Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tad'auketa takaita wajaje daban-daban, dukdan ta d'ebe mata kewar gida dana 'yan uwa.


Baramu lek'a Nijeria kuma.
Amma zanbar xoxo a UK kawai๐Ÿ˜œ



*_Nigeria_*

Baffah ya sanarma Ammah zancen fad'ima, bak'armin farinciki Ammah tayiba kam, Dan shikansa baffan yayi mamakin yanda Ammah ta nuna murnarta sosai.
Takumace karyaji komai ita zata sanarma matansa.
Bikinsu fadeelah ma da ita za'ayishi.
Yaji dad'in kalamanta kam, dan haka yafara shirye-shirye abinsa.

Baffah shiri babu amincewar amarya๐Ÿ˜‚.



*_Kano_*

Tunda mama suka dawo daga Jigawa abubuwa dayawa suke caccakar mata rai, amma saita d'ebesu tawatsar baya saboda shirin bikinsu Fadeelah dayaketa kawo jiki.
Shiri akeyi sosai, Dan kawu bilyamin da kawu Ahmad suna k'ok'ari, tamkar Malam Abubakar mahaifin su Aysha nadarai.
Amare Hafsat & fadeela kam aii ba'a magana.
Sunata shan gyara wajen gwaggo Asma'u, Dan kusan sati biyu kenan tad'aukesu suna wajenta a katsina.


_____________________________
Zaune suke awajen shak'atawar, wajene had'ad'd'e Wanda akayishi Dan hutawa kawai, yaran turawa da iyayensu kowa nata uzurinsa awajen, bak'ak'en fata d'ai-d'ai sukan gitta.
Meerah sanye take da wandon jins bak'i tad'ora wata farar Riga mai santsi, sai jibgegiyar rigar sanyi ja data saka a sama, takawo siririn gyale tarufe kanta dashi, tayi k'yau sosai masha ALLAH.
Aysha kam Na sanye da wando da Riga itama, Jan wando da yellow d'in Riga, tasaka pink d'in rigar sanyi Asama, bata saka d'ankwaliba, saidai taja hular rigar sanyin har saman kanta, takalminta mai igiya yellow yayima k'afarta k'yau ainun, zagaye wajen sukeyi anutse suna 'Yar hirarsu cikin harshen Hausa.
Aysha tsaya tareda rik'e k'ugunta tana dad'in wash Anty meerah, ALLAH nagaji over.
Matashin saurayi bak'in fata dake zaune bisa kujera yana karatun wani story book yad'ago da sauri danjin yarensa a inda baiyi zatoba.
Kallon Aysha da meerah yakeyi cikeda mamaki.
Meerah tayi dariya, to raguwa zomu k'arasa can muzauna kihuta.
Binsu yayi da kallo harsuka zauna, yasauke ajiyar zuciya yana maida kansa ga karatunsa, amma saidai yakasa hakan.
Tsam yamik'e yanufi indasu Aysha kezaune sunacin popcorn๐Ÿฟ...........๐Ÿ–Š


*_tofa masu karatu, kowaye wanan?._*๐Ÿค”

Kubiyo mata agidan Abdus'salam kawai๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐ŸŒน








*_inayinku yasin๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜_*โœŒ๐Ÿป

[8/11, 4:23 PM] Aisha Galadima: *_Typing๐Ÿ“ฒ_*



๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_



*_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*๐Ÿ˜œ


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿ˜ญ



*_part 1_*
(littafi na d'aya๐Ÿ“•)


_su tawan anji dad'in UK anmak'ale acan, waibazata dawoba sai Aysha tagama karatu๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ_
*_Miss Xoxo a UK_*
Maisak'o yakawo nakai mata.๐Ÿ˜‚โœŒ๐Ÿป


2โƒฃ4โƒฃ

Assalamu alaikum 'yan mata.

Atare suka d'ago kai, cikin tsantsar mamaki suke kallonsa, Dan basu ta6a tunanin jin yarensu abakinsaba.
Ya d'age gira sama tareda fad'in Ku amsa mana.
Aysha Ce tayi k'arfin halin amsashi.
Amma meerah har yanzu baki bud'e take kallonsa.
Shimad'in hankalinsa Na kanta, yace zan iya zama?.
Yanzuma Aysha Ce tabashi amsa cikin gyad'a kanta.
Zama yayi bisa kujerar dake kallonsu, kuyi hak'uri idan natakura mukufa.
Sai sanan meerah tasami bakin magana, a'a babu takura, sai daifa.........
Kinyi mamakin jin nayi Hausa ko?.
Yak'arasa mata maganar cikin murmushi.
Kanta tagyad'a masa.
Yayi 'Yar dariyar basarwa tareda mik'a hannu yad'ebi popcorn d'in cinyar Aysha, yakai bakinsa yana fad'in dukda ba'amin tayiba kam.
Sorry uncle, Aysha tafad'a tana langa6e kai.
Murmushi yamata, thanks my lil sister.
Yamaida kallonsa wajen meerah.
Anty meerah koba'ayi maraba dani baneba?.
A'a, kayi hak'uri, mamakine kawai dai nakeyi.
Karkiyi mamaki akaina, sunan Naufal yahaya Zubair, d'an asalin k'asar Nigeria, amma haihuwar Canada, babana d'an Nigeria, Mamana 'Yar Canada, so nayi rayuwar Nigeria sosai shiyyasa na'iya Hausa, yanzu haka mom & dad, brothers-Sisters d'ina duk suna Canada, aikine Na wattani 6 yakawoni nan Georgetown.
Yak'are maganar da d'age gira sama.
Murmushi sukayi suduka.
Yace, "friends nawafa?".
Meerah tad'an murmusa, mukam labarin namu bashida tushen dazakayi sha'awar jinsa.
Ko? To shikenan, nabada uzuri, afad'amin suna.
Ameerah & Aysha.
Nice names drillings.
Hira sosai yake musu, harsuka saki jiki dashi, Dan Naufal yanada saurin sabo kam.
Shine yakaisu har gida, bayan uwar sayayya daya narka musu.
Anty glo...... Sai Murna take meerah tayo babban kamu.



Nace hummm.


____________________________
Biki kam ya kankama, bak'i suncika gidansu Aysha, sai hidimomi akeyi.
Gida yagama d'inkewa kasancewar gobene d'aurin aure.
Washe gari wajen 10am babu zato saigasu Anty Mamie akano, hardasu inna 'yan jigawa.
Mama rasa wane irin farinciki zatayi tayi, saikawai tarungume Anty Mamie suka saka kuka atare.
Nanfa akaita lallashinsu daban magana.
Duk wani ainan ainan da aunty Mamie akaita yinsa.
Hakama Amal, Hamdiyya, Naseeba, Shuhuda sunshige cikinsu Fadeela amare anata abubuwan arzik'i dasu.
Gabda d'aurin aure gayyar matasan gidan suka iso, ya khaleel ne kawai babu, danyana kasar Algeria tun jiya.

Bayan an d'aura aure, Anty Mamie tace mama taje falon Abbansu Aysha ana kiranta.
Bata kawo komai arantaba tatashi tafita.
Sanye take da jar atanfa mai ratsin brown d'in zane, tamata matuk'ar kyau, kasancewar mama batada k'iba kuma batawani haihu da yawaba sai shekarunta suka 6uya sosai, tana nan k'yak'yk'yawarta fara tas.

Da sallama tashiga falon, k'amshin turarensa yafara mata sallama, cikin dakiya tashiga, amma ganinsa saiya sakata fad'uwar gaba, (waimi Alhaji Abdallah keso da'itane?)
Idonsa akanta yace, "kiyi hak'uri fad'ima ki k'araso ciki".
Kamar zata juya saikuma tadawo tashiga, kobabu komai hidimarta yahalarta shida iyalansa. Baikamata ta wulak'antasaba.
Zama tayi kujerar dake nesa dashi, kanta ak'asa tace ina yini, anzo lfy.
Murmushi yayi, haryanzu Fad'imarsa Na nan bata sauyaba, mace mai zafi da sauk'inkai.
Ya amsa mata gaisuwa tareda murnar aurensu fadeelah, yad'ora damata gaisuwar mijinsu.
Daganan shiru yabiyo baya.
Ganin haka mama tamik'e tana fad'in mungodefa, ALLAH ya maidaku gida lfy.
Da sauri yakatseta, sorry inaso muyi magana.
Komawa tayi tazauna, saidai yanayinta yacanja kam.
Ganin haka shima saiyaci serious.
Fad'ima nasan haryanzu abinda yafaru abaya yanasaki jin haushina, amma ina so kigane cewa k'addarace da rabon haihuwar wad'annan 'ya'yan, wani baya haihuwar d'an wani, ALLAH ya rubuto saikinzo kin haifesu anan, amma inaso kisan haryanzu kina cikin ruhin Abdallah Rufa'ee. Muba yara baneba, baikamata muzauna zancen yaraba, ina rok'onki arzik'i kidawo d'akinki, amatsayin matata, kenafaso aduniya, kuma har yanzu inasonki.

Bak'aramar razana maganarshi tasaka mamaba, muryarta narawa tace anya kasan mikake fad'a kuwa?.
Nasani fad'ima, yardarki kawai nake buk'ata, wlhy inhar kin amince ayau d'inan za'a maida aurenmu.
Zumbur mama tamik'e, cikin fusata tace, ban aminceba, bakuma zanta6a amincewarba, wanan maganar tatsaya iya ni da kai, Dan banaso takawo 6acinran mutane dayawa.
Tana gama fad'a tafice daga falon.
Baffah yadafe kansa dake sara masa, ahankali yafurta fad'ima ki canja mana, wlhy dolene ki amince da buk'atata koda yardarki ko babu.


Nikam nace baffah Ashe kai ya khaleel yabiyo jarumta๐Ÿ˜‚.
Magani to kaida hajia mama wakeda nasara๐Ÿคฃ.


_____________________________
Sabo sosai yashiga tsakanin Naufal dasu Aysha, yanzukam Aysha tasamu Uncle, sosai takejinsa matsayin d'an uwa, shima hakan take agareshi, yarik'e Aysha da meerah tamkar 'yan uwansa dukda haryanzu baisan komai akansuba.
Sosai Aysha take maida ahankali akan karatunta, k'awance itada Ariana kam kullum k'ara dank'o yakeyi, ga uncle d'inta da Anty meerah suna bata kulawa sosai, tazama 'Yar gata, jinta yakeyi kamar tana tareda su mama, agefe d'aya kuma son ya khaleel nata kuma sakin jijiya da rassa azuciyarta, ita kanta har mamaki lamarin ke bata, idan kuma tatuna shid'in jinin hajia babba ne sai tsoro yakamata.
Saidai tanata gayama ALLAH, Dan sosai bata wasa da ibada, har azumin litinin da alhamis yitake abinta. Wanan yake k'arama meerah k'arfin guywa itama, akoda yaushe take kara tubarma ALLAH 6arnar data aikata, tanakuma nemawa mahaifiyarta shiriya itama, shiyyasa take kara k'aunar Aysha aranta, domin itace silar komai.

Dawowarta kenan daga school taci karo da motar ya Naufal, k'arasawa tayi wajen motar tana washe baki.
Shima tundaga nesa yake hangota, Dan haka yabud'e motar yafito.
Ya Naufal lfy naganka kai 1? Ina aunty d'in?.
Murmushi yayi tareda fad'in no lil sholy yanzu tashiga gida zata d'akko Abu. Ya school?.
Alhmdllh ya Naufal.
Kinadai k'ok'ari ko?.
Eh wlhy inayi Yaya, insha ALLAH Sonake wanan karonma aje dani grade 3.
Eye kaga big girl, kinga daga nan sai high school kenan?.
Cikin dariya tace insha ALLAH Yaya.
Ana haka saiga meerah tafito, Aysha tarungumeta tana fad'in I miss you my sweet Anty.
Me 2 my lil sholy.

Ya Naufal yay dariya, dansuna birgeshi, kaikace ciki d'aya suka fito.
Aysha tashige gida yayinda sukuma suke binta da kallo suna murmushi, suna k'aunar yarinyar harcikin zuciyarsu, Dan ta cancanta asota akuma k'aunaceta.
Naufal yadawo da kallonsa kan meerah cikin sauke ajiyar zuciya.
Meerah nidai haryanzu ina barar jin labarinku kam, munzama d'aya amma har yanzu bansan komai akankuba.
Hum karka damu lokaci nazuwa dazaka San komai, bamu 6oye makaba Dan rashin yarda, a'a lokacine kawai baiyiba.
Naufal mutumne mai sauk'in kai, Dan haka yace o right babu damuwa, ALLAH yakaimu lokacin.
Amen meerah ta fad'a.
Daga nan fira sukacigaba dayi har Aysha tafito sanye da doguwar Riga brown ta d'ora farar rigar sanyi asama, hannunta d'aukeda robar ice-cream.

(Nace kaga 'Yar hutu๐Ÿ˜„).

La ban hanaki shan kayan sanyinnanba sholy? wai bak'ya ganin yanda mura tatasoki gabane?.
Langa6e kai Aysha tayi gefe, cikin shagwa6a tace, "sorry ya Naufal, ALLAH katanbayi Anty meerah sau d'aya kawai nakesha arana.
Kallonsa yamaida kan meerah, kekike biye mata kenan? banace kidaina saya mataba.
Hannu biyu meerah tahad'e alamar ban hak'uri, kayi hak'uri ya Naufal, ALLAH Lola Ce tasaya mata baniba, nima ganinsa kawai nayi ahannunta bayan tabata, danma kada nakwace shine takaima Lyn ajiya.
Girgiza kai Naufal yayi, yace, " zand'au mataki aii".
Ganin kamar ransa ya6aci Aysha tamik'a masa robar ice-cream d'in gabad'aya. Kayi hak'uri Yaya bazan sakeba, tayi maganar tana kama kunnuwamta.
Murmushi yayi yana fad'in promise?.
Yes my sweet Yaya promise.
Shikenan kisha wanan, amma yazama first & least, duk randa nakeson kisha zan sayo miki dakaina kinji.
Murna taitayi, tana kar6a takoma cikin gida dagudu.
Dariya Naufal da meerah sukayi, Dan sunsan haryanzu k'uruciya Na d'awauniya da ayshar, haryanzu tana 14years ne, amma gab take dashiga 15.
Sallama shima yayma meerah yatafi gida, dama daga wajen aiki yabiyo danyaga lafiyarsu.

Daga Aysha sai Serah da Queen a gidan, saikuma meerah data shigo yanzun, saurankam suna wajen shek'e ayarsu.
Besi ma anzama 'yan gari tuni, harka take da manyan guys kam.


______________________________
Ansha biki an shashshare, yanzu dagasu saisu, kowa Na mamakin rashin zuwan gwaggo bintu kuwa, gashi wayartama bata shiga gabad'aya.

Basusan tanacan tanashan wahalaba wajen Anty zuwairah ba, kokad'an yaran Anty zuwairah basuda kunya, karma Najwa da Huzaifa suji labari, sunyi mugun raina gwaggo bintu, duk wata k'urar aikinsu saisu d'auka sukai mata.
Bata isa kuma tayi maganaba su had'ata da mamarsu, Anty zuwairah kam ta balbaleta damasifa ga gori da cin mutunci.
Haka gwaggo bintu zataita sharar kwallah, gaba d'aya zaman gidan ya isheta, jitake kamarma tagudu Kano.
To amma idan taje wace amsa zata basma mama idan ta tambayi d'iyarta?.
Wanan shike tad'a mata hankali, ranar da lissafinta Yakama bikinsu Hafsat jitayi kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano, amma babu dama.


A 6angaren zancen mama da baffah kam Anty Mamie tayi iya bakin k'ok'arinta Dan mama ta fahimta amma Sam tace babu wanan maganar a tsakaninsu.
Hardai suka tafi babu wani canji daga mamar akan ra'ayin rik'au d'inta.

Wanan yasa bayan biki da kwanaki 6 baffah yazo yasami kawu bilyamin da zancen, sun tattauna sosai harda yanda zasu 6ulloma lamarin.
Wanan yasaka zuciyar baffah d'an samun sauk'i, harya Tara manyan 'ya'yansa maza yafad'a musu zai dawo da matarsa fad'ima.
Duk sunmasa addu'ar fatan alkairi, Dan ba'a musu tarbiyyar rashin fahimtar abuba, dama kuma Anty Mamie tasanar dasu komai tunkafimma suje d'aurin aure su Fadeelah.
Saidai har yanzu Uwargida sarautar mata hajia babba da Umme amarya basusan waynar da'ake toyawaba, Dan baffah ya kwakwkwafi yaran akan suyi gum dabakinsu da zancen harsai ya tabbata.

Saidai kuma kash baffah ya makaro, Dan hajia babba ta tunkaro d'akinsa aranar dayake sanarma ya khaleel daya dawo jiya zancen yashiga kunnenta.
Hummm airanar saida ta tada hankalin kowa agidankam.
Dole baffah yabar mata gidan dankarsu tafka abin kunya agaban yara.
Umme amarya kam koda tadawo taji zancen batace komaiba, Dan ita wanan baya d'aya daga cikin matsalolimta kam.

Washe gari babu Wanda yasani hajia babba da hajia khaltum suka nufi Kano Dan sun sami address d'in gidansu mama ahannun Tasleem dasuka tsare da kurari.
Tana kuka tabasu, amma tayi gum dabakinta bata sanarma Anty Mamie ba gudum kartasha fad'a, kilama harda duka Anty Mamie zata mata..............๐Ÿ–Š



Hummmm masu karatu koya zata kaya? Idan su hajia babba sun Isa Kano?.๐Ÿค”

Bara mubisu muma domin ganema idonmu๐Ÿคฅ.



Duk mai buk'atar ciki da gaskiya.... Daga farko Yaje wajen mai wannan number zai samu๐Ÿ˜‚.
08100955951







I love you all my Fan's๐Ÿค—๐Ÿค—๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜.
[8/12, 4:08 PM] Aisha Galadima: *_Typing๐Ÿ“ฒ_*



๐Ÿคฐ๐Ÿป
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{๐Ÿ”ชwuk'a bata hudashi๐Ÿ—ก}_



*_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*๐Ÿ˜œ


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
๐Ÿคฒ๐Ÿป๐Ÿ˜ญ



*_part 1_*
(littafi na d'aya๐Ÿ“•)

_Deexerh, my sweet Dee.....wanga page nakine ke kad'ai, yau sai islands uk๐Ÿ˜๐Ÿ˜._

2โƒฃ5โƒฃ

Indai Dan Maman Hafsat kika dage dak'in yarda da aurenan yakamata ki amince yanzu Maman Aysha, tunda kindaiji itama d'in tagoyi bayan kiyi aurenki.
Itama kuma inhar ta amince nid'in M. Basher yanada burin aurenta, kuma tasan zancen tunda anfad'a mata, sabodake kuma tace bata aminceba, tunda yanzu kema gashi zakiyi saikuyi hak'uri kawai kiyi. Auren shine mutuncinku, Dan Yaya Abubakar bazai ta6a dawowaba, dolene kuma yaranku saida tsawatawar namiji.
Mama ta share kwallar data cika mata idanu, nifa kawunsu aurensane bazanyiba kam, dacanma damuke da kuruciya ban zauna da uwargidansa lfy ba bare yanzu, banason yawan fitina gsky..

Kafin kawu bilyamin yace wani Abu sunji ana kwala sallama a tsakar gida.
Fitowa sukayi suduka, saidai ganin manyan hajiyoyin yasakasu tsayawa suna kallonsu da mama ki.
Itakam mama tunda taga hajia khaltum da hajia Laura ta shaidasu, wanan yasa tamaida kallonta ga kawu bilyamin tana fad'in kagani ko, wanan shine abinda nakeso kugane kaidashi kawunsu.
Wacece ita?.
Matarsace mana, kanagani tundaga Abuja tawanko k'afa harzuwa Kano sabodani.
Aii na'isa kenan, hajia babba tafad'a cikin kakkausar murya tana k'arasowa wajen mama, tanunata da yatsa tana fad'in Fad'ima! Kamar yanda gidan mijina yafi k'arfin zamanki abaya, ayanzuma wlhy yafi k'arfinki, duk aure auren Abdullah babu Wanda bataiminba sama dake, saiko waccan bak'ar dagar Bilkeesu, itama kuma gaf nake dayin maganinta, kunhad'a plan keda ita akan ki koma, hhhhhh kunyi kuskure wlhy, Dan baki Isa komawa wanan gidanba kisaka aranki!!!.

Ke kam wacce irin macece haka?.
Kawu bilyamin yay maganar wa hajia babba.
Harara ta ballamasa amma bata tankaba.
Mama tace, "kawunsu yi shirunka, aii baki yafad'a kuma dolene abashi amsa daidai dashi".
Hajia Laurah kinyi kuskuren tunanin kin Isa hana fad'ima komawa gidan Abdullahi, kema kinsan wacece fad'ima, kuma haryanzu ina nan yanda kika sanni ban canjaba, adakam kinyi nasanar raboni da gidan Abdullahi, wanan kuma k'addarace darabon haihuwar 'ya'yan da ALLAH bai k'addaro zasu zama nasaba.
amma kinsan wani Abu kuwa? adakam babu tunanin komawa gidansa ataredani kodaya buk'aci hakan, amma a yanzu kodan Na nunamiki ked'in banza a banzace zankoma.
Kishirya tarbar fad'ima amatsayin kishiya nanda sati d'aya rak Laurah.
Kuma kiyi hanzarin barinmmin gida kafin nasaka afiddaki awani yanayi.....
Hajia khaltum ta hayayyak'o cikin masifa, itakam hajia babba saidai antayama mama kallon banza takeyi.
Da sauri mama tadakatar da hajia khaltum. A'a 'Yar kore! Tsaya matsayinki, kinsanni ba hak'urine daniba yanzu saina sassa6a miki kamanni. Kama kanki tunkafin asamu matsala, kuma karku bari Na aikata abinda nafad'a muku.
Mama tai shigewarta d'akinta, su Umma da kawu bilyamin suna take mata baya.
Aifa su hajia babba sai zabga jaraba akeyi, dacin mutunci wasu mama.
Babu Wanda yasake kulasu, harsuka kai aya sukabar gidan, hajia baba arikice take da kalaman mama dantasan zata iya aikatawa, wanan kad'anne daga aikin fad'ima, adad'inma bata raga mataba Dan ita bata d'aukar raini.
Dama ajirgi sukazo, kuma ajirgin suka koma.


Mama kam kaitsaye tasanarma kawu bilyamin ta amince.
Koda yakira baffah yafad'a masa duk yanda komai yafaru sai baffah yayta farinciki. Shikam zuwan hajia Laurah yamasa rana, badan karya takalo tsiyaba dahar k'yautar kud'i zai mata, ya tabbata badan hakan tafaruba fad'ima bazata ta6a amincewaba, tunda har Ammah da inna sukai mata magana amma tabasu hak'uri.
Sun tsaida komai, ranar sati kuma za'a d'aura auren๐Ÿ˜‚.

Yeee baffah yaci nasara, is a gold! ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป is a goooooal!!!, shaku shaku is a goal! One corner is a goal!!๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป, zamusha bidiri yasin.

Team, baffah & mama๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ’ช๐Ÿป.



*_Bayan sati 1_*

Masha ALLAH an d'aura auren baffah da mama, m. Bashir da Ummah, wanan aure kam yabama mutane dayawa mama ki, amma ansaka albarka sosai aciki.
Sunce babu wani biki dazasuyi, Umma ma zatayi zamanta ne agidan, mama kuwa sai Abuja.


Agurguje please๐Ÿคง

Hajia babba tatada hankalin kowa agidan, wanan yasaka ya khaleel 6acin rai, suna dawowa daga d'aurin auren baffah yad'iba kaya kala uku yay tafiyarsa gidan Taheer.

Kwana uku kuma da d'aura auren mama tatare, sunsha kuka itada Umma, Dan Umma da matan kawu bilyamin ne sukad'ai sukamata rakkiya, sai gwaggo Asma'u da gwaggo Asubi k'anwar mama.
Sun sami tarbar arzik'i daga wajen Anty Mamie da Ammah, amma hajia babba kam lamarin sai addu'a, umme amarya kam koma ganinta basuyiba.

To mama dai tatare agidan baffah. Saimuce ALLAH yabada zaman lfy.

Keda hajia babba kam masu karatu sunci karki raga mata๐Ÿ˜‚๐Ÿค.


Masoyan hajia babba amin afuwa๐Ÿคฃ๐Ÿ™Œ๐Ÿป.



__________________________
*_Bayan wani lokaci mai nisan zango_*๐Ÿ˜ฌ


Abubuwa dayawa sunfaru awanan lokuta dasuka shud'e, masu dad'i damarasa dad'i, Na dariya dana kuka.
Aciki harda kammala karatun Aysha, tasamu sakamako mai k'yau, yanzunkam inhar tasamu dama zata wuce da karatuntane zuwa high school, (college University) saidai bamuda tabbacin hakan zai iya faruwa kam, Dan bamusan misu Anty glory ke shirya ma rayuwar ayshar ba.
Har yanzu tana nan da dagiya akan addu'a, tak'ara girma da k'yau, saboda yanayin abinci mai inganta jiki, dakuma canjin muhallin zama.
Meerah ma dai alhmdllh, matsaloli sunmata sauk'i saboda su Anty glory suna zaton soyayya takeyi da Naufal.
Itadai batacewa komai, Dan baita6a cewa yana sontaba. Amma suna samun kulawa awajensa itada Aysha, dukda kuma har yanzun baisan komai dangane dasuba. Shi azatonsama tare suke dawani nasu anan k'asar.

Tashin hankalinsu yanzukam bai wuce kwanakin aikinsa dasuka taho gangarar k'arewaba, yana shirin komawa Canada.
Abin nadamun Aysha kam, idan ta tuna ya Naufal zai barsu har kuka takeyi.
Ita kanta meerah dauriya kawai takeyi amma tana cikin damuwa, gashi takula su Anty glory sunata k'ule-k'ulle akan Aysha, amma tagaza gane namiye?.
Sosai yanzu Anty glory tamaida hankalinta wajen kula da ayshar da koya mata abubuwa kala-kala, gyaran jiki bata abubuwa Wanda meerah tasan basu dace da ayshar bama gaba d'aya.
Tarasa ina zata saka kanta danta samu hanyar ku6tar da Aysha, danta d'auki alk'awari bazata ta6a bari su Anty glory su ruguza rayuwar ayshaba kam.

Yau duk suna gida, babu Wanda yakwana a waje, kid'ane ketashi acikin gidan, kowa da harkokin dayakeyi, Aysha dai hankalinta nakan game acikin IPad d'in da Ya Naufal ya saya mata, gaba d'aya Attention d'inta yatafi ga game d'in, sai sakin murmushi takeyi saboda yanda take enjoying d'in game d'in.
Meerah sai kallonta takeyi cikin tausayawa, kokad'an bata damu da tata rayuwarba, Dan tuni tasan tazama tarihi wajen rugujewa, ta Aysha ce agabanta ayanzu.
Amma takula kuruciya tasaka Aysha shagala da mance abinda aka kawota yi, kodan saboda kulawar datake samune

2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment