Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu zata rabu da mijinta, duk da ba sonshi takeyi ba amma zata so ta zauna da dan'uwanta. Kuma taga yana mata murmushi. Wata zuciya tace fateema yake yiwa ba fatu ba. Kar ma kisa shi a ranki, a duk lokacin da ya gano kece fatu bazai qara kulaki ba. Wasu zafafan hawaye ne suka qara gangaro mata tayi saurin gogewa, farouq ne ya shigo dakinta wai ta sauko yin lunch, goge fuskarta tayi suka fita tare da yake tana fashin sallah.

Acan garin modibbo kuwa mal usman ya kai saqo kamar kullum. Mal aminu ke tambayarsa? Ina uwargidan nawa, da fatan tana lafiya? Mal usman yace "tana lafiya kalau, tace a gaisheka ma. Kuma a bata takardun makarantar ta zata cigaba da karatu. Cikin jin dadi kaka ya dauko komai da komai ya bashi, da yake duk takardun nata a gurin kaka yake.
Bayan mal usman ya dawo ya bawa hajia, nan da nan tasa a nema wa fatu admission a GSU cikin qanqanin lokaci aka sama mata, aka gama komai ta fara zuwa lectures.


Anan zamu tsaya a FATU A BIRNI insha Allah bayan sallah zamu cigaba.
Kuyi hakuri na rashin post da wuri hakan ya samo asaline na rashin charge.
FATU NA MUKU HAPPY RAMADANπŸ‰πŸπŸŽπŸπŸŠπŸ‰
Allah ya bamu ladan dake cikin wannan wata ta Ramadan. Ameeen
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣0⃣

Fatu ta kalli lubna tace "he's on his way" jinjina kai lubna tayi ta fara magana "ki kula kiyi duk abunda ya dace, zan fita in nemo mijina nima" daria suka sanya dukansu, hijabi ta sanya ta fice a gidan a yar qaramar motarta, a waje ta hadu da sultan sukayi gaisuwan light ta harba titi shi kuma ya shige gidan maigadi ya rufe gate.
Da sallamansa ya shigo falon fatu data bashi keya ta juyo a kasalance ta amsa sallaman, daskarewa yayi a gurin yayinda ita kuma take jefanshi da malalacin murmushi tace "ka shigo mana" samun kanshi yayi da bin umarninta, a 1sitter ya zauna yayinda ita kuma take 2sitter suna fuskantar juna, bai taba ganinta haka ba gyale ko hijab ba sai yau, manyan idanunshi sexy ya zuba mata kamar yau ya taba kallonta, kunya ce ta rufe ta ta dago ido tace "kai yayana wannan kallon" bai sani ba bakinshi ya furta "u luk gorgeous" "tnx" ta furta mishi. Tashi tayi tace "mutanen gidan basa nan bari in dauko maka ruwa" a hankali take tafiya wanda ya bawa sultan daman kare ma bayanta kallo, tana shigewa kitchen ya jijjiga kanshi yace "control sultan, control" saisaita kanshi yayi ya gyara zama yana tunanin ta ina zai fara mata magana, bai gama shawara ba ta fito da tire a hannunta ruwa ne da cups sai juice, nan dinma kura mata ido yayi har ta iso ta jawo centre table kusa dashi ta ajiye kana ta sunkuyo yanda dole ya shaqi kamshin jikinta, tace "wanne za'a zuba maka? Sultan da ya lula shaqar kamshinta ya kuma shagala da kallon kirjinta yace "na'am" sarai tasan abunda yake kallo amma ta nuna bata ganeba cikin ranta kuma tace ka kalla halalinka ne. Miqewa tayi tsaye ta qara maimaita masa tambayar da sauri yace "juice" don yasan dole ta tsaya shaking dinsa kafin ta zuba masa hakan kuma na nufin shaking din abunda yake son kallo Murmushi tayi ta dauki juice din ta shaking dinsa daga tsaye ta sunkuya tana saka masa a cup, tana gama sawa ta koma gurin zamanta shi kuma ji yayi inama tayita tsiyaya masa har gobe, kodai yace ta saka mishi ruwa ne? "Control sultan" ya fada a sanyaye ya dauki kofin yasha kadan ya ajiye. "As u said kana son ganina" fatu tace dashi yayinda take harde kafuwanta, yace "ehh" tace "gani to".

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣1⃣

Sunanta ya kira "Fateema" tsikar jikinta ne ya tashi tace "na'am" yace "magana ce tafe dani very important" yayi shiru tace "ehen i'm ol ears" yace "fateey tun ranar da na fara ganinki nake jinki cikin raina _love at first sight_ da tunaninki nake kwana dashi nake tashi, nayi amfani da lokacin da muka dauka tare don mu shaqu nd to knw more about each other" fatu da tun daya fara magana kanta na qasa naga murmushi ya subuce a fuskarta, "fateey" ya kira sunanta a hnkali, dago idanunta tayi suka sarqe cikin nashi "I'm really madly deeply in love with you fateema" Da sauri ta sauqe kwayar idonta yayinda wani siririn hawaye ya biyo kuncinta, na rasa gane na farinciki ne ko ko! Shiru tayi, zufa ne ya fara keto masa ba dai tana da wanda take so ba! "Fateema ko kinada wanda kike so ne? Ya fada cikin tashin hankali. Kada mishi kai tayi alamar a'a. "Bakya so na ne? Talk to me fateema, idan bakya sona zan iya jiran har lokacin da kikaji kin fara sona, shirunki kan iya sa jinina ya hau pls talk to me" ya qarasa maganar yana dafe kanshi da yaji yana barazanar tsagewa. Lura da yanayinsa yasa tace "Ina buqatar time nayi tunani" yace "zuwa yaushe? Tace "ko nan da 2 weeks" yaqe yyi 'wanda masu iya magana suka ce mugun kuka' yace "kiyi hakuri na baki 5 hours, zan kiraki anjima in d nyt" zatayi magana ya tari numfashinta yace "kiji tausayina please" ya langabar da kai kaman qaramin yaro dolenta yasa tace "to Allah ya kaimu" yace "Ameen matata" daria tayi tace "tun kafin inyi tunanin? Kana gaggawa" shima darian yayi ya mance ciwon kan daya fara damunshi dazu yace "I knw tunaninki zai kasance positively" daga nan suka bige da hira yana sako maganan soyayyarshi tana basarwa. Kiran sallan da aka fara ne yayi daidai da shigowan lubna da jameel sai darawa sukeyi, ganin fatu ta sultan yasa sukayi kasaqe suna kallonsu, sultan tadi yayi tadi ya dawo 2sitter inda fatu take sai hiransu suke. Gyaran muryan jameel yasa suka farga yace "sannunku" fatu tayi saurin daukan gyalenta ta yane jikinta sultan kuma ya miqe yace "ai sai muje sallah ko, tunda kaji ana kira" bai kula darian da jameel ke mishi ba ya fita daga falon shima jameel ya bishi suka wuce masallaci yana tsokanarshi wai akan yarinya ya dawo parrot.
Suna fita lubna tace "mutumiyata ya akayi" labarin yanda akayi fatu ta bata duka. Kallon sama lubna tayi tana murmushi tace "sai nan da 4 days zamuyi move din mu na biyu" fatu tace "na fara tsoro anty lubna, anya bazai..... "noo insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi, mu hada da addu'a" Daga nan suka shiga daki sukayi sallah suka girka simple abinci mara nauyi, ana kiran isha sukayi sallah bayan sun idar ne su sultan suka dawo. Lubna tasa fatu ta qara gyara fuskarta sai dai wannan karon da gyalenta suka fito falo, abinci suka fara ci wanda fatu duk a takure take yayinda lubna, Jameel da sultan ko a jikinsu, suna qare cin abincin Jameel da lubna suka rako su bakin mota, inka gansu sai sun burge ka, a gaba ta zauna suka tafi.
Suna isowa gida tana kokarin budewa ya sa lock tayi tayi ta bude ta kasa, kallonshi tayi ya zuba mata sexy eyes dinshi yana murmushi, anan ta gane shi yasa lock, da shagwaba tace "amma ka wahalar dani, Allah na dauka yaqi buduwa ne" kwaikwayanta yayi yace "ai ban gaji da kallonki bane" daria tayi tace "kai ko? Bude mata yayi yace "sai na kiraki, kar kiyi bacci" "ok" tace yayinda ta fita ta maida marfin motar, daga mishi hannu tayi alamar bye amma bawan Allah yaqi tafiya, har cikin zuciyarta take jinjina irin son da sultan ke yiwa fateema. "Allah ka barmin mijina" ta furta a hankali ta shige cikin gida, shima sai daya ga kulewarta yayi ajiyan zuciya yace "Allah ka taimakeni" kana ya wuce gid[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣4⃣
Gefen sultan kuma yana komawa gida ya wuce dakinsa ya kwanta yana tunanin fateema, wayarshi ce ta katse masa tunaninsa, ganin number jameel yasa shi miqewa tare da amsa wayar "ka shigo ne?........ ok bari in fito. A haraban gidan ya ga jameel bayan sun gaisa ne kai tsaye suka shige cikin palourn gidan, mammi ce kadai zaune tana rubutu a wani memo, sallaman da sukayi yasa ta cire tabarau idonta "lale marhabin da mutanen S Africa" zama sukayi, bayan sun gaisa da mammi ne suka fito haraban gidan, sultan yace "dude yau ma tazo gidan nan wallahi, har rakata bakin gidanku nayi" ya fada yana shafa sajensa daya kwanta luff a fuskar sa, jameel dai kallon mamaki yake binshi dashi, tunda suke sultan bai taba cewa yana son wata ba, shi har ya fara tunanin ko yana da matsala ne, mata sunsha warce kansu a gurinshi amma ko kallonsu baya yi, amma akan wata wai fateema ya gama rudewa. Koyaushe sukayi waya sai sultan yayi maganar ta, jameel yana so yaga wacece fateeyn nan da take qoqarin zautar masa aboki. "Wai dama haka love din yake? Da ita nake bacci da ita nake tashi, jameel na rasa yadda zanyi" Jameel da ya tsaya kallonshi sai yanzu ya samu bakin magana "why not ka tunkareta? Ajiyar zuciya mai qarfi sultan ya sauke yace "I cant! Tana min kwarjini da yawa, to me zan ce mata ma? Kuma I asked farouq bata riqe waya nd tura wasiqa ka gane yayi yawa" Jameel yace "amma ka taba sanin tana da saurayi? Sultan yace "ko a skul bata kula kowa qawarta ma daya ce, a gida ma babu wanda yake zuwa mata, all I know shine ita TAWA CE! "Bravo alaika" jameel ya fada yana tafa masa, "ka iya yanda zakayi ka samu details akanta amma baka san yanda zakayi ka mata magana ba" sultan yace "kai dai ka taimakeni" "yanzu dai muje gidana ma qarasa maganar acan" shiga cars dinsu sukayi suka fita.
Gidan jameel ya hadu shima ba laifi, dai dai zaman mace daya. Driver na ajiyesu farouq ya fito da gudu ya shige cikin gidan, fatu ma ta fito tacewa mal habu ya jirasu yanzu zasu fito. Tana shiga motocin su jameel suka shigo. Bayan sun fito ne jameel yake tambayan mal habu ko aika ne ya kawo, yace masa ya kawo farouq da fateema ne, sultan dake gefe yayiwa jameel ido, jameel yace "ok kaje zan dawo dasu anjima" ba musu habu ya tafi. Su kuma suka tsaya anan suka cigaba da maganansu. Farouq a daki ya tarar da lubna tana gyara cikin wardrobe dinta, tace "farouq yaushe kazo" yace "yanzun nan, ni da anty fateema ne" tace waye kuma anty fateema" yayinda ta riqo hannunshi suka fito palour inda fatu tayi wa kanta masauqi a daya daga cikin kujerun da suka qawata palour.
Sannu da zuwa lubna tayi wa fatu tace bari in dauko miki ruwa, fatu tace "a'a nagode, ban jima da sha ba" suka gaisa anan lubna tace "sai dai ban ganeki ba" farouq yace "nace miki sunanta anty fateema kuma tazo karatu ne gurin mummy" daria sukayi lubna tace "to uban yan surutu, kai na tambaya? Bai kulata ba don ya danno tashan cartoon. Maida hankalinta tayi kan fatu tace "ke yar uwarsu ce kenan, kamar na taba ganinki, daga bauchi kike ko? Fatu tace "ehh, mummy tace a kawo muku abinci, kun dawo lafiya? "Lafiya kalau" lubna ta bata amsa. Fatu ta kalli farouq tace "my sojaa lets go" ba musu ya miqe yace "bye anty lubna, kuma sai na fadawa mummy kince nine uban yan surutu" zaro ido lubna tayi tace "kaji dashi" fita yayi zuwa inda sukayi parking amma wayam ba mota, sai motoci biu da ya gani, zai juya ya koma ya hango sultan da jameel da bayan cars din. Gurinsu ya nufa dai dai nan su fatu suka fito suma. Fatu tana ganin ba motan su tace "ba dai mal habu tafiya yayi ya barmu ba? Sai dana ce ya jiramu fa" ta karisa maganan kamar zatayi kuka. "DJ" lubna ta kwalawa jameel kira suka taho dukansu sultan n Nna cewa "oyoyo uwargida, don yanzu kin tsufa wata sabuwa zamu kawo" lubna ta harareshi na wasa tace "hurul ain kenan? Suna can suna jiransa insha Allah" gaisawa sukayi tsakaninsu fatu na gefe riqe da hannun farouq tana wasa dashi, can tace "ya jameel sannu da dawowa" yace "yauwa, fateema ko? Tace "ehh" gaisawa sukayi tace sai anjiman ku. Da sauri sultan yace "ina zaki je" bata kalle shi ba taja hannun farouq tace "gida" jameel yace "ni nacewa mal habu ya tafi zan maida ku in munyi sallah" ba yanda ta iya dole ta koma, su kuma suka wuce masallaci da farouq. Lubna taja fatu dakinta sukayi sallah, sai tadi sukeyi kamar sun jima da sanin juna, anan ta tayata qarisa gyaran wardrobe din, suka share dakin duk da kafin su dawo an share da gyara ko ina na gidan. Su sultan basu dawo ba sai bayan sunyi sallah isha. A palour suka tarar da su lubna da fatu suna ta tadinsu, sallama sukayi suka shigo, Lubna tace "ba dai har anyi sallah isha ba? Jameel ya zauna kusa da ita yace "ina zaki sani tunda kin samu abokiar hira" lubna ne ta canja tasha zuwa cartoon wa farouq tace "fateema ki shiga daki kiyi sallah, bari inyi serving dinsu abinci" shigan fatu keda wuya suma suka wuce kan dinning jameel yace "mutumina ka tafi da yawa fa, irin wannan kallon haka" cike da tsokana ya karasa maganar. Lubna tace "ba dai fateema yake kallo ba? Sultan yace "dadina dake yawan tambaya, ni kawai ki tayani campaign" Jameel yace "ni dai kaman na taba ganinta a bauchi, amma inaga mahmud zai fi saninta don ya fini shiga ziyara, ko hutu yazo sai yaje bauchi ya zaga dangi" nan dai sukayi ta tattaunawa har suka samu solution, fitowan fatu yasa sukayi shiru, ganin haka ta gane maganarta sukeyi kawai ta wayance ta zauna kusa da farouq. Bata dade da zama ba suka kammala jameel yace "muje ko fateey" sun fito haraban gidan jameel yace "ohh ashee ba mai da yawa a mota na, pls sultan ka sauqesu mana" sai da yayi dan jimm kana yace "ok" jameel ya tura farouq baya, lubna kuma ta budewa fatu gaba tace "ki zauna a gaba ke" ba musu ta shiga, lubna ta miqo mata leda tace "ga tsaraba ba yawa" godia fatu tayi sultan yaja su suka tafi.

Taku a [truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [4:05PM, 7/26/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣2⃣

Fatu na shiga gida ta samu farouq na kallo ya mata oyoyo tace "har yanzu bakayi bacci ba? Yace "yau saturday, remember? Ba skul gobe" tace "yess hakane, ina mummy? Yace "tana falon daddy" tace "ok, bari in shiga in watsa ruwa".
Wanka tayi ta sa sleeping dress ta dora hijab kana ta fito palour, ganin mahmud a zaune kusa da farouq wanda har yayi bacci yasa kirjinta dukan uku uku! Tun dawowan shi yake tsare ta da tambayoyi yana so yasan daga cikin wani gida take a familyn nasu, answers da take bashi basa gamsar dashi kuma akwai alamun rashin gaskia a tattare a ita, _real lawyer_ πŸ˜„. Rufin asirinta daya shine after walima na gama karatunshi ya fara aiki a abuja, ba kowanne weekend yake dawowa ba, duk randa ya dawo kuma bata bari su zauna su kadai, in kuma suka zauna zai fara tambayoyi, in mummy na kusa sai tace "mamuda nan fa ba kotu bane da zaka dame yarinya da questions, distant relative ce baza ka ganeta ba" To yau kam qaryanta ya qare tunda ba mummy mai rufe bakinsa. Murmushi ta qaqalo tace "ahh mutan abuja sauqar yaushe" murmushin shima yayi yace "dazu da yamma, kina fita na shigo, naje gidan jameel din ma na samu kuna maganarku ke da matarsa, so bana son katse muku sai na tsaya, da naji bamai qarewa bane yasa na tafi" cikinta ne ya bada sautin qulululu... kirjinta na bugawa da sauri da sauri tace "m..me..me.. kaji? Murmushin cin nasara yayi ya qara narkewa a cikin kujeran yace "abunda kuka gama magana akai" Shiru tayi fuskarta na qasa tace "can u kip a secret?" bai motsa daga kwanciyar ba yace "yess, amma ina son details" briefly ta fada masa abunda ya dace, ta qarisa maganar da cewa "promise me babu wanda zaka fada wa" daria yayi yace "ni banida gulma, bincike na iya" daria sukayi dukansu hkan yayi daidai da shigowan mummy tana cewa "oya farouq kallon ya isa haka kaje ka kwanta" ganin su fatu yasa ta yin shiru Tace "fateema kin dawo? Fatu tace "eeh mummy, anty lubna tace a gaisheki kuma tana godia da kunun aya" da murmushi a fuskar hajia tace "madallah, mahmud dauki farouq ka kaishi dakinsa" Mahmud na haurawa tace "fateema akwai matsala ne? Naga mahmuda yana damunki da tambayoyi" murmushi fatu tayi tace "babu komai mummy, munyi magana dashi" hakan yayi daidai da dawowan mahmud mummy tace "to asuba ta gari, fateema ki locking kofa ki kashe wuta, na tafi" suka mata sai da safe ta wuce side din daddy.
5mins ya qara shima ya mata sai da safe, kopa ta kulle ta kashe wuta ta wuce dakinta. Tana hawa gado ta lalubo wayarta ta kira xahra "badai kinyi bacci ba? Fatu tace da ita xahra wacce da alama tayi nisa da baccinta tace "8:30 ma ina kan gado" fatu tace "ok dama labari zan baki amma tunda kin fara bacci sai da safe" da sauri xahra ta miqe zaune harda kunne bedside lamp tace "bani in sha, wallahi na tashi" daria sosai fatu tayi tace "shegen son labari"

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[9:37PM, 7/26/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣3⃣

Labarta mata yanda akayi duka tayi. Shiruu xahra tayi can tace "anya wannan plan din babu hatsari a ciki, kar garin neman gira a rasa ido fa" itama fatun shiru tayi xahra ce tace "are you there? "Yess" fatu ta bata amsa ta cigaba da cewa "insha Allah ba matsala, ki tayani da addu'a, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" "Ameen" xahra tace suka cigaba da tattaunawa daga baya sukayi hanging.
Missed calls din sultan ta gani kusan goma a screen din wayarta tace yaushe ya kirani? (Har yanzu dai sabin shiga ne) Wani kiran ne ya qara shigowa ta dauka tace "hello" bai amsa ba ya watso mata tambaya "da waye kike waya? Ina kiranki ana cewa call waiting" murmushi tayi kaman yana kusa da ita tace "levels ne fa, ka koma lafiya? Shima murmushin yayi yace "lafiya lau, ya maganar mu? Tace "wacce kenan? Shiru yayi kaman bazaiyi magana ba, a kalla babes sun kai goma shima yana musu irin tambayan nan cikin jin kai, amma reshe ya juye da mujiya yau shi ake yiwa! "Answer na dazu, u said zakiyi tunani" fatu tace "ok, na tuna" yace "ina jinki" shiru tayi yayinda shi kuma ya qagu yaji matsayinsa a gurinta, gani yakeyi in ya rasa fateema duk matar da ya aura baza ta samu soyayyar da yake yiwa fateema ba. Sunanta ya kira "fateey, kinyi shiru" sai da ta dauki 5seconds kana tace "yess, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" farinciki fal a fuskarsa yace "u mean kin amince? Tace "yeah". Hira suka yi cikin wayewa da natsuwa, sai da sukayi 30mins yace "ya kamata in barki haka kiyi bacci, amma ban gaji da jin sweet voice naki ba" qanqame wayar tayi a kunnenta tana lumshe ido ta qara qasa da murya tace "okay, gud nyt" yace "nyt dear, karki manta kiyi addu'an bacci" tace "ok tnx" sallama sukayi. Suna kashe wayan fatu ta tashi ta dauko pic dinsu tare da kudin sadakinta ta qura musu ido, kuka ne ya kwace mata tayi mai isarta har bacci ya dauketa. Sultan kuma yana ajiye wayan yace "saura fatu" murmushi yayi ya fara danne dannen laptop akan business dinshi. Yau kimanin 4days da fara soyayyarsu, in kaga yanda suke love sai ka aza sun shekara, wani zazzafan soyayya sultan yake nunawa fatu, yayinda itama take nuna masa bata da kowa like him. Haka da yamma zaizo ya dauketa suje yawon shaqatawa su sha hiransu ya dawo da ita, ga shopping niki niki. Wata rana kuma a gidan jameel zasu yi hiran, sai dare ya dawo da ita, nan ma sai an qara bata time kafin ta shiga gida. *love kenan* Mummy ta lura da hakan ta kira fatu tace "meke faruwa tsakaninki da sultan? Cikin jin kunya tace "wai mummy sona yakeyi" murmushi mummy tayi tace "kefa? Kina sonshi? Rufe fuska fatu tayi hakan yasa mummy ta gano answer dinta, "Alhamdulillah" mummy ta furta a hankali, tace "kin fada mishi matsayinki a gurinshi? Da sauri fatu tace "a'a mummy ba yanzu ba, kuma zan fada mishi da kaina in lokaci yayi" mummy taso ta gane wani abu amma ta basar a cewarta tunda suna son junansu shykenan. Ranar da suka cika 5 days suka hadu a gidan jameel. Hiransu sukeyi gwanin ban sha'awa, lubna ne ta fito da pics ta rarraba musu suna kallo, na daria suyi daria, na a bada labari a labarta, caraf a cikin pics din dake hannun fatu taga hotonsu itada sultan, turo baki tayi tace "honey wacece kusa da kai haka? Ta wani manne maka! Ta qarisa maganan tana miqawa lubna pic din, lubna na karba tace "laa fatu ce, uwargidan sultan" sultan da tunda fatu ta fara magana notinan kanshi ya sunce, ji yakeyi kaman ya rusa ihu, shikam fatu ta cuce shi, a 'yan kwanakin da yayi da fateema ya lura tana da kishi, yanzu in tasan fatu matarsa ce ya zaiyi. "Innalillahi" yayinda fatu ta miqe tsaye tana dafe kirji "lubna matarsa fa kika ce"..[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [9:45PM, 7/19/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣8⃣

Sultan na fita gidansu ya nufa, kai tsaye room dinsa ya nufa ya zauna akan daya daga cikin kujerun da suke room din. Shi gabadaya jin haushin fatu yakeyi, ta bata mishi plan din rayuwarsa, gashi akanta har sun sami matsala da abokinshi wanda tun suna yara rabon da hakan ya faru, shi fa bazai iya ba, never!! Zai saketa ya kawota gurin mammi ya kuma gargadeta tayi kipp da bakinta. Laifinshi ne ma daya qarfafa bincike wajen nemo innar tashi. Tunani ya fara shekara biyu da suka wuce yana tare da mammin shi a dakinta suna hira lokaci daya tayi shiru yace "mammi lafiya" tace "tunanin 'yar uwata nakeyi, ko ya take? A ina take? ita kadai ce 'yar uwata da muke uwa daya, sai kannena da muke uba daya, shekarana 6 a lokacin aurensu ya mutu, ba yanda ba'ayiba a maida auren abun ya faskara, a haka aka barsu amma kuma ana tare don rabuwansu bai raba zumuncin dake tsakanin babanta da babanshi wanda suke yan uwan juna ba. Ina shekara 7 muka je dukku anan wani da ake cewa mal sirajo ya ganta yace yana so, a lokacin yana da mata da 'yayansa 4, da kyar aka bashi aurenta don ma tace itama tana sonshi ne, saboda bakin cikin hakan dangin mu suka tattara suka bar garin a cewarsu ta zabi bare akan dan'uwanta, duk da shi din ma bafulatanin ne, amma wai su fulanin yawo ne. Na sha kuka dana rabu da ita, bamu wuce ko ina ba sai yola dama can ne asalin garin mu, anan muka zauna har babana ya fara shiga birni yana kasuwanci anan yaga yara na zuwa skul ya saka ni, har Allah ya buda masa sosai yayi aure, kamar yanda ka sani kannena biu, rufa'I da musa. Mahaifinka shima auren dangi aka hada ni dashi, a can na haifeku duka muka dawo nan gombe lokacin ina goyon amrah. Na tashi cikin dangi amma ina

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment