Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara ɗaukar action ni kuma a matsayina na mace a bani damar duba wa ko zan iya manage da shi amma sam abin ba haka yake ba nice ma zan cusa kaina lallai mummyn nan har yanzu baki san wace asmau ba



Da yamma ina cikin yin dinner na kusa kammalawa ma sai naji call na intercom ɗin kitchen ɗin yana ringing kasancewar ba kowa ya sani zuwa ɗauka,


"hello" naji ance ko bacci nake yi nasan muryar ɗan renin hankalin nan amma sai na nuna ban sani ba


"hello waye" na amsa

"mijinki ne" na ji ya bada da amsa, murmushin mugunta nayi sannan na mai da masa martani bayan na maƙe muryata na shake ta sannan na gyara ta


"kana nan ƙalau ya gidan da komai da komai wallahi ina kewar ka sosai" ina jin ɗan murmushin daya saki sannan yace min

"da gaske"

"zan maka ƙarya ne kasan ni kasan zuciyata kasan banda wani sai ka, lkc kawai muke jira ya kasance mu kasance waje ɗaya har abada"


Daɗine ya lulluɓe shi kamar me, ni kuwa da yake nasan abinda nake shukawa ya sani ƙara sakin baki sai faɗa masa kalaman soyayya nake yi shi kuma yana biye min sai can dana ga ya shiga sosai sai nace masa


"ya maidugurin kuwa, Allah dai ya san ƴam matan can basa kalle min kai dan sunga bana kusa da kai" shiru yayi na ɗan wani lkc yai jim


"ABDUL baka jina ne" na kuma maimaitawa


"uban waye abdul" na ji ya faɗa, sai da na ɗauke phone ɗin daga kunne na na ƙyalƙyala dariya ta sannan na mai da ta na kuma cewa

"ba abdul ɗina bane na maiduguri ba, don Allah waye ya kira ni sannan yace min matar sa" wani ƙasurgumin zagi da luluƙo ya antayo min ni da abdul ɗin ya sani cire phone ɗin daga kunne na na kuma ƙyaƙyacewa da dariya



"Abinda kike yi Kenan dama da auren ki to yau Allah ya tona miki asiri kuma wallahi zaki san baki da wayo" sai da ya gama bala'in sa sannan ya kashe wayar



Dariya na ci gaba da yi gobe ma ka kuma kirana, ni abin ma dariga ya bani wai mijin ki ne, ko ta ina ya zama mijin nawan mijin suna dai girki na na cigaba da yi ina yi ina maimaita conversation ɗin mu ina dariya ni kaɗai lallai yau na kunna sabit



********************


Takaicine ya ishi sabit har ya rasa yadda zai yi, tun yana kwance ya tashi ya zauna ya kuma kwanciya amma duk da haka ya rasa mafita, ya ze yi da wannan ƴar iskar yarinyar


Wai da auren shi akanta amma take kula wani ƙato, har da cewa lkc kawai take jira su kasance tare, kenan da take nufin kashe auren da gaske take



Gaskiya da sake ya za ayi ma in bar ta ta tafi, lallai ma dole ne in samu mafita, mummy ce kawai ta faɗo masa a rai, lallai mummy ce kawai zata iya kawo ƙarshen wannan lamarin



Miƙewa yayi ya nufi ɓangaren mummy sam be nuna mata komai ba kawai sai yace mata


"mummy kinga badia bata nan part ɗin nawa ba mace don haka me zai hana ki saka waccen yarinyar ta koma tunda akwai spare ɗaki a ƙasa sai ta zauna anan"


Daɗi ne sosai ya kama mummy har tana jin daɗi ita a tunanin ta asmau ce ta ɗau shawarar ta ta fara aikin da ta saka ta


"to shike nan auta ai dama tun farko kai kaso hakan kana da mata har biyu amma ki ɗige a guda gudar ma mara quality" ɓata ransa yayi shi sam har yanzu be ga aibin badia ba da mummy kullum take cikin kushe ta



Ko ma dai menene yanzu ba lkcn maganar badia a bane yanzu ta ƴar iskar yarinyar can ake yi



Mummy shawara ta ci gaba da bashi akan yadda zai kula da asmau da kuma yadda asmaun zatai masa rana da kuma yadda zata kula shi fiye da badiar


Jinta kawai yake yi amma yanzu ba lkcn wannan bane yanzu burin sa kawai yaga asmau a part ɗinsa ya koya mata hankali



******************


Sai da na gama dinner tsab sannan na zuba aka raba aka kai wa kowa nashi sannan na ɗauki na mummy domin kai mata


Ina shiga part ɗin ta tana zaune tana kallo nai sallama na jiye mata na tashi zan fita kenan sai ta kira ni


"asmau idan kin gama abinda kike yi ki tattara kayanki a yau ki koma part ɗin mijin ki da zama zaman naki a BQ ya ƙare, su ma ragowar ƴan uwan nakin na gaya musu daga yau koya ya dinga girkin sa kin dena mijin ki yace ki koma"



Tsayawa nayi na saki baki kamar wata wawiya ina kallon ta me wannan yake nufi kenan in koma ɓangaren sabit wulaƙanci ke nan sunfari sunfari zan dinga kwasa gaskiya da sake bazan iya ba


"mummy amma me yasa zan koma kin............" bata bari na ƙarasa ba ta hau yi min faɗa kamar zata ari baki, wai dama ni shegen taurin kai gare ni,


Wata macen ce mijinta ya gayyace ta ta koma ɓangaren ta a matsayin matar sa kamar yadda kowacce mace take da matsayi amma ta ƙi kina nufin kin ta zama kenan a matsayin cook ai dama wataran dolr ne ya nemi ki koma ki karɓi girki



Faɗa ta dinga min daga nan kuma ta hau faɗa min wai yadda mallaki zuciyar sabit cikin ruwan sanyi, sannan da yadda zan dinga masa biyayya tare da yin duk abinda ya sani



Duk wani faɗan ta ya ƙare ne akan yadda zan farantawa ɗan ta sabit sam bata damu da halin da zan shiga ba ƙiri ƙiri na nuna mata bana ƙaunar komawa amma hakana sam be gamsar da ita ba itadai in koma in farantawa ɗanta





Miƙewa nayi jikina a sanyaye na kama hanyar fita, sai naji mummy tana kiran me aikin ta wai ta raka ni ta taya ni haɗa kayana sannan ta raka ni ɗakina

"ai ba a bar amarya ta tare ita kaɗai ba ba ɗan rakiya"


Wannan kalmar ta amarya tafi komai ƙona min rai lallai ma waya ga amarya


Tas matar nan tasa na haɗe kayana na kwashe su ta taimaka min kwasar su sai part ɗin sabit abin haushi ma yana zaune a falon yana kallo



Wani takaici ne ya ziyarce ni danaga mun shigo ya wani taso har da karɓar jakar hannuna na tare da yi mana welcome, ita kuma babar har wani washe baki take tana cewa


"ga amarya nan na kawo maka ita Allah ya bada zaman lfy ya kawo ƙazantar ɗaki" nuna mana ɗakin yayi


"ga ɗakin ta can sai ta shiga da kayan natan" tare muka shi da babar ni ko ƙala bance masa sai da taga na shiga na ajiye kayan nawa sannan tai min sai da safe ta fice


Kayana na fara gyarawa inda duk na jera su a kwabar da nagani a ɗakin sannan sai kayan kwalliyata waɗanda na jera su a kan dreesing mirrow



Sai dana ga na gama gyaran sannan na shiga toilet nai wanka na ɗauro alwala, sallah na gabatar ta ishsha sannan na kwanta



Ina cikin addua naji an buɗe ƙofar ɗakin, gabana ne ya yanke ya faɗi, ko da dai fitilar ɗakin a kashe take amma ai nasan sabit ne


Da sauri na miƙe na nemi wani zani da ke kusa da don in ɗaura, ban kai ga ɗauka ba naga hasken pitilar ɗakin ta kauraye ɗakin ya ɗau haske



Ga wata ƴar mitsitsiyar rigar bacci da ke jiki na, saurin lalubar zanin nayi sannan ɓata rai tare da ce masa

"me ya kawo ka"


"zuwa nayi in karɓi haƙƙin ta ko ta ƙarfi ko ta tsiya na ga alamar innai sanya sai a kai wa wani abanza a wofi" gaba na ne ya yanke ya faɗi amma sai na dake don kar yaga ma tsorata ya rena min wayo



Matsowa ya fara yi kusa dani gabana yana ƙara faɗuwa

"abinda kike burin kaiwa abdul ne nake son ruguza wa, tunda yanzu halak ɗina ne me zai hana in mori kayana tun kafin a kai wa wani banza, gwanda in karɓi kayana da hujja" fara matsawa nayi baya kashe fitilar yayi sai ɗakin ya ɗau duhu wanda hakan yasa na kasa gane a ina yake,



Haƙuri na fara bashi na don Allah ya ƙyale ni wallahi wasa nake masa, jinshi nayi kusa da ni wannan ya ƙara firgita ni


Ganin bashi da niyyar ƙyale ni yasa ni ma na fara kokawa da shi wallahi bazan bari yayi abinda yaga dama dani ba ai nia ina da ƙarfi



********************

Wayyo Allah sabit ya cuce ya raba ni da budurcina ba lallami ba daɗin baki ba komai sai azaba da nuna ƙarfi in short zan iya cewa raping ɗina ma yayi


Kuma abun takaici yana gamawa yayi wulli da ni sannan ya fice bayan rashin mutuncin da ɗiban albarka daya min, ina kwance nai rigingine ina ta kuka ba abinda nake ji sai tsabar raɗaɗi


Wayyo ni asmau wannan wace irin rayuwa ce mijina ya same ni budurwa sannan yai min wannan aika aikar amma sam a lamarin sa ba tausayawa wayyo sai yaushe wai zan samu me sona ne na gaskiya gashi abinda nake ta tattalin sa ina alfahari da shi yanzu babu kuma a wulaƙance ya ba wani daraja ko nuna mutunci ko wani abu gaskiya sabit ya gama cutata har abada








👩🏽‍🍳 *menu of d day* 👩🏽‍🍳


*fatan doya, meat balls and mixed fruit juice*

*fatan doya*

```ingredients```


-doya
-wake
-attaruhu
-albasa
-kifi
-salt
-sugar
-mai



*method*

1) ki zuba mai a tukunya da albasa idan yayi zafi sai ki zuba jajjagen ki na attaruhu da albasa

2) idan ya sayu sai ki zuba ruwa da maggi da salt daga nan sai ki bar shi ya tafasa idan ya tafasa sai ki wanke waken ki ki zuba sannan ki rufe ki barshi ya dahu


3) ki fere doyar ki sannan, sai kin tabbatar da waken ya dahu sannan sai ki zuba doyar ki zuba sugar ki ƙara albasa sannan ki dagargaza soyayyan kifi a ciki ki rufe har dahu idan ya ɗauko dahuwa a rage masa wuta


*Meat balls*

```ingredients```


-nama
-kwai
-garin bushashen burodi
-maggi
-albasa
-attaruhu
-mai


*method*

1) ki dafa naman ki da albasa maggi, tafarnuwa idan ya dahu sai ki sauke sannan sai ki daka


2) bayan ya daku sai ki fasa masa kwai ɗaya sannan sai ki zuba daddakekken attaruhu da albasa da maggi in yana buƙata ki zuba garin burodi ki ɗaure shi sannan sai ki fara dunƙule wa kamar ƙwallo


3) ki fasa ƙwai a bowl daban sannan ki kaɗa shi, ki ɗora mai a wuta idan yayi zafi sai a ɗauko ƙwallon naman nan a saka shi a cikin garin burodi a jujjuya sannan a tsoma shi a kwai daga nan sai kasko a soya idan yayi brown sai a sauke



*fruit salad*


```ingredients```

Seasonal fruits


*method*

1) a samu duk fruit ɗin da kike son amfani da shi amma wanda yake bozo ki wanke ki fere sannan a yanka shi sannan a markaɗa sai a tace a zuba sugar a saka a ƙanƙara a sha



👩🏽‍🍳 *BON APPETIT*👩🏽‍🍳


*ASMA'UN SABIT*
[10:54PM, 5/2/2018] ‪+234 806 399 9164‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 17🌹






Sai dana gama wanka na tsab na fito ɗakina na ɗauki jakata na fara haɗa kayana ina hawaye yau dole ne in barwa sabit gidan nan



Ban dan ko nawa ne kuɗi na a wajen mummy ba amma dole yau zan bar gidan nan ko da kuwa tace baza ta bani kuɗina ba na tafi inje gidan abincin hjy munnira ina mata aiki inna samu kuɗin in koma garin mu amma gaskiya wulaƙanci yayi yawa sosai na faɗa ina hawaye



Ƙarar buɗe ƙofar ɗakin nawa naji ko ban kalli ƙofar ba nasan cewar sabit ne don kuwa ƙamshi turaren sa kawai nake ji sam ban kalli inda yake ba na ci gaba da abinda nakeyi


"ke meye wannan kike yin haka nan"


"tafiya zan yi ai ko aure ma sai da ra'ayi ake zama to na bincika har ƙasan zuciyata banni da ra'ayin zama da kai bana ƙaunar ban taɓa son ka ba kamar yadda kake ikirarin hakan to meye dalilin da zai sa mu ci gaba da zama bayan bama ƙaunar juna"



Ina magana hawaye na zuba daga ido na sakin baki yayi yana kallona daga dukkan alamu be ɗauka zan masa haka ba


"da izinin wa zaki fita ko ita fannar da zakije wajen ta barin ki zama zatayi"


"ban ma tafi ba kenan in dai a waken anty fannah zan zauna, garin mu zan tafi aure tsakanina da kai babu shi ka bani takarda ta an gama show ɗin daga yanzu"


"daɗin abindai sakin a hannuna yake kuma bazan sake ki ba har sai lkcn da na ga dama, wai ke asmau me kike so ne meye bana baki saboda tsabar rashin godiyar Allah da rashin gode masa shine zaki tafi ko ki tafin mu gani in hakan ne zai sani ƙara miki matsayin"



Ficewa yayi daga ɗakin ni kuma naci gaba da haɗa kayana, sai da na gama haɗa komai na sannan na ɗauko jaka ta na fito


Ko kaɗan banji wani abu ba wai zqn bar gidan duk da dai bam san wace irin rayuwa zanyi a azoren ba amma ni a ganina gwanda in tafi da wannan cin zarafin da sabit yake min



A garƙame na tarar da ƙofar fita daga falon, an rufe da mukulli daga waje jijjiga ƙofar nq fara yi tare da dukan ta ko ta buɗe duk da dai nasan a banza nake amma kuma ance baka fidda rai da tsammani



Sai da na gaji da dukan ƙofar sannan na sulale ƙasa na zauna ina kuka na, alamar buɗe ƙofar naji nasan sabit ne zai shigo muciya na shiga kitchen na ɗauko da niyyar yana buɗewa in muƙa masa sannan in tsere


Anty fannah ce ta shigo ganina da muciya a hannu ya sata ɓata rai tare da ƙwacewa ta yar sannan ta ja hannuna zuwa ɗakin na

"me ye haka sai kace wata matar ƙauye, kamar wacce bata da ilimi ina karatun da nake koya miki kar dai kice ba ɗauka kike ba kawai zuba ta nake yi kamar ƴaƴan kanya"



Bayan ta sabit ne ya shigo, faɗa ta shiga min wai sabit ya kai mata ƙarata akan ina mishi rashin kunya, sakin baki nayi ina kallon mutumin nan wanda yake ta danne danne sa a wayar sa kamar baya wurin


"Wallahi anty ba haka bane ƙar........" ban ƙarasa ba naji ta toshe min baki


"kar ma ki ƙaryata mijinki da ido na na gani kin ɗauko muciya zaki doke masa kai, in banda shima sabit ɗin me haƙurine wane namijin ne zai yadda da irin wannan cin kashin"



Fashe mata nayi da kuka ina rants rantse na wanda sam kamar ma bata yadda ba don bata nuna alamar yadda ba


Sabit da ke gefe wanda tunda aka fara bece komai ba sai yanzu


"anty ni fa bana kawo ki bane don kiyi mata faɗa ba kawai so nake yi ki ja mata kunne akan abinda take yi be dace ba"


"yi haƙuri sabit zan mata faɗa tashi ka tafiyar ka uzurinka" miƙewa yayi tare da zira hannu a aljihu sa sannan ya fice, bin bayan shi nayi da harara



"au ko a gaban nawa bazaki bari yi masa rashin kunyar ba, haba asmau wallahi duk abinda kike yi Allah dai yana kallon ki" ƙara fashe mata nayi da kuka nan na hau labarta mata duk zaman da muke yi da shi bata katse ni ba sannan sam bata nuna alamar tausayawa ba ko wani abu


Sai da nagama tsab sannan tace min in share hawaye na, tas na goge fuskata ta, na nutsa sannan ta kalle ni tace min


"Asma'u shawara ɗaya zan baki ko ki ƙi ko ki sa amma ɗaya ce ba ƙari, duk wannan abun da kika ga sabit yana yi har yanzu be san meye so bane kawai dai yana bin sahun ƙyal ƙyal banza ne


In kina son sanin ainihin waye sabit me sabit yake so kamata yayi ki zauna ki karance shi ki karanci aban da yake so kafin ki fara judging ɗin sa


Har ga Allah ina sonki da sabit kuma duk wani abunda nasan zai ƙara ku
kusanta da shi shi nake miki amma na lura sam ke ba haka kike so ba kin fison tafiya ko" ta tambaya da alamar tambaya


Gyaɗa mata kai nayi alamar ni na fison tafiyar

"to shike nan duk yadda kike so hakan za ai miki yanzu abinda da so da ke shine ki kwantar da hankali sosai akan sabit duk abinda yake so kiyi masa sai a lkcn da ya saba da ke da duk wani abu naki sai ki tsiri rama abinda yai miki tas ki rama kar ki yadda kice zaki raga masa daga lkcn idan yaga abin ya mishi yawa sai kiga ya sake ki salin alin ko ya kika ce"



Tsayawa nayi ina tunani shin anya kuwa wannan mafita ce ko kuma wani sabon salon ƙara jawo sabit gare ni ne, ganin ban amsa ba ya sa ta miƙewa


"to bari in tafi tunda na baki shawara amma naga kamar bata miki ba"

Hannun ta na kamo sannan nace mata

"ba haka bane kawai dai ni bana son abinda zai sake haɗa ni ne da shi"


"to shike nan duk abinda yai miki ya tashi a banza kenan, ai in baki koyi rama abinda ɗa namiji yai miki ba daga farko to ko kin ƙara auren ma ƙila abinda zaki tarar kenan amma kin ga inkin saba ba abinda zai zame miki sabo"



Shiru nayi ina tunani to wai ramuwar dole ce na faɗa a zuciyata ni fa sam abinda ya danganci sabit nr bana so


"kinga in shawara ta bata yi ba na yi gaba sai kine mi me baki shawara nan gaba" ganin cewar in ta tafi shikenan a ina zan samu wanda zai haɗa ni da wanda yake son irin na


Don haka dai na riƙe mata hannu tare da cewa

"na haƙura amma wallahi saboda ke" shafamin gefen fuska ta tayi sannan tace


"yauwa ƴar albarka" zama tayi ta dinga bani saƙwanni ta yadda zan kama sabit jinta kawai nake yi amma abu guda banjin zan iya amma kasancewar bana son tace na ƙi jin maganar ta yasa kawai sai gyaɗa mata kai nake yi kamar ina ji ta gama zancen ta sannan tai min sallama ta fice nice har da rakata bakin ƙofa sannan mukai sallama


********************


Tun daga lckn na koma bana yi wa sabit musu duk abinda yake so ina mishi amma fa babu batun sakin jiki kadaran de kadahan



Rannan da safe yana zaune akan dining table yana break fast sai ga call, yadda naga naga ya ɓata fuskar sa sai na ɗauka ko wani wanda yake damun sa ne amma ga mamaki na sai naji yace


"only ya dubai" ban san me tace masa nadai ji ya amsa mata da



"only ki yi zamanki ku gama siyayyar ku a nitse ni sam ba a takure nake ba am taking really good care of myself don haka kar ki damu"


Shiru yayi inda ta ci gaba da mai masa da martani

"only ba komai ko wata ɗaya zaku ƙara is ok by mee, ni yanzu am really busy at d office inna fita tun safe karfe 06 : 00am bana dawowa sai 12 :00 na dare don haka am really busy gwanda kawai ki nutsu kiyi shopping ɗinki"


Wayaga zuƙi ta malle ina kitchen ina iya jiyo sa yana ta zankaɗawa matar sa gidoga 🤣 wai office tun safe sai yamma mutumin da sai kusan 09 :00am yake fita kuma duk inda 06 :00 tayi na yamma ya dawo amma shine yake shararowa matar sa wannan sharhi kai gaskiya wasu mazan ma sai a slow da lamarin su



Ina jin sa ya gama lallashin ta akan kar ta dawo ko ta gama shopping ɗin ta zauna ta huta, har da wani cewa ko kin gama ki zauna ki huta a can, wato ga banza ka samu ko to wallahi sai na san yadda na samu number badiar na saka ta ta dawo don in samu in huta



Sai da suka gama wayar sannan ya ajiye wayar ya ƙarasa cin abincin sa, ya na gama wa ya kirani inzo in kwashe kayan



Sama ya hau inda ni kuma na fara kwashe kayan, har na zo wuce ta ta kusa tv set ɗin falon sai na hango wayar tasan tana chargy da sauri na na je na ajiye kayan sannan na zo na ɗauka na rubutawa badiar text


```only nayi missing ɗinki dana ce miki ki zauna wallahi am joking pls ki yi sauri ki dawo as soon as possible i miss u a lot```


Nai mata sending ina shirin deleting naji foot steps ɗin sa don haka sai kawai na kashe wayar na mayar na ajiye rigima ba uban wanda ta kashe barin ma rigimata da sabit mun saba




Yana saukowa ya ɗauki wayar ya fice, farin ciki ne ya rufe nk Allah dai yasa message ɗin ya shiga


Be daɗe da fita ba sai gashi ya dawo a fusace daga ganin sa nai kitchen a gujr na ɗauko muciya, gadan gadan ya nufo ni fuskar nan tasa a murtike kamar an masa mutuwa


"wallahi idan ka ƙaraso kusa da ni sai na muƙa maka ita" tsayawa yayi ya kallo muciyar da ke hannun sannan sai ya ja burki


"uban wa yace ki taɓa min wayata balle har ki min text"


"meye text" na tamyaba cike da renin sense

"baki ma san meye text ba, da kika ɗauka kikai wa badia text wai ina missing ɗin ta ta dawo zaki ce baki san text ba"


"ni tunda nake ban taɓa riƙe waya ba tayaya za a yi in san yadda ake yin text" na kuma bashi amsa


"to ni da waye a gidan da har akai wa badia text amma baki gani ba bayan anan na ajiye wayar na hau sama kuma lkcn da na hau sama akai mata text ɗin"


"oho ni dai ban sani ba don ba taɓa riƙe wayar nayi ba balle in iya wani abu wai shi text" duk wannan maganar da muke yi muciyata na ɗage daya matso kusa da ni in muƙa masa


Kallo na ya tsaya yana yi tabbas da badan muciyar nan ba da tuni ya fara muguntar tasa, amma babu halin hakan tunda yanzu am armed 🤺



Ƙwafa yayi sannan yace

"zaki gane kuren ki" a zuciyara nace oho dai nasan ta inda zaka rama kuma am already immune to it, na riga na saba yanzu bana jin komai wani lkcn ma sai

Please Login or Register in order to submit comment