Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kulafa, babban Yaya yana harararka.
Da sauri musleem yad'ago suka kuwa had'a ido da shi, ya watsa masa uwar harara, kasa dakai musleem yayi damamakin hararar, babu yanda za'ayi yace yaji maganar dayakeyi da yarinyar. Amma irin sannan uwar harara haka.
Ita Aysha ma tuni tayi gaba, harta zubama Hafiz, tana kaiwa kan mufeedah ta ajiye bowl d'in hannunta tadawo wajen zamanta.
Wani tuk'in bak'in ciki yatokare makoshin mufeedah, wai agola tazo tana nuna musu Isa, wadda in auren wuri tayi saita kusa haihuwar kamarta.
Aysha kam ko'a kwalar rigarta, dan ita duk abinda yashafi hajia babba ta tsaneshi, ya khaleel ne kawai yafita zakka acikinsu.
Kowa yagama zuba abincin baffah yay bismillah, kowa yayi aka fara break, Aysha dukata takura, sai juya cokalin takeyi, shikam wandama takeyi da shi ko'a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance, duk sanda zata d'ago saisun had'a ido da Musleem da Zunnurain, saita kuma zama atakure, tarasa wannan kallon kurullah dasuke jifanta da shi, hakadai aka kammala cin abincin kowa yafara kama gabansa Aysha bata wani ci abin kirkiba.
Itace ta biyard'in mik'ewa.
Hartaja kujerarta baya tamike tajiyo muryarsa yana fad'in dawo ki zaune.
Kowa saida yad'ago ya kalleshi, Aysha datasan da ita yake tayi kamar bata ganeba tafara tafiya, da d'an k'arfi yace Aee'sha dake nake.
Yanda yakira sunan saida tsigar jikin Aysha yatashi, kowa kuma kallonsu kawai yakeyi, babu Wanda yasaka baki.
Dawowa ayshar tayi ta zauna, yad'ago suka had'a ido, tayi saurin janye nata, filet d'in abincinta da cup d'in shayi yanuna mata, wakika barma wanna🍡🍝?.
Kwal-kwal tayi da idanu, cikin turo baki tace nifa Na k'oshi.
Shiru yayi yacigaba dashan tea d'insa.
Mama ta dakama Aysha harara, wakike turama wannan shegen bakin? Koshi sa'ankine?.
No barni da'ita mama, tabari harna gama shan tea d'inan batayi abinda naceba taga yanda zanyi da'ita.
Anty Mamie tace a'a babana ba'ayi hakaba, Aysha zauna kici kinji, zama da yunwa bashida dad'i, INA kallonki bakici wani abincin kirkiba kam, kobak'yasonsa?.
Da sauri Aysha tace a'a Anty Mamie, to maza kici kinji.
Kai tad'aga, idonta tab da hawaye, bawai ta k'oshi baneba, har yanzu takasa sabawa da d'and'anon abincin 9ja, tafison taci snacks kawai tad'ansha Ice-cream d'inta.
Baffah dai baice komaiba sai murmushi, yatashi yabar wajen, daga haka kowa yafara zare jikinsa kafin ta shafesa shima.
Dagashi sai ita aka bari, tura abincin kawai takeyi badan dad'iba.
Saida taci mai yawa sannan ta saci kallonsa, harta fara hawaye tace ni wlhy nak'oshi, cikina zai fashe.
Banza yay mata, saida takuma maimaitawa sannan ya harareta, daga yau kikuma min rashin kunya, ALLAH saina saita wannan bakin naki, faratun banza, tashimin anan.......
Baikai karsheba tamik'e, d'an tsaki taja Wanda yasakashi d'agowa da sauri ya kalleta, ta murgud'a bakinta ahankali tace ALLAH ya isana kuma.
Da gudu tabar wajen.
Shiba gunkiba shiba butun butumiba haka Yakoma awajen, hanyar databi kawai yabi da kallon, dolensane ya saita wannan matsiwaciyar yarinyar, shi baima ta6a ganin wadda ta rainashi kamar yarinyarnanba, wai yama akayi hakan tafaru?, tunda suka fara had'uwa a Canada yarinyar nan tafara masa rashin kunya, dolene ya gyara mata zama kafin lamarin ya wuce haka, tashi yayi zuwa 6angarensu, zuciyarsa cikeda tunani matakin daya kamata yad'auka akan yarinyar.


_______________________________

Bayan su Aysha sunyi wanka mama tamusu iso zuwa wajen baffah, yana zaune afalo shida Nuredin, Noor da y'an uku.
Su Aysha sukayi sallama.
Cikin fara'a ya amsa musu, suka zauna ak'asa suna k'ara gaidashi, nanma cikeda kulawa ya amsa, ya kar6i ummuhanee yamata addu'a, to fadeelah da ankoma yakamata kuma ki koma gidan mijinki kinji, wankan yayi haka.
Kan fadeela ak'asa tace to baffah insha ALLAH.
Ya maida kallonsa kan Aysha da itama kan nata na ak'asa tana wasada zoben hannunta, Aysha ya karatun? Anyo nasara dai ko?.
Kanta tad'ago fuskarta d'aukeda murmushi, eh baffah, komai Alhmdllh, nasamu result mai k'yau, yanzu hakama bautar k'asa zanyi.
Yayi k'yau, ALLAH yayi jagora.
Mama datun d'azun bata saka bakiba tace, ''dama kin cire wannan batun aranki, babu wata bautar k'asa dazakije, kawu bilyamin yace aure zai muku, domin k ma ya jinkirta saka ranar su Rufaida, gwarama kinutsu ki fidda mijin aure.
Hawaye suka zubo a kumatun Aysha, baffah ya kalli mama ransa ad'an 6ace, haba fad'ima, miyasa zaku hanata cikar burinta?, Aysha dai d'iya tace nima, kuma ina bata goyon baya, zankira m. Bilyamin d'in muyi magana.
Muryar mama a sanyaye tace kayi hak'uri to.
Baice komaiba yamaida hankalinsa akansu Aysha, nasiha yamusu sosai dakuma nuna musu shima mahaifinsune, Duk sanda suke buk'atar Abu babu wani shamaki su sanar masa, ashirye yake damusu komiye inhar baifi k'arfinsaba.
Godiya su Aysha sukayi masa, dajin k'aunar tsohon mai mutunci dasanin darajar d'an Adam, suma suna kallon sane tamkar mahaifi, zakuma sucigaba da hakan har karshen rayuwarsu, Haka yayta jansu da hira, har suka saki jiki dashi, sund'an dad'e awajensa sannan suka fito.
Mama tace suje su gaida hajiya babba.
Saida gaban Aysha yafad'i.
Tunda suka doshi 6angaren suke jiyo dariyarsu Husnah, da alama rayuwar tamusu dad'i, koda su Aysha sukayi sallama babu Wanda ya amsa musu sallama, saboda dariya taci k'arfinsu, har itama hajia babba dariyar takeyi, kowannensu da dawani kati a hannu saikace hotuna, kuma tabbas abinda sukema dariyar kenan.
Sallamar suka k'arayi dad'an k'arfi, sai sannan Mufeeda dake kujerar kusada k'ofa taji, waygowa tayi zata amsa......amma ganin fadeelah yasakata fasawa, ta gimtse fuska.
Suma su momyn daina dariyar sukayi, kowa yaci magani, Aysha da fadeela suka durk'usa k'asa momy ina kwana? Munsameku lfy?.
Wata yatsina hajia babba tayi, cikin ko inkula tace lau.
Daga nan babu Wanda yasake tankawa, durk'uson ne ya ishi Aysha da kallon banzar da'ake musu, tad'anja tsaki tareda yunk'urin mik'ewa tsaye.
Da sauri suka kalleta suduka, gaban hajia babbane ya fad'i, sai yanzu talura da Aysha, gani take kamar ta ta6a ganinta.
Ganin yanda tadasa mata idanu yasaka Aysha kauda kai tana Neman tsarin ALLAH daga sharrinta, tareda k'arajin tsanarta azuciya.
Hasnah tace k! Ubanwa kikema tsaki?.
Kalon banza Aysha tamata ta ta6e baki, kinga Yaya fadeelah tashi muwuce kinji, Aysha tayi maganar cikeda salon tura haushi.
Da sauri hasnah tamik'e tayo kan Aysha, kam balastin, aikam yau saina sauke miki abinda ke kanki.
Murmushi Aysha tayi, Wanda ya k'ona ran Hasnar, tace ni mai saukemin kayan kaina saiya shirya y'an mata, Dan nafi k'arfin manyankima balle ke, Aysha ruwan daminace, kona wuce saina dawo, kumani k'adan garen bakin tuluce, akarni akar tulu, abarci Na 6ata ruwa.
Sak'o Na Isar ba shawarabaπŸ™…β€β™€.


🀣magana cikin magana Aysha tafad'a.

Amma babu Wanda yafuskanci zancen nata, tara6a hasnah dake tsaye tamkar gunki tafice abinta, fadeelah ma ta take mata baya, itama zuciyarta cikeda nazarin maganar k'anwar tata, Dan bata fuskanci inda zancen yadosaba..................✍














😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘.
[8/29, 6:44 PM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)

_my dear Ayusher Muh'd, gaisuwa agareki da fatan alkairi, ALLAH yabarmu tare,, alkairin ALLAH ya iso agareki k'awar arzik'i_
Bilyn Abdul na yinki wlhy 100%.
❀😍😘
Masoyan buks d'inta kuyi shiri Na musamman, Dan tana nan tafe da buk d'in mai suna *_YUSRAH!!_* kada kubari ayi babuku, karkuma kumanta da sunan.
*_YUSRAH!_*
Coming soonπŸ‘ˆπŸ»πŸ˜



3⃣9⃣

Wai nikam mikike nufi da maganarki Aysha?.
Lah babu komaifa Yaya fadelah, ganinai zasu raina mana wayo, nifa bana d'aukar raini wlhy.
Shiru fadeelah tayi bata tankaba, Dan bata aminta da kallon da hajia babba kema Aysha ba.
Haka kawai takejin aranta akwai lauje cikin nad'i.



_____________________________
Tunda abin yafaru yakasa barin zuciyarsa, gani yakeyi ya aikata babban lefi, tunda yasan kansa baita6a rungumar d'iyar kowaba sai yarinyarnan, ALLAH kuma shine shaidarsa baiyi hakan dawata manufaba, sai danya bata kariya, amma kokad'an zuciyarsa takasa sukuni, jiya kwana yayi akan abin sallah yana Neman gafarar ubangiji akan hakan, ya lumshe idanunsa ahankali yana mai cije le6ensa Na k'asa, shiru nad'an wani lokaci baisake koda motsawaba.
Wayarsace tafara wringing, yabud'e idonsa da k'yar tareda jawo wayar, ganin mai kiran yasakashi mik'ewa zaune, cikin girmamawa yace momy barka da rana.
Bansan mitace masaba dagacan, nagadai yamik'e yanacewa OK inazuwa.

Da sallama yashiga falon, k'annen nasa suka shiga gaidashi, ya amsa fuska babu walwala.
Zama yayi kusada momynsa ya d'ora kansa gefen kafad'arta, my momy I miss you wlhy.
Murmushi tayi, tashafo kansa, nima haka yarona, inafatan komai normal.
Alhmdllh momyna.
Nazo d'azun kinata barci abinki.
Wlhy kuwa nagajine shiyyasa.
Momyna ki ajiye aikinnan haka ki huta mana, basai kifara kasuwanciba, ni zan baki jari da kainama.
Karka damu Ibraheem, insha ALLAH ina gab da ajiyewar, nima nagaji.
Yauwa momyna kokefa.

Takardar dake gefenta ta mik'a masa yatashi daga kafad'arta yana kallon takardar, momy miye aciki haka?.
Kar6i kaduba mana.
Amsa yayi yabud'e, hotunane wajen 8 aciki, cikin rashin fahimta yakalli momyn tasa, momy pictures d'in waye?.
Dad'ina dakai kenan, kaduba mana.
Zamansa yagyara sosai yafara kallon hotunan, k'yak'yk'yawar yarinyace ajiki kuma fara tas, komai da mace ke buk'ata Na burga ALLAH yabata kam, ya khaleel yad'an ta6e bakinsa tareda maida pictures d'in a takardar, yace momy nagani to.
Bakace tayi k'yauba to?.
Ah momy miye had'ina da'ita dazan yaba k'yanta?, amma tunda sokike nafad'a to tayi k'yau, saidai shigar tata batadace data y'ay'an musulmai hausa fulaniba.
Y'ar dariya momy tayi, tace wannan tayine dominka, sunanta Aleeya, d'iya ga tsohon minister kud'i, ayanzu kuma jakada a k'asar England, su biyu iyayensu suka haifa, itace auta, cikakkiyar likitace kuma kwararriya acan England, naza6a maka ita amatsayin matar aure, ALLAH yasa zaka yabama k'ok'arina.
Y'ar zabura yayi saboda maganar tayi mugun shigarsa, yace, ''momy matar aurefa? ahakan?.
d'aure fuska momy tayi, tareda kallonsa, Aleeya ta cancanci zama matarka, d'iyace mai nasaba, tanada ilimi, ga uwa uba k'yawu, nasan duk iya lalubenka baka samo koda wadda takama k'afarta, abaya nace ka auri Abida, amma ganin Aleeya saina canja shawara, yanzu itace za6ina.
Bai iya cewa komaiba sai kallon momyn dayakeyi.
Husnah tace ALLAH ya khaleel Anty Aleeya tahad'u, kuma zata dace da ra'ayinka, kasanf...........

Hararar daya balla matace tasakata jan bakinta ta tsuke, yace kutashi anan.
Suduka suka mik'e da sauri kowa tanufi d'akinta.
Shikuma yadawo da kallonsa kan momy daketa hucin 6acin rai.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru yacije le6ensa, shiru nawasu mintuna babu Wanda yasake magana.
Zuwacan Yace shikenan momy zanyi bincike akanta, insha ALLAH inhar tacika yanda nake buk'ata zaki sameni mai biyayya agareki, dukda banji sontaba ko kad'an araina.
Washe baki momy tayi tana kamo hannunsa, karka damu yarona, insha ALLAH Ma zaka sota wata rana, kwanan nanma zatazo Nigeria, ALLAH yatabbatar da alkairi, nagaji da zamanka haka babu aurene, ga baffanku NATA damuna akan aurnka, shiyyasa namaka za6in girma, Wanda su Bilkeesu zasu tabbatar har Abadan namusu rata, tabar k'afafa y'ay'anta sun rigaka yin aure.
Baice komaiba sai d'aga kansa dayayi kawai tareda cije le6ensa, shikad'ai yasan k'unar da zuciyarsa ke masa.
Daga nan shiru sukayi, hakan yasa momy ta shafa kansa cikin murmushi tace jeka ka kwanta ka huta kaji, idan ka nutsu mayi maganar.
Kansa ya jinjina, batareda yace uffanba yafice daga falon.
Afalo ya iskesu Aysha itada Zunnurain, jiyayi zuciyarsa takuma hasala, harya wuce saikuma yadawo baya.
Karaf suka had'a idanu da Aysha, ya watsa mata harara, murgud'a masa baki tayi ta kauda kanta gefe.
Ransane yakuma 6aci, cikin kaushin murya ya kwala kiran Zunnurain!!.
Zunnurain dabaisan da shigowarsa falonba yajuyo da sauri, na'am Yaya, yafad'a yana tasowa.
CiGaba yayi da tafiya, wannan yasaka Zunnurain bin bayansa yana cema Aysha ina zuwa.
OK tafad'a.


Koda suka shiga sai kawai yacema Zunnurain ya zauna wani aiki zai masa.
Zunnurain yad'anso yayi zargin wani abu, amma saiya kauda hakan aransa, Dan baisan wane aiki zai masaba, kuma yasan wanene yayan nasu.
System d'insa ya d'akko ya kawo masa, tareda nuna masa aikin dazai masa, shikansa baisan dalilinsa nayin hakanba, kawaidai bayason ganinsa da yarinyarne kawai.


Aysha data gaji da jira saita tashi takoma d'aki, dama suna maganane akan bautar k'asarta datakeson zuwa.


______________________________
Da yamma meerah takira Aysha akan sun dawo, zuwa anjima zasuzoma nan gidan su gaida su mama.
Sosai Aysha take farinciki, dantayi missing d'insu sosai, da murnarta ta sanarma mama da yaya fadeelah.
Suma sunyi farinciki, dandanan aka shirya abincin tararsu.
Bayan sallar magriba kuwa saigasu, Aysha da Ifteehal da anty meerah suka rungume juna, sunacike da murnar sake had'uwa, tasakesu takoma kan mom, itama tayi kewar ayshar, su Safwan ma suka rungumeta, ya Naufal yanata murmushi dabin Aysha da kallo.
Saida tagama murnar ganinsu sannan tace ya Naufal I miss you.
Oh sai yanzu kika san dani?, kofa kirana awaya bak'yayi?.
Hannu tasaka tarufe fuskartaπŸ™ˆ, sorry yayana, amin afuwa, wlhy murnar ganin su mamane ya mantar dani.
Maheer dake gefe shida shakur yace habawa yarinya, ALLAH saina rama nima.
Wayyo ya Maheer d'ina, inata kewarka, inata kewarka kamar nayi tsuntsuwa nazo Kd.
Bakinsa yata6e yana mata hararar wasa, to sarkin tsari, nibama wajenki nazoba dama, mama nazo gaidawa.
Aff nasan saikamafi kowa kewata ALLAH, dojewa kawai kakeyi.
kafin yabata amsa Shakur yace beauty kin k'ara k'yau da girma.
Ita saima yanzu tagansa, gidan su yazo, shiyyasa bazata masa wulak'anciba, tayi y'ar dariya tana kallonsa, da gaske ya Shakur?.
ALLAH kuwa beautyna.
Baki tad'an ta6e taigaba tana kar6ar Raudat dake hannun ya Naufal.
Dad da baffah suka k'araso, daka gansu kasan sunsan juna dama.
Mazan 6angaren baffah suka shiga, matan kuma 6angaren Anty Mamie, dan tace itace uwar y'ar.
Ansha hirar yaushe gamo, yayinda su mom suka saki jiki dasu mama saboda tarbar mutunci dasuka samu.
Aysha taja anty meerah d'aki ta zayyane mata komai gameda Auren mama da baffah.
Sosai meerah tayi murna, tace yauwa Aysha wannan shine matakin farko nacikar burinmu, amma ina gwaggonki?.
Nima Tunda nazo gidan bangantaba, bankuma tambayaba, kinsan abin saida taka tsantsan, yanzudai sonake nafara ganin Bishrah, awajentane kawai zansamu dukkan bayanan danakeso.
Gaskiyane, ammafa nayi farinciki da kowa yakasa ganeki agidanan.
Wlhy nima haka Anty meerah, hakan yana cikin nasarar aikinmu shima.
Aikamdai, ya khaleel fa?.
Baki Aysha ta ta6e, yana nan shima, Aysha takwashe yanda sukai dashi a shoprite dakuma had'uwarsu agidan.
Dariya sosai Anty meerah tayi, lallai Aysha kinyi jarumta sosai, ammafa karki yarda yasan kina sonsa, ki kama kanki sosai.
Tab yo Anty meerah hauka nakeyi, rashin kunyarma dakiga ina masa ganinai yana Neman shiga hancina, amma karki damu zan sake takune, saidai damuwata mama da kawu bilyamin.
Wai bazanje bautar k'asaba aure za'amin, ni basusan inada buruka agabanabane.
Dariya meerah tayi, cikin tsokana tace, kawai kice ya khaleel yafito musha shagali abinmuπŸ’ƒπŸ».
Kai Anty meerah, kema hadake ko?, nifa koda nake sonsa bawai inason aure baneba yanzu.
Hhhhh to shikenan maida bakin, yanzu dai kawo kunnenki kiji wani Abu.
Matsawa Aysha tayi, cikin rad'a meerah takema Aysha magana, wannan yasa banji misuke magana akaibaπŸ€•.


Fitowata nayi nabarsu awajen.



A 6angaren su baffah kuwa sunata hirarsu da dad, sunsan juna tuni, baffah yakira ya khaleel awaya yazo suka gaisa, dad sai mamaki yanda khaleel d'in yakoma yakeyi, Dan rabonsa dashi tun bai wuce 18years ba.
Dad yace andai ajiye iyali ko?.
K'asa ya khaleel yayi dakai yana murmushi.
Baffah yace baiyiba, inata fama, amma kuma insha ALLAH Ana gab dayi.
Da sauri ya khaleel yad'ago yana kallon baffah, cikin tsinkewar zuciya ya maimaita maganar ta baffah a zuciyarsa, _ana gab dayi!_, to gabda yin me?.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa, baffah yana lura da halin dayake ciki, aransa yayi dariya yana fad'in d'an jakar uba aii maganinka zanyi wannan karon.
Tundaga nan ya khaleel yadaina saka baki a hirar, dama can eh, a'a Ce maganar tasa.

Sai around 11 suka bar gidan, tuni sabo yashiga tsakaninsu da mutan gidan, kowa yayi aboki kuma.
Aysha harda 'yan kwallanta, taso ace tafiyar dazasuyi Sokoto gobe harda ita aciki wlhy.
Bayan tafiyarsu suka dawo d'aki, mama sai yaba kirkin bayin ALLAHN takeyi, suna d'an hirar zuwan bak'in wayar mama tayi wringing.
Ummah ce, Dan haka tad'auka da murmushi, Yaya ina yini? Kune da daddare haka?.
Wlhy kuwa fad'ima, ya yarana?.
Lfy lau suke, duk gasunan muna tare dasu, bak'i akayi yanzu suka tafi, mama tabama Ummah labarin zuwansu mom.
Sosai Ummah taji dad'in hakan.
Ummah tace munfara maganar bintu dake d'azu wayata tamutu, shiyyasa nakasa hak'uri nak'ara kiranki yanzu.
Au wlhy kuwa Yaya, tana nan babu lfy, abinda yasa kenan banmata maganar Aysha ba, sonake ta warke, Dan inason jin wasu bayanai daga gareta, Dan tareda Bilkeesu mukaje dubata ranar, shiyyasama nakuma k'yaleta.
Hummm abin mamaki, yakamata kam ki bincikar mana ita, kidubafa tunda tatafi da yarinyar nan bata kuma zuwa kano ba, kuma kince tunda kikaje gidan baki ta6a ganintaba.
Wlhy kuwa yaya, shiyyasa kawai naji yakamata nasan wani Abu, sainake ganin kamar kawai lauje cikin nad'i bamu saniba, tunda tace mai gidanne yabiya kud'in karatun, harma da y'ay'ansa ciki, kuma banga wannan alamarba, hasalima babu Wanda ya nuna yasan Aysha agidan.
Lallai maganarki gaskiya akwai lauje cikin nad'i, yanzudai bara nabarki saida safen.
Ki gaishe da jama'ar gidan.
To zasuji yaya, nima agaidamin yarana.

Bayan sunyi sallama fadeelah tace mama wai miya farune?.
Babu komai fadeelah.
Ina ayshar kuma?.
Tashiga wanka.
OK, kijeto ki kwanta, nasan k'awayen naki nacan nazuba ido.
Jin jina kai fadeelah tayi, tamik'e, dama ummuhanee nawajensu Hamdiyya, tafita zuciyarta na waswasi akan abubuwa dayawa, saidai batasan yazata kama lamarinba harya zama hujja agareta.................✍












❀❀❀❀😘😘😘😘😍
[8/29, 6:44 PM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1 πŸ”š_*
(K'arshen littafi na d'ayaπŸ“•)

*_Alhmdllh masoyan ciki da gaskiya, wannan shafin nakune aduk inda kuke, ngd sosai da k'aunar dakuke nunama buk d'in, ALLAH yabar zuminci, nima ina sonku da k'aunarku over wlhy._*
❀❀❀❀😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘.



4⃣0⃣

Duk zungurar da mama tayima Aysha adaren jiya saboda gwaggo bintu, Aysha tak'i cewa uffan, kuma tadage akan ba nan gidan suka zaunaba sanda ta d'akkota.
K'yaleta mama tayi, Dan batason Aysha ta fahimci wani Abu, saidai batasan ayshar tagane komaiba.
Saidai tunaninta ina gwaggo bintun?.


Washe gari bayan sun kammala break fast Aysha tazare jikinta zuwa 6angaren masu aikin gidan, shiga tayi tamkar mai neman wani Abu, Rabi da iya hama kawai ta taras a falo suna kallo, aranta tace ana nandai da hali.
Suna ganinta suka hau washe baki, Rabi tace ko ana kiranmu ne?.
Murmushi Aysha tayi, cikin basarwa tace, "a'a, kawai zan wuce garden ne najiyo dariyarku, shine nace bara Nagano miya baku dariya haka?.
Iya hama tagyara zama tana fad'in wlhy babu komai. film ne muke kallo.
Aysha takalli TV n, Indian hausane suke kallo, batace komaiba tafito, can cikin garden tashige, takira wayar Anty meerah, bayan sun gaisa ta shaida mata bataga alamun gwaggo bintu na gidanba, Dan d'akinta arufe

2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment