Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kewar mahaifiyata Muna dawowa gombe na je dukku ganin mahaifiyata amma aka ce ta rasu, kanwata kuma tayi aure, nayi nayi su fada min inda tayi auren amma suka ce sun manta, sultan ina kaunar naga wani tsatso daga mahaifiyata" kwallan daya taru a idonta ne ya saurin zubowa ta share. Tun daga wannan lokacin sultan ya qudura aniyar nemowa mahaifiyarsa 'yar uwarta, yaje sau daya shima suka fada masa haka, zuwansa na biyu shigan dare yayi da wasu soldiers da yayi hayansu, tsoro sosai suka bawa mal jauro wanda ya fadi inda take aure har da sunan mijin nata. Yanzu a dalilin haka ya jawo wa kanshi damuwa.
[11:06PM, 7/20/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣9⃣

Fatu na isa gidan jameel ta shiga gabanta na dukan uku uku, a palour ta tarar da lubna na zaune "kin iso? Tace da ita, sai da ta zauna tukun tace "ehh, Allah yasa lafiya" hoton ta ajiye akan cinyar fatu wanda lokaci qanqane dan walwalar da yake fuskarta ya bace ya koma matsanancin damuwa, ido ta kurawa hoton kamar yau taba kallon irinsa, lubna da ta kafe ta da ido tana nazarinta tace "explain please" hawaye naga yana zarya a kumatun fatu tana girgiza kai tace "its over, d charade" lubna ta matso kusa da ita ta dafa kafadunta tace "its not over yet, yanxu aka fara, trust me" tiryan tiryan fatu ta fara bata labarin har zuwanta gombe da yanda hajia ta taimaketa ta sakata a skul ta maida ita *FATUN BIRNI* ta kuma dauketa tamkar 'yar cikinta da ta haifa. Ajiyar zuciya lubna tayi tace "one last question, do u love sultan" dago idonta tayi da sukayi dan jaa don kuka tace "anty lubna......a life without sultan, even an immortal life would be empty, I wish to stay on earth with him" murmushi mai bayyana 32 lubna tayi tace "kamar yanda na fada miki its not over, to hakan ne" magana suka fara wanda nayi nayi inji amma fateey na ta dameni da kuka, naga dai lubna na zazzago magana yayinda fatu ke ta maida hankali 100% tana ji, can naji tace "he'll love her too" fatu da ta kasa boye farincikinta ta ruqunqume lubna tana daria kamar ance yau za'a kaita gidan sultan. Sai da suka natsa tace "anty lubna tnx alot Allah ya bar mini ke" "Ameen" ta bata amsa tana murmushi. Kiran sallah la'asar yasa suka farga dat its time. Lubna ta shiga bandakinta ta hadawa fatu ruwa a bathtub turarukan wanka naga ta diga a ciki, tayi alwala ta fito, ta bawa fatu towel ta shiga bathroom din yayinda ita kuma ta fara sallah. 15mins ta dauka tana dirja jikinta kamar yau aka haifetaπŸ˜‰ kana tayi alwala ta fito, zani da hijab lubna ta bata tasa tayi sallah, daga nan ta feshe jikinta da body spray ta shafa humra da kulacca duk na lubna, nan da nan dakin ya dau asirtaccen kamshin da komin gulmanka bazaka gane me da me aka hada ba. Wani swiss lace red nd black naga lubna ta dauko ta bawa fatu ta saka, fatu tace "na taho da kayana fa" "ban taba saka shiba, ko DJ bai san da zaman shiba, jst ki saka" ba musu ta karba ta saka, kamar a jikinta aka dinka, figure 8 dinta ya fito tarr, zaunar da ita lubna tayi akan kujera ta fara tsara mata make up, dauri ta kafa mata wanda yasa gashinta ya fito ta tsakiya ya kwanta a bayanta, Qara feshe ta tayi da wani turare mai sanyin kamshi, tace "done! Kallon kanta tayi a mirrow, ita kanta tasan tayi kyau bana wasa ba, kamar wata amaryan da za'aje dinner, qaran phone dinta ya katse kallon qurilla da take yiwa kanta, sultan nagani a screen din, dauka tayi ta kashe murya tace "Hello" sultan da yake kusa da motarsa yayin saurin dafawa don yanda muryan ya kashe masa jijiyoyin jikinsa, "hey" ya fada a sanyaye, ya cigaba "gani zan fito yanzu, kina gida ne in biya mu tafi tare? Sai data ja aji tace "nop, ina gidan yanzu haka" yace "ok gani zuwa" ya kashe wayan. Tsayawa nayi na qare masa kallo yau, dogo ne amma ba can ba, kuma da alama yana motsa jiki, fuskarsa irin na fulani sak, dogon fuska, manyan idanuwa, dogon hanci da bakinsa dan daidai, ga saje daya zagaye fuskar da quarter million suka qara qawata shi, gashin kansa kamar na fulani Aww ashe fulanin ne, black ga santsi a kwance. Fatar jikinsa Brownie ne kuma ba chocolate ba, daka ganshi kasan hutu da kudi sun zauna hade da kwanciyar hankali. Half jumfa ne a jikinsa na dakakkiyar shadda mai launin blue, takalmin shi da agogon shi black, ya hadu ne iya haduwa Dan Fulanin. Motarsa ya shige sai gidan ja[truncated by WhatsApp]
[8:50pm, 8/5/2016] Dara: [10:51AM, 7/31/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣4⃣

Fatu ta juyo da kallonta gurin sultan tace "matarka? Pls kace wasa ne" bai dago ya kalleta ba zuciyarsa na tafarfasa, ya dafe kanshi yayi shiru, lubna ta miqe tayi daki dama jameel yana gurin aiki. "alama ya nuna gaskia ne kenan, ya Allah" juyi tayi ta cigaba "ashe yaudarata kakeyi? Na dauka kai mutumin kirki ne ashe ba haka ba ne, why me sultan? Jin muryanta kaman tana kuka yasa ya dago da kanshi, hawaye ne ke sintiri a fuskarta, ji yyi bazai iya ganin su suna zuba ba, kamo hannunta yyi ya zaunar da ita a 2sitter shima ya zauna, still hannun su na cikin na juna, yace "aure aka min amma bada son raina ba, ke kanki kinsan ke kadai nake so, ki fahimceni" juya masa baya tayi tana share hawaye tace "na fahimta amma ka sani ni bazan zauna da kishiya ba, kaje ka zauna da matarka, Allah ya baku zaman lafiya" cikin kidimewa ya juyo da fuskarta yace "what? Yanzu fateema zaki iya rabuwa dani? Wallahi bana sonta ko kadan kuma nakusa zuwa in bata takardar ta, nima bazan iya zama da villager irinta ba" wasu zafafan hawayene suka sauqo wa fatu yayinda wani baqin ciki ya turnuqe ta, wato itace villagern!!! daukan hoton tayi ta yayyaga kuci kuci, ta zubar a palourn tace "maza duk halinku daya, jiki da kwalliyan mace kuke bi, baku damu da kamala ba, karka qara taka inda nake" ficewa tayi a gidan ta barshi zaune a gun yana jin radadin maganarta. Shi a iya saninshi mace bata taba hararansa balle ta gaya masa magana. Me take nufi da kalamanta? Tattara pieces na pic din yyi yasa a small dustbin din da yake falon, shima ya fita daga gidan.
Fatu kuma tana fita ta tari keke napep ya kaita gida, tana shigowa palour Allah yaso ba kowa ta haura upstairs zuwa dakin ta, zaman yan bori tayi a tsakiyar room din tacigaba da kukanta. Meyasa mazan ynzu basu damu da addinin mace da kamun kanta ba? Sunfi son wayayya yar boko wacce ta dace ta zauna a gaban mota kuma ta nunawa duniya? Meyasa taimako da tausayi yayi qaranci wanda har ana raba zumunci don son zuciya da kyale kyalen duniya? Tayi alqawari muddin ya saki fatu to bashi ba ita har abada, kallon kanta tayi a mirrow, me ya qaru a jikinta kuma me ya ragu? Gayu da gogewan da tayi yake so ba ba ita ba. "Villager" ta furta ta qara rushewa da kuka, ita tayi setting din draman amma ya dawo mata real life, a tunaninta zai so matarsa fatu ita kuma ta fada masa gaskian wacece ita! But sai hakan bai faru ba, miqewa tayi kaman wanda aka tsikara tace "yanzu inya sakeni ya zanyi? Ni fatu ya zanyi" zuciyar ta taji na mata quna, hakan yasa ta kwanciya akan gado tana aukin zubar da hawaye har bacci yayi gaba da ita.

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[10:54AM, 7/31/2016] Mum Fateey: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣5⃣

Sultan gidansu ya nufa kai tsaye yayi hanyar garden a can ya zauna. Maganar gaskia yana son fateema amma wani gefe guda kuma yana jin bazai iya sakin fatu ba, don da zai iya da tuntuni ya aikata hakan tun bayan aurensu da 1month, a lokacin ya fara mata aika mata kudi, yaso ya rubuta amma zuciyarsa ta haneshi da aikata hakan, a baki kawai yake fada amma shi kanshi yasan ko yaya zaiyi bazai iya ba. "Shes quit nd innocent" daukan wayarsa yayi ya turawa fateema text....

_ban yaudareki ba kuma bana fatan hakan ya taba faruwa, duk da bana sonta 'yar uwata ce kuma marainiya, I dunno what to do, bana jin zan iya sakinta, amma please ki daina batun rabuwa dani, I cnt take it fateema_

Tsawon minti goma da turawa ba'a masa reply ba, hakan yasa yace "bata huce ba har yanzu, ya kamata na bata lokaci"
Fatu na tashi daga bacci kusan bayan la'asar tayi wanka da sallah, yanzu kam ta daina jin qunar da zuciyarta yake mata, wayoyinta ta dauko ta fito palour, ba kowa kamar mummy ta fita unguwa farouq kuma yana islamiyya, a kitchen ta tarar da dija na yankan kayan miya suka gaisa dija tace "ya na ganki kamar bakida lafiya? Fatu tace "kaina ke ciwo, ina mummy? Tace "tana gidan hajia sadia, a zubo miki abinci ne? Fatu tace "a'a kiyi aikinki zan zuba" daukan plate tayi ta zuba tuwon shinkafa ne miyar ugwu yasha kifi da nama sai kamshi yakeyi, spoon ta dauka ta fito daga kitchen din, a dinning ta zauna tafara cin abicinta, wayarta ta dauka sai a sannan taga text din sultan, fuskarta ba yabo ba fallasa ta ajiye, tana gama cin abinci takai kitchen ta dawo falo ta kunna data wayarta, mssgs na sultan ta gani duk na ban hakuri, ta karancesu tsaf ta kashe data ta kunna kallo amma hankalinta baya kai sai tunani, a haka mummy ta shigo tayi sallama bata jita ba, sai da ta taba ta sannan ta juyo a dan tsorice, ganin mummy ne ya sata fara'a tace "sannu da dawowa mummy" Mummy ta kalle ta fuskarta da damuwa, zama tayi tace "fateema lafiyanki kuwa? Idan akwai abunda ke damunki ki fada min, karki boyemin komai I'm ur mum" kanta ta kwantar akan kafadan mummy yayinda hawaye masu dumi suka biyo fuskarta tace "mummy nayi missing din gida ne, tunda nazo banje ba haka kuma banji daga garesu ba" shafa kanta mummy tayi tace "karki damu, in kin kusa komawa skul zakije musu, saboda akwai abunda nake so in aiwatar kafin kije"

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣7⃣

Basu sha wahalan gane gidan ba duk da dan sauyin da aka samu kusan shekara da rabi, yau ma a kofar gida suka samu mal Ameenu yana zaune da wani mutum suna magana. Tun dosowar motar mal Ameenu yake kallonta duk da bashi sultan ya taba zuwa da ita ba amma yana kyautata zaton yau fatu tazo da mijinta. Nesa dasu kadan suka parking yayinda suka fito kowa da dan murmushi a fuskarsa, ganinsu yasa mal Ameenu fadada fara'arsa kaman an mishi bushara, yana leqen bayansu yaga ta inda zaiga *FATUN BIRNI* Kawu muntari da yake gefen mal Aminu yace "baba, ko dai maigidan fatu ne yazo? Gyada masa kai yayi saboda sun iso, sallama sukayi aka amsa musu suka sami guri akan babban tabarman suka zauna, kaka yace "muntari shiga gida ka samo musu ruwa" kawu muntari ya tashi da sauri ya shiga gida. Gaggaisawa sukayi cikin mutunci kaka bakinshi yaqi rufuwa sai hamdala yakeyi yace "ai na aza da ita zaku zo, ashe ku kadai ne" Jameel yace "na'am baba" don bai fahimci maganar ba sultan ma haka. Kaka ya cigaba da cewa "bbu abunda zance maka sultanu sai Allah ya maka albarka, yasa ka gama da duniya lafiya, wato naji dadin wasiqarka, shekara da auranku baka zo ba, nayi tsammanin ko baka son hadin da aka maka ne, har na fara maganan raba auren ganin yanda aka fara surutu a kauyen nan, mutane sunyi gaskia da suka ce 'mai hakuri shi kan dafa dutse har yasha romonsa' nan din ma hakan ya faru, ranar da kayi aika ta hadu da mal usman a hanya ya bata saqon kamar kullum" kallonsu kaka yayi da fara'ar da har ynzu bata bar fuskarsa ba, daga jameel har sultan sun zuba mishi ido, ya cigaba "wasiqan da na gani a ciki yasa na dauka ko ka sauwaqe mata ne, data karanta muka gane" daria kaka yayi amma babu wanda ya tayashi don gabadaya kansu ya daure, sun rasa inda maganarshi ya dosa, fitowan muntari yasa jameel cewa "me ya rubuta" muntari yace "rubutawa sultanun yayi cewa fatu ta bishi gombe zai yiwa mamarsa bazata, ko ba haka kace min ba baba? Kaka ya amshe "ehh" muntari yace "ai naso inje aga gurin da kuke din saboda ziyara, amma fatun tace ita kadai kace taje" tari ne ya sarqe sultan yanayi ba kakkautawa ruwa aka miqa mishi yasha sannan ya tsaya idonshi har yayi jaa, Jameel ne yayi qarfin halin qaqaro murmushi yace "haka fa, abun zai kai wata nawa ma? Daga kanshi yayi kamar mai son tunowa muntari yayi caraf yace "wata takwas ai ko" kiran sallah azahar da aka fara yasa sukayi shiru kowa da abunda yake saqawa a ransa, sai da aka idar mal Ameenu yace bari a kawo muku buta kuyi alwala, shiga gidan kaka yayi da kawu muntari aka barsu su kadai, a sannan ne sultan ya dubi jameel da tsananin damuwa a fuskarsa don a yanzu sun gane komai daya faru yace "ina cikin duhu jameel" girgiza kai jameel yayi yace "ita ta rubuta wasiqa kace taje, tun wata takwas da suka wuce kuma da alama har yau bata dawo ba, sultan, fatu ta bata" shiru sukayi sultan ji yakeyi kamar ya kurma ihu ko zaiji sassauci a zuciyarsa, _FATU TA BATA! IDAN MAL AMEENU YA GANE BATA TARE DASHI YA ZAIYI? IDAN MAHAIFIYARSHI TAJI ABUNDA YA AIKATA HAR HAKAN YA JANYO BACEWAR YAR QANWARTA YA ZAIYI? SHIN FATU TANA RAYE? IDAN TANA RAYE TA INA ZAI FARA NEMANTA? TA INA?_ Tambayoyin da suka cika brain din sultan wanda babu wanda zai iya amsa mishi, ji yayi zuciyarshi na zafi yana ganin duhu duhu, hakan yayi daidai da fitowan kaka da muntari suka ajiye buta miqewan da sultan zaiyi yaji kanshi yayi nauyi ya zube a qasa.

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣6⃣

Yau saturday ya kama ranar da sultan zaije garin modibbo, da kyar da lallami yasa jameel ya shirya ya rakashi, wayarsa ya dauka ya turawa fatu text,

_yau zan tafi garin modibbo, pray for me_

Sai daya tura kuma yaji haushin kansa, yau kusan kwana uku bata daukan wayarshi bata amsa text dinshi, ko yazo ya aika ta fito bata zuwa, rabon daya ganta tun ranar da lubna ta kopsa masa, amma hala kawai ko abinci zaici sai ya mata text, zuwa unguwa da sauransu, amma bata kula shi. Shiga mota yayi ya zauna yana jiran jameel ya fito daga gidansa. Fitowa jameel yyi tare da lubna sai wani mannewa juna sukeyi suna I miss u, I miss u, haushi ne ya cika sultan ya danna horn da karfi wanda yasa suka dawo cikin hayyacinsu, tsaki jameel yaja yace "mallam zaka kashe min kunnen yaro" ko kulashi baiyiba, yanashiga yaja motar suka fara tafiya. Tittitititi alamar shigowan saqo da sauri sultan yaja birki wanda yasa jameel tsorita shi ya aza ma sun buge wani ne, da sauri Ya dauki wayan ya duba saqone daga fatu

_ka gaisheta_

Shine abunda ya gani, wato duk mssgs dinshi tana gani wannan ne kawai taji zata amsa? Jameel wanda har yanzu zuciyarsa bai daina bugu ba yace "amma kai dan iska ne sultan, wannan wani irin ganganci ne zaka tsayar da mota cikin sauri haka? Kuma akan wata kake qoqarin kashe mu duka? Da mamakin shi sultan murmushi yake yi yace "srry dude, na love" jameel bai iya qara cewa komai ba don tsananin mamaki, shi ko ada da yake cewa in soyayya ya kama sultan zaisha wahala to bai taba zaton abun zai kai haka ba. "This is madness" sultan ya kunna motar yace "indeed". A haka suka kama hanyan kumo, jefi jefi sultan na bude saqon yana dubawa, da jameel yaga abun yayi yawa yasa ya karbi driving din, sultan yayi ta gwada calling fatu ko zata dauka amma taqi dauka, daya gaji ya hakura. Fatu kuma yau levels ta kawo mata ziyara, a daki na gansu suna zaune akan gado, fatu tayi wani _silent_ kamar marainiya xahra na bata baki "bai kamata kisa damuwa a ranki, duk da nasan its hardly ace baki damun ba amma gaskia ki sassautawa zuciyanki, addu'a zaki cigaba dayi, ki barwa Allah komai, kinji kam? Fatu da alama bata jin abunda xahra k fadi don wayarta take dannawa a hankali, kwace wayar xahra tayi pics din sultan take kallo, ido xahra ta bita dashi yayinda fatu ta gyara kwanciyarta ta bawa xahra baya, "ehh lallai babyn nan wato ni na zauna ina baki shawara kin maida ni bi ta can ko? Kinata kallon mijinki" tashi xahra tayi ta dauko laptop din fatu da sultan ya saya mata wai na karatu tace "me ma pasaword din? Sarai tasani amma ta tambaya _"SULTAN"_ fatu ta bata amsa, daria xahra tayi tace "soyayya ko wahala" ta cigaba da danne dannen ta har ta samu film din da take so ta fara kallo. Fatu kuma tunani ne fall a ranta na abunda zai faru in sultan ya isa ya tarar fatu ta fita nemansa months back!!!

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣9⃣

Ba fatu kadai ba har lubna da xahra mamakine a fuskarsu, tsintan pieces na pic din sultan ya fara yana ajiyewa a gefe, jameel ne ya shigo ya tsaya a kanshi yayinda su fatu ma suka matso suna ganin ikon Allah. Sai daya gama tarawa ya kwashe, yazo zai wuce ta kusa da fatu, tsayawa yayi yana kallonta itama ta tsura masa ido, har ta fara tausaya masa ganin a yini daya har ya fara susucewa, kawar da kanta tayi shima ya wuce bai ce mata komai ba, zama yayi a kujera ya jawo centre table ya baza pieces din ya fara jerawa, jameel ne ya zauna kusa dashi ya dafa kafadarshi yace "sultan" bai kalleshi ba yaci gaba da jerawa amma ko kadan basu jeru ba don kuci kuci suke, gumin da yake hadawa ya diga akan wani piece yayi saurin gogewa hakan yasa abunda yayi qoqarin hadawa kusan minti 10 ya wargaje, watsa nakan table din yayi a qasa ya dafe kanshi, ya kwantar da kanshi akan kujera, jameel da yake gefenshi yace "kayi addu'a sultan" addu'o'I ya fara idonshi a rufe yana dafe da kanshi. Jameel ne ya fara basu labarin abunda ya faru tun zuwansu, yana qarisawa sultan ya tashi zai fita, jameel ya tareshi yace "ina zaka je? Ka huta tukun" girgiza kanshi yayi yace "zanje gida ne, ka kai hoton gidan tv a fara cikiyanta don Allah, da gidan radio please" yana gama maganarshi ya fice, jameel yabi bayanshi. Lubna ta juyo da dubanta gurin fatu wacce take danna wayarta alamar bata da matsala tace "fateey ya kamata ki fada mishi kece, kiga fa yanda yake qoqarin zaucewa" tsayawa tayi da danne dannen tace "dadina daya da basu bayyana wa kakana ba" xahra tace "u have to talk to him" tashi tayi ta tsaya tace "a'a ba yanzu ba" murmushi tayi tacigaba "na zauna tsawon shekara daya cikin zullumin inda mijina yake, nayi kuka, nayi addu'a, duk inda nabi mutane magana sukeyi anacewa ga bazar bazar, wato mace mai aure amma ba miji, kaka ya hana ni fita, haka na zama tamkar mujiya, cikin gidan ma ba'a barni ba, goggo asabe cikin gaya min baqaqen maganganu take" juyo da dubanta tayi kan su xahra tacigaba "duk akan waye na sha wannan bakin ciki? Akan sultan, dalilin cewa ni baqauyiya ce, wacce bata waye ba, ban dace dashi ba" lubna tayi ajiyar xuciya tace "bawai na raina halin dakika shiga bane, a'a kinaji yanda DJ ya fadi abunda ya faru, har suma fa yayi" murmushi fatu tayi tace "babu abunda zai sameshi, xahra mu tafi" sallama sukayi wa lubna suka wuce gida, ita lubna har ta fara tausayawa sultan, fatun ma ta tausaya mishi amma tayi alqawarin saiya horu tukun, tana son nuna mushi dan adam ba abun wulakantawa bane, kuma cewa "kare ma yanada rana, balle mutum dan adam mai tunani da hankali"

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:50pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣8⃣

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" abunda kowannensu yake furtawa kenan sukayo kanshi, jameel ne ya shiga jijjiga shi yana "sultan, sultan ka tashi" yama manta cewa shi doctor ne, ruwan buta yasa aka miqo masa ya yayyafa masa, ajiyar zuciya mai qarfi ya sauqe kafin ya bude idonshi a hankali yace "ina fatu? Ganin zai qara magana yasa jameel saurin cewa "mu daga shi mu kaishi mota, dole sai an kaishi asibiti" mal Ameenu da yake da salallamai a gefe yace "muntari tayashi ku dauke shi, maza maza" hannayensa suka saka a kafadunsu suka kaishi mota kaka na "ashsha Allah ya bashi lafiya" yana girgiza kai. Suna sakashi a mota yana cewa "ina fatu? Ina fatu? Jameel yayi saurin shiga driver sit ya kunna motar, yana tunanin yanda zasu fara nemo fatu, tunawa da yayi cewa fateema ta yaga pic din fatu da suke dashi yasa yayi saurin fitowa daga motar ya samu kaka fuskar shi gwanin tausayi muntari na cewa "baba, sai cewa yakeyi ina fatu fa" alamar akwai matsala kenan, kaka na ganin jameel bai ko saurari muntari ba yace "jikin ne? Ko dai a qira madam nasi (nurse daya da suke dashi a qauyen) ta dubashi? Jameel yace "a'a nima doctor ne, fatu yake son gani, in akwai hotonta a bani" kaka cikin jimami yace "kayya wannan wani irin cuta ce? Fatu bata daukan hoto sai hoton ta daya da aka dauketa tana shekaru uku" da azama jameel yace "a bamu" kaka yayi saurin shiga gida muntari ya mara masa baya, shi kuma jameel ya koma gurin sultan a mota. Yana isa ya samu sultan ya fara dawowa hayyacinsa yace "yarinyar nan tana son kashe ni, tana jawomin matsala a rayuwata ta koyaushe, ina take? Bubbuga bayanshi jameel yakeyi yana cewa "be strong, be strong dude, zamu nemota insha Allah, I'm with u" jameel kaman ya fadawa kaka batan fatu amma yana hango tsananin tashin hankalin da zasu shiga in suka ji labari shiyasa ya shirya qaryan cewa sultan nason ganin hoton ta ne, fitowa kaka yayi muntari na binshi a baya kamar jela, da sauri jameel ya isa gurinsu ya karbi hoton tare da cewa "mungode, amma dole sai mun dangana da asibiti" muntari yace "to wani irin cuta ce wannan da zaisa mutum suma ya tashi da son kallon matarsa? Kaka ne ya harare shi kana ya maida kallonshi kan jameel yace "ai ya kamata ku hanzarta tafiya kafin wata matsala ta kunno" sallama sukayi jameel ya koma mota, ya samu sultan ya dafe kanshi yace "ka rage tunani sultan don kar ka jawowa kanka matsala, zamu nemota duk inda take" motar yaja suka tafi suka bar kaka cikin daurewan kai, meke faruwa ne?

Fatu na kwance kamar wacce aka tsikara ta tashi tace "xahra akwai matsala" xahra tasa pause ta juyo tace "a ina? "Yanzu idan suka je suka fadawa kaka bana tare dasu wallahi hankalinshi zai mugun tashi dama gashi da hawan jini, yanzu ya zanyi? Ido xahra ta qura mata tana tuna maganar fatu da take cewa rayuwarta kamar a film, wannan shine asalin film. Kafin xahra ta bude baki fatu ta

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment