Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa club itama?.
Wata 'Yar dariya meerah tasaki, kai lil sholy kinda abin dariya, aii tafiyar tamu duk d'ayace da ita, nima abinda yahanani fita saboda kene, banason abarki ke d'aya agidan. Waima mi aunty glo.....tafad'a miki jiya danaga takiraki d'akinta?.
Mik'ewa Aysha tayi daga inda tayi sallan, tacire hijjabinta, doguwar rigace ajikinta pink har k'asa, tayi masifar mata k'au da haska farar fatarta, gashi tad'an k'ara girma da murjewa saboda yanayin k'asar ya kar6eta.
Prigh tanufa tad'akko robar ice-cream, Zama tayi abakin gadon, tareda bud'ewa tafara shan kayanta, itadai meerah tana binta da kallo.
Anty meerah waikinsan mita fad'amin?.
Saikin fad'a lilyna.

Humm catayi wai mutumin ranar yace, "tamaidani school, yanzu haka sunkammala komai akan makarantar, zanfara zuwa, wai yanaso na iya turamci sosai.
Waini Anty meerah waye shi agidannan?.
Girgiza kai kawai meerah tayi cikin k'unar rai, tace, "Aysha bani Aron hankalinki nan nafad'a miki mikikazoyi *Cayman islands (UK)*.
Aciki zakiji tarihina da k'addarar data kawoni nan, dukda dai dagabaya muka dawo wannan k'asar, da a India muke zaune.

Idon Aysha kam akan meerah dake sharar kwallah, itama duksai ranta ya jagule. amma tana saurarenta.
Meerah race...........



Amin afuwa muhad'u page 20 danjin mi meerah zata sanarma ayshar neπŸ€”?????.




*************************
Ya khaleel kam yaje k'asar Indonesia, inda yay kwanaki 9, dama aikine yakaishi, yabaro k'asar yanufi France inda Headquarter d'insu take, a birnin *Lyon*, nan d'inma yasamu kwanaki 12 yabaro yataho k'asar haihuwarsa Nigeria............πŸ–Š




*_Dan girman ALLAH kudaina cewa ina wuta d'innan kuna bina da feturπŸ™πŸ», karku fad'a abakin mala'iku surubutaπŸ€•, gara kuma mahaifina addu'ar neman gafara, zaifi sakani cikin farinciki da yadda da k'aunarku gareni😭, shine zai nunamin jin dad'inku._*
inayinku my Fan'sπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ».



_idan nasamu dama k'ila nak'ara anjimaπŸ˜‚_





😍😍😍😍😍😍😍😻
[8/7, 7:39 AM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)

KUKAN KURCIYA.....πŸ‘‡πŸ»πŸ€•
*_Shugaban kasa Buhari yayi jawabi mai ban tausayi da kuma sanyaya jikin duk mai hankali, jiya Al-hamis a Bauchi._*
*_A ziyaran da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai birnin Bauchin Yakubu, shugaba Buhari yayi jawabai masu sosa rai dangane da makomar Kasar mu Nigeria da tsarin siyasar miyagun shugabanni 'yan jari hujja_*Shugaba Buhari yace: "Allah Ya sani bisa kokarin tunani na shine in tabbatar na dora Nigeria kan mizanin da zaku yi alfahari da ita nan gaba.*
*_Akwai wahala cikin kawo sauyi a Kasa , amma muna jure shi iyakar iyawar mu, ko makiya sun tabbatar mun dauki saiti kan makomar Kasar mu Nigeria, amma 'yan jari-hujja munyi musu laifin da bazasu yafe_*mana ba, laifin shine rufe musu kofofin sata, su ba damuwar su bane Nigeria ta kone ta babbake su sayar da tokan ta su gudu*, *Sun sako mu a gaba yanzu da dukkan karfin su suna bukatar a kyale su su wargaza 'dan abinda muka fara gyarawa.*
*_Basa fatan alheri ko miskala-zarratin wa Nigeria da al'ummar ta_* *_Babu wani zabi gare mu, zabi yana gare ku al'ummar Nigeria, idan kun gaskata kokarin mu ku sake zaban mu mu dora daga inda muka tsaya, hakan zai zama alheri gare ku, idan kuma kun karyata mu ku_* *koma gare su ('Yan jari hujja) su lalata makomar ku da Kasar ku.*
*_Amma tabbas wata rana zaku tuna na fada muku gaskiya, kuma na dora ku akan gaskiya, kuma na rike ku da gaskiya, zabi naku ne, kan makomar Kasar ku ba batun siyasa ce a raina ba wallahi face makomar ku nan gaba.."_*
Jawabin shugaban Kasa MuhammaduBuhari Hafizahullah
kenan.
Alherin Allah Ya kai ga shugaba Buhari
Allah Ka tsare manashi daga dukkan sharri
Allah Ka daukaka darajar sa duniya da lahira
Allah Ka bashi dukkan nasarar da yake nema
Allah Ka zama jagoran sa.

Bilyn Abdull
*_idan kagane ba buhari zakaimawaba, kanka zaka taimaka da yankinka, harma da addininka, Idan har mai hankali zai nutsu to zaigane 'yan arewane keta wannan haukan , saboda son mulki da hanyar Neman yin wawaso akan dukiyarmu kamar yanda suka saba abaya_*
_Wlhy 'yan arewa mu farka, domin kauda mak'iyanmu, wad'anda shekaru aru-aru basu kawo mana sauyi a arewarmuba, kuma wlhy yanzuma yaudararmu sukeyi bazasu gyaraba, shiyyasa suka KASA had'a hannu damai kishinmu sudawo da martabar Yankin mu, burunsu kawai kud'unmu, da mulkarmu_.
_mubar siyasar shirme, mukoma ta cancanta kamar yanda kudancin k'asarmu keyiπŸ˜­πŸ‘ˆπŸ»_


2⃣0⃣

Sunana na yanka Halematussa'adiyya, kasancewar sunan kakata naci iyayena ke kirana Ameerah.
Ni 'Yar asalin garin sokoto ce, amma yanzu muna zaune da iyayena a Kaduna, nima a Kaduna aka haifeni, mahaifina mutumin kirkine, yanada k'ok'ari wajen kare mana mutunci dukda bamai kud'i baneba.
Ga mahaifiyata kam Sam bahaka baneba, macece mai son birga da son mu'a mullah da hajiyoyin birni.
Mu 5 iyayenmu suka haifa, nice d'iya ta uku acikinmu, yayyena biyu Suwaiba da 'Daheera duk halin mama suka biyo, kuma suna bin hud'ubarta daki-daki, wannan yasa suka tashi a fand'are, abin nadamun mahaifinmu, amma bashida damar tankawa.
Awajena kawai yake samun sauk'i da sassauci, Dan bana k'etare zancensa, ahaka muka kammala secondary, yayinda nikad'aice nayi sauka acikinsu.
Mahaifinmu yakiramu tareda sanar damu mu fido mijin aure, yabamu watanni uku rak.
Nad'an shiga damuwa, saboda bana kula kowa, amma inada samari masu sona, ahaka nafidda Aminullah acikinsu, yayindasu Anty 'Daheera baba nata fama dasu, saida ya tsoratar dasu akan zai saki mama sannan suka kawo mazajen aure.
Ansaka mana biki wata 11 saboda baba yasamu kammala yimana kayan d'aki.
Bikinmu yarage saura wattani hud'u ALLAH yayma baba rasuwa, sakamakon had'arin mota daga Kano zuwa Kaduna.
Mutuwar baba tata6ani matuk'a kuma najigatu nida sauran k'annena biyu baza.
Amma gasu mama da su Anty Suwaiba bahaka bane, domin sufa duniya sabuwa fill, ko arba'in d'in rasuwar baba ba'ayiba mama ta aika gidan samarinmu cewar tafasa aurar damu.
Dan acewarta bamu gama morar kanmuba bazamuje muyita bautawa k'artan banzaba, nashiga tashin hankali Aysha, Dan alokacin auren kawai nake buk'ata kasancewata mace mai yawan sha'awa.
Rashin mafita yasakani dagewa dayawan azumi domin kame kaina daga halaka.
Humm awata ranar laraba nadawo daga islamiyya agajiye saboda inazuwa hadda alokacin, saina tararda su mama sunbaje kud'i afalo suna irga, kud'ine masu shegen yawa, tsoron kud'in yasakani zaro ido waje da tambayar ina suka samu?.
Mamace cikin hasala tace satowa mukayi Dan ubanki.
Shiru nayi, jiki a sanyaye nashige d'aki domin cire uniform d'ina.
Damuwar ganin kud'innan tahaifarmin dayawan kuka, na tabbata bata k'yak'yk'yawar hanya su mama suka samu kud'inba, to amma tambayata itace a ina suka samun?.
Bansaniba, wannan yasaka nasama zuciyata salama, sati biyu da kawo kud'inan akafara gyaran gidanmu, gyara kuma namasu kud'i ahannu, aikam kamar jira 'yan anguwa keyi akafara surutu mahaifiyarmu tasakamu karuwanci, dama shiyyasa ta lalata aurenmu.
Maganarnan tana k'onamin rai, amma banida amsar gamsar da jama'a, Dan nima bansan tushen kud'inba.
Hummm inafad'a miki Aysha ranar saiga wata hamshak'iyar hajiya tazo gidanmu, dakaga matar nan kasan kud'i sungama zaunawa agareta, sunyi maganganunsu da mama, daga k'arshe aka kirani, wai matar nan tad'auki nauyin karatuna zuwa turai, tunda takarduna sunyi k'yau.
ALLAH sairki rashin Sani, sainaita tsallen murna, Dan aganina zanbar gidanmu da abubuwan bak'inciki suka tare aciki.
Cikin k'ank'anin lokaci aka gama mana komai, muka cane k'asar India.

Wannan tafiya itace tazamarmin tushen nadama da Dana Sani. Itace ta wargatsa rayuwata daduk wani tanadina, itace ta zama hajijiya dake wajiga zaren rayuwata ayanzu, tayi maganar tana kuka maicin zuciya.
Aysha ma natayata.
Tacigaba dafad'in munsauka k'asar india, hajia Fanta Ce takawo mu, intak'aicemiki dai bantashi nadama ba, saida john yaketa haddina adaren Dana kwana 2 dashigowata k'asar India, saida suka shayar dani kayan maye a drink sannan yayi yanda yaso dani, nayi kuka nakuma yi bak'inciki.
Ashe ba makaranta zanyiba, kawoni akayi nayi karuwanci kawai, ankawonine domin cin amanar ubangijina.
Abubuwa sun kwa6emin Aysha babu mai lallashina ko tausaya min, tun ina d'ari-d'ari da harkar har zuciyata takarye saboda bak'incikin mahaifiyata nafad'a tsundum, na tabbata tasan komai amma tabadani aka taho dani wata k'asar, Aysha mahaifiyata fa, wadda duk duniya tafi kowa sanin zafina, kaico da hali irin nami Mamana.
Meerah tafashe da kula.
Aysha bata hanataba, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Meerah tace, ayshan shed'anci da shagala yasakani daina sallah, nadaina azumi, na daina karatun alkur ani, dukna maye gurbin wad'annan da shaye-shaye, kwana a club, wlhy Aysha har blue film anta6ayi dani.
Bak'aramar zabura Aysha tayi da jin furucin meerah ba.
Cikin tsoro tace, ''Anty meerah da gaske?.
Murmushi mai ciwo meerah tayi, tacije le6enta nakasa, tareda fad'in humm Aysha kedai abar kaza cikin gashinta kawai, ni k'arancin tunanina nayi hakane dundan aita d'orama mahaifiyata zunubi, tunda itace silar komai.

Girgiza kai Aysha tashigayi, cikin kula tace, "Anty meerah kinyi kuskure, ba'a gyara 6arna da 6arna, kinyi sakaci dakika bar ALLAH, Barin sallah shine mak'asudin ruguza dukkan rayuwarki, barin azumi da karatun alkur'ani sune dalilin haddasuwa k'unci ya yawaita aduniyarki.
Dakinsani kin kar6i k'addararki tafarko saboda fyad'e aka miki, bacikin hankalinki kika aikataba, kifa Sani yanzu ba mama kad'ai ake rubutama zunubiba hardake kanki, tawani fanninma kinfita wlhy.
Anty meerah kituba tunda lokaci bai k'ure mikiba, ki gyara mu'amullarki da ALLAH tunkan yakamaki da azabarsa, kiyi gaggawar farkawa daga nannauyan barcinki tunkan mutuwa tazo ta d'aukeki, wlhy kikabar duniya ahaka wuta zakije, saboda kindaina sallah, kindaina azumi, kindaina karatun alkur'ani zancen ALLAH, Anty meerah banbancin kafiri da musulmifa sallah, duk Wanda yabar sallah yayi asarar daza'a shekara dubu anamasa jaje.
Please Anty meerah😭😭😭😭😭 kicanja, kinada sauran lokaci, karki bari yawuce abanza agareki Dan Alfarmar mazonmu.

Itakanta meerah kuka takeyi kamar zata shid'e, suka rungume juna itada Aysha suna kuka mai cin rai da zuciya, saida sukayi mai isarsu sannan Aysha tafara bana meerah NATA labarin.....

Sosai meerah ta girgiza da labarin Aysha, cikin raunin murya tace, "Aysha sun yaudareki keda iyayenki, babu wani karatu dasuka kawoki ko kula damai ciki, sunkawokine kiyi karuwanci, danki samamusu kud'i.
Nasan hajia kaltume sosai, itama dila ce ta safarar yara, hajia babba cedai gasky ban saniba, inaga sune dillalan zaune masu samo yara subayar, wad'an nan sunfi kowa samun kud'i, Dan inhar suka samo yarinyar za'a d'auki hotonta aturama su hajia fanta, sai sukuma suturama wad'anda ake kaima yaran k'asa-k'asa irinsu Anty Glory kenan, sumafa zasu saka hoton yaranne akasuwa, idan ansamu Wanda yataya to zai biya mak'udan kud'i, hardana jirgi da duk wani cuku-cuku daza'ayi kafin kisamu nasarar baro k'asarki, kinsandai Yanda yankinmu na Africa yagama lalacewa da cin hanci da rashawa, su sunsan hanyar dazasubi abaro k'asar dake, ak'asashen turai kuwa kowaccenmu da abinda yakawota ake sakawa, wasu karatu, wasukuma abubuwane daban-daban, amma mafi yawanmu karatune.
Wannan millions kud'in dasuka tura shine za'aita rabawa tundaga kan iyayenki, dillaliyar data samoki, dakuma wadda zata fiddoki k'asar.
So wani yabiyane kizauna dashi natsawon shekaru biyu ko d'aya, harma uku, wasu kuma sau ma 1 kacal, karki d'auka wai 'yan Nigeria kawai ake kawowa, a'a 'yan k'asashen Africa ne daban-daban.
Wannan shegen john d'in dakike gani, duk yarinyar da'aka kawo shike fara amfani da ita, inhar wajen Anty glory aka kawota, idan yay amfani dake saiya had'aki dawani kuma, dagananfa ke harka tabud'e miki, zakije kiyi harkokinkima kisamu kud'inki kisa ajaka.

Aysha nayadda babu abinda yakai addu'a daraja da kariya, lallai addu'a da maida lamarinki ga ALLAH ya d'oraki akan azzauman nan har suka yanke shawarar kaiki makaranta, Queen tacemin tanada shekaru 13 aka kawota amma wannan baihana john kaca-kaca da itaba, dukdama su yawancinsu dasaninsu sukazo.
Amma kinga ke aranar saiya hak'ura yabarki, wlhy john tantirine dakike ganinsa, kariyar ALLAH ce kawai tahana ya6alle k'ofar yayi yanda yaso dake.
Kicigaba da godema ALLAH.
Sannan kada kisa wasa akaratun dazasu sakani kiyi, kitsaya kiyi domin zai amfanemu.
Insha ALLAH zan ku6tar dake dakud'in Dana tara, kedai kisaka himma, kicigaba da kare mutuncinki, karki biyema k'awaye dansuma suna taka rawar gani wajen wargaza tarbiyya, ballan tanama anan turai da 'ya'yamsu suke 'ya'yan ido, tunda komai kayi su awajensu 'yancine.

Godiya sosai Aysha taitayima meerah, suka rungume juna sunajinsu tamkar jini d'aya, uwa d'aya uba d'aya.
Aysha tace Anty meerah to kema Dan ALLAH ki canja, kituba ki daidaita rayuwarki, kibar shaye-shaye daduk wani Abu mara k'yau, kikoma tamkar yanda kike adad'inki, Ameerah maison Addini da tsoron ALLAH.
cikin murmushi ameerah tace namiki alk'awari zan canja Aysha, zan koma yanda kike buk'ata, zan koma Ameerah ta tagari, dagayau namiki alk'awari bazan sake shan wani abin mayeba, bazan sake aikata zinah ba, da duk wani abinda yasa6ama ubangina, zancigaba dayin istigifari domin ubangiji mai yawan gafarane, zanyi tuba irin Wanda ALLAH keso.
Tsalle Aysha tadoka tad'are meerah tana murna.
Oh my lili I Love you, kinzamemin alkairi aduniyata, inaji ajikina ALLAH ya turokine domin ki canjani, ALLAH yakareminke, ya ALLAH kada kabasu damar cin galabar wannan marainiyar yarinyar dabatasan komaiba gameda rayuwa har yanzun.


Daga nan meerah takuma sabuwar kalmar shahadah, acewarta (da karta tazama cikin kokwanto gamma tayi komai yanda hankalinta zai kwanta), harda wankan shiga musulinci tayi, tad'auro alwala tafito, dukwani abinda yasa6ama shari'a dake ajikinta tacireshi, kama daga gashi farce da sauransu.
Jinta takeyi sakayau, takoma wata halitta daban, saida Aysha takuma tunamata wasu abubuwa dayawan sannan sukayi sallar asubahi tare, Dan yaukam kwanan zaune sukayi.πŸ˜ƒ
Bayan sunyi karatun alkur'ani Wanda kowaccensu ALLAH yabata baiwar ajiyarsa a kwakwalwarta, sukayi azkar suka kwanta, Dan har sannan su Serah basu dawo gidanba, hakan yana nuna ansha shagali jiya a club............


___________________________
Gaba d'aya hankalin gwaggo bintu atashe yake, tasan wanene khaleel, tasan aikinsa da bin kwankwanto akan Abu, bak'aramar razanata kallonsa yayiba, tana tsoron abinda zaije yadawo.
Ganin batada mafita tanufi 6angaren hajia babba, dawowarta kenan daga aiki.
Dafarko hajia babba tayi nufin korar gwaggo bintu, amma ganinta abirkice yasa ta saurareta.
Itama hankalinta yatashi, tasan halin d'an nata sarai.
Cikin matuk'ar damuwa tace, bintu dolene kibar gidannan awannan ga6ar.
Idanu gwaggo bintu tazaro waje, hajia babba ki tausayamin, banida inda yafi nan wlhy.
No, kwantar da hankalinki, bawai zaki koma Kano baneba, Lagos zaki tafi gidan zuwairah, kizauna nawani lokaci kafin abubuwa su daidaita, wannan shine kawai kwanciyar hankalinki.
Tana gama fad'ar haka tanuna mata k'ofa alamar tatafi.
Tamkar gwaggo bintu zata fasa kuka haka tabar 6angaren...........πŸ–Š


*_nace hum gwaggo bintu!, dukfa d'an daya hana uwarsa barci, wlhy shima bazaiyibaπŸ‘ˆπŸ»β˜Ή_*




Masoyan gwaggo bintu amin afuwa🀣






*_Barka da dare my Fan's😍😍😍😍😍😘😘😘😘_*
[8/7, 9:24 PM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)

*_Nagode sosai da addu'arku ga mahaifina, ALLAH ya gafarta dukkun musulmai baki d'aya, kuna sakani farinciki wlhy masoyana, ngd, inayinku sosai-sosai._*
I love you k'atin-k'atinπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜»πŸ˜»πŸ˜»πŸ˜˜πŸ˜‚


2⃣1⃣

*_Kano_*
Alhmadulillh su mama sun fita takaba tuni, suna zamansu lafiya da k'yautatama juna kamar yanda suka saba.
Matar uncle Ahmad tahaihu suketa shirin zuwa Jigawa suna.
Kawu bilyamin dakansa yabada mota akaisu harda iyalansa.
Sun isa Jigawa lafiya ansha suna kuma lfy, da yamma mama tashirya danufin zuwa wani gida gaida abokan arzik'i data sani.
Itadasu Rufaida suka tafi da sadiya.
Tun'a k'ofar gidan sukaci karo da zuk'ek'iyar mota bak'a wulik, su Rufaida sunata santin motar, mamadai batace dasu komaiba, sai murmushi datakeyi.
Gidane madaidaici mai d'akuna uku, babu kowa a tsakar gidan, amma a share yake tas, saida sukayi sallama sau kusan uku sannan aka amsa, wata dattijuwar tsohuwa tafito tana kuyi hak'uri inata amsawa, karar TV tahana kuji......
Maganarta takatse saboda ganin su mama, kai wanake gani kamar fad'ima haka?.
'Yar dariya mama tayi, tace, "wlhy kuwa inna mune mukazo garin, shine nace bara Nazo Na gaidaku andad'e ba'a had'uba.
Aikuwadai wlhy, 'yanmata kushigo kunji.
Rufaida da Safiya suka shiga gaba, mama nabinsu abaya.
Falone irinna tsoffi, amma komai atsare, sai 'yanmata biyu dake zaune, kowa da 'abinda takeyi.
Bayan sun gaisa inna tace haba fad'ima shikenan kuma anyanke zuminci shekara kusan ashirin?.
Kuyi hak'uri inna, nayi laifikam amma amin afuwa, insha ALLAHU za'a canja.
To ALLAH yayi albarka, wad'annan jikokinane ko?.
Dariya mama tad'anyi, kanta ak'asa tace eh inna amma nawajen abokiyar zamatane.
ALLAH sarki, masha ALLAH, amma fad'ima kardai had yanzu Baki haihuba?.
A'a inna akwai uku.
ALLAH Sarki, ALLAH ya albarkacesu.
Ta kalli 'yanmatan nan biyu datum d'azu suke satar kallon mama Dan tamusu kama dawata dasukanta6a Sani. Tasleem tashi kuhad'o abinci mana ga mamanku wadda Baku saniba.
To inna, tasleem da maleeka suka fad'a suna mik'ewa.
Mama tabisu da kallo tana murmushi, inna wad'annanfa nawajen waye?.
Fad'ima 'ya'yankine aii, 'Yar farar tawajen bilki Ce, d'ayar kuma d'iyar amaryarsuce, tare suke da Ibraheem da babansu.
Ikon ALLAH, yanzu yaran Bilkeesu nawa?.
Wai aii bilki anzama kaza uwar 'ya'ya, aibayan bariwarki gidannan haihuwarta 12, saidai d'aya yarasu kusan wattani goma kenan.
Lallai Bilkeesu ALLAH yaraya manasu to...
Ameen dai fad'ima, yanzu kuwa kuna inane dazama?.
Inna INA nan cikin Kano, amma ALLAH yayima maigidanma rasuwa kusan wattani Biyar kenan.
Sallallami inna tafara dafad'in oh ni Dije ALLAH yajik'an musulmai........
Shigowar mutanen biyu yasaka su Rufaida gaishesu.
Muryar Wanda mama taji yasakata kid'ima tad'ago ido da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna, ita tafara janye nata ido tayi k'asa dakai.
Inna tace Abdillahi kundawo?.
Jikinsa a sanyaye yace, ''eh inna mundawo.
Matashin saurayi yace, "lallaima tsohuwarnan, nibazakice nadawoba ko?.
Dariya inna tamasa yo Ibraheem kakoma mana, aidai bakaine Malam irona Na gaskiyaba ko? Aini tunda k'akiyin aure munraba jaha.
Aikam saidai muraba harma k'asa kuwa.
Dariya akad'anyi.
Mama tagaida dattijon mutumin, ya amsa mata cikin kafeta da idanu, itakuma tak'i kallonsa.
Shi ya khaleel ma sai yanzu yalura dasu mama, gaisheda mama yayi yanason tuno ina yasan wannan fuskar?.
Su maleeka suka shigo da kulolin abinci.
Mama tayi k'arfin halin fad'in wai Babane yagirma haka?.
Kwarai kuwa fad'ima shine, Ashe zaki ganeshi?, gashinan d'an kwal uban yak'i aure.
Kai Dan gidanku mamarkace wannan.
Ya khaleel yashafa kansa, cikin murmushi yace, " inna aiban santaba kuma."
Katanbayi Abdillahi aishi yasan kowacece.
Juyawa yayi yana kallon Baffah datuni tsohon tsumi yamotsa masa, sai satar kallon mama yakeyi.
Baffah fad'amin to.
Dak'k'uwa Baffa yawatsa masa, yana fad'in ungo wannan Dan k'aniyarka.
Dariya sukad'anyi.
Su Rufaida kam dukda kasancewarsu yara tuni ya khaleel yatafi da imaninsu.
Yau sanye yake cikin shadda marun, wando dariga d'inkin zamani, rigar iyakarta cinyarsa, ya d'ora hulla zanna Bukar datai mugun fito da ainahin suffarsa ta Hausawa, sai k'amshi yake tashi ajikinsa mai sanyin dad'i.
And'an ta6a hira wadda mama da baffa suka kasa sakewa, kowa da abinda yake sak'ama ransa.
Ya khaleel madai baya cikin hirar, Dan tuni Yakoma can gefe saman wata kujera yazauna yanata danne-danne awayarsa, lokaci-lokaci yakan amsa calls da ake masa.
Su mama sukamik'e domin tafiya.
Inna tace, 'Dan ALLAH fad'ima kidinga waygowa yanzun, kuma insha ALLAH zamuzo bikin Fadeelah, Agaida yaran Dan da abokiyar zaman, ALLAH yak'ara hak'uri kinji.
Amin inna mungode, ALLAH yak'ara lafiya.
Su maleeka suka mik'e danyin rakiyarsu, Dan tuni har sabo yashiga tsakaninsu dasu Sadiya.
Baffa yakira Tasleem yabata Rafa's d'in kud'i yace tabasu suhau mota, shima ya khaleel yakira yay dad'i akai.
Inna dama fad'ima nazuwa gidannan?.
A'a wlhy, rabona da ita tunda kuka rabu, nima nayi mamakin ganinta, Ashe k'anin mijintane yake anan, matarsa ta haihu shine sukazo suna, 'Yar albarka bata mantamuba tazo gaishemu.
Jinjina kai kawai baffa yayi, batareda yace komaiba.
Ya khaleel daya dawo falon yace, "wai Dan ALLAH inna wacece ita?".
Matar babankuce dasuka rabu bayan haihuwarka da wattani uku, yarinya mai hankali dasanin darajar mutane, kagadai ni amatsayin uwar kishiya nake gunta, amma wlhy tamkar mahaifiyarta tad'aukeni, (inna mahaifiyar aunty Mamie Ce masu karatu).
Shiru ya khaleel yayi, danshikam k'yaunar matar tashigeshi sosai.
Inna tace, ''kajima mijin nata yarasu wattanni 5 dasuka wuce.
Da Sauri baffa ya kalli inna, suna had'a ido yay k'asa da kansa.
Murmushinsu Na manya inna tayi, danta gano wani Abu ga Baffan.......


To komiye masu karatu?.πŸ˜‚


_____________________________


2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment