Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣3⃣
Fatu bata farka sai 12:23. A hankali take bude idonta har ta fara gani rass. Juyo da kanta tayi gefe inda taji muryan mace na mata sannu, kyakkyawar mata ce mai dan jiki kadan wanda da alama ta danbmanyanta, "Ya jiki ta qara cewa da fatu, a hankali ta furta da sauqi. Sannan ta fara qoqarin tashi, matar tayi hanxarin taimaka mata ta zauna. Tace "ki dan huta sai kici abinci. Bari in hada miki tea. Tea ta hada mata mai kauri tasha kadan tayi hamdala. Sannan matar tace meye sunanki, kuma a ina iyayenki suke? "Suna na fateema ana cemin fatu, dangina suna kauye mai suna Garin Modibbo dake karkashin qaramar hukumar Akko. Matar tace "sunana hajia kulsum, nice na buge ki da mota ina sauri zan kai dana makaranta. Kiyi hakuri. Hope yanxu bakya jin ciwo? Daga kai fatu tayi, hajia kulsum tace "gurin wa kika zo nan garin? Ina son in kaiki in bada hakuri. Saurin girgiza kai tayi kanta na qasa tace "a'a hajia hakama ya isa, ba sai kinje ba, nagode. Hajia kulsum ta tashi ta deba mata abinci da kyar fatu taci rabin plate tace ta koshi tasha ruwa. Hajia na lura da yanayinta, yarinyar tana cikin damuwa. "Hajia ina son zuwa bandaki" hajia kulsum ta taimaka mata taje bandaki, kama ruwa tayi sannan tayi alwala ta fito. Zama ta qara yi a kan gadon, shiru sukayi na dan lokaci sannan aka fara kiraye kirayen sallah. Sukayi sallah, sannan Doc ta shigo ta duba fatu, ta mata questions game da yadda take ji. Doc ta juya gurin hajia kulsum tace "zaku iya tafiya gida, shes gud now" ta fita. Hajia ta fita taje ta biya kudi ta dawo tace mu tafi. Sun fito harabar hospital dinne fatu tace "hajia ko kun tsinci jakata" hajia tace "eehh, yana gidana manta wa nayi ban dauko miki ba. Amma muje sai ki karba. Mota suka shiga suka tafi. Unguwar GRA suka shiga, ita dai fatu in banda kalle kalle bbu abunda takeyi, wani layi suka shiga wanda yafi ko ina haduwa don gidaje 20 suna kallon juna sai titi a shimfide a tsakiyarsu. Gaskiya fadin tsaruwar houses din ma bata lokaci ne. Nidai mmn fa'iz nace kamar a turai. Fatu kuma tace Aljannar duniya. A cikin jerin gidajen wata mota hadaddiya ta fito ta hau kan titi, hakan yyi daidai da juyowar fatu wacce take kalle kalle tun shigar ta unguwar mutumin da ta gani a cikin motar shiya sata daskarewa, bakinta a bude tana nuna shi da yatsa, har yazo ya wuce baima san tanayi ba don waya ma yakeyi yana murmushi. Horn hajia tayi a bakin gate din gidanta wanda yake kallon gidan da mutumin ya fito. Aka wangale gate ta kusa hancin motar har ta samu parking space tayi. Sai a sannan ta lura da fatu wacce idanunta na tsiyayar hawaye tana nuna glass da yatsa, fatu" ta kira sunanta amma bata amsa ba, dafa kafadarta tayi ta juyo a firgice sannan ta fashe da matsanancin kuka wanda yasa hajia cikin wasi wasi. Anya yarinyar nan ba aljanu gareta ba? Ace yarinya da ita ta fito daga garinsu ba kowa tare da ita, kuma ba'a mata komai ba tana kuka tana nuna glass. Whats wrong with her? Kodai auren dole za'a mata ta gudu? Ko ko ko?

Maman Fa'izπŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣2⃣
Hospital:
Tana isa asibiti ta shiga sai gata ta fito da nurses biu hade da gadon tura mara lafiya. Suka ciccibi fatu suka daura akan gadon sukayi ciki da ita cikin sauri. Emergency aka shigar da ita, bayan 15 minutes wata doctor ta fito da sauri matar ta tare ta, tace "ya patient din? Doc tace "da sauqi don bata buge sosai ba, tsoritan da tayi ne yasa ta suma, sai kurjewa da tayi a kafa. Ynxu za'a kaita dakin hutawa zata farka nan da 4-5 hours. Don tana bukatar hutu. Tana gama fadan hka tayi gaba abinta yyinta wata nurse da gangaro fatu a kan gadon marasa lfyn ta kaita dakin hutu matar ba biye da ita. Ta kai minti biu tsaye a kanta sannan ta juya ta koma mota, yaronta dan kimanin 7 yrs yace 'mum ina wanda kika bugen? Sai a sannan ta tuna ashe tare suke, school zata kaishi da yake yau monday tana sauri kar y makara, shine hatsarin ya faru. Shafa kanshi tayi tace 'farouq tana ciki an bata gado, muje in kaika school.
Acan school tayiwa teachers bayanin abunda ya faru don yara sun dde da shiga class. Komawa gida tayi wanda a lokacin 9 da yan mintuna. Ta samu dija mai aiki tana goge a palour, 'sannu da dawowa hajia' hajia ta amsa tace 'kiyi abinci da mutum 1 za'a kai asibiti, na buge wata yarinya a hanya. Bata farfado ba balle in san gidansu, na duba jakanta banga tana da phone ba ko ID card. Cikin jimami dija tace "to hajia Allah ya kiyaye na gaba, taji ciwo sosai ne? Hajia ta mata bayanin da Doc ta mata sannan ta haura sama tana tunanin yarinyar game da tambayoyi cike a kanta wanda bbu wanda zai bata amsan sai yarinyar. Don daga ganin shigar da tayi zaka gane yar kauye ce, amma cikin jakarta kudi dari biyar biyar sabbi wanda yawansu zai kai 25k, kuma jakan nata irin na yara masu zuwa makaranta ne, sai kaya kala uku. Ni kaina mmn Fa'iz sai da zare😳. Duk answers na gurin fatu wacce har ynxu tana gadon asibiti bata san duniyar da take cikiba.

Taku Maman Fa'izπŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣4⃣
Fitowa hajia tayi daga motar ta zagayo inda fatu take, bude murfin kofan tayi ta kamo hannun fatu suka shigo cikin gida ta zaunar sa ita kan kujera a palour. Fatu ta cigaba da kukanta. "Dija dija" dija ta fito dga kitchen ta ce "gani hajia" hajia tace "taimaka min da ruwa pls" komawa kitchen tayi ta fito da tray an daura swan water da cup. Ta ajiye ta koma tana tunanin wace yarinya ce haka hajia ta samu? Daga kafada tayi tace hala yar aiki ce. Hajia ta tsiyayi ruwa ta miqa ma fatu wacce kukanta ya tsaya sai sheshsheka takeyi tace "kisha ruwa" ba musu ta karba ta sha, tayi ajiyar zuciya. Hajia ta numfasa ta fara magana "fatu a yanda na lura da yanayinki kina cikin matsala, kuma kinyi yarinya a barki ki fito daga kauyenku ke kadai ba tare da wani dan uwanki ba. Tambaya nake son miki, ki fadi tsakaninki da Allah, gurin waye kika zo anan garin? Fatu da tunda hajia ta fara magana kanta na qasa tace "gurin dan'uwa na nazo" " a ina yake? Fatu tace "na manta sunan unguwan amma yana cikin jakata. "Farouq farouq hajia ta kira shi yana room dinshi yana buga game, tun 12:30 y dawo daga skul. "Gani mummy" "jeka room dina ka dauko min wani skul bag akan bedside drower. Yace "to, amm mummy wannan ba itace ta mutu dazu ba? A cikin motarki. Hajia tayi daria tace a'a suma tayi not mutuwa, now get d bag. Ya juya da gudu ya dauko ya miqawa hajia ita kuma ta miqawa fatu, gurin fatu yaje da take kallonsa tun farkon shigowarsa. Yace daxu mum ta bugeki, kinji ciwone? Tace "a'a tana murmushi, amma kin suma ko? Tace ehh. Zai qara wata tambayar hajia ta katse shi tace " farouq jeka fara shirin islamiyya. In ka dawo she wll answer all ur questions. Ya haura sama da gudu yana cewa to mummy kar ta tafi, ta jirani fa.
Aljihun gefe na skul bag din fatu ta bude ta ciro wani pic hade da guntun paper ta miqawa hajia kulsum. Mamakine ya bayyana qarara a fuskar hajia data kalli pic din, paper ta bude ta qara gaskata abunda ta gani. Ba komai ta gani ba illa pic din sultan gefenshi kuma fatu ce, a kauye aka dauki pic din,don ga irin bukkan rumbun nan da ake ajiye amfanin gona. A cikin paper kuma adress na gidansu sultan ne, wato gida mai kallon gidanta.
Hajia ta dubi fatu tace "wannan dan'uwanki ne? Fatu tace ehhh, "ya dangantakar ku take? Fatu ta numfasa tace hajia zan fada miki ko zaki taimaka min in shiga cikin gidan, don naga kamar sai da mota ake shiga irin gidajenku.
β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

ASALIN LABARIN
Taku
Maman Fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣1⃣
CIKIN TASHA:
Mutanen dake fitowa daga cikin bus din ne na hango wata matashiyar budurwa, wacce inka lura da yadda take waige waige tana zare idanu zaka tabbatar yaune farkon shigowanta garin Gombe, "Gombawa diban fari, ba'a kwana daku ba an tashi daku"😜 Itama FATU haka ya ksance da ita don ynxu misalin karfe 7:20 na safe. Matsawa gefe tayi ta tsaya inda bbu mutane sosai ta cigaba da dube dubenta. Can nesa ta hango wata mai sayar da kosai da dankali a cikin tashan. Nufanta tayi da sauri cikinta na bada wani sauti qululululu don rabon da taci abinci tun jiya da rana sai fura kadan da kakanta ya bata da dare. Sauri take yi har ta isa, sallama tayiwa mata mai sayar da kosai, matar ta amsa, fatu tace a bata kosai da dankali na dari, matar ta sa mata a leda ta miqa mata, kudi ta ciro 500 daga cikin jakarta ta miqawa matar, aka bata canji, gurin wasu yara masu sayarda pure water taje gefe kadan da mai sayar da kosan. Ta sayi guda biu. Anan ta fara tunanin a ina zata zauna taci, don har masu shaguna sun fara budewa. Bakin wani shago taje inda bbu mutane ta zauna, juya baya tayi yanda baxa a ganta ba ta fara cin kosan tana korawa da pure water. Sauri sauri har ta gama. Alhamdulillah ta furta, sannan ta wanke hannunta ta goge bakinta da zumbulelen hijabinta. Minti biyu da haka ta miqe hade da karkade jikinta ta dauki jakanta ta rataya ta cikin hijabi. Wajen tashar ta fito tana tunani barkatai a cikin zuciyarta. Kuuuuuuuuuuu sai timm. Innalillahi abunta matar dake cikin motar ta fada cikin kidimewa. Kafin ta fito har an fara taruwa akan fatu, tana fitowa tayi kan yarinyar da saurinta tana su taimaka mata su saka ta cikin motar ta. Wasu mata yan sharan titi ne suka taimaka mata suka sata a mota yayin da matar ta shiga driver seat ta cilla kan titi sai hospital.
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣5⃣
ASALIN LABARIN
Kamar yadda na fada miki sunana fatima. Dangin mahaifina yan asalin garin modibbo ne, fulanine usul. Dangin mahaifiya ta kuma yan dukku ne, suma fulani.
Kaka na mallam Aminu malami ne sosae wanda yake koyarda almajirai da manya, yana da matarsa binta wacce tun auren saurayi da budurwa suke tare, auren dangi aka hadasu. Yayansu biyar amma biyu ba rai, uku ne suka rayu har girma, goggo innani itace babba, sai sama'ila da kaninshi jamilu sune suka rasu, sai babana mamuda da kaninshi muntari. Tun kafin a haifi muntari goggo innani tayi aure. Tun tasowan babana Allah y yishi mai kokari ta fannin karatu da neman na kanshi, baiyi boko ba amma yyi arabi sosae. Tun yana saurayi ya fara kasuwanci, inda yake bin kasuwannin kauyuka yana sayar da busheshen kubewa. In damina tazo kuma ya taya bbanshi noma. A yawonsa na bin kauyuka ya hadu da mamata a Dukku, tazo siyan kubewa ya ganta yace yana so, itama ta nuna ra'ayin hakan, bai bata lokaci ba ya samu babanta ya masa bayanin inda ya fito da sana'ar sa kuma yaga diyarsa yana so. Babanta yayi murna da jin haka, don akoyaushe addu'arsa bai wuce Rahmatu ta samu miji tayi aure ba, don tun tana karama mahaifiyarta ta rasu anan zamanta ya dawo gurin kishiyar mamanta, ba irin duka zagi da wahala rahmatu bata dandana ba, babanta kuma bashi da bakin magana kamar an asirce shi. Bukatarsa kullum ta samu miji tayi aure ko zata huta. Ya sami yayansa da maganan inda yaqi amincewa, wai tunda gida bai koshi ba baza a bawa bare ba. Kuma ai zatayi nisa da gida. Shi a sonsa a hada ta aure da dansa wanda duk garin bbu wanda baisan yana dauke dauke ba, bashi da takamaimen sana'a. Babanta ya nuna rashin amincewarsa shima, a haka suka tashi ba tare da tsayayyem magana ba. Babana kuma yana komawa gida ya sanar da iyayenshi inda sukayi murna da fatan alkhairi.
Sati daya da maganan babana ya koma dukku don jin amsarsa, Inda ya tafi da kakana wato malam Aminu. mallam sirajo (baban mamana) ya musu iso yasa aka shimfida musu tabarma a zaure, fura da nono aka kawo musu hade da ruwa suka sha sukayi hamdala, sannan aka fara magana. Yayan babana na aka kira yazo, koda aka koro masa bayani yace shi sam bai san zancen ba, fada yakeyi sosai ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, wai sai da baki suka zo sannan za'a kirashi, kuma sai da sirajo ya amince? To me zaice? Ai yarsa ce yayi abunda yaga dama. Don anga danshi bashida abun hannu amma da mai kudi yazo shine xa'a bata? Karshe ma cewa yayi bbu ruwansa akanta yayi tafiyarsa. Zuciyar fulani ta tashi na mallam sirajo ya cewa mallam Aminu a yau za'a daura auren, karshen iko kenan. A ranar aka daura auren a masallacin garin bayan an idar da sallahn azahar. Sai shigowa da akayi da goro da cingam cikin gida yara na cewa an daura auren rahmatu da mamuda. Da farko ta aza wasane sai da taga inna haule (kishiyar mamanta) na watso mata kayanta waje tana cewa ta hada ta kulle yau zata tafi gidan mijinta. Tana hawaye tana hada kayanta inna haule bata daina masifa ba da yake bakinta daya da su yayan mallam sirajo da matarsa. Wasu na cewa bakin cikinsu ne ya kashe maman rahmatun. Babanta ya mata nasiha ya miqa amanarta gurin kakana. Tana kuka yana hawaye suka rabu. Basu dawo ba sai bayan isha. Kakata tana jiran isowansu sai kawai taga har da amaryan aka taho. Bayan sun huta sunci abinci mallam Amenu yake sanar da ita komai. Ta jinjina lamarin inda ta tausayawa mamata. Dakin babana aka gyara musu inda ya siyo mata duk kayan daki da ake sayawa amarya na wannan lokacin.

Hajia kulsum ta numfasa tace fatu ki tsaya anan. Lokacin sallar la'asar yayi. Dakin hajia suka shiga anan ta nuna mata yanda zatayi amfani da toilet din taa barta a ciki ta sauko kasa tana kiran farouq yazo driver ya kaishi islamiyah time yayi. Bayan ta shigo daki ne ta samu fatu har tayi alwala ta fito, sallaya ta miqa mata ta nuna alkiblah sannan ta shiga toilet din don gabatar da alwala. Fatu sake baki tayi tana kallon duniya tun a toilet din take kauyanci taba nan taba can da kyar ta yi alwalan ta fito, a dakin ma sai da taga kamar hajia zata fito ne ta tada kabbara[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣7⃣
Inda sukace jininta ne ya hau sosai, bata jima a asibitin ba ta koma ga mahaliccinta. Damuwa goma da ashirin.

Anan fatu ta fara hawaye, hajia kulsum cikin tausayawa ta miqa mata tissue paper ta goge fuskarta sannan taci gaba.
Na shaku da kakata sosai, a matsayin mahaifiya na dauke ta. Bana jin rasuwar mahaifiyata kamar nata. Bayan rasuwan kakatace zamana ya dawo gurin goggo asabe, nine wankinta dana 'yayanta da yake duk maza ne sai autar ta zainab yar shekara 4. Shara, wanke wanke da girki ya zama daily work dina, duka zagi da tsangwama kuma har na saba dasu. Duk abunda yake faruwa kakana bai sani ba, da yake baya zaman gida yana can masallaci tare da tsofi irinsa suna karatu. Idan ya ganni ina kuka sai yayita lallashina da inyi hakuri komai zai wuce inyi ta musu addu'a, Tunaninshi mutuwar iyayena yake damuna, bai san harda wahalan da nakesha yanxu bane. Kwatsam ranar wata friday bayan an dawo daga sallahn juma'a goggo ta sameni da duka wai ban gama abincin rana da wuri ba, na tsaya wasa, tace "shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya ki gama abincin sannan kixo kiyi wanki, kuma wallahi kika kai la'asar sai naci uwarki. Ta aza mini rankwashi a kaina wanda ya sani sakin wani wahalallen qara, "kina jina ina miki magana kina daga min kai kamar wata kadangaruwa don ubanki" da sauri nace "goggo kiyi hakuri" na cigaba da sheshshekar kuka, na tashi da sauri na fada kitchen. Kakana ne ya shigo da sallamarsa ta amsa tana muzurai, Allah yasa baiji abunda tayiwa fatu ba, don batayi tsammaninsa yanzu ba, baya dawowa a wannan lokacin. Ya shige dakinsa ya jima sannan ya kwala min kira, ina sauri zanje ta yafuto ni, naje, murde min kunne tayi tace "saura ki fada masa wani abu sai na ballaki, bulaliya kawai" ta sake ni hade hankada ni har ina cin tuntube na shiga dakin kakana. Cewa yayi inje inyi wanka zan rakashi unguwa. Na fito na fada mata ta harareni tayi kitchen. Da sauri na watsa ruwa na fito, kaya nasa da hijabi na cewa kakana na shirya muka fita. Maimakon naga mun shiga gari sai naga munyi hanyar gona. A cikin gonarshi a karkashin wata bishiyar dorawa muka zauna. Yace "fatu me asabe take miki a gida? Don yau naji wasu maganganu sabanin hankalina" ban yi jayayyaba na fada mishi komai. Idonshi yayi jawur yace " mahaifiyarki rahmatu amanace a gurina haka kema amanace, bazan bari ta maida ke baiwa ba insha Allah zan nema miki mijin aure kwanan nan inda zaki sami yancinki. Nayi farin ciki da haka sosai. Yayita bani baki hade da nasiha sai yamma liss muka koma gida. Muna zuwa yace in shimfida mishi tabarma a kofar dakinshi ya zauna. Daga ranar ya dawo wuni a gida yana waje tare da mutane, zai aika a kirani sau goma shi ma zai shiga gida sau goma. Abun yana damun goggo asabe sai dai bbu yanda ta iya. Na murmure na fara samun kwanciyan hankali, kaka ya sama min miji dan ladanin garinmu. Hafizu yarone mai hankali da nutsuwa, ga karatun addini baiyi boko ba amma yana da sana'arsa ta dinki, Yana samu ba laifi. Kaka yace "ga zabina wato hafizu dan ladan, idan kin amince inje in sami babansa muyi magana" gaskia bana jin sonshi a raina amma hankali da nitsuwarshi sun kwanta min. Nace "kaka duk wanda ka zaba shine zabina, fatana Allah yasa in samu zaman lafiya da kwanciyar hankali" kaka yaji dadin furucina yace "Allah ya miki albarka uwargidana" daria nayi nace "Ameen tsoho na" carbinsa ya dauka da niyyan min dukan wasa nayi saurin shigewa gida ina daria shima yana daria. Daga kan da zaiyi ya hango wata mota tana tahowa ta layin unguwanmu ga yara rudududu suna binta da gudu, parking tayi a jikin katangar gidanmu. Samari biyu ne suka fito suka nufo kakana da har yanzu yake zaune a kofar gida bai motsa ba. Kallo ya dawo kansu aka manta da mota. Sun fi kama da turawa ko aljanu.

Taku a kullum

Maman fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣6⃣
Sunyi sallah inda fatu taci gaba da labarinta..
Zaman lafiya akeyi tsakanin mamata da surkunanta, abu daya ya ke damun mahaifiyata rashin haihuwa. Duk lokacin da goggo innani tazo sai ta samu bakar magana ta yaba mata, nan ma kakata na mata fada. Ta shekara biyu ne ta shirya zuwa ganin gida. Tana isa ta tarar babanta ba lafiya sosai sai dai a kwantar a tayar, tayi kukan halin da yake ciki shi kuma yayi murnar ganinta, don tayi kyau tayi kiba. Ta bawa kowa tsarabar sa bbu wanda ta manta, bayan kwana biu tace a kaishi asibiti, mallam jauro (yayan babanta) yace ba za'a kaishi ba, ai rubutu da maganin gargajiyan da ta raina shi ya kawo shi har yau, yayi ta mita. Satin ta uku tana jinyarsa Allah ya amshi abunsa. Tayi kuka sosai bbu wanda bai tausaya mata ba. Bayan sadakan arba'insa akace azo ayi rabiyan gado, aka raba da yake ita mace ce bata tashi da komai ba sai budurwar akuya. Tun suna bata abinci har rannan mallam jauro yace shi ya gaji da ciyar da ita, hala wani mugun abun tayi acan mijin ya korota shine zata zo tace wai tazo ganin gida, ai wata biun ya cika mijin baizo ba, tana kuka tana bashi hakuri amma ko a jikinsa, hasalima inna haule da matarsa ce suke zugashi, a cewarsu zata cinyesu in suna bata abinci, Akuyarta ta sayar take cin abinci. Ranar sai ga babana ya zo inda ya tarar da rasuwan surikinsa, ya musu ta'aziyya yace zai dauki matarsa su tafi. Budan bakin mallam jauro cewa yayi kar rahmatu ta sake

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment