Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faru cikin shekaru kusan ukun da suka biyo bayan auren Aziza. Dakta Aliyu mutum ne mai yawan hakuri da tawakkali, amma duk da haka sai da ya yi wata guda a asibiti yana fama da hauhawar jini shekararsa daya baya kula wata 'ya mace a duniya.

Kwatsam! Sai suka hadu da Balaraba, wata rana tana fitowa daga cikin asibiti, lokacin da ya ganta, sai da ya kusan faduwa saboda karfin bugun da zuciyarsa ta yi. A tsammaninsa Aziza ce.

"Allah mai yadda ya so" Dakta Ali yace cikin zuciyarsa, kamar ita wallahi, hakika sun yi mutukar kama da Aziza, to amma sa'ar da ta matso kusa sai ya ga ko kashi hamsin bata dauka ba na kyawun Aziza, to amma duk da haka dai sun yi matukar kama a fuska.

Bai san yadda aka yi ba ya sami kansa yana mai yi mata murmushi.

Yan mata wa kike nema...." Ta dubeshi cikin girmamawa. "Dakta Ali na ke nema..

Hakanan cikin sauki, kamar a dirama sai soyayya ta kullu a tsakaninsu. Dakta Ali yayi mamakin irin yadda ya ji kaunarta ta mamaye zuciyarsa. To amma can cikin ransa, shi ya san ba wani dalili bane, sai dan kawai sun yi kama da Aziza.

Wata shida kacal da fara soyayyar aka daura musu Aure. Duk da yake dai sati daya kawai suka yi na farin ciki, to amma shi Dakta Ali yana mutukar jin dadin zama da ita hakanan. Ba dan komai ba kuwa sai dan zama da ita yayi sanadiyyar ginuwar wata katanga a zuciyarsa, katangar da ta dusashe tunanin Aziza daga zuciyarsa, domin kullum idan ya dubi Balaraba sai ya ga kamar Aziza yake kallo, musamman ma a cikin duhu-duhun dare wannan kawai ita ta sa shi yake zama da ita amma in ba dan haka ba, da hanyar jirgi daban ta mota da ban, akwai dalili.
Na farko dai ta cika, almabuzzaranci, kullum a kashe-kashen kudi take sayi banza, sayi wofi, ga ta da rashin kamun kai, mafi muni kuma daga cikin halayyarta shine kusan kullum sai ta fita unguwa, ko da rana, ko da daddare, ko yana so, ko ba ya so dole sai ya yarda. To amma duk da wannan halayya tata Dakta Ali bai taɓa tsammanin zata janyo masa kwarto har dakinsa ba... wannan abu... ya isa ya rusa katangar zuciya duk kwarinta...

Dakta Ali ya yi firgigit, cikin razana. Ashe kofar bandakin ce ake bugawa. Ya mike tsaye da kayan a hammatarsa gami da ajjiyar zuciya, sai yanzu ya fahimci ashe tun dazu tunani ya ke yi dogon tunani mai kamar mafarki. Ya bude kofar bandakin, sannan ba tare da ya dubi kwarton ba sai ya jefa masa kayan yace. "Yi maza kasa kayanka muci abinci" Mintina biyu, kwarton ya gama sa kayan. Dakta Ali ya sako shi a gaba suka dawo cikin falon. Balaraba na tsaye a falon sanye da doguwar riga idanunta jajur dasu kamar garwashin wuta, har sun fara kunbura. "Ina abincin?" Ali ya tambayeta bata amsa masa ba, sai ta sake zubewa a tsakar dakin tana kuka. Dakta Ali ya juya ya dubi KWARTON ABOKINSA yace.AZIZA-09

Dakta Ali ya juya ya dubi KWARTON ABOKINSA yace Wannan magana babu wanda ya santa daga ni sai ku, saboda haka yi tafiyarka na barku da fitowar rana da faduwarta, Allah shine mai sakamako ma fi alkhairi"

"Alhaji Isa ya durkusa yana godiya.

"Bari dan Allah, kai dai ɓacemin kawai da gani kada kasa na sauya niyyata". Kwarton ya nufi kofa cikin sauri jikinsa na rawa.

Dakta Ali ya tsallake matarsa wacce ke zaune a tsakar dakin tana cin uban kuka, ya nufi kan kujerar zai zauna kenan sai wayar tarhon dake dakin ta dauki kara. Jikinsa na rawa ya dauki wayar tarho din domin ya tabbata daga asibiti ne aka gaji da jiransa aka bugo wayar. "Halo" Dakta Ali yace "Na yi sa'a wallahi, na dauka ma ai kana
gurin aiki" wata murya tace dashi daga can daya ɓangaren, akwai alamar doki a cikin muryar.

"Aminu Haruna ne ke magana banza!" "Ah, Aminu, wallahi ban gane muryar ka ba"
"Saurara da kyau Aliyu, yanzun nan ina shirin kwanciya wani abokina daga tarauni, ya kawomin wani labari wai auren mutuniyarka ya mutu?" gaban dakta Ali ya fadi

"Wa kake nufi..." Aminu ya fashe da dariya yace.
"Yarinyar data kusan ta yi sanadiyyar ajalinka, AZIZA nake nufi "Aziza ah!....." bai iya karasawa ba sai yayi shiru, ga mamakinsa sai yaji kwalla ta fara zubowa akan kumatunsa.

"Am.....Aminu, ka jirani a gida, gobe in Allah ya kaimu da sassafe zan sauka a Kano".

"To shikenan amma..." Dakta Ali ya katse shi.

"Kabar komai sai na zo Aminu, kasan fa yadda nake sonta... Me yiyuwa Allah ne ya karbi addu'ata zai yayemin bakin ciki...Aminu.... Ina kyautata tsamanin ni zan aureta a wannan karon, ko da kuwa zan mutu ne...

Balaraba ta nufo in da yake tana kuka sa'ar da taga ya ajje kan tarho din.
....Aliyu...ina zaka tafi....gobe ka yi hakuri dan Allah". "Ni babu abin da kika yimin, aure dai na hakura dashi, kije na

sake ki saki daya". Balaraba ta fashe da kuka, "...Wajen wa to zaka a Kano?"

"Gurin AZIZA.... Wacce a sanadiyyar ta ne ma har na auri kwartuwa kamarki! Allah ya dawo min da masoyiyata ita zan Aura.

BABI NA UKU 3

BAUCHI

TALATA

JANAIRU 5

6:AM NA SAFE

Yusif yayi tsalle gefe guda hannunsa akan fuskarsa jini yana ta zuba ta baki ta hanci.

"Ke! Kina da hankali kuwa dubi fa abin da kika yimini"

Yace da matar dake kwance akan gadon kusan duk rabin jikinta tsirara kanta babu dan kwali.

"Kadan ma ka gani mitsiyaci! Yanzu ma na fara.. wallahi in baka bani takarda ta ba, ni zan yi ajalinka!"AZIZA-10

BABI NA UKU 3

BAUCHI

TALATA

JANAIRU 5

6:AM NA SAFE

Yusif yayi tsalle gefe guda hannunsa akan fuskarsa jini yana ta zuba ta baki ta hanci.

"Ke! Kina da hankali kuwa dubi fa abin da kika yimini"
yace da matar dake kwance akan gadon kusan duk rabin jikinta tsirara kanta babu dan kwali.

"Kadan ma ka gani mitsiyaci! Yanzu ma na fara.. wallahi in baka bani takarda ta ba, ni zan yi ajalinka!" matar tace dashi cikin karaji. Jini ya ci gaba da zuba akan fuskarsa. Yusif ya sa hannun rigarsa yana taro jini, sannu a hankali sai hannun rigar ya fara rinewa da jini. "Dubi fa abin da kika yimin?" Yusif ya sake nuna mata fuskarsa cikin takaici.

"Nace da kai yanzu ma na fara! In dai naci ne aikinka, to wallahi ka kusa ka rasa aikin yi domin nacin ya kusa karewa..." ta yi shiru tana maida numfashi sannan ta ci gaba. "Bance da kai kada ka kara raɓar inda na ke ba..?" Yusif ya katseta

"Kada ki zargeni Nafisa, kin san biyayya kawai nake ga iyayena shi yasa na ke zaune, amma in badan haka ba ke kin san ba ma ke ba, wata 'ya mace ma a duniya na gama soyayya da ita ballantana har azo ga zancen aure".

Fuskar Nafisa ta yamutse sa'ar da ta ji abin da yace. Wani masifaffen kishi ya soki zuciyarta. Babu abin da ta tsana a rayuwarta irin mijinta Yusif hakanan kuma babu abin da take tsananin kishi da shi kamarsa.

AMMA SAIDAI KASH......
DAGA AZIZA....AZIZA-11

Fuskar Nafisa ya yamutse sa'ar dataji abunda yace wani masifaffen kishi ya soki zuciyarta babu abinda ta tsana arayuwarta irin mijinta Yusuf hakanan kuma babu abinda take tsananin kishi dashi kamarsa.

Abin ya zame mata kamar jaraba, gashi dai ta Tsane shi kamar mutawarta amma da zarar ya tuno mata dalilin da yasa aka hada auren gida, sai ta ji zuciyarta na soyewa... domin ta san har yanzu ya fi son waccen tsinanniyar da ita. "To ba sai ka sake ni ba! ni nace bani sonka... kuma in kana da zuciya to yanzu ma ka rubuta min takarda ta ka bi ta can gidan mijn ka aure ta!"

"Abin da nake fata kenan a kullum". Yusif yace da ita, har yanzu hannunsa a dafe ya ke da fuskarsa, jinin ya fara tsayawa.

"Har kwanan gobe Nafisa, ban taba fitar da ran za ta fito na aureta ba, in ma gatse kike yi to kaicon ki, bakin cikin ki, domin abin da kike fadi tamkar addu'a ce a gare ni, ina fatan Allah Sarkin komai ya biye bakinki... Nafisa".

Hakan da yace shi ya dada harzukata, taji ta kuma tsanarsa, hakanan kuma kishi mai tsanani ya lulluɓe zuciyarta.

"To... to naji... in dai kana da zuciya, in kana yiwa uwarka da ubanka ka bani takarda ta yanzu ka koma gurinta. Yusif yaji wani abu ya soki zuciyarsa zai iya jure komai amma banda zagin iyaye. A karo na farko tun sa'ar da aka daura masa tanbaɗadden auren sai yaga lokaci ya yi da ya kamata ya saki wannan tsinanniyar mata. Tuntuni daman biyayyace ta sa shi zama da ita. "Ka yi hakuri Yusif, bi ta a hankali yarinya ce, za ta daina duk abin da take"
Wata kakarsa ce ta taba cewa da shi hakan sa'ar da 'yan uwa suka sa shi a gaba a ranar fadansu na farko da Nafisa. A shekara daya da daurin aurensu sun yi fada sau ashirin da takwas, ko yaushe shi ake baiwa hakuri.

Yusif ya dubeta cikin kunan rai ya ce..

"Ta shi ki hada kayanki, yan zunnan zan rubuta miki takarda". Nafisa ta mike a fusace ta nufi falo, kanta ba dankwali, rabinta tsirara tana cewa.
"Ta fi nono fari...Sai ka bita gidan mijin ka dawo da ita ta maye gurbina" Ta mako kofar dakin da karfi har dakin ya girgiza.

Yusif ya nufi kan teburi da niyyar ya dauko takarda domin akwai alkalami a cikin aljihunsa, to amma sai ya ji duk ya gaji, don haka sai ya zauna jagwaf a bakin gadon.

Hakika ya gaji da abubuwa da dama, na farko dai a yanzu ya gaji da cin mutuncin Nafisa, abaya dai ya hakurcewa izgilancinta da dama amma a yanzu bai iya jure zagin iyaye sa gashi har ta fara barazanar kashe shi me yayi zafi? Ya tambayi kansa Ba Nafisa kadai Yusif ya gaji da ita ba, hakika ya gaji da kunar zuciya kunar zuciyar da a kullum sai karuwa ya ke yi duk kuwa da cewa yau kusan shekars tara kenan da yiwa zuciyar tasa rauni "Sai ka bi ta gidan mijinta ka auro ta" wannan kalma ta Nafisa ita ta famawa Yusif tsohon raunin dake zuciyarsa, sakamakon hakan yasa jinin da ke zuba cikin zuciyarsa a yanzu ya fi wanda ke zuba kan fuskarsa

Dama ace.... Inama ace Allah ya biya bakin Nafisa hakance kawai za ta iya warkar da ciwon dake zuciyarsa ya aureta ina ma Ya dade da fitar da rai, duk kuwa da cewa har yanzu tunaninta na
nan cikin zuciyarsa kamar ma a lokacin abin ya faru. Kullum idan Yusif ya tuna da farkon al'amarin ya kan ce TSAUTSAYI

Tsautsayi to mana. Tun da dai shekarunsa bakwai a makarantar "yan mata dake misau, amma dai-dai da rana daya bai taɓa sakin fuska a gaban kowacce daliba ba ballantana ma har a yi zancen wargi. Ya yi kaurin suna a gurin dalibai, domin bashi da wasa hakanan idan daliba tayi laifi to bulala mafi kankanta ita ce bulala biyar. Haka kawai ma babu laifin komai idan Malam Yusif ya ga dama sai yayi musu bulala. Wannan ce ma tasa har 'yan matan makarantar suka sauya masa suna suke cewa dashi Malam YUSIF ZAZZAƁI.

Kwatsam rannan sai aka jefa Malam Yusif wani aji biyar na 'yan mata dake makarantar domin ya koya musu lissafi, domin abin da ya karanta kenan.

A ranar da ya fara koyarwa ta farko ce to tsautsayin ya afku. Lokacin da Malam Yusif ya fara rubutu akan allo sai ya fara jiyo surutu kasa-kasa daga can bayan ajin. Abin ya bashi mamaki, domin a yadda ake jin tsoronsa a makarantar ko wucewa ya zo yi ta kusa da aji sai ka ji an yi shiru. Amma abin mamaki sai gashi yau yana cikin ajin ma amma ana surutu.

Ya juyo a murtuke yana kallon daliban. "Ina shugabar daliban ajinnan?" ya tambaya wata 'yar siririyar budurwa ta mike tsaye kanta da jan dankwali. "Rubutamin sunan wacce ke surutun nan a baya, idan an koma ofis ki bata sunan a takarda ta kawomin ofis da kanta". Sauran daliban suka yi ajjiyar zuciya cikin kaduwa, lokaci guda kuma duk kawuna suka juya suna duba izuwa yarinyar da ita suke tsammanın ta yi surutun
"Yau...ta shiga uku" wata yarinya tace cikin zuciyarta Jikinta na rawa. Ya taba yi mata bulala goma.

Bayan an tashi daga makaranta sai dalibai suka yi cincirindo awata bishiya da ke can nesa da ofishin, Malam Yusif, duk sun kasa kunnuwa suna jira su ji yarinyar ta fara ihu. Yusif ya ajjiye 'yan littattafansa na lissafi da guntun allin da ya rage akan teburi sannan ya mika hannunsa ya bude tagar ofishin saboda tuni har ya fara gumi saboda zafi. Budewarsa ke da wuya sai duk 'yan matan da ke tare a gindin bishiyar suka watse cikin fargaba domin daga inda yake yana iya hangensu ta tagar ofishin. Yusif ya yiwa kansa murmushi, shi kansa yasan yadda dalibai ke tsoronsa.

Ya zauna a hankali akan kujerar dake ofishin sannan ya zaro katuwar bulalar ya dora ta akan teburin. Sa'annan ya lumshe idanunsa yana tinanin irin horon da zai yiwa yarinyar idan ta shigo, domin rabon da wata daliba ta yi surutu yana cikin aji har ya manta.

Bulala goma... wata zuciya tace dashi... a'a bulala biyar dai da share-sharen bandaki... haka dai yayi ta tunane-tunane. Har sa'ar da yaji an yi sallama.

"Salamu alaikum" wata zazzakar murya mai taushi ce tayi sallamar. Ba wai zakin muryar bane kawai ya bashi mamaki, akwai wani inganci a cikin sautin muryar da ya sa zuciyarsa harbawa, domin babu alamar rawa ko kuma rauni a cikin muryar, saɓanin sauran dalibai da idan suka yi laifi da kyarma suke iya buda bakinsu a gabansa.

Abin ya zo mishi a bazata domin bai taɓa tsammanin yarinyar da zata zo masa a matsayin mai laifin ba kyakkyawa ce.
Ya kasa motsi na 'yan dadiku yana duban hikimar Ubangiji, 'yar budurwar dake tsaye a gabansa kyakkyawace kamar balarabiya, kai ko a cikin litttafin hotuna na zaben sarauniyar kyau na kasar masar da ya taba gani, bai ga mai kyawun wannan matashiyar budurwa dake gabansa ba.

Yusif yayi mamakin kansa sa'ar da yaji ya sassauta muryarsa yace.
....kece kike mana surutu a cikin aji" Yarinyar ta dan sunkuyar da kai sannan ga dadin mamakinsa sai wani tattausan murmushi ya subuce daga madai-daicin bakinta.

"Aisha kawai nake yiwa magana, ita ma cewa na yi da ita ina sha'awar yadda kake rubutu Malam Yusif kura mata idanu a rude, shi kansa bai san abin da ya kamata yace da ita ha. To amma saboda son ya sake jin dadin zazzakar muryar sai yace. "Kuma ke wato ba za ki iya bari ba har sai an tashi ba ko?"

"Yar budurwar ta sake dubansa cikin kunya kunya dariya dariya
"Ka yi hakuri Malam, ni da na dauka idan an yabi mutum farin ciki yake yi shi yasa na fadi da dan karfi ko ka ji" Zuciyarsa ta harba me take nufi?
"Ba'a wasa a wajen karatu, in za ka yabi mutum sai ka bari sai kai dashi". Bai son ya daina jin dadin muryar so yake tayi ta magana yana saurarenta. Abin kuma da ya fi bashi mamaki shine da duk zamansa a makarantar bai taɓa sanin taba.

"Ina fatan nan gaba za ki kula, domin idan kika sake zamu gauraya dake".

"A wani abin da ban ba", "yar budurwa tace cikin zuciyarta. "Ina fatan kin gane?" Ta gyada kanta cikin gamsuwa sa'annan sai tayi abin da ba'a taɓa yi masa ba. Ta matsa kusa da teburin da yake gabansa, ta taba katuwar bulalar sannan tace.
"Kai...Malam.... Wannan idan ka daki mutum da ita ai matuwa zai yi". Sannan sai ta juya abinta tana cewa.
"Malam na gode gobe kenan idan ka zo aji..." " "Tsaya mana" Ta juyo tana dubansa cikin dan ladabi.

"Ina takardar da nace a rubuto sunanki a baki ki kawo?" "Af... wallahi mantawa na yi". Ta lalubi aljihunta, sannan ta mika masa lokaci guda kuma ta juya abinta ta nufi kofar ofishin. Yusif yayi ajiyar zuciya, lokaci guda kuma ya dubi sunan da ke jikin takardar an rubuta. AZIZA.

Ya dago kansa a dai-dai lokacin da ta kai daf da kofar ofishin, sai ta juyo suka bada ido, ta jefe shi da murmushi, sannan ta fice daga ofishin tana rausaya ta barshi a nan yana duban kofar ofishin cikin kaduwa.

To amma kuma daliban dake waje suna jiran suji ihun kukanta, su suka fi kowa kaduwa sa'ar da suka hangeta ta fito tana murmushi, hakoranta farare sol kamar gonar AUDUGA.

******** ******** ******** ********* ***************

Labarin soyayyar Malam Yusif da dilbarsa Aziza ya fara yaduwa sannu a hankali cikin makarantar kamar gobarar daji. To dalibai na yi a Boye har suka fara fitowa fili, musamman ma ranar da aka wayi gari an tsige shugabar daliban makarantar an nada Aziza

Kwarjinin Malam Yusif ya zube a don dalibai, suka daina tsoronsa, daga Karshe kuma suka fara raira wakoki, na zambo, Wata rana da daddare Malam Yusif yaje gidan su Aziza suna hira
sai tace dashi. "Ka da ka damu da duk abin da suke yi ma... wallahi abin ma damuna domin na fahimci soyayarka da ni ta janyo ma zubewar mutunci... ka yi hakuri... In Allah ya so duk bakin cikinsu sai mun yı Aure an ga 'ya'yanmu". Malam Yusif yayi murmushi farin ciki. Bai cika yawan magana ba, ya fi so ya yi ta sauraren daddadar muryarta. A ranar a farfajiyar tangamemen gidan su Aziza suke, hasken
farin watan ya dada kawata furannin da ke zagaye da farfajiyar.

"Na manta ban fada maka ba" Malam Yusif ya dubela da murmushi
"Me kike son fada?" "Na kusan komawa garinmu, da mun gama jarrabawar karshen nan zan tafi" Ya dubeta a karo na biyu cikin mamaki zuciyarsa na bugawa. "Ban fahimce ki ba... ina kike son tafiya?" Aziza ta sunkuyar da kai tana wasa da awarwaron dake hannunta.

"Ai kasan nan ba gidan mu bane tun ina karama kanwar babata ta daukoni daga KANO ta dawo dani gurinsu, to shine babana ya aiko yace idan na gama sakandire a maida ni can, domin wai... shi a Jami'ar Bayero yake son naci gaba da karatu".

Yusif yayi jim kamar ruwa ya cinye shi, zuciyarsa ta fara kuna nan da nan gumi ya fara kwarara a goshinsa.

"Haba Yusif.....mene ne kuma na damuwa ai ba mun rabu da kai ba kenan" Aziza tace dashi lokacin da ta ga halin daya fada. Yusif ya dago kai kamar zai fashe da kuka.
"Ai dole ne na damu Aziza, domin rabuwa da ke ba karamar masifa bace a gurina...kuma..kuma... kin ga kenan a yadda kike fadi sai kin gama jami'a za muyi aure... shekaru hudu!" Aziza ta matso kusa dashi ta dafa hannunsa tace.

"Alkawari ne Yusif, duk tsanani, duk tsawon lokaci, duk nisan inda nake duk tsawon zamani, ina nan tare da kai, ai shekara hudu tamkar kwana hudu ce.........

ABINDA BAISANI BA SHINE.....AZIZA-12

Shekara Hudu Ai tamkar kwana hudu ce, kuma zancen ganina abune mai sauki, duk hotu zan ke zuwa nan garin mu Kare hutun da kai, hotunana ba za su yanke maka ba... duk da yake dai babana yana da tsanani... Ba zai taba barina na tsaya da wani saurayi ba nasan halinsa, to amma kullum in kana so, zamu iya yin hiramu ta wayar tarho" Hakan da tace shi ya fi tayarwa da Yusif hankali.

"Kina nufin kenan ba zan sake ganinki a zahiri ba sa bayan shekara hudu Aziza ta yi sauri ta girgiza kai tace.

"Haba Yusif, ba nace da kai zan ke zuwa hutu nan ba?" Yusif yayi shiru numfashinsa sama-sama ya kasa magana, domin bai san kuma abin da zaice ba, Aziza ta dada kamo hannunsa, ta dora akan
cinyarta tace. "Ka rike alkawari Yusif, ni dai bani da kowa sai kai... kai zan Aura!"

Shekaru hudu suka wuce. To amma sun wuce da abubuwa da dama, domin saboda yawan fashi da rashin kulawa kan aikinsa, aka kori Yusif daga aiki. Bashi da tunani sai na Aziza. Daga baya ya sami aiki a wani gidan gona. Da farko bayan Aziza ta bar bauci, kullum sai sun yi hira da Yusif ta tarho, daga baya kuma suka dawo sati-sati kai daga karshe ma sai da takai a wata sai da kyar yake iya samun darajar yin magana sau daya da ita a tarho.

Tunda ya rage shekara guda Aziza ta gama karatu a Jami'ar Bayero, Yusif ya gama hada kayan aurensa. Ya rage wata daya ta kammala karatunta Aziza tlma bugo masa waya.
"Yusif...burinmu ya kusa cika yau saura wata daya mu kammala... ina fatan dai har yanzu ina ranka... domin ni ko barci ba na yi saboda kaunarka.

Yusif ya dade bai ji magana mai dadin wannan ba, domin a yanzu ya tabbatar cewa har yanzu yana zuciyar AZIZA

Karfe shida na safe Yusif ya fito kofar gida yana sake-sake kwanan Aziza uku da kammala jarabawarta, amma har yanzu shiru ba wani labari, domin a wayar da ta bugo masa ta karshe ta ce dashi da sun gama za ta bugo masa waya. Tun ana sauran kwana biyar su kammala, Yusif ya sayi katuna masu tsadar gaske ya aika mata kyautarsa na nuna murnar kammala jarabawarta.

Karfe shida da minti goma ne to Saddiq ya sami Yusif zaune a fofar gida daga shi sai gajeren wando. Saddiq da ne ga marikiyar aziza a nan Bauchi, Yusif yana son yaron, domin a lokacin da Aziza tana nan Bauchi, idan ya je hira Saddiq ne dan aikensa. Haka nan kuma idan ta aiko da hotuna shi ke kawo masa. Ya taba cewa da Yusif "Yaya Yusif, Allah sa ka auri Yaya Aziza" wannan itace addu'a mafi dadi da Yusif ya taba ji a shekarar.

Yusif ya tari yaron cikin farin ciki sa'ar da ya hangoshi. "Sannu da zuwa Saddiq, farin jakada, nasan da labari" Yusif yace yana dariya, Saddiq shima yayi dariya sannan ya mikawa Yusif wata Katuwar ambulan ruwan kasa.

"Yaya Aziza ce tace a kawo maka, shi ya sa na zo da sassafe dan kada ka tafi gurin aiki". Cikin doki, Yusif ya mikawa yaron naira hamsin, sannan ya shige gida, bai ko tsaya ba a farfajiya sai ya wuce dakinsa ya rufe kofa. Ya zauna a bakin gado, yana bude ambulan din, akwai alamar
murmushi a fuskarsa, domin ya tabbata sakon farantawa ne kamar
yadda ta saba. Ko da ya zazzage abubuwan dake cikin ambulan din sai ya ji gabansa ya fadi, murmushin dake fuskarsa ya subuce. A cikin ambulan din 'yar madai-daiciyar kalanda ce rangadadau, wacce ke dauke da hoton wani kyakkyawan saurryi wankan tarwada shi da AZIZA. Hannunsa na rawa ya dauki wasikar da ke kusa da hoton ya fara karantawa, domin a tunaninsa wasikar na iya faranta masa...

YUSIF
Ina mai bakin cikin bayyana maka cewa mahaifina ya daura min aure da wani domin wai 'yarsa ba za ta iya auren tsohon malamin makaranta ba.

.....Har a nade kasa ba zan daina kaunarka ba. Ka rike hakan a zuciyarka....

AZIZA

Karfe goma sha biyu na rana mahaifiyarsa... Hajjo ta same shi kwance a dakin hoton a gabansa kamar matacce kafin magriba kuwa duk gidan babu wanda bai san da labarin ba, saboda masifar mahaifiyarsa.

"Ai kin banza... to kada Allah ya sa ta aureka din! shegu marasa mutunci za su kashe min da!, kaga tashi zaune daina kuka.... Yan mata ga su nan kamar jamfa a Jos... kuma in Alah ya yarda kaima cikin watannan za ka yi aure... Ga NAFISA nan 'yar gidan kanwata Hajara ta Gombe, sai mu hadaku daman tuntuni muke yi maka tunaninta, amma gudun taurin kanku ne yaran zamani yasa muka yi shiru tun da munga kana soyayya da wannan tsinanniyar AZIZA din!

Shekaru tara kenan da faruwar duk wannan badakalar. To amma har yanzun nan da Yusif ya ke zaune bakin gadon, yana iya jin maganar ta mahaifiyar sa na ruruwa cikin kwakwalwarsa TSINANNIYAR AZIZA DIN!

Duk da abin da Aziza ta yi masa, duk da cewa kuma mahaifiyarsa ce ke maganar, sai da tsinuwar da ta yiwa Aziza ta kona masa rai. Domin duk abin da ya faru-dai-dai da dakika daya bai taɓa ganin laifin Aziza ba sai na iyayenta". Har a nade kasa bazan daina kaunar ka ba" maganar Aziza ta fado masa a zuciya.

Nafisa ta fado cikin dakin a fusace tana huci, amma a wannan karon da sutura a jikinta "Ba ni takarda ta" Yusif ya mike tsaye, kalaman Aziza na shekaru tara

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

5 months ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

4 months ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment