Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa garin don wanda ya hada ya raba, (kuji rashin tunani da imani) in kuma tazo ta nemi inda zata sauka badai gidansa ba. Mamata tayi kuka kamar ranta zai fita haka babana ya jata suka tafi. Anan yake tambayanta yan'uwan mahaifiyarta. Tace fulani masu yawo ne, sunzo dukku babanta mallam sirajo ya ga mahaifiyar ta wacce ta taba aure a cikin yan'uwansu amma zaman baiyi dadi ba, 'yarsu daya suka rabu da mijin, aka daura musu aure, bayan wata 2 sauran kuma suka kara gaba. Daga nan basu kara yowa ta dukku ba. Sun dawo gida ta samu muntari yayi amarya. Shekararsu 9 Allah bai basu haihuwa ba, inda amarya asabe ta haifi 'yaya 4, goggo innani ta hada kai da asaben muntari suna kuntata wa mamata kakata na tsawatar musu. Ana haka har ta samu cikina sunyi murna sosai amma cikin yazo da laulayi ta wahala sosai inda tana haihuwata tace ga garinku. Babana yayi kukan rashin matarsa mai hakuri da juriya ga sanin dattako. Ran suna naci sunan kakata (mamar babana) wato Fatima inda ake ce mini fatu. Na taso cikin kulawan mutum uku, kakannina da babana. Don yanzu kawu muntari ya fara bin hudubar su goggo innani wai an fi sona akan yayansu. Na yi primary anan kauyen mu. Inda duk garinmu bbu wanda ya kaini kokari, sannan na shiga secondry ina jss 2 babana ya hadu da accident akan hanyarshi ta zuwa kasuwanci. Bamu da labari sai gawarsa da aka kawo. Fadin irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne. Nayi kuka har na rasa inda zan tsoma raina. Anan nake tunanin kodai gaskiansu goggo asabe cewa dangin mu akwai mayu masu cinye duk wanda suka rabe su. Kakata kuma tun daga lokacin ta fara kananun rashin lafiya. Na cigaba da karatuna inda kakana ya jajirce sai na gama secondry skul, duk sa'annina sunyi aure daga mai 'ya'ya biu sai mai uku. Na kuma faranta masa nayi candy daga nan kuma samari suka min caaa! Don duk wanda yazo gurina kakana kance mishi sai na gama karatu. A cikinsu kuwa harda dan kawu muntari da dan goggo innani. Ni kuma wallahi duk cikinsu bbu wanda nake so.
Rannan ina bacci da dare naji ana shafani, bude idon da zanyi naga babangida dan kawu muntari ne. Zan yi ihu ya toshe bakina, na takarkare na dankara mushi cizo sannan nayi ihu. Mutanen gida suka fito ana haskawa. Fitowa nayi da gudu cikin gida ina haki, kaka yace "mene fatu me ya sameki? Nace "babangida ne ya shiga dakina kuma yana tabani" na fada ina matsar kwalla wanda har lokacin jikina bai daina rawa ba. Inna asabe ta cabe "munafuka, sharri zaki yiwa yayan naki? Me zaiyi da ke jiki kamar na aljanu" kaka ya dakatar da ita yace "ina babangidan? Ya ce gani nan, "kaji abunda fatu tace? Yace "wallahi karya take min, na fito zaga bayan gida ne naji kamar nishin mutum a daki, nayi zaton batada lafiya ne da na haskata sai naga mafarki takeyi tana wannan nishin. Shine na bugi hannunta tana tashi tasa ihu. Salallamai goggo asabe tasa wai nayiwa danta sharri. Shi kuma ya fita zaure inda dakinsu yake yana mita wai dama ba'a sonsu a gidan. Ni kuma sai rantse rantse nake, kakanina da kawu muntari sun yarda don zai aikata. Kakatace ta jawoni dakinta na karasa kwana anan. Daga ranan na dawo dakinta kwana. Sati da faruwar lamarin kakata ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzabi ga jiri da yake dibanta, anyi magani na gida har asibiti aka je inda suka ce [truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣8⃣

Sallama sukayi ya amsa, kana ya dubi yaran da sukayi dandazo suna kallon samarin yace su tafi wasan su, kan kace me kowa ya watse don basu da rashin kunya. daya daga cikin samarin yace
"Don Allah baba nan ne gidan mallam mahmudu? Duk'ar da kai kaka yayi sannan yace "ehh" still wanda yayi tambaya na farkon yace "gurinshi muka zo shi da matarshi, daga gombe muke" kaka yayi dan jimm sannan yace "Allah ya musu rasuwa dukansu" "sun rasu" saurayi na biyu ya fada cikin firgici, sannan ya nemi guri ya tsuguna yana "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya jikanku".
Saurayi na farkon ya dubi kaka da tarin damuwa a fuskarsa yace "Allah ya jikansu yasa sun huta" "Amin Amin" kaka ya furta yana goge hawayen da ya zubo mishi ba shiri. Saurayi na tsugunne yace "jameel mu tafi" ya miqe jikinshi a sanyaye ya nufi mota. Kaka ne yace "zaku tafi baku sanar dani alakar ku ba" jameel yace "wancan abokina nane, sunanshi sultan, matar mallam mamudu wato aunty rahmatu qanwar mamanshi ce, uwarsu daya. "Allahu Akbar Alhamdulillah" kaka ya fada cikin tsananin mamaki don baiyi tsammanin za'a ga dangin mahaifiyar rahmatu ba cikin ruwan sanyi haka. "ai akwai rabo tsakaninsu sun sami 'ya mace fatu, tana nan, ni mahaifin mahmudu ne" farinciki ne kwance a fuskar kaka yana murmushi. Jameel ne ya kwalawa sultan kira ya fito daga mota still jikinshi a sanyaye, jameel yace "akwai cousin dinka fatu, 'yar aunty rahmatun ce" cikin doki yace "ina take? Yana kallon zauren gidan. Kaka yace "tana ciki, amma in bazaku damu ba ina son magana daku.
Tabarma kaka ya shimfida musu a zaure suka zauna, shiga gida yayi ya sameni tsakar gida ina karanta wani littafi, yace "uwargida ki samin ruwa a kofi nayi baki" nace "to". Miqa mishi kofin nayi ya karba ya wuce cikin zauren. Bayan sun qara gaisawa ne kaka ya fara basu labarin mamata har zuwa kaina, bai rage komai ba harda wahalan da nake sha gurin asabe idan taga kaka baya nan. Kaka ya qarasa magananshi da cewa "idan baza ka damu ba kai sultanu ka auri qanwarka zata fi jin dadi cikin ku, nasan dana fadi na mutu fatu bata da gata sai Allah, don wadannan ba riqeta da gaskia zasuyi ba" kaka ya cigaba da maganarsa duk akan sultan ya aureni ya taimaka min. Kan sultan ne yadau zafi yayi dana sanin nemo su, gaskia bazata sabu ba. Shiru yayi kansa a qasa ko motsi mai kyau bayayi, ya bude baki zaiyi magana kenan Jameel yayi caraf yace "hakan yayi kyau, Allah ya tabbatar da alheri" Amin. Kallon mamaki sultan yake bin jameel dashi don ya wargaza mishi plan, wata dabara ce tazo mishi in akayi sa'a zai fita.
Yace "mallam zamu koma gida sai daga baya inshaAllah magabata su zo. Kaka yace "mutum bai san ranar mutuwanshi ba, watakila bazan kai zuwa gobe ba har zuwa lokacin da zaka turo magabatanka, kamar yadda na fada maka nine ke riqe da fatu, ayau nabar dunia zasu iya aura mata wanda ransu yake so, inda zata cigaba da shan wahala. Nafi aminta dakai shiyasa nake so ayau a daura muku aure, "Shikenan" abunda sultan ya iya fadi kenan don tsohon ya cika kwarjini bazai iya mishi musu ba.

An daura aurena da sultan a masallaci bayan an idar da sallah. Inda kaka ya zame min waliyyi liman kuma waliyyin sultan. (Tarihi ya maimaita kansa). Gida suka dawo inda kaka yace ya tafi dani, amma sultan yace zai tafi wani course na wata biyu inya dawo zaizo ya daukeni, kaka bai kawo komai ransa ba ya yarda. Shiga cikin gida yayi ya barsu a zaure inda ya aika in kai musu abinci don ranar ni nayi girki. Har lokacin banida labari don kawu muntari yayi tafiya, asabe kuma taje ganin gida. 'yayansu kuma ba zuwa masallaci suke ba. Na fita na kai musu, durkusawa har kasa nayi na gaishesu mutum daya ne ya amsa yana min murmushi, amma dayan ko dago kai baiyi ba. Mai murmushin yace "me sunanki" nace "fatu" yace "masha Allah abokina yayi sa'ar mata" fita nayi ina mamakin maganarsa, to a ina hafizu ya sami abokai yan birni haka.
Shiga na keda wuya kaka ya kirani dakinsa, da farko nasiha ya fara min kan ya bani labarin abunda ya faru. Babu abinda na iyacewa illah hawaye da ya dinga bin fuskata, na rasa hawayen menene, ta wani gurin ina farincikin samun dangin mamata, while ta wani gurin ina tausayawa kaina don wanda aka aura min ko kallona bai yi ba. Na dade a dakin kaka sanna ya fita dubo bakinshi ko sun gama cin abinci. Ya fita ya samu jameel yaci amma sultan ko ruwa bai sha ba, jameel ne yake cewa wai sultan din azumi yakeyi.
Kaka ya musu iso cikin gida aka shimfida musu tabarma ta bayan dakunan mu gurin akwai bishiiya gefenta kuma rumbun ajiye abinci ne. Kaka ya wuce yana cewa bari ya kira fatun. Gefen su kadan na zauna akan wani dutse na sunkuyar dakai ina wasa da yatsuna. Mijin nawa dai har yanzu kansa na kasa bazaka game yanayin da yake ciki ba. Ja[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣9⃣

Jameel ne ya fara magana "Amaryanmu kina lafiya" nace "lafiya kalau" ya kara cewa "sai kika ji an daura aure babu wani taro babu al'adu irinsu zance, bayarwa, kayan aure da sauransu. "Uhmm" na iya cewa. "Komai da kika gani muqaddari ne daga Allah, wannan aure naku insha Allah baza kuyi dana sani ba. Ya cigaba da maganan shi inda yake nuna mana mu riqe junan mu cikin amana duk da ba auren soyayya bane, ya karasa magananshi cikin nasiha. Duk abunda yake cewa sultan bai ce uffan ba, don wayarsa ya dauka yana dannawa. Mikewa yayi sannan yace "bari in barku kuyi magana, kar in takuraku da yawa" ya fada cikin tsokana. Mun fi minti biyar b wanda yayi magana can yace "kinyi makaranta? Nace "ehh" "ina kika tsaya" "secondry" yace "shekarunki nawa? Nace "17" sai lokacin ya dago kai ya kalleni 4 d first time nayi saurin sunkuyar da kaina. Can ya kara cewa "kin taba shiga birni" nace "Aa'aa" yace cikin bata rai "kin min yarinta da yawa, kuma karatunki baiyi zurfi ba, bana jin zan iya rayuwa da irinki" dai dai nan jameel ya dawo yace "times up, kar muyi yamma a hanya" hope kun daidata? Ya fada yana murmushi. Babu wanda ya kula shi don ni ina kokarin mayar da hawayen da yake son zubo min ne, jameel ne yace in matso kusa da sultan zai daukemu hoto. Shiru nayi sai da ya kara maimaitawa na taso na tsaya nesa dashi, turo sultan yayi gurina wanda yake aika masa harara ta ko'ina, baya yayi yace mu dago fuskokin mu, still kowa kansa na qasa, yace to bari in kira kaka, may be zaku fi jin magiyarsa. Saurin dago da kanmu mukayi yace "smile" sannan ya daukemu a hoto. Abun mamaki yana daukan hoton wani abu ya fito daga cikin camera, ya kara daukan mu abun ya qara fitowa. Miqa min na farkon yayi na karba ban duba ba. Sultan har ya fita waje, ciro kati yayi daga aljihunshi ya bani, yace "wannan shine address na gidansu sultan, abokina yana da wuyar sha'ani amma in kika yi hakuri komai zaiyi karshe, ki ajiye address din don bamusan gaba me zata haifar ba" ya karashe maganarsa cikin tausayawa. Nace "Nagode Allah ya kiyaye hanya" shima fitan yayi inda ya iske kaka da sultan suna hira kamar bashi ne yake bata rai dazu ba. Tafiya sukayi kaka ya shigo cikin gida yana mai farincikin fatu tayi sa'ar miji. Ni kuma tun tafiyan jameel na nade tabarman na shige dakina ina kuka mai tsuma zuciya, daa kaka yasan wa ya aura min da bazaiyi farin ciki ba. Kiran da kaka yake min yasa nayi saurin goge fuskata na fita ina murmushi yace in sameshi a dakinsa. A dakinsa na samu guri na zauna ya miqo min kudi yace "sadakin ki ne dubu ashirin" nace ya dauka ni bana so, yace ai hakkina ne maza in karba. Na karba na wuce dakina na cigaba da kukana har bacci ya daukeni. Bugun kafa na naji anayi na tashi ya firgice goggo asabe na gani tsaye a kaina fuskar nan a tamke, tace "wani jita-jita nake ji a gari wai an daura miki aure hka ne? Nace "ehh" nan ta fara masifa ai dama dangin mu haka suke sai sunga mai kudi suke aura, ga babangida yana sona amma kaka ya hana shi. Allah yasa mijin nawa ma dan yankan kai ne, kallonta nayi ido cikin ido nace "ba kudin shi muka bi ba, sultan dan'uwana ne, mahaifiyarsa addar mamata ce" cikin mamaki tace 'eeeyeee' nace "kwarai" fita tayi daga dakin tana jin bakin cikin auren, don yadda aka fada musu mijin nawa dan birni ne kuma ga kudi akace da mota irin ta sarkin Kumo yazo. Sadakina na boye don nasan ko ita ki 'yayanta wani zai biyo dare. An koma baya don goggo asabe tana ganin kaka ya fita zata fara cin zalina, girki kuma da shara wanke wanke nice keyi da kaka yayi maganan a rage min koda daya ne cewa tayi horar dani takeyi, gidan wani zanje don haka ya kamata in saba da aiki, kaka kuwa ya yarda da magananta. Bayan wata da daurin aure na wani mutum yazo da envelope ya bani yace aikoshi akayi daga gombe. Na aza wasika ce amma sai naga kudi ne 30k. Kakana na kaiwa yayi godia yana cewa sultan bai mance dani ba tunda har yana kokarin sauke wasu hakkina. Bayan wata daya muna tsammaninshi sai muka ga dan aikan rannan. Yace sultan yace a fada mana zai qara yin wata uku. Kowanne karshen wata sai dan aiken yazo da envelope kudine a ciki wataran 50k watarana 30k. Koyaushe aka kawo zanyi tsammanin akwai wasiqar sultan a ciki amma babu. Har wata 3 ya wuce babu labarinsa daga nan su goggo asabe suka fara habaici "ai nasan za'a rina, hala kakaba mishi ita akayi, yoo dama me zaiyi da kucakar yarinyar nan; shi dan birni. A haka zakiyi ta zama har ki tsufe, dama kudi kuke so to ai gashi ana turo muku" idan ta fara maganganun nan nakan shiga daki inyi ta kuka ina kallon hoton[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣1⃣
Dawowa na gida na iske kaka na yana masallaci, don haka kai tsaye dakina na fada na ajiye kayan na fito nayi alwala nayi sallah. Ina idar wa naji kakana ya dawo, goggo asabe ta kirani in kai mishi abinci, naje na karba, har zan juya ta kirani na jiyo, "amm fatu yau ba'a kawo miki saqo bane, wallahi rance nake so ki bani na dubu uku, masifaffiyar goggon kin nan innani na ara a gurinta, don tsiya jiya har da aiko sadiqa tayi tamin rashin mutunci" nan ta fara matsar kwalla, kar ki manta hajia duk randa aka aiko kudi rabashi akeyi duk abunda aka bani ita ke amshe wa da wayo, wani tace zata biya bashi wani kuma tace zata karbo min maganin bakin mutane, Wani kashin na abincin gida, don wani abincin da muke ci ba'a cinsa a gidan maigari, kinga kamar taliya da dan waken fulawa, wallahi wataran harda macaro muke ci (inji jawaheerπŸ˜‚πŸ˜‚). Hajia tace "Macaroni kike nufi? Fatu tace "ehh, sauran a ajiye saboda bukatun yau da kullum. Nace "an kawo in kaka ya bani zan kawo miki" na fita a zuciyana ina cewa anji kanku. Dakina na fara bi na dauko envelope din na wuce dakin kaka. A daki na iske shi yana kishingide, na masa sallama ya amsa, ajiye abincin na miqa mishi saqon nace a hanya na hadu dashi ya bani. Ya karba jikinshi a sanyaye yace zai kirani anjima. Ina fita naga goggo asabe a kofar dakinta tana jirana, sai da na isa tace ina kudin? Nace " sai yaci abinci sannan zai bani. Shiga dakinta tayi bata kulani ba ni kuma nayi shigewata daki ina jiran kiran kaka don karanta wasiqa. Bayan Minti sha biyar lamido dan goggo asabe ya zo ya kirani hijabi nasa na fita. Shiga nayi na samu guri na zauna nace "kaka gani" yace "takarda na gani a cikin kudin Allah yasa ba abunda nake zato bane, ya fada yana mai girgixa kai cikin damuwa. Nace "ba komai kaka Allah ya zaba mana mafi alkairi. Yace "ameen" hade da mikomin paper. "Hajia kinsan abunda na rubuta? Hajia tace "a'aa" fatu tacigaba "rubuta ban hakuri nayi na jimawan da sultan yayi bai zo ba, hakan ya samu asali ne ga riqeshin da akayi a kasar wajen, kuma kaka ya bari inzo gombe gidansu yana so yayi wa mamarsa suprise"
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣0⃣

Idan na gaji inyi alwala inyi sallah in kai kukana gurin Allah.
Sati daya daya wuce na cika shekara daya da aure, a cikin shekaran kuma dan aika yana kan zuwa kowanne month. Idan muka tambayeshi labarin sultan sai yace bai dawo bane. Hankalin kaka ya fara tashi ya fara dana sanin daura auren, akwai lokacin da ya kirani ya ke cemin ko zamuje kotu a raba auren? Nace mishi a'a, don nasan gwanda zamana da igiyar sultan akaina akan in zama bazawara hankalin kaka zai fi tashi. A ranar da zan cika shekara da aure muke tsammanin zuwan dan aika, a ranar na shirya plan dina don sanin matsayina. Yawanci bayan azahar dan aika yake kawo kudi, kaka na samu a kofar gida karfe 12:30 nace zan shiga jeji debo ganyen lalle, yace in aika yara mana, nace ina son zuwa da kaina ne, bai kawo komai a ransa ba ya mini izini. Already na gama shiri na fito, hanya kawai na yanka na shiga jeji inda nan ne hanyar shigowa cikin gari. Sai da na debo ganyen lallen na fito bakin hanya na tsaya a gindin bishiya ina jiran dan aika.
Nafi minti 30 na hangoshi yana tahowa kamar kullum a kan machine dinshi. Fitowa nayi ina tafiya nayi kamar ban ganshi ba, yazo dab dani na juya ya ganni ya ce ahh fatu me kikeyi anan? Yana kokarin tsayar da machine din, nace laa nazo tsinkar ganyen lalle ne yanxuma gida na nufa. Yace in hau ya isar dani, nace a'a nagode. Yace to ga aikan tunda na hadu dake a hanya, ki gaishe min da mallam Ameenu. Na karba nayi godia ya juya ya koma. Sai dana tabbatar yayi nisa sannan na bude envelope din, yau ma kamar kullum kudine babu wasiqa. Na fito da yar takarda daga cikin ledan da tun fitowana daga gida yana cikin hijabi na, hade da dan kunu a farar leda takardan na tura cikin envelope din na shapa kunu na liqe kamar ba'a budeba nayi hanyar gida ina mai farin cikin hukuncin dana yanke.

Jama'a menene fatu ta rubuta? 😳😳😳😳
Ina mai bawa masoya hakuri na rashin jina kwana biyu, phone dina ne ya samu matsala.
Luv u ol

Taku a kullum
Maman Fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣3⃣
Sun idar da sallah suka ci abinci, dija mai aiki ta tattare gurin fatu ta taya ta suka kai kitchen ta fito palour, farouq sai zuba surutu yakeyi fatu tana biye mishi har aka kira sallan isha ya tafi mosque suma suka tashi don yin sallah. Bayan sun idar da sallah ne suka dawo palour hajia ke tambayar fatu "sultan din bai baku number wayarshi ba? Fatu tace "hajia ai address din ma ya jameel ne ya bani bashi ba" kuma ni ban taba yin waya bama, to da waye zanyi? Ta karasa tana daria. "Babangida da kawu muntari ne kadai masu waya a gidanmu sai goggo asabe da ta taba siya tayi wata hudu ba'a kirata ba shine ta sayarπŸ˜‚πŸ˜‚. Murmushi hajia tayi tace "to yanxu fatu ya za'ayi ki tunkari sultan har kice ya sauwaqe miki? Fatu tayi dan jimm sannan tace "hajia tunda innar tawa qawarki ce sai ki fada mata ita tayi mishi magana" hajia tace "ke bakya dokin ganin innar taki ce"? Fatu tace "hajia inaga abunda sultan ya mini itama shi zata min, mahaifiyata suka zo nema bani ba, kinga ko baza su damu dani ba, nima kuma bazan tura kaina cikinsu ba" Haajia tace "fatu mahaifiyar sultan zata so ki sosai, don tun muna jeka da fari ta je dukku gurin mamanta wato kakarki, sunje aka ce musu ta rasu, 'yarta rahmatu kuma tayi aure a wani gari. Hajia sadiya (maman sultan) ba yanda ba tayi su fada mata sunan garin ba amma suka ce sun manta, zuwanta na biyu bana mantawa bamu dade da dawowa nan gidan ba ta qara zuwa, wannan karon Cewa sukayi karta qara zuwa gurinsu, don basu hada dangi da ita ba, wacce suka hadan ma sun yafe ta. Duk maganganun nan daga bakin yayan kakan ki yake fitowa, wai sunan shi mal jauro, ina mamakin yanda akayi sultan ya nemo ku". Fatu tayi shiru tana tunanin ya auntyn ta hajia sadiya zata karbeta, taji dadin jin ance tana son su. Hajia ta cigaba da cewa "ni a nawa shawaran ki zauna anan har lokacin da kike tunanin zaki iya samunshi ki masa magana, batun hajia sadiya kuma baza ta taba yarda sultan ya sake ki ba, don haka ki zauna anan ki fara makaranta har zuwa lokacin da naga ya dace ki tunkareshi. Fatu tayi shiru tana tunanin maganan hajia, hala in taje gurinshi yanzu yace bazai saketa ba ya korata kauye, amma in ta zama 'YAR BIRNI bazai wulakanta ta ba zai bata abunda take nema cikin salama tunda yasan tana da ilimi.
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣6⃣

A guje fatu ta shigo palour, hajia dake qoqarin haurawa sama ta dakata tace "lafiya fatu? Fatu tace "mummy wallahi mal usman na gani, mai kawo min saqo din nan, yana tura gate" hajia tace "mal usman ne yake kai miki saqo dama? No wonder kowanne month yakance zaije kumo kai saqo, kuma ban taba tambayarshi ba, da yake shi dan garin kumon ne" fatu dai bata ce komai ba sai zare eyes da take yi. Hajia tace "karki damu, nasan abun yi, kije ki shirya ki sauqo muyi breakfast" fatu tace "to" kana ta miqe ta haura zuwa dakinta.
Hajia kuma hijabinta ta saka ta nufi bakin gate gurin mal usman. Yana ganinta ya taso da sauri har yana duqawa ya gaishe ta, ta amsa masa cikin fara'a kana tace "mal usman saqo da kake kaiwa kumo gurin waye kake kaiwa" mal usman yace "gurin wata yarinya da kakanta ne, shekara kenan ina kaiwa, inaga na taimako ne ko kuma yar uwarsu yallabai sultanun ne" harda abunda ba'a tambayeshi ba ya fada. Hajia ta nisa tace "Yarinyar tana nan gidana amma shi sultan bai sani ba, idan ya baka saqon next month ka kai can garin modibbon, idan kakan ya tambayeka labarin fatu kace tana nan lafiya kalau, kar ka nuna masa ba'a gidan su sultan din take ba, zaka min wannan alfarmar? Kai tsaye mal usman yace "hajia duk yanda kika ce haka za'ayi" hajia tace "nagode kuma shima sultan din kar ka nuna mishi komai" hajia ta fada sannan ta shige cikin gida. Shi kuma ya koma bakin aikinsa don ta daure masa kai, amma dai yasan duk rintsi hajia baza ta taba cutan wani ba, kuma in ba kwanan nan ba basu san cewa Iyalai biyun ba dangin juna bane.
Sake curtain din window fatu tayi bayan taga hajia ta koma palour tayi ajiyar zuciya ta fada toilet tana mai addu'an Allah yasa mal usman ya bada hadin kai.
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣4⃣
Da wannan tunanin tace "hajia na amince in har zaki yarda ki dauke ni, wanke wanke da shara ko girki zan dinga yi? Hajia tace "ban gane ba"

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment