Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake kallo yasa ta fara tafiya tana cewa "to mammi" hajia sadia kuma ta koma ciki tana jindadi, don tun ba yau ba take son sultan da fateema, don yarinyar ta mata, ga nitsuwa da hankali, har cikin ranta take son fatu. A bakin gate ya cim mata, wani sauri takeyi bata son wani abu ya hada su, gudun kar ta kopsa ya ganeta. Sultan yace "madam ba haka tafiyanki yake ba" dolenta ta fara tafiya yanda ta saba, hakan ya bashi daman jerawa da ita. "Ina wuni" fatu tace dashi, yace "lafiya kalau fateey, kina lafiya" a gajarce tace "lafiya" dai dai nan suka iso bakin gate ta shige abunta, shi kuma ya juya ya fara tafiya, tana shiga taga bai biyota ba, sai taga sam bata kyauta ba, ko godia babu, leqawa tayi tace "hey" ya juyo ta sakar masa murmushin da ya saka shi jin sansanyar iska na bin jinin jikinshi. Yace "yess" tace "thanks" bata jira amsar sa ba ta shige. Samun kansa yayi da tsayawa a gurin yana doka uban murmushi da yasa hakoransa shan iska yana kallon kofar, yafi 5mins a gurin wucewar wata mota ce ta sa shi dawowa hayyacinsa ya koma gidansu. Ita kuma tana shiga a farfajiyan gidan ta hadu da mahmud zaune a irin kujerun shan iska nan yana karanta newspaper tazo ta gurinshi tace "sannu da hutawa" ya sauqe jaridan yace "yauwa" tayi wucewarta. A ranshi yace wacece wannan? May be dangin su sultan ce don tana kama dasu, amma dai ta hadu ba laifi, tashi yayi ya shiga cikin gidan shima, mummy ne ta fara ganinshi tace "mahmud har ka dawo? Yace "ehh" ya nemi guri ya zauna. Fatu tace "mummy shine ya mahmud? Mummy tace "shine" fatu ta gaishe shi ta masa sannu da dawowa ya amsa. Tace "na hadu dashi a waje ban zata shi bane ai" mummy tace "ayya, kina bacci suka dawo shiyasa" mahmud yace "mummy banganeta ba" mummy tace "yar uwarku ce daga bauchi tazo karatu ne" tana fadan haka ta tashi ta shige kitchen. Kallon fatu yayi yace "a gidan wa kike a bauchin, don ban taba ganinki ba duk zuwa na" shiru tayi ta rasa me zata ce can ta qakalo murmushi ta ce "ko na fada ma baza ka gane ba" zai qara magana mummy ta fito da basket a hannun ta tace "fateema ko zaki kai abincin gidan jameel? Ta nan sai ki musu sannu da dawowa" da dokin ta tace "ai kuwa mummy" "amma ki jira yanzu farouq zai dawo daga islamiyya sai ku tafi tare driver ya kai ku" yamma liss farouq ya dawo driver ya kaisu gidan jameel da amarya lubna.

Afuwan fans, sai yau Allah yayi na turo FATU A BIRNI. Ba jan ranku nayi ba, lokaci ne ban samu ba. Barka Da Sallah. Allah ya maimaita mana. Ameen

Taku a[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣7⃣

Wankanta ta tsala ta fito ta shafa mai da dan pop powder dinta na 100, sai kwallinta data sawa idonta, ta lakuti vaseline ta shafawa lips dinta. Doguwar rigan da hajia ta bata ta saka black ne mai adon sky blue a gaban rigan, kana ta dauki gyalensa shima sky blue ta yane kanta Wahoho jama'a sai yau na qarewa fatu kallo. Fara ce amma ba tass ba, tana da matsakaicin tsayi, figure 8 ce don rigan anyi shaping dinta, idanunta ba manya bane kuma ba kanana ba, tana da dogon hanci ba laifi, bakinta dan tsurut kamar bakin bottle, tana da gashin gira dai dai, fuskarta mai yawan murmushi. Itama kallon kanta ta tsaya yi a jikin mirrow tana smilling, sannan ta nufi kofa ta fita. Tun daga kan steps hajia ta ganta a ranta tace "masha Allah" don sultan yayi sa'ar mata, ga kyau ga ilimi both arabi da boko ga nutsuwa ga kuma ladabi da biyayya. Fatu ta iso ta dan duqa tace "mummy sannu da aiki" har ranta hajia taji dadin yanda fatu ta saki jikinta tana kiranta da mummy. Dinning suka nufa fatu tayi serving dinsu indomie da dankali da kwai sai tea. Suna ci suna hira duk akan yanda skul din fatu zai kasance. Bayan sun gama ne hajia tace zata yi bacci kadan kana ta haura sama. Fatu ta tattare gurin ta kai kitchen ta samu dija na wanke wanke,;ta tayata suka qarisa cikin tadi da raha, suka gyara kitchen din. Anan ne dija take tambayar fatu dangantakarta da hajia fatu tace "zan fada miki amma ba yanzu ba" dija tayi daria tace "to Allah ya kaimu ranar" fatu tace ameen ta haura sama itama ko zata runtsa.

Taku a kullum

Maman Fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣0⃣

Tafiya take yi a hankali zuwa gurinsa don ita duk a tunaninta ya ganeta, tazo dab dashi ya aika mata da murmushi yace "sannu yan mata" tsayawa tayi cakk, a ranta tace ashe bai ganeta ba, don haka ta fuske tace "sannunka" kana ta cigaba da tafiyanta zuwa gurin mal usman. Ta gaishe shi tace "mummy tace tana son ganinka kafin ka tafi" yace "to" kana yayi qasa da muryansa yace "fatu yallabai ya ganeki kuwa? (Mal usman gulmaπŸ˜‚) shiru tayi tana kallon gefe, sannan tace "ka manta abunda hajia tace ne? Duqawa yayi kamar me neman gafara yace cikin karamin murya "ahh yi hakuri, wallahi mantawa nayi fateema, bakin nawa ne ba sakata" murmushi tayi tace "ba komai" wuce wa tazo ta sake yi ta gaban sultan wanda tun tafiyanta gurin mal usman ya tsaya ya zuba musu ido, sai dai bai san me suke cewa ba. Tana shiga palour ta isar wa hajia saqonta tayi saurin haurawa sama, hakan yayi dai dai da shigowan sultan ya zuba ma bayanta ido, sai yake ganin duk duniya babu wanda hawan step ya masa kyau irin wannan babe din. Sai da ta shige ya juyo da kallonsa palourn ganin idonπŸ‘€ mummy qurrr a kansa yasa yaji kunya. Daya daga cikin kujeran ya samu ya zauna yace "sannu mummy" tace "kaima sannunka" dariya yayi don duk a tsarge yake kamashi da mummy tayi yana kalla mata baquwa. Suka gaisa, mummy ke jajensa tace "wato don jameel baya nan shine ko kafanka ba'a gani ko" murmushi yayi yana sosa qeya yace "wallahi mummy ban zauna bane, last wik ma dawowana daga china, kuma nazo farouq yace kina bacci" hajia tace "ba komai in abokin naka ya dawo ai zamu na ganinka, Kaga shikam yayi iyali, kai kuma naga alama so kake azumin nan a fara kada maka gangan tuzuru" daria yayi sosai yace "mummy ki shirya bayan sallah zakuyi bikina, na samu mata sai dai bamu daidaita ba" Mummy ta kallesa tace "a ina" sultan yace "kin santa ma mummy, ki tayani addu'a kawai" da jin haka mummy ta gane fateeman ta yake nufi, sai ta fuske tace "nidai ban gane wacece ba, Allah ya baka sa'a" ganin bai samu fuska ba yasa ya maida kallonshi kan tv, yafi kusan 30 mins xaune da hajia suna hira sai dai ko kadan bata kawo masa tadin baquwarta ba, fatu kuwa qin fitowa tayi. Ya gaji da jiran fitowan ta yayiwa hajia sallama ya fita.

Taku a kullum

Maman Fa'izπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣8⃣

Shigan fatu daki ta kwanta a gado tana tunanin rayuwarta, ita kanta mamakin yanda ta sake a gidan takeyi, amma da ta tuna da yanda hajia ta karramata sai take ganin ko me hajia tace tayi zatayi in dai bai kauce shari'a ba. Duba agogo tayi 8:34, kakanta ne ya fado mata a rai, yanzu haka yana can yana kewanta, Allah sarki, hawaye ne ya fara sintiri a beautifull face dinta idonta a rufe, a haka har bacci ya dauketa.
11:00 ta farka, bandaki ta shiga ta kama ruwa sannan ta sauqo palour, babu kowa sai kamshin girki da yake tashi a kitchen, ta shiga kitchen din ta samu dija tana girka abincin rana, fatu ta mata sannu da aiki ta kama sunayi tare. Fatu tace "maman isya (dija) mummy bata fito bane? Dija tace "ta fito dazu ta fadi abinda za'a girka" Fried rice wanda yaji hanta da kayan lambu sukayi sai coslow, fatu tace "akwai zobo ne?" Dija ta kawo mata, tace "mman isya a ina zan samu bawon abarba? Dija tace "sai dai a aika habu driver ya karbo, akwai masu sayar da fruits a bakin hanya" dija ta fita ta bawa habu driver aika, minti goma ya dawo da bawon abarba mai yawa, fatu ta karba ta daura akan wuta tasa ginger, kanunfari da zobon, suka ci gaba da hiransu suna gyara inda suka bata har zobon yayi, ta sauke dija ta tace shi a wani bokitin roba ya dan huce suka sa sugar sukayi blending cucumber suka saka. Dija ne ta fara tabawa tace "zuwaiiitt kenan, hajia zata ji dadin wannan zobo dama bata cika son na kwalin nan ba" fatu tayi murmushi itama ta taba tabbas yayi dadi don bata taba yi ba, time din da take secondary tayi food and nutrition to anan ta dan iya wasu girke girken sai dai ba kowanne ta gwada saboda yanayin gidansu. Freezer suka kai don yayi sanyi da wuri, barin dija tayi a kitchen Din ta fito palour, hakan yayi dai dai da shigowan farouq 12:40 da sauri ta rungumeshi tana masa oyoyo, peck ya mata a kumatu tayi murmushi itama ta masa duk suka sa daria, wa yaga FATU A BIRNI har an fara wayewa😜. Duk abunda sukeyi hajia na kallonsu tana jindadin shakuwarsu na kwana 1. Da gudu yaje gurin hajia itama ya mata peck ta masa oyoyo.
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣7⃣

Jameel yace "I am sorry to say bazan iya raka ka ba, I cnt face da dattijo" yana gama fadan haka ya fice daga palourn, sultan ya bi bayansa amma yana fita jameel already yaja motarsa ya bar gidan, shima ya fita.
Lubna dake kitchen ta fito jiki a sanyaye da alama taji duk hiransu, jameel ya bata labarin fatu tun ba yau ba, haka kawai itama take kaunar sultan da fatu, ko ba komai 'yar uwarsa ce, marainiya mai neman taimako, kuma a yanda taji jameel ya fada fatun tayi karatu har zuwa secondary, so why not ya maida ta skul in educated wife din yake so, tunani barkatai lubna tayi akan fatu, tana tausayawa yarinyar. Tashi tayi ta shige dakin jameel ta bude drawer da yake ajiye pictures, da kyar ta samo pic din sultan da matarsa fatu. *WHAT*? naji ta furta da karfi hade da miqewa tsaye harta manta cikin 6months da yake jikinta.

Fatu na isa gida tayiwa mummy kunun aya tasa mata a fridge, fitowanta daga kitchen din yayi dai dai da shigowan mummy gidan, fatu tace "sannu da dawowa mummy" tace "yauwa fateema" fatu tace "farouq daya dawo daga skul yace zai biki gidan mammi, yaje ne" hajia tace "dan rigima yaje, ynxuma na barsu zasu je unguwa da amrah ne" fatu tace "ayya, nima inason zuwa gidan anty lubna anjima" mummy tace "Allah ya kaimu" fatu tace "Ameen, na gama kunun ayan, yana fridge" da murmushi a fuskar hajia tace "nagode 'yata Allah ya miki albarka" "Ameen mummy" fatu tace ta bar mummy a palour ta shige dakinta don tadan huta zuwa yamma, ko meyasa sultan yake nemanta oho. Wayarta ta dauka don tayi chattin amma sai taga missed calls din lubna 4, da sauri ta kirata don ita ta dauka ma ba lafiya ne. Ringing daya biyu ta dauka tace "Hello fateema kina gidana ne? Tace "ina gida, naga missed calls dinki ne, lafiya kam? Lubna tace "sai alkhairi, don Allah ina son ganinki yanzu yanzu" fatu tace "ai anjima ina zuwa da yamma" lubna tace "a'a its urgent pls ko minti biyar karki qara" fatu tace "to pls bari inyi wanka" "ohhh fateema kiyi hakuri ki dauko kayan da zakisa in kinzo kiyi anan" fatu tace "to gani nan zuwa" kashe wayan tayi zuciyarta na dukan uku uku. Anya ba ganeta sultan da jameel sukayi ba? Saisaita kanta tayi ta dauki abubuwan da take bukata taje dakin mummy tace "mummy bari inje yanxu anty lubna ta kirani" mummy tace "to shykenan Allah ya kiyaye hanya, ki dauka mata kunun ayan nan naga itama tana so" murmushi fatu tayi tace "to mummy" bayan ta dauka ne ta fita mal habu ya drivin dinta sai gidan jameel.

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣6⃣

Yau kimanin wata biu da sati biu kenan da haduwan sultan da fatu a a gidan jameel, shakuwa mai tsanani ya shiga tsakaninsu, wanda yawanci in sultan na qasar shi yake kaita school, waya kuma kowanne dare sai sunyi b4 bacci, no love jst qanwa da yaya. Chattin babu wanda fatu batayi da taimakon qawarta xahra levels. fatu har sunyi exams na second semester suna hutu. Yau saturday sunyi da levels zasu je saloon, Karfe 11 na safe tana gidansu levels daga nan suka rankaya gurin saloon din da yake ba nisa tsakaninsu.

A gidan jameel naga sultan da abokin nashi a palour suna magana, jameel yace "its time ka furtawa fateema cewa kana sonta, don kun saba wanda nasan lokacin da kuka dauka kuna tare itama ta fara sonka" sosa kai sultan yayi yace "kana ganin ta fara sona? "Kwarai insha Allah" Jameel ya bashi amsa. Sunkuyar da kai sultan yayi kana ya dago yana kallon gefe. Muryan jameel yaji yace "FATU FA?? Da sauri sultan ya juyo da kanshi gurin jameel zuciyarsa na dukan uku uku, don shi ya manta ma da wata fatu, yau kimanin wata uku kenan ko aika da yake mata ya daina, fateema ta mantar dashi cewa yana da mata ajiyayya. Jameel ya qura masa ido yana jiran yaji mai zai ce, shi dai fatu ta masa tun ranan har yanxu kuma yana tausaya mata a matsayinta na marainiya abar tausayi, "baka yi magana ba" jameel yace dashi, sultan da har yanzu bai gama saita kanshi ba yace "ni fateema nake so, bani da ra'ayin zama da mata biu kuma. Inaga its time itama da zan furta mata abunda ya dace da ita" jameel zaiyi magana sultan yace "jameel u knw yanda aka hada auren, sam babu yarda ta. I cnt live with her" Shiru jameel yayi, sultan sai da ji hankalinshi ya dawo jikinshi ya dauki wayarsa yayi dialing numbern fatu.
Bayan an gama musu suka rankayo gida. Fatu ne da xahra ke hira kan sultan levels na cewa "wallahi qawa har yanzu ina mamakin wai sultan mijinki ne amma kuma bai ganeki ba, kuma wai he's in love with new fateema" murmushin daya fi kuka ciwo fatu tayi tace "labarin rayuwata kamar a movie, bansan nan gaba ya zaya kasance ba, zan rabu dashi ne ko zamu kasance a inuwa daya a matsayin mata da miji, levels ki tayani addu'a kawai. Allah ne kadai abun dogaro na" siririn hawaye ta goge hakan yayi dai dai da ringing din da wayarta ya fara "dan halal, yaqi ambato" cewar fatu yayin da murmushi ya bayyana a fuskarta, xahra ta bita da kallon tausayi. "Assalam alaika yayan fateey" "wa'alaiku mussalam qanwata, ya kike? Tace "lafiya lau, ya aiki? Yace "da godia, jiya kince zaki je saloon kinje ne? Tace "ehh, yanzu muka dawo ina gidansu levels ne" Yace "ok, in baza ki damuba anjima da yamma inason ganinki" tace "ok yayana, zaka zo gidane? Yace "noo, mu hadu a gidan jameel" sukayi sallama sukayi hanging. Fatu ta kalli levels tace "I gotta go, zanyi wa mummy kunun aya nd sultan yana son ganina" levels kada kai tayi kawai ta rakata haraban gidansu tasa drivernsu ya maida fatu gida.
Sultan na ajiye waya yace "jameel insha Allah nan da 1 week zamu je Garin Modibbo gurin FATU"

Maman FateeyπŸ‘―πŸ‘―
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣5⃣

Tun shiganta motan kamshin jikinsu ya gauraya ya bada wani ni'imantaccen scent mai kwantar da hankali, ga a'c ya sanyaya ko ina. Ba sultan kadai ba har fatu taso inama suyi ta zama haka har abada *what? Fatu ar u in love?* tsohuwar cool music na celin dion mai taken _TITANIC_ ya saka musu (in d nyt in my dreams I see u, I feel u....) yana bi a hankali, fatu da ta gama narkewa ta juya kanta gurin window tana jin kalaman waqar har cikin zuciyarta yana ratsa ta. Maimakon taga anyi hanyar gida sai ya biya wani guri, basu tsaya a ko"ina ba sai katafaren gurin sayar da phones. Ya juya zaiyiwa farouq magana yaga yayi bacci. Fatu ta juyo tace "baka ce zaka yi branching ba, srry mun takuraka" yace "no wahala, abu zan saya kuma gashi farouq yayi bacci banida dan rakiya, muje ki rakani" tace "no, in kai alone ne zaka fi sauri" Yace "noo, to ki biyani rakiyan dana miki dazu" yanda yyi maganar kamar yaro yasa fatu daria tace "muje to". Suka shiga tana binshi a baya, yace "pls ki tayani zabe, amrah nake son sayawa waya" tasan dai amrah nada waya koda yake abunka da masu shi, tara wayoyi a hannu qaramin aikinsu ne. Iphone latest ta nuna tace "wannan yayi" Yace "irin nawa" tace "sai kuyi anko" yace "hakan za'ayi" Qaramin Nokia ya qara dauka ya biya kudinsu, anan ya qara sayan sim cards 2 dfffrnt layi suka fita. Har komawansu mota farouq na baccinsa, basu zame ko ina ba sai *eman* ya saya musu ice cream da snacks, daga nan suka yoo gida wajen tara saura. Har cikin gidan ya shiga yayi parking suka fito daga motan, fatu na qoqarin daukan farouq yace "lemme help" ba musu ta matsa masa ya dauke sa suka shige gidan, a palour ya kwantar dashi mummy kuma da alama tana dakinta, Fatu tace "thanks" yace kinyi mantuwa a mota, tace "ni? Ok tsaraban da anty lubna ta bani" fita sukayi ya bude motar ya dauko ledojin da sukayi shoppin ya miqa mata, tace "wannan ne nawa" ta karba yace "dan tsaya pls" tayi juyi irin ta gajin nan, yace "srry" bude ledan wayoyin yayi ya saka musu layi duk tana tsaye ya kunna ya miqa mata, yace "bari in gwada kira" ita duk bata dauka wani abu ba ta karba, wayarshi ya ciro sak irin na hannunta ya kira sai ga numbern shi ya bayyana a screen din, miqa mishi tayi tace "yayi" yace "kip it, naki ne" cikin zaro ido tace "what? Noo kayi hakuri.... kafin ta qara magana ya rufe motarsa yayi reverse tana tsaye har aka wangale masa gate ya fita, ta jima kana ta koma gida jiki a sanyaye, a palour ta tarar har mummy ta shigar da farouq dakinsa, tana sauqowa qasa, fatu tace "mummy mun dawo" hajia tace "sai yanzu kenan? Jameel din ne yadawo daku? Fatu tace "a'a amm.... yayan amrah ne" sarai hajia tasan sultan ne ya dawo dasu don tana ganin shigowarsu duka, tace "bari in duba kullin masan nan, gobe da safe dadynku zai sauqo yace shi yake sha'awa" har hajia ta dubo ta fito fatu na tsaye a gun, hajia tace "auu baki haura bane? Kaman zatayi kuka tace "mummy wayoyi ya bani fa" da fara'a hajia tace "a ina" fatu ta labarta mata komai, hajia taga wayoyin tace "amma sunyi kyau Allah ya amfana" fatu da mamaki ya gama lullubeta tace "mummy gobe zan mayar masa dai ko? bata fuska hajia tayi tace "maganar gaskia fateema ki nemi soyayyar mijinki, abunda zan iya fada miki kenan, kibi komai a hankali da nutsuwa" har zata juya fatu tace "mummy ga tsaraba anty lubna ta bani" mummy ta gani tayi Allah ya amfana tayi upstairs. Zama jugum fatu tayi tana aukin tunani, ita ta rasa a wani yanayi take, shin tana son mijinta ne ko bata sonshi? Kodai kawai son yan'uwantaka ne? Amma deep inside her heart tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba. Da taga tunani bazai fishhe ta ba tace "Allah ka shige min gaba" tashi tayi ta dauki roban ice cream daya da snack iya wanda zata ci sauran tasa a fridge, kashe wuta tayi ta kulle kofa tayi dakinta, bayan ta gama ci ne tayi wanka ta fito taga leda akan mirrow nata, murmushi tayi tace tsaraban mummy ne. Ta duba takalma ne yan ubansu guda uku kowanne da jakansa, na lubna kuma turaruka ne da cosmetics, adana su tayi ta kwanta. Qarar wayanta ne yasa ta tashi zaune a tsorice (sabon shigaπŸ˜‚πŸ€“) a hankali tasa hannu ta dauka, number ta gani wanda tasan na sultan ne tace "hello" can gefe akace "hii" shiru ya biyo baya, can a gefe yace "sultan ne ya gajia? Tace "lafiya, nagode fa Allah ya saka" har cikin ranshi yaji dadin addu'anta yace "ameen, sai da safe, karki shanye ice cream din ki ragewa farouq nashi" daria dukansu sukayi kana sukayi hanging, daga ita har shi da murmushi a fuskarsu bacci ya dauke su. Hmm _lovebird[truncated by WhatsApp]
[8:14pm, 8/5/2016] Dara: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻FATU A BIRNIπŸ‘œπŸ‘  🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣1⃣

Sultan na fita ya hadu da farouq ya dawo daga skul, tafawa sukayi yace "big boy, ka dawo? Ya skul" yace "lafiya kalau, yau muka yi games, mukayi gudu muna waqan soldiers" sultan yace "Ai ana ganinka anga sojaa, give me five" suka qara tafawa, kana sultan yace "amm sojaa, nikam wacece baquwar mummyn nan? Farouq yace "anty fateema ce, tazo karatu ne" da yake hajia ta gargade shi kan duk wanda ya tambayeshi fateema ya fadi haka nan. Yace "ok good boy, maza in ka shiga gida kace ina gaisheta" yace to. "Fateema" sunan ta mai dadi, murmushi yyi ya shafi face dinsa kana ya dan bugi kirjinsa saitin heart dinsa, (ko me hakan ke nufi oho😜) fita yayi daga gidan, a bakin gate ya hango mal ahmadu yazo karban mal usman guard tunda zaije aika. Suka gaisa ya wuce gidansu.
Dawowan farouq yasa fatu sauqowa kasa ta masa oyoyo, yace "bro sultan yace yana gaisheki" kallon mummy tayi taga hankalinta na kan tv don haka tace "yaushe" yace "yanzu na hadu dashi a bakin gate, kin ganeshi? Shine wanda nake baki labarin ya kawo min tsaraba zuwansa china, muje in qara nuna miki tsaraban" fatu tace "awww yanzu na tuna, kaje kayi wanka kayi sallah sai muci abinci, akwai labarin da zan baka" ya tafi dakinsa. Mal usman ne ya shigo ya gaishe da hajia ya tsaya a bakin kofa, hajia tace "sultan ya baka aika ne? Yace "ehh" tace "ka bawa fateema ta dubamin, miqa ma fatu yayi ta bude kudi ne dai har yanzu, har zata rufe taga wata karamar paper da dauka ta miqa wa hajia. Hajia tace "a'a letter dinki ne" rufe envelope din tayi ta bawa mal usman yasa a aljihu. Hajia tace wa fatu shikenan kije dakinki. Ta wuce. Hajia tace "mal usman kamar yadda na fada maka fateema tana nan amma kakanta bai sani ba, haka sultan, inaso a dauka a gidansu sultan take, kakanta kan iya tambayarka fatu, kace masa tana lafiya, kuma a baka takardun karatun ta duka, sultan zai saka ta a makaranta" da saurinsa yace "hajia an gama" kudi ta bashi ya karba yana godia kana ya fita.
Fatu kuwa tana shiga dakinta ta fada kan gado tana tariyo yanda sultan ya mata murmushi, karo na biyu kenan da taga smillin dinshi. Ya qara mata kyau da kwarjini, dazu tayi matuqar yin qoqarin ganin bata kwapsa ba balle ya ganota. Papern tayi saurin budewa, ta fara karantawa

Hii

""Ki cewa mal Ameenu na gaishe shi, ki kuma bashi hakurin rashin ganina, may be bayan sallah zanzo""

Samun kanta tayi tana nanata wasiqar, duk da ba ita akayiwa ba amma taji dadin sa. Murmushi naga ya subuce a fuskarta can kuma ta fara hawaye, tana tausayin kanta,

2 Comments On FATU A BIRNI
avatar
call-mae

1 year ago

Reply

Hi

avatar
fatima-aliyu

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment