Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



*Aisha ibrahim maina (mmn mummy) ga page ɗinki nan takanas na ta tashi na hana kaina bacci nayi typing ɗin shi saboda ke, don haka ashaa karatu lfy, ga girki nan a ƙasa da fatan za a ƙawata bbn mummy da shi*


*my asmy i lobe u cikin kwanon shaaa*😘 🤣🤣🤣🤣



*Amrath amrath & asmau ta hikima grp asmaun sabit na miƙo miki 😘, my asmy ba ke ba ɗayar Allah yasa ta gane kanta*



P⃗a⃗g⃗e⃗ 13🌹




Ɗakin anty fannah na bita inda ta haɗa min turaruka masu kyau sosai, daga nan sai tace min wai zan rakata shopping, kasancewar bana fita yasa ni yin murna sannan na sanar da mummy abinda mummy tace shine

"ki dawo da wuri saboda ɗora abinci" naji daɗin yadda bata hanani fita ba ko tace sai na tambayi ɗan renin hankalin can


Kuɗina na wajen ta na karɓa kasancewar kuɗin aiki na a wajen ta yake na fito sai ɓangaren anty fannah inda na tarar da ita ta gama shiryawa muka kama hanya



Shoprite muka nufa don yin siyayyar mu, wurin man shafa wa muka je sannan sai wurin turaruka, sutura, nai mamakin irin kuɗin da anty fannah take kashe wa kamar bata san ciwon su ba



Rasa me zan siya na yi, sai dana ga alamar muna neman hanyar fita sannan nace wa anty fannah


"ni fa ban siya komai ba kuma ga kuɗina na zo da su" kallo na tayi sannan tai murmushi


"ai duk wannan siyayyar taki ce, jiya isma'il ya bani kuɗi kuma ba abinda zanyi da su don haka sai nace bari kawai in kashe miki su"


Riƙe baki nayi ina kallon ikon Allah ni na rasa bakin gode mata ma, can dai sai na ɗan buɗe baki sannan nace mata "na gode"


Yi tayi kamar bata ji ba, muka je counter ta biya sannan aka loda mana kayan mu a boot ɗin motar muka kama hanya


Na ɗauka gida zamu wuce sai kawai ganin mu nayi a saloon, muka shiga, ba kowa don haka muna zuwa aka hau yi mana gyaran kai, inda hair dreeser ɗin ta buɗe kaina wanda ya kusan sati uku da wata shegiyar kalba da nayi wa kaina



Sai da ta tsefe min sannan tai min steaming ɗin sa tunda bana retouching kan nan nawa ya sha gyara dama gani da gashi, don ma bana kula da shi,


tuni ya sauko har baya na, su ma kansu mutanen shagon sai yaba gashin nawa suke anty fannah ce ta kalle ni sannan tace


"kin ga waɗan nan ma sun yaba balle sabit" haɗe gira ta nayi

"ni wallahi anty fannah indai don sabit kike min wannan gyaran gwanda ma ki daina don ni ba san shi nake yi kuma babu abinda zai haɗa ni da shi"


"ko kaɗan ba don shi nake yi, asmau buri na ki zama mace yadda ko sabit ya sauwaƙe miki zaki zama me class yadda samun namijin da zai soki bazai yi wuya ba, kinga maza ba abinda suke so kamar mace me gyara, gyara shine mace


Amma dube ki dubi fuskar ki tukunyar kitchen ɗin ma tafi fuskar ki samun kulawa, haba asmau in ba kya son sabit mu bar zancen shi a gefe akwai wani ƙanina wallahi irinku yake so, ke dai kawai abinda nake so da ke shi, duk abinda na siyo miki kiyi amfani da su har ki goge wannan baƙin naki me dusashewa ya koma baƙi me kyau a lkcn zan sa sabit ya sake ki sannan in haɗa ki da ƙanin nawa wallahi zaki sha gata"



Ta ƙare zancen ta da murmushi daɗi ne ya cika ni ganin zan samu wanda zai soni, amma ni da sabit haihata haihata, har aka gama mana gyaran kai da kuma pedicure da manicure tana bani duk wasu tips na gyara mace inda ni kuma nake recording a ƙwaƙwalwata



Sai gab da magariba sannan muka koma gida, don haka kawai sai na ɗora wa gidan jollof na spag ɗuk da de na san sabit baya son



A zuciyata nace in bazai ci ba matar sa ta dafa masa wani ai tana koyon girki (a ƙaryar ta) anty fannah ce ta tana ni muka gama sannan ta sani yin wanka na shafa sabon man data siyo min tare da turare na kwanta



Dama haka ƴan gayu suke ko ba miji a kusa da kai sai ka baɗe jikin ka da turare ka nemi lfyr katifa ka kwanta hmmm nima in shaa Allah sai na zama ƴar gayu sai na kwatar wa kaina ƴanci daga wajen sabit sannan sai na auri mijin da zai ji dani murmushi nayi dana tuno da ƙanin anty fannah



********************



Cikin hukuncin Allah nima na fara canza wa, wannan baƙin nawa wanda yake tsokane idon mutane ya fara kyau inda na koma chocolate colour sannan ƙamshi ya fara ratsa ni amma duk da haka sai anty fannah tace be mata ba don haka sai muka fara shirin zuwa maiduguri wai zata ganin gida inda ni kuma zan mata rakiya


Da ƙyar aka shawo kan mummy ta yadda muje muyi kwana uku, inda anty fannah tace

"taga tafiyar dawowa ba sai lkcn da muke so ba"


Ban sani ba ashe ta samu sabit sai tayi masa zancen tafiyar tamu buɗar bakin sa sai yace


"in ta tafi wa zai dinga mana girki
Wai yarinyar sam bata san aikin ta bane, bata san biyan ta ake ba zata wani tsiri tafiya to ban yadda ba in kuwa ta sake ta biki wallahi sai na zare a albashinta" ya faɗa a fusace


"sabit matar ka ce faa kana nufin ba ka hanata bane saboda matar ka ce a a ka hanata ne saboda abincin da take maka anya kasan haqqin aure kuwa"


Wani banzan kallo ya bita da shi sannan tace

"itace ta ke gaya miki ni mijinta ne, bata gaya miki sharaɗin auren namu bane, wai yarinyar nan me take nufi ne, ni me zanyi da ita Allah ya sauwake min zama da baƙar mace ai ni sai fara kamar yadda nake farin nan"



Babu yadda anty fannah batai ba akan ya gaya mata yadda asmaun take a wajen sa amma duk kalmar da zata fito daga bakin sa game da asmaun ta ashsha ce da kuma yi wa kansa Allah ya tsare shi da baƙar mace


"shike nan tunda ka rainata saboda baƙa ce ka bata takarda ta inya so sai ta samu wani ta aura wanda zai so ta"



Nuna mata yayi ko a jikin sa sannan ya ƙara gaba, tsayawa tayi tana ƙare masa kallo lalle ma sabit ɗin nan ashe haka yake,


Shi ya ɗauka kyan mace a fuska ne kawai be san duk kyan mace in dai bata haɗa abubuwan da ake so na zama cikakkiyar mace hoto ce kawai kuma na wani ɗan lkc ne da an ɗan zauna an zama jiki shike nan sai kyan ya gushe kuma sai a koma zaman gaskiya zaman da ba kwaskwarima ba ƙyalƙyal banza


Amma shi sam kamar be fahimta ba shike nan mu zuba ido ni da kai sabit zamu ga wa zai zo nan gaba yana ƴar murya, lallai ma sabit ɗin nan ta kuma maimaitawa tana yin gaba abinta



Shiri muka soma yi na tafiya, ni dai murnata ɗaya zan huta sannan zanje in haɗu da wanda zai soni kamar yadda nake so, sannan in samu kulawa



Cikin ikon Allah muka kama hanyar maid. ni da anty fannah tafiyar da ta canza min rayuwa, wacce ta fidda ni ƙuncin nan sannan ta saka ni cikin wani hali da babu abinda zance sai godiyar Allah



Muna sauka muka wuce gidan su anty fannah, babban gida ne nayi mamakin irin girman gidan su, sassane daban daban, family house ne wanda yake cike da iyalai daban daban


Mahaifin anty fannah shine babba a gidan kuma shine me abin hannun gida duk da dai kowa yana da nashi amma nashi ya fi na kowa


Ɓangaren su ƙato inda mahaifiyar anty fannah ce kawai mata a wajen bbn su, tunda muka sauka nake zare ido inga ko zanga ƙanin natan da take cewa zata haɗa ni, wayaga azarɓaɓi



Sauka ta musammam akai min, kasancewar yaren su na kanuri suke yi yasa sam ban ma gane me suke nufi ba amma kuma kamar da ni suke don naga alamar sukan ɗan saci kallo na sannan su ci gaba



Kunya ce ta kamani, ko anty fannah tana wa mmn bayanin nice wacce za ta haɗa da ƙanin ta Allah ya sa na faɗa a raina cike da kunya




Sai da suka gama tsab sannan anty fannah ta ja ni zuwa ɗakinta muka ci abinci inda take gaya min cewar zamu koma gidan ƙanwar mmn ta da zama acan za ai mata gyara jiki ne in ina so sai in faɗa sai ai min



Ganin cewar jikina a haka is ok ya sani cewar bana so nafi son gani na a haka, sam bata tanka ba ko ta musa min sai da muka gama komai sannan muka shirya inda muka kama hanyar gidan kanwar mmn tata



Mun isa gidan ana kiran sallah la'asar gida ne de irin namu na mutan kano, tsarkar gida ne babba sosai sai ɗakuna da suka zagaye gidan sai banɗaki sannan wani tafkeken kitchen



Kusan rabin tsakar gidan cike yake da shirgi, da tukwane waɗanda duk aka ajiye su, sai uban itatuwa a buhu buhu sai kace ƴar me magani



Gidan banda ƙamshin turare babu abinda yake yi kamar ma'aikatr sarrafa turaruka, mata ne sun kai kusan 20 kowacce da abinda take yi, daga masu haɗa turare sai masu sassaƙa icce ko dai wani abu.


Suna ganin shigowar mu su hau yaren su, wanda sam bana ganewa amma daga dukkan alamu murnar ganin anty fannah suke, kayan mu suka karɓa, sannan suka shigar mana da shi wani ɗakin inda muma muka shiga bayan mun gama gaisawa



Wata mata ce zaune a kan tafkeken carpet ɗin daya malale ɗakin tana ta magana a waya wanda sam ban san me take cewa ba, amma fuskar ta taf da fara'ar ganin mu sannan sai ta dinga ma na nuni da hannu na alamar mu zauna


Wuri muka samu muka zauna sai da ta gama tsab sannan ta juyo gare mu, inda anty fannah ta ɗan kƙara durƙusawa tare da gaishe ta da yaren su ni ma durƙusawar nayi amma sai nayi gum



Anty fannah ce take mata bayanin gaishe ta nake, da hannu ta saka ta yafito ni inda ni kuma na tashi na ƙarasa kusa da ita


Yaran su ta dinga yi tare da ƙare min kallo ido na kai kan anty fannah sai take cewa

"tace kina da kyau" kunya ce ta kamani na sunkuyar da kaina


Wani ɗan mai ta ɗakko kusa da ita a wata ƙatuwar roba ta kwaɓa min a fuskar ta ba abinda man yake sai ƙamshi


A hankali ta fara shafa min shi sai daya game fuskar tawa gabaɗayan ta sannan ta soma murza min kamar nayi kuka don zafi amma sai na dake


Sai da ta gaji don kanta sannan ta dena ta juya tayi wa anty fannah yaren su wanda anty fannah tabi matar da murmushi nuna jin daɗin ta



Wai magunguna ta ɗauko sannan ta kira wata mata inda ta dinga ɗiba tana yi wa matar bayanin yadda za ai amfani da su ni dai ko kalma ɗaya bana fahinta,


Sai da ta gama sannan anty fannah tace min

"tashi ki bita ita zata miki gyaran jikin" tsayawa nayi na saki baki sai da ta ƙara maimaita min sannan na tashi na bayan mayar


Wani ɗaki naga mun shiga wanda ada ban ganshi ba domin yana ƙarshen gidan, muna shiga ɗakin kamar kitchen haka yake saboda tsabar tarkacen sannan tukwane sai wasu robobi manya manya ga kuma wani abu da akayi shi kamar da icce me ko me gashi nan dai kala kala


Wani ƙaton baho ta ɗauko ta zuba wani ruwa ta gama haɗe haɗen ta sannan tai min nuni da in yi wanka da ruwa, bokiti na ɗauka na zundumin ruwan sannan na kama hanyar toilet don in watsa, ko da na shiga banɗakin sai ga matar ta biyo ni


Tsayawa nayi ina kallon matar nan kar dai tace min itace zata min wanka, tsare ta nayi da ido don in san me take shirin yi



Wani riga ta ɗauko min ƴar ƙarama kamar shimi amma half vest, da wandon sa tace min in saka, ganin na ƙi karɓa ya sa ta fara min faɗa


Karɓa nayi sannan na juya mata baya, kayan sababbi ne na saka sai da na gama sannan ta juyo,


Wani botiki ta ɗauko, ta lakuci wani sabulu sannan ta fara gurza min, zafi ne kawai yake ziyartata


Ko ina na jikina wanda yake waje haka ta dinga bin jikin nawa tana dirza tana ƙara sheƙa min ruwan tare da ƙara saɓar sabulun tana ƙara wanke ni


Sai da ruwan ya ƙare ta kuma fita ta kuma ƙarowa, ko da ta dawo, sai ta ɗibo ruwa tace min in ɗauraye jikina



Ruwan na zuba na ɗauraye jiki na sannan ta kuma zaunar da ni akan wata kujera inda ƙasan kujerar




Turiri yake fita yana ratsa ni ta ƙasan sannan jikina kuma tana ta saɓar min shi kai ranar na gurzu sai kace za a canza min fata



Sai da aka gama tsab sannan na cire rigar jikina da wandon na ɗauro zani na fito, inda tazo ta sakani a cikin wani abu shi ba kwando gashi nan dai


Turare ne yake ta tashi a cikin sa gabaɗay jikina na ciki in banda kaina da ke waje, gaskiya ranar na sha gashi


Shi kanshi kai na ba a barshi a baya ba, haka ya sha gyara sai wani ni'imantaccen ƙamshi yake fiddawa



Kwanan na 7 sati ɗaya kenan ana min wannan gyaran wanda nasan dana gama zan haɗu da ƙanin anty fannah nasan yana ganina zai ruɗe yace saini


Ga kuma na sha wanda shi wannan da anty fannah muke sha, lkcn da aka gama aka bani izinin kallon mudubi na ɗauka ba ni bace 🤣


Ɗau haka na yi da baƙin nawa amma ba kamar na da ba, ƙwal haka na koma kai sai kayi zaton daga inji na fito ga wani ƙamshi daya ke tashi a jiki na kamar wacce tayi wanka da ruwan turare sannan ga santsi da laushin duk na haɗa


Ni kaina daɗin taɓa fatar jikina nake yi balle kuma wani ya taɓa, ita kanta anty fannah sai yaba min take da irin wannan haɗuwar dana ɗauka



"kin ganki kuwa asmau ai wallahi yanzu idan sabit ya ganki sai ya ruɗe ya dena kula wannan ja ja amalen tasa"


Zunɓurar baki nayi sannan nace

"ni fa ba don shi nayi wannan gyaran ba fatana Allah ya haɗa ni da mijin da zai so ni kamar ba gobe ba wannan ɗan renin hankalin ba"


Dariya tayi sannan tace

"hmmmm shima sabit ɗin bari ya afka tarkon nan zaki ga love 😍 har sai kince ya ishe ki" ni sam maganar wani sabit ma bana so balle inyi tunanin zai so ni



Me ya haɗa ni da shi ai na riga na gama da babin sa, haka muka ci gaba da hira na so ace ta kuma sako zancen ƙanin natan sai naji bata sako ba Allah dai ya sa ba ta manta bane



Satin mu biyu a maid. muka kama hanyar abj, cike da samun nasara daban daban barin ma ni ƙara kilewa da nayi da kuma gogewa,



Lfy lau muka sauka agida inda na wuce part ɗin mummy directly don inyi reporting na dawo, nai mamakin yadda ta saki baki tana kallo na kamar bata taɓa ganina ba


"mummy lfy ko sai kace yau kika fara ganina"

"asmau wannan canji haka sai kace inji kika shiga a maidugurin, kinga yadda kika koma kuwa lallai maa shaa Allah wannan gyara yayi sai dai kawai ace wa sabit ya kawo kuɗi"


Ɓata rai na nayi sannan nace


"mummy sabit ɗin daya ce in matar sa ta iya girki sakina zai yi nima ai a hakan take, ina gama haɗa kuɗin da nake so ko matar sa ta iya girki ko bata iya ba dolen sa ya ƙyale ni in tafi"


"shi yace miki idan matar sa ta iya girkin zai sake kin" shiru nayi don be faɗa min haka ba amma alamu ne suka nuna min


"asmau har yanzu sabit be san irin baiwar da Allah yai miki ba amma daya gano hakan wallahi bazai iya rabuwa da ke ba, ni ma kaina bazan so hakan ba kuma bazan bari ba"

Tsayawa nayi ina kallon ikon Allah naga alamar matar nan ma son kanta ma yayi yawa don haka nasan duk yadda zan fadalta rashin son zama na da sabit baza ta gane ba


Bana son shi kamar yadda shima yake ikirarin rashin sona da baya yi, miƙewa nayi sannan nace

"mummy ni na gudu kitchen gwanda inje in ɗaura abincin gidan don kowa yasan na dawo" murmushi kawai tayi sannan ta gyaɗa kanta inda ni kuma na fice




👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳


*curry rice served egg sauce and banana cocktail*

*curry rice*

```ingredients```

-shinkafa
-curry
-gishiri

*method*

1) ki zuba ruwa a tukunya idan ya tafasa sai ki auno shinkafar ki ki wanke ki zuba ki barta tayi tafasa ɗaya sannan ki sauke ki tace ruwan ki wanke ta

2) ki ƙara zuba ruwa amma ba dayawa ba yadda zata ƙarasa dafa miki shinkafar, idan ruwan ya tafasa sai ki zuba curry da gishiri ki barshi kamar minti ɗaya haka sai ki zuba shinkafar ki ki rage mata wuta a barta ta ƙarasa idan ta dahu sai a sauke



*egg sauce*

```ingrdients```

-egg
-attaruhu
-albasa
-maggi
-sardine


*method*

1) ki jajjaga attaruhu da albasa sannan ki a jiye su

2) ki samu sauce pan ki zuba mai da albasa kaɗan idan man yai zafi sai ki zuba jajjagenki sai ki bari ya tafasa


3) kasancewar ba ruwa don haka bazai ɗau lkcn ba, ki zuba maggi, da sardine (bayan ki dagargaza shi) sai ki juya

3) ki fasa ƙwai a bowl daban sai ki kaɗa, idan miyar ta ɗan ƙara soyuwa sai ki zuba kwan sai a barshi kar a juya amma a rage masa wuta


4) idan ƙwan ya dahu sai a ɗan juya kaɗan don kar ƙwan ya dagargaje sai a saike



*banana cocktail*

```ingredients```

-banana
-sugar syrup
-milk
-flavour


*method*

1) ki tasafa ruwa kaɗan da sugar idan sugar ta narke sai ki sauke ki juye don ya huce


2) ki zuba madara a cocktail bowl sai ki zuba syrup da flavour ɗin ki sai ki saka a fridge don yayi sanyi, idan an tashi za ci sai a yanyanka ayaba ƙanana a zuba sai aci a take


👩🏽‍🍳 *BON APPETIT*👩🏽‍🍳



*ASMA'UN SABIT*
[10:33PM, 5/2/2018] ‪+234 806 399 9164‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 14🌹




Gyara jikina ya kankama ko dana koma gida ban dena ba sai ma abinda ya ƙaru yanzu na zama ƴar gayu don anty fannah har tsokana ta take yi wai na kile na haɗu saura haɗuwar mu da sabit


Na kan ɓata rai a ni yanzu na fi ƙarfin sabit sai wanda zai so ni mu gwada soyayya tare wacce zata kasance a tsaftace ba mix ba irin ta sabita ba



Duk wannan abun da nake bamu taɓa haduwa da shi ba tunda ba ɓangaren sa nake zuwa ba tunda badia tayi ɓari Allah ya yaye min wannan bautar


Sai dai ita badiar wacce ganina da ita na farko bayan na waye sai da ta tsorata da ganina inda ta dake sannan ta fara kushe ni har da cemin


"inde ma don sabit kike yi to ki sa ranki a inuwa don bazaki taɓa birgeshi ba sabit sai ni kaɗai" sam ban raga mata ba nima clna ce mata


"ai ni mijin da zan aura sabo zai kasance dal a leda ba saura ba" maganar ya ƙona mata rai kuma ƙiri ƙiri ta nuna hakan



Tana shirin mai da martani ne sai anty fannah don haka sai ta haɗe rai tare da barin wurin tunda basa shiri dama ko da anty fannah ta tambaye ni me ya haɗa mu sai nace mata ba komai


Don bana son ta ga ko na zaƙu in haɗu da ƙanin ta na fi son ta fara yi min maganar sa da kanta bana son nuna gazawa ta bayan na zama me class 😎


Rannan da safe na tashi mai na ya ƙare don haka sai naje part ɗin anty fannah na faɗa mata in zata fita zan bata kudi ta siyo min, sai ma tace min inzo bayan azahar sai muje siyayyar tare don itama zatayi


Da murnata na koma na je na ɗauka girki kafin wannan na gama na bayar aka kai kowanne part nashi sannan na ɗauki na mummy don in kai mata


Da sallama na shiga falon na ajiye mata, tunda na ɗau gyara na zama kamar wata sabuwar aba a wajen mummy kullum na shiga sai tayi ta bina da kallo kamar bata taɓa gani na ba








Yau ma haka na kai mata har nayi hanyar waje zan fita sai ta kira ni, dawowa nayi na tsaya sai kuma ta rasa abinda zata faɗa min can dai sai tace


"kije kice wa badia ina son ganin ta" rai nane ya ɓaci ba abinda na tsana daya wuce wai inje part ɗin sabit


Jikina a saɓule haka na fice na kama hanyar, na zo dai dai hanyar da zan shiga part ɗin sabit ne naga anty fannah


"muje ko don na gama shirya wa" ta faɗa min


"gani nan zuwa mummy ce ta aike ni wurin anty badia" na faɗa murmushi naga ta saki sannam tace min


"maza kije ki dawo kuma ki dinga tafiya da nutsuwa kamar yadda na koya miki" ban kula taba hmmm kaji ta tafiyar da tace min sai a gaban mijina zanyi shi shine take son inyi shi zan shiga part ɗin wannan mara *M* ɗin


Ƙara sauri nayi ko dana ga na kusa zuwa ƙofar falon sai na saka gudu don inje in dawo da wuri,


Kiciɓis muka ci da wani dai dai corridor ɗin da zai sada ni da ƙofar falon, ruƙo ni yayi wanda da badan ruƙon ba da tuni nayi ƙasa


Ko da nayi gaining balance ɗina maimakon ya sake ki sai ya ƙara riƙe ni tare da shaƙar ƙamshin da nake yi



Can sai ya sassauta min riƙon inda ya kwantar da ni akan hannun sa muka haɗa ido *WAT* sabit ne



"kina gudu ina zaki je, dubi jikin ki lenge lenge kamar bakya cin abinci da badan na riƙe ki ba da tuni kinyi ƙasa kuma irin masu jikinku basa wahalar karye wa"





Please Login or Register in order to submit comment