Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalla goma domin bayanin nawa na da dan tsayi". Aziza ta dubi agogo, nan da mintuna talatin Usman zai fito daga nasa darasin, dan haka sai taga da ta zauna zaman jira me zai hana ta saurari wannan magidancin a Kalla dai ba sace ta zai yi ba, kuma tasan dai koma me zai ce tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ta koki, domin sauda yawa irin wadannan mutanen masu budurwar zuciya sun sha neman soyayyarta a baya, wasu takan yi watsi da su, wasu kuwa idan taga kamar za su banbaru sai ta ci gaba da wankarsu bar zuwa ranar da za su rabu dutse hannun riga

Aziza ta jefeshi da Kwararren murmushinta na yaudara tace "In dai har ba zaka wuce minti goma ba, bismillah ina sauraronka

"Anan zamu tsaya ko kuwa mu shiga daga cikin mota Aziza ta dube shi "Duk inda kace, ai duk daya ne", mutumin ya sake kallonta da murmushi
"Da zamu shiga dai daga cikin motar ina ganin zai fi sirri". Ya juya a nutse Aziza ta bishi a baya suka nufi motarsa. Ya bude mata gidan gaba shi kuma ya zagayo ya zauna a gurin direba kana ya rufe kolar ya kunna na'urar sanyi. "Nayi matukar farin ciki da kika nuna min yarda Aziza tayi yar dariya ta sunkuyar da, kasa kamar mai jin kunyarsa.
"Ina sauraronka

"Kafin mu fara zan so na san sunanki "Aziza ta dube shi ta dan yi masa far-far da idanu, tace "sunana Aziza Mutumin ya gyada kai cikin gamsuwa, ya dan yi shiru na dan lokaci sannan sai ya fara da cewa

"Ni dai sumana Alhaji Mukhtar, asalin iyayena ba yan Najeriya bane mutanen kasar kamaru ne, acan ska haifeni har na girma Ina dan shekara goma sha biyar aka kashe iyayena, inda daga nan na bar Kamari na tsero Najeriya dan daman iyayen nawa su kadai nake desu a duniya, bani da wa ko kani sai yan uwa wadanda akwa ne kamar babu.

Lokacin da na sauka a Najeriya Ikko na fara zama, a lokacin ina da 'yan kudi Naira dari biyar Alhaj Mukhtar ya danyi shiru yana duban Aziza cikin murmushi
"Aziza a wannan lokacin dari biyar kudi ne masu daraja ba kamar yanzu ba.
Da su na fara kasuwanci, da farko na'urorin wuta na fara sayarwa, talabijin rediyo, dutsen guga da dai sauran su, sannu a hankali na fara habaka, tun ina sayar da na hannu har na zo na fara sayar da sababbi. Ba'a dade ba muka yi hadin gwiwa ni da wani abokina mutumin Nijar muka bude kambin sabulun wanki, Allah ya albarkaci kamfanin tun muna yi a dan kango har ta kaimu ga sayen dan guri muka gine shi" Alhaji Mukhtar yayi shiru ya dubi Aziza
Ina fatan. kina saurarena Aziza, duk da yake dai nasan laharin nawa na da mutakar gundura.

Aziza ta gyada kai tace "Ina sauraronka, saidai ni kam har yanzu ban fahimci inda duk wannan labari yasa gaba ba domin bai shafe ni ba, ban kuma ga alakarsa da ni ba"

Akwa alamun damuwa karara a muryarta.
"Kada ki damu yanzun nan zan takaita labarin, na kuma alakanta ki da shi Aziza ta dube shi cikin Shakka. SHI KUWA YACI GABA......AZIZA-21

Akwa alamun damuwa karara a muryarta.
"Kada ki damu yanzun nan zan takaita labarin, na kuma alakanta ki da shi Aziza ta dube shi cikin Shakka.
Shi kuwa yaci gaba da cewa In takaita miki dai Aziza yanzu haka ina da kamfanunnuka a kasar nan sama da ashirin Aziza ta rike numfashinta, sai dai bata bari Alhaji Mukhtar ya fahimci hakan ba

"Matsala daya da ke damuna Aziza shine tun da nake ban taba aure ba, bani da kowna agarin nan sai abokan arziki . "Yadanyi shiru yana duban fuskar Aziza "Nasan da wahala ki yarda, to hakika ina tabbatar miki cewa ban taba yin aure ba, dalilin rashin auren kuwa ni kadai na barwa kaina sai Allah, masanin komai. Hankali na ya tashi Aziza domin kamar yadda kike iya gani tsufa ya rigaya yazo min ga shi banida magada ko daya ga tarin dukiya, wani abin bakin ciki kuma Aziza yau shekaru kusan ashirin kenan ina fama da cutar suga, in da ace bani da kudi me yiyuwa da tuni na dade da mutuwa... Sai gashi watan da ya gabata cutar ta tashi likita na ya auna ni yace da wahala na wuce sama da shekara biyu a duniya zan mutu Aziza ta rike numfashi cikin firgici, in har akwai abinda ta ki jini a duniya shine zancen mutuwa. Alhaji Mukhtar yayi dariya kana yace

"Alakarki da labarin Aziza shine, ina rokonki in har kina so ba wai takura miki zan yi ba ki yimin wani taimako daya". Aziza ta dube shi cikin mamaki, in dai duk abin da ya faci gaskiya ne taimako kuma zata yi masa bayan ya hore masa tarin dukiya

"Wane taimako kuma ni zan iya yi maka?" Alhaji Mukhtar ya shafi saman hularsa kana ya fara kida da dan yantsansa na dama akan sitiyarin motar

"So nake ki aureni Aziza, ni dai nasan tawa ta kare, nan da shekara biyu me yiyuwa Allah zai yimin cikawa, ina fatan Allah ya bani magaji tare dake, wanda zai gaji duk dukiyata ku zauna ke da danki, a kalla dai ba za'a manta dani a duniya da wuri ba". Aziza taji abin kamar na mai tabin hankali

"Na aureka kamar yaya, kana mufin kace duk kudinka ka rasa wacce zata aureka sai ni". Alhaji Mukhtar ya dubeta cikin dariya kana yasa alamun nutsuwa a fuskarsa yace."Duk da dai cewa likita yace ba zan wuce sama da shekaru biyu a duniya ba, zan so ace matar da zan bari takaba kyakkyawa ce kamarki, haba Aziza dube ki fa, ko a fadin duniya a daɗe ana zagawa kafin a sami mai kyawunki, kaddarar zamu hadu da ke ce ta kawo ni makarantar nan domin akwai yarinyar da na gani shekaranjiya a Abuja kadan ya rage na nemi aurenta". Ya danyi shiru sannan sai ya dubi Aziza ido-da-ido yace.
"Zabi ya rage naki Aziza, ba dole bane, kuma koda baki amince dani ba, ni ba zan taɓa mantawa da ke ba kuma na gode miki, me kika gani Aziza, ki taimake ni domin ni yanzu kusan daya nake da matacce so nake na mika dukiyata inda ta dace kafin na bar duniya". Kwakwalwar Aziza ta rude ta birkice sama ta dawo kasa, zuciyarta ta fara yi mata saka. Ki bi a hankali Azizar duniya, cikin shekaru biyu idan kika yi hakuri kina iya zama miloniya, yana mutuwa ke zaki gaje duk dukiyarsa tun da dai bashi da kowa a garin nan sai ke idan ya aure ki. Haihuwa? Me me ya kawo zancen ki haifa masa da, zuciyar ta ce take cewa da ita haka. Ba sai kiyi ta shan magungunan hana daukar ciki ba, ki lallaɓashi har shekara biyun tayi ya mace ki gaje dukiyar. Tunanin Usman ya fado mata a zuciya. Tana mutuwar son Usman gashi dai ba wani dadewa tayi da shi ba, amma ta tabbata duk duniya ba wanda zata aura taji dadin soyayya in ba Usman ba. To amma Usman zai iya tsaya mata duk abin da take so? Usman talaka ne, in ma aurensa tayi ita za tayi ta wahala dashi, domin ko aiki ya fara ba karamin aiki ne zai iya rike bukatunta ba, domin tasan a kullum satin duniya takan kashe albashin wasu masu digirin guda biyu. Wannan wata mafita ce tazo mata. Aziza tace da kanta. Na auri mutumin nan kawai bayan shekara biyu idan ya mutu sai na dawo na auri Usman dina... nasan zai fahimta idan nayi masa bayani kuma.....

"Aziza.." muryar Alhaji Mukhtar ta katse tunaninta. "Tunanin me kike?" Aziza ta dube shi gami da ajiyar zuciya tace.

"A gaskiya Alhaji ina da wanda na ke so zan aura kuma kaga..." Alhaji Mukhtar ya katseta ta hanyar daga mata hannu."Kada ki jahilci bayanina Aziza, sanin kaina ne zai yi wuya ace kyakkyawa kamarki bata da wanda zata aura, amma abinda nake so dake shine kiyi masa-bayani mana ai zai fahimta, shekara biyu kawai nake bukata sai ki dawo ki auri abinki." Ya danyi shiru yana mayar da numfashi "Yaron da kike son ki aura yana da kudi ne?" Aziza ta dubeshi tsahon lokaci sannan ta girgiza kai. "Me kike ganin ya kamata mu yi masa". Nan da nan Aziza tayi sauri tace: "Talaka ne bashida kudi, in har kana so na aure ka saika bashi kudin da za su iya biya masa duk bukatunsa kafin nan da shekaru biyu. Alhaji Mukhtar yayi murmushi yace. "Miliyan ashirin sun isheshi, Ko a kara masa?" Idanun Aziza suka firfito cikin kaduwa "Miliyan ashirin ai sun so su yi ma yawa": Alhaji Mukhtar ya fashe da dariya, cikin sauri ya lalubi aljihunsa ya dauko littafin cek na banki, ya yi rubutu ajiki yana gamawa sai ya mikawa Aiza yace.

"Gashi nan ki bashi, yauma idan yana so yana iya karbar kudinsa a bankin". Aziza ta dubi cek din, a jiki ya rubuta Naira Miliyana shirin da biyar. Aziza ta dube shi cikin kaduwa "Miliyan ashirin da biyar! "Alhaji Mukhtar ya daga girarsa sama yace
"Ko yayi kadanne in kara masa?"

Sati uku da faruwar wannan al'amari aka daura auren Aziza da Alhaji Mukhtar.

Da ace auren da aka yi tsakanin Alhaji Mukhtar da Aziza aurene na aminci da kauna, da ba karamin bala'i zai zamewa Aziza ba a shekarar auren na farko. To amma da yake daman tuni an yi shine kan yarjejeniya, Aziza bata jefa kanta cikin damuwa sosai ba. Amma duk da haka dai sai da abin ya fara tayar mata da hankali

Abin da Aziza bata sani ba shine ashe Alhaji Mukhtar mugun mashayin giya ne. Kwana uku kacal da tarewarta a sabon gidansa dake Abuja Alhaji Mukhtar ya fara nuna mata kansa.

Da daddare ne misalin karfe biyu da rabi shiru-shiru ango bai dawo gida ba, ko a jikin Aziza wai an tsinkuni kakkausa, ko kusa bata damu ba domin daman ba kaunarsa take ba, ita ason ranta ma bata kiba a lokacin azo ace mata ya yi hatsari ya mutu Aziza bata ma kara tsanarsa ba sai da ta aure shi. Kwanaki uku kacal har ya gundure ta, kullum tunaninta Usman. A ranar farko Alhaji Mukhtar ya fita ya barta ita kadai a gidan, daga ita sai wata tsohuwa mai yi mata hidima wai ita Adama Yana fita sai ta bugawa Usman waya suka yi ta hira, domin shima yanzu ya gama shiga cikin wadatar rigar arziki.

A daren wannan rana ta uku ne Alhaji Mukhtar ya shigo dakin yasha yayi mankas da shi sai wari yake. Aziza ta dubi lokaci karfe uku na dare. Alhaji Mukhtar yana zuwa sai ya fada akan gado, ba'a dade ba sai babban direbansa ya shigo masa da Bakar jakarsa wacce ke dauke da takardun ayyukansa.

"Barka da dare Hajiya "yace da Aziza Aziza ta dube shi a yatsine tace "sannun ka dai". Bayan ya fice daga dakin bai ko yi nisa da barin dakin ba, sai Alhaji Mukhtar ya hau Aziza da zagi. "Dan ubanki baki iya yiwa mutum sannu da zuwa ba Aziza tayi tsalle gefe guda a tsorace, rabon da wani kato ya zage ta har ta manta. A ranar bata kwana a dakin ba, sai dakin saukar baki ta koma ta kwanta. Washe gari tunda sassafe bayan ya dawo hankalinsa, sai ya tafi dakin saukar bakin ya dawo da ita dakinta, sannan ya dubeta yace.

"Kiyi hakuri Aziza, mantawa na yi ban fada miki ba cewa ni mashayine sai dai kiyi hakuri da halina kafin nan kafin Allah ya raba. Aziza ta rasa abin cewa dan haka sai kawai ta gyada masa kai.

Haka abubuwa suka yi ta faruwa sannu a hankali watanni na bin 'yan'uwansu suna wucewa har shekara ta wuce, sannan. shekaru biyu suka wuce, kai har dai aka shiga shekara ta biyu da rabi. Aviza taga ko ciwon kai Alhaji Mukhtar bai taba yi ba........

HAHA 😂 AKWAI CHAKWAKIYA FAAZIZA-22

Haka abubuwa suka yi ta faruwa sannu a hankali watanni na bin 'yan uwansu suna wucewa har shekara ta wuce, sannan, shekaru biyu suka wuce, kai har dai aka shiga shekara ta biyu da rabi, Aziza taga ko ciwon kai Alhaji Mukhtar bai taha yi ba tunda ta aure shi, wani abu kuma dake bata mamaki da sa ta damuwa shine kafin ta aure shi yace da ita yana da cutar suga, sai gashi kuma duk wani abu na kwalam da makulashe Alhaji Mukhtar bai daina ci ba, haka kuma ko zazzabin rana daya bai taba yi ba, maimakon haka ma sai dada tumbi yake yi abinsa, wannan ita tasa Aziza ta tutsiye shi a ranar wata lahadi da safe, ranar ita tayi dai-dai da shekaru biyu da rabi cif-cif da daurin aurensu.

Sun gama karin kumallon safe kenan sai Aziza ta dube shi tace. "Alhaji... yau fa wata shida kenan da cikar alkawarinmu... shekaru biyu sun gama shudewa kamar wasa... kasan kuma fa akwai wanda ke jira na". Alhaji Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa na tsawon lokaci yana kallon kilishin dake kasan falon, daga karshe ya dago kai yace.
Ashe dai kin kagauta da na mutu na bar muku duniyar." Aziza taji zuciyarta ta harba. "Ban fahimce ka ba". Alhaji Mukhtar ya saki wani
buasasshen murmushi yace. "In ke baki fahimce ni ba ai ni na fahimce ki, ashe ke yanzu duk zaman da kike a gidan nan sama da shekara biyu zaman jiran mutuwata kike?". Aziza ta dube shi a rude. "Kai fa ka fadamin... ba kai kace dani likita yace ba zaka wuce sama da shekara biyu zaka mutu ba". Alhaji Mukhtar ya kyalkyale da dariya yace. "Wani lokacin mata kuna daban dariya, in banda abinki dan likita ya fadi magana sai ta kasance? Dole ne, fadar alkur'ani ce,? kin san dai ai bani mutuwa har sai kwanana ya kare". Ya mike tsaye. Aziza taji zuciyarta na soyewa, tabbas tasan ya gama da ita.
"Wato yanzu dai kana... nufin kace abubuwan da ka
fadamin a baya duk karya ne", Alhaji Mukhtar ya karkatar da ka gefe guda kamar zakara sannan yace "Eh to, ba'a ce duka karya ne ba, kusan duk bayanin da na fada miki a baya gaskiya ne in kika dauke kirkirarrun zantuka guda biyu". Nan da nan sai hawaye ya fara sartu akan kumatun Aziza. Na shiga uku tace cikin zuciyarta.

"Kada ki bata hawayenki a banza Aziza domin karairayin da na yi miki guda biyu ne kawai ba wasu masu yawa bane, karya ta farko dai itace, tabbas na taba aure, amma na saki matar tana can yanzu haka a kaduna da 'ya'yanta guda goma sha shida Karya ta biyu kuwa ita ce lafiya ta kaulau bani da wata cutar suga, na lura ne da yanayinki, in har nace zan fada maki gaskiya ba zaki taba aure na ba". ya danyi shiru sannan yace cikin murmushi.

"Ya kamata ki mance da komai kawai kiyi zamanki lafiya, me kika rasa? Kuma in kina tunanin usman dinki ne ai ɓata lokacin ki kike yi domin na tabbata shima ba wani son ki yake ba". Aziza ta mike tsaye a fusace ta fara kuka gami da "Allah ya isa tsakanina da kai macuci tsohon banza, ka bani takardata tsinanne ni nasan Usman me kaunata ne. Alhaji Mukhtar ya daga girarsa sama yace.
"Yana kaunar taki na bashi naira miliyan ashirin da biyar ya bar min ke, Eh!, amsamin mana! Bari kiji Aziza ni dinnan a yanzu zan iya cika miki bakin cewa nafi Usman kaunarki dari bisa dari domin babu wasu kudi a duniya da za'a bani in rabu da ke.." Aziza ta fara ihu a dakin cikin kuka.

"Ka sakeni! ni ba na sonka na tsane ka mayaudari. Alhaji Mukhtar yayi tsaye abinsa yana dubanta cikin murmushi sai da ta gama buge-bugenta sannan ya dubeta yace "Ba zan taɓa sakinki ba Aziza ina son matata".

********* ******* ********* ******** ************

Alhaji Mukhtar yana barin gida da sassafe sai Aiza ta nufi wayar tarho cikin gaggawa idanunta luhu-luhu sun yi jajur da su sakamakon uban kukan da ta kwana tana yi. dan lokaci tana danne-danne daga karshe ta kara a kunnenta..
"Halo wake magana" muryar Usman ta ratsa kwakwalwarta. "Nice Aziza Usman" ta fara cewa dashi cikin kuka, sannan cikin shassheka sai taci gaba da yi masa bayani daki--daki duk abubuwanda suka faru tsakaninta da mijinta.
Bayan ta gama labarin usman ya dade acan daya bangaren bai ce da ita komai ba. Usman, kace wani abu mana dan Allah".

"Ina nan Aziza, dan jirani kadan tunani na ke yi". Akwai alamun fusata karara a muryarsa. Bayan dan lokaci sai yace da "Aziza ina da dabara, amma sai idan zaki iya dake zuciyarki, za ki iya kuwa. "Bakin Aziza na rawa tace ko mene ne
ka fada Usman zan iya.... Wallahi na tsane shi". "Kada ki damu saurara kiji dabarar tawa..........*************

..Ga al'adar Aziza tun sa'ar da ta fahimci cewa mijinta cikakken dan ruwa ne sai take rufe cfakinta idan zata kwanta. Dan haka a ranar koda mijin nata ya dawo cikin dare idan ya fara buga kofar ba zata bude ba har sai taji alamun muryarsa idan bai yiyo sha ba.

Sabanin sauran ranaku, yau Aziza a zaune take tana jiran dawowarsa. Tun Karfe goma sha dayan dare aka fara tafka uban ruwan sama kamar da bakin kwarya. Aziza tayi mutukar jin dadin wannan ruwa domin ko ba komai dai tasan ruwan zai kora "yar tsurkun tsohuwar nan daki, Adama mai yi mata hidima. Sau da yawa tasha kama tsohuwar tana lekensu idan suna fada da Alhaji Mukhtar, wani sa'in kuwa har kara kunne take yi ajikin kofa tana sauraron irin abin da ake cewa a cikin dakin. Da yake Aziza tasan zamanta a gidan zaman wucin gadi ne bata tabi damuwa da al'amarin tsohuwar ba, kai hasali ma ita ce ta sa Alhaji Mukhtar ya dawo da tsohuwar harabarsu domin ta rinka dauke mata kewa amma a ka'ida kamata yayi ace tsohuwar tana can bangaren da sauran hadiman gidan suke kwana.

Aziza ta mike tsaye ta nufi katuwar tagar mai gilasai ta alfarma dake kallon lambun shakatawar dake gidan, daga inda lake tsaye a hawa na uku take. Aziza ta tuno da ranar da Alhaji Mukhtar ya kawo ta Abuja domin ta ga gidan idan ya yi mata.

"Yaya ki kaga gidan yayi miki ko?" Yace cikin murmushi Aziza ta dubi dogon benen zungurere shi katai atsakiyar shuke- shuken alfarma na fulawowi da bishiyoyin ado, ta dube shi tace.
"Yayi kyau, amma me yasa ka zabi a yi ma wannan dogon bene har hawa uku kamar wani jemage... ai ina ganin masu kudi kamar ku basu fiye irin wannan gini ba". Alhaji Mukhtar ya fashe da dariya har da kyakyatawa.

"Aziza kenan, wato abin da baki sani ba shine, ni Allah ya yini mutum ne mai tunanin son na ringa kallon korayen shuke- shuke daga can sama, suna mutukar debemin kewa, shi yasa nasa aka gina min wannan gida mai bene hawa uku, hawan farko na masu gadi ne da sauran ma'aikatan gida, hawa na biyu kuwa na saukar baki, yayin da hawa uku kuma namu ne ni dake kawai.." ya fashe da dariya.

Aziza tayi wa kanta murmushi sa'ar da ta gama tunanin, ashe dai dogon benen zai yi mata amfani. Tace da kanta, tabbas dabarar Usman ita zata bi, meye to..mene idan ma an rasa shi sai me wa yayi asara? A dai-dai lokacinne to taji motsin tafiya an nufo dakin. Cikin sauri Aziza ta mike ta nufi kofar dakin ta leka domin taga halin da Alhaji Mukhtar ya zo gida a ranar. Aziza ta yiwa kanta murmushin yake sa'ar da taga sai tangadi yake yana ta bugun kofar benen mai kawanya, da ke shinfide da jan kilishi, cikin sauri Aziza ta dawo dakin, sannan ta dauki wata 'yar kujera ta azurfa ta kai gindim katuwar tagar dakin ta ajiye sannan ta zauna gami da harde kafa, zuciyarta na harbawa, yawun bakinta ya bushe karaf haka nan da kyar take shakar numfashi. A zuciyarta tasan cewa tabbas abin da zata aikata yana daya daga cikin mafi munin zunubai, to amma shaidan sai kururuwa yake yi mata, yana cewa da ita ke shashashar banza dabarar da Usman
ya fada miki ita kadai ce mafitarki. Ba'a dade ba Alhaji Mukhtar ya shigo yana tangadi, Babban yaronsa a baya rike da jaka, wani sa'in idan yayi layi kamar zai fadi sai babban yaron nasa ya tokare shi.

"Yau yasha da yawa ko?" Aziza ta tambayi mutumin da ya rakoshi. Mutumin ya dubi Aziza a ladabce domin yana mutukar girmamata, yace.

"Eh wallahi Hajiya sai fa ki kula da shi". Yana ajje jakar saiya fice daga dakin. Aziza tayi alilyar zuciya. Har yanzu ruwan saman ake makawa kamar da bakin kwarya. Aziza ta baro gindin tagar ta nufi kofar dakin ta janyo ta rufe gami da sa sakata,
Domin koda Adama ma zata zo tsurku a banza. Aziza ta dawo gindin tagar ta zauna, zuciyarta na tunanin dabarar Usman. "Me ki ke yi har yanzu baki yi barci ba". Alhaji Mukhtar yace cikin muryar 'yan giya. Aziza tayi banza dashi. Yayiwo taga-taga ya nufi gindin tagar dakin inda Aziza take zaune
ya tsaya akanta yana layi kamar zai fadi. "Me ki... ke....yi a gindin taga ke kadai..." Abin da Aziza ke jira ya tambaya kenan. Tabbas daman Usman ya fada mata yana iya tambayarta haka. Aziza ta mike tsaye lokaci guda kuma ta bude gilasan tangamemiyar tagar sannan ta dubi Alhaji Mukhtar tace
"Leken korayen shuke-shuken dake cikin lambunnan na ke yi ko zaka zo ka taya ni, nasan kaima suna burge ka". Alhaji Mukhtar ya tangada yana duban Aziza can sai ya matso kusa da ita Aziza ta yi sauri ta tallafeshi sannan ta dora masa hannayensa biyu a bakin tagar Warin giya ya bugi hancinta, ta riga ta saba dashi.
"Mene ne.... wannan?" Alhaji Mukhtar ya nuna can kasan benen, cikin lambun dake haske tarwai da fitulun alfarma, kwayoyin ruwan saman dake zuba su suka da da kawatashi. "Lambunka ne abin da kafi so,, ko zaka sauka ka gano...Aziza tace zuciyarta na harbawa. Alhaji Mukhtar ya daga kafa sama ya zurata ta cikin katuwar tagar, sannan ya juyo a buge idanunsa a rufe yace. "Ciccibani in tafi in gani yanzun nan zan dawo... kada fa ki tafi ko ina A dai-dai lokacin aka saki wata katuwar aradu, iska ta feso ruwa ya daki fuskar Aziza. Zuciyarta na harbawa ta dubi Alhaji Mukhtar, sannan sai maganar da Usman ya fada mata ta dawo zuciyarta."Hankada shi kawai za ki yi mu huta". Ko da Aziza ta dubi halin da Alhaji Mukhtar yake, taga bashi da wani mataimaki a wannan lokaci sai Allah, sai taji zuciyarta ta karaya, a dai-dai lokacin ne to shaidan ya fara wasa da ita". Shashshar banza damar ki kenan rufe idonki kawai ki tura shi kasa kin hutawa bakin cikin rayuwa. Aziza ta cije lebban bakinta, sannan ta sunkuya, zuciyarta na harbawa, ta hada Karfinta guri guda, sai ta ciccibo kafar Alhaji Mukhtar ta hankadashi Kasan benan da Karfin gaske. Alhaji Mukhtar ya fada kasan benan- ba tare da wani kakkwaran sauti ba sakamakon aradun da ake ta rusawa. Ko shurawa bai yi ba ya mutu. Washe gari sa'ar da Aziza ta rafsa kururuwa tana kuka, babu wani mutum da yayi mamakin fadawarsa kasan beben, domin kowa yasan kullum a cikin giya yake, dan giya ko na iya yin komai...

******* ********* ******** ******** *************

Aka kwankwasa kofar bandakin wannan shi ya tsamo Aziza daga cikin kogin tunanin da ta tsunduma. Tabbas wannan duk wani abune da ya wuce da mako guda. Aka sake kwankwasa kofar a hankali. Aziza ta bude idanunta kana ta tashi zaune a cikin katon komin wankan ta dubi kofar bandakin , cikin mamaki, waye ke kwankwasa mata kofa? Ta riga tasan in zata shafe awa ashirin da hudu cikin bandaki mahaifiyarta bazata taba damunta ba, domin a kullum tana alfahari da 'yarta wajan iya kwalliya. To idan ba mahaifiyarta bace wanene? Tabbas mahaifinta ya fice tun dazu. A'a, ko kuma Usman ne yazo mahaifiyata ke son sanar da ita. Fuskarta ta washe tabbas haka ne ma. Aziza ta yunkura zata mike tsaye kenan sai taga kofar bandakin ta fara budewa, sannu a hankali mutumin ya shigo cikin bandakin sannan ya jingina bayansa jikin kofar ya rufe. Abin duk

2 Comments On AZIZA
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Gaskiya naji dadin samun taskar nan sabida akwai dinbin littafai masu debe kewa Ina godiya da fatan alkhairi

avatar
taskar

1 month ago

Reply

Replying to mustapha-6-6

Mu ma muna godiya kwarai, ka samu ka yi subscribtioon na mu koda na 1k ne domin ka fi jin dadin samun littatafan tunda zaka samu daman downloading na su

Please Login or Register in order to submit comment