi ma abin da har ka mutu ba zaka manta dani ba". Tana gama fadi sai ta juya aguje ta shige gida. A lokacin da abin ya faru karfe tara da mintuna ashirin.

Karfe biyu saura na dare, Musti na kwance a dakinsa yana ta juye-juye ya kasa barci. Tuni ya fara nadamar abin da ya yi a farkon daren. Yasan cewa sun gama batawa kenan da Aziza. A lokacin ne to ya yi kuskurensa na farko Musti ya mike zumbur cikin damuwa. Bari in je har dakinta na bata hakuri tabbas idan ta ganni cikin uban daren nan tana iya yafemin abin da na yi mata zata san lallai na damu da ita.

Jikinsa na rawa ya shiga babban falon gidan, ya riga yasan kowanne lungu a gidan kamar tafin hannunsa, cikin sanda ya nufi kofar dakin Aziza zuciyarsa na bugawa tsakanin hakarkarinsa. Ga mamakinsa sai yaga akwai alamun haske a dakin Aziza Musti ya mika hannunsa a hankali ya murda mabudin kofar sai yaji a bude yake kamar yadda yake tsammani. Ya tura a hankali ya shiga dakin. Yana shiga sai suka yi ido biyu da Aziza, wacce ke kwance akan gado ta rufe duk jikinta da farin mayafi wanda aka yiwa ado da furanni kanta ne kawai a waje. "Me ya kawo ka kuma dakina tsinanne... ko zuwa kayi
nima ka dake ni Muryar Musti na rawa yace. "Zuwa nayi na baki hakuri Aziza wallahi tsananin kishi da kaunarki ne ya sani na aikata abin da nayi dazu.
"Allah ya yi min tsari da kai, fice min daga daki".

"Bazan fita ba har sai kin yafemin Aziza". A wannan takin lokacin ne dabarar ramuwar gayya ta fado a zuciyar Aziza. "ba zaka fita ba ko?" Aziza ta tashi zaune mayafin da ta rufe jikinta, ta zuro Kafafunta ta sauko daga kan gadon ta na saukowa sai ta jefar da mayafin a kasa. Musti ya dubeta cikin kaduwa, Ashe Aziza tsirara take daga ita sai dan kamfai."

"Me ye haka... Aziza... rufe jikinki" Musti yace muryarsa na rawa. Aziza ta nufo shi a guje tayi tsalle ta rungume shi sannan ta daddage ta kwalla ihu.

"Wayyo Allah na, na shiga uku wayyo Mama!".

Kafin kiftawa da bismillah duk wani mai rai dake gidan ya farka, mahaifiyarta Mariya ce ta fara shigowa dakin aguje.

"Lah-lailaha illallahu... me zan gani yau na shiga uku". Tana zuwa sai ta rukume Musti ta haushi da duka, Aziza ta fadi wanwar a kasa tana ta numfarfashi sama-sama, tana kuka kasa- kasa. Alhaji Ibrahim ya shigo dakin shida masu gadi guda biyu domin sa'ar da ya ji ihun ya dauka barayi ne. Alhaji Ibrahim ya yi turus sa'ar da ya shigo dakin cikin mamaki. Ya dubi Aziza kwance tsirara, ya dubi Musti kana ya dubi Mariya wacce sai kaiwa Musti dan duka take yana karewa.

"Ai dama sai da na fada ma... nace dakai dan iskane gashi yanzu ka kawoshi gida zai tona mana asiri". Mariya ta fashe da kuka, Alhaji Ibrahim ya dubi Musti a fusace yace.
"Ka cika maci amana Mustafa!. Na daukoka a lokacin da kowa yake kinka na janyo ka jikina gashi yau ka tonamin asiri yanzu Musti "yata zaka yiwa FYADE!".

Washegari labari ya watsu a duk fadin unguwar, jama'a da dama basu yi mamaki ba, daman sun dade suna zaton sai wani mummunan abu ya faru a gidan tun da dai Alhaji Ibrahim ya dauki annoba Musti ya kai gidansa.

Da yake ba laifin fashi da makami aka kama Musti dashi ba, sai aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai, sakamakon waccen tsohuwar yarjejeniya da aka yi dashi a ofishin 'yansandan ciki in da ya rubuta da hannunsa akan cewa idan ya sake wani mummunan laifi a yi masa kowane irin hukunci ne.

Daman kuma jami'an tsaro da dama suna tarkon ya sake fadowa hannun shari'a domin ya gama isarsu.... Aziza tayi ajiyar zuciya a cikin komin wankan sa'ar data
dawo daga dogon tunaninta. Duk wannan wani abune da ya faru tun da dadewa "Fita waje... Musti kayana nake son nasa". Aziza tace a tsorace, akwai wani abu a tattare da kallonsa da ke matukar sata kaduwa. Musti ya yi dariya sannan ya baro kofar bandakin ya matso bakin komin wankan yace AZIZA....AZIZA-25

ƘARSHE

Akwai wani abu a tattare da kallonsa da ke matukar sata kaduwa. Musti ya yi dariya sannan ya baro kofar bandakin ya matso bakin komin wankan yace AZIZA
Bakya bukatar wasu kaya a duniya Aziza".

Aziza ta dube shi a tsorace tace muryarta na rawa. "Musti... me zaka yi min" Musti ya fashe da dariya kasa-kasa yace. "KASHE KI ZAN YI AZIZA domin in har kina raye bazan taba jin dadin rayuwata ba". Aziza ta buda baki zata kwalla ihu, cikin zafin nama na mamaki sai Musti ya cafi makoshinta ya shake, sannan ya buga kanta da karfi a jikin tangaran din komin wankan, sa'anan sai ya dannan kanta cikin ruwan, yasa hannu biyu ya dada dannan ta da karfi, tun Aziza na harbe-harbe da Kafafunta har da ta daina motsi, rai ya fice daga jikinta, abu na karshe da ya fado zuciyarta kafin ranta ya fita shine ba zata sake ganin Usman ba.

Ba a gano gawar Aziza ba sai kusan karfe shida da minti ashirin da biyar. A dai lokacin ne to Sunusi ya karaso kofar gidan ya tarar da mahaifiyar Aziza tana ta kururuwa ana rirriketa. A lokacin da Sunusi ya karaso kofar gidan ko gawar Aziza ma ba'a gama tsamowa daga cikin komin wankan ba.

****** ******* ******* ******* ******** **********

Da safe misalin karfe tara saura kwata Dakta Ali ya fesa turare, ya dubi kansa jikin madubin dake dakinsa a Daula Otal. Abin da ya gani ya yi mutukar burgeshi, sai da ya shafe sama da minti talatin yana tunanin rigar da zai sa, domin zai so ace bayan tsahon shekarun da suka wuce Aziza bata ganshi ba, ace yanzu idan ta ganshi taga babu canji da wancan tsohon lokaci, kayan dake jikinsa wata koriyar kwat ce da wandonta, kafafunsa sanye cikin takalmi, sai kyalli yake yana daukar idanu kamar madubi, sannan idanunsa Boye cikin wani farin tabarau, wanda yazo da shi tun daga kasar Rasha a lokacin da yaje karin karatu. Ba wani abu ne ya sa dakta Ali sa wadannan kayan ba sai dan wata rana Aziza ta laba cewa dashi.
"Aliyu, wallahi babu kayan da nake mutuwar son na ga ka sa irin kwat, domin

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

1 month ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment