Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[8/7, 7:35 AM] Aisha Galadima: *_typing_*๐Ÿ“ฒ



๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA.........!!._*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi!๐Ÿ—ก}_


*_Bilyn Abdul Ce_*๐Ÿค™๐Ÿป


*_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*๐Ÿ˜œ


( ุจูุณู’ู…ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽูฐู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู…ู )

_Da sลฉnan Allah, Mai rahama, Mai jin ฦ™ai._


*SADAUKARWA*
_Wannan littafi sadaukarwane ga mahaifina *Malam Ibraheem Musa (Na-Ali),* ya Rabbi kakai Rahma, Ni'ima, gafara a kabarinsa, ya ALLAH ka ni'imta ruhinsa zuwa aljannarka, da dukkan sauran musulmai, mudaya bari ALLAH ka rayamu cikin ni'imominka da rahmarka._๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘๐Ÿป
_Ya ALLAH ka hana mak'iya da shaid'anu samun nasarar raba kayinmu, ALLAH kabamu ikon aikata khairan akowanne lokaci๐Ÿ˜ญ._
*I love you so much baba*
_(Muna kewarka wlhy)_๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ


*Na gaisheku, nagartattun dangi*
Nafisat Ibraheem Musa
Hauwa'u Ibraheem Musa
Musa Ibraheem Musa (Abba)
Fateema Ibraheem Musa (ummi)
Muh'd Atteku Ibraheem Musa
Libabatu Ibraheem Musa
Shu'aibu Ibraheem Musa
Jameela Ibraheem Musa
Muh'd shamsuddeen Ibraheem Musa
Aisha Ibraheem Musa.

*_bilkeesa Ibraheem Musa_*๐Ÿ˜‰
Namik'o gaisuwar bangirma marayun ALLAH, ALLAH ka k'aramana soyayyar juna๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜


*_'yan uwana ababen alfaharina_*
Yaya Abdullah (city phone's)
Aunty Ruk'ayyat (Maman khausar & Raudah).

_Ina k'aunarku sosai, fiye da tunanin mai hasashe, ALLAH ka k'ara had'e kayinmu har Abadan, ALLAH ka k'arama mahaifiyarmu lafiya da tsawon kwana._๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘๐Ÿป


*_inamai farincikin sake had'uwa daku fan's, a buk na 12 dana rubuta, ALLAH yasa mu amfana da abinda zaizo._*


_ya ALLAH ina Neman tsari daga cecekucen social media_๐Ÿ‘๐Ÿป


*idan kasan bazaka/bazaki iya jurewaba, karki/karka karantamin littafi, Dan sak'ona zan Isar, duk Wanda bashida hangen fahimtar sak'on, kada ya wahalar dakansa wajen bibiya, Dan banason gutsiri tsoma๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿคซ.*
_kuma duk Wanda yacanjamin wani Abu ban yafeba_๐Ÿค



*_part 1 loading_*
_(littafi Na d'aya๐Ÿ“•)_



0โƒฃ1โƒฃ


*Sautin* kukane ketashi acikin gidan, wasuma harda kururuwa da ambaton sun shiga uku, wasu nafad'uwa k'asa ana kamosu, duk Wanda kagani acikin gidan kasan yana cikin matuk'ar tashin hankalin rasa wani abu muhimmi.

Nikaina dai kukan nasu yatada hankalina.

Nakoma dagacan gefen wata matashiyar budurwa dabazata wuce shekaru 13 ba aduniya, dukda k'arancin shekarunta sainaga Nisan hankalinta, domin kuwa ita kukan NATA yana fita cikin salamane, babu kururuwa balle fad'uwa k'asa, kamar yanda sauran 'yan uwanta keyi.

Kafin na samu damar tanbayarta dalilin kukan nasu? naji ta furta *ALLAH sarki babanmu, ALLAH ya gafarta maka*, yau katafi kabarmu, ALLAH daya bamukai babu shawararmu, yau yakar6eka babu shawararmu, (ALLAH kenan, buwayi gagara misali), jiya iyanzu yana taredamu, yaukuma mun wayi gari and'aukesa.
Takuma fashewa da kukanta mai tsuma rai, Wanda inba kusada ita kakeba, bazaka ta6ajin sautinsaba.

(Humm wannan rasuwa ta tadamin mikin nawa tabon Na rasa mahaifina, a ranar 1 ga watan Rajab, wata uku kenan๐Ÿ˜ญ, ALLAH yagafarta musu baki d'aya, ameen).

Wani dattijone datun d'azu suke shigi da fici daga wani d'aki zuwa tsakar gidan yace, "ya salam! Habadai Dan ALLAH, wannan kuka bashine zaidawo mana da Malam Abubakar duniyaba, amatsayinku Na musulmai wannan kururuwar da ihun bai kamacekuba, addu'a Malam yake buk'ata agareku amatsayinku Na iyalansa, kukanmu bazai dawo mana dashiba, amma hak'urinmu da nutsuwarmu zaisa murok'a masa gafarar UBANGIJIN Al'arshi.
Dan ALLAH muyi hak'uri hakanan, ALLAH ya gafarta masa, yabamu hak'urin rashinsa.
Tunda dattijo yafara magana gidan yay tsit, wannan nasiha tashi tayi tasirin saka kowa yin shiru, saidai shashshekar kukan wasu da ajiyar zuciya.
Cikin 2hours aka gama had'a gawar marigayi Malam Abubakar, nagartaccen malami, masani akan ilimin addini, mai kishin musulinci da musulmai, mafad'in gsky komai d'acinta, mai hak'uri da kawaici, mai uzuri ga komai Na rayuwa da halayen bil-adam.
ALLAH ya gafarta masa, Dan bak'aramin rashi akayiba kam yau, ALLAH yad'auki Malam Abubakar bayan gajeriyar jinyar dayasha ta kwana 18 kacal, wadda tazama sanadin ajalinsa, yabar duniya bayan sallar asubahi, mintuna 3 da idar da sallar da ALLAH yabashi ikon sallata, wadda tazama ibadarsa tak'arshe adoron k'asa.
Yarasu akan abin sallarsa, dan ko gusawa baiyiba saida aka zare ransane d'ansa da k'anwarsa dake d'akin sukaga ya tuntsure kasa yaraf.
To saimuce ALLAH ya gafarta masa, da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu gidan gsky.

*_marayu inayinku wlhy๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€, ALLAH yak'ara mana hak'uri๐Ÿ˜ญ_*

Bayan kammala had'ashi, aka kira matansa biyu Barirah & Fad'ima domin yin bankwana, sunmasa addu'a da Neman gafararsa, sannan suka fito cikin kuka.
Daga nan aka buk'aci ganin 'ya'yansa, wad'anda suka kasance adadin su 9. d'akin barirah uwar gida nada 6, sai amarya Fad'ima nada 3.
Suma sunma mahaifinsu addu'a da fatan alkairi, duk suka fito cikin kuka.
Mintuna kamar 17 da haka aka fito da gawar Malam Abubakar zuwa gidansa na gsky, sosai sautin kuka yafara tashi, haka akafitadashi sunaji suna gani, basuda damar hanawa.๐Ÿ˜ญ


*_mutuwa kenan, maimaida mata zawarawa, mai mayar da yaro maraya, mai yanke jin dad'in duniya, mai yanke abota da 'yan uwantaka._*๐Ÿ˜ญ
Yakai bawa ka aikata alkairi kodan tsoron wannan ranar๐Ÿ‘ˆ๐Ÿป, yau babana yarasu, gobe abokina, jibi matata, gata d'ana, wlhy watarana Kaine zaka tafi๐Ÿ‘ˆ๐Ÿป๐Ÿ˜ซ.

An sallaci gawar Malam Abubakar a k'ofar gidansa, sannan yasamu rakkiyar d'umbin mutane zuwa makwancinsa.
Zuwa yanzun kam gidan yagama cika da mutane, anata gaisuwa ga wad'anda abin ashafa.
To dama akance idan kaje gidan mutuwa kakan shaida Wanda akaimawa, wannan maganar haka take, dankuwa zuwa k'arfe 2na rana wasu harsun fara sakewa, harma suna lodama cikinsu abinci, saidai ga 'ya'yansa bahaka bane, Dan kallo d'aya zaka musu ka tabbatar har sannan suna tartare da damuwa sosai.

Wannan kenan๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ.


*7days ago*

Ayau akayi addu'ar bakwai d'in Malam Abubakar, bayan lafawar komai kuma shak'ik'ansa suka had'a taro Na family.
Ba'a samu nutsuwar kowaba sai 1:43pm zuwa sannan mutane duksun baje, 'yan uwa Na nesa Dana kusa kowa Yakama gabansa, sai shak'ik'ai, irinsu k'annensa da yayunsa.

Dattijo m. Bilyamin shiya fara gabatar da sallama agaresu, yayi doguwar addu'a ga mamaci Malam Abubakar, harmada sauran al'ummar musulmi dasuka rigamu.
Daga nan yaja dogon bayani akan gado da kuma biyama mamaci bashi da kar6o abinda yakebi, yaymusu nasiha da nusar dasu muhimmancin rik'e zuminci, da kuma addu'oi ga mahaifinsu, yanda zasu rik'e maraicinsu harya amfanesu.
Ya tausasa murya tareda binsu da kallo d'aya bayan d'aya, ya ce, "kuyi hak'uri da abinda zan fad'a, musammanma iyayenku mata, nasan duk uwa tana buk'atar tarayune da 'ya'yanta, saidai k'addara tarabasu, badan ansoba, kamar dai yanda nake gani kuma yau zata nisantaku da naku, Dan hakan shine babban gata dazamuyi gareku, kuma shine abinda zamuyi mu kwatanta k'yaunarmu ga d'an uwanmu, bayan k'asa tarufe idonsa mukula da zuriar daya bari.
Sosai naga tashin hankali a fuskar iyayensu dasu Kansu 'ya'yan.
M Bilyamin yacigaba da fad'in, bazamu kwashe mukusu dukaba, amma ZAMU d'auke k'ananun cikinsu, saboda sunfi buk'atar kulawarmu.
Kamar yanda kuka sani, Jafar da Murtala sun mallaki hankalinsu, kuma yakamata abarsu domin kula daku iyayensu mata, basukai k'arfin daza'a bar musu nauyin k'annensuba tukunna, dukda kuwa sunada shekaru 24&26 aduniya.
Saikuma Fadeela & Hafsat suma zasu k'arasa zamansu da iyayensu mata tunda aurensu saura wata 1 da sati 1.
To amma Sadiya da Rufaida da Aysha zasu dawo hannuna, Sadiq(Abba) zai koma wajen Asma'u, Ummulkhairi zata koma wajen Ahmad, ALLAH yasa hakan danayi yayi daidai kuma zaku goyamin baya.
Gaba d'aya suka amsa da gamsuwa.
M bilyamin yaji dad'in hakan dasukai masa.

Kukan Gwaggo bintu ne yakatsesu, cikin kuka mai tsanani tace, "yaya bilya ni mizaisa awareni ak'i bani d'a ko d'aya acikin tsatson Yaya babba, shin har yanzu baku yarda da tubanaba kenan? Kuna k'yamata kamar kamar baya?, aganina nafi kowa buk'atar yarannan, kodan rashin haihuwa daban samuba, amma babu komai namuku uzuri. Tamik'e tana sharar kwallah dafad'in zan koma, ALLAH ya gafartama yaya babba...
Harta fara tafiya Malam bilyamin ya tsayar da ita dafad'in bintu!.
Cak tatsaya, tana cigaba da matse kwallah.
Yace, " dawo ki zauna".
Babu musu tadawo wajen zamanta.
Cikin tausasa harshe yace, "kiyi hak'uri bintu, banhanaki d'aukar yaro kod'ayaba, saidai ina dubi da cewar bakina zaune bane a gidan mijinki, kema akare kike, wlhy bintu muna tausayinki akan rashin haihuwa, amma munsan ALLAH shine mai badawa, k'ila rashin haihuwar taki shine alkairi agareki.
Kanta ta jinjina tana share kwalla, tace nayarda dakai yaya, kuma nagamsu da hujjarka, amma batun akare nake bai tasoba, agidan *Alhaji Abdallah Jigawa* ban rasa komaiba, kuma inada k'yak'yk'yawan muhali kamar namai aure, gidan sunada tarbiyar danasan konaje da wani acikin yarannan baza'ayi nadama ba.
Kuma Alhaji Abdallah zai rik'esu tamkar 'ya'yansa, tunda shima yana rik'on marayun, Dan ALLAH kuji tausayina kubani 1, nima zan kalla naji dad'i, tunda ALLAH ya k'addara nikad'aice ware acikinku.
Sosai maganganunta suka ta6a musu zuciya.
Kuma sunsan tabbas suka hana bintu d'iyansu duniya zata zagesu da kallon danbasu fito CIKI d'aya baneba (Dan ita gwaggo bintu baba suka had'a dasu malam bilyamin, itakad'ai babarta tahaifa agidansu, kuma ita kad'aice 'yar uba).
Dogon numfashi Malam bilyamin yasauke, yace shikenan, saiki d'auki d'aya, wakika za6a?.
Caraf gwaggo bintu tace, ''Ai'sha yaya.
Gaban Ai'sha da mamanta ya yanke yafad'i, sosai tsoro ya bayyana agaresu.

Shikamsa Malam bilyamin saida mamakinsa ya bayyana, Dan kuwa kowa yasan gwaggo bintu basa shiru da Maman Aysha, tuni basa shiri.
Jin sunyi shiru gwaggo bintu takatsesu da fad'in yaya kodai akwai matsalane?.
Da Sauri Malam bilyamin yace, "a'a bintu, anbaki, ALLAH yatayaki rik'o.
Duk aka amsa da ameen.

Amma banda Aysha da mamanta, wad'anda suka shiga tsananin tashin hankali.........๐Ÿ–Š



_hummm komiyasa ba'a son bama gwaggo bintu Aysha?, Wayema Alhaji Abdallah Jigawa? Miyekuma alak'ar zamanta da gidan?, idanma tatafi da Aysha wane irin zama zatayi a can d'in?, shin yama tarbiyar gidan take? Tanada inganci kamar yanda gwaggo bintu tafad'a?._
Dukma abar wannan batun, Aysha zata amince tabi gwaggo bintu gidan Alhaji Abdallah Jigawa kuwa? Mikuma yasa gwaggo bintu ta za6i Ayshar ma to?.




Taku har kullum, Bilkeesa Ibraheem musa (bilyn Abdul).


Kukasance dani๐Ÿ˜‰๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ, awannan labari mai matuk'ar rikita-rikita.๐Ÿค


Yanzufa aka fara Fan's, kumuje zuwa oooh




*_I love you all my fan's_*๐Ÿ˜
[8/7, 7:35 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*๐Ÿ“ฒ



๐Ÿคฐ
*_CIKI DA GASKIYA.......!!_*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_



*_Bilyn Abdul ce๐Ÿค™๐Ÿป_*


*_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*๐Ÿ˜œ


*Sadaukarwa*
_My sweet dady_
(ALLAH ya gafarta maka)๐Ÿคฒ๐Ÿป



*_part 1_*
(littafi na d'aya)


0โƒฃ2โƒฃ

Bak'aramin kuka Aysha tasha ba, hakama mamanta tayi kukan a 6oye, fadeelama tasha kuka Dan za'a rabata da 'yan k'annenta masu d'ebe kewarta, amma babu yanda zatayi, Dan dolene kowa yabi umarnin k'anin mahaifin nasu, Wanda ayanzu ya maye musu gurbin mahaifi agaresu, tunda basuda kamarsa.

Tunda safe gwaggo Asma'u tawuce da Abba katsina, (a can take aure).
Hakama uncle Ahmad yawuce da Ummulkhairi Jigawa wajen aikinsa (shima iyalinsa nacan).
Itakam Aysha sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu da safe zasu wuce da gwaggo bintu zuwa Abuja.


_______________________
*Washe gari*

*(Sabuwar rayuwa)*

Haka Ai'sha tatashi sukuku kasancewar kuka datasha itada fadeelah yayarta a daren jiya, haka sukaita kuka har saida mama ta tsawatar musu, daga baya kuma tayi musu nasiha da nuna musu muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara, tak'arashe dayima Aysha nasiha akan takare mutuncinta a bak'on muhallin dazata tsinci kanta.
Kada ta kasance mai kwad'ayi da shiga sabgar da babu ruwanta, banda rashin kunya ganagaba da ita, takuma ringa yima gwaggo bintu biyayya amatsayinta na k'anwar mahaifinta, kada tasake wani yarud'eta ya lalata mata tarbiyyar dasuka gina tsawon shekara 13, koda kuwa a yaran gidanne, tarik'e addininta kada tazama mai sakaci dashi, takula sosai.
Nasihar mama tashigi Aysha, kuma ta kar6a cikin kuka da alhinin rabuwa da mahaifiyar tasu, wadda tunda tayi wayau basu ta6a rabuwaba koda na kwana d'aya, Dan marigayi baya barinsu zuwa ko ina Hutu, indai ziyara tawuce ta wuni d'aya basa zuwanta.

Haka suka kwana Aysha na kwakume da mama har asubahi, bayan sunyi sallar Asuba gwaggo bintu tashigo tace Aysha tashirya dan sotake su Isa da wuri.
Itadai mama batace uffanba, tana zaune tana lazimi, Aysha tamik'e tana shiri tana kuka, gwaggo bintu kam tafita tanamai ta6e bakinta.


*6:30am*
Aysha tashiga d'akin Umma (abokiyar zaman mama), Umma nazaune afalo tana waya Aysha tashigo ta zauna ak'asa tana sharar kwallah.
Ganin haka Umma takatse wayar tata, takamo hannun Aysha tamik'e, kusada ita ta zaunar da'ita tareda rungumeta, ALLAH Sarki shatu d'iyar albarka, kiyi hak'uri kinji, yazamuyi, haka ALLAH ya tsaramana rabuwa daku badan mun shiryaba, inamiki fatan Alkhairi kinji, kibar kuka tunda kinga nanda wata 1 ma zaku zo bikinsu Hafsat, insha ALLAH zamu kasance masu muku Addu'a aduk inda kuka tsinci kanku, amma kirik'e addininki, kada kiyarda kiyi sakaci dashi, banda biyema shed'anun mutane, kitsare mutuncinki kikula da kanki kinji, ALLAH yabamu hak'urin rashin juna, ALLAH yajik'an Malam.
Sosai Aysha taji dad'in nasihar Umma, Dan tana kallontane tamkar mama, tanajin dad'in yanda Umma da mama ke zaman lfy, tunda take bata ta6ajin sunyi fad'aba, ko kuma habaici irinna kishiyoyi.
Gwaggo bintu ce shigo tana fad'in yaya barirah barta mutafi hakanan, nikam ina mamakin son 'ya'ya irin naku, yakamata dai kusama zukatanku salama.
Umma batace komaiba, Dan tasan bak'ar magana gwaggo bintu tafad'a mata, kuma idan dasabo sun sabaji, Dan kokad'an gwaggo bintu batada kirki, (irin dangin mijinnanne masu d'aukar matan 'yan uwansu da zafi).
Sudukansu ba k'aunarsu takeba, saidai tafi nuna k'iyayyarta ga Maman Aysha, kasancewar Maman Aysha tanada zafi, bata barin saita kwana, Dan bata ragama gwaggo bintu kokad'an.
sunaji suna gani gwaggo bintu tad'auke Aysha suka tafi.
Kukakam sunshashi, barema sa'adiyya da Rufaida, wad'anda suka kasance kusan sa'anni, amma yazasuyi an rabasu da 'yar uwarsu.
Mama kam k'in fitowama tayi daga d'akinta harsu Aysha suka tafi.




*_ABUJA_*

K'arfe 12:30 a garin Abuja tayi musu, tunda sukataho Aysha tanata barcinta, bayan tagama shan uban kuka, kokad'an gwaggo bintu batace mata uffanba barema ta lalasheta, sun tsaya awata tasha wadda Aysha batasan inaneba, daganan suka shiga wata taxi wadda tatsinkayi maganar gwaggo bintu tana fad'in akaisu mai-tama.

Tafiyar dabata wuce 47mnts ba takawosu wata katafariyar anguwa, mai k'yawun gaske, wadda aka k'awata da manyan gidaje na alfarma, tun ahanya Aysha taketa yaba k'yawun birnin na Abuja, aganintama yanda ake fad'arsa yaci uban haka k'yau, Dan wlhy kamar ba 9ja ba.
Tunanin Aysha baikuma tainkewaba saida suka kutsa kai cikin gida mai k'aton bak'in gate, Wanda ba'a bud'e musuba saida mai gadi yatabbatar dasu waye, ganin gwaggo bintu yasashi washe baki tareda bud'e musu k'ofar.
Mai gadi yace, "Maman yara kece yanzu da rana tsaka?.
Wlhy kuwa d'an gwari nice, nasameku lfy?.
Lfy lau, yak'arin hak'urinku?.
To sai godiyar ALLAH, d'an gwari, bara muk'arasa ciki, namaji gidan tsit ko lfy?.
A lfy lau, kinsan yara suna makaranta, samarin gidanma duk sunfice wajen aiki, wasu kuma makaranta. Hajiya babba ma tana wajen aiki.
Sanin shegen surutun d'an gwari yasa Gwaggo bintu katseshi dafad'in to ALLAH yadawo dasu lfy bara muk'arasa muhuta.
Har sun fara tafiya d'an gwari yace, "Maman yara! Ina kuma kika samo mana wannan mai k'yau d'in haka?.
Cikin k'osawa da surutunsa tace, " d'iya tace. Batajira amsarsaba tacigaba da tafiya, ganin haka yasa Aysha tacigaba da binta abaya.
Masha ALLAH!, Aysha tafirta ahankali Dan ganin wani katafaren falo mai kamada gari guda, iya had'uwa falon yahad'u, ank'awatashi da kujeru sets uku akowace kusurwa, set d'aya jajaye, d'anyan farare, d'ayan bak'ak'e, kowanne 6angare kuma akwai kayan kallo, sai can gefe ankafa dogon tebir mai d'aukeda kujeru rututu, aranta tace kaji wani dinning saikace tebirin taro.
Babu kowa afalon, sai sassanyan k'amshi dake tashi acikinsa, Dan ko'ina tsaf yake, kuma k'al-k'al, babu wutar lantarki, wannan yasa akad'an d'aga wasu daga cikin labulolin falon hasken rana yashigo, dukda kuwa a gefen danning akwai wani dogon gilas fari tas da'aka k'awata wajen dashi, hakanne yak'arama falon k'awataccen haske mai cika idanu.....
Jin an mangareta yasata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin, gwaggo bintu ce ta watsa mata harara amma batace komaiba, sai yanzu Aysha tafarga da matar dake tsaye cikin shiga ta alfarma, bazata wuce shekaru 53 ba aduniya, saidai yanayin jikin k'iba datake dashi yak'ara mata yawan shekaru da girma, durk'ushewa Aysha tayi awajen tana gaisheta.
A d'an yatsine ta amsa, saidai bata d'aure musu fuskaba, amma dukda haka Aysha taji babu dad'i.
Maganar gwaggo bintu taja hankalin Aysha, cikin muryar ladabi gwaggo bintu ke fad'in hajiya ga d'iyatanan nazo da ita danta d'an ringa taimakona dawasu ayyukan saboda girma dake k'ara saukamin.
Yayi.
kaiwai hajiya tafad'a, sannan tagyara zaman Jakarta tana fad'in nawuce aiki saina dawo.
Kai gwaggo bintu ta jinjina tana mata addu'ar dawowa lfy.
Jikin Aysha yayi sanyi sosai, Dan yau taga wulak'anci irinna masu kud'i da'ake fad'a, ko kad'an batason dizgi arayuwarta, saima abinda yafi firgitata shine furicin gwaggo bintu datace wai tataho daita danta tayata aiki. Kenan aikatau aka taho da'ita tayi?, gabantane yayi mummunar fad'uwa, da sauri tace kai ALLAH ya kiyaye, nida gatana nazama 'yar aiki? Ina bahaka baneba, banji zance daidaibane.
Jan hannunta gwaggo bintu tayi suka nufi wajen dining table, wata k'ofa daked'an gefe ta Gila's suka nufa, gwaggo bintu ta danna wani green d'in Abu k'ofar tabud'e, wani k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'a yadoki hancinansu, mutanene ak'alla sunkai hud'u a kichin d'in.
Kusan atare sukace lale marhabin da Maman yara, baki sosai gwaggo bintu ta washe tareda musu sannu da aiki, tak'arasa gaban wata k'yak'yk'yawar mace, fara tas da'ita, itama tanada d'an jiki, amma matar d'azu tafita k'iba, ita kuma wannan kamar zatafi ta d'azun shekaru, Dan zatakai ak'alla 48year's aduniya, saidai k'yawunta da kwarjininta sun 6oye yawan shekarunta, (aganina harda jin dad'ima) tana sanye da doguwar riga bak'a wadda tak'awatu da adon fararen duwatsu, tayi rolling d'ankwalin rigar a kanta, bak'aramin k'yau tayiba kuwa, kaikace tafito daga jinsin larabawane.
Durk'usawa gwaggo bintu tayi yanzuma, cikin nuna girmamawa tace hajiya ina yini? Munsameku lfy?.
Fuskarta d'aukeda murmushi tace lfy lau Alhmdllh Maman yara, yak'arin hak'uri kuma? ALLAH yagafarta masa.
Ameen yarabbi hajiya, ya yaran?.
Duk suna lfy. Kowa yana makaranta.
Aysha dake durk'ushe itama tace inayini?.
Kallonta sosai hajiya tayi, haka kawai taji girarta tadama ta harba, hakama k'irjinta saida yad'an buga, ahankali tafirta "innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un". Sannan ta amsama Aysha gaisuwarta, har yanzu idonta nakan Ayshar, tace Maman yara wannanfa?.
d'iya tace Aunty Amarya, tawajen mai rasuwarce nataho da ita.
ALLAH sarki 'yanmata ya sunanki?.
Kan Aysha ak'asa tace, "A'ISHA!".
Masha ALLAH Ayshatu humairah, yahak'urin rashin mahaifi?.
Idon Aysha taf da kwallah tace, " Alhamdllh mama.
Aunty Amarya taji dad'in sunan da Aysha takirata dashi, tace ALLAH yagafarta masa, yabaku hak'urin rashinsa kinji.
Kowa a kichin d'in ya amsa da amin.
Bayan gwaggo bintu tagama gaisawa da sauran mutanen sukaimata gaisuwa, Aysha dai kuka yahanata gaidasu.
Kulada kukan datakeyi hajiya tace, "Maman yara kushiga cikin Ku huta kafin muk'arasa girki, yau mun makarane wlhy.
Da girmamawa gwaggo bintu ta amsa tareda Jan hannun Aysha suka fita.
Binsu da kallo hajiya tayi, wani tausayin Aysha da k'aunarta suka tsarga zuciyarta lokaci d'aya, haka kawai yarinyar tashiga ranta, (amma saita alak'anta hakan da tausayinta na maraici).


Nace humm anya kuwa Hajiya?.๐Ÿค”

Daga nana fita suka kumayi daga falon gaba d'aya zuwa

2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment