Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake, kuma bataga bishirah ba.
To Aysha wakike ganin zaki tambaya batareda ya zargi komaiba?.
Tab aikam hakan zai zama Matsala, danni bansan mi mama keson ganowaba, jiyafa titsiyeni tayi damuka kwanta.
Tofa, saifa munlura sosai, Dan inhar suka gano dakansu za'a wargaza mana aiki. Kiyi k'ok'ari Sanin Inda gwaggo bintu take ko bishirah, sune kawai murfin rife sirrinmu, Dan su hajia babba hatsibi baine.
Karki damu zan k'ara himma insha ALLAH, k'arfe NAWA zaku wuce birnin Shehu?.
Saida yamma ma, zamubi jirgin 5pm ne.
OK zankiraki, ammafa dole musake secret numbers, wasu zasu iyamana bincike a wayoyi su wargaza mana aikinmu Anty meerah.
Nima nayi tunanin haka Aysha, amma kibari mudawo daga soskot.......
Motsin dataji abayantane yasakata saurin kashe wayar, tajuyo da sauri, gabantane yafad'i Dan ganinsa tsaye abayanta, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa Na bak'in jins, yanda yakafeta da mayun idon nan nasane yasakata aro sabuwar nutsuwa ta yafama kanta, sannan ta had'e fuska tareda kauda kai daga kallonsa.
Mamaki tabasa, yarinyar abubuwanta sunfara bashi tsoro, kullum da Sabon salo zaka ganta, yaukuma a sahun munafunci yaganta, yo idanba munafinciba mizai kawota k'arshen garden yin waya? Duk yawan d'akunan gidan.
Ra6awa tayi tagefensa zata wuce yace, "k!.
Shiru tamasa tacigaba da tafiyarta.
Tsawar daya Daka matace tasakata tsayawa cak, bak'aramin wakitawa y'an hanjinta sukayiba, damacan dauriya takeyi, Dan atsorace take da tunanin koya ji mitake fad'ane, dama akuma kamar yana mata zargin wani Abu daban, tunda ranarma ya tambayeta ko an turota lek'en asirinsane?, hawaye suka cika mata idanu, amma tayi jarumtar tsaidasu.
Batasan yak'araso Inda takeba, saida alamun tsayuwarsa taji kusada ita, wannan yasakata d'an d'agowa tasaci kallonsa, idanunsa k'yam akanta, ahankali ta janye NATA tareda lumshesu.
Shima saiya kauda Kansa daga kallonta yana furzar da huci abakinsa.
Baki yabud'e zaiyi magana wayarsa data fara wringing takatsesa.
Cirota yayi daga aljihun wandonsa yakara akunne.
Hello Youseef miya farune?.
J! Kana inane?.
Ina gida mana, miya faru kake magana akid'ime haka?.
J! Kayi sauri, ina k'auyen Dutsen Alhaji, nabiyo bayan Barau modibbo ne, please kayi Sauri.

What!!, barau modibbo fa?.
Kasan mikake fad'ama? da gaske kakeyi kuwa?.
Wlhy da gaske nakeyi j!, tundaga airport nake binsa, naje raka Abbah zai tafi Egypt ne, naga Barau modibbo ya sauka a jirgin dayazo daga Spain.
OK OK ina zuwa, kakira su Ema.... Kace muhad'u acan, basai sunzo d'aukataba zanje dakaina.
Da sauri ya kalli Aysha dake tsaye har yanzu tana sauraren wayar tasa, please maza d'akina cikin drowan gefen gado ki d'akkomin bindiga da key d'in mota, maza da sauri.
Yama manta waya aika, saboda akid'ime yake.

Hajia babba dake k'ok'arin shigowa garden d'in tatsaya cak, jin wayar da ya khaleel keyi tayi mugun kid'imata, ta maimaita sunan cikin matuk'ar razana, *BARAU MODIBBO!!* lallai yau k'arya zata k'are musu, umarnin dataji yana bama Aysha ne yasakata juyawa da sauri 6angarenta, akid'ime tad'auki waya tashige bedroom d'inta, harda kullewa, wayar hajia Khaltum takira, number busy.
Tasaki wani irin tsaki, jikinta har rawa yakeyi.
A hanzarce Aysha tadawo d'aukeda guns guda biyu, ta lullu6esu dawani hanky d'insa gudun kada wani yaganta.
A harabar gidan ta isakeshi yana yaye tamfol da aka lullu6e dawata azababbiyar mota mai k'yau da tsari.
Ya kar6a cikin hanzari, yashige motar, aguje yafigeta, ganin haka d'an gwari yabud'e gate da sauri.

Bak'aramar kid'ima hajia babba tayiba, saboda tana hangen fitar figa da ya khaleel yayi saga gidan ta window d'in d'akinta, gumine yashiga karyo mata.
Hannunta Na rawa takuma kiran number hajia khaltum.
Yanzun kan ta sameta, tana d'agawa tace aminiya k'aryarmu ta k'are.
Kamarya aminiya? Miya kawo maganarnan?.
Ibraheem sun d'anama Barau modibbo tarko, kuma kinsan kamashi tamkar muma an kamamune, Dan bamuda wani sirri Wanda yawuce Barau modibbo.
Bak'aramin wuntsilawa y'an hanjin cikin hajia khaltum sukayiba, tunda taji bayanin Aminiyar tata.
Itama kanta zufar ke keto mata, muryarta Na rawa tace Aminiya mun d'ebo ruwan dafa kanmu, lallai yau naga sharrin d'an kunama.πŸ¦‚
Bata jira amsar hajia babba ba tayanke wayar, tareda fara Neman layin Barau modibbo.


___________

Aysha Na tsaye inda ya khaleel yabarta tamkar gunki taji wayarta Na wringing, dubawa tayi saitaga mama.
Batareda tad'agaba ta nufi cikin gidan.
A d'aki ta iske mama da yaya fadeelah, mama tana sakama ummuhanee kaya, fadeela kuma Na d'aura d'an kwalinta.
Mama tad'ago tana kallon Aysha data shigo sukuku, ke lfyarki kuwa?.
Babu komai mama, Aysha tafad'a da sauri.
Ido mamar ta tsura mata, kimsan banason k'arya dai.
Kamar Aysha zatayi kuka tace, "mama ya khaleel ne".
Khaleel kuma? Miya faru dashi?.
Babu komaifa, naga ankirashi awayane, ya d'auki bindugu yafita akid'ime, wlhy tausayi yabani, inajin tsoro, tak'arashe maganar da matso kwalla.
Murmushi mama tayi, danta gano wani Abu tartare fa ayshar, tacigaba da sakama ummuhanee kayan tana fad'in to kimasa addu'a, ALLAH ya tsaresa, insha ALLAH babu abinda zai samesa, aikinsane yazo da hakan.
Kai Aysha tad'aga kamar zata rushe da Kuka.
Mama tace jeki shirya zakuje dubiya asibiti.
Da to Aysha ta amsa, tashiga bayi tad'an wanko fuskarta tafito, bak'ar doguwar Riga mama tabata.
Badan taso sakawarba tasaka, Dan Rabin hankalinta yana kan ya khaleel, jitake kamar tayi tsuntsuwa tabisa, komai yafaru a gaban idonta.
Fadeelah takar6i d'an kwalin rigar ta nad'a mata, kaikace wata balarabiya ce, dukda batayi kwalliyaba, farar fauda kawai tashafa kad'an sai kwalli.
Mama tabasu kud'i tace su sayi kayan marmari a hanya, suje ga Ramadan can yana jiransu a waje.
Har zasu fita, Aysha tace mama wai wama zamuje dubawa?.
Kuje mana, aii zaku gani, Ramadan yana jirankufa, zaitafi aikine narok'esa ya ajiyeku tunda asibitin yake, kukuma bakusan asibitinba.
To mama saimun dawo.
Adawo lfy mama tafad'a tana mik'ewa, jikinaba, a cikeda tunanin yanayin Ayshar, afili tace Aysha dama kin fidda khaleel aranki, babu yanda za'ayi gudan jinina yahad'u da gudan jinin hajia laurah, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan, dama cikin y'ay'an Bilkeesu ne tabbas Dana amince miki, amma d'an hajia laurah bazai ta6a Auren y'arda tafito daga tsokar jikinabaπŸ€• wannan ALWASHI neπŸ‘‰πŸ».


Afalo suka iske ya Ramadan yana jiransu, ganin sun fito yamik'e, yauwa kumuje karna makara ko, yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
Fita sukayi har bakin motarsa, fadeelah tashiga baya, dole Aysha tashiga gaba, shima ya zauna a mazauninsa yaja motar suka fice.
Saida yatsaya wajen saida kayan fruits kamar yanda fadeelah tarok'a, dakansa yafita yasayo komai da'ake buk'ata da kud'insa, sannan yadawo suka cigaba da tafiya.


________________
Neman duniya hajia khaltum takasa samun Barau modibbo, takira wani makusancin yaronsama yak'i d'auka, bak'aramin tashin hankali takuma shigaba, sai kai kawo takeyi tsakanin falonta da bedroom, ga zufa dake ketowa adukkan sassan jikinta, tasan wanene Ibraheem Abdallah, takuma San mizai iyayi, wlhy kasancewar mahaifiyarsa a wannan lamarin bazai ta6a d'aga musu k'afaba, tabbas bayyanarsu a wannan harkar itada mahaifiyarsa tamkar bayyanar wani tone-tone ne agaresu, dolene Ayi *Walk'iya* kowama yagansu, wata gudawace taji tazo mata babu shiri, dagudu tanufi bayi.
Tana gudawa tana turama Barau modibbo massage a wayarsa.



______________
Duk yanda youseef kemasa kwatance haka yabi, har ya isa cikin dutsen Alhaji, a can k'arshen gari gidan Na Barau modibbo yake, shikad'ai, tamkar gidan mayu, dagani kasan wannan gidansane Na sirri, babu Wanda yasan dashi.
Rigar makarin bullet Adams yabashi yasaka, yakuma d'urama bindigarsa bullet, saida yacikasu fam sannan suka zagaye gidan, kuwa tafiya yakeyi cikin sand'a, idan and'an tafi sai a tsaya ana sauraren ko akwai Wanda yafito, dahaka har wasunsu suka sami damar shigewa ainahin cikin gidan.
Cikin sand'a ya khaleel yabi tabayan wani mazgegen k'ato dake tsaye da bindiga AK 47 ahannu, bakimsa yay saurin toshewa da hannunsa ya murd'e wuyansa, jikake k'ak'assss!!!!! Ya karya Wuyan, yajefar dashi awajen tim, sannan yakuma rik'e bindigarsa cikeda kula, yana tafiya cikin sand'a.
Wani yakuma hangowa agabansa, yay saurin janyo buhun ledar dake kan wani dirom a tsakar gidan, tafiya yake cikin sand'a yana bin bango, harya kai inda yake, da sauri ya kunshe kamsa acikin buhun ya kulle, buge buge yafara saboda rashin fitar numfashi, ya khaleel yakuma murd'a bakin bukun, bai sakiba saida yaga jikin mutumin yasaki alamar ya mutu sannan ya hankad'ashi ya daki bango.
Wani icce yad'auka ya mazgama Wanda ke tsaye bakin k'ofar a kai, da sauri yazube awajen tareda sakin razananniyar k'ara, wannan ne yasaka su Barau modibbo farga da abinda ke faruwa....


_______________
Su Aysha sun isa asibitin, har d'akin da gwaggo bintu take kwance, da bishirah Aysha tafara cin karo, wata iriyar zabura tayi da zare ido waje, tayi saurin kai dubanta ga gwaggo bintu dake kwance bisa gadon.
Cikin muguwar fad'uwar gaba gwaggo bintu take kallon Aysha, dukda batada tabbacin itad'ince ko ba ita bace, Dan Aysha ta canja sosai...............✍






_to masu karatu, idanfa kereπŸ‘ Na yawo zamoπŸ‡na yawo wataran za'a had'u._

*yau dai ga Aysha ga kuma gwaggo bintu, shin mikuke tunanin zai farune?.*

*ga ya khaleel can zai damk'i ogan su hajia babba, mikuke tsammanin zai biyo baya?.*

*mama Na zargin gwaggo bintu, kuma tanada burin bincikenta akan wanda yafidda Aysha k'asar waje karatu, kunga koda Aysha tayi yunk'urin 6oyewa mamafa zata tono, yakuke ganin za'a kwashe?.*

*ya maganar auren Aleeya da ya khaleel? Kunsan dai ya khaleel ya d'aukama mama alk'awarin amincewa, aganinku babu lauje cikin nad'i akan had'in auren Aleeya da ya khaleel?, kuyi nazari, gakuma baffah yayi wani furuci akan auren ya khaleel d'in, shin shikuma wacece za6insa? Dan nasan ba shirinsu d'aya da hajia babba ba, kuna ganin hajia babba zata yadda?, kokuwa baffah zaiyi hak'uri danasa za6in?, ko za'a had'a masa sune suduka?, towama baffan zai za6ama ya khaleel?.*

*mi Aysha da meerah suke shiryawa su gwaggo bintu?, tabbas akwai 6oyayyen tarko dasuke shirya musu, to amma nami? Kuma zasu sami nasara?.*


*ya maganar soyayyar da Aysha kema ya khaleel?, ga mama ta d'auki alwashi akan hakan, shin burin Aysha zai cika kuwa?.*



_kutttt cakwakiya nacikin *CIKI DA GASKIYA* part 2, karku bari abaku labari, zaizo muku da abubuwan mamaki, soyayya mai k'ayatarwa, k'aryar wasu zata k'are, gad'an Karen tone-tone, za'ayi WALK'IYA fa, kuma zamuga kowa, hardama wad'anda bakuyi tunaniba, akwai abubuwan al'ajabi, mamaki, tsoro, k'ayatarwa, kai hardama naban haushi._

Kudai kawai Ku kasance da Bilkeesa Ibraheem Musa, (bilyn Andull) danjin yanda zata kaya.

Marubuciyar...

_Rashin Sani!!._
_Auren k'addara ko biyyaya?._
_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?._
_Ni da aminayata!!_
_Nawaff!!._
_Sabon al'amaree!!_
_Kukan kurciya....!!_
_Ban saketa ba!!_
_Abdul-maleek bobo!!_
_Karayar arzeek'i!!_
_Sanadin bikin sallah!!_
_Ciki da gaskiya...!!_

Wanda bai karantaba yanema akasuwar online🀣😘😜



K'ak'ak'ak'a, wata rikita rikita sai a CIKI DA GASKIYA part 2, yana nan tafe nan kusa kad'an.










*_CIKI DA GAAKIYA!!.... (wuk'a bats hudashi), kashi Na biyu._*

*COMING SOON!!!!!.*




Ngd sosai masoya, ina alfahari daku, ina k'aunarku, inayinku 100%, karku gaji, kukasance dani a part 2❀❀❀❀❀😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘.



K'aunarku dabance a zuciyar bilyn AbdulπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€saikun jini.πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ».

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment