Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatu tace "kince zan zauna anan inyi karatu to kuma banida kudi kuma ai bazan zauna hakanan ba tareda ina muku aiki ba" murmushi hajia tayi sannan tace "ni babu abunda zaki min, kudin makaranta kuma nice zan biya, dake dasu jameel duk daya na dauke ku" fatu harda hawayen farinciki tana kwararawa hajia kulsum addu'a sai da ta dakatar da ita. Fatu tace "hajia to kakana fa? Don yace in sanar dasu in na isa" hajia tace "karki damu nasan abunyi" farouq ne ya shigo da sallaman shi ya nemi guri kusa da fatu ya zauna hajia tace " farouq a ina ka zauna tun tafiyanka sallah isha? Yanzu gashi har 8:42" yace "mummy gurin baba mai gadi na tsaya, yana bani labarin sojoji ne, kinsan ina son zama soja" hajia tace "kai kam da son soja, shima mal amadu da yake biye maka kana sa shi surutu" daria sukayi dukansu, farouq yaje ya dauko home work dinshi ya kaiwa fatu wai ta tayashi. Yanda take nuna mai komai dalla dallah yasa hajia cikin mamaki, don ta english take masa bayanin wanda in bai gane ba sai ta masa da hausa, sun gama ya dauki bag dinshi ya musu sai da safe ya wuce dakinshi. Hajia ta dubi fatu wacce tafiyan farouq bai mata dadi ba, don har ta fara takura kana tace "fatu kince a kauyenku kikayi primary, to sec fa? Fatu tace " a garin kumo nayi scndry skul dina, abokin babana ne wanda ya kawo ni tasha yake zuwa da sassafe ya kaini, in an tashi ni kuma in hau acaba ya mayar dani kauye, anan na fara tun daga jss1 har nayi waec da neco, na samu kyautuka da dama ranar speech and prize giving day din mu. After months result ya fito na samu both waec and neco, sai dai banyi jamb a shekarar ba. Bayan aure na ne nayi jamb ina tunanin in sultan ya yarda sai inyi university dina. To da yake bai zo ba sai abun ya mulmulce" hajia tace "kinci jamb dinne? Fatu tace "eeh naci, ina da 220 points" hajia tace "ahh lalle kinyi kokari, last year ne kikayi ko this year? Fatu tace "nayi last year kuma nayi this year" hajia tace "ashe bazamu sha wahalan sama miki admission ba, yanzu dare yayi muje ki kwanta ki huta, gobe in Allah ya kaimu zamu qarasa magana" kashe komai na wuta sukayi suka haura sama hajia ta kaita wani daki kusa da na farouq, daki ne madaidaici da toilet dinshi a ciki, komai na dakin pink nd white ne, gadon Mai dan girma, sai wardrobe dinshi da mirrow duka pink, can gefe kuma gurin karatu ne desk da chair white, labulayen pink nd white sai paint na dakin sky blue mai oily sai sheqi yakeyi. Sana'ar dai fatu ta sake yi wato sake baki, hajia tace "nan dakin aisha ne yanzu kuma ya dawo naki" fatu tace "hajia duka wannan, nikam ko da mai aikin ki zan dinga kwana" hajia tace "a'a anan zaki zauna na fada miki bana son kina banbanta kanki dasu farouq, duk daya kuke, ki saki jikinki tamkar nan ne gidanku, abunda nake bukata daga gareki kenan in har zan samu" fatu tayi saurin riqo hannun hajia tace "kinfi karfin bukatar abu a gurina sai dai ki bani umarni, insha Allah zaki sameni mai miki biyayya, wallahi ban taba tsammanin akwai masu kudi da son jama'a irinku ba hajia. Nagode Allah ya biyaki da Aljannah ya kuma raya miki 'yayanki" "Ameen Ameen" hajia ta fada sannan ta mata sai da safe ta wuce dakinta, rufe kofar fatu tayi ta ajiye jakanta a gado, ta hau kan gadon tana daddannawa, can ta miqe ta shiga toilet din sai da ta gama qare masa kallo tana daria sannan ta fito ta cire hijabinta ta bude jakanta ta dauko soso da sabulu hade da brush da tootpaste ta ajiye a gefe. Cire kayanta tayi ta dauki Wani extra zani da alama na wankanta ne tasa ta shiga wanka, bata dade ba ta fito ta sane jikinta ta shafa mai, tazo daukan wani kaya ne taga wasu night wears riga da wando orange colour masu laushi akan gadon, taga kuma an saka bedsheet an lailaye gadon wahoho fatu tace "Alhamdulillah" tasa kayan ta jera kayanta kala uku a cikin wadrobe din jakan ma tasa shi a ciki wanda akwai kudinta a ciki. Ta kashe wuta ta haye kan gadon tayi addua ta rufe idonta tana tunani har bacci ya dauketa.

Taku a k[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣2⃣
Tunda na fara kaka murmushi yakeyi cikin jindadi, har bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba, na share ba tareda ya gani ba. Sai dana gama yace " fatu Allah ya amsa addu'a na, kullum burina mijinki yazo ya dauke ki, ayau Allah ya nuna min ranar" kwalla taff a idon kaka na farinciki. Hajia nayi dana sanin rubuta wannan wasiqar don bawai inason zuwa gurin sultan don ya karbe ni a matsayin matarsa bane, a'a don ya sauwaqe min ne nima in samu dai dai ni in aura. Kuma hakan zaisa kaka ya samu kwanciyar hankali. To amma tsananin farincikin dana hango shimfide fuskarsa sai tausayinsa ya kamani, ban kyauta masa ba. Kaka yace in shirya gobe in tafi. Kuka na fara Nace a'a sai shi sultan din yazo, zanyi ta zama da igiyarsa a kaina har ranar da Allah ya kawo shi. Ban taba yiwa kaka musu ba sai ranar. Bai ce min komai ba har na tashi na tafi dakina na cigaba da kukana, ina tausayin kaina da kaka. Da kawu muntari ya dawo aka fada masa abunda mijina ya rubuta shima ya bada goyon baya in tafi, goggo asabe kuwa hankalinta ne ya tashi don bata son taga abu mai kyau ya rabe ni. Ana gobe zan taho na fara shirin tafiya gombe don inje ayita ta qare, na kasance koyaushe ina tunani da addu'ar Allah yasa zuwana ya kasance alkhairi. Hajia har abinci nake kasa ci, ace an daura mini aure yau shekara amma mijin bai ko waiwayeni ba. Abunda kaka ya fada min ne ya girgiza ni, wai da kawu muntari zanyi tafiyan!!! Tirkashi😳😳
Nace masa ai a wasiqar sultan yace inzo ni daya, na nuna masa tunda nayi karatun boko ai bazan bata ba koda a kano ne😜, Kaka ya amince. Da dare kasa cin abinci nayi don ina da tabbacin in naje sultan zai sake ni kamar yadda zan bukata. Da kyar kaka yasa na sha fura da daddare a dakinsa, mun kusan kai karfe goma yana min nasiha gameda inda zan koma wato gidan mijina, jinshi kawai nake yi ina mai tausaya mana.
Tun da asuba na gama shiri kaka yana dawowa daga masallaci naje na gaishe shi, ya miqo min 15k wai in riqe zai min amfani a can din. 5 din saman na dauka nace zai ishe ni, ya qara min nasiha ya bani addu'o'I. A lokacin gari ya fara haske, machine din abokin baba ne mukaji yana diri a kofar gida. Har daki na sami goggo asabe na Mata sallama, duk 'yan gida aka fito domin ganin tafiyana. Ban dauki komai ba sai 'yar jakana na skull da kudin sadakina 20k sai kayana kala 3 don nasan ba jimawa zanyi ba. Kudin kuma bashi kayanshi zanyi. Na haye machine din ina hawaye haka muka kama hanya suna daga min hannu. 6:22 muka iso kumo, direct tasha muka isa ya sakani a motar gombe, shi ya biyamin kudin motan ma, yayi tafiyarsa don anan kumon yake aiki. Bakwai saura motar mu ta tashi mune bamu shigo garin gombe ba sai 7:30. Anan na sauka na sayi abinci, fitowana kuwa tsautsayi ya afka dani. Wannan shine takaitaccen tarihina.

Shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa a ransa, farouq ne ya dawo yana mummy oyoyo, hajia ta shafa kanshi tace "Ka dawo" yace "ehh, yauwa mummy kika ce dama baza ta tafi ba, to yanzu in mata questions din? Hajia tace "gata a gabanka ai" zuwa gurin fatu yayi yace "dama tambaya daya ya rage, ina ne gidanku? Kai tsaye fatu tace "a kauyen kumo, ka taba zuwa kumo? Yace "aa'aa" tace "kana kama min da wani sunan shi jameel" yayi caraf yace " ya jameel yayi aure rannan ya tafi da matarsa south africa wai yana aiki, amma naji dady na cewa ya kusa dawowa" kafin ya qara bude baki hajia ta katse shi tace "aje a canja kaya ayi shirin zuwa sallah magrib" ba musu ya haura sama da gudu. Hajia ta juyo ta kalli fatu da kanta na qasa tace " jameel dana ne yana da kanne 4, mahmud ne mai binsa sai khadija da Aisha da autana umar farouq. Mahmud yana karatu a cyprus lawyer ne, insha Allah nan da 4 months zai kammala ya dawo gida. Khadija da Aisha sunyi aure inda khadija ke Abuja Aisha ke kano. Jameel abokin sultan ne tun suna yara, daa ba'a unguwan nan muke ba, muna jeka da fari ne, Allah cikin ikonsa ya budawa mahaifansu inda suka sayi fili anan GRA, In kin lura yanayin ginin gidajen iri daya ne amma kowanne da design dinshi. Skul daya sukayi tun daga primary har sec, inda a university kowa da zabinsa, don sultan fita waje yayi ya karanci Business ad, while jameel yana gwags karantan likita. Alhamdulillah sun kammala with flying colors. 8months da suka wuce jameel yayi aure ya tafi da matarsa south africa akan karatunsa. Mahaifiyar sultan qawatace sosai, hakama dads dinsu suke abokai.
Kiran sallah da aka fara ya tsayar da hajia, sai da aka idar tacewa fatu ta isa daki tayi sallah, ita kuma hajia ta nufi kitchen don duba me aka girka.


Nima na fita daga gidan don inje in daura nawa sanwar kar oga ya dawo babu abinci, kunsan bature yace "Hungry man is an Angry man"πŸƒπŸ½πŸƒπŸ½πŸƒπŸ½πŸƒπŸ½πŸƒπŸ½
Taku a[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣5⃣

Bangaren hajia kuwa wautan fatu take gani, ace miji kamar sultan kaso rabuwa dashi? Ita dai bazata bari hakan ta faru ba shiyasa take son fatun tayi karatu ta kuma waye yanda shi sultan bazai so koda kuda ya gifta tsakaninsu ba. Duk da sultan bai kyauta ba amma ba taga laifin shi sosai ba don rayuwar turai yayi, ya saba ganin mata masu class da wayewa zai so matar sa ta kasance kamar su.
Don haka hajia tayiwa kanta alkawarin kai fatu gidan sultan cikin so da kaunar junansu.

Tun asuba fatu ta tashi tayi sallah ta dan jima tana addu'o'inta sannan ta shafa. Ta kusan minti 30 a zaune tana tunanin ko ta fita ne ta taya mutanen gidan aiki ko ta zauna ne oho. A haka har gari ya fara haske Knocking kofarta taji anayi da sauri ta tashi ta bude. Hajia ta gani ta durkusa har kasa ta gaisheta, hajia ta amsa tana murmushi tace "ya kwanan baqunta" fatu tace "Alhamdulillah" hajia ta miqo mata wata doguwar riga tace "idan kinyi wanka ki saka, sai ki sauqo kasa breakfast ni zan je in shirya farouq zuwa skul" fatu ta karba tayi godia ta ajiye kan gado Sannan tayi hanyar fita daga dakin hajia tace "ina zaki je" fatu tace "zanje in shirya farouq dinne" bata jira me hajia zata ce ba ta fita ta shiga dakin farouq don kusa da nata yake, tattausan murmushi hajia tayi sannan itama ta fice zuwa dakinta. Fatu tana shiga dakin ta samu shi baccinshi ma yakeyi, a hankali da wayo ta tashe shi ya shiga wanka bayan ta hada mishi ruwan wankan. Da ya fito ta tsane mishi jikinshi ta shafa mishi mai hade da sanya mishi uniform dinshi, gurin sa neck tie ne suka kai ruwa rana, don daga ita har farouq din babu wanda ya iya. Daria yake ta mata yace "mummy ta iya, muje ta saka min" daukan skul bag dinshi tayi suka sauqo zuwa palour anan suka sami hajia tana rufe lunch box din farouq. Tace "iyee har kun gama ne?" Cikin daria farouq yake bata labarin yanda fatu ta rinqa kokawa da neck tie wai bata iya ba, hajia ta dara kadan ta kirashi tana saka masa duk fatu tana gani. Dinning hajia ta kaishi aka hada mishi tea ga hadedden indomie dinshi a gefe, cikin nitsuwa ya cinye ba tareda ya bata kayansa ba, kana ya tashi yace "mum yau ma kece zaki kaini skul" hajia tace "noo, driver zai kaika, jiya ma don yayi asubancin tafiya garinsu ne" Farouq ya hade rai hajia na lallashinshi don kar ya makara. Fatu ce ta jawo shi jikinta ta rada masa magana a kunne, duk iya gulma na banji me ta fada masa ba, kawai naga suna daria ta riqo hannunshi tace "muje in raka ka mota" hajia da ta tsaya kallonsu tace "ohh wariya za'a min kenan? Farouq yayi saurin hugging dinta tace "a'a mummy kema zan fada miki in na dawo, bye" har mota fatu ta rakashi ya shiga suna dagawa juna hannu, baba maigadi ne ya bude gate suka fita, yana kokarin rufe gate din fatu ta kalleshi da kyau.
O M G 😳 mai kawo mata aika ne. Da gudu ta koma palour shi bai ma ganta ba.

Taku a kullum

Maman Fai'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣9⃣

Hajia tace yaje yayi wanka ya sauqo yin lunch, fatu ta riqe hannunsa suka tafi dakinsa tana tambayarshi labarin skul. Yayi wanka fatu ta wuce dakinta don gabatar da sallah, shima farouq wucewa mosque yayi. Bayan ya dawo ne suka hallara a dinning don cin abinci, suna kan ci fatu ta dauko musu zobo, ta tsiyayawa kowa kana ta zauna. Farouq ne ya fara tabawa yace "mummy wannan Ribena ne? Mummy tace " kamar zobo ne lemme taste it" hajia ta dan kurba tace "natural" kana ta kira dija tazo "haba dija, dama kin iya irin wannan zobon amma baki taba mana ba? Dija tace "hajia bani bane fa, fatu ce tayi" nan hajia ta maida dubanta ga fatu wacce cin abincinta take hankali kwance, tace "fateema a ina kika koyi wannan zobon? Fatu tace "mummy a skul ne, nayi food nd nut ai" fatu ta fada mata yanda sukayi. hajia tayi smile tace "zaki koya min nima, gashi babu wani flavour ko color, komai natural sai qarin lafiya ba abun cutarwa" duk sukayi daria, in banyi qarya ba kowa yasha zobo cup 5😜.

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, yau fatu ta cika 3 weeks a gidan, tayi fresh tayi kyau abunta, hajia tana nuna mata gata ba qarya, don kaya kala kala naga fatu na sawa ita da tazo da kala 3, shoes and bags ma gasu nan kamar na wata yar gwamna, make up kuwa takanas hajia ta kaita PRETTY AYSHA PALOUR ta koya mata kwalliya na zamani.

Sanye take cikin wani swiss lace mai pink nd blue, tayi simple make up amma tayi matuqar kyau, kayan sun amshe ta kamar ka sace ka gudu, gyalenta ta dauka ta yafa a kafada ta fito palour ta samu hajia na kallo manara tv. "Sannu da hutawa mummy" hajia ta juyo tace "yauwa yar mummy, gurin mal usman zaki je kice kafin ya wuce kumo ina son ganinsa" fatu tace "to mummy" ta fita daga palourn ta nufi bakin gate. Turuss ta tsaya ganin sultan na magana da mal usman din. Rabon da ta ganshi tun ranar shigowanta gombe. Zuciyarta ne yake dukan uku uku, kar fa ya ganeta ya korata kauye ko kuma yaci mutuncinta, wayyo Allah! A zuciyarta tana ina ma bata fito yanzu ba. Yana gama maganansa ya miqa wa mal usman envelope yana cewa "bari in gaisa da mummy" juyowan da zaiyi yayi arba da ita, dumm gabansa ya fadi, "tsarki ya tabbata ga Allah da ya tsara wannan halitta" sultan ya fada a zuciyarsa yana mai qarewa fatu kallo ita ma din shi take kallo, sunfi 1 min a haka, fatu ce tayi qarfin halin fara tafiya ta nufi gurinsa.

Taku a kullum
Maman Fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: [3:15PM, 7/11/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣2⃣

Kwanaki sun shude yau watan fatu biyar da barin garinsu tayi nisa a karatunta kuma tana fahimta, qawarta daya sunanta itama ma fatima. Qawancen su ya samu asali ne ranan wata monday fatu tayi latti sosai gashi har an shiga lecture kuma lecturer baya barin a shiga, fatu sai safa da marwa takeyi a bakin hall din, fatima da take ciki ta hango ta sai ta bata tausayi, don tana lura da fatu, irin dodging lecture da students sukeyi ita sam bata yi ga kokari kamar me! Tana cikin tunaninta taji an jefe ta da abu; dumm gabanta ya fadi don tasan lalle yau zai korata waje, maimakon taji ance yi waje sai taji yace "Me kike kallo a waje? Bata san lokacin da tace "qawata ce" "u can join her" abunda ya fada kenan. Zare ido ta fara yi tace "sir bata da lafiya ne, ko dazu she called me tace bazata samu zuwa ba, so ganinta da nayi ne ya ban mamaki" sai da yayi dan jimm sannan ya mawa fatu hannu da take waje ta sake baki tana kallon ikon Allah. (Sana'ar ta ne dama sake bakiπŸ˜‚). Sai da ta shigo yace "get well dear" tana in ina tace "thank you sir" guri ta samu ta zauna aka cigaba da lecture. Bayan ya fita ne ta samu fatima ta miqa mata hannu hade da sallama ta amsa hade da shaking hannunta. Fatu tace "amma kin taimakeni nagode sosai, gashi ya bamu light akan abunda zai fito a exams. Fatima tayi murmushi tace "ai kuwa, me sunanki? Fatu ta amsa "Fateema Mahmud" tayi carab tace "sunan mu daya amma ana kira na xahra levels" fatu tace "I like it" xahra tace "tnks namesey"
Haka qawancen su ya cigaba cikin aminci. Suna ziyaran junansu lokaci lokaci, hajia ta yaba da hankalin xahra shiyasa take barin fatu tana ziyartar ta. Bangaren sultan kuma soyayyar fateema ta gama narkewa a zuciyansa, sukan gaisa amma daga nan yake tsayawa, dan gaisuwan da yake yawan shigowan ma ya rage, don akwai ranar da yazo fatu tana ganinshi ta haura sama, yazo ya zauna suka gaisa da mummy, hajia tace "nikam sai kora min 'ya kakeyi, da ta ganka sai ta tafi" yayi murmushi yace "afuwa mummy" Haka suka cigaba da hiransu har yake tambayanta daddy tace yana Abuja, don shi bai cika zama a gida ba, lokacin zuwan fatu ma baya gida, da ya dawo hajia ta bashi labarin ta bai yi comment akai ba, illa cewa da yayi Allah ya taimaka. Yasa hajia ta kira masa ita ya mata questions akan rayuwarta ta bashi amsa, kana ya mata nasiha yace ta dauki gidan kamar gidansu, kuma ta maida hankali akan karatu.
Yau shirye shirye akeyi a gidan don tarban manyan baki, mahmud ne zai dawo daga cyprus sai jameel da matarsa suma zasu dawo daga south Africa. Hajia ta kasa zaune ko tsaye haka fatu, duk wani shiri da girke girke an kammala sai isowan su kadai ake jira, karfe 2 na rana sukayi waya sun sauqo, nan da nan hajia ta aika driver a dauko su, farouq yaso a je tarbansu hajia tace nooo. Bayan tafiyan driver fatu tace wa hajia zata je tayi wanka kafin su dawo, hajia tace to. Fatu ansha aiki, tana shiga daki tace bari ta dan miqe a gado kadan, bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba.
Jameel sun dawo cikin dokin ganin gida, hajia tayi murnan ganinsu harda kwallanta, farouq murna kamar ranar ne sallah. Bayan an gama gaishe gaishe aka nufi dinning cin abinci, amaryan jameel, lubna mai dauke da qaramin ciki tafi kowa kwasan girki, sai santi take zubawa, mahmud da yake qanin mijinta yana ta tsokananta kota kulashi, mummy dai dadi ya hanata magana. Can hajia tace "mahmud kai kuma maimakon kana gama karatunka kayo gida shine ka biya can south africa ko, wato ko missin din gida baka yi? Riqe hannunta yayi yace "wlh mummy jameel ne ya dameni wai in biya can tunda suma sun kusa dawowa wa, mummy 3 wiks kawai nayi a can din fa" ya qarasa maganarsa cikin shagwaba, daria sukayi lubna tace "ji shi kamar wani yaro" "yaro nake tunda ban kusa ajiye baby ba" mahmud ya bata amsan da ya saka ta kunya, don haka tayi shiru. Murmushi Jameel yace "mummy nafi son mu dawo rana daya ne thats why nace ya biya can, nd he enjoyed staying there" hajia tace "Alhamdulillah tunda kun dawo lafiya all, sai shirye shirye walima da party na taya murna, in da next 1 week" murmushin jindadi mahmud yayi yace "thanks mum, Allah ya biyaku dawainiyan da kukeyi akan mu" dukansu suka amsa da Ameen.
Bayan kammala cin abinci kowa ya nufi part dinshi, jameel ya dauki matarsa suka tafi gidansu da yake basu da nisa da gidan iyayen nashi.
[3:19PM, 7/11/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣3⃣

Fatu bata farka ba sai bayan la'asar, kallon agogo tayi ta saka salati ta shige bathroom. Wanka tayo da alwala ta bada farali kana tasa kaya hade da light make up. Palour ta fito taji shiru tace ba dai har sun kammala ba. Kitchen ta shiga ta samu dija na aikin girkin dare ta tsaya tambayanta hajia dasu jameel, dija tace "ai tun dazu su lubna suka tafi, mahmud kuma inaga ya shiga cikin gari. Fatu tace "mmn isya yanda kika san an mini duka haka nake jin jikina dazu, ina shiga daki kawai na kwanta in huta ashe bacci ya kwashe ni" Dija tace "kinyi kokari ai" fita daga kitchen din tayi dakin hajia, sai da ta knockin tayi sallama aka amsa ta shiga. Hajia ta samu zaune a bakin gado tana waya da aunty sadiya (maman sultan). Kujera na dressin mirrow taja ta zauna Sai da hajia tayi hangin fatu tace "mummy ya gajiyan yau? Hajia tayi mrmshi tace "ai ke za'a cewa ya gajiyan yau, kikayi ta bacci abunki" daria fatu tayi tace "Allah mummy nima bansan tym din da bacci ya debe ni ba, kuma farouq ma ko yazo ya tasheni" mummy tace "ni nace ya barki ki huta. Ki dauki wancan jakan ki kaiwa hajia sadia tsaraban su ne, naki kuma sai kin dawo ki gani" fatu tace "tooo" daukan jakan tayi ta fito, room dinta ta shiga ta dauko hijabi iya gwuiwa tasa ta fito.
A palour ta tarar da qanwarsa Amrah tana danne danne a waya, zata kai 13 yrs, "anty fateema oyoyo" amrah tace da fatu yayinda take zuwa gurinta ta karbi ledan hannunta suka zauna, fatu tace "washhh, Ina mammi" amrah tace "tana dakinta, bari in kirata" bata jima da shiga ba suka fito tare, hajia sadia na cewa "amrah bi kitchen ki daukowa fateema ruwa" zama tayi akan kujera fuskarta dauke da murmushi tace "sannunki da zuwa fateeman mummy" murmushin fatu ma takeyi amma fuskarta a qasa, ta zamo daga kan kujeran ta gaisheta kana ta koma ta zauna. "Mummy ne tace in kawo muku tsarabanku" ta fada yayin da take miqawa hajia ledan. Amrah ta kawo wa fatu ruwa ta tsiyaya mata ta koma kusa da hajia sadia ta zauna tana cewa "mammi ina nawa" hajia sadia tace "gashi nan, kinga na kowa Anyi wrapping dinshi da suna" ta karba tace "anty fateema kice nagode sosai" fatu tace "to amrah" amrah ta wuce dakinta don ganin tsarabanta. Fatu ta miqe tace "mammi sai anjima" hajia sadia tace "daga zuwa? Ko ruwa baki sha ba" fatu tace "mammi na sha" sultan ne ya shigo a dai dai inda hajia sadia ke cewa "ki gaishe min da mummyn naki" sultan yace "muje in raka ki" saurin dago da kanta tayi ganin ita

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment