Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai a hankali". Aziza ta gyada kai ba tare da ta dube shi ba.

"Usman ina so na taimake ka, saboda matsayin da ka ke dashi a gurina". Usman ya dimauce, jiya-jiyan nan fa suka fara magana, wane matsayi zai samu haka da gaggawa?

"Ban fahimce ki ba".

"Kyauta na ke son na yi ma da kuma wani kwakkwaran alkawari. "Aziza ta karshe maganar da 'yar dariya, sannan sai ta janyo wata bakar jaka dake gaban motar ta ta bude ta, daga cikinta ta zaro damin kudi guda hudu ta mika masa. Usman ya dubeta cikin kaduwa.

"Na mene ne wannan??"

"Kyauta ce na yi ma Usman, ka san kuwa babu mai mayar da hannunta baya sai shaidan" Ta dora masa kudin akan cinya.

"Amma... Aziza wannan ai sun yimin yawa!" Aziza ta harare shi. "Yawa!, wane irin yawa? Kasan kana bukatar sababbin kaya... Ina jin sai na karo maka ma wasu gobe". Usman ya sunkuyar da kai saboda tsabar mamaki da kaduwa. Tsahon lokaci kafin ya dago kai ya dubi Aziza yace.

"Ban san irin godiyar da zan yi miki ba Aziza... Bani da kamar ki a duniya". Aziza ta ji wani dadi ya lullubeta jin cewa bashi da kamarta a duniya, cikin jin dadi ta matso kusa dashi ta dafa hannunsa tace.

Usman a zuciyarka fa? Usman yaji kwakwalwarsa tafara juyawa. "Aziza ki tsaga zuciyata gida biyu... za ki ga sunanki a rubuce." Aziza taji kamar ta rungume shi......

Aziza tayi firgigit ta dawo daga dogon tunanin da ta tsunduma, maganar mahaifiyarta take ji tsaye akanta. "Aziza wane irin tunani kike yi har zan yi kiranki sau biyar baki ji ba".

Aziza ta girgiza kai ta mike tsaye kana ta dubi agogo. Me 'yahana shi zuwa ne har yanzu". Ta tambayi kanta.

"Ana sallama dake a waje, kiyi sauri kuma ki dawo, kina jin dai irin cacar bakin da muke ta fama da mahaifinki duk a kanki. Aziza taji gabanta ya fadi, kana wani dadi ya lullubeta, tabbas shine yazo yaushe rabo da ta gan shi. "Yanzu zan dawo MAMA" tace cikin fara'a kana ta nufi farfajiyar gidan aguje, tana zuwa sai tayi turus gabanta yayi mugun faduwa. Mutumin da ke tsaye yana dubanta shine mutum na karshe da Aziza take Sammanin gani a duniya, ko shakka bata yi shine, tsohon Malaminta a makarantar Sakandire dake Bauchi, haka nan tsohon saurayinta, tabbas shine rabon da ta ganshi yau shekaru bakwai kenan.

(Ka rike alkawari Yusif, ni dai bani da kowa sai kai... kai zan aura!) maganar da ta fada masa ta karshe ta fado a zuciyarsa tabbas shine. "YUSIF... kaine yau a gari" Aziza tace da mutumen a.
sanyaye. Ya yi ajiyar zuciya yace. "Nine AZIZA, ashe dai baki manta da sunana ba. Aziza ta dubeshi da murmushin yake tace. "In banda abinka wa zai manta da tsohon MALAMINSA?

BABI NA SHIDA 6

KANO

JUMA'A-8 JANAIRU

3:50pm NA RANA........AZIZA-19

BABI NA 6

KANO JUMA'A

JANAIRU 8 3:50PM NA RANA

Karfe biyu na rana dai-dai Dakta Aliyu ya iso Kano cikin motarsa ruwan kasa Kirar Honda, tuni har an rufe shatale-talen gyadi-gyadi da wani dogon karfe sakamakon sallar juma'ar da ake gudanarwa a masallacin Aliyu bin Abu dalib, hakan shi ya tilastawa Dakta Aliyu sallah a masallacin, sabanin yadda ya yiwo niyya tun farko cewa zai yi sallah a masallacin cikin gari".

A yadda Dakta Aliyu ya yi niyya tun a daren jiya, yaso ya iso Kano tun da sassafe, to amma hakan bai yiyu ba, sabanin wani tunani da ya zo masa a zuciya. Bai kyautu na je wa Aziza haka zikau ba, ya kamata in je mata da kyaututtuka na musamman. Yace da kansa, wannan shi ya sa shi jinkiri domin sai da ya biya ta banki ya karbo kudi, kana kuma bugu da kari a kayi rashin sa'a a ranar wata kanwar mahaifiyarsa ta tashi a jigace daman ta dade tana fama da hauhawar jini, sai bayan da ya gama duddubata ya tabbatar da yayi mata duk abin da ya kamata kana ya kamo hanyar Kano, in banda matsayin Aziza a cikin zuciyarsa, da babu abin da zai kawo shi birnin Kano a ranar, to amma Aziza ita ce jinin jikinsa, tunaninsa, da duk wata basira
Tasa, dakta Aliyu ya tabbata da ace a ranar zai yiwa wani majinyacin tiyata, babu abin da zai hana shi manto almakashi a cikin mutumin.

Karfe biyu da rabi saura ya baro masallacin. Aliyu bin Abitalib, kafin ya baro sai da yayi doguwar addu'a yana rokon Allah ya bashi Aziza. A haka ya kamo hanya, har ya kawo shatale-talen gidan Murtala zuciyarsa tana ta wasi-wasi, da farko da yayi niyyar ya wuce kai tsaye zuwa Tarauni gidan su Aziza, can kuma sai wata zuciyar ta ce da shi gara ya fara biyawa ta gidan su abokinsa Haruna domin ya sami cikakken abin da ke faruwa, wannan shawara ita Dakta Ali ya fi amanna da ita, sai dai kuma duk da hakannan ya kamata ya nemi masauki mai kyau, domin yasan a kalla zai dauki mako guda kafin ya gama da al'amarin Aziza, wanan ita ta sa shi kai tsaye ya wuce zuwa Daula Otal ya kama daki.

Karfe uku da minti arba'in da bakwai ya isa Daula Otal. Ba'a dade ba ya gama biyan kudin dakin na sati guda, kana wasu samari guda biyu sanye da kodadaddun wandunen jeans, da fararen shat suka dauko masa jakunkunansa guda biyu suka rako shi har zuwa dakin. Dakta Ali ya yi musu godiya gami da mika musu tukwicin Naira dari biyu.

Bayan samarin biyu sun ajje jakunkunan sun fita, sai Dakta Ali ya nufi tagar dakin ya budeta ba tare da ya dubi inda na'urar sanyaya dakin take ba domin, ga ra'ayinsa sau da yawa yafi shiri da tsabtatacciyar iska daga Subhanahu Wata'ala fiye da na'urar sanyaya daki, idan kaga ya kunna na'urar sanyaya daki, to tabbas akwai karancin iska a ranar.

Dakta Ali ya juyo ya yi nazarin dan madai-daicin dakin shakatawar, babu laifi yace a ransa, daben dakin a malale yake da jan kilishi, akwai kujera mai taushi doguwa guda daya, gami da Kanana guda shida sun zagaya sun bada surar bakin (U), daga can Bangaren kudu na dakin wani dan teburi ne mai siraran kafafu kamar wani zakaran kekuwa yana dakon wata katuwar talabijin kirar (Panasonic), wata mata ce a tashar (Channel O) tana famar ihu a matsayin waka, cikin sauri Dakta Aliyu yanufi talabijin din ya rage sautinta, kana ya leka dakin kwanciyar, dake kallon falon kai tsaye. Dakin ya yi mutukar burge shi musamman ma gadon da luntsumemiyar katilar mai numfashi dake kai.

Dakta Aliyu ya cire rigarsa ya jefa akan gadon kana ya buda daya daga cikin jakunkunansa ya zaro tawul din wanka, cikin sauri ya nufi bandaki. Ba'a dade ba ya fito, mintina biyar da faruwar hakan ya gama kimtsa kansa, sanye yake da doguwar riga ta shadda galila shudiya, kansa sanye cikin dara, sai dai taso tayi masa yawa, kamar hular gado.

Dakta Aliyu ya nufi tagar dakin ya leka zuciyarsa na ta wasi-wasin abin da ya kamata ya fara yi. Da farko dai ya yanke shawarar ya bugawa Aziza waya ya sanar da ita cewa yana gari kuma gashi nan zuwa, sannan in yaso daga baya ya bugawa abokinsa Haruna waya sai yazo nan Otal din ya same shi. Dakta Ali na nan tsaye gindin tagar yana kallon fulawowi da furanni gami da 'yan gajerun bishiyoyi irin na ado, amma dangin bishiyar dabino, sai ya hangi wata mata ta fito tana zagawa a cikin furanni. Nan da nan sai Dakta Aliyu yaji zuciyarsa ta fara harbawa das-das kayan da matar tasa sun yi matukar burge shi, tuni har zuciyarsa ta fara fada masa cewa da a jikin Aziza suke da sai sun fi kyau nesa ba kusa ba, tun da dai ita wannan matar ko daya bisa hudun kyawun Aziza bata dauka ba. Idanun dakta Ali suka kai kan dandasheshen takalmin dake kafar matar, zuciyarsa ta dada kadawa, "Tabbas wannan ma zai yiwa Aziza ta kyau" yace cikin zuciyarsa. Ga mamakinsa sai yaji yana mai tsananin shaukin ya dora idanunsa akan Aziza, ya kuma saurari muryarta mai kamar sarewa wacce rabonsa da ita yau kusan shekaru hudu kenan. Dakta Aliyu na nan tsaye ya kurawa kayan dake jikin matar idanu yana kokarin haddace kalarsu, katsam babu zato babu tsammani sai matar ta waigo suka hada idanu dashi, kallon da ya yiwa jikinta ne ya bata cewa ana kallonta, suka dubi juna na tsahon dakiku shida bakwai, sannan ga mamakin Dakta Aliyu sai matar ta dago masa hannu cikin murmushi sannan lokaci guda ta boye kanta cikin shuke-shuken. Dakta Ali yayı ajiyar zuciya. Sa'annan ya juyo cikin sauri ya nufi inda tarho yake ajje a gefen teburin da talebijin din take, yana zuwa sai ya danna sifili sannan ya kara kan talfon din a kunnensa, ba'a dade ba aka amsa masa a canɗakin karɓar baki.

"(Yes), kana bukatar wani abu ne?" wata zukekiyar murya mai rawa ta tambaya, akwai alamun ladabi a cikinta duk kuwa da cewa mai maganar ba ganin dakta Aliyu yake ba.
"Da Allah a ina zan sami kayan sawa na mata masu kyau a garin nan". Aka yi shiru na dan lokaci a can daya bangaren, Dakta Ali bai yi mamaki ba domin yasan tambayar tasa na da ban mamaki. A dai-dai lokacin da ya fara tunanin ko ya sake yin tambayar ne sai yaji ance dashi.

"Kana iya bincika WELL CARE, suna nan gabas damu, da ka fita daga Otal dinnan gabas za kayi ka ci gaba da duban hannunka na hagun zaka ga kantin".

"Na gode" Dakta Ali yace, sannan ya mayar da kan talfon din kan uwar goyonsa ya kura masa idanu. Tsahon lokaci yana nan haka, daga karshe sai ya dauki dan mukullin motarsa ya mike da nufin tafiya (WELL CARE) domin sayowa Aziza kyauttuka na musamman, to amma sai yaji a zuciyarsa ba zai iya kara minti biyar ba bai ji muryar masoyiyarsa Aziza ba! cikin sauri ya koma ya zauna, sa annan sannun a hankali jikinsa na rawa sai ya fara danna lambobin wayar talfon din gidan su Aziza, wani zazzafan gumi ya fara sartu akan fuskarsa, sa'ar da ya tuna da talfon dinsa na karshe da ya buga gidan da kuma mummunan amsar da ya samu daga gurin mahaifiyarta, azuciyarsa yana mai addu'ar Allah raba shi da mugun ji. Tsahon lokaci, kan tarfon din na kare a kunnen Dakta Ali, zuciyarsa na bugawa, gumi na sartu ko'ina a jikinsa kamar mai hadiyar kunama, hakanan babu alamar yawu a bakinsa, a can daya bangaren, yana iya jiyo talfon din yana bugawa. A dai-dai lokacin da Dakta Ali ya fara tunanin ko babu kowa a gidan sai yaji ance dashi

"Halo wa ke magana...." Zuciyarsa ta harba da karli a jere a jere har sau shida, kana daga karshe ta fara bugawa dai-dai kamar dukan ganga, ko shakka baya yi muryar da ke yi masa magana duk duniya babu mai irinta sai AZIZA.

"Aziza ce?" Dakta Ali ya tambaya bakinsa na rawa. "Eh nice wa ke magana" Akwai alamun kaguwa da gundura a muryarta. Dakta Ali ya runtsue idanu yana kokarin ya sai-saita numfashinsa domin dakyar ya ke shakar iska. "Aziza... nine Dakta Ali" lokaci guda yaji ta rike numfashi

Sannan sai tace. "Dakta Ali kaine yau ka tuna damu? Daga ina kake magana?" "Ina nan kusa dake Aziza! Ina nan garin Kano!".

******** ******* ***** ******* ******* *************

Daga inda Yusif yake tsaye a farfajiyar gidan yana iya hangen wasu manya-manyan agwagi irin na turawa farare masu dogon wuya, gashinsu sai sheki yake a cikin dan abin da ya rage na daga hasken ranar yammacin, agwagin sai kai kawo suke abinsu cikin shuke-shuken fulawowi da furanni. Yusif yayi mamakin kyau da kwarjini na 'gidan su Azizar yasha wuya kafin ya sami gidan, domin da tsohon kwatancen da Aziza ta bashi tun shekaru bakwai da suka wuce yazo.

Kusan minti guda suna tsaye suna duban juna, Aziza a zuciyarta, tana cewa wannan kuma wahalallen daga ina ya fado.. A zuciyar Yusif yana cewa, wallahi ta kara kyau da kwarjini yaji wani masifaffen sonta ya sake mamaye zuciyarsa. Aziza ce ta fara magana a fili bayan dan tsaikon da aka samu.
"Malam Yusif tsahon lokaci ina ka shiga". Malam Yusif! Me take nufi? Yusif ya tambayi kansa, kirjinsa ya fara bugawa da karfi, shin ta manta da shi ne a matsayin tsohon masoyinta ko kuwa me take nufi? Rabon da ta kirashi da Malam Yusif tun kafin su fara soyayya. "Ina nan Aziza... Ya dan yi shiru gami da sunkuyar da kai kana ya dada da cewa.
"Ina nan zaman jiranki" yayi karfin hali ya dago kai ya dubi Aziza ido-da-ido duk kuwa da mugun kwarjinin da take yi masa.

"Zaman jira na?" Aziza ta tambaye shi baki bude akwai alamar mamaki karara a fuskarta. Yusif ya gyara 'yar jakar dake rataye a kafadarsa domin ta fara yi masa nauyi hakanan gwiwowinsa sun fara rauni, irin sautin dake fita daga bakin Aziza a yanzu ba karamin karya masa zuciya yake ba.

"Aziza kiyimin rai ki karfafamin gwiwa...kina gani dai sai karyamin zuciya kike yi" Aziza ta saki wata tattausar dariya ta izgili.

"A'a, yanzu har karya ma gwiwa nayi, to me nace". Yusif ya gyara tsayuwa zuciyarsa na radadi.

"Kin rigaya kin sani Aziza dukkan wani siriri na zuciyata da zan fada miki a yanzu tamkar mai-maici ne ga abubuwan da na rigaya na fada a baya". Aziza ta gyada kai gami da harde hannayenta akan yalwataccen kirjinta. 'Ina jinka Malam Yusif".
"Wannan shi yasa ina samun labarin mutuwar aurenki na baro Bauchi na taho har nan Kano domin na tabbatar da irin kaunar da kika ce kina yimin a can baya, na yarda na yi imani da cewa a wancan lokacin da ya shude Allah ne ya kaddara bani zan aure ki ba, to amma yanzu fa Aziza?"

Aziza ta dago hannunta na dama ta dubi agogon dake hannunta wanda ke daukar idanu kamar madubi, kana ta dube shi ido-da-ido tace.
"Wanda ya kai maka gulmar auren nawa ya mutu bai ce da kai IDDA na ke yi ba?"

Yusif yaji gumi ya fara sartu akan goshinsa.

"Aziza abin bai kai da zafi haka ba, domin ba wani mutum ne ya kaimin labarin ba sai dan uwanki na Bauchi... kaninki Saddiq, "Aziza ta karkatar da kai gefe guda tace.
"Duk na fahimce ka Yusif amma bai ce dakai IDDA na ke yi ba?" Yusif ya dubeta kallon nutsuwa a karo na farko ba kallon tsoro ba, IDDA! Sai yanzu ne ya lura da damammen wandon Jeans mai beza daga kasa gami da jar fingilgilar rigar dake jikinta. Aziza ta lura da kallon da Yusif' ke yi mata dan haka sai ta yi murmushi tace.......AZIZA-20

Baka taba ganina a baka ba ko? Kasan zaman aure tsohon mijina mangayi ke son nasa masa irin wayannan kayan shiyasa na saba da su Idanun Yusif suka firfito cikin karduwa

"Marigayi fa kika ce?" Aziza ta saki wani tattausan murmushi gami da gyada kai". Tabbas mutuwa yayi... yanzu ma zaman takaba na ke yi Yusif ya dada kallon Aziza ko kusa ko alama wannan bata yi kama da Azizar da ya sani ba Waccan Azizar me kaunarsa me jifansa da murmushin Kauna tabhas ta sauya Wannan Azizar dake gabansa "yar duniyace fikakkiyar marar kunya mai ji da kanta, wannan sabon sauyi ba Karamin karya zuciyar Yusif ya yi ba "Duk da haka dai Aziza." Yusif yaci gaba da cewa cikin
wata rarraunar murya
"Ina son ki fahimci cewa Kaunarki ce ta sani tahowa zuwa gare ki batare da kin.... Maganar ta makale a fatar bakinsa bai Karasa ba ya lura da cewa duk kusan abin da yake cewa da Aziza ba saurarsa take ba, domin duk kusan dakiku biyar sai ta dubi agogo tabbas hankalinta baya tare dashi

"Aziza Yusif ya kira sunanta muryarsa na rawa" Tunnin me kike Aziza tayi ajiyar zuciya sannan ta dubt agogo ta dawo da hankalinta inda yake tace
"Don Allah Yusif kayi hakuri gobe ka dawo sai mu Karasa tattaunawar kasan ina cikin damuwa har yanzu tunanin mutuwar tsohon mijina na ke yi Ni zan tafi Tana gama maganar sai ta fara juyawa. Yusif cikin kunan rai yace
Gobe da yaushe zan sake dawowa "kana iya dawowa da safe ma ko da daddare duk lokacin da kaga yayi ma" Tana gama fadin haka sai ta jefeshi da murmushi kana ta dada da cewa
"Yusif ina matar taka naji ance kayi aure ko"

Bata jira amsar ta sa ba ta juya cikin sauri ta nufi cikin gidan, tabbas yanzu akwai alamun damuwa karara a fuskarta, shin ina Usman ya tsaya ne har yanzu bai zo ba? Aziza ta shige cikin ginin gidan ba ta juyo ta kalli inda Yusif ke tsaye ba da katuwar jakarsa a rataye kamar dan magori

Ta wuce mahaifiyarta a falo tana ferar dankalin turawa bata ko dubeta ba sai ta wace kai tsaye zuwa dakinta, ta sake zama akan gadon ta, domin samun damar tunanin babban masoyinta a duniya Usman, a zuciyarta, tana ta tananin wauta da sakarci irin na mutanen duniya, ta tuna da irin muguwar yaudarar da ta yiwa Yusif amma wai har yanzu shashashan sonta yake "Kai shi dai akwai sakarai wallahi Tace cikin zuciyarta sannan sai ta dada da cewa, "me zai hana ya hakura da ita ya fice taga rayuwarta kamar yadda SUNUSI, da MUSTY, da kuma DAKTA Ali suka mance da ita Aziza ta yiwa kanta murmushi wannan duk wani abune da ya wuce a baya ba zai taba dawowa ba.

A dai-dai wannan lokacin ne taji kan tarhon da ke dakin shakatawa ya dauki ruri. Aziza ta mike tsaye zumbur domin jikinta ya bata cewa ita ake nema tabbas Usman ne. Cikin sauri ta nufi dakin shakatawar tayi ko Sa'a a lokacin mahaifiyarta ta gama ferar dankalin turawan ta Shige dakin girki
Jikinta na rawa ta dauki kan talfondin, sannan gamida mamakin jin dadi gami da nishadi sai ta tausasa murya tace "Halo, wa ke magana?" Dan takin lokaci sai ta ji wata sassanyar marya tace "Aziza ce"? Nan da nan taji ranta ya Baci wannan ba murya Usman ba ce, yanzu haka ma daya daga cikin shashashen samarin nan ne ke son damunta

"Eh nice, wake magana? Ta tambaya cikin kaguwa dan Allah-Allah take ta ajje kan wayar, tunanin usman duk ya fi mata wannan shirmen, daman gashi wannan marar zuciyar ya katse mata tunanin da take na Masoyinta yanzu kuma ga wani zai bata mata lokaci. A dai-dai lokacin ne to taji a can daya bangaren sassanyar muryar tace
"Aziza, nine Dakta Ali" Gabanta yayi mugun faduwa. Dakta Ali nan da nan taji duk wani nishadi dake tattare da ita ya narke tamkar yadda alewar siwit kamfo kan narke a bakin yan yara, Aziza ta rike numifashinta, a zuciyarta tace, Na shiga uku da Tarko Yusif, yanzu kuma Dakta Ali! To nan gaba kuma sai wa zai bayyana? Yanzu kam ko shakka ba tayi tasan shi ma labarin mutuwar aurenta ya samu. Aziza bata ji dadi a zuciyarta ba. domin duk a cikin samarin da ta watsar a baya babu wanda take girmamawa kamarsa, mutum ne mai kirki, sura ga kuma ilmi in da ace zata-auri wani daga cikinsu, da Dakta Ali za ta aura, to sai dai kuma duk a cikinsu wanene zai iya jure masifaffen kisan kudinta in ba marigayi tsohon mijinta ba? "Dakta Ali kaine yau ka tuna damu daga ina kake magana
"Ina nan kusa da ke ina nan birnin Kano" Aziza taji Tausayinsa ya kamata, tabbas tana girmama Dakta Ali. "Aziza yaya al'amura bayan rabuwa?"
Aziza ta amsa. "Lafiya lau Dakta Ali... mun gode Allah". Ranar da suka fara haduwa a jami'a ta fado mata a zuciya ta tuno da irin taimakon da ya yi mata. Suka dan yi shiru na dan lokaci. Ga mamakin Dakta Ali sai yaji tace,

"Yaushe za ka zo!"

"Shine abin da yasa na bugo miki domin ki bani lokacin da zamu hadu, kada inzo a lokacin da bai dace ba". Aziza ta lumshe idanu, in badan usman ya gama shigewa zuciyarta kamar sartse ba, da babu wanda za ta aura Sai Dakta Ali-domin tana son mutum mai aji, wanda kuma yasan ya kamata, ba kamar wannan SHASHASHAN Yusif ba wanda ya zo mata bakatatan.

"Kana iya zuwa gobe da safe Dakta.." Ta danyi shiru "Ina fatan kuma za ka dauki abin da ya faru a baya a matsayin kaddara". Dakta Ali ya ji wani dadi marar misaltuwa ya lullufie zuciyarsa, ko shakka bayayi har yanzu Aziza na Kaunarsa, yanzu kam ya tabbata babu abin da zai hana ya aureta, to me ma zai hana bayan gashi yanzu da kanta ta ke tambayarsa lokacin da zai zo tabbas shi ta ke jira.

"Kada ki damu Aziza, ni musulmi ne na yarda da kaddara na kuma yi imani da cewa in dai ke rabona ce sai na aure ki". To na gode Dakta Ali.... Sai goben kenan" Sannan ta dubi
agogo "Sai goben to Aziza, ki mika gaisuwata gurin Hajiya kafin nazi Aziza ta ajje kan talfon din jikinta na rawa. Wanan wacce irin rana ce? Cikin sauri ta nufi jikin dogon madubin da ke dakinta ta dubi kanta, kamar yadda tayi tsammani haka ta gani
fuskarta tayi sharkaf da gumi, duk kwalliyarta ta baci, cikin sauri ta cire kayan dake jikinta ta daura zani kana ta wuce kai tsaye zuwa bandaki domin ta sake wanka, babu ta yadda za'ayi ta bari Usman dinta yazo ya sameta a haka a hargitse. Aziza ta taka a hankali ta shige cikin komin wanka na tangaran, sassanyar ruwar ya ratsata, hakan shi ya sa ta lumshe idanunta tana sake-sake, Ina ma ace Usman na nan kusa dani.
Tace da kanta, babu wanda zan aura sai shi, Aziza ta yiwa kanta murmushi ta dada lumshe idanu, zuciyarta ta koma kan tsohon tunaninta da zuwan Yusif ya katse mata, a kullum kwanan duniya takan ji dadi idan ta tunano rayuwar su da masoyinta Usman a jami'a....

Washegari ranar da ta yiwa Usman kyautar kudin da zai Sayi sutura ne ta fara haduwa da Alhaji Mukhtari. A lokacin fitowarta kenan daga dakin karatu Tana fitowa sai ta nufi inda tayi fakin da motarta cikin sauri domin sun yi da Usman cewa da sun gama darasin ranar a nan za su hadu, za ta kai shi cikin gari zai yi sayayya. Aziza ta ratsa ta tsakanin gommin motocin dake jejjere a gurin ta isa ga motarta ta mika hannun kenan zata bude sai taji a bayanta ance "Har kin tashi ne?" Aziza ta juyo cikin mamaki domin bata
shaida muryar mai kiran ba. Aziza tayi ido biyu da mutumin, dogone fari kakkaura, zai yi wahala ka iya fadin takamaiman shekarunsa, me yiyuwa arba'in da biyar ko arba'in, babu mamaki ma hamsin, domin tuni har mutuwa ta fara watsa masa gishiri aka, akwai jefi-jefin furfura nan da can a gefen gashinsa da kuma gemunsa wanda ya zagaye bakinsa kamar kuri. Yana da dogon hanci wanda ya lankwasa kasa kamar hancin aku kuturu, hakanan yana da yawan girar idanu duzu-duzu kamar gashin baki, to sai dai kuma idanunsa kanana ne mici-mici kamar idanun kififiya, sanye yake da babbar riga, 'yar ciki da wandonta na farar shadda, kafarsa cikin takalmi shudi wanda aka yi masa ado da gashin jimina kai kace wata tsiyane shi a sarauta, duk wannan Aziza ta lura da sune a kallo daya, a lokacin da ta ganshi tsaye yake jingine da katuwar lexus dinsa baka tana sheki Wal-Wal

Sannunka Malam Aziza tace, mutumin ya mayar da hamnayensa baya, daya daga cikin hannayen rike yake da dan mukullin motarsa Ya matso kadan kusa da inda Aziza ke tsaye

Tun safe ai ina nan, naga sa'ar da kika nazo lokacin na kawo wani abokina nan a zaiga (VC) ganinki ne yasa nayi jira har kika tashi domin ina son magana da ke, "mutumn ya rufe kalaminsa da tattausin murmushi Aziza ta dube shi, inama ace saurayi ne, tace cikin zuciyarta, tayi mamakin ganin jerin hakoransa farare tas! Suke da karfinsu ko guda daya bai cire ba duk kuwa da cewa ya yi sa'a da mahaifinta

"Wace magana kenan kake nufi?" Aziza ta tambaye shi tana kakkashe idanu lokaci guda kuma tana hange-hange ko zata gano Usman Mutumin ya kalleta da murmushi sa'annan ya dawa da Hannayensa gaba yana karkada dan mukullin motarsa.

"In baki damu ba yan mata, zan so ki bani "yan mintuna a

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

1 month ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment