Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waini meerah kindaina zuwa club ne? naga 2days saikice kinajin barci, kodai kinyi fad'a da babyn kine?.
Murmushi meerah dakema Aysha kitson makaranta tayi kawai, amma batace komaiba.
Lyn ta ta6e baki tana hararar meerar, o miskilancin yamotsane? Kokuma kinsha abinda yafi k'arfin kankine?.
Eh, meerah tafad'a batareda takalli inda Lyn takeba.
Itama saitaja bakinta tayi shiru, dantasan sarai meerah tafita buyagin rashin mutunci.
Aysha najinsu, saidai tanata danne danne awayar meerah abinta.

Washe gari akakai Aysha wata had'ad'd'iyar makaranta dake nan bayansu, komai nad'an gata aka matashi, saita saje da 'ya'yan turawan kasancewarta fara tas, kuma k'yak'yk'yawa, kawai dai duk inda bak'i yashiga acikin turawa dolene ka shaidashi saboda yanayin halittarmu datasu akwai banbance-banbance. Amma badan hakaba saika rantse cikin tsatsonsu tafito.
Taji nasihar meerah sosai, wannan yasakata maida hankali akan abinda yakaita, dukda haka tayi k'awa maisuna *Arena* itama baturiyace 'Yar asalin k'asar, amma tanada yanayin sanyi kamar Na Aysha, tasu tazo d'aya kam da Aysha sosai, kuma itace ke k'ok'arin k'ara fahimtar da Aysha abinda bata saniba, kasancewar har yanzu tanada sauran rashin gane turancin.


____________________________
Gwaggo bintu tuni tahad'a inata inata tacane Lagos, tatafine akan zata zauna da aunty zuwairah saboda cikin datake dashi, sudai su aunty Mamie sunyi matuk'ar mamaki, danba yau Anty zuwairah tafara cikiba, kuma wani baita6a zuwa ya zauna mataba sai awanan Karon, alhalin wannanma itace haihuwa ta hud'u dazatayi.
Tunda gwaggo bintu tasauka gidan Anty zuwairah bataga wata fiskar rahamaba agareta, babu wata tarbar mutunci data samu, ballatana kallon arzik'i.
d'akin masu aikin gidan aka kaita.
Aikam bak'in ciki tamkar yakarta🀣.


______________________________
Tunda baffa sukadawo daga Jigawa yakasa sukuni, duk-yar zama wani kala dashi, har yanzu yana k'aunar fad'ima, Dan itace first love nasa, auren had'i akamasa da hajia babba, amma fad'ima za6inshice, akanta yafarason wata 'ya mace aduniya, shiyyasa yakan jita daban acikin mata, tundaga randa yafara ganin Aysha tatuno masa da Fad'imarsa, saboda wata muguwar kama dayaga yarinyar nayi da ita, baikawo komai aransaba alokacin, amma tabbas tundaga lokacin yaji yana begen son ganin fad'ima, saidai basan ina zai dosaba wajen sansanin indama take, gashi iyayenta duksun rasu tuni.
Yaduk'ufa da addu'a tun'a lokacin, saigashi ALLAH ya kar6a masa, harda albishir mafisaka farinciki, shine fad'ima batada auren kowa akanta yanzu, harma ta kammala ida, Abu mafi damunsa kuma, halin ko'in kula da fad'ima tanuna akanshi dasuka had'u a Jigawa, 'ya'yansa kawai tasakarma fuska, saikuma matarsa bilkisu dataita tanbayar labarinta, amma shi yitayi kamarma bata sanshiba, yacije le6ensa tareda juya kwanciyarsa, gaba d'aya yarasa walwalarsa.
Umme amarya dake gefensa kwance duktana lura dashi, kasa hak'uri tayi, tace, "waini alhaji lfy kuwa?".
Murmushin k'arfin hali kawai yasakar mata, muryarsa a sanyaye yace, ''babu komai Saudah, kawai kainane yake ciwo".
Ayya todakasha magani.
A'a barshi kawai, kedai yi barcinki, kinga gobe idan ALLAH yakaimu kinada aiki.
Shiru tamasa, kasancewarta mace mai halin ko inkula akan abinda bai shafetaba, amma amatsayinta Na lauya ta tabbatar yanada damuwa, bayason fad'a matane kawai. To itama batadamu dasonjiba. Kowa yaji da matsalarsa kawai.
Shikam yak'i sanarmatane saboda gudun rigima, yatabbata kaf matan NASA Bilkeesu Ce kawai zai Tara da zancen azauna lfya, danhaka zaiyi hak'uri har ranar aikinta tazo, Dan gobema hajia babba Ce dashi.


Anty Mamie kam tun randa sukadawo daga Jigawa su Tasleem sukabata labarin komai, kuma mahaifiyartama tasanar da ita komai awaya, tayi farinciki matuk'a, kuma tana addu'ar ALLAH ya tabbatar baffah yace zai dawo da Yaya Fad'ima gidansa, zatafi kowa farinciki, dantana k'aunar matar, bata ta6a mata kallon kishiyaba saidai 'Yar uwarta. Tayi gum dabakintane Dan taga iya gudun ruwan baffan, tafiso yafad'a mata da kansa kamar yanda inna tace taja bakinta ta tsuke............πŸ–Š




*_tofa masu karatu, wannan cakwakiya dayawa take, daga wannan sai wannan, kucigaba dabin d'iyar Malam danjin yanda abubuwa zasuyita warwarar zare._*πŸ˜‰πŸ˜…βœŒπŸ»








😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😁
[8/8, 8:05 PM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)

_Wannan page nakune 'yan Group d'in *FIDDAUSI SODANGI* & *NICE & CUL HAUSA NOVELS* I love you so much my Darlings Fan's, inayinku, ina sonku, kamar yanda kuke sona._
πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜»πŸ˜˜πŸ˜‚


2⃣2⃣

Nikam momy miyasa zaki turomin matarnan?, nifa bancemiki ina buk'atar 'yan aikiba, nawa sun isheni.
to naji, amma kimin alfarmar barinta tazauna anan zuwa wani d'an lokaci, nima bacanayi tazauna ananba aii.
Shikenan momy, ammafa wlhy aikin zanke sata, danbazata zauna min saidai taci ta kwantaba.
Bakida matsalar wanan, kisakata komiyema, itama aii 'Yar aikince, shikuma d'an aiki babu wani banbanci tsakanin babba da k'arami, duk'a mizani d'aya suke.
To waini momy miyasama kikace tabar nan Abuja?.
Wannan sirrinane kam zuwairah.
Hummm momy kenan, kekomai da anta6aki saikice sirrinkine, ninarasa wanne sirrine haka?. Ina khaleel? Koyabar k'asar?.
Yana nan, bakwa wayane?.
Gaskiya kwana biyu bamu gaisaba, kinsandai halinsa da shegen shariyar tsiya, saidai kai kagaji kakirashi, amma hakanan dai bazaka ta6a ganin kiransaba.
Saikuta hak'uri dashi, idan yay aure k'ila matar ta canjashi, sai anjima, agaida yaran. Yauwa kayan dakika turo hajia maryama tad'auki Na 2million's, sai hajia Fanta ma tad'auki Na 1.5million.
OK momy, Dan ALLAH kimatsa musu wannan karon suhad'amin kud'ina dawuri, Dan dadyn Najwa yace, "nanda sati biyu zaije Germany, inaso nabashi yamin Oder d'in wasu kaya.
To babu damuwa, kikira Khursum kuyi maganafa.
Zankirata momy, agaidamin 2wins da mufeeda, shima khaleel ace ina fushi wlhy.
Dariya momy tayi ta yanke wayar tana fad'in dukzan fad'a to.

Ajiye wayar babu dad'ewa ya khaleel yashigo falon da sallama, sanye yake da wando ja iya guywa, sai bak'ar riga mai gajeren hannu, hannunsa d'aukeda system da wayoyinsa.
Harya zauna momy nabinsa da kallo, yace, " wash ALLAH nagaji momy".
Baki momy tata6e, Ibraheem ainazata kamanta danima agidan?.
😳ido yazaro waje, momy mantawafa?, ni khaleelu jikan Rufa'ee da Mujeetafa, na Isa manta uwata duniyata.
Yay maganar yana tasowa daga inda yake, yadawo kusada momy yazauna.
A shagwa6e yakamo hannunta tareda kwantar da Kansa saman kafad'arta, haba momy dabakinki kike fad'ar Na manta dake?, to ashema Ibraheem zai manta da kansa kawai sanyin idaniyata?.
Da irin wad'annan kalaman yakan tausasa zafin momy aduk lokacin datau hayak'i akansa, tuni kuwa yayi tasirin sanyaya zucyarta, cikin mirmushi takai hannu tashafa fuskarsa.
To yarona kaid'inne wani lokacin saina rasa kanka, dama nasan wasu abubuwan bayinkanka baneba, anjuyarmin dakaine kawai.
Murmushi ya khaleel yayi kawai, yasan momy bazata ta6a canjawaba kam, yad'ago hannunta nadama dake rik'e a hannunsa Wanda yasha Jan lalle da manyan zobuna Na zeenari har uku ya sumbata, cikin shagwa6a yace, "karki damu my first love d'ina, bazasu ta6a rabani dakeba, Dan kekad'aice mai Ibraheem khaleel duk duniya, ko baffah saidai yabiyo sahu.πŸ˜…
Bak'aramin farinciki kalam d'an NATA suka sakataba, Dan haka tace, " ALLAH yamaka albarka Ibraheem, kai d'ane ain alfaharin kowacce uwa, ALLAH yacigaba da tsareminkai kaji.
Amin mamyna.
Yanzudai yunwa nakeji, mizaki bani naci?.
Mikakeson ci to?.
Komike akwai zanci momy, sonake nad'anyi wani aiki.
OK tom bara Nagano mike a kichin d'in?.
To momyna, amma naji shiru, inasu Mufeeda?.
Mufeeda taje Raka k'awarta biki tunda yamma, basu dawoba.
'Yan biyu kuma sunje wajen baffanku kar6o kud'i, sunason zuwa shopping gobe.
Kai momy! Kai momy! ALLAH yarannan basajin magana, yanzu bana hanasu fitar dareba kota yamma gefin magriba?, amma harkika bar mufeedah zuwa biki?.
To kayi hak'uri, wlhy magiya taita yimin harda kukanta, wai k'awarsuce, bara nazo nakirata tadawo gida.
Baice komaiba yajingina da kujerar yana k'aramin tsaki.
Su hasnah suka shigo da murnar samo abinda sukaje nema, amma ganin ya khaleel sai kowacce ta kama kanta, suka aro nitsuwa suka yafama kansu. Ya khaleel barka da dare.
Idonsa yabud'e akansu, ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin fuskarsa da d'an sauk'in d'aurewa suka zauna a falon, amma kowacce a d'arare. Yana kula dasu amma yashare.
Saima yad'auki wayarsa yahau kiran mufeeda.
Harta tsinke bata d'aukaba, saida yay kira Na uku sannan ta d'auka gabda zata tsinke.
Wlhy nabaki nanda 15minutes, inhar baki bayyana agidaba sainaci ubanki adarenan, danhar wajen iskancin naku zanzo Na 6a66allaki 'Yar iska kawai.
Abinda yafad'a kenan ya yanke wayar.

gaba d'aya Mufeeda takid'ime, fad'itake nashiga uku ya khaleel yana gida, cikin hanzari take had'a inata-inata.
K'awayenta suka shiga tambayar lfy kuwa mufeey?..
Kai kubarni tafiya zanyi wlhy, ya khaleel yana gida shine yakirani yanzu, dayawansu sunsan khaleel d'in, harma damasu dakon soyayyarsa acikinsu.
Harbakin mota sukamata rakiya, dama birthday d'in wani boyfriend nata sukazo, babu wani biki...........


Anty Mamie zaune gefen baffah tana had'a masa dinner cikin nutsuwarta.
Tagama tahad'a komai agabansa tareda fad'in bismillah.
Murmushi yamata, cikin tsokana yace, "saidai kibani abaki".
'Yar dariya tayi, lallai baffansu, yakamatafa kasan ka girma, ga 'ya'ya ga jikoki, ko Najwa d'in Zuwairah aka aurar yanzu zama zatayifa.
girarsa yad'age yana fad'in ummyim shikenan kuma Dan inada jika data kusa isa aure bazanyi soyayyaba?.
Kanta ta girgiza masa tana murmushi, tace, " wane mutum, ai soyayya bata cancanci kasuwa daga gwarzo irin Abdallah naba.
Wata dariyar jin dad'i yayi, yagyara zama yafara cin abincinsa, sunayi suna hira har ya gangaro inda yakeson zuwa.
Yauwa nikam Bilkeesu su maleeka sun fad'a miki munhad'u da fad'ima a Jigawa?.
Kanta ta girgiza alamar a'a, tad'ora dafad'in kasan basusan wacece itaba shiyyasa bazasu kawo komai.
ALLAH Sarki Yaya fad'ima baiwar ALLAH, yanzu kotana inane da aure? Wlhy ina k'aunar baiwar ALLAHrnan baffansu.
Murmushi yayi, yad'auki ruwa yasha sannan yagoge bakinsa da tissue, idonsa akan aunty Mamie yace, "ai yanzu batada aure, mijinta yarasu wata biyar kenan, harma tagama iddah.
Wani zumud'in farinciki Anty Mamie tayi, cikin matuk'ar murnarta tace, " wayyo baffansu dama kadawo da ita d'akinta, wlhy danayi farinciki.
Shiru yayi yatsuramata idanu, yarasa Bilkeesu wace irin macece mai dattako da hangen nesa, (baya raba d'ayan biyu tasan sirrinsa) shine tabiyo masa ta wannan hanyar danta k'arfafashi, ( haka take, inhar talura da yadamu da Abu tokobai fad'a mataba zataita karantarshi harta fahimta, koda abinnan baimata dad'iba to insha ALLAH zatayishi danta faranta masa rai.
Rungumota yayi jikinsa yana fad'in Bilkeesu ALLAH yayi miki albarka, ketadabance acikin mata, amma kina ganin dawo da fad'ima gidanan bazai zama matsalaba?, kuma itama sainaga kamar bazata amincebafa? Dan wlhy ajigawa yitai tamkar bata sanniba.
Karka damu muyita addu'a insha ALLAH babu abinda zai faru sai alkairi, batun Yaya fad'ima kuma kabari zanje gareta dakaina, tunda kace zata aurar da yariya ko?.
Kansa ya d'aga mata.
Tace, "amma kasanarma Ammah?.
A'a dama kunakeji, amma nasan Ammah zatayi farinciki, dan tanason fad'ima.
Hakane, ALLAH yashige mana gaba.
Daga nan suka cigaba da tattaunawa, ak'asan ran baffah kam yana tunanin yanda zai tunkari sauran matan nasa, dukda yana ganin Na Umme Amarya mai sauk'ine, hajia babba Ce matsalar, tunda dama bason Fad'ima takeba, harta bar gidan basu ta6a zama lfy ba, kasancewar fad'ima Nada zafi, bata d'aukar raini gakowa.


Yanacin abinci tashigo, sai la6e-la6e takeyi, momy ce tace, " waike Mufeeda la6e-la6en mikikema mutanene?.
Da baki tama momy nuni da ya khaleel.
Momy tamaida kallonta ga ya khaleel daketa cin abincinsa hankali kwance, duk kuma abinda ke faruwa yana kallonsu ta gefen ido, amma yayi kamar baisan abinda akeyiba.
Ibraheem!.
Momy tafad'a tana ta6ashi a kafad'a.
d'agowa yayi yace, ''na'am momy".
Kayi hak'uri.
Momy hak'urinmi? Mikikamin?.
Baniba mufeedah.
Maida kansa yayi yacigaba dacin abincinsa, momy bar 'Yar iskarcan, tacemiki biki taje, amma k'arya takeyi.
Inataje to?.
Tafad'amiki da bakinta.

Momy tamaida kallonta ga mufeeda, inakikaje? bacakikaimin ana kamun seematu ba yau?.
Shiru mufeedah tayi tana tura baki gaba.
Ya khaleel yadaka mata tsawa, Dan ubanki badake ake maganaba?.
Zabura tayi gefe, cikin rawar baki race, momy wlhy fa....um....um.
Um...um...mi? Mufeeda wai mikikeson maida kankine? Nifa wlhy halayenki sunfara bani tsoro, lfy lau narabu da zuwairah da Shukrah, ammake naga baki biyo hanyar hakanba, to wlhy bazan d'aukaba, babanku zanma magana yahad'a aurenki danasu Sultan wlhy, bazan iyaba, banyi iskanciba, bazan haifi 'Yar iskaba.

(Nace, hummm momy kenan, kin salwantar da 'ya'yan mutane, amma kike tunanin naki zasu sami tsaro, a'a momy, ba'a shuka shinkafa agirbi alkama.🀣🀣).

Ya khaleel daya gama cin abinci yature gefe, k'afafunsa yakwashe yamaida saman table d'in bayan Hasnah takwashe kwanikan. Yace, ''momy harda laifinki, yarannan babu maifad'a musu basuyi daidaiba agidannan saidai Idan inanan, yanzu ace kamarsu Sultan bazasuga yaranana Na Abu mara k'yauba su tsawata musu? haba momy mana, to wlhy yanzu wani abokinane Hasheem yake sanar dani yaganta a wani Hotel suna rawa suda samari, wai na birthday d'in boyfriend nasu.
Amma dayake ita batada mutunci saitace dake biki suka tafi, ALLAH yau saina kusa 6allaki agidanan mara hankali kawai, saboda kingama degree kinfara aiki shine kanji ke hayak'in iskanci ko? To zan sauke mikishi yanzunnan yay maganar yana mik'ewa kanta
Kafin tayi yunk'urin guduwa kam ya cafkota, damaruka yafara mata, tad'an daku kam tasamu tagudu d'aki, momy batace komaiba, Dan itakam gwara yayma mufeedan haka kartaje takwaso mata abin kunya, kishiyoyi susami abin yimata gori agida, wannan yasa ta kauda kanta bata hana ya khaleel dukan mufeedar ba..........πŸ–Š


*_Bara mulek'a mutanen UK su Aysha sholy_*πŸ€ͺ









*_gaisuwaπŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€_*
[8/10, 4:28 PM] Aisha Galadima: *_TypingπŸ“²_*



🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🀲🏻😭



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)

2⃣3⃣

*_yaukam tafiyar tawa akawai 'Yar rakiya, Dan miss xoxo tahad'o kaya itafa sai UKπŸ‘œ._*
*_Tagaji so take tagano muku Aysharku🀣_*
Idan munrasa kud'in jirgin dawowa saimu mak'ale a can kawai, dama kullum da ji6in goshi nake had'a natafiyarπŸ˜‚.



*_Islands (UK)_*

_Da acefa zan aureka, zan biyayya abayanka._

_ina sonka, nayaba da halinka, k'yanjiki da surarka, sahibi da hannunka kaban ruwa._

_ninai sa'a kan masoyi mai fara'a, kaikafara sa shadda duk garinmu an shaida d'an uwa._

K! Wai lafiyarki kuwa?. Meerah tafad'a tana zungurin Aysha dake kwance akan gado idonta arufe tanata rero wak'ok'i, tayi wannan tasaki takama waccan.
Firgigit Aysha tatshi zaune, ganin Anty meerah sai kunya takamata tayi k'asa dakai tana murmushi da fad'in Anty meerah yaushe kikazo?.
Ya za'ayi kisan nashigo sholy? Kinfad'a soyayya, dama nadad'e ina zargin hakan wlhy, meerah tayi maganar cikin damuwa da fargabar kodai Aysha tafad'a tarkon wani cikin yaran turawannan?, karfa ayi gudun gara, afad'a gidan zago kuma.
Meerah tace, "sholy please kifad'amin gaskiya waye zai wargazamin tanadina danakeyi akanki?".
Yanda meerah tayi maganar cikin damuwa yasaka Aysha d'ago manyan idanunta dake cike da gashi ta saukesu kan Anty meerah, kaitashiga girgiza mata cikin sanyinta tace, " wlhy Anty meerah babu kowa".
To amma Aysha wannan wak'ok'in hausar dakikeyi koda yaushe suna nunamin akwai soyayyar wani aranki, kada ki 6oyemin, bazan hanaki sonshiba, zanduba cancantarsane kawai. Dan ALLAH kada ki 6oyemin, inhar kind'aukeni yanda na d'aukeki.
Ajiyar zuciya Aysha tasauke tareda had'iye yawu, muryarta Na rawa alamar shirin yin kuka tace wlhy Anty ba anan yakebafa, tun a gida Nijeria ne, kumafa nima banyarda sonshi nakeyiba, Arena ce tacemin sonshi nakeyi.
Meerah ta girgiza kai tana kallon ainahin k'uruciyar ayshar, matsowa tayi kusada ita takama hannunta, to nayarda ba sonshi kikeyiba, amma fad'amin wanene?.
Aysha tad'ago ido tad'an kalli meerah saikuma tayi murmushi, ALLAH Anty ba sonshi nakeyiba, haka kawaidai nakejin nadamu dashi, kofa nature tunaninsa saiya dawo, ninamasan yafi k'arfina.
Hhh aini sunansa nace fad'amin my lil.
Kai Anty ya khaleel nefa.
Bak'aramar dariya meerah tayiba, wai Aysha tasan soyayya, takatse dariyar tana kallon aysha, karki damu, Indai ya khaleel ne baifi k'arfinkiba, kedai kitsaya kiyi karatu, duk sanda yaganki dakansa zai soki, kuma zakice ninafad'a miki.
Aidama tuni nafahimci wani Abu, tunda kika bani labarin gidansu, yanda kike Shiga shauk'i inkinzo Kansa da kurantashi dakikeyi nagane yayi kamun zuciyar sholynaπŸ˜‚.
6oye fuskarta Aysha tayi tana dariya.
Meerah kuma taita tsokanarta.

A6angaren karatun Aysha kam saidai muce Alhamdullahi, komai yana tafiya yanda yakamata kam, tana k'ok'ari dak'ara fahimtar abubuwa yanda yakamata, Arena kuma nak'ara bata taimako wajen zaburar da ita abinda bata saniba.
Wad'annan abubuwan suka had'u wajan bunk'asa ilimin Aysha da k'arin kwazonta, ayanzu haka suna shirin yin exams, wannan yasaka ayshar sake maida hankali sosai, meerah ma Na taimakonta wajen k'yautata mata da d'auke hankalinta ga damuwa ko tunanin gida da ayshar kanyi akoda yaushe, inhar ta tuno gida takan zauna tasha kuka harsai taji tagaji, meerah bata hanata, Dan aganinta kukan zai rage mata nauyin zuciya da damuwarta.
Alhmdllh itama meerah a 6angarenta komai natafiya yanda yakamata, tayi tuba Na gaskiya, duk abinda tasan zai ta6a imaninta tana guje masa, kullum da k'aryar dazata sambad'a saboda kartaje club, bata shaye-shaye yanzun, Anty glory tatsareta ranar da tambaya akan canjawa datayi.
Sai kawai meerah tafashe mata da kuka.
Hankalin Anty glo yatashi sosai, tashiga tambayarta miya farune?.
Meerah kan ta karkace ta sambad'o k'arya wai sunyi fad'a da saurayinta, Dan takamashi yana muna furtarta da wata budurwa.
Anty glo....tayi tsaki, yo saime? Shine zakiyi kuka akansa? Kema kiwatsar dashi, gari dayawa wai mutuwa tashiga birni.
Karin maganar Anty glo.... Tasaka Aysha dake gefe tana duba books d'in school NATA gumtse dariya.
Anty glo....tacigaba dafad'in kibarsa nasan wani zaizo aii, kinada k'yanki da k'uruciya, shine banza Dan dama nagaji da ganinku tare.
Dama madam Joy ta turomin kaya daga Nijeria suna zuwa Zamfara had'aku keda Aysha da besi, yanzu kihuta kawai abinki harsai kinsha gyaran kece raini.
Gaban Aysha yafad'i, itakam haryanzu fargabar kaidinsu Anty glo.... Nabata tsoro, kuzo Ku ajiye yara kawai Dan biyan buk'atarku, aranta tace, "ALLAH yamana tsari daga sharrinku".
A can kuwa meerah cewa tayi inayinki Anty glo..... d'inmu, aikinki Na kyau tayi maganar tana rungumeta, aranta kuwa fad'i take tsinanniya aniyarki tabiki, awanan karon tuba nayi Na gaskiya, insha ALLAH kun kusa nemanmu kurasama, baradai Aysha takammala karatunta.
Anty glo....taji dad'in furucin meerah kam, sai washe hakwara takeyi.
Ahaka happy tashigo ta samesu, daga ita sai bes iyakar cinya, ko bra babu ajikinta, 🎁abinda ke hannunta tamik'ama Anty glo....., waigashi wani yakawo abaiwa sholy.
Ido Aysha tazaro waje, Anty happy nifa?.
Eh ked'in, cewar happy.
Kar6a Anty glo.... Tayi tabud'e, πŸ’filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma d'an kwalba mai kyau anzuba k'ananun kifin roba aciki da ruwa, sunata yawo acikin ruwan, wata 'Yar takarda Anty glo.... ta zaro anrubuta.
*_for you! my Hayatee._*
Cikin mamaki duk suke kallon Aysha, Anty glo.... tamik'ama Aysha kayan.
Itamadai juyasu take tayi, amma tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tata6a jin k'amshinan, to amma a ina?, wannan itace tambayar.
Sholy waye ya aiko miki?.
Wlhy Anty glo....ban saniba nima?.
Anty glo.... Tamaida kallonta ga happy, happy waye yakawo?.
Wata 'Yar budurwace Anty glo....
Aysha tayi saurin fad'in ALLAH Arena cemato.
Kai amma ta rud'ar dani.
Suma su Anty glo.... Duksun amince hakad'inne.

(Nikamdai nace ALLAH yasa to)🀭



Washe gari koda suka had'u a makaranta Aysha batayima Arena maganarba, tace, "inhar batayi mataba, itama bazata yimataba ko".
Har suka kammala exams d'in kuwa arena batayi maganarba, itama Aysha ta share batayimataba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, su Aysha sunkammala exam d'imsu, Alhmdllh tayi kwazo kam, dantasamu nasarar shiga grade 2, (kunsan sufa ba jss ko ss suke cewaba) kuma kwakwalwarka ke kwatarka sukam.
Sosai Aysha tak'ara maida hankali akaratunta, Dan Arena Na taimakonta sosai, turancikam anwuce wajen tuni, idan tana zuba yaren turanci saika d'auka haihuwa da girman cance, abincinsuma tafara kwarewa daciπŸ˜‚.

Yau takama weekend basuda school, Dan haka meerah tace, ''tashirya suzaga gari".
Dama haka take mata, inhar batada school ko wani uzuri sai Anty meerah

2 Comments On CIKI DA GASKIYA PART 1
avatar
nusaiba-4-8

1 year ago

Reply

Inason in karanta saboda Ina Jin Dadin littafin marubuciyar

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to nusaiba-4-8

ki yi subscription namu sai ki downloading

Please Login or Register in order to submit comment